Kenza eBookz

Abraham complete by nooreemaan - Chapter 15

Abraham complete by nooreemaan - Chapter 15

Abraham complete by nooreemaan Chapter 15: Abraham complete by nooreemaan Chapter 15. Gabanta ne ya fadi ganin Babu shi kan kujerar sa, "toh Ina ya tafi?"…

3,333 words

Gabanta ne ya fadi ganin Babu shi kan kujerar sa, "toh Ina ya tafi?" Ta San dai ba tafiya yake ba bare tace ko Wani waje ya tafi, gabadaya k'wak'walwarta ya toshe, hawaye suka cika idanun ta, kamar status haka ta tsaya bata motsa ba.

Wani sanyayyar kamshi taji ya bugi hanci ta, hakan yasa ta waiwaya da sauri, fidda manyan zararran idanunta tayi waje, cikin zallan mamaki da al'ajabi sak'amak'on abinda ta gani.

_hey fans! Hope you all enjoyed this episode? let me know In your comment_

Share fisabilillah

Comment

✨NoorEemaan✨ 07082281566

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 0806626851 [10/13, 12:30 PM] 💖NoorEemaan💖: 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇 ABRAHAM 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇

*First edition*

*WATTPAD* @NoorEemaan

https://facebook.com/groups/943534712916776/ Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.

*Powerful Dua Please Don't Ignore Or Skip*

Ya ubangiji Kaine kake azurtawa ka azurtamu da rabo Mai albarka, ka yafe mana ya ubangiji, ka haskaka zukatanmu da alkhairi ka biya bukatunmu na alkhairi kasa mu cika da kyau da lmani, ya ubangiji ka tsare mu daga aikata barna da aikin dana sani ka tsaremu daga saba maka ya ubangiji, kasa mufi karfin zuciyoyinmu da kuma sharrin shaidan, ya ubangiji ka tsaremu daga biyewa zuciya ka rabamu da aikin dana sani ka sanya mana tausayi da juriya da hak'uri a zuciyoyinmu. Ƴa ubangiji duk Mai neman haihuwa da Mai bukatar aure darajar wannan watan Mai albarka ka biya wa kowa bukatar shi ta alkhairi, ya Allah Wandanda suke da auren ka zaunar dasu lafiya, ka basu farin ciki da yiwa junansu adalci tare da rike Amana da kuma biyan hakkin aure dake kansu, ya ubangiji ka karemu, ka yafe mana ka yi mana arziki ka mana budi mafi alkhairi a rayuwar mu ka yafe mana, ka sanyaya zuciyoyinmu ka rabamu da aikin dana sani, ya ubangiji ka biyawa kowa bukatar shi ta alkhairi.

Chapter 51-52

Abraham tsaye kan kafafun sa cikin shigar kananun kaya Yana kallon ta fuskar sa a sake, ja baya ta shiga yi, ta kasa yarda cewa Wanda ta bari kan keken guragu ne mintuna kadan da suka shude ne ke tsaye yanzu kan kafafun sa yanzu, ganin kamar da tsoro a tare da ita yasa Abraham zama a bakin gado, dama kafar sa bata gama kwari ba saboda watanin Daya diba a zaune bai taka ba.

"Da gaske shine ko kuma gizo idanuna ke mun? Ya rabb!" Ta fada a bayyana tana sulale kasa, sai kuma ta saka kuka, Wanda na zallan farinciki ne, tabbas tayi masa murnan samun lafiya, Amma har yanzu al'ajabi da mamaki bai sake ta ba, domin ba ta taba tunanin ko kawo wa a ranta cewa zai warke Nan kusa ba.

Jin kukan ta yasa shi dago Kansa da sauri, mamaki yake meya sa ta kuka haka all of a sudden, tabbas ba ta cancanci kuka ba a yanzu da yake da damar ba ta hakuri ba, domin ita din haske ce cikin rayuwar sa, sannan Mai zuciyar taimako, bai taba zama da mace Mai kyawun hali kamar ta ba, duk da karancin shekarun ta. Hakika bazai taba manta alkhairi ta gareshi ba, so yake yayi magana, amma rashin jin yaren juna yasa shi kasa yin maganar da ya yi niyya.

"Shhhh!" Yace yana dora hannun sa kan lips din sa, yayin da ya kura mata sexy eyes din sa.

Shiru tayi kamar ruwa ya cinye ta, cikin sanyi da calm voice yace "is alright, stop crying ok?"

Duk da bata fahimci abinda yace ba, haka ta shiga daga masa Kai da sauri...

"Good girl" yace Yana Dan sakar mata murmushin sa Mai kyau, Dadi taji a ranta, Hakan yasa ita ma ta mayar masa da martani, littafin da suke yiwa juna magana ta dauko kana ta rubuta "na Maka murna yallabai da dawowa kan kafafun ka, Allah ya kara lafiya, ya kuma tsare gaba"

Tana gamawa ta ajiye a kusa dashi kana ta fita daga dakin cikin takun nutsuwarta, da kallo ya bita har ta fita kana ya dawo da idanun sa kan takardun bayan ya shiga app dinan ya Yi typing, fassasar abinda ta rubuta da turanci ya fito...

Sau uku Yana karanta rubutun kana ya yi murmushi, ya kuma ji dadi a ransa, saboda shi mutum ne dake matuk'ar son a nuna masa kulawa, ajiye takardan yayi sannan ya mike ya fice daga gidan gabadaya, duk da cewa dare yayi Amma Yana son fita ya tattaka kafar sa, bayan ya fito ya hadu da Mai gadi, zaune a bakin aikin sa...

Hannu Abraham ya daga wa Mai gadi ganin irin kallon da yake masa, Mai gadi kuwa cikin sauri ya nufo shi da cikin zallan mamaki da farinciki, sai da yazo daidai gaban sa ya ja ya tsaya sannan ya dan taba shi yace "ya salamullahi! ashe kai din ne da gaske oga, ba shakka Babu abinda ya gagari ubangiji, gaskiya oga I dey happy for you well well, Kai congrats, congrats Mai gidana" ya karasa cikin gurbatacciyar turancin sa.

Murmushi Abraham yayi, kana yace "Thank you" sannan ya fita ta karamin gate, ganin shi a waje yaji Wani yanayi Mai Dadi na ratsa shi, domim robon shi da waje har ya manta, sosai zuciyar sa ke cike da farinciki.

Mai gadi na kiran "oga ba zaka fita a mota ba?" Amma bai samu amsa ba, domin yallabai Abraham har ya gama ficewa.

Tafiya ya cigaba da yi a hankali cikin nishadi har yazo babban titi, sannan ya samu mai Keke napep ya tara ya shiga.

Supermarket dake kan hanyar da suka dauka ya sauka, ya biya mai dan sahu sannan ya shiga ciki, abubuwan amfanin sa da babu ya Siya, domin yana Shirin yin shopping ne dama ya ji gubar nan, har ya nufi wurin biya sai kuma ya dago da baya, haka kawai ya ga ta cancanci ya Yi mata shopping ita ma, duk da Bai San abubuwan da take so ba.

Man shafawa, shower gel, Dan karamin makeup kit da kuma ice cream babban roba ya daukar mata, yayi transfer kasancewar Babu ATM cards dinsa a tare da shi, bayan ya fito yaga a Wajen supermarket din ana siyar da gashashen kifi ya siyi Leda biyu, sannan ya kara tarar Mai Keke napep ya hau, inda tafiyar mintuna goma Sha biyar ne suka kawo shi kofar gida, Dari biyar din da ta rage a aljihun wandon sa ya bawa Mai napep kana ya shiga gida, Yana Jin Mai Keke na masa godiya domin ka'idar kudin sa 300 ne.

Mai gadi ya mika wa Leda Daya na kifi inda ya dinga Yi masa godiya, Amma Abraham Bai ko juyo ba, domin shi mutum ne da Bai son yayi abu a dinga Yi masa godiya.

Bayan ya shiga general falo, ko ina shiru babu motsin komai sai na Karan AC, sai kuma TV dake aiki shi kadai, remote ya dauka ya kashe Tv'n sannan ya fara hawa step case domin isa dakin sa.

Da shigar sa dakin sa kuwa ya ajiye kayan duka kan gado kana ya shiga toilet ya sake watsa ruwa yayi brush, sannan ya fito ya shirya cikin pyjamas blue black ya fesa body spray kana ya zauna a bakin gado, nannauyyar ajiyar zuciya ya sauke, yana kara gode wa Allah a ransa, hakika duk wanda yake da cikakkiyar lafiya ya dinga godewa Allah kullum, komai Taulacin sa kuwa, domin gashi Yana da Arziki da dukkanin ababen more rayuwa, Amma baya Jin dadin su saboda tafiyar da baya iyawa.

" Thank you lord, Thank you jesus!" Abraham yace a hankali.

Idanun sa ne ya sauka kan abincin da Aysha ta shirya masa, dan yamutsa fuska yayi, cikin sa dake lafe masu dauke da manya-manyan six packs ya shiga shafawa a hankali, k'watak'wata baya Jin yunwa, domin farinciki daya cika zuciyar sa.

Kallon ledojin daya shigo dasu yayi, ganin bata shigo ba yasa shi kwashe siyayyar daya Yi mata ya nufi dakin ta, ƙwanƙwansawa yayi ba tare da kuma ya Jira ta bashi izinin shigowa ba ya tura kofar ciki...

Zaune ya hangon ta kan sallaya, hannun ta a sama tana addu'a, yayin fuskar ta ya nuna farinciki, ta burge shi kwarai, musamman kwayar idanunta fare kal da suke kallon sama, sannan yanda ta bawa addnin ta muhimmanci ya burge shi ainun, domin ko kallon inda take Bai yi ba, bare ta damu da wanda ya shigo, addu'ar ta ta cigaba da yi, duk da cewa taji shigowar shi, janye idanun sa yayi kana ya ajiye ledojin ya fita...

*30Minutes later* A hankali Aysha ta shiga cire hijab dinta, tana sakin murmurshi, Dadi sosai take ji ganin Abraham ya warke, so take ta kira Inna ta mata albishir sai ta kuma ta Yi tunanin sun yi bacci, haka ta hakura da tunanin gobe zata kira ta.

Ledojin ta bude ta fito da abubuwan ciki, duk da bata furta ba, Amma tayi farinciki da siyayyar da ya Yi mata, kifin da Ice cream ta ajiye a gabanta ta shiga ci, domin dama ita Mai son kifi ce, sosai taci har ya rage dan kadan, sannan ta Sha ice cream kwatan roban. Bayan ta gama ta shiga toilet ta wanke hannunta, sannan ta sake Yin brush saboda Karnin kifin, rogowar Ice cream da kifin ta dauka ta sauka kasa ta ajiye ice cream a fridge, ragowar kifin kuma ta ajiye a kitchen, sannan ta koma dakin ta ta yi Shirin kwanciya ranta fari kal, tana Jin farincikin da ta jima ba tayi irin shi ba.

*** *** ***

*BANGAREN ANTY SARAH*

Zaune take a madaidaicin dakin ta, ta Kara lalacewa yayin da tsufa ya bayyana karara a fuska da jikin ta, musamman da babu gyara da ingantaccen abinci, muskutawa tayi sannan ta zabga tagumi, mafarkin da ta Yi kan Nonye yau ya kara firgitata, burinta ta hada yan kudin mota da zai ishe ta domin taje Imo state, Abraham kadai zata nema, domin ta tono asirin dake boye sannan su nufi gombe gidan da ta ajiye yaran ta gudu, domin shi kadai ne hanyar dazai sa ta samu dan kwanciyar hankali, ta sani cewa ita da samun kwanciyar hankali Mai dorewa sai Wani iKon Allah domin kashe rai ba abun wasa bane.

*Bayan kwana biyu* _2:30am_

A yanda take kwance da kuma yanda take shura kafafun ta zai tabattar Maka da cewa, mafarki mara dadi take...

A firgice ta farka, gumi sai tsatsafo mata yake, gaba Daya ta jika yar T-shirt din jikinta daya gama tsufa saboda dadewa, "zan tona asirin da muka dade da binnewa, Dan Allah kiyi hakuri Nonye, Wayyo Allah ka taimake ni na tuba" Anty Sarah ta fada da yaren Igbo cikin fitar hayyaci...

**********

Da safe a sanyayye take komai domin mafarkin da ta yi Yana makale a ranta, gashi kudin bai taru bare ta tafi yau, Yan kayan abincin da take samu a gona ta dauka, sannan ta nufi makotan su, ta siyar musu a raha, musamman da suka ga tana da bukatar kudi, hakan yasa suka mata tayin wulakanci, Amma bata da zabi Daya wuce ta siyar din, domin a gobe take son tafiya. Amma abin daya bata mamaki a yau shine lami lafiya ta kwanta bata yi mafarki ba.

Da misalin karfe shida na safe ta dau hanyar Imo state, sun yi tafiya mai tsayin zango sannan ta sauka a tasha, taxi ta tara ta shiga sannan tace ya kai ta wordbank estate...

Bayan sun iso, ta biya shi kudin sa sannan ta sauka, kallon gidan ta shiga yi, har abada bazata taba Manta gidan nan ba, yana nan yanda Yake sai Dan abinda ba a rasa ba aka Sanja, sosai abubuwa da dama suka shiga dawowa brain din ta, musamman mugayen Abubuwan da suka aikata, hawaye ta share na nadama, sannan ta karasa jikin kofar gidan ta shiga k'wank'wansa wa a hankali, mintuna biyu kacal Wani katon mutum Mai sanye da blue da black uniform ya Bude kofar Yana muzurai...

"Madam how may i help you?" Ya fada da k'akk'auran muryan sa mai amon sauti.

Cikin rawar baki Anty Sarah ta ce....

Share fisabilillah☑️ Comment ☑️

NoorEemaan 07082281566

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 0806626851 [10/13, 12:59 PM] 💖NoorEemaan💖: 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇 ABRAHAM 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇

*WATTPAD* @NoorEemaan

https://facebook.com/groups/943534712916776/ Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din

Page 53-54

"'ple.... p...le...ase can i see your boss, i mean Abraham"

Cikin rashin fahimta mai gadi ke kallon ta, domin iya sanin sa ba sunan uban gidan sa Abraham ba, ita kuma Anty sarah ta gane shi tsaf domin shi ne dai mai gadin Abraham na da, amma bata nuna ta gane shi ba.

Shiru mai gadi yayi kamar yace batan gida tayi, sai kuma yayi saurin cewa "oh! Oh!! Oh!!!" Alamun ya tuna Abraham tsohon mai gidan sa, nan ya shiga bawa Anty Sarah labarin tashin sa daga garin ba kuma ya san ina suka koma ba, yana gama bata labari ya rufe gate din ya ruga cikin gidan da gudu sak'amak'on kiran da matar gidan ke masa.

Anty Sarah sulalewa kasa tayi ta ɗora hannun ta akai ta sa kuka mara sauti yayinda hawaye ke sulalowa daga idanun ta, gwanin tausayi, ita kam ina zata je? Ta ina zata fara neman su a fadin duniyar nan? Ta jima zaune a wajen cikin rashin sanin abin yi, ga duk wanda zan wuce sai ya dinga kallon ta, hakan yasa a sanyayye ta mike ta shiga tafiya domin komawa garin su....

••• ••• •••

Zaune yake a had'add'en office din sa dake cikin ma'aikatar sa, yau kwanasa uku da dawowa aiki, inda sosai ma'aikatan sa suka yi murna da dawowar sa.

A shirye yake cikin suit baƙi, sosai hakan ya fito da kwarjinin sa hadi da haibar sa, Google ya shiga yayi searching wani abu sannan lambar dake karshen rubutun ya dauka, wayar sa yasa ya danna kiran lambar, magana biyu zuwa uku ya ajiye wayar, sannan ya mike ya dauki key din mota da waya, sake gyara zaman rigar sa yayi, murya kasa-kasa yace "yeah! I guess this is the only solution" ya karasa fada yana bude kofar office din ya fita, parking space dake company ya nufa ya shiga Mota, security da masu gadi na masa a dawo lafiya, hannu kawai ya daga musu kana ya fice...

Tafiyar mintuna arba'in ya kawo shi babban ginin mai dake da rubutun *MM HARUNA ENGLISH ACADEMY* kallo daya yayi wa ginin kana ya dauke kansa, lambar dazu yayi dialling, bayan anyi picking ya fada musu yana wajen ginin...

Mintuna uku kacal wani matashi ya fito, cikin girmamawa ya gaishe da Abraham, fuska a sake Abraham ya bashi hannu ya suka yi musabaha, sannan suka jera cikin wajen, office din shugaban su matashin nan ya nuna masa kana ya koma...

Bayan sun gaisa da shi, Abraham yayi gyaran murya yace "am.... I want to register a girl here, i don't mind to pay extra money if she can be fluent in speaking English" Ya karasa Yana dan bugu teburin office din da yatsun sa biyu a hankali, bai sani ba ko Aysha zata yi na'am da wannan makarantar ta koyan turanci da zai sa ta ba, kawai yana so ta iya ne domin ya saukaka musu wajen magana da juna, ya lura cewa bata yi karatun boko ba, matuƙar ta bashi hadin kai, tana kuma kaunar karatun zai bata dukkan wata gudunmawa domin ta cigaba, domin tana daya daga cikin halittun da bazai iya taɓa mantawa ba a rayuwarsa, shiyasa take da dubbin darajar a idanunsa.

Maganar shugaban makarantar ce ta sa shi daga kansa, sannan ya daina buga yatsun sa kan teburin, cikin turanci mutumin yace... "In Sha Allah zaka yi mamaki yanda zata kware a fannin turanci, karka damu, sannan kamar yadda kace za ka iya ƙara kuɗi domin ta fi saurin kwarewa. Toh zan yi making arrangement a saka ta a special class domin a koya mata komai yanda ya kamata, sannan yace zata iya farawa ranar juma'a, tunda yau Laraba, domin dama kwana uku kaɗai ake karatun juma'a, asabar, da Lahadi"

Hannu Abraham ya bashi suka yi musabaha, sannan ya biya dukkanin kuɗin da ake bukata, sannan aka bashi Form ya cike mata sannan a yi attaching passport din ta da filling foam din, karba Abraham yayi, domin bai san sunan ta ba, bare ya cike mata, baya ga haka ma babu passport din ta a wajen sa, hakan yasa ya karbi Form din yace zai je gida ya cike gobe zai dawo dashi, da haka ya bar wajen

Bayan ya koma office, babu jimawa P.A dinan na shi ya shigo bayan ya bashi izinin shigowa, a sake suke tattauna da Abraham kan abinda ya shafi business din su musamman da bayan nan, yana masa bayanin komai da komai, bayan sun gama maganar business din yace "boss!" Abraham ya dage girar sa alamun amsawa. "Wallahi matar ka tana da kirki sosai"... Dan waro ido Abraham yayi saboda mamakin kiran kalmar *mata* da personal assistance din sa yayi, shi kuwa P.A bai lura da yanayin fuskar Abraham ba, nan ya shiga bawa shi labari tun daga zuwan sa gidan da karramawar da Aysha tayi masa, sannan maganar da suka tattauna kan yana k'asar waje, komai dai bai boye ba...

*Some minutes later* Bayan fitar P.A "What!" Abraham yace Yana sakin murmushin gefen baki, "so this Hausa girl is smart as this, oh my goodness" sosai ta burge shi, musamman karkashin ta, dakewar ta, hadi da boye rashin lafiyar sa da ta yi, ya jima yana tunanin a kanta da irin hallacin data yi masa...

••••••• ••••••• ••••••

Da misalin ƙarfe hudu ya bar company'n sa zuwa gida. Biyar saura mintuna k'alilan ya iso gida saboda dan hold up dake hanya, a parking space ya faka motar sa, kana ya fito rike da brief case din sa, har ya fara tafiya ya tuna da Form din, ya kuwa ya d'auka sannan ya nufi cikin gidan.....

Kamar kullum fakon shiru sai plasma dake aiki she kad'ai, kamshi yaji ya bugi hancinsa wanda ya tabbatar masa da cewa tana kitchen kenan, bai ce komai ba, ya haura sama, bayan ya ajiye Form dinan a dining table ya ɗora remote control akan takardan.

_7:55pm_ A daidai lokacin Abraham ke saukowa sanye da fararen kaya na shan iska da suka yi matukar karban chocolate skin din sa, kan dining table ya zauna, yana jiran Aysha tazo tayi serving din sa, domin sosai ya fara jin yunwa tun abincin safe, a hankali ya daga kansa ya kalli sama, a ransa cewa kila sallah take yi.

Bayan mintuna goma ya ji takun tafiyar ta, sanye take da hijab ja har kasa, yayi matukar karban farar fatar ta, tamkar wata zinariya haka ta yi kyau.

Kallon ta Abraham ke yi, maganganun da P.A yayi masa ke dawowa ƙwaƙwalwar sa, innocent face dinta ya ke kallo, ba tare da sanin sa ba, murmushi ya subuce masa, tana da sanyi sosai, yayi mamaki kwarai data samu kwarin gwiwa har haka.

Gefen sa ta tsaya tace " sannu da zuwa! Ina wuni"

Daga maka kai kawai yayi, domin bai ji abinda tace ba, kwara ina kwana yafi gane mai, Aysha bata kara cewa komai ba shiga serving din sa, bayan ta gama ta fara kokarin barin wajen.

"Hey! Sit" yace Yana nuna mata kujeran dining table, a sanyayye ta dawo ta zauna, alamu yayi mata kan taji abinci, girgiza masa tayi sannan ta motsa kananan lips dinta tace "Na koshi"

Readers Also Read