Kenza eBookz

Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy - Chapter 57

Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy - Chapter 57

Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 57: Abokin rayuwa Complete by khadeeja candy Chapter 57. "Ki fada masa komai, amman ban da mutuwar aurena"

3,493 words

"Ki fada masa komai, amman ban da mutuwar aurena"

"Why? Za ki komawa mahaifinsu Kameela ne?"

"Ba lallai ba, na lura kamar ya dauki abun da zafi sosai, ni kuma ban shirya auren kowa a yanzu har sai na aurar da duka yarana, by that time kuma na san aure ya fita kaina"

"Amman da yanzu ace Mahaifinsu Kameela zai dawo zaki koma masa"

"To me zai hana?"

Ta amsa tana murmushi, Emily ta kalleta ta sauke kai ga dukan alamu tana son tsohon mijinta, sai dai kuma zama ya kare a tsakani. Sai dare Aliyu ya zo ya dauke ta bayan ya ajewa Mama Baraka siyaya kamar yadda ya saba. Abuja suka fara tafiya sai da suka kwana a gidan Dr A-B da ya bukaci su kwana a gidan amman Aliyu be yarda ba, sai ya kwana a gidansu gurin Ummi. Emily kuma ta kwana a gidan ɗan'uwanta.

Matarsa wayayyiya ce kamar shi, tana da son mutane da nuna kulawa Emily ta yaba da yadda aka tarbe ta. Alhaji Bulama na da na shi uzurin haka ya saka Dr A-B ba samu alfarma tafiya a jirgin mahaifinsa ba sai na kasuwa. Ba a cika samun direct flight daga Nigeria zuwa Scotland kai tsaye ba. Yawanci Ana tashi daga Lagos (Murtala Muhammed International Airport LOS) ko Abuja, kasancewar a Abuja suka kwana a nan jirginsu ya daga sai ya sauka a London Heathrow, sai da suka huta a wani hotel dake kusa da airport din sannan suka dawo suka shiga wani jirgin ya ɗaga zuwa Scotland. Tafiyar daga Abuja zuwa London ta ɗauke su kusan 6-7 hours. [9/7, 7:58 AM] 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t

*🍒 ABOKIN RAYUWA 🍒*

*© Khadeeja Candy*

Page 7️⃣7️⃣

Kin dade kina sha'awar sayen kaya a wajen Khadeeja Candy amma ba ki samu dama ba? Kin shirya fara tanadin kayan Sallah ko na azumi tun yanzu? Ko kuma tanadin kayan auranki ko na 'yarki? To, ga sauƙi ya iso!

ADASHE NE NA GATA! Ki zuba kuɗi, ki ɗauki abin da kike so daga:

Sutura da zannuwan gado

Kayan kitchen

Kayan electronics (fridge, freezer, washing machine, gas cooker, da sauransu)

Talkami da jaka

Zanen gado

Frames (flowers decoration ko standing ones)

Console mirror

Boxes na Lefe ko na traveling.

Warmers iri-iri

Food flask iri daban-daban

Jugs da flask. Kai abin fa sai wanda rai ya so!

Sauƙi ya zo, za ki mallaki duk abin da kike so a wajen Khadeeja Candy cikin aminci da kwanciyar hankali, babu cuta babu cutarwa.

📌 Tsarin: Zubi ne wata-wata da kuma sati-sati. 📌 Akwai sharudda da ka'idoji.

Domin ƙarin bayani, ki/ka tuntube ni ta wannan lamba: 08036126660 Ko ta hanyar WhatsApp 👉 Danna nan https://wa.me/message/2Y7RIJEODZO2K1

Ko kuma ku yi join WhatsApp Group https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t

Thank you 😍 🙏

Daga London zuwa Edinburgh/Glasgow kusan 1 hour flight ne. Jimilla tafiyar ta zame musu ta 10 - 12 hours bisa layin jirgin da suka bi. Scottish, Scotland tana cikin United Kingdom (UK) ne, arewacin Ingila take. Tana da manyan birane kamar Edinburgh (babban birni), Glasgow, Aberdeen, Dundee. Yanayin can yawanci sanyi ne sosai, musamman lokacin hunturu (November-March), akwai ruwan sama da iska mai ƙarfi, balle kuma yanzu da yake January. Shiyasa suna sauka filing jirgin Edinburgh Airport (EDI) dake garin Edinburgh, Aliyu ya rufe matarsa da rigar sanyi da ya riko mata, dan kam tun a jirgi yayi masa tanadi daman shi yake kula da abunsa..

Tun da suka sauka kasar Emily ta tabbatar sun zo garin yan'uwanta domin yawan mutane kasar kowa zaka gani jan gashi ne irin nata, tana ta kallon manyan gine ginen da kawar gari ta zo inda bata sani ba. New Town, wata sabuwar unguwa ce da mai taxi ya kaisu bayan Dr A-B Ya Fada masa domin a unguwar mahaifinsu yake. Aliyu ya fara fita motar yana rike da Abulkhary dake bachi sannan ya bude mata ta fito tana kallon gaban gidan da suka tsaya wanda tsarinsa ya sha banban da na mu na hausawa.

Karamin gate ne ba mai tsawo sosai ba an saka flower gefe gefen na gida ga haske normal ba. Gidan sama ne mai fadi amman ba mai ado da lankwashe lankwashe kamar na mu ba. Aliyu ya tsaya a gabanta ya saka hannunsa daya ya gyara mata fuskarta,.ya cire mata hullar kanta gashinta ya bayyana sai ya baza mata gashin ko'ina, sannan ya rika hannunta suka nufi kofar shiga gidan.

Dr A-B ne a gaba tare da matarsa Emily tana daga baya tare da Aliyu. Door bell ya taba sannan ya kara fuskar sa gaban ring camera yayi magana kasancewar sun shigo da dare ne a lokacin da sawu ya fara daukewa. Wata kyakkyawar matashiyar yarinya ce ta fara bude kofar tana ganin Dr A-B ta saka ihu ta rumgume shi shi ma ya rumgumeta yana murmushi. Aliyu ya kara matse hannun Emily take hannunsa domin ya lura fargaba ta cikata ta ko'ina. Da suka shiga ciki kowa kallon Emily yake saboda an labarta musu ita tun kamin ta zo, kuma sun ga zahiri domin bata rage komai daga kammanin mutumen dake tsaye gabanta yana kallonta ba.

"Dad wannan ce Emily yarka, Emily wannan shi ne mahaifinki"

Ya dade yana kallonta kamar ya rasa abun yi, bata bar komai daga kammaninsa ba, shi kasan da ya ganta sai da yayi rabin mutuwar tsaye, domin duk yayansa babu wanda yake kama da shi sosai da sosai kamar yadda ita take yi. ita ma tana ta kallonsa sai hawaye take.

"Dare yayi ya kamata kowa ya kwanta gobe za mu yi abun da ya kamata domin tabbatarwa"

"Dad baka ga kamammi ba?"

"Kammanin kawai ba su isa su wadatar ba ya kamata mu bi ka'idodi"

Kamar wanda be san taya zai karbe ta ba, haka ya tarbe ta sai duk kuzarinta ya gushe. Sai dai Aliyu da Dr A-B sun kafarara mata guiwa, a dokar kasar be isa ya amsa cewar shi ne mahaifinta kai tsaye ba ta hanyar kammani ko sheidu sai da takardun shedai gwajin jini kuma sai ya zama tana bin sunansa ne. Emily ta kwana da tunani, washe gari da suka hadu teburin cin abinci sai ta lura babu mahaifinta a gurin sai yan'uwnta maza biyu da mace biyu da kuma matarsa da tun jiya suke rigima saboda abun da ya aikata shekaru da yawa da suka wuce.

Kusan kowa be saki jiki da ita a gidan ba, saboda dokar bata tabbatar ba, har sai da suja tafi Asibiti aka yi musu gwajin kwayoyin halitta ita da mutumen da take ikirarin ɗanta ne results din ya fito at 98% sannan mahaifinta ya yarda. Tana zaune wajen asibitin ita da Aliyu dake rike da hannunta ta dora kanta a kafadarsa. Mahaifinta ya fito daga cikin asibitin yana rike da takardun gwajin.

Emily na ganinsa ya mike tsaye tana kallonsa ya nufo inda yake with so much emotional tana jiran ya fada mata results din dake hannunsa sai ta ga kawai ya rumgumeta. Aliyu ya sauke sanyayar ajiyar zuciya yana murmushi tare da yi ma Allah godiya. Shi kansa abun da ya faru jiya ya ba shi tsoro. Ya dagota daga jikinsa ya duba fuskarta ya taba ya sake maida ita jikinsa.

"Na san kin zo da tari tambayoyi da suka bukatar amsa.."

Ya sunbance saman kanta.

"No na riga na san amsar komai, na san duk abum da na ke son sani, komai ya faru ne ba da son ran kowa ba"

"Yeah ki yafe min, da ace na san tana dauke da cikinki ba zan juya baya ba, dukan mu muna kuskure na yi kuskure na sani I'm sorry"

Emily ta rike hannayensa.

"Mu daina tuna baya, na zo nan ne saboda samun karin farinciki da kuma sanin asalina, ba amfanin tuna abun da ya wuce"

Ta juya ta nuna Aliyu.

"Wannan mijina ne, wannan kuma yarona"

Ya mikawa Aliyu hannu suka gaisawa, da ya tara hannu zai karbi Abulkhary sai yaki zuwa saboda kewa yake yi baya yarda da kowa sai iyayensa.

Duk yadda Dr A-B zai yi ya fahimtar da Step Mom dinsa mahaifinsa ya aikata kuskure kuma yayi nadama sai da yayi, domin a gurinsu kamin abu ne ta maka shi a kotu ta nemi a raba auren, kuma a raba har ma da ganimar daukar dukiyarsa a damka mata kuma a bata ragamar yayanta. Ta inda ta saurara masa be aikata hakan a lokacin da yake aurenta ba. Ya aikata ne kamin ya hadu da ita.

Sam ita kam baya yarda ta karbi Emily ba, sai ya zama ma. Kamar tana kishinta saboda Emily ta fi kama da mahaifinta fiye da yayanta, ga shakuwa da ta shiga tsakaninsu na dan zaman da ta yi a gidan, yaran ma sun sake jiki maza da mata amman ita bata yarda da Emily ba. Mahaifinta ya kaita gurare da yawa, ya nuna mata abubuwa wasu daga tarihinsu wasu kuma daga tarihin garin.

Mutumen mai kaunar karensa sosai duk inda yaje yana tafiya da su domin rakiya, tun tana tsoro har ta daina. Wata rana da ya tafi da ita gurin da yake kamun kifi ne yake tambaya labarin Mama Baraka, ta fada masa kuma ta labarta masa yadda abubuwa suka faru da ita. Ya tausaya mata matuka, ta nuna masa hoton Fatima a wayarta.

Honeymoon din da Aliyu be samu tafiya yayi da matarsa ba lokacin da suka yi aure shi yayi da ita a nan. Ya jata sun shiga gari sun yi yawa har makotan garin sun ziyarci gurare dabam dabam. Sati daya ta yi a gidan ya dauke matarsa suka tafi yawon amarci. Dr A-B daga can wata kasar ya bulla. Mahaifinta ya saka ta gaba suka tafi aka ayi komai a rubuce da ka'ida cewar shi ne mahaifinta a doka.

Da za su tafi Emily ta yi kuka sosai tana ta kewar mahaifinta, ta rumgumi yan'uwanta ta yi musu bankwana tare da jaddda musu za ta dawo a duk lokacin da ta bukaci haka. ya rumgume yarsa ya saka mata wata sarka tashi mai tarihi ya dauko kudi mai yawa ya bawa Emily amman bata karba daman bata zo domin kudinsa ba sai dan ta san waye ubanta shi ma kuma ya san wacece ita, amman ta karbi kyautar agogo da hotuna da yayi mata...

Karfe bakwai na safe suka bar kasar ita da Aliyu, sai da suka sake daukar awanin da suka dauka da farko sannan jirginsu ya isa Nigeria suka sauka da dare saboda awaninin ba daya ba. Ummi ta aika da mota aka dauko su daga Airport, zuwa gidan inda suka samu tarba ta musamman. Washe gari suka sha hira da Ummi na abubuwan da suka faru da kuma yanayin garin da guraren da suka ziyarta, hotunan da suka dauka da sauransu.

Satinsu daya Abuja sannan suka dawo Kaduna, rayuwa ta cigaba kamar yadda aka saba. Da Fatima ta yi arba da hotunan da aka dauka a wayar Emily ta sha kuka sosai ba a tafi da ita, Emily ta mata alkawarin idan zata koma da ita zata tafi. Har a lokacin Ammy bata yarda Fatima ta zauna a hannun Emily sai dai ta rika zuwa tana dawowa, sai kuma idan fitsarar Fatima ya tashi ta nace sai ta kwana a gidan.

Emily na yaye Abulkhary Aliyu ya biya mata Ummara ta tafi tare da Fatima da shi, da Abulkhary, a can suka yi sallah karama ba su dawo na sai bayan Sallah. Da lokacin hajji yayi kuma ya cika mata kawarin da ya daukar mata tun tana da cikin ɗansa. Ita kadai ta tafi ta yi hajji ba da shi ba saboda yanayin aikinsa.

TURHAN POV.

A shekarar da Emily ta tafi hajji a shekarar Turhan ya yafi, shi da matarsa sai dai har kowa yai ibadarsa ya gama be hadu da dan'uwansa ba saboda jirginsa kasar da masaukin kowa dabam. Turhan yana zaune yana waya da Fatima yana fada mata abubuwan da ya tara mata a dakinta dake gidan. Matarsa ta shigo, ta zauna can nesa da shi ta zauna, haka take a duk lokacin da yake magana da yarsa saboda tana kishin Fatima ba yarta ba ce, kuma tana kishin duk wani abu da zai dauke hankalin mijinta daga gareta. Ta jira har sai da ya gama wayar sannan ta koma kusa da shi ta tsaya tana murmushi.

"Rufe idonka"

Ya kalleta cike da shauki, yayi murmushi ya rufe idon kamar yadda ta bukata. Ta kama hannunsa ta saka masa abu a hannu, ya lakaba abun sannan ya bude idon. Wasu yan mitsitsinan kayan yara ne irin na yar tsana amman na jarirai.

"Da leek.. laken testanna tisʿa shuhur."

"Wannan domin kai ne, amman ka jira sai nan da wata tara"

Turhan ya kalleta ya sake kallon kayan, kamin tunaninsa ya ba shi abun da ya dade yana tsammani daga gareta. Wani irin tsalle Turhan yayi ya dauke matarsa yayi sama da ita yana juyawa. Kamin ya sauke ta tambayeta.

"Kina ciki da gaske?"

Ta daga mishi kai tana hawaye. Sai ya sake rumgumeta

"Wallahi ana baḥibbik shadeed.. Enti addayteeni al-farha al-bat kunt baftaš ʿalaiha, khalleetini mabsoota li-daraja ma baʾat mihtaaja ay farha taanya."

"Wallahi ina kaunarki.. Kin ba ni farinciki da nake nema, kin faranta min baya na rasa wani farinciki. Alhamdulillah ya Rabbi, Alhamdulillah Allah"

A lokacin ne ya gane rokon da yayi a saudi be tafi a banza ba, rasa Emily ya samu wani farinciki ta inda ya cire rai da samu, ada yayi zaton Fatima ce kadai yarsa, ashe ba iya haka farincikin zai tsaya ba. Da Ammy ta samu labari kamar ta zuba ruwa kasa ta sha tsabar farinciki, kusan duk wanda ke masarautar ya taya Turhan murna da farinciki a lokaci da cikin ya bayyana. Wani irin kula na musamman da tarairaiya kamar kwai Turhan ya shiga yi ma matarsa.

Ko da baya son ya shirya kula da abun cikinta balle kuma yana kaunar matarsa tun asali a yanzu ne ma kaunarta take ninkuwa. Ba ma kamar lokacin da ta haifa masa yan biyu mace da namiji, kamar mahaukaci haka ya zama tsabar farinciki macen aka saka mata sunan Ammy namijin kuma ya saka masa sunan da matarsa ta zaba. Sai da suka yi kwari sosai sannan ya cilastawa matarsa shiryawa suka tafi Nigeria a tare aka kaiwa Ammy da Fatima yaran suka gani.

Da ya ji labarin Emily na da wani cikin gurin yarsa, sai da zuciyarsa ya sosu, har kullum ba zai cire rai da fatan rabuwar auren Aliyu da Emily ba, yana ji a jikinsa komai daren dadewa Aliyu zai juyawa Emily baya. Ammy ma haka take saka rai saboda tana ganin Emily da Aliyu sun musu butulci.

EMILY POV

Emily ta saba da ciwon zuciya. Duk wanda ya zo mata a baya sai ya bar ta da hawaye da raunukan da ba sa ganin ido amma zuciya tana ji. Auren farko ta zame mata yaudara, na aure na biyu ya zame mata jinya.

Lokacin da ta daina tsammanin farin ciki, sai ta haɗu da Aliyu. A farko ta ɗauke shi ma kamar sauran mutanen me, ya shimfida mata soyayya sai ta hau ya juya baya. Sai dai lokaci ya nuna mata kuskuren tunaninta.

Aliyu bai tsorata da raunukan da take ɗauke da su ba. Ya tsaya mata kamar likita ga mara lafiya. Ya saurare ta ba tare da gaggawa ba, ya rungume ta ba tare da sharadi ba, ya nuna mata cewa akwai wanda zai iya sauya ciwon zuciyarta ya mayar da shi farin ciki.

A hankali Emily ta fara murmushi inda ta saba zubar da hawaye. Zuciyarta ta buɗe kamar furanni da suka ji ruwan sama bayan dogon fari...

***

Tana tsaye a Kitchen tana juya miyar dake kan wuta Aliyu ya shigo, bayanta ya kaiwa duka kadan sannan ya juyo da ita tana dariya ya sumbance ta.

"Me kika girkawa haka kamshi har office ya tarar da ni"

Ta yi dariya.

"Kuma fa yau ba da kai na girka ba"

Ya hade rai.

"Kai kin ma isa?"

"Kai haka kake da kyau daman?"

Ya kai mata mitsika a kumatu

"Miyasa kika raina ni wai? Kin san fa ni oganki ne"

"A baya ba, a yanzu kuma Abokin Rayuwa"

Ya rumgume yana murmushi ya shafa katon cikinta.

"je ki huta bari na zuba abincin ai yayi ko?"

Ta daga mishi kai.

"Baka siyo min komai ba?"

"Na siyo mana, wani mai nama na gani yana soyawa na cire masa zuciyata na ce ya soya min na kawo miki"

Ta chakuli cikinsa tana dariya, shi ma dariyar yayi ya kashe gas din, ya dauki cooler da aka siya mata gurin Khadeeja Candy ya fara zuba miyar.

Falo ta dawo ta zauna ta bude ledar kayan cikin dake ta kamshi tana fara ci, tana jin kaunar mijinta, a yanzu ta gane ba dukkan soyayyar gaskiya ake samunta cikin sauƙi ba. Wata soyayyar sai da jinya, sai da yaudara, sannan daga ƙarshe Allah ya kawo maka wanda zai goge komai ya mayar da ke sabuwa. Aliyu ya zama wannan kyauta,

Wani lokaci idan ta tsaya gaban madubi, sai ta dubi fuskarta dake cikin madubin tana tambayar kanta

"Shin ni ce waccan Emily da ta sha kuka da hawaye a baya? Ni ce waccan yarinyar da ta yi ta fadi-tashi a soyayya, ta rasa uwa, ta rasa gata?"

Madubin ya kan nuna mata fuskar mace, amma cikin zuciyarta hotunan rayuwarta take gani, yadda ta yi ta neman wanda zai tsaya mata, yadda ta sha karya da yaudara, yadda ta sha jin kalmar "ki yi hakuri" ba tare da wani ya share mata hawaye ba.

Amma yanzu abubuwa sun canza. Wani haske ya bayyana a rayuwarta, hasken da bai zo da wuri ba, sai bayan dogon lokaci. Duk jarabawar da ta sha, duk fuskokin da suka juya mata baya, duk hawayen da ta kwanta da su, sun zame mata darasi guda, hakuri wanda shi ne makullin kowane sauyi mai kyau.

Da farko, hakuri ya yi mata nauyi. Amma da ta dage da shi, sai ta ga riba. Ta gane cewa bayan wuya akwai daɗi. Ta dandani zafin lokaci, amma kuma tana kan dandana zaƙin sakamako. A yanzu idan ta kalli kanta a madubi, ba kawai tana ganin mace ba, tana ganin ƙarfi da jarumtarta, tana ganin mace da ta yi tafiya kan wuta ta jure har ta kukanta ya sauya zuwa murmushi. tana kallon wata karamar yarinya da zama uwa, yar'uwa, ƴa kuma mata ga mutumen da ya san darajarta, mutumen daya sauya lafiyar rayuwarta, ya canja tunaninta ya sabunta duniyar da abubuwan da bata sani ba, bata saba ba kuma bata taba tunanin za ta samu ba.

Emily ta sha taskon rayuwa, an haifeta ba da aure ba, kuma mutane suka ɗora mata nauyin da ba nata ba. Ta taso cikin hawaye, cikin rashin gata, har sai da zuciyarta ta gushe daga neman farin ciki. A Lokacin da Khaleefa ya yaudareta, ta yi zaton soyayya ba gaskiya bace sai ta karyata gaskiyarta, da Turhan ya juya mata baya, dan zaren farinciki daya rage mata sai ya tsinke, duk da irin hallacin da ta yi wa mahaifiyarsa, ya kasa ganin darajarta.

Amman a yau dukansu su biyun sun rasata, bayan doguwar jinyar cin amana da kowanensu yayi a zuciyarsa. Idan cin amana tana da rana Khaleefa ya gani, idan butulci yana da ciwo Turhan ya fi kowa fahimtar haka a yau, yana dauke da ciwon kaunarta gashi ta masa nisa, Khaleefa kuma be isa ko kusa da ita ya tsaya ba. Emily ta samu gata a wajen Aliyu, wanda ya rike ta da gaskiya, wurinsa ta san daɗin addinin Musulunci, a wurinsa ta gane cewa soyayya rahama ce, gata ce. Ta tashi daga matar da ake wulakantawa zuwa wanda ake alfahari da ita.

Ta zama uwar ƴaƴa a gidan Aliyu, kuma mata ga mutumen da ya fahimce ta tun farko, ya girmamata, ya so ta, ya bata gata, ya mantar da ita damuwa. Asalinta be hana ta zama abar so a gurinsa ba. Rayuwa ta karantarta ita duk inda aka haife ka da aure ko ba aure ba kai halittar Allah ne mai daraja, kuma ba laifin ka ba ne...

Na gyara miki rubutun gaba ɗaya my Lady 🌹, na haɗa da abin da kika buƙata, tare da ƙarin salo mai kyau da ɗan jan hankali ga masu karatu:

---

Godiya ga Allah da Ya bani ikon fara wannan littafi har na kammala shi cikin nasara. Alhamdulillah. 🙏✨

Wannan littafi na sadaukar da shi ga Big Sis Habiba Muhammad I love you more than words can ever express. 💖

Masu karatu zan so jin daga gare ku

Wane darasi kuka koya daga cikin littafin?

Wace ɓangare ya fi burge ku?

Kuma da me za ku fi tunawa da littafin Abokin Rayuwa?

Kada ku manta, ni ce Khadeeja Candy mai siyar da kaya masu kyau da inganci a farashi mai sauƙi. 🛍️✨ 👉 Khadeeja Candy Store https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08?mode=ac_t

Sai mun haɗu a littafi na gaba mai suna GUMBAR DUTSE, in sha Allah.

I love you all dearly ina yi muku fatan alheri fiye da yadda kalmomi za su iya bayyana. ❤️🥰

Readers Also Read