Kenza eBookz

Abraham complete by nooreemaan - Chapter 14

Abraham complete by nooreemaan - Chapter 14

Abraham complete by nooreemaan Chapter 14: Abraham complete by nooreemaan Chapter 14. Bayan ya gama ci ya sha cucumber juice dinsa ta tattara wajen ta fita…

3,371 words

Bayan ya gama ci ya sha cucumber juice dinsa ta tattara wajen ta fita da kwanukan, tana sauka ta hango Madam Gloria hakimce kan dinning table tana cin abincin, gabanta ne ya fadi, amma ta dake....

"ke! wa kika kai wa abinci?"

Madam ta tambaya cikin muryan ta Mai kama da fada-fada.

cikin rudu Aysha tace "hm.....hmmm yallabai na...na kai wa"

"Hmmmm... ya ci iya cin sa a yanzu, domin daga rana irin ta yau zai bar wanna duniyar yabi iyayen sa, idan yana bukatar kari ma ki kara masa, bai dame ni ba"

ta fada a bayyana, amma cikin yaren Igbo wanda hakan yasa Aysha dake zaro ido kasa gane me ta ce.

Madam Gloria kuwa hannu tayi wa Aysha alamun ta bar gaban ta, cikin sauri Aysha ta nufi kitchen har tana tuntube.

Da gayya ta shiga wanke-wanke a hankali gudun kada ta fito ta tarar da madam Gloria, aikuwa sai bayan mintuna talatin ta fito, ajiyar zuciya ta sauke ganin babu Madam a dining table, hakan yasa ta nufi upstairs da gudu kamar wacce taga abin tsoro.

*********

6:00pm Bayan Aysha ta gama dinner Mai sauki, ta ajiye na madam a dining table, sannan shima ta kai masa na sa dakin sa...

Dakin ta ta fada tayi wanka, bayan ta gama ta daura alwalan magriba ta fito, tana cikin shiryawa aka kira magriba.

Bayan tayi sallah ta kishingida da jikin gadon ta, ba tare da ta shiryawa Hakan ba Wani bacci Mai Dadi ya dauke ta.

*1:45pm* AYSHA

A firgice ta farka cikin tsoro, sak'amak'on baccin da ta Yi Mai tsayi, cikin sauri ta mike salati dauke a bakinta, dafe gefen kanta daya tsara mata tayi, sannan ta nufi toilet domin daura alwalan Isha da bata Yi ba.

*********

Mintuna goma Sha biyar ya dauke ta yin sallah'n Isha Hadi da sha'afi da wutiri.

Bayan ta iddar ta zauna shiru, tunanin Abraham ya shiga yawo cikin brain din ta, kasa zama tayi Hakan yasa ta mike domin ta je gareshi, duk da cewa dare ne Amma ta San cewa matuk'ar bata je ba hankalin ta bazai taba kwanciya ba.

A hankali ta tura kofar dakin ta shiga, gabanta ne ya bada ras sak'amak'on ganin sa zaune ya kura wa hanyar shigowa ido, tamk'ar Yana jiran isowar ta ne.

Kallon gefen da ta ajiye masa abinci tayi, taga ko taba wa bai yi ba, sosai taji ba Dadi a ranta...

"Kila yunwa yake ji shiyasa ya kasa bacci"

Ta fada a ranta yayin da fuskar ta ke k'wabe kamar zata saki kuka...

A hankali ta karasa Wajen abincin domin zuba masa sai dai...

Karfaffan hannun sa Mai tsayi ya daga mata alamun ta barshi, mamaki Hakan taji, a sanyayye ta dago tace

"Dan Allah ka bari na zuba Maka, wallahi bacci ne ya dauke ni kaji"

Sleepyn face dinta ya kalla kana ya jefa mata Wani kallo daya sa ta sulale kasan tiles ta zauna.

Abraham kuwa Bai fahimci abinda tace ba, Amma duk Wanda ya kalle ta a wanna lokacin zai fahimci cewa bacci tayi, ba kuma fushi yake da ita ba, domin Yana ganin kokarin ta sosai, Hakan Nan tana da kima a zuciyar sa sosai, sannan baya jin yunwa ko kadan.

Duk da cewa ya gaji matuk'a da zaman wheelchair din, domin ba Abu bane Mai sauki, Amma ya yarda da kaddara mai kyau da akasin ta, yasan cewa Allah ne ya jarrabe shi, ba kuma zai Yi butulci ga Allah ba, illa yayi addu'a Allah ya bashi lafiya, domin yasan Babu kaddara mara kyau da zai dawwama.

Aysha kuwa kasa komawa dakinta tayi... karaf idanunta suka sauka kan qur'anin da ta ajiye a bedside drawer din sa tun da rana, ajiyar zuciya ta sauke domin zama shirun ya soma gunduran ta, cikin sauri ta dauko shi ta koma ta zauna, suratul yasin ta Bude tayi Bismillah ta shiga karantawa cikin zazzak'ar murya kasa-kasa tana bawa kowacce harafi hakkin ta.

A kuma daidai lokacin ne Madam Gloria ke tsaye a dakin ta rike da kwaryan nan Mai dauke da wanna abun Mai tsananin haske , sanye take da wasu jajayen kaya Mai ratsin Baki.

Wanna abun na cikin kwaryan ta Sanya a tafin hannun ta, sosai hannun ta ya shiga rawa saboda karfin abun, wasu kalamai marasa dadin ji ta shiga karantawa da Wani yare, idanun ta kyaar kan wanna abun na cikin tafin hannu ta....

💞NoorEemaan💞

Thank you for reading my novel #Abraham.

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 0806626851 [10/13, 12:13 PM] 💖NoorEemaan💖: 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇 ABRAHAM 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇

*First edition*

*WATTPAD* @NoorEemaan

https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din

Chapter 47-48

Ta dauki tsawon mintuna goma tana karanta suddabarun ta kana ta hura iskar bakin ta izuwa ga abin tsafin dake hannun ta, kamar a mafarki abin ya bar hannun ta ya shiga tafiya shuuuuu ya bi ta bangon dakin ya fita...

Murmushin farinciki Madam Gloria ta saki ganin burin ta na daf da cika. Bayan Mintuna biyu kacal murnan ta ya koma ciki, firgice da tashin hankali suka maye gurbin farinciki da take ciki sak'amak'on abin tsafin daya dawo hannun ta, Wanda hakan alamun rashin nasara ne.

Gabanta ne ya bada ras! domin lalacewar wanna aikin daidai yake da lalacewar dukkanin Shirin ta, kamar zararriya tace "meyasa? Meke Shirin faruwa ne, Wani irin taurin rai ne da kai Abraham, wallahi bazan bar ka ba, har sai na ga ka zama gawa!" Ta karasa a tsawace.

A karo na biyu ta Kara Yi, Bai je ko ina ba ya sake dawowa ya fada cikin tafin hannun ta. Wani fushi ya zo mata, dukkanin nutsuwarta ta tattaro ga abin tsafin kana ta shiga karanta suddabarun ta, sai ta hura iskan bakin ta izuwa ga abin tsafin, wannan karon abin tsafin ya koma cikin kwaryan, a hankali launin kwaryan da abin tsafin Nan ya dawo Wani bakinkirin, jikin ta ne ya shiga rawa, Hakan yasa kwaryan ya subuce daga hannunta ya fadi kasa ya tarwartse, zubewa tayi a kasa ta saki Wani Kara, yayinda hawaye Mai zafi ya biyo kuncin ta hugu...

Kamar zararriya ta shiga birgima a kasa tana surutai, so take ta mike domin zuwa duba Abraham ta ga abin sa ya hana aikin ta cika, domin ta ga dalilin da ya hana shi mutuwa, Amma ta kasa tashi saboda tashin hankali da fargaban da take ciki yasa jikin ta mutuwa, tsoro sosai ya shige ta domin bata manta da abinda bokan Nan yace Mata ba, kafin ta karbo kwaryan tsafin.

Kamar almara, wanna fashashen kwaryan nan Mai dauke da abin tsafi ya shiga tattara Kansa waje Daya, kana ya bace bat, daidai inda kwaryan ya bace Wani bakin hayaki ya tashi yayi sama Wajen pop'n dakin.

Duk Madam Gloria na kallon abinda ke faruwa Amma ta kasa motsa ko da yatsan ta ne, kamar wacce aka datsa haka ta kasance.

ABRAHAM Cikin birgewa yake kallon Dan tsut din bakin ta dake karanta littafi Mai sarki, his attention is hundred percent with her, har lau Bai San abinda take karantawa ba, Amma Yana sintar Kansa cikin nutsuwa a duk lokacin da yake Jin zazzak'ar muryan ta Mai sanyin amo na karatun qur'anin, ji yake dama su dauwamma a haka, iska Mai sanyi ya furzar daga bakin sa Yana sake mayar da hankalin sa gare ta.

Aysha kuwa bata San ma Yana Yi ba, karatun ta ta cigaba da Yi tana Jin fargaban da ke damunta tun safe da bata San Kona menene ba na barin zuciyar ta, salama da Wani sanyin ni'ima daga Allah ya maye gurbin tsoron ta, haka ta dauki tsahon lokaci tana karatu, har bacci yaci karfin idanun ta, ba tare da ta shiryawa Hakan ba Wani bacci Mai dadin gaske ya dauke ta a zaune qur'anin ta na rungume a kirjin ta.

ABRAHAM Kallon innocent face din ta yake, Yana Jin Wani nishadi da Bai San Kona menene ba na ratsa shi, yanda numfashin ta ke fita a hankali da yanda zararran eyelashes dinta ke rufe yafi komai Jan hankalin sa.

"Oh! Jesus Christ" Ya fada a hankali Yana lumshe idanun sa, haka ya cigaba da zama har akayi Kiran sallah daga masallacin unguwar...

Idanun sa da suka bata awannin a rufe, ba kuma bacci yake ba ya Bude a hankali, ya ga sai bacci take, domin zuwa yanzu ta sulale kasan tiles din Amma still qur'anin ta na rungume a kirjin ta.

A hankali ya tura keken sa zuwa gaban inda take kwance, yace "hey!" Shiru Aysha na duniya bacci bata San Yana Yi ba, kafarta ya kalla, kana ya daga kafar sa ya Dora kan tafin kafarta...

Can cikin bacci Aysha ta ji Wani sanyi na ratsa ta, a hankali ta shiga Bude idanun ta, sai kuma ta sake rufewa alamun baccin Bai ishe ta, "hey! Wake up it's time for your prayer (ke! Ki tashi, lokacin sallar ku yayi)" fada da turanci Yana Dan murza kafar sa kan na ta kafar.

Cikin sauri ta mike salati dauke a bakinta tana murza idanun ta, kalle-kalle ta shiga Yi, taga dai tabbas dakin sa ne, cikin muryan bacci tace" yaushe nayi bacci a dakin Nan ban sani ba?" Ganin bata da Mai bata amsa yasa ta mike a hankali ta bar dakin tana waiwayen sa, da kallo ya bi bayanta Yana sakin ajiyar zuciya, Wani Abu kamar rashin jin Dadi game da barin ta dakin na ratsa zuciyar sa...

************************

9:05am A daidai lokacin Aysha ke haurawa da breakfast din sa sama, a hankali ta shiga dakin bakin ta dauke da sallama, dago Kansa yayi ya shiga bin ta da kallo, bayan ta ajiye ta Dan risina tace

"Ina kwana"

Daga mata Kai kawai yayi, domin zuwa yanzu yasan Ina kwana kamar gaisuwa ce, duk da Bai San ma'anar ba, Amma ganin tana yawan fadin Kalmar ya sa ya zauna a Kansa..

Bayan tayi serving dinsa sannan ta Kara warming maganin jiya ta bashi, Babu tunanin komai ya karba ya shanye. Ganin Haka yasa ta barin dakin domin tayi wanka sannan tazo tayi masa rubutu. Da shigar ta wakan da shiryawan mintuna ashirin ya dauke ta sannan ta dawo dakin sa tayi masa rubutu a allo ta bashi, Nan ma babu musu ya karba ya Sha, domin ya gama bata dukkanin wata yarda...

Bayan Nan ta gyara masa dakin sa ta sauka da kwanukan, dakin madam Gloria tabi da kallo ta girgiza kanta kana ta hayo sama abinta, domin taje kofar dakin ta ta dinga kwankwansawa domin ta Yi mata gyaran dakin Amma bata Bude ba, dakin ta ta koma domin Wani mugun bacci take ji.

MADAM GLORIA

Sai safa da marwa take saboda tashin hankali, rashin cikar burin ta a daren jiya yafi komai daga hankalin ta, hanyar kofar ta nufa tana huci kamar wata zak'anya, cikin ranta take fadin "yaro yaro ne! Yaro man kaza, idan ka San wata baka San wata ba" ta karasa fada kana cikin sauri ta nufi dakin sa. Tana shiga ta tarar da Abraham zaune Yana bacci a tunanin ta, , domin idanun sa a lumshe suke, sa dai abinda bata sani ba, duk Yana sane da shigowar ta, duk da idanun sa a rufe suke Amma Yana kallonta ta tsakankanin eyelashes dinsa.

Kallon shi take daga sama izuwa kasa saboda ganin Bai yi rama ko lalacewa kamar yanda tayi tunani ba, "Amma wake kula dashi haka?" Ta fada a ranta tana tabe Baki tare da Jin haushin ganin sa tsaf tsaf duk da bawai kamar lokacin da yake da lafiya bane, ganin zata bata lokacin ta yasa ta dauke kanta daga garesa.

Bincike ta shiga Yi a dakin, gabadaya ta birkita dakin, mukullan motar sa duka ta kwashe, sannan ta fara Neman dukkanin takardun company'n sa Amma bata gani ba, haka ATM cards din sa, domin ta San pin din sa kasancewar ya bata dukkanin wata yarda a matsayin mahaifiyar sa.

Numfashi ta shiga saukewa kamar wacce tseren gudu, saboda zirga-zirgan da ta Yi a dakin, kallon dakin take tana Neman Ina Zata samu takardun sa domin yafi komai muhimmanci cikin kadarorin sa, kallon ta ta Kai inda Abraham ke zauna ta watsa masa Wani kallon tsana, tayi mugun tsanar sa fiye da baya, domin shi kadai ke bata ciwon Kai, a yanzu tunanin kashe shi ba tare da Wani tsafi ba take tunani, Amma abin da kamar wuya, domin Abraham Wani irin powerful halitta ne, kashe shi kuma ba Abu bane Mai sauki duk da kasancewar sa a zaune kan keken guragu, haka Allah ya hallice shi gifted ne.

Kamar guguwa haka ta bar dakin fuuu da mukullan motocin, tana Jin haushin rashin ganin takardun sa...

A hankali Abraham ya shiga Bude idanun sa da suka Sanja launi saboda fushi da karyewan zuciya, mummy'n sa yake gani ta Sanja ta zama wata muguwar hallita, dama haka take duk tsahon shekarun Nan Amma ya kasa gane hakan...

Killer smile yayi Mai tattare da ciwo Yana cije labban'sa masu taushi, a hankali ya ga an turo kofar, dago Kansa yayi ya kalli Mai shigowar, ajiyar zuciya yayi ganin wacce ta shigo.

Share fisabilillah

Comment for more typing....

✨NoorEemaan✨ 07082281566

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 0806626851 [10/13, 12:18 PM] 💖NoorEemaan💖: 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇 ABRAHAM 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇

*First edition*

https://facebook.com/groups/943534712916776/ Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din

*WATTPAD* @NoorEemaan

Chapter 49-50

*AYSHA* Kallon dakin take ganin yadda ya hargitse ya tabattar mata da cewa an shigo dakin, amma bata ko yi magana ba ta shiga gyarawa, domin tambayar waya shigo ba hurumin ta bane.

Abraham kuwa zuba mata sexy eyes din sa yayi, Ya kuma fahimci abinda ke ranta, Amma Bai yi magana ba, tana cikin gyaran ne taji keypad dinta na ringing, sai a lokacin ta tuna cewa wayar na dakin Abraham, bata dauka ba, cikin sauri ta nufi Wajen wayar domin tana da tabbacin Inna ce, domin idan ma ba ita bace toh anty Bintu ce domin su kadai ke da numbern ta.

Tana dubawa kuwa ta ga Innar ce, cikin sauri ta yi picking Hadi da sawa a handsfree "Ammuh!" "Ammuh!!" Muryan su Anwar ta cika wayar basu ma bari Inna tayi magana ba, siririyar dariya Aisha ta saki, hakan ya saka Abraham dagowa ya kalle ta, domin yau ne karon farko Daya ji dariyar ta haka, da alama tana matukar kaunar y'ay'an ta ya aiyana a ransa. Tuno Nonye da cikin ta yasa ya hadiyi Wani abu Mai daci a ransa, yasan cewa da ace tana raye da yanzu yar su ko dan su tayi wayo, Jin muryoyin yaran yasa Wani mugun so y'ay'a da sha'awar su ya kama shi...

"Ammar! Anwar!!" Ku bari mu gaisa da Inna ko"

"Ammar!"

Abraham ya kira sunan da harshen sa na yan Igbo, tabbas wanna sunan yaji a bakin Aysha a ranar da ta fara shigowa dakin sa, a kuma duk lokacin da ta kira sunan sai zuciyar sa ta buga, me Hakan ke nufi kenan? Ya Yi wa Kansa tambayar da bai da amsar shi.

"Assalamualaikum, Innata! Ina kwana"

"Lafiya lou diyar albarka, yakike ya aikin?"

"Alhamdulillah Inna, fatan Babu wata matsala?"

"Alhamdulillah Babu komai, ya Mai jikin?"

Dan satar kallon Abraham tayi suka hada ido, saurin dauke kanta tayi kana tace "da sauki Inna"

"Masha Allah, toh Allah ya bashi lafiya, ki mai sannu"

"Toh inna"

"Yawwa, ga yaran ki ku gaisa, sannan ki dage dayi masa rubutun Nan da bashi maganin kinji ko" Inna ta fada daga dayan bangaren tana ajiye wayar gaban su Anwar domin raba rigima, saboda matuk'ar ta bawa Daya waya toh akwai rigima kenan...

"Toh Inna nagode, Yaran albarka, kun tashi lafiya?"

Hada Baki suka Yi wurin amsawa, "lafiya kalau Ammuh!" Nan suka shiga bata labari tana biye musu har kudin Inna ya kare, ba Dan sun so ba suka hakura.

Farinciki ne ya cika zuciyar Aysha Jin muryoyin yaran ta, ajiyar zuciya ta sauke murmushi dauke kan fuskar ta, sosai take kaunar su Anwar a ranta, domin kallon y'ay'a take musu da kuma kanne da bata dasu, ta dago kanta kenan taga sun hada ido, sauke kanta tayi kasa tace "hmmm... Inna tace na Maka ya ji...." Sai kuma tayi shiru tuno cewa ba fahimtar abinda tace zai Yi ba, Abu mai sauki kawai ta dauki biro ta memo din shi ta rubuta, sannan ta hada da wayar sa dake gefen gado ta mika masa, domin sakon Inna ne dolen ta ta isar masa.

Karba yayi ya shiga app dinan mai fassara kalmomi daga Hausa izuwa turanci.

Amsar da app din ya bashi ya kura wa ido, ashe matar da bata San ko shi wane ne ba ta damu da sanin lafiyar sa haka? Amma wacce ya dauka a matsayin mahaifiya bata ko damu da lafiya da lafiyar sa ba, bama ta kaunar ganin sa a doran kasa, ashe Aysha ta dauki shi da muhimmanci har ta sanar da mahaifiyar ta rashin lafiyar sa.

"Oh God! This people are damn amazing" ya fada a ransa cikin yabon kyawun halayen su.

Dagowa yayi ya sakar mata murmushin sa mai kyau domin yaji Dadi har ransa da kulawar Inna garesa, itama murmushi tayi kana ta bar dakin.

Da misalin karfe uku na yamma madam Gloria ta fito daga gidan,, sai dai bata dauki mota ba, a bakin gate ta tsaya bayan ta fito kana ta saki murmushin mugunta a Fili tace "wanna karon ba za ka Sha ba, duk taurin ranka dole ne ka mutu a duk lokacin Dana dawo, domin a mugun shirye nake yanzu"

"Bayan kwana uku*

Cikin kwanakin Nan Abraham na Jin sanje-sanje a jikin sa, domin sosai Aysha ke kokari safe, rana, dare wurin bashi magani da rubutu.

Ranar daya cika kwana bakwai da fara Shan magani Abraham yaji kamar an yaye masa ciwon cikin Nan, sannan ko da ya Dan motsa jikin sa baya Jin zafi kamar da, tamk'ar an dauke masa dutse daga kan cikin na sa haka yake jin shi qwanin Dadi, duk da Bai gwada mikewa ba, Amma tabbas farinciki ya cika zuciyar sa, domin tunda yaci gubar Nan Bai kara lafiya irin na yau ba, dama daurewa ciwon kawai yake.

A kuma daidai lokacin ne Aysha ta shiga dakin ta domin yin sallar magriba... sai a sannan Abraham ya gwada mikewa, iKon Allah buwayi gagara misali, kamar almara lo magic haka ya mike.

"Thank you Jesus Christ" shine kalmar daya fara fita a bakin sa, yayin da husky voice dinsa ke bayyana tarin farincikin sa.

Taku uku yayi, ya sake dawowa gaban well chair din sa, kamar karamin yaro haka ya fada kan gado ya dunkule hannun sa yace "yes! Am back on my feet, Jehovah thank you, oh Lord! Thank you" Ya ma rasa kalmar da zan fada saboda tarin farinciki, gaban gadon ya dawo yayi kneel down worship song na christian ya shiga Yi kana ya Dora da addu'a, bayan ya gama ya mike ya shige toilet, domin tsaftace jikin sa.

AYSHA Bayan ta iddar da sallah ta sauko kasa domin karasa musu abincin dare, yau kam ta makara bata gama da wuri ba, Allah ya taimake ta Madam Gloria bata nan, da ta banu a hannun ta yau.

Sai da ta sake daukar wasu mintuna ashirin a kitchen din sannan ta gama, had'add'en spaghetti🍝 da miyar stew Daya Sha zallan sokan namomi ta girka, ta zuba masa a warmer, sannan ta daukar masa lemo da ruwa ta nufi dakin sa, kamar kullum bakin ta dauke da sallama ta tura kofar dakin ciki....

Sam bata lura Babu shi kan wheelchair din sa ba, sai da ta ajiye abincin a centre table kana ta dago kanta taga wayam Babu shi...

Readers Also Read