Kenza eBookz

Abraham complete by nooreemaan - Chapter 4

Abraham complete by nooreemaan - Chapter 4

Abraham complete by nooreemaan Chapter 4: Abraham complete by nooreemaan Chapter 4. Jinjina kai baffa yayi kana yace "tabbas ba karya, abinda ke raina…

3,327 words

Jinjina kai baffa yayi kana yace "tabbas ba karya, abinda ke raina Kenan, na kuma kara tabbatar da hakan ta dalilin matar da ta ajiye su ta gudu yanayin shigar ta kadai ya isa ya sanar da hakan, dama haka Allah yake ikon sa, ya fitar da mummuna daga cikin kyakyawa, haka Zalika zai iya fitar da kyakyawa daga cikin mummuna, banda ikon Allah 'yayy'an da iyayen su ba Muslumai, amma gashi sun shigo cikin Rayuwar Muslimai"

Jinjina kai Inna tayi cikin tabbaci, numfashi baffa ya sauke yace "ina ganin wannan album din zai taimaka mana kwarai wurin nemo iyayen su, in sha Allah zuwa gobe idan naji dama-dama zan fita cikin gari domin nemo gidan talabijin(television) ko redio domin mu bada cigiyar su, har ga raina banason rabuwa da yan biyu, domin ina so su taso cikin hasken musulunci amma hakan bazai hana mu nemo iyayen su ba saboda bamu San a wani halin damuwa suke ciki ba, kuma in sha Allah idan suna da rabo zasu samu shiga muslunci...."

"Assalama alaykum Innah ki........ laa baffana yaushe ka shigo" Aysha da ta shigo yanzu ta katsewa baffa maganar sa.

Murmushi baffan yayi kana yace "indon baffa Kenan, ai yanzu kin daina ji da baffan ki sai su Ammar" dariya tayi cikin jin kunya.

Mika masa Anwar dake ta tsalle yana kallon baffa tayi, kana ta zauna kusa dashi rike da ammar, take idaunta suka sauka kan sarkan Nonye, hannu tasa ta dauka kana cikin murna tace "wayyo baffa siyomin kayi, kalli kaga sai daukar ido take" ta fada cikin murna da yarinta.

"ke! ajiye" innah ta fada a dan kausashe

rau rau tayi da ido kana ta mai da dubanta ga baffa tace "baffana" a shagwab'e...

"ki bi maganar Innar ki kin ji ko ? Baya ga haka gobe nakeso In sha Allah naje na bada cigiyar iyayen su Ammar da taimako sarkan nan hadi da photo album dinnan, dan haka ki ajiye kinji idan naje cikin birni zan siyo miki mai kyau"

Ihu Indo ta fara yi hadi da shure² ita fa ba za a raba ta da su yan biyu ba, cikin fada Innah tace " ke rufemin baki a wajen kafin na make ki, ke kin san dadin su bakya son rabuwa dasu, mahaifan su fa? kin San a wani hali suke ciki? Kin San wani radadi suke ji a halin yanzu? mu kan mu bamu so rabuwa dasu ba, amma tunda mun samu shaida dole mu sada y'ayy'an ga iyayen su"

*1 hour later*

Ganin da gaske kukan yaki karewa ya sanya baffa yiwa inna sigina kana yace "yi shiru Indon ta baffalle, mun ji mun hakura bazamu raba ku ba, maza share hawayen ki"

Shiru tayi tana k'amk'ame Ammar hadi da sauke ajiyar zuciya, daga nan su Innah suka shiga Jan ta da hira domin ta manta da komai, ai kuwa ta saki jikin ta ta cigaba da wasan ta da su Ammar, fita tayi waje da ammar a hannun ta, still sarkan nan na zaune daram a ranta...

ganin fitar Indo ya sanya baffa kallon Inna yace "dole cikin dabara zamu fitar da yaran ta yanda Ayshatu ba zata gane ba, idan Allah ya bayyana iyayen su yaran nan"

Dariya Inna tayi tace "gaskiya dai, in ba haka ba rigimar Indo yafi karfina"

Murmushi baffan yayi yana kara jin kaunar tilon 'yarsa na shiga zuciyar sa.

Da magriba baffa ya lallaba ya tafi masallaci domin yana jin ciwon cikin na lafawa, anjima ya fara, Inna kuma ta shige bandaki domin kama ruwa, sadaf-sadaf lndo ta shige dakin baffa ta dauki jakar nan kana ta koma dakin ta, bude jakar tayi ta dauki sakar kana ta mayar da zip din ta rufe bata damu da ko kallon album din ba, zata fita ta mayar da jakar kenan, taji motsin Inna ta fito hakan yasa cikin sauri ta cusa jakar kasan kayan ta sannan ta raya a ranta cewa anjima zata mayar idan Inna ta shige bandakin, sarkar ta saka a wuyanta hadi da mayar da hijab dinta jikin ta, dama tunda ta yi Wayo bata fiye zama ba hijab ba....

WASHEGARI 6:00am

Bayan baffa ya dawo daga sallar asuba yaji ciwon cikin nasa ya matsa masa gadan-gadan ya kuma kara shan maganin yaji ciwon bai lafa ba, hankalin su innah ya tashi sosai, ga yan biyu dake ta kuka sosai wanda ya kara dagawa su Innah lissafi...

*kullun nafsin za'ikatul maut* da misalin 9:00am na safiyar juma'ar baffa ya amsa Kiran ubangiji, mutuwar data girgiza dubban jama'a, inda kowa ke masa fatan ya dace domin yayi mutuwar shahada, Inna tayi namijin kokari wurin danne zuciyar ta matuk'a, domin ko kuka bata yi ba, sai na zuci daya fi na fili ciwo, yayin da Indon baffa ta sha kuka har da suman ta, domin kowa yasan tarin kaunar dake tsakanin su, haka suka hakura suka fawwalawa Allah lamarin su, sannan suka bi baffa da addu'a domin abinda ya fi bukata Kenan....

*************************

BAYAN KWANA ARBA'IN

A yau baffa ya cika kwana arba'in da rasuwa, zuwa yanzu su Inna sun hakura har su fara sabawa da rashin 6affa, amma yana nan daram a ransu, domin manta baffa ba abu bane mai sauki, zai kasance a ransu har abada, Bayan an gama addu'o'i, an raba abin sadaka mutane duk sun tafi, amma banda yan'uwan baffa da suka rage, dakin Inna suka shige, inda wan baffa mai suna sule ne a gaba, kallon Inna da ta rame sosai yayi, cikin gadara yace "baya ga wanna shanayen guda biyar da rago biyun nan ina sauran kadaran Mijin ki"

A sanyaye Inna tace "yaya babu komai, baya ga abinda ka lissafo sai gidanan babu wani kadara da ta yi saura"

"toh ai shikenan, shanayen zamu tafi dasu, eh zamu tafi da su, domin mu ma dole mu ci gadon dan'uwan mu, ke da yarki Kuma ku rike rago biyun nan" yana fadin haka ya fita, sauran suka mara masa baya, wasu hawaye masu zafi inna taji sun zubo mata, meyasa mutanen yanzu suka shagalta da son duniya suka manta da lahira, yaushe baffan ya rasu da har zasu hau kan gadon sa? Hakika mutuwa tayi musu yankan kauna, da yan biyu basu yi wayo ba, dame zasu dinga shayar dasu tunda sun kwashe shanayen? Inda taji dadi sun dan fara cin abinci kadan² Indo dake kallon inna ta share mata hawaye, domin duk da kananun shekarun ta amma ta fahimci wasu abubuwan dake faruwa...

*************

A haka suka cigaba da Rayuwar su cikin rufin asirin Allah, da tafiya tayi tafiya kudin hannun Inna ya kare, dole basu da zabi daya fi su siyar da ragunan biyun nan kacal, kayan abinci Inna ta siyo, wanda ta San zai dade musu kafin ya Kare...

*IMO STATE*

Sanye yake da wando 3quarter blue-black, da riga body hug fara daya yi matuk'ar yi masa kyau, zaune yake kan daga daya cikin had'add'un kujeran daya kara k'awata falon, idanunsa a lumshe tamkar mai yin bacci, madam Gloria dake gefensa a zaune ta kurawa plasma screen din ido wanda ba wani kallo take ba, lokaci zuwa lokaci tana juyowa ta jefa Abraham da wani irin kallo mai dauke da ma'anoni masu tarin yawa...

Bata zata ba, bare tsammani ta tsinci muryar sa kamar kullum cikin turanci domin bai fiye magana da igbo ba yace "mummy cikin satin nan zamu bar imo zuwa kaduna state , bazan juri cigaba da zama a nan ba kuma, I think zan fi samun peace of mind idan nayi nesa da Imo, I want to start a new life, already na siyi gida da duk wani abun bukata a can" ya karasa ko motsi bai yi ba, kai ka rantse bashi yayi magana yanzu ba.

Gaban madam Gloria ya fadi ras! Cikin tashin hankali tace "why son? You can still live a better life here, just forget about the the past and face the future, you re too young for all this, and why did you even prefer Northern state, if you don't want to stay here in Imo, then we can move to delta state or other Eastern state, but why kaduna uhmm son?"

Boyayyen ajiyar zuciya ya sauke, shi ma bai San meye zo kan shi ba, hakan nan shi ma yaji yana son zama a arewacin Nigeria, abinda bai taba bashi sha'awa ba Kenan, amma yanzu yaji zaman imo ya fita a ransa gabadaya, dama baya da company ko daya a garin, baya ga gidan nan, wanda shi ma ya riga ya siyar dashi ga wani attajiri.

Mikewa yayi tsaye yana gyara zaman rigar sa kana ya bar wajen cikin takun sa na lafiyayyen namiji mai ji da kuruciya...

Da wani mugun kallo madam Gloria ta bi bayan sa har ya bacewa ganinta, ta San cewa shi din kaifi daya ne, baya magana biyu, Kwafa taja kana tace "da Sannu kai ma zaka bi bayan Nonye na more duniyata Dan taurin rai kawai, kaje ka siyi gida a wani gari ban sani ba sai yanzu, babu abinda ya bari a halin shegiyar uwar sa"

*I WEEK LATER* Kaduna state unguwar barnawa

Yau kwanan su Abraham uku da dawowa kaduna, duplex house ne da ginin ya tsaru sosai, yayinda aka zuba abubuwan k'awa a ko wani lungu da sako na gidan, fadin kyau da haduwar gidan bata time ne, just mai karatu ya yi imagine din gidan masu hannu da shuni.

Zaune madam Gloria take a had'add'en kuma yalwataccen falon kan daya daga cikin kujerun, ta harde kafa daya kan daya tana shan wine, ta chaba ado sosai tamkar zata je gidan biki yayinda take latsa tsad'ad'iyyar wayar hannunta kirar iPhone 13promax.

ABRAHAM ne ya fito daga saman bene inda nan ne bangaren sa, sanye yake da kananun kaya ga key din mota a hannun sa da alama fita yakeson yi, dagowa madam Gloria tayi cikin fara'a tace "my handsome son, ina zaka je? Gashi ina son mu yi magana, na fadawa musa mai gadi ya nemo yan aiki, yace min akwai Wata mai aiki a gidan dake jikin namu, ya fadamaka, ta ma zo mun yi magana tace a bata nan da 1 week zata nemo su"

"zan fita shopping ne mummy, idan na dawo zamu yi magana" ya amsa mata a takaice kana ya bata side hug ya fita cikin sauri, mota ya fada, sabon mai gadin su musa ya wangale masa gate din ya fita, duk da bai San ko ina a garin ba, amma ya San bazai bata ba, tunda yanzu duniya ta cigaba, kuma in dai mutum ya iya karatu an gama, goggle ya shiga yayi browsering nearest supermarket, take kuwa goggle ta fito masa da ita, wuta ya bawa motar ya harba kan kwalta....

WANENE ABRAHAM?.....

*Note*

(karfa ku manta da yaren igbo hadi da turanci madam Gloria da Abraham suke duk Wata magana, ina yawan amfanin da hausa ne domin mai karatu ya gane, sannan ya fahimci inda labarin ya dosa)

Share fisabilillah

Comment for more typing...

Noor🦋 07082281566

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 0806626851

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥 _Kamar yadda na fada, Abraham ba sabon Novel bane, hakan ne yasa ban bude masa group na musamman ba, ma'ana group iya posting Abraham din, amma saboda massages na min yawa kan ana son na bude group, amma ban bazan iya bude wa ba gaskiya, domin bana son tarkarcen groups da yawa, Ina da dai group ɗaya na novel wanda ga link nan zaku iya joining, Ngd sosai jazakallahu Khair, ina godiya da soyayyar da kuke nuna wa books dina_.

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JwYkGXFKcLH95WSHP9QoUg [10/6, 7:51 PM] 💖NoorEemaan💖: #NoorEemaan

🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇 ABRAHAM 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇

*First edition*

https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din

ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚✍️

*WATTPAD* @NoorEemaan

Banyi editing ba🤒

Chapter 15-16

Asalin Abraham dan kabilar igbo ne na jihar imo state, haka zalika iyayen sa, mahaifin sa (Patrick Samuel) shahararren dan kasuwa ne, wanda duniya ta San da shi, inda ya hadu da mahaifiyar Abraham (Victoria) a wani bussiness trip daya je Canada, inda ita kuma Victoria tana hada master's dinta ne a lokaci, inda ita ma yar mai kudi ce domin mahaifinta babban lawyer ne.

Basu dauki lokaci me tsayi ba suka fahimci Juna, Bayan ta gama hada masters dinta ta gabatar da Patrick ga iyayen ta, inda ba a samu wata matsala ba iyayen ta suka amince kasancewar suna kaunar farincikin diyar su, sannan kuma Patrick ya kwanta musu a rai kasancewar ya hada dukkanin quality's din da suke so ga namijin da zai auri 'yar ta su, traditional wedding din su aka fara yi, inda aka gudanar da dukkanin Wata al'adar su a yayin biki.

Bayan Wata daya aka daura musu aure ma'ana dai suka yi Church wedding, farinciki da kwanciyar hankali hadi da zallan kauna ne yake wanzuwa a gidan Patrick...

Auren su na da wata bakwai Victoria ta samu shigar ciki, inda ba karamin farinciki Patrick yayi ba, son duniya suka d'aurawa cikin, in da suke a K'age Dan ya fito duniya suyi tozali dashi....

Bayan wasu Watanin Victoria ta haifi santalelle kuma lafiyayyen dan ta, sosai murna ya karu a gidan Patrick, in da suka dora son duniya ga yaron, ranar suna yaro yaci suna ABRAHAM kamar yadda Patrick yaci burin saka wa dansa matuk'ar yayi aure ya haihu...

*************************

*10 Years Later*

A kwana a tashi babu wuya wurin Allah, domin shekarun Abraham yanzu goma cif, ya gama primary school a wani tsad'add'en makarantar private dake imo, inda baya taba zuwa na biyu a school dinsu saboda tsananin kwazon sa...

***********

Bayan an gama bikin birthday dinsa da kwanaki iyayen sa suka yi masa rakiya zuwa England inda zai cigaba da karatun sa har jami'a kamar yadda Patrick yayi masa sha'awar yin karatu a waje, aka kuma yi sa'a ra'ayin su yazo daya da Abraham, duk da Victoria bata son danta yayi nesa da ita amma babu yanda ta iya domin tafi kaunar farincikin sa fiye da nata.

Sai da suka tabbatar komai yayi daidai kana suka dawo Cike da kewar tilon dansu, a rana sai su yi video call dashi sama da goma, as time goes on suka fara sabawa da rashin sa a kusa, inda duk bayan Wata hudu suke zuwa duba Abraham....

*Bayan shekaru biyu*

Patrick na hanyar dawowa gida daga ma'aikatansa ya ga Kiran Victoria ya shigo wayar sa, inda take sanar dashi kanta na ciwo sosai bata samu yi masa girki ba, kuma ta San baya son abincin yan aiki, Sannu yayi mata cikin kulawa, gama wayar su ke da wuya ya hango wani gidan Abinci, umarnin ya bawa driver kan su karasa gidan abincin, sauka yayi ya nufi cikin wajen da kan sa inda ya samu Wata budurwa Wacce take bangaren serving din mutane, kallo daya mutum zai mata ya karanci cewa ta Bude ido da yawa, ga iya kissa, Gloria Kenan...

Fried rice with chicken da hadin salad partrick yace ta hada masa takeaway ba tare da ya lura da karairayen da take masa ba, ita kuwa Gloria lokaci daya taji ya tafi da ita, bata bari ya tafi ba sai da tayi iya yinta ta samu number'n wayar sa.

_12:05am_

Kwance suke suna bacci su cikin kwanciyar hankali Kiran Gloria ya shigo wayar Patrick, wanda hakan yasa ya farka a zabure domin wayar na saitin kunnen sa, saurin danna answer yayi, zai yi magana Kenan yaji Gloria tace "Am so sorry for calling you at this time, is just that I couldn't help i......" kit ya kashe wayar gabadaya, domin ya gane matashiyar gidan Abinci nan ce, banda bata da tunanin a wanna daren zata kira shi, ko da bashi da aure bare yana da, ko meya shiga kansa har ya dauki number ya bata oho ya fada a ransa yana Jan tsaki, mai da kallon sa ga Victoria yayi yaga bacci take, ajiyar zuciya ya sauke ya koma ya kwanta.....

*Washegari*

Zaune mahaifin Abraham Patrick yake a office dinsa yana duba wasu files Kiran matashiya Gloria ya shigo cikin wayar sa, dauke idon sa yayi daga kan file din ya mayar kan wayar, take ya fahimci number'n yarinyar jiya ce, latsa kore yayi hadi da kara wayar a kunne sa ba tare da yayi magana ba...

"kayi hakuri sir, na kira ka cikin dare, bamu tashi daga restaurant ba sai after 11 ni kuma ina son jin muryar ka shiyasa na kira, forgive me please " ta karasa cikin wani salo na jan hankali...

"is okay, amma ki kiyaye because ina da mata banason Kiran daren nan"

"mata!" ta fada azabure...

"yes of course" ya amsa hadi da katse Kiran, domin hakan nan yaji yarinyar bata kwanta masa ba.

Daga bangaren Gloria kuwa wani huci mai zafi ta furzar, domin bata taba kawowa a ranta cewa yana da mata ba, kasancewar yawanci mazan igbo da matan su basu fiye aure a kananun shekaru ba, shiyasa bata kawo masa cewa yana aure ba, take ta ji wani matsanancin kishin matar tasa, kuma bata jin zata iya hakura dashi domin sosai ta kamu da son sa, ga alamun tarin arziki data hango a tare dashi....

kawar ta Sarah ta kira inda ta bata wasu shawarwari ta yanda zata mallaki Partick din cikin sauki...

Haka Rayuwa ta cigaba da juyawa, inda kullum Gloria bata gajiya sai ta kira wayar Patrick, shima tun yana ignoring dinta har suka fara gaisawa sama_sama, Gloria macece shu'uma mai bud'add'en ido inda ta san hanyoyi da dabarun janye hankalin da namiji, sai dai Abu daya ne yake damunta har yanzu bata ga alamun yana nuna kulawa ko so ga ita ba, bare ta kai ga maganar aure, hakan yasa taje har gidan kawar ta kuma abokiyar shawarar ta wato Sarah, inda ta bata shawaran su je wajen boka domin a k'ark'ato da hankalin Patrick zuwa gareta sai abinda tace dashi, hakan kuwa akayi, cikin lokaci kalilan Patrick ya haukace a son ta...

**********************★★★

Victoria mum Abraham na zaune Patrick ya kawo mata zancen zai kara aure, inda kirjin ta yayi wani irin tsalle, bambarakwai taji abun, domin da wuya kaga namiji ya kara aure irin haka a al'adar su da ma addnin su, bayan akwai matar sa a gida ba wai mutuwa tayi ba.

Abu kamar wasa fa Patrick ya dage lallai shi fa aure zai kara, labari ya basu a dangi da abokan arziki inda suma sunyi mamakin hakan kwarai, domin kamar sabon Abu ne a wajen su kasancewar hakan bai saba faruwa a gare su ba, iyayen Victoria suka yi fushi kana suka ce yayi divorcing yar su, domin bazata zauna da kishiya ba.

Abu fa ya kara tsamari, inda har iyayen Patrick din suna fushi dashi amma Sam bai damu ba, baya ganin kowa sai Gloria.

Da kyar Victoria ta lallaba iyayenta kan su yi hakuri kar a raba su tana son mijin ta uban dan ta, zata cigaba da zama dashi komai wuya komai dadi...

A lokacin Patrick ya sanar da Gloria yana da d'a Dake karatu a kasar waje ba karamin tashin hankali ta shiga ba, domin Sam bata San ya ma haihu ba, amma bata nuna a fuska ba, sai dai kamar yadda ta tsani Victoria haka ta tsani Abraham duk da bata taba ganin daya daga cikin su ba...

Bayan auren su Gloria ta tare a gidan, a lokacin ne victoria tayi hannu riga da farinciki, sosai Gloria ta matsa mata, duk da cewa ba shiga harkan ta take ba, ga Patrick yanzu Sam baya da lokacin ta, amma daurewa take tana shanye duk wani bacin ran da suke sa mata.

Kamar ko wani wata hudu suna kai wa Abraham ziyara England, wanna karon har da Gloria aka shirya tafiyar....

Readers Also Read