Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy - Chapter 37
Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 37: Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 37. "Saboda.... Ta yi tunanin ya rasu ne... Bata son…
4,421 words
"Saboda.... Ta yi tunanin ya rasu ne... Bata son ta fada miki ki shiga damuwa shiyasa take fada miki haka, amman yanzu mun gane yana da rai shiyasa aka kawo ki nan dan ki san shi kuma ki saba da shi, dan haka ki zama yarinyar kirki yi rika jin magana karki ce zaki yi tsiwa kinji ko?"
"Ba zaka zo ka dauke ni ba?"
"Zan zo amman sai kin kwana biyu kin saba da shi tukuna, sai na zo na dauke ki, ba na san kina son uba ba? Kina son canja sunanki ki hada da na mahaifi to daga yanzu zai canja"
"Ba sunanka kace zaka saka min ba? Ni bana son sunan wannan ni bana son shi ni kai nake so, i don't want this old woman and her Son kai nake so da Momy"
Ita kawai bata saba da su ba ne, tana son uba amman ta fi sha'awar ace akwai wani wanda ta wani a kusa.
"Okay za mu zo ai, amman sai idan kin yi biyayya kin zama yarinyar kirki, bana son rashin magana da tsiwa, idan kina musu fushi ba zan zo ba, amman idan kika zama yarinyar kirki zan zo"
"Okay i will be a good girl"
"Yauwa, i love you can you say you love me back?"
"I love you ka zo da sauri"
"Okay bye"
Turhan ya karɓe wayar ya datse kiran ko da be iya mayarda duka yaren turanci ba ai yana jin abun da yake fada kuma ya fahimci komai, kamar zai buga wayar a kasa sai kuma ya daure ya saki murmushi ya mika mata wayar, sai ta kura masa ido tana ta kallonsa ya rage tsawonsq ya duka daidai ita sai ta matsa jikinsa ta kwanta ya rungume suka zauna a gurin Each and every second sai ta daga kai ta kalleshi ya kalleta tana kuka mai karfi ta ce
"Zan fadawa yan makarantarmu ina da Baba, zan tafi kai zan nuna musu, i hate Momy i hate her"
Hawaye ya cika idon Turhan Ammy daman tuni ta fara zubar da nata.
"Ni ma zan fadawa family ina da ya, ina da kaso a jinjina, zan baki duk wani gata da kika rasa Fatima, ki yi hakuri na zo a makare"
Ammy ta share hawayenta tana murmushin farinciki.
"A yau zaka kara sanin muhimmanci na Turhan, zaka san abun da ake kira da iyaye, zaka san sha'anin yaya"
Ta dauki jakarta ta fice daga dakin tana kara shaye hawayenta, sai da ta fito sannan ta sanar da direban ya fito ya same ta ya bude mata mota ta shiga, ta zauna kenan wayarta ta yi ringing sai ta ciro wayar daga jakarta ta duba sai ta ga bakuwar number.
"Sallamu Alaikum"
Mai kiran ta amsa mata ta dayan bangaren sannan ta gabatar mata da kanta.
"Sunana Hajiya Barakat, amman yara suna kirana da Mama Baraka"
"Maa Shaa Allahu, sai dai ban gane ki ba"
"Eh to ba mu taba magana ba, ba lallai ki yi saurin gane ni ba, ni step mother din Kameela ce matar Aliyu abokin danki"
"Okay Tohm Lafiya?"
"Ba lafiya ba, ina son mu yi magana da ke ne akan Emily da kuma yarta Fatima da take gurinku"
"Ina saurarenki"
"Ba maganar waya ba ce ina son ganinki ne"
"Zaki iya zuwa gidana zuwa anjima yanzu dai ina hanyar tafiya wani gurin ne, idan zaki taso sai ki sanar da ni na kwatanta miki"
"Tohm shi kenan"
Ammy ta sauke wayar tana mamakin kiran, zuciyarta na raya mata wata kila Kameela tana son ta karbe Fatima ne ta maidata gurin Emily saboda Aliyu, ko kuma dai wani abun ne tun da Allah kadai ya san me ya faru na kawo yarinyar da Kameela ta yi ba tare da izinin Aliyu ba. Haka dai Ammy ta yi ta sake sake har suka isa gidan Ummi. [7/11, 10:21 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy
*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
Page 5️⃣0️⃣
Ummi na falo tana ta gaisawa da mutane yan'uwa da abokan arziki da suka zo mata jaje sai ga Mama Barakat ta shigo falon da sallamata tare da rakiyar yarinyarta ta biyu. Ummi na ganinta ta dan daure fuska kadan domin ta san zuwanta ba zai wuce saboda Kameela ba, sama sama suka gaisa da Ummi sai Ummi ta maida hankalinta gurin sauran baki bata sake bi ta kan Mama Barakat ba har sai da Mama Barakat ta gaji da zama ta ce.
"Hajiya gurinki na zo"
Ummi ta maido da hankalinta gurinta sannan ta mike tsaye ta nufi wani dakin baki dake falon ta shiga tana fadin.
"Bismillah Hajiya Baraka"
Ummi ta fara shiga ta zauna sai ga Mama Baraka ta shigo ta zauna kan kujerar dake dakin.
"Na katse ki kina da baki, na tafi asibiti ai aka ce kin zo gida kuma ba su yarda na shiga na duba Aliyun ba"
"Eh ana son ya huta ne, kuma saboda abun da ya faru da shi ya saka ake ba shi tsoro dole a san suwa suke shiga da fita"
"Allah sarki, Allah ya ba shi lafiya kuma ya tsare gaba, mu ma a gari muka ji abun da yake faruwa"
"Ameen Ya Rabbi"
Daga haka sai shiru ya biyo baya, Mama Barakat bata sake cewa komai ba hakan ya saka domin ta yi tunanin wata kila ta zo nan ne amadadin mahaifiyar Kameela, dan haka Ummi ta tari hanzarinta tun kamin ta fara magana.
"Hajiya Baraka Allah dai ya sa ba kin zo maganar Kameela ba ne, domin dai yanzu Aliyu yana bukatar hutu da kwanciyar hankali, kuma iya hakuri ni dai na yi a matsayi na uwarsa na dauke ido iya yadda zan iya, yanzu kan abun ya wuce duk inda ake tunani ba kuma zan yarda ta kashe min ɗana ba saboda kishinta na banza. Abun ya kai har ta saka masa guba kin ga ai ba so ba ne ba kuma kishi ba hauka ne"
"Subhanallahi, guba fa kika ce Hajiya"
"Da bakinsa ya fada min, shi ne dalilin turo ta gida da yayi ai, amman be fadawa kowa ba sai a yanzu da ta kai shi makura, kin ga yanzu ko za su zauna da junansu ni ba yarda zan yi ba, ba zai yiyu su da aure ni da zaman zullumi da fargabar me zai faru ba"
"Ban taba ji wannan, amman Kameela bata yi ma kanta adalci ba, Subhanallahi, ni ba ma zancen ta ya kawo ni ba, Wallahi ba dan kowa na zo ba sai dan yarinyar da aka ce saboda ita Aliyu ya saki Kameela, shiyasa na tafi asibiti aka ce baki can na tambaya dan Allah ita Emily tana tare da shi ne na kwatanta musu ita suka ce min kun taho tare"
"Emily? Toh Allah yasa ba daga mata hankali za'ayi ba, domin yarinyar nan tana cikin damuwa, kuma kamar amana take a gurina"
"Haba Hajiya ni ma fa Uwa ce, ta ina zan nemi daga hankalin wata ya? Magana kawai nake son yi da ita, saboda ina tunanin kamar ita ce yarinyar da aka taba hada mu da ita a lokacin da muka je Abuja, na zo da ita har Kaduna sai ta gudu bata tsaya ma na taimaka mata ba"
"Allah sarki Ashe kin santa"
Nan Hajiya Barakat ta labarta ma Ummi farkon haduwarsu da kuma dalilin haduwa.
"Toh ki haura sama, tana nan daki na farko hannun hagu"
"Toh na gode Hajiya"
Mama Barakat ta tashi tare da Ummi suka fito Ummi ta koma gurin Mutanenta Mama Barakat kuma ta nufi upstairs ta haura sama ta bi hagu da ita kamar yadda Ummi ta fada mata, dakin farko ta fara turawa a hankali ta leka sai ta hango Emily zaune kan gadon Aliyu tana rutsar kuka a hankali marar sauti. A take zuciyar Mama Barakat ta kara karyewa daman ta shigo gidan zuciyarta cike da rauni, ta shiga ciki gaba daya ta maida kofar ta rufe karar rufe kofar ya saka Emily ta kalli kofar sai ta yi hanzarin takaita kukanta ta sauke kanta kasa. Mama Barakat ta karasa cikin dakin ta zauna bakin gadon tana kallon Emily babu shiri hawaye suka zubo mata, yadda Emily ta takure guri daya ya bata tausayi sosai.
"Ba lallai ki gane ni ba, sunana Mama Barakat, mun tana haduwa da ke a lokacin da kika bar Sudan Mrs Deborah ta zo da ke, sai tace na zo da ke Kaduna saboda kin fada mata a nan kike, kamin ayi bincike ba ki ma zauna a gidana sai kika gudu ko kin gane ni?"
Emily ta kalleta da kyau ta daga mata kai, daman tun farkon shigowarta ta ga alamar kamar ta taba ganinta. Cikin kuka Mama Barakat ta ce.
"Meyasa kika gudu? Me yasa baki tsaya ba? Wata kila da yanzu baki shiga cikin wata damuwa ba, baki yarda da ni ba ne a lokacin? Na yi tunanin ke musulma ce a lokacin?"
Emily ta kalleta hawaye na sauko mata.
"Gaba daya ni a yanzu ban fahimci rayuwa ba, ban gane me take nufi da ni ba, daga wannan sai na fadawa wannan, idan har iyayena ko yan'uwana ba za su iya rike ni tun a lokacin da ban san komai ba, bana tunanin akwai wanda sai rike ni na samu mafita, bayan barin gidanki abubuwa da yawa sun faru, a lokacin na samu gata kuma ina da yarana har biyu, sai ga shi kuma rayuwa ta sake juye min ta kawo ni nan, babu gatan babu uwa ba uba ba babu yaran, dayan ya mutu dayan an karbe, ni yanzu na kasa fahimtar komai"
Ta fashe da kuka, Mama Barakat ta matsa kusa da Emily ta rungumota ta kwanto da ita jikinta ita ma ya fashe da kuka mai karfi wanda ya fi na Emily shiga zuciya da sosai rai, ta rumgume Emily sosai tana shafa kanta. Emily ta lafe a jikin Mama Barakat daman tana neman wanda zai rumgume ta kamar haka a yanzu, sai duk ta ji kewa da son kasancewa da tata uwar duk da yake bata taba sanin ya dadinta yake ba, amman ta sani idan har akwai iyaye a tare da ita ko yan'uwa na jini wasu abubuwan za su zo mata da sauki.
"I Need my own parents, ni mace ce kawai mai son iyayenta da yan'uwanta a kusa da ita, why all this? Me na yi musu? Me na yi ma rayuwar? Me yasa kaddara take ta juya ni haka? Na gaji na gaji na gaji"
Tana maganar tana kuka mai ban tausayi ta takure sosai a jikin Mama Barakat kamar zata shige jikinta, bankarewa Mama Barakat ta yi ta daga kai sama tana ta yaki da numfashi da kuma kukan dake son sakata ihu, hawaye suka rika sauko mata ta gefen ido wasu na bin wasu. Sai da ta kai ruwa rana tsakanin kukanta da numfashinta sannan natsuwarta ta samu daidaituwa, ta maido idonta akan Emily ta shafa kanta.
"Na samu labarin abun da ya same ki a yanzu nw ta gurin Kameela saboda sakin da Aliyu yayi mata na abu...."
Mama Barakat bata kai aya ba Emily ta daga daga jikinta da sauri ta matsa baya.
"Fita dakin nan"
Mama Barakat ta girgiza kai da sauri.
"Ba ki gane ba ne, bana goyon bayan Kameela ina tare da ke ne..."
"Ki fitar min daga nan, bana son Kameela bana son duk wani abin da ya shafe ta, fita yanzu nan"
Mama Baraka ta mike tsaye ta dauki jakarta kamar mai tsoro jikinta har rawa yake.
"Tohm, zan fita amman idan kina bukatar wani abu ko taimako zaki iya tuntuba ta, kuma zan kasance kusa da ke daga yanzu In Shaa Allahu, idan kina bukatar wani abu ki fadawa Aliyu zai fada min yana da number wayana"
Ta nufi kofa tana yi tana juyo ta kalli Emily har ta fice, sai da ta tsaya ta share hawayen ta sannan ta sauko jiki babu karfi murya kuma ta sauya ga ido ma be isa ya karyata cewar ya zubar da hawaye ba. Ta sauko tana ta masa kasa da ido bata son hada ido ta mutane saboda bata son kowa ya gane ta yi kuka, amman hakan be hana Ummi tambayar lafiya ba bayan ta tambaye ta sun gana.
"Eh mun yi magana da ita"
"Allah yasa dai lafiya, yanayinki kamar ya canja Hajiya Barakat"
"Lafiya kalau, dan Allah zan iya samun number mahaifiyar abokin Aliyu nan a gurinki? Domin na kira Aliyu be daga ba, na manta sunan abokin nasa dai amman wanda aka kaiwa yarinyar ta Emily"
"Oh Turhan? Eh ina da number mahaifiyarsa"
Ummi ta kai hannu ta dauko wayarta ta kamo number ta karanta mata, Mama Barakat ta saka sannan ta yi mata godiya ta yi mata sallama ta fice tare da yarta wacce ta rakota. Fitar Mama Barakat mutane suka ragu har Ummi ta samu damar amsa waya daya daga cikin mutanen da suke kiranta, sannan ta haura sama ta yi wanka ta sauko domin shiryawa Daddy wani abu kamin ya iso, daman bata yarda mijinta ya ci abincin kowa sai ita, sai idan bata gida ko kuma wani babba uzuri ya sha gabanta. Tana Kitchen tana tsaka da girkin ne ta ji sallamar Ammy, sai ta rage wutar gas din ta yi kasa sannan ta fito.
"Maraba da Hajiya Maijidda, yau Ammy ce a gidan na mu"
"Ni ce Ummi, fatan mun same ku lafiya"
"Toh Alhamdulillah, ya gidan ya kwana biyu"
"Sai godiya, ya Aliyu da jiki? Ashe haka abu ya faru? Tohm Allah ya saukewa ya tsare gaba"
"Ameen Ameen, ashe kun ji"
"Eh ai kin san abu irin wannan yana saurin yado, balle kuma wayarsa tana gidanmu gurin Fatima, to yawan kiran da ake ne nake amsawa ta nan na ji"
"Oh ashe wayar tana tare da ku, ikon Allah to yarinyar take?"
"Tana nan lafiya kalau"
"Maa Shaa Allah, tohm bari na duba girkina"
"Tsaya dai tukuna Ummi na zo nan saboda mu tattauna abubuwan da suka faru"
Ummi ta koma ta zauna.
"Toh kamar me kenan?"
"Haba ki daina yin kamar baki san komai ba mana, Aliyu be fada miki abun da ya aikata mana ba? Kuma na san Emily ai tana nan ko?"
"Eh haka ne, Emily tana nan tare da mu, Aliyu kuma be fada min ya aikata muku wani abu ba"
Ammy ta sauke ajiyar zuciya.
"Na san kin san yadda muke ta faman neman Emily, shi kansa Aliyun ya fi kowa sani domin Turhan be boye masa komai ba, amman ace Aliyu ya san inda Emily take wai har da ya a tsakaninsu amman ko da wasa be kyankyawasa Turhan ba?"
Ummi ta hade yawu.
"Ammy a yanzu ba zan iya bawa Aliyu kariya ko wanka ko dora masa laifi ba, Aliyu dai danki ne kamata yayi ace ki same shi ku tattauna"
Ammy ta yi murmushi mai sauti.
"Emily tana gurinki ne duk tsawon lokaci nan ko kuma dai a yanzu ne ta zo nan"
"Aa ni ma a yanzu na san da ita, shi ma saboda abubuwan da suka faru ne na daukar yarta da Kameela ta yi ta kai muku ba tare da izininta ba"
"Ai Kameela ta kyauta mana Wallahi, ba dan ita ba wata kila da har yanzu ba mu san komai ba, kuma Aliyu ya san yadda Turhan yake ta neman yaya"
"Ta kyauta tun da ta raba uwa da ƴa, kuma ta raba igiyar aurenta kin ga ai ta ci riba, ni kuma sai na yi mamakin da aka ce Fatima tana hannunku kun riketa uwarta tana nan tana fama da kewar da damuwa, kun san yarinyar bata da gata sai Allah, gashi yanzu har ta bar musulunci"
"Ummi ya kike magana kamar kina goyon bayan Aliyu? Kina ganin hakan daidai ne kenan?"
"Bana goyon bayan Aliyu, amman ni dai na san ban manta lokacin da kike zuwa kamun kafa a gurin Daddyn Aliyu ba saboda kina neman a baki dama ki samu ganin Turhan, daga baya kuma kika koma rokon a bar shi ya rika zuwa inda kike, ke dai uwa ce na san kin san zafin rabuwar da da uwa, ya kike tunanin Emily tana ji a yanzu? Yarinya ta raini yarta shekara da shakaru rana tsaka ku dira a rayuwarta ku karbe mata ya? Anya kun yi adalci kuwa? Abun ma ai da kunya"
"Ba karbe muka yi ba, mun rike ta ne ta yadda zata saba da mu, ke kin sani Turhan kadaina haifa, ko kare aka ce nasa ne ya kike tunanin zan so shi balle jika? Ni dai ban aurawa Emily Turhan da nufin cutar da ita ba, idan ma ba su fahimci juna ita da Turhan ba, ni be kamata ta saka ni ciki ba, kuma ko yaya dai za a juya a juyo Emily tana da igiyar auren Turhan a kanta karki manta da wannan"
"Ammy idan kin zo saboda Emily ne, tana sama daki na farko hannun hagu, ni dai ba zan fada miki fari da baki akan jikarki da yarki ba, kabli da ba'adin rayuwa kin sani, idan kin yi daidai ko akasin haka a bayyane yake, ni zan shiga na karasa girkina"
Ummi ta mike tsaye ta nufi kitchen, Ammy ta bita da kallo mai wuyar fassara sannan ta tashi ta haura sama ta shiga dakin da Ummi ta fada mata Emily tana ciki. Emily ta sauko da kafafuwanta kasa ta kalli kofar tana jin tsanar sunan Kameela ma balle kuma abun da ya alakance ta. Mikewa ta yi tsaye ta nufi inda take kyautata zaton bandaki ta tura ta shiga. Kallon ko'ina ta yi komai yana nan na gyara jiki ko gashi na maza kai kace Aliyu yana rayuwa a gidan har lokacin. Shaving cream ta fara dauka ta duba sannan ta duba shower gel, ta nufo shower ta kunna ta daga kai tana kallo ta tara hannunta ruwan ya zuba a hannunta sai kuma ta juyo gurin madubi ta kalli kanta kamin ta kunna tab ta fara wanke fuskarta, bayan ta gama ta dauki karamin tawul data gani aje a gurin ta dauka ta goge fuskarta ta aje sannan ta fito, tana karewa dakin kallo gaban madubin gadon ta fara nufa tana duba turaruka da suke gurin da mayuka na maza na gyara jiki, daya bayan daya ta dauka tana dubawa sannan ta aje ta nufi closet ta bude tana kallon tufafinsa talkaminsa da kuma hulluna.
"Assalamu Alaikum"
Sallamar Ammy ce ta saka ta juyowa ta kalli kofar sai ta maida kanta gurin kayan da take kallo ba tare da ya amsa ba.
"Kina fushi da ni har yanzu, amman baki fahimce ni ba ne Aisha, bana nufin cutar da ke, daga lokacin da kika bar min wasikar nan kika gudu ba sake walwala ba, Turhan be saka samun damata ba, na yi mamakin da na ganki a cikin wannan shiga da kuma canja addinin da kika yi, wannan duk be dace da ke ba"
Emily ta juyo ta kalleta.
"Toh me ya dace da ni? Cigaba da zama da mutumen da na fi kaunar mutuwata a kansa? Ko kuma yarda da surukar da ta fifita farincikinta akan nawa? Ke kika fada min danki zai ba ni farinciki zai ba ni gata, sai gashi danki ya maida ni baiwa a masarautar da shi ya kamata ya ba ni gata, ya maida ni kurma alhalin ina ji, ya gabatar da ni masarautar a matsayin baiwa da kika ba shi, ko wace safiya sai na wanke bangaren matarsa, bana iya cin abincinsu a haka nake daurewa, ko da yake laifina ne, ai ya gargade ni tun kamin na aure shi, yace kar na amince, amman saboda ina son na faranta miki rai na miki sakamako da abu mai kyau na amince, ban taba son Turhan ba, kuma ba zan taba son shi ba, na aure shi saboda ke, a daren ranar da aka daura auren ya fada min bakar rana ce a gurinsa, a daren da aka samu cikin Fatima ya fada min bakar rana ce a gurinsa, ya fada min ba zai taba so na ko son abun da zai fito daga gareni ba, na azabtu a masarautar nan kyautar da ni aka yi ga wata mata matsayin baiwa da haka na zamu yanci, na raini cikin yata cikin wahala na haife ta ta girma ba tare da kulawa daga ubanta ba... Ko da yake ba zaki fahimta ba danki ne a gabanki..."
Ta karasa tana girgiza ka tana share hawaye. Ammy ta kai zaune tana hawaye.
"Na aura miki shi ne da tunanin ke da shi kuna son junanku, ni ma na yi makamanciyar rayuwar da kuka yi, amman ni na cutu ne saboda mahaifinsa baya so na, ban yi tunanin Turhan zai kyamace ki ba, shiyasa sai da na zaba na mika masa, ban ba shi gama garin bakar fata kamar sauran ba, ban yi nufin kulla Sheri ba Emily alheri na yi nufi"
Emily ta dauke kai. Ammy ta nuna kusa da ita.
"Zauna... Zauna ki fada min wane irin zama kuka yi, kuma me kike bukata a yanzu?"
Emily ta kalli Ammy da idonta suke cike da hawaye sannan ta zauna tana aje numfashi mai nauyi a muhallinsa. [7/14, 6:25 PM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy
*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*
*© Khadeeja Candy*
Page 5️⃣1️⃣
Cikin kuka da shesshekar kuka Emily ta karasawa Ammy labarin irin zaman da ta yi a Sudan da kuma rayuwar da ta biyo bayan zamanta a can, yadda ta hadu da Vito ta canja addini har zuwa haduwarta da Aliyu da irin rokon da ta yi masa na kar ya sanar da Turhan inda take, Emily bata boye mata ba, ta fada mata har auren nw ta yi ne saboda ita ba dan tana son Turhan ba. Ammy yaja numfashi da nauyi ta sauke hawaye na sauko mata kuka take sosai tata rayuwar take tunawa, yadda abubuwa ta yi zama da mahaifin Turhan.
"Zuciyata ta raya min dole akwai abin da yake faruwa da ya saka kika gudu kuma kika bar min wannan sakon, amman ban taba tambayarsa wane irin zama kuka yi da juna ba, ni dai damuwata na yadda za a gano ki ne, wannan dalilin ya saka na daga hankalin Turhan na sauya masa fuska, na yi duk yadda uwa zata yi idan ta rasa yarsa, kin san saboda me? Saboda na gane shim Turhan mai biyayya ne a gareni? Kuma saboda ya nemo ki, ban manta lokacin da kika fada min baki da kowa ba, ina yawan tuna wannan, kuma ina jin wata kila idan na taimake ki zan iya samu aljannata ta nan, ashe ma akwai jinina a tare da ke, na aura miki Turhan ne saboda ni da ke mu samu mafita, ke ki samu miji mai nagarta mai kulawa, ni kuma na samu ɗana da zuri'arsa a kusa da ni, amman na yi kuskure, na jahilci ɗana, na yi zaton zai riritaki ne, ashe yayi miki rikon da kadan ya banbanta da wanda mahaifinsa yayi min"
Ammy ta kai hannu zata taba Emily sai Emily ta matsa tana hawaye.
"Baki fahimce ni ba ne Aisha, amman har gobe baki da wata uwa sai ni, ban yi nufin cutar da ke ba, na hada aurenki da Turhan ne saboda ina tunanin zai so ki, na duba kyanki a lokaci da yadda siffarki ta banbanta da yayan hausawa, wai ina zaton haka zai daga kimarki a gurinsa, sama da ace bakar fata na aura masa, na so ki kamar yar da na haifa a cikina, har gobe ni uwarki ce"
Emily ta kalleta.
"Zan tabbatar da hakan ne kadai idan kika saka ɗanki ya sake ni!!! Idan kika yi haka zan tabbatar kin dauke a matsayin Ƴa!"
Ammy ta hade yawu da karfi ta yi jimmm na dan lokaci kamin ta sake hade yawun a karo na biyu ta daga kai.
"Zan tabbatar miki da haka Aisha, ba zan so yarki ta tashi da iyaye a rabe ba, ke kin san zafin haka, haka kuma na so ki da jinina na yi nufin yanzu mu kyautata gareki, amman zan shure komai saboda farincikinki zan miki yadda kike bukata"
Ammy ta mike tsaye ta dauki jakar har ta fara tafiya sai kuma ta juyo.
"Zan roki alfarma daya, karki cusa tsanarmu a zuciyar Fatima, haka kuma ba zan iya shiga tsakanin uwa da ƴa ba, ba zan iya yanke hukunci akan Fatima ko Turhan ba, amman dai a tsakaninku ni na hada kuma zan raba, na barki lafiya"
Ta juya ta cigaba da tafiyarta har ta isa bakin kofar ta bude ta fice, ta sauko kasa kenan ta hadu da Ummi da zata hauro sama.
"Kin fito?"
Ammy ta kalli Ummi ido cikin ido.
"Eh na fito, Turhan zai saki Aisha zan tabbatar mata da cewar tabbas a ya na dauke ta, idan ya sake ta sai Aliyu ya aureta, na barki cikin amincin Allah"
Ammy ta nufi kofa ta bar Ummi tsaye da mamaki tana kallonta har ta fice. Ummi ta haura sama ta tura dakin Aliyu da Emily take ta leka sai ta hangota tana kuka.
"Ke haka zaki zauna kullum kuka kuka? Shiga ki wanke fuskarki ki fito muje kitchen"
Emily ta mike tsaye ta shiga bandakin ta wanke fuskarta ta fito Ummi ta rike mata kofa ta fito suka sauka kasa, Kitchen din suka nufa ba dan ran Emily ya so ba sai dan Ummi ta bukata, a tare suka karasa aikin sai da suka jera komai a dinning sannan Ummi ta kalleta ta ce.
"Kina fifita farincikin wasu akan naki, kina fargaba tunkarar wasu da abun da yake zuciyarki, shiyasa kika cutar da kanki, ko da yake ta wani bangaren ba laifin ba ne, kin tashi ba tare da kowa ba, duk wanda ya rasa iyaye ko ya tashi a maraya farincikinsa ragagge ne, a kullum yana tsoro ko fargabar rasa farincikin wani fiye da nasa, ko da yaushe kina jin ke baki da amfani wasu ne masu amfani, karki sake tsorata ko cilasta kanki abun da ba shi kike bukata ba, aikim nan da muka yi ranki be so ba ni na sani, amman kin kasa fada saboda kar raina ya bace"
Emily bata ce komai ba idonta dai ya cika da hawaye. Ummi ta dauki cup ta zuba ruwa
"Shiga dakin ki wanka, Nafisa zata kawo miki wasu tufafin ki saka kamin a siyo miki irin wadanda kika saba sakawa, idan kin ci abinci sai ki kwanta ki huta"
Emily ta juyo ta fara tafiya, sai Ummi ta aje cup din hannunta ta fasa shan ruwa ta kira sunan Emily.
"Emily"