Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy - Chapter 36
Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 36: Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 36. Ya bude ido yana jin jikinsa yayi masa nauyi…
4,462 words
Ya bude ido yana jin jikinsa yayi masa nauyi sosai kamar ba na shi ba, kuma yayi matsa tsami, amman karfin hali irin na namiji da juriya yana hada ido da mahaifiyarsa sai ya saka matar murmushi. Yayi yunkurin bude baki yayi mata magana sai ya ji bakin yayi masa nauyi kansa kuma ya fara ciwo daman shi ma kan na shi yayi masa nauyi. Ummi ta yi ma wata yar'uwarta magana ta fita ta kira likita ya shigo da sauri ya duba shi ya cire masa ruwan dake jikinsa ya taimaka masa ya tashi zaune aka kawo roba ya wanka bakinsa Ummi ta hada masa tea ya sha aka ba shi magani ya sha. Ummi na kusa da shi zaune sai matsar kwalla take tana kallonsa.
"Ummi da sauki fa kina gani to kuka na me kuma?"
Cikin kuka Ummi ta ce.
"Allah kadai ya san zafin da kake ji amman ba zaka nuna ba dan kar na damu, kalli yadda suka maka rauni a kafa, jiki ko'ina duka"
"Saukin abun ma babu karaya, amman ko suwa gaskiya kashe ka suka so yi"
"Ni ban san ko suwaye ba, ni dai ina tsaye ina waya da Ummi kawai na ji duka ta ko'ina da itace da hannu, Allah yasa inda na tsaya kusa da mutane ne kuma ana hada hadar shiga Sallah Magariba domin an yi kira ne lokacin sai mutane suka hankalta da wuri suka kawo dauki, mutanen suka gudu, na ji dai ana ta Innalillahi ni ma kuma ina ta tun da suka hau ni da dukan, a nan jama'a suka taimaka aka dauke ni aka dora ni a babur din wani aka yo asibiti da ni, suka ce ba za su karba ba, saboda kaina da kafata suna zubar da jini lokacin ga hannayenta sun duka bana ma iya daga su, to daga nan dai hankalina ya bace ban san ya aka yi ba sai yanzu da na farko nan"
Ummi ta ce.
"Muna wayar nan da kai na ji kana ambaton innalillahi sai ina jin karar duka na san ba lafiya ba, ko dai ita yarinyar ko kuma Kameela tun da su ma ba hankali da su ba ko kuma shi Turhan din cikinsu akwai wanda ya saka aka yi maka haka, kiran yankewa yayi na fito na shiga bangaren Daddynka na fada mishi da ya gwada kira sai ta shiga, Allah yasa yana gida a lokacin shi yayi magana da su ya fadi asibitin da za a kaika kuma ya kira CP ya sanar masa maka, yanzu haka kofar nan police ne awaje ba abarin kowa ya shigo, sun ce sai ka farka za su shigo su dauki bayanai"
"Ummi ya aka yi kika zo?"
"A dare nan ban iya kwana a Abuja ba ai, mota muka biyo da rakiyar jami'an soji sha biyu na dare na sauka garin nan, kowaye ya maka wannan abun ba zai tsira ba In Shaa Allahu"
"Allah y sauwake, idan kun dan gana sai a bar shi ya samu hutawa saboda ya ji ciwo a kai yawan magana zai iya haifar masa da matsala"
Likitan ya fada sannan ya fice.
"Emilyn ma tun dazun take kira ta zo nan ba su barta ta shigo ba"
Aliyu ya kalli Ummi.
"Taya aka yi ta sani?"
"Ban sani ba, amman dazun wayar tana hannun mubarak ya fada min ta kira ya fada mata kana asibiti"
Ummi na rufe baki sai ga kiran Emily ya shigowa a wayar Aliyu dake hannun Ummi.
"Gata nan ta sake kira"
"Ummi abarta ta shigo mana"
"Kana ta ciwo wa yake ta wani Emily? Waya sani ko ita ta saka aka yi maka haka saboda yarinyarta"
"Ba zata yi haka ba Wallahi na san ranta ya bace amman ba zata saka yi min haka ba, ita ma fa tana cikin matsala, dan Allah Ummi ki barta ta shigo kuma dan Allah Ummi karki nuna mata wani abu ko da ta zo dan ta yi fada da ni ne, Wallahi ta fi ni gaskiya kuma ni ne ban kyauta mata ba, sannan kuma yarinyar ancutar da ita an kuntata mata har tana kallon musulmai a matsayin azzalumai, tana son musulunci na fada miki kafira ce ta musulunta wahala ya saka ta koma ruwa, wannan abun nake son na kankare a ranta kuma na dawo da ita tafarki na kwarai, labarin da na baki jiya ko rabi ban fada miki ba na wahalar da sha a rayuwa, ni kadai ne mutumen da ta yarda da shi, dan Allah karki nuna mata wani abu, idan muka kyautata hali da kuma zamantakewa da ita har ta fahimci musulmai mutanen kirki ne kuma ta dawo addinin ai mun yi jihadi babba ba karami ba"
"Ya isa haka, likita yace karka rika yawan magana"
Yayi murmushi.
"Ummi tana tsoron rasa dan autanta"
"Autan da baya jin magana ma? Ashe har guba yarinyar nan ta saka maka amma... Dai bari ka ji sauki tukuna, sai na ci mutuncinka Wallahi Aliyu"
Yayi murmushi, ita kuma ta mike tsaye ta mika masa wayar.
"Cire min password din"
Sai ya fada mata password dinsa sunanta ne tare da numbers, ta yi murmushinn jindadi ta fice daga dakin, sai da ta fita waje sannan ya kira Emily da wayar Aliyu.
"Hello... Aliyu"
Emily ta amsa da muryar kuka.
"Ba shi ba ne mahaifiyarsa ce, kina ina"
"Ina wajen asibitin na zo an hana ni shiga, Aliyun yana lafiya"
"Daidai ta ina?"
Ummi ta tambaye ta tana ina Emily ta fada, sai ta fita da kanta ta isa har gurin da Emily ta fada mata, Emily na hango Ummi ta mike tsaye gabanta na faduwa ta yi tunanin idan Ummi ta karaso gurin zata mata fada ne ko ta tuhumeta, sai da Ummi ta kawo sai ta ce.
"Ke ce Emily?"
Emily ta amsa ta hanyar daga mata kai a hankali cike da tsoro abubuwa biyu ta ci mutunci ko kuma ta fada mata wani abun ya sami Aliyu wanda ba shi take fata ba. Sai kawai ta ga Ummi ta rumgumeta.
"Ki yi hakuri, ba a kyauta miki ba kuma hakika an zalince ke"
Emily ta fashe da kuka Ummi ta dagota ta kama hannunta.
"Zo muje ki ga Aliyun"
Taja hannunta suka koma cikin asibitin Ummi ta shiga da ita har dakin da Aliyu yake.
"Gata nan ka yi a hankali ka san dai yanayin da kake ciki da kuma abun da likita ya fada"
Cewar Ummi sai kuma ta kalli Emily take share hawaye ta sake kallon Aliyu ta ce.
"Kuma ka bi a hankali karka kuskura ka ce zaka fada mata wata magana marar dadi, ka san dai ta fika tarin damuwa, ba zan lamunci hakan ba"
Aliyu ya kalli Ummi cikin wani irin jindadi da alfahari na furuncin da ta yi a yanzu, Emily ma ta kalleta tana mamaki da tunani. Ummi ta juya ta fita daga dakin ta rufe musu kofa. Sai shiru ya biyo baya Aliyu ya kasa kallonta ita ma ta kasa kallonsa sai jan majina take tana yawo da ido. A lokacin da ta yi jihadin dagowa ta kalleshi a lokacin ne shi ma sarkin ya fada masa ya kamata yayi nasa jihadin.
"How are you Aliyu"
"How are you Emily"
Suka hada ido da baki gurin tambayar junansu ya kowanensu yake, shi ya damu ya san halin da take ciki a yanzu bayan rabuwa da yarta da kuma abubuwan da suka faru, ita ma kuma ta damu ta san ya yake ji a jikinsa na abun da ya same shi domin ta ga bandage a kansa da kafarsa da jikin ya nuna alamar duka ta ko'ina. Shi ya fara sauke idonsa daga barin kallonta yana jefar da tambayar da amsar ta yi masa nauyi gurin dauka.
"Har yanzu akwai igiyar auren Turhan akanki? Da igiyar aurensa kika gudu?"
"Ba shi da amfani, na rika na sake shi, ba ni da wata alaka da shi yanzu"
Yayi murmushi ya koma ya jingina da ginin dake jikin gadonsa ya rufe ido. Ba shi da dalilin rashin jindadi amsarta, dan haka ba zai ayyana abun da ya ji a yanzu a matsayin rashin jindadi ba, sai dan tausayin rayuwarta da kuma na yarta, ko da yake yadda Turhan yake neman haihuwa yasan ba zai cutar da Fatima ba, ita ma kuma yadda Ammy ta juya masa baya ba zai yarda ya aikata abun da zai saka ya sake rasa Emily ba.
"Kin manta baki fada min wannan ba a cikin labarinki"
Ya fada bayan ya bude idonsa.
"Ba shi da amfani, na riga na sake shi"
Yayi murmushi mai nauyi.
"A musulunci mace bata sakin kanta, ke matarsa ce har yanzu"
"Ni ba musulma bace a yanzu, kuma a addininmu mace sakin namiji idan bata ra'ayi"
"Ai amman idan ta yi signing papers ko? Ke baki yi ko daya ba"
"Saboda ba a coci aka daura mana aure ba ko kotu"
"Shiyasa kike matarsa har yanzu"
"Duk tsawon lokacin nan? Duk bayan abun da yayi min?"
"It does not matter ke kika gudu ba shi ya barki ba, Emily you're still his wife"
Ta matsa kusa da shi ciki bacin rai.
"I hate you for telling me that"
"I know"
Ya amsa mata, ta nuna idanuwanta.
"Na yi bakinciki wannan hawayen da na zubar saboda kai, hankali ya tashi saboda abun da ya same ka yanzu ka farka kana fada min I'm still Turhan wife, i hate you Aliyu... I hate you... I hate you... I hate you... So much"
Ta furta da karfi ba tare data daga murya ba, sai yayi murmushi mai sauti.
"i hate myself more, what else?"
"Na tsane ka da ka kasance abokin Turhan"
Ta juya zata fice sai ya ce.
"Idan kika fita baza su bari ki sake shigowa ba, and we need to talk akan gurin da zaki zauna da kuma Fatima"
Sai ta juyo kawai ta fashe masa da kuka ta zube a gurin zaune, komawa yayi ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya. [7/10, 1:55 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy
*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
Page 4️⃣9️⃣
"Kina son zama da ummi na ko hotel za a kama miki? Ko da yake Hotel ba tsoro, ke ma kuma baki jin magana, dan haka zaki zauna da Ummi"
Bata kula shi ba sai kuka take rarewa.
"Emily kina son karasa ni ne, hawayen ki nan na san akwai kaso na a cikin zubarsu, ba ni da lafiya ki gani, zubar hawayen nan na ki kuma ya saka zuciyata nauyi, so kike na mutu ne?"
"Babu wanda zai fahimce ni, ni kadai na san wahalar da na sha, ni kadai na san damuwar da take cikin kaina, ba ni da kowa wannan ma kawai ya ishe ni bakinciki, yanzu kuma ya karbe min yarinya, be kamata ka kalleni ka fada min wannan maganar ba, Khalifa da Turhan ba ni da makiya irinsu a duniyar nan"
"Na fada miki ne, saboda shatawa kaina da ke da duk wanda zai rabe ki layi, abu ne da yake a hukunce ba ni na dora miki ba"
Ta kara fashewa da kuka har da buga kafa a kasa kamar yar yarinya, Aliyu ya tashi zaune kenan Ummi ta turo kofar dakin ta shigo, ganin Emily na kuka ya saka ta kalli Aliyu.
"Me ka mata?"
"Me zan mata Ummi ni da nake haka?"
"Toh dadi ya sakata kuka kenan?"
"Aa saboda na fada mata har yanzu akwai aure tsakanin ta Turhan ne"
Ummi ta dafata ta mikar da ita tsaye.
"Taso yata share hawayenki, ki daina bari ana ganin rauninki"
"Ummi zaku je da ita gida zata zauna saboda nan bata da kowa sai mu"
"Ita kuwa take da kowa tun da take da mu, je waje ki jirani kinji"
Emily ta share hawayenta ta fita dakin.
"Ka kwanta ka huta, zamu je da ita gida"
"Ummi karki bari ta gudu, kuma dan Allah ki kula da ita ki kwantar mata da hankali, Wallahi bana son damuwar Emily ko kadan, kuma ki fada mata da zarar na ji sauki zan dawo mata da yarta, sannu a hankali komai zai zama daidai"
"Zan kwantar mata da hankali, amman dai karka manta kai ma fa ka fada akwai igiyar auren Turhan akanta, karka manta da wannan"
Aliyu ya kalleta.
"Eh kuma hakan ba zai hana na taimaka mata ba, ko kwantar mata da hankali"
"Amman dai kar a wuce gona da iri, kar a tsallake iyakokin ubangiji"
"Subhanallahi, Wallahi ba abun da kika tunani ba ne Ummi sam sam sam babu wannan ko kadan, kawai dai ina tausayinta ne kuma ina son ta samu farinciki, ta dawo tafarkin musulunci"
"Ka san ni uwa ce, na kan iya hango abun da zai taho tun kamin ya taso"
"Toh gaskiya a nan baki hango daidai ba"
"Toh ga mu zuwa, Allah ya baka lafiya"
"Ameen, zan baki mamaki Ummi"
"Daman Mamakin nake son ka ba ni ai"
Ta shafa kansa ta yi murmushi.
"Zan je na girka maka abinci mai kyau, kamin na dawo na san ka samu yin bachi"
"Okay, can i have my phone please?"
Ya amsa yana sauke ajiyar zuciya, Ummi ta mika masa wayarsa sannan ta fice dakin taja masa kofa a hankali, a tsaye ta samu Emily ta rika hannunta suka fara tafiya Ummi na kwantar mata da hankali har suka isa gurin motar da aka kawo Ummi ita da Ummi suka shiga baya, daman front seat din akwai dan sanda daya a ciki, direba yaja motar yana tukawa a hankali har suka isa Family house dinsu Aliyu wato gidan da Ummi take zaune a Kaduna tare da Daddy, direban na faka motar harabar katon gidan dake cike da yan'uwa da abokan arziki da suka ji abun da ya faru da Aliyu kuma sun tafi Asibiti ba a barsu sun shiga ba. Ummi ta bude motar ta fita tana amsa wayar Daddy dake sanar mata yanzu jirginsa zai taso daga Abuja zuwa Kaduna, ta doshi Entrance din gidan, Emily ma ta bude ta fito ta bi bayanta sai ta ji an kira sunanta da muryar da bata wayanci ko ta waye ba.
"Emily..."
Ta juyo domin jin dalilin kiran arba ta yi da direban da ya kawo su a yanzu, sai dai har ga Allah bata wayance shi ba domin rabin fuskarsa a kone take, ta sake juya domin be ce mata komai ba ita ma kuma ba ce masa zata yi ba saboda bata san waye ba.
"Emily... Ni ne Khaleefa ne.. Baki gane ni ba? Ni kam ba zan iya mantawa dake ba duk yadda kika chanja, tun da kika shigo motar nan na gane ke ce"
Yana magana cikin rawar jiki da rawar murya kamar mai shirin yin kuka. Tun da ya furta cewar Khaleefa ne Emily bata juyo ba ta cigaba da tafiya, a lokacin ne Ummi ta juyo bayan ta kare wayar da take sai ga Emily ta biyo bayanta Khaleepa kuma ya biyo ta yana mata magana.
"Dan Allah ki taya dan girman Allah ki saurare ni"
"Kin san shi ne?"
Ummi ta tambaya. Sai Emily ta tsaya a gabanta
"Tsohon mijina ne, shi ne ya fara cutar da ni, shi ya budewa kowa kofa, shi ne mutumen da ya fara raba ni da gata, shi ne ya fara karantar da ni rauta tata, shi ya janyo min duk masifar da nake ciki yanzu, shi ne uban da har ɗana ya mutu ba taba ganinsa ba, shi ne mutumen da ya koreni da tsohon cikin dansa, yan'uwansa suka juyo min baya, su suka fara kirana da tubabbiya"
Ummi ta matsa daga gaban Emily fuska a hade ta kalli Khaleefa.
"Karka sake ko da wasa ka sake mata magana, taya zan shigo da bakuwa ka tari gabanta ba tare da neman izini ba? Direba ne kai a nan karka manta da wannan"
"Tohm Hajiya ayi hakuri"
Ya fada yana tare hawayen da suka cika idonsa. Ummi ta kama hannun Emily suka shiga ciki kowa sai kallonta yake saboda dress din dake jikinta ga kuma sarkar cross, Ummi ta shiga da ita ciki ta kaita dakin da Aliyu dake gidan.
"Nan dakin ɗana ne Aliyu, ki zauna a ciki ki yi duk yadda kika so, ki sake jikinki kamar kina cikin gidanki"
Emily ta kalli dakin.
"Idan kin bani dama zan je na dan ji da bakin da suka zo mana jaje"
Emily ta saki hannun Ummi ta nufi gadon da Aliyu yake kwana a lokacin da yake gidan ta zauna. Ummi kuma ta juya ta fice, kwantawa Emily ta yi kan gadon ya lumshe ido zuciyarta na mata wani irin zafi.
"Wayyo Zuciya"
Komai ya taru a zuciyar ya tsaya mata...
TURHAN POV.
"Kamata yayi kawai na koma na daukota, to miyasa amfanin barinta a can ma? Macen da na shekara nawa ina nema yanzu na ganta na bari wani katon banza yana controlling dinta"
"Idan ka je daukar ta zata yarda ta biyoka ne? Tun da fari da baka bata komai ba, ai duk haka ba zai faru ba, ni na ma manta ban tambaye ka ba, sakinta ka yi ko guduwa ta yi?"
"Guduwa ta yi ni ban sake ta ba"
"Amman ka munana mata a zamantakewarku?"
"Ba cancan ba, sai dai wani abun ta dauke shi da zafi saboda bata son zama da ni yanzu, kuma dole za a samu abubuwa da ba za su mata dadi ba, Ammy saboda Al'adar ba daya ba, kuma kin ga ina da mata, ko ma dai minene Ammy abun da ya wuce ai ya wuce yanzu ake fuskanta, tun da gashi har da yarinya a tsakaninmu, kuma matar nan ita muke da ni ma saboda gyara kuskuren da na aikata, ke da kanki fa kin ce na gyara abun da na bata"
Ammy ta sauke numfashi.
"Tun da har an ganta, to komai ya zo da sauki, balle kuma har ga ya tsakani, ka rika bin abubuwa a hankali, yanzu idan ka ce zaka yi rigima ai zaka karawa kanka bakin jini ne kawai a gurin Emily"
"Amman kuma sai na bar wani katon banza yana kallar min mata yana jin sautin muryarta yana karanta mata karya da gasjiya akaina"
Ya mike tsaye.
"Zan je na yi magana da ita zan bi duk wasu matakai da suka dace ta ruwan sanyi tsakanina da ita, kuma zan jawa Aliyu kunne, shi yana da tasa mata ni kuma yana son ya kashe min aure saboda ya bata tsakanina dake kuma da Fatima, ni na rasa me na tarewa Aliyu ne Wallahi, ashe haka hassada take"
"Karka je"
"Ammy me yasa kike hana ni abubuwa ne? Miyasa kika kin goya min baya a komai, yau na tabbatar da ace ni na na aikata abin da Aliyu ya aikata Wallahi ba zaki goya min baya ba, amman da idona na ga Ummi ta fito ta rungume Emily sun shiga tare, kin ga ta goyawa danta baya kenan da saninta ake komai waya sani ma ko Emily a gidanta take, shiyasa har Kameela ta san da komai"
"Turhan..."
Ammy ta kira sunansa, ya kalleta ba tare da amsa ba.
"Zauna"
Ya koma ya zauna.
"Mahaifinka ya fada maka ni na dauki cikinka wata ta haife ka ne?"
"Aa"
"To taya kake tunanin zan fi son wasu da kai? Duk abubuwa na nake maka ko nake fushi da kai akansu saboda ina kaunarka ne, na aura maka yarinyar nan saboda na samu ka yi kusa da ni, kuma ita ma ina hango mata jindadi a zamantakewarku, saboda ta auri wani bata dace ba, ina ganin idan aka kyautata mata kamar an yi ma musulunci hidima ne, daga lokacin da ta gudu ta bar min bakar wasika na san zamanku be tafi a yadda na yi tsammani ba, shiyasa ban taba tambayar ya kuka yi zaman ba, amman a zuciyata na ji babu dadi kuma na ji idan har baka nemo yarinyar nan ba, ni da kai ba mu gyara abun da ka bata ba, ba zan samu salama ba, na yi fushi da kai ne saboda na auna hakikan abun da yake zuciyarka da gaske zaka iya min biyayya ko aa kuma zaka so abun da nake so ko aa, daga lokacin da ka dage kana neman yarinyar nan zuwa yau data bayyana a garemu, ya tabbatar min da biyayyarka da kuma son farinciki da gujewa bacin raina, gashi kuma ta zo mana da alheri haihuwar da kake ta nema sanadinta ka samu, ko bana raye na san zaka yi alfahari da hakan, kuma na san zaka rike yan'uwa ka rika ziyartarsu, aurenka da Emily zai kara kusancinka da ni, na san yanzu ba zata yarda ta bika ba, amman zata yarda ta zauna a nan, kuma na san a yanzu kam dole zaka bata hakkinta, inda kana son zama da ita kana son yarta dole zaka zo, toh kuma sai ka yi tunanin ba zan taya ka wannan yakin ba?"
Kalman Ammy sun kwantar masa da hankali kuma sun saka ya ji sanyi kana sun karfafa nasa guiwa, sai dai hakan be kawar da abun da yake ji na kiyayyar ganin Emily ko magana da ita da Aliyu yake ba, domin baya kusa da ita yanzu.
"Tashi ka tafi gurin yarka, ni zan shirya yanzu na tafi gurin Ummi zan yi magana da ita dole ai ayi ma tukar hanci"
Turhan ya mike tsaye ya karasa inda Ammy take zaune ya kama hannayenta ya sumbanta sannan ya sumbanci goshinta.
"Na gode Ammy"
Ya nufi sama, sai ta bi bayansa da kallo tana murmushin jindadi, a yanzu ba ɗa kadai take da shi ba har da jika gashi kuma Emily ta dawo komai zai daidaita ya zama daidai a rayuwarsu. Tashi ta yi ta shiga ciki ta shirya shirin fita kamin ta fito Nurse dake duba jininta ta shigo ta hauro har sama ta auna jinin.
"Maa Shaa Allah, Hajiya jiki ya sauka sosai daman Dr yace idan na auna jinin na ga be hau ba, to na fada miki karki sake shan maganinki sai ya shigo anjima zai canja miki da su kuma ya fada miki yadda ya kamata a sha"
"Alhamdulillah, hankali na ne ya fara kwanciya yanzu, ciwon sugar ma ina tunanin zai sauka In Shaa Allahu"
"Eh shi ma naga jiya ya sauka sosai, Allah ya kara lafiya"
"Ameen"
Ammy ta janyo jakarta ta ciro kudi mai kauri ta mikawa Nurse din.
"Aa Hajiya"
"Haba ki karba mana, alheri ne ai ba a maida hannun kyauta baya"
Nurse din ta karba tana mata godiya sannan ta fice. Waya Ammy ta janyo ta nemo number Ummi ta kirata sai da wayar ta fara ringing sannan Ammy ta karaa kunne. Ummi ta amsa tare da amsa sallamar da Ammy ta yi, bayan sun gaisa Ammy ta ce.
"Ya Aliyu da karfin jikin?"
"Alhamdulillah"
"Ina son na shigo ne, kina gida ko kina asibiti?"
"Ina gida"
"Toh gani nan zuwa"
Ta aje wayar sannan ta dauki mayafinta ta yafa a jiki ta dauki jakarta ta saka talkaminta ta fice, dakin da Fatima take ta fara turawa a hankali sai ta hangota zaune a kasa Turhan yana zaune gabanta.
"Zan tafi"
"Okay Allah ya kiyaye Ammy, Wallahi Aliyu yayi min Illa Ammy yarinyar yanzu sunansa kawai take kira sai na mahaifiyarta, tana da hujjar kiran sunan Aisha amman Aliyu fa? Miye hadinta dashi? Yanzu fa ko da na shigo ya kirata a waya magana suke yi"
"Ka bi komai a sannu, ai mutum be taba cin amana ya ga nasara a rayuwa ba"
"Ni mamana nake so, na tsane ku duka, sace ni kuka yi, Uncle Aliyu zai zo ya dauke ni"
Fatima ta fada tana hararar Ammy daman karamin aikinta ne rashin kunya. Ammy ta saki kofar dakin ta shigo ciki ta karaso inda Fatima take zauna ta rikota sai Fatima ta fisge hannunta, Ammy ta sake rikota ta dagota ta nufi gaban madubi da ita ta dorata tsaye akan kujerar madubin, sai Turhan ya taso ya zo ya tsaya kusa da ita yana kallon madubin. Ta cikin madubin Ammy ta nuna mata Turhan tace
"Kalli wannan mutunen"
Fatima ta kalleshi tana kumbura baki.
"Kalli wannan yarinyar"
Fatima ta kalli kanta.
"Fada min da wa take kama?"
Fatima ta kara turo baki ta ki ta yi magana, ba dan kuma bata fahimci me Ammy take fada ba sai dan shakiyancin ba zai barta ta bada amsa ba.
"Wannan yarinyar ta yi kama da wannan mutumen ko baki gani ba?"
Fatima ta sake kallon Turhan ta cikin madubi ta kalli kanta.
"Saboda wacan mutumen shi ne mahaifin wannan yarinyar"
"Ba ni da mahaifina Momy ta fada min haka aka haifa ni ba ni da mahaifi, baki ji sunana ba Fatima Emily Aisha"
"Aa kina da shi, kowa na duniyar nan yana da uba sai ke kadai ce za ace baki da uba? Kina uba Fatima ni kuma kakarki ce, ke yar dangi ce jinin sarauta daga da baya kuma yar larabawa, kina da uba Fatima kalli ki gani kin taba ganin wani wanda kuka yi kama kamar wannan"
Fatima ta juya ta kalleshi.
"Meyasa Momy tace bani da Baba? Kuma miyasa be taba zuwa ba?"
"Yanzu su ya kamata ki tambaya, kowanensu sai ya baki amsa, amman tabbas wannan mahaifinki ne, daga sunanki ya tashi daga Fatima Emily Aisha, ya kuma Fatima Turhan Muhammed Abdo, idan ba mu da alaka da ke ai ba zai taba yayu mu rike ki mahaifiyarki ta kyale ba"
Fatima ta kalleshi da cikin madubi ta ga kamaninsu sosai kuma tana ji ya kwanta mata a rai a matsayin uba tun a ranar daya rungume ta, sai dai kawai bata yarda da su ba ne, domin ba mahaifiyarta ce ta fada mata ba. Fatima ta fashe da kuka
"Miyasa Momy tace ba ni da Baba? Idan shi Babana ne miyasa be zo ba shekara da yawa? Yan makarantarmu suna min dariyar sunana, suna cewa ba ni da Baba"
"Tsawon lokacin nan, nemanki muke ke da Emily ba mu san inda za mu ganku ba, sai a yanzu da Aliyu ya zo da ke, wata kila shiyasa ya zo dake saboda ya nuna miki mahaifinki ne"
"Ina son na yi magana da shi"
Ta sauka daga kan kujerar ta nufi inda wayar Aliyu take ta dauka ta mikawa Turhan.
"Kira shi"
Turhan ya karɓi wayar ya rike, har sai da Ammy ta ce.
"Kira mata Aliyun"
Kamar zai musa sai kuma ya taba number Aliyu ya saka hands-free, yana jin zuciyarsa kamar zata fashe tsabar bakinciki
"Hello My Beautiful Angel"
"Uncle Aliyuuuuu wani ne a nan yana cewa shi ne Babana da wata tsohuwa, a nan gidan da wannan matar ta kawo ni gaskiya ne? Tun ranar yake cewa shi ne mahaifina, kuma yana kama da ni"
Aliyu yayi shiru na dakiku.
"Eh mahaifinki ne"
"Miyasa Momy tayi min karya tace ba ni da Baba?"