Kenza eBookz

Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy - Chapter 27

Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy - Chapter 27

Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 27: Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 27. "Hello"

4,499 words

"Hello"

"Assalamu Alaikum"

Ta amsa, sai kuma ta yi shiru.

"Gimbiyar tawa ta shirya ne?"

"Oh oh oh Fatima?"

"Yeah"

"Eh ta shirya"

"Toh a fito min da ita, ina waje nesa da ku sai kin saka ido sosai zaki iya ganina gida na uku kamin na ku, bana son na zo kusa ne ban san ko Vito yana ciki ba kar yace zai miki fada ko ya dake ki, kin san ni kuwa a yanzu ba zan saka ido ko yatsa wani ya nuna miki ba"

Ta yi murmushi mai sauki tana jindadi tare da sauke numfashin da ya ji shi har cikin zuciyarsa. Ya zauna a motar na tsawon mintuna goma sannan ya hango ta ta fito sanye da bakar abaya ta rolling dankwalin abayar ta rufe kanta kai kace musulma ce, ta yi kwalliya sosai har da jan baki, tun daga nesa Aliyu yake kallon fuskarta tafiyarta da yadda bakar abayar ta yi mata shegen kyau ko kyaltawa baya yi gaba daya ta dauke hankalinsa ko Fatima da ya zo domin ita be gani ba sai Emily, da ta iso gurin motar sai ya sauke gilashin ya jingina da kujerar motar yana kallonta kamar wanda ya zauce.

"Sannu"

Ta fada ta muryar mai dadi idonta suna jan hankalinsa ga wani tsadadden murmushi a fuskarta. Yayi murmushi ya sauke kansa kasa.

"Emily ashe kina da kyau, na gode da kika karramani, wannan shigar ta dace da kyau, kin yi ma abayar kyau sosai"

Ta yi murmushi ita kanta ta san ta yi kyau.

"Wata kila da zaki rika suturta jikinki haka da manyan kaya masu sauko miki su rufe tsiraicinki da zan yi ta kula ina fahimtar kyaunki ne, kuma zan fi sake jiki na jidadi, kin san ban taba kula da kina da kyau ba sai yanzu?"

"Saboda na saka abaya?"

Ya girgiza yana kallonta da murmushi.

"Aa saboda kin rufe jiki, kin dace da sunan Aisha, daga yau ba zan sake kiranki da Emily ba, sai Aisha"

A bakin gaskiyarsa yake fada mata tufafin yayi mata kyau domin yayi mata kyau babu karya, sai dai yana karfafa mata guiwa ne saboda ya dawo mata da sha'awar saka tufafin da musulunci ya yarda mace ta saka, so yake ta ji wannan alfarma yaja hankali da abun da yake gani da jin shi ya dace da ita. Fatima ta daga masa hannu tana masa waving domin ta lura be ganta ba, bayan kuma Emily ta fada mata ita ya zo dauka za su tafi yawo.

Ku yi hakuri dan ni dan Allah Wallahi uzuri ne yake rike ni. [6/17, 9:33 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_writing

🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*

*© Khadeeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen... ✍️

Page 3️⃣6️⃣

"Hey Fatima ya kike?"

Ya fada yana kallonta sai ta amsa cike da far'a da zumudi.

"Fine"

Aliyu ya kalli Emily.

"Ni fa ba ke na zo dauka ba, Fatima kawai nace zan dauka"

"Ni ma ka ji nace ka tafi da ni ne?"

"Ina karantar abun da yake cikin zuciyarki a fuskarki da idonki shiyasa kika yi anko da ni, ni bakin voile ke bakin abaya"

"Saboda an rubuta a fuskata ina son ka tafi da ni?"

"Bana bukatar a rubuta, saboda ina iya karanta rubutun da alkalin zuciyarki ya ayyana ko babu tawada"

Ta bude baki zata yi magana ya tare numfashinta.

"Ki cigaba da musawa daman ai kin saba"

Sai ta yi murmushi ta sauke kanta kasa, shi ma murmushin yayi ya mika hannu ya bude gaban motar, Fatima bata jira yace ta shiga ba ta shige front seat. Emily ta duba wayarta ganin kiran Vito na shigowa wayarta ya daga mata hankali sai ta yi hanzarin kallon Aliyu.

"Ku yi hanzari ku tafi"

"Ke fa?"

Ta girgiza kai ta rufe motar.

"Ba zan je ba"

Aliyu ya kalli wayar dake hannunta da yadda hankalinta ya tashi a take sai ya kashe motar.

"Dan Allah ka tafi kuma karka dawo da ita sai idan na kiraka"

"Idan baki ra'ayin tafiya yawon da ni ba zan cilasta miki ba, amman ke ki fara tafiya gidan tukuna"

"Aa sai ka wuce hankali zai fi kwanciya idan ka tafi"

"I'm your boss ni zan baki umarni ba ke zaki ba ni ba"

Ta kalli titin ta sake kallonsa cikin tashin hankalin da take boyewa.

"Amman kace baka son bacin raina, dan Allah ka tafi"

Tana fadar hakan ya murzawa motar key cikin wani yanayi na am masa dole ya hau titi, bata bar gurin ba sai da ta daina hango su, sannan ta koma cikin gidan da sauri, ta shiga falon cikin tsoro sannan ta haura sama zuwa dakinta wayarta ta fara kashewa ta boyewa tana dagowa sai ga Vito ya shigo fuska kamar bakin maciji, wani irin cin burki yayi ya tsaya kallonta daga sama zuwa kasa, ganinta da Abaya ya ninka masa bacin rai.

"Miye wannan a jikinki?"

Ta yi shiru bata amsa masa ba. Sai yayi cikinta mayafin abayar ya fara fisgewa ya jefar ya rike wuyanta da karfi.

"Ina Fatima take? Ina kika je? Meyasa kika saka wannan kayan?"

Ta ture shi da karfi ta fara magana cikin tsawa.

"Saboda ina ra'ayin sakawa, na gaji da abun da kake min Vito komai na rayuwar duniya sai ka zaba min zan yi? Tufafi sai wanda kake so? Bana mu'alama da kowa sai wanda ka yarda da shi? Yar aiki mai gadi duk sai wanda ka zaba?"

"No ba zaba miki tufafi ba, ki saka duk wanda kika so, amman ban da wannan! Ke yanzu ba abun kunya ba ne a gurinki ki yi koyi da musulmai? Ina hankalinki ya tafi? Me kike son zama Emily? Zan amince miki ki yi komai zan baki gata amman ban da canja addini Emily ba zan taba yarda da wannan ba"

"Bana son zama da kai, ina son na bar gidan nan na yi rayuwata ni kadai"

"Baki da wannan ikon, wane yake hure miki kunne ko? Ina kika tafi? Ina Fatima?"

"Ba ruwanka da wannan"

Ta sake riko wuyanta.

"Miye bana miki Emily? Wane irin gata ne ban baki ba? Wane irin jira ne ban yi ba akanki? A duk lokacin da na miki maganar aure hankalinki wani gurin yake tafiya, gaba daya ba nine a gabanki, na gaji yanzu, waya zo gurinki ko kuma gurin wa kika tafi?"

Ta ki ta yi magana, a take ya wulgar da ita kasa da dukannin karfinsa, sai kuma ya bita ta kama abayar jikinta daga saman gurin v shafe dake gaban rigar ya yaga daga sama har kasa.

"Ba zaki sake saka wannan tufafin ba, ba zaki sake kula kowa ba, you already know yadda raina yake baci idan kika kula wani miyasa kika yi? Me yasa kika kasa karbata har yanzu?"

Ta dauke ta da mari, ya kai mata duka a fuska kamin ya mike tsaye ya cire belt din jikinsa ya fara dukanta tana ihu, and he keep questioning her. Sai da yayi mata duka sosai irin dukan da be taba yi mata ba sannan ya jefar da belt din ya zauna kan kujera tana kallon yadda take murza jikinta tana kuka, a yanzu kuma sai ya ji ransa ya fi baci akan duka da yayi mata fiye da laifin da ta aikata. Bedsheet din kan gadon ya yaye ya lulluba mata a jikinta da babu komai sai underwears, ya zauna a gurin ya rike kansa.

"I'm sorry"

"Ka kashe ni kawai, na gaji"

"Ba zan kashe ki ba, amman zan kashe mutumen da yake ziga ki, na san ba zai wuce wannan dan iskan yaron na gurin aikinku, ba mamaki shi ya turo NDELA har gida na"

Emily na jin haka ta yi karfin halin tashi zaune.

"ba shi ba ne, karka dauki alhakinsa, mutumen da nake aiki a tare da shi shi ne mutumen da ya taimaki ni lokacin da na kusa rasa rayuwata da cikin Fatima, shi ne mutumen da nake ta ajiyar agogonsa, he has nothing to do with this, karka cutar da shi Vito, idan wani abu ya same shi ba zan taba yafe maka ba, kuma ba zan taba yafewa kaina ba"

Ta karasa daker tana kuka, ya kalleta ya sake kallonta ya sake kallonta a karo na uku, ya rasa me yasa ta kasa kaunarsa ta kasa bashi hadin kan da yake bukata, bayan duk abun da yayi mata, bayan duk tsawon shekarun nan da suka dauka tare bayan dubun kyautatawa. Mikewa yayi tsaye ya fice daga dakin ya dawo falo ya zauna ya saka hannunsa aljihu ya ciro wani karamin kwalba mai kamar akwati ta zuba wata farar hoda a hannunsa ta shaka da karfi ya rufe ido yana juya kai na dan lokaci, sannan ya tashi ya fice daga gidan gaba daya.

ALIYU POV.

Da farko yawo ya so yayi da Fatima sosai kuma yayi mata siyayya amman halin da ya bar Emily ya tsaya masa a zuciya, hakan ya saka shi canja kudirinsa na kai Fatima park da guraren shakatawa ya tafi da ita super market kawai ya siya mata kayan wasa da na ciye ciye, tana zabar abun da take so yana tambayarta sallah nawa ake a wuni, me ake karantawa da wane lokaci ake yi, kuma ita tana yi ta bashi amsa daidai ban da yin sallah, tana yi sallah ne a duk lokacin da take sha'awar yin sallah, sai da suka shiga mota ya kama hannunta yana murmushi yace.

"Yanzu ki min alkawari kullum zaki yi kowace sallah babu fashi, kuma komai kike zaki aje ki yi sallah"

"Wata rana ina gajiya fa"

"Eh ko kin gaji ki yi a haka, ai ba zaki so idan kin mutu a kona ki ba ko?"

"Eh"

"Good kina son idan kin mutum na musance a aljanna ko? Guri mai kyau da ni'ima kuma komai ake so za a samu a ciki"

"Har da kayan wasa"

"Sosai da kayan dadi kala kala, amman sai idan mutum yana yin sallah, kin ga ina son ki ba zan so ki shiga wuta ba"

"Eh ba zan shiga ba wuta ba, Momy ce zata shiga wuta ita ce bata sallah, kuma ita ce kafira"

Aliyu yayi murmushi mai sauti.

"Toh a duk lokacin da kika yi sallah ki rika rokon Allah yasa Momy ta dawo hanyar musulunci, ai ba zaki so a kone ta ba ko?"

"Eh amman wata rana ina son a kone ta sai a cireta"

"Aa babu kyau Momyki tana sonki ita ma ba zata so ki kone a wuta ba, duk wanda kake so ba zaka so ya shiga wuta ba"

"Sai wanda baka so? Toh Vito ina son ya kone a wuta yayi baki ya soyu"

Nan ma Aliyu dariya yayi

"Aa shi ma ki masa addu'a Allah ya shirya shi ya dawo musulunci"

Ta lake kafada ta turo baki gaba.

"No bana son shi ba zan yi ba"

"Zan rika biyanki idan kina musu addu'a"

"Noooooo bana son shi i hate him ni bana son shi"

"Da alama kina da kafiya Fatima ki daina ba shi da kyau kinji don't be a stubborn girl"

Ta makale kafada ta juya masa, murmushi kawai yayi ya daga wayarsa ya kira number Emily sai ya ji ta a rufe hakan ya dan kara masa damuwa.

"Fatima da kuka fito Vito na cikin gidan?"

"Aa Chidimma ce kawai"

Ya sake gwada kiran still switch off. A take hankalinsa ya tashi, gashi tace kar ya zo har sai ta kira be san me zai yi ba a yanzu kuma be san a wane hali take ciki ba. Sai da ya fara tuka motar yayi nisa yana ta sake sake kamin ya kama hanyar gidan Tasmia ya faka harabar sannan ya fita ya taka zuwa kofar shiga gurinta ya kwankwasa, shiru ya sake knocking nan ma shiru, wayarsa ya ciro ya shiga WhatsApp ya lalubo chat dinsa da Tasmia ya duba number ta yayi coping ya saka a dial ya kirata, ringing uku ta yi kamin ta yi na hudu ta yi picking.

"Hello"

Sai yayi mata sallama kamar yadda ya saba yi na kowa, ta amsa masa ta gaishe shi, bayan ya amsa ya dora mata da dalilin kiransa.

"Am... Alfarma nake nema"

Ta yi jimmmmm kamin ta amsa.

"Fadi komai kake so Aliyu, ai ban kai matsayin da zaka nemi alfarma ba, sai dai ka yi min umarni, kuma dole na na bi ko da kuwa wuta ka ce na fada"

Ta fada with excitement.

"Interesting... Okay.. Anyway na zo gidanki ban same ki ba"

"Allah yasa ba laifi aka ce na yi ba ba"

"No ina son kije gidan Emily ne ki duba min ita, ina tare da Fatima a yanzu, bana son na je gidan har sai na yi magana da ita, kuma jikina yana ba ni ba lafiya ba"

A take yanayin muryarta ya sauya saukin kiran da take ya ragu.

"Ni fa bana son jefa kai a matsala, kana son shiga sha'anin Emily Aliyu kamar ka manta waye kai, musulmi kuma mai iyal..."

Bata karasa ba ya yake wayar ya koma motarsa sai ga kiranta ya biyo, when he pick ya fada mata.

"Kar kiran da na yi miki ya baki damar fada min magana, kuma idan kika dame ni zan bata miki rai ne"

"Ka yi hakuri, ina camp ne zaka iya zuwa ka dauke ni, sai mu je na dubata"

"Ba kai ki zan yi ba, ke zaki je ki dubata, duk abun da ake ciki sai ki fada min"

Yana kaiwa nan ya kashe kansa wayar.

"Matarka ce? Daman kana da mata?"

Fatima ta tambaya tana shan ice cream.

"Aa ba matata ba ce"

"Toh kana son mata"

Ya kalleta kawai yayi murmushi.

"Kana son Momyna?"

Ya sake yin murmushi.

"Fatima zan tafi dake gidana na zauna a can mu huta kamin Momynki ta kira sai na maida ke"

"Tohm"

Taja motar suka kama hanya, tana ta masa surutu har suka isa gidan, a lokacin da ta fito motar ta kalli gidan ta ga babba ne sai ta ce.

"Da zaka yarda sai mu dawo nan gidan tare da Momy da Chidimma, mu bar gidan Vito, ba za mu maka barna ba"

Shi dai be ce mata komai ba ya bude motar ya dauko wasu daga cikin kayan da suka siyo ya wuce cikin gidan tana biye shi tana ta masa surutunta da fluent English dinta pure one domin bata iya hausa ba, duk wata magana da ake da ita da halshen turanci ne, hausa kadan ta iya saboda Emily bata damu ta koya mata ba, kuma bata taso a gurin da ake hausar sosai ba, ba kamar Emily ba.

TASMIA POV.

Da tufafinta na bautar kasa ta tafi gidan Emily fuskarta sanye da mask, bakin gate din aka ajeta, ta sallami mai okada sannan ta buga gate din mai gadin ya leko, sai ta masa karyar Emily ce ta kira ta da kanta tace tana son ganinta.

"Idan ka shiga ka fada mata Tasmia tana waje"

Mai gadin ya kira wayar Emily ga ji ta a kashe, sai ya shiga ciki ya kwankwansa Chidimma ta bude ya tambaya ko Emily ta san da zuwan wata kawarta, sai ta amsa masa da eh alhali bata da tabbaci. Mai gadin ya koma ya budewa Tasmia ta shigo, da yaren turanci ta tambaye Emily Chidimma ta nuna mata upstairs, har ta nufi saman sai kuma ta juyo ta saka tambayar Chidimma ko Vito yana nan Chidimma tace mata baya gidan sai ta haura sama da sauri jikinta na rawa, na dan tana son faranta ran Aliyu ba da kuma yi ma kanta yaki, da babu abin da zai saka ta risking rayuwarta a gidan Emily, kiranta kawai da Aliyu yayi a karan kansa ya faranta mata rai balle kuma har ya nemi alfarma a gurinta, a ganinta hakan ma wani matakin nasara ne, domin da sannu bako ke zama dan gida.

Tsabar rikicewa ma dakin Fatima ta fara shiga, ta fito da sauri ta tura dayar kofar ta leka sannan ta shiga. Sautin kukan Emily ta fara ji kamin ta hango ta kwance a kasa, ta karasa da sauri.

"Lafiya me ya same ki?"

Ganin Tasmia ya saka Emily ta dan ji sanyi sanyi har ta dago ta jingina jikin Tasmia tana duka tana fada mata Vito ne ya duke ta. Tasmia ta kalli kofa sannan ta rage murya.

"Me kika masa?"

Emily ta kasa magana sai kuka take. Tasmia ta kalli yadda fuskarta ta yi ja wani gefen ya kumbura ga kuma shatin belt a saman kafadunta, kana gani ka san dukanta aka yi, kuma ko bata fada mata ba, ta sani ba zai wuce ace saboda Aliyu ba, shiyasa shi ma ya damu ya san halin da take ciki.

"Wata kila ya gaji da halinki ne Emily ta ina zaki zauna kina wahalar da shi, bayan duk hallacin da yayi min? Ko da yake ban san me ya faru ba, amman kina cin amanar mutumen nan, yana sonki kin kasa fahimta"

Emily ta takaita kukan da take ta share hawayenta.

"Ya aka yi kika samu shigowa nan?"

"Karya na yi ma mai gadi cewar kin san da zuwa, na ce ya zo ya tambaye ki sai yace na shigo kin san da zuwa"

"Be shigo nan ba, ban yi magana da shi ba"

Mamaki ya cika fuskar Tasmia.

"Toh taya ya bar ni na shigo, ni daman dai na zo ne kawai na duba ki"

Emily ta yi shiru alamar tunanin sannan tace.

"Tashi ki tafi kar Vito ya tarar da ke a nan, ransa a bace yake"

Emily na rufe baki Tasmia ta zabura tsaye ko sau anjima bata cewa Emily ba ta fice gidan fuuuu kamar walkiya. Hankali be kwanta ba sai da ta isa gida, sai kuwa aka yi a daidai tana shiga gidan kiran Aliyu na shigowa wayarta domin hankalinsa ya tafi gurin son sanin halin da Emily take ciki.

"Hello"

Ta amsa da far'arta kamar gaske.

"Assalamu Alaikum"

"Wa'alaikumussalam"

Ta yi shiru tana jiran sai ya tambaye ta.

"Lafiya take?"

"Lafiya Kalau take na same ta ma girki take yi"

"Vito na gidan ko da kika je?"

"A A Baya gidan mai aikinta ce kawai shiyasa ban tsaya komai na ina ganin lafiyarta sai na fito, kar ya zo ya tarar da ni a samu matsala, ba dan kai ba a yanzu da babu abun da zai kai ni gidan Emily ko dan gudun fitina"

"Me yasa wayarta take a kashe"

"Toh ban sani ba, wata kila tana gudun a kira ne yana nan, amman lafiyarta kalau na same ta ma ta sha ado abunta"

Idan be ce mata thank you ba ai be kyauta ba ko ba komai ta cancanci godiya domin hankalinsa zai kwnata a yanzu sanin cewar Emily na cikin aminci.

"Na gode"

"Always Aliyu, ka aje duk wani tunani da kake, ka dauke ni a matsayin kanwarka, bayan shi babu wani ba"

Ba tare da ya sake furta komai ba ya kashe wayar. [6/20, 7:25 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08

*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*

*© Khadeeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen... ✍️

FOLLOW ME ON 👇🏻

FACEBOOK https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914

TIKTOK https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1

INSTAGRAM https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0

CHANNEL https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

KHADEEJA CANDY STORE https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08

Page 3️⃣7️⃣

ALIYU POV.

Ya dan ji wani iri shi dai aganinsa babu abun burgewa namiji ya tare da matar da a daura musu aure ba a gida daya da sunan budurwarsa ko wadda zai aura, hakan sai ya saka ya ji addinin musulunci ya kara burge shi domin addinin Musulunci be yarda da wannan ba, a ta dayan bangaren kuma yana tambayar kansa anyaba shi da zunubi na aje mata ya a nan a can kuma ya bata damar shakatawa da yi yadda take so da mutumen da ba muharraminta ba? Ya kalli Fatima dake ta ciye ciyen kayan dadinta hankali kwance.

"Fatima mu tafi gida haka nan?"

A take ta bata fuska.

"No bana so mu tafi yanzu"

Ya mike tsaye ya nufi Kitchen, ruwa ya dauko ya sha ya dawo falon ya zauna.

"Kai ma baka da kowa kamar Momy na?"

Ya dubeta.

"Waya ce miki bata da kowa?"

"Bata da kowa sai ni kadai"

"Sai Vito"

Ta girgiza masa kai.

"Aa i hate him"

"Why do you hate him? Me kake miki ne?"

"Baya dariya, kuma yana da fada yana duka, kuma ba ya bari kowa ya zo gurinmu"

"Toh mamanki tana da ni yanzu"

"Yeehhhhhh"

Sai yayi murmushi ya shafa kanta, sai ya ji duk ta burge shi.

"Mun zama mu uku ko?"

"Yes, zaka zama Babana? Ni kadai ce ba ni da Baba a duniyar nan kowa yana da Baba amman kace zaka maida sunana Fatima Aliyu amman baka yi ba, har yanxu ana kirana Fatima Aisha Emily...."

"Ke ma kina da mahaifi Fatima, kuma na san da zai ganki zai kaunace ki sosai zaki ji dadi, da ace mahaifiyarki zata aje abun da ke zuciyarta ta dubi maslaharki da kin yi farinciki sosai, kina da uba sunanshi Turhan"

Ta dafa shi, hakan ya farfado da shi daga guntun tunanin da yake.

"Ka ji"

Ya lumshe ya bude sannan ya daga taya matsa da ita saman jikinsa ya rumgume ta, ba dan ya ji abun da take tambayarsa ba sai dan tausayinta da ya kama shi. Kiran Emily be shigo wayarsa ba sai kusan Isha'i a lokacin da yayi alwala yana warwarar hannun rigarsa Fatima ta shigo masa da wayar da ya bari a falo, har dakin da yake ta mika masa. Ya karba ya kara a kunne, for the first time sai ya ji nauyi fara yi mata sallama.

"Salam alaikum"

Ta masa sallamar sai yayi murmushi ba tare da ya amsa ba ya ce.

"Yau dai kina da nuna min hallayarki na kwarai ashe kin iya sallama"

"Na iya mana, ni da na zauna da musulmai kuma Hausawa"

"Kina lafiya Emily?"

Ya tambaya, sai ta lumshe ido hawaye na sauko mata, ta girgiza kai kamar yana gabanta tana jin kamar ta fada masa ba lafiya ba, amman tana gudun abun da zai je ya dawo.

"Anyways na kira wayarki a kashe, saboda hankali na be kwanta ba da yanayin da na barki, kuma da na ji wayar kashe na damu sai na saka Tasmia ta bincika min ke"

Da ya kai iya nan sai ya yanke maganar saboda yana son ya gano idan Tasmia gaskiya ta fada masa ko akasin haka. Emily ta hade kukanta ba tare data bude ido ba ta ce.

"Me tace maka?"

"Me kika ce tace min?"

"Ban fada mata komai ba, bata ma min maganarka ba"

"Okay, ta fada min ta same ki kin yi ado kina yi ma Vito girki, nace toh ina nan na damu ita kuma tana can tana girki ma wanda ba mijinta ba, Allah yasa dai kar na samu zunubi"

Ta cige baki hawaye na sauko mata kana ta bude ta sauke numfashi a hankali.

"Ado tun wanda ka tarar na yi ne, ban sake wani ado ba, ina Fatima tana tare da kai"

Ya kalli Fatima dake cin apple.

"Yeah, amman Aisha na tambaye ki mana"

"Uhmmm, ku haka addininku ya yardar ku zauna da mutane musamman namiji kuna tarayya ko daba muharraminku ba ne...? Mu a gurinmu hakan ba abu ne mai kyau ba"

"Ban taba tarayya da Vito ba, wani abu be taba shiga tsakaninmu ba, a tsawon zaman da muka yi, yana jiran sai na aminta da soyayyarsa ne, ni kuma zuciyarta ta kasa fahimtarsa, wannan abun yana wahalar da rayuwata yana jefani a matsala, ni ban taba mu'amala da kowa ba sai Khaleepa da Turhan, shi ma Turhan ya fada min kan kuskure ne, kuma bakar rana ta biyu a gurinsa bayan ranar da aka daura mana aure, yana daga cikin dalilin da ya saka nake son gina rayuwata ni kadai ina son na zama mai ikon kaina"

Jin cewar bata taba zina ba ya burge shi, haka kuma jin cewa Turhan ya kira ranar da ya aure da bakar rana a gurinsa ya saka shi kara dora ayar tambaya akan zamantakewar aurensu.

"Fahimta, I'm sorry for misunderstanding you"

"Dan Allah ka bar Fatima ta kwana a gurinka, gobe sai a kawota"

"Okay"

Ta bukataci hakan ne gudun kar ya zo kawo Fatima ya hadu da Vito ko kuma ya ga dukan da Vito yayi mata yace zai dauki mataki ya jefa kansa a matsala. Falo Fatima ta koma tana kallo, shi kuma ya tsaya a dakin yayi sallah, be dago daga sujudarsa ta karshe ba sai da yayi ma Emily addu'a, bayan ya gama ya sauko falon ya umarce tayi alwala ta yi sallah, ba musu ta tashi zuwa jnda ta yi alwalar magariba ta yi ta dawo falon ta dauki hijab din Kameela daya dauko mata a dazun ta saka ta fara sallah, shi kuma ya shiga Kitchen ya fara gyara tattasai da attarugu da albarba ya kunna gas ya dora nama akai, ya fara yanka vegetables, sai ga Fatima ta shigo Kitchen tana tambayar me yake yi.

"Jallof zan girka kina ci?"

"Ka iya girki?"

"Sosai ma"

Ita ta yi ta taya shi hira yana girkin, duk abun da ya zuba sai ya daga ta ta gani da ya gaji sai ya goyata a bayansa ta leko kanta ta saman wuyansa tana kallon yadda yake girki, idan yayi abun da bata saba gani ba sai tace masa ba a haka ake yi ba, shi dai dariya kawai yake ya cigaba, da ya gama hada komai sai ya koma tare da ita falon suka zauna sai da ya nuna sannan ya koma ya zubo musu a plate daya shi da ita.

"Kai kadai zaka ci?"

"Aa ni da ke"

"A plate daya"

"eh ko baki cin abinci a plate daya da wani?"

Ta yi dariyar jindadi

"A gida raba mana ake kowa plate dinsa dabam, amman ina so"

Ya zauna ya sake komawa ya dauko ruwa da lemu, sannan yace ta zo su ci, madadin ta zauna a gefensa ko gabansa sai ta tsallake abinci ta zauna a kan ciyarsa, yana ganin haka sai ya aje Spoon daya ya dauki dayan yana ciyar da ita da shi shi ma sai ya ci, ko loma nawa yayi sai ta kirga tun be hankara ba har ya fara dariya, ita da shi suka ci abinci cikin nishadi, har wayarsa ya dauko yayi mata hoto yayi mata video, kusan a lokacin ne ya ji yana matukar kaunar samun nasa yaran, Fatima kuma ta yi enjoying moment din tana jinsa kamar mahaifinta.

Bayan sun gama ya bude quran app din wayarsa ya tana karanta dan abun da ta iya yana mata gyara, har bachi ya dauke ta, daukar ta yayi ya haura da ita sama ya kwantar da ita kan gadonsa ya lullubeta ya zauna gafen gadon ya karanta mata addu'a ya tofa mata sai ta bude ido ta kalleshi.

"Meyasa kake watsa min yawu"

"Addu'a ce ta tsari idan aka karanta ma yara ko suka karanta babu abun da zai same su har safe, Momy ki bata miki idan zaki kwanga bachi?"

"Aa"

"Toh ki koya ki rika yi ma kanki kin ji?"

Readers Also Read