Kenza eBookz

Abraham complete by nooreemaan - Chapter 16

Abraham complete by nooreemaan - Chapter 16

Abraham complete by nooreemaan Chapter 16: Abraham complete by nooreemaan Chapter 16. Bai kara magana ba ganin har ta fara raurau da idanu, sai da ya ci…

3,296 words

Bai kara magana ba ganin har ta fara raurau da idanu, sai da ya ci fiye da rabi sannan ya mika mata wata takarda, Domin kafin ya sauko ya shiga app dinnan, yayi typing da turanci kan bayanai abinda za a cike Form da shi, abun ya fito da amsa da turanci, ya yi coping a paper, idan ta rubuta masa, she kuma sai ya cike mata Form din da kansa.

Duk da tayi mamakin mezai yi da sunan ta, shekaran ta, da sauran personal details dinta, amma bata tambaya ba ta shiga rubuta komai a inda ya bar space gashi rubutun da Hausa wanda Hakan yayi mata sauki kwarai...

Bayan ta gama rubutuwa ta lura da wasu rubutu still da Hausa a kasan takardan "Ban san yanda zaki dauki abun ba, amma na saki a wata makaranta ta koyan turanci, inda zaki dinga zuwa juma'a asabar da Lahadi, gobe zamu je ayi miki passport idan na dawo, amma idan bakya so zaki iya fadamin"

A hankali ta dago kanta fuskar ta dauke da murmushi, kasancewar ita yake kallo yasa shi ganin murmushin, wani sanyi yaji a ransa, hannayenta ta dage alamun godiya kana tace "Nagode sosai, Allah ya saka...."

Hannun ya ɗora a lips din sa alamun tayi shiru, saboda ya fahimci godiya take kokarin masa.

Bayan ya gama ya sha lemo sannan ya janyo Form din da abinda ta rubuta ya shiga cike mata. Aysha kuma ta mike ta gyara dining table, sannan ta kai plate da cups da yayi amfani dasu ta wanke kana ta fito... "sai da safe" tace tana hayewa sama, bai je komai, domin bai fahimta ba, sai bin ta da ido yayi har ta bacewa ganin sa...

Numfashi ya furzar, kana ya kai idanun sa kan dakin Madam Gloria, wani abu ya daki zuciyarsa tuno wacce mummy, domin sai Yanzu ainihin hallayen ta suka bayyana, ashe duk zaman da suke fuska biyu ce! Bai sani ba, bata kuma taɓa nuna wata alama ba, ganin ransa zai fara ɓaci yasa shi daina tunanin Madam Gloria, sannan ya raya a ransa cewa da safe kafin yaje office zai biya bank ya sanja pin account din sa, saboda a ranar data kwashe ATM din duk yana jin ta, dama pretending baccin karya yayi...

Yana jima a zaune yana sake-sake kana ya kashe duka kayan wutan dakin da plasma ya nufi dakin sa domin bacci...

*WASHEGARI* Hudu saura mintuna takwas Abraham ya dawo, domin ya yi alƙawarin cewa yau zasu je tayi passport, cikin dan sauri-sauri yake tafiya. Dakin sa ya shiga dake a kimtse gwanin burgewa sai kamshi ke tashi, kayan jikin sa ya cire, daura towel, sannan ya jefa wanda ya cire a laundary basket kana ya shiga wanka, mintuna goma kacal yayi ya fito ya shiga shiryawa...

Bayan ya gama ya fito, har zai leka dakin ta ya kira ta, sai kuma ya hango ta zaune a downstairs, da alama shi take jira, bayan ya gama saukowa ba tare da ya kalle ta ba yace "let's go"

Duk da bata gane abinda yace ba, amma haka ta bi bayan sa ganin ya nufi waje, sai Yanzu take jin son turanci a ranta, musamman da Abraham ke yi, domin sosai take dad'i a bakin sa...

Har zata shiga baya, taga ya buɗe mata gaban motar, ba musu ta shiga ta zauna. Wani babban gidan hoto Mai suna *INFINITY* ya kawo su, Bayan yayi parking, kusan a tare suka fito daga motar, cikin wajen suka nufa, cikin girmamawa ake karɓe su, nan mai yin passport din ya sanar dasu cewa passport takwas 3,500 hake yake yin sa...

Wani had'add'en dakin hoton aka shigar da Ita, mintuna biyar ta fito ta zauna gefen kujerar da aka tanadar wa Abraham two sitter.

Bayan an gama hada komai aka saka mata envelope, Ya mika mata, karba Aysha tayi ta ɗan buɗe ta ga yayi kyau sosai kamar dai hoto normal saboda haduwar sa.

Maimakon su koma gida sai ta ga ya nufi wani restaurant yayi musu takeaway, domin sam Yau baya son tayi girki, yana matukar ganin kokarin ta wajen iya girki da kula da gida tamkar babbar mace, at least once in the while ya kamata tana hutawa.

•••••. ••••••. •••••

MADAM GLORIA Tafiya take cikin wani kusurmin daji mai matukar ban tsoro da abubuwan al'ajabi kala ² tun jiya take tafiya amma har yanzu bata kara so inda take so ba, ko wahala bare tsoro bata ji saboda mugun nufin daya cika zuciyar ta...

Tana cigaba da tafiya taji wata murya ta fara dariya cikin wata amo mai ban tsoro hadi da ruda ƙwaƙwalwar mutum, juye juye ta shiga yi ko zata ga mai dariya amma bata kowa ba, can kuma dif cikin wata murya da amon sa ke fidda zallan fushi taji an ce....

Share

Comment

NoorEemaan 07082281566

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 0806626851 [10/13, 1:15 PM] 💖NoorEemaan💖: 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇 ABRAHAM 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇

*First edition*

*WATTPAD* @NoorEemaan

https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din

Chapter 55-56

Tana shiga cikin fadar bokan nan mai sunan Nandera, ta ga macizai iri daban-daban na ta shawagi a cikin fadar.

Wani sabon tsoro ne ya sake kamata, domin duk bakin halinta idan akwai halittar da take matuƙar tsoro toh bai wuce maciji ba.

Kasa gaba bare baya tayi, sai k'ak'arwa jikin ta ke yi kamar an jona electric shock, domin macizan har zagaye ta suke, ba tare da sun mata komai ba.

Wannan karon wani abu mai kama da danasanin zuwa wajen boka Nandera take, ba wai kuma saboda Allah tayi danasanin ba, sai dan tsoro.

Boka Nandera dake zaune kansa a kasa ya fara sakin wata mahaukaciyar dariya mara daɗin amo, wasu Surutai ya shiga yi tsahon Mintuna biyar sannan macizan nan suka koma wani gefe suka lafe, basu ƙara motsi ba.

Bakar fuskar sa mai dauke da kasumba abin k'yank'yami ya d'ago, sannan ya kalli Madam GLORIA da jajayen idanunsa yan ƙanana yace "karaso da baya ki shigo fada ta mai cike da abubuwa iri daban-daban, hhhhhh"

Jiki na rawa Madam GLORIA ta karaso da baya ta zauna a gaban boka Nandera kamar yadda yace.

Gaba-daya ta birkice, sai faman waiwayon macizan dake gefe take, domin gani take da ta daina kallon su zasu kawo mata sara.

"Ke nutsu! Babu abinda zasu miki sai na basu umarnin haka, hhhhhh" ya fada cikin ƙatuwar muryan sa.

Dan nutsuwa tayi, cikin dake wa ta shiga mai wasu kirari da manya- manyan kalamai. (a'uzubillah!)

Boka Nandera kuwa sai faman buɗe kafada yake cikin takama da isa hadi da jin dadi.

Bayan ta gama boka yace " hakika na jima ba a min kirari irin wannan ba, hakan yasa zan yi miki aiki mai zafin gaske, duk wahalar da kika sha shekara da shekaru wurin hallaka dan kishiyar ki yazo karshe"

"Toh ya...."

"Kada kice komai, nasan matsalar ki, na kuma san abinda kike so, saboda haka ki jira ki ga abin mamaki, ba a cika ni da tambayoyi, sannan zamu rike ki na tsawon wata Biyar da kwanaki a nan, haka ka'idar aikin yake, hhhhhh"

Azabure Madam GLORIA ta kalle shi, tana maimaita wata shidan a ranta, yayi mata mugun nisa, tamk'ar shekara dubu sittin haka take ganin su saboda muradin cika Burinta"

Dago kanta tayi domin yin magana ko zai rage watanni saboda a gaskiya wata shida yayi mata mugun nisa, sai dai tana dago kanta suka hada ido da boka ta kasa magana.

Boka kuwa ganin ya samu nasara ya shiga sakin dariya da ƙatuwar muryan sa mara daɗin ji.

*KADUNA* Zaune Abraham yake cikin motar sa a daidai building din MM HARUNA ENGLISH ACADEMY yana jiran Aysha ta fito, haka kawai yau yaji shi ya cancanci yazo ya dauke ta, kasancewar driver ke zuwa kai ta ya kuma dauko ta, dalibai sai wucewa suke, amma bai ga Aysha ba, har ya fara kosawa da zaman, sannan ya hangota ta mirror tana tafiya Cikin nutsuwar ta.

Kasa ɗauke idanunsa daga kanta yayi, duk da cewa yau kimanin sati biyu da fara zuwa makarantar ta kenan, amma yana ganin improvment daga gare ta, musamman yanda take dagewa wurin tilawar abinda ake koya mata, duk da cewa har abubuwan yan primary one ana koya mata domin ta fi gane wa sosai, amma yana ganin kokarin ta kasancewar bata taɓa zama a ajin boko ba.

AYSHA Sai faman kalle kalle take ta ina zata hango driver, Sam bata ma lura da motar Abraham ba, shima ya fahimci hakan, sai ya zuge glass din window ya leko da kan sa, karaf suka hada ido, zaro idanun ta tayi saboda mamaki ganin sa, domin bata taɓa kawowa a ranta cewa zai zo daukar ta ba.

Dayan bangaren ta zagaya ta shiga ba tare da tace komai ba, shima bai ce komai ba ya tada motar suka bar haraban wajen.

Bayan sun iso gida Aysha ta buɗe motar, ta saka santala-santala kafafunta kasa sannan ta waiwayo ta ɗan rusuna kanta tace

"welcome tank" (ita nufin ta so take tace weldone thanks)

Jinjina kan sa kawai yayi yana matse dariyar sa, sannan ta fita izuwa cikin gida.

Ajiyar zuciya kakarfa ya sauke a lokacin daya daina hango ta.

Wasu lokutan yakan ji wani iri musamman idan ta kama shi yana kallon ta, amma ya kasa daina kallon ta, ya sani cewa ba wani abu ke burge shi a jikin ta ba bare ace shi yake kallo, domin idan diri ne bata kamo Chinonyen sa ba, amma kuma baya kallon Nonye kamar yadda yake kallon Aysha, ya rasa dalili, sai dai a kullum idan yana tambayar kansa game da yawan kallon da yake mata, his heart always tells him that hallaci da kyawun zuciyar ta yake kallon deep inside her.

Amma abinda Abraham bai sani ba shine ya kamu da son Aysha tun daga ranar da suka fara haduwa a adaidaitasahu, a kuma ranar ne zuciyar sa ta fara bugawa domin ta.

Haka ya kwashe tsawon mintuna a motar sannan ya kashe motar ya fito, direct dakin sa ya wuce, ya fada kan gado yana tunanin rayuwar sa, kewa sosai yake ji yanzu musamman da babu wani nasa da zai gani ya ji dad'i, dan ma Aysha na gidan yana ganin Allah ne ya kawo ta cikin rayuwar sa, ta masa abubuwan da ko wani dangin sa bazai iya masa ita ba, duk da cewa yana biyan ta Albashi...

Numfashi ya furzar tuno cewa kusan wata daya rabon da mummy ta bar gidan nan kenan, "where is she?" ya tambayi kansa, sanin ba shida amsa yasa shi lumshe idanun sa yana fitar da numfashi daya-daya.

Har lau yana jin mummy a ransa, yana mata kallon uwa da bai da shi, duk da cewa bai san dalilin ta na son ganin ta kashe shi ba, amma yana kokarin matuka gurin ganin ya cire ta a matsayin uwa daya ɗora mata, domin babu wata uwa ta gari da zata zo kashe danta.

Aysha dake kitchen tana girki kuwa kusan tunani ɗaya suke yi, ita mamakin wannan abu take, ace uwa ki fita ba tare da kin damu da sanin halin da ɗan ki ke ciki ba, shi ma daya warke, bai nema ta ba, kanta ya kulle ta rasa gane kan abun nasu, ganin wannan abun bai shafe ta ba ne yasa ta ta6e baki ta cigaba da hada masa had'add'en fish pepper soup daya ji vegetable da spices, sai pure orange juice da zata hada masa.

Wanna kenan!

•••• •••• ••••

*BAYAN WATA BIYAR DA KWANA GOMA*

Cikin wadannan watannin abubuwa da dama sun faru, ciki har da zuwan Anty Sarah Gombe gidan su Aysha, ko Allah yasa mutanen su taimaka mata wajen tayata neman Abraham, domin cikin watannin nan ta sha wahala gaba-daya ta sake fita a hayyacin ta, sak'amak'on yawan mafarke-mafarken ma rasa kyau da take yi, har abun ya fara mata gizo, gaba-daya ta rasa nutsuwar ta, hakan yasa ta zo Gombe, sai dai abin mamaki duk bulayinta ta kasa gane gidan, unguwar ya sanja mata, komai ya kwance mata, amma bata hakura ba...

Kullum daddadare sai ta je kasan gada in da mahaukata da masu Bara ke kwanciya, nan take shiga Cikin su ta kwanta, washegari ta kuma cigaba da neman gidan amma bata samu ba, amma still bata hakura ba.

***. ***. ***.

*KADUNA*

"Aysha! Aysha!!"

A hankali Aysha ta waiwayo da murmushi saman fuskar ta domin ta san mai kiran ta.

Ta kara kyau, girma, da wani wayewa daya bayyana ƙarara a tare da ita, komai yanzu cikin aji da wayewar addini take yin sa, saboda mu'amala da mutane musamman yammata iri daban-daban hakan yasa komai tayi tana burge mutane, gashi yanzu ta kara ilimi sosai, turanci daidai gwargwado tana yi, tana kuma ji, kana tana tana iya rubutawa, tsakanin ta da Abraham yanzu babu musayar rubuta da takarda, ta kan yi mai magana da turanci shima idan yana bukatar abu zai fada mata da turanci.

hakika MM HARUNA ENGLISH ACADEMY sun yi kokari matuƙa wurin koya wa Aysha turanci, musamman da suka ga Abraham ya sake musu kudi...

"Aysha! Why are you so In hurry, Ina zaki haka?"

Bola da ta kasance yar ajin su ta fada. Ta su ta zo daya da Aysha sosai, duk da kasancewar Bola bayerabiya amma musulma ce, tana amfanin da sunan Yaren ta ne a makaranta, kasancewar tun tana karama da sunan aka fi kiran ta.

"Bola! my boss is coming back from Dubai today, i have to rush home so that I can made him some meals"

"Oh yeah i remember, that's nice, shall well?" Bola ta fada tana mata nuni da hanya alamun su cigaba da tafiya...

Yanda Bola tayi da hannu sai ya bawa Aysha dariya...

Nan suka cigaba da hira har suka zo wajen driver, suka yi sallama da Bola, Aysha kuwa ta shiga Mota suka nufi gida.

Tana zuwa gidan jakar makarantar ta kawai ta ajiye ta shiga kitchen, tunani tayi tunda yaje dubai kusan wata ɗaya tasan ba lallai ya samu abinci irin na nan Nigeria ba, hakan yasa tayi tunanin dafa masa abinda zai rike cikin sa sosai, had'add'en miyar efforiro tayi masa daya sha namomi da ganda, sákwárá take son Yi Amma Allah ya gani bata da karfin dakawa, hakan yasa ta tuka masa *pando yam* na leda, ai kuwa sak sákwárá haka yayi danko ya kuma yi kyau, bayan nan tayi masa pepper chicken, ta zuba komai ta jera a dining table sannan ta gyara kitchen.

Dakinta ta nufa domin yin wanka saboda har an fara kiraye-kirayen Sallah....

A gurguje tayi wanka ta shower gel wanda Abraham ya siyo mata, har yanzu bai kare ba domin bata fiye amfani da shi ba, gashi 2.5L ne gashi da kumfa sosai, ita kam bata fiye son shower gel ba, sai mita take a ranta wai sabulun nan bata son shi sai ya yi ta sa jikin mutum sulbi kamar tayi wanka da klin ko da ruwan sama.

Bayan ta iddar da sallar ta sauko falo ta zauna shiru, so take ta kira Inna amma kuma bata son damun su, saboda kafin ta tafi makaranta sun yi waya.

Har aka fara kiraye-kirayen sallar Ishaq bai zo ba, har ta kosa da zaman sannan ta damu da rashin karasowar sa har yanzu, fatan ta Allah yasa lafiya.

Kasancewar ta na da alwala ga Kuma hijab a jikin ta yasa ta mike ta koma gefe ta kalli gabas ta tada sallah, cikin sallah taji abu na dan kauri daga kitchen, amma bata motsa ba, haka ta cigaba da salla domin bazata iya katse sallar ta ba.

Daidai lokacin Abraham ya karaso gidan... tun kafin ya shiga falon yaji kauri sosai, mamaki ne ya kama shi, yana murda kofar ya shiga yaga Aysha tsaye a gefe tana sallah a nutse, taku biyu kacal yayi Cikin falon yaji bumm!!! Ƙaran ya fito daga kitchen, ga wuta daya fara ci bal-bal...

Cikin sauri da tashin hankali ya kalli AYSHA a tsawace yace "hey! Run, i said run outside my friend"

Amma Ina Aysha'n ka bata ko motsa ba sai sallar da ta cigaba da yi nutsuwa.

Cikin sauri ya nufi abin kashe wutar nan da ake manna wa a bangon ( fire extinguisher) ya zaro ta ya shiga fesawa cikin kitchen din, shima ya kare, wutan bai mutu ba ya sake zaro dayan ya cigaba da kashe wutan har ya mutu, sai mugun hayaki daya cika kitchen din har ma da falo, fitilar wayar sa ya kunna da kyar ya karasa shiga kitchen ɗin domin hayakin yasa baya gani sosai, murda gas din yayi zuwa off, inda ya tabbatar Aysha ta manta ne bata kashe ba, tukunyar mai dake kan gas ne yayi mugun zafi har ya kama da wuta, Allah yaso wutar bata ratsa pipe din silinder ba da tuni labari ya sha bambam.

Fitowa yayi falo ya zube kan kujerar yana sakin tari saboda hayaki daya shaka over, ya kuma gode wa Allah daya takaita.

Sai faman fadin "Thank you Jesus, Jesus is Lord yake". (Allah ya ganar da duk Wanda yake hanyar bata Ameen!)

Sai da tarin ya lafa ya d'ago kansa, a razane ya kai idanunsa inda Aysha take dazu, so his greatest surprise har yanzu tana nan hankali a kwance tana sallah...

Zaro ido yayi, "Jesus Christ" ya fada kana ya nufi wajen ta, yana zuwa daidai wajen ta tana sallame shaf'i da wutri.

Hannun ta ya ja da karfi ya mikar da ita, cikin fadan da bai san ya iya ba yace "Are You insane? Did you want to kill your self huun? da ban zo da wuri ba haka zaki bari wutar ta kama ta kona ki, bayan Kina da halin guduwa, ki tsaya all in the name of praying, wait! like are you for real?" Ya fada unbelievable yana jijjiga dan kafadar ta da karfi"

Kuka mara sauti Aysha ta sakar masa, cikin rawar murya tace "Am sorry! My religion, or i should say Islam is beyond your expectations, i have already started praying, i can't run, na yarda cewa idan yau kwanana zai rage ko na gudu ko na tsaya zan mutu, addinin Muslunci ba kamar sauran addinai bane, zan iya guduwa na katse sallar sannan na roki Allah yafiya, amma katse sallar is not Good ln Islam sai da wata Babbar hujja da zai iya fadawa Allah idan ya mutu, but na zabi na tsaya ne, domin Ina son gwada zama muslumar kwarai, jaruma kan addinin ta, zan iya sadaukar da rayuwa ta ga Muslunci and I will be happy idan na mutu ta silar hakan"

Jikin sa ne ya mutu, zubewa yayi kan cushion ya zuba mata ido kamar ya samu hoto, tabbas addini Muslunci ya girmama tunanin sa kamar yadda ta fada, suna kaunar addini su, sannan suna bada dukkanin nutsuwar su wurin yin ibada basa wasa, Musliman kwarai zasu iya sadaukar da rayuwa da dukiyarsu wurin kare addinin su.

A duk lokacin daya ji Aysha na karatun qur'anin ya kan ji tana burge shi har baya son ta daina, amma a yau saboda jarumtar ta, son addinin Muslunci ne ya mamaye ilairin zuciyar sa. (Allahu Akbar!)

Cikin mutuwar jiki ya mike bayan ya gama tunani, daf da ita yazo yace "Am sorry too for yelling at you" ya karasa cikin sanyin murya sannan ya ra6a ta gefen ta cikin sauri ya haura sama...

Yana shiga dakinsa ya cire kayan jikin sa, Sannan ya nufi toilet, shower ya sakar wa kansa, ya shiga dukan kansa zuwa murd'add'en jikinsa

Readers Also Read