Kenza eBookz

Abraham complete by nooreemaan - Chapter 5

Abraham complete by nooreemaan - Chapter 5

Abraham complete by nooreemaan Chapter 5: Abraham complete by nooreemaan Chapter 5. Inda bayan sun je Abraham ya tambayi mummy'nsa cewa wace ce Gloria? ta…

3,355 words

Inda bayan sun je Abraham ya tambayi mummy'nsa cewa wace ce Gloria? ta gayamasa cewa sabuwar mummy'nsa ce, sannan ya dinga bata respect kamar yanda yake basu, Gloria kuwa sai kulawa hadi da soyaaya take nunawa Abraham kamar gaske, da kuma taimakon Victoria Abraham ya sake da ita, sosai kuma Patrick yaji dadin yanda Gloria ke son Dan shi, kwanan su hudu suka dawo Nigeria.

*10 YEARS LATER*

Abubuwa da Dama sun faru cikin Wadannan shekarun, ciki har da mutuwar Patrick shekara daya Kenan, sak'amak'on hadarin mota da yayi, sosai matan sa suka ji mutuwar sa, bare ma mummyn Abraham, duk da babu wata soyaaya a tsakanin su har ya mutu, haka zalika cikin shekarun nan Abraham yayi nasaran gama secondary school din sa

*****************

Lokacin da lawyer din Patrick ya zo yana zayyana musu tarin dukiyar da Patrick ya bari, ba karamin mamaki ne ya kama Gloria ba, sabanin Victoria da ta San cewa mijin ta zai iya tara fiye da hakan domin yana da zuciyar nema.

Tun daga wannan lokaci Gloria ke neman hanyar da zata bi domin hallak'a Victoria saboda ta mallaki dukiyar gabadaya, a cewar ta Abraham karamin alhaki ne, bata ci nasara ba sai bayan wata uku, ta yiwa fruit din da Victoria zata ci allurar guba, kasancewar Victoria akwai son kayan itatuwa.

Ta kuma San yawancin mutanen zasu zata cewa tunanin mutuwar mijin su ne yayi ajalinta....

A lokacin da ta mutu kukan da madam Gloria tayi ba kadan bane, Abraham ma ya shiga matsanancin hali, kamar zai haukace, domin ya mallaki hankalin kansa yanzu, sosai rashin son maganar sa ta karu, haka zalika bayason shiga jama'a ko kadan.

Yan'uwan Patrick sun so Abraham ya dawo hannun sa madam Gloria ta sa kukan zallan makirci tace a bar mata shi zata kula dashi tamkar Ita ta tsugunna ta haife shi, Dan sun ga Allah bai bata haihuwa ba za a raba ta dashi, basu musa ba suka bar mata shi, kuma sun yarda da son da take yiwa Abraham, tunda sun sha ganin tana nuna so ga Abraham din idan sun zo gidan.

*Bayan Wata Biyu* Abraham ya koma England ya cigaba da karatun sa, wanda ko sau daya madam Gloria bata je ba, sai dai ta kira shi a waya, shima bai damu ba, bai kuma sake take kafarsa a Nigeria ba sai daya hada masters dinsa a bangaren business administration, inda ya fito da sakamako masu kyau...

Bayan ya dawo Nigeria ya cigaba da kula da harkokin mahaifin sa, inda cikin kankanin lokaci ya farfad'o da bussiness din, ya hab'aka sosai, har mutane na cewa Abraham yafi mahaifin sa Patrick iya bussiness...

Madam Gloria tayi iya yin domin ta hallaka Abraham ta yanda zata kwashe dukiya ta gudu amma har yanzu hakan ta bai cimma ruwa ba....

KO MADAM GLORIA ZATA CI NASARA??? MUJE ZUWA ABRAHAM FANS....

*************************

DAWOWAN LABARI (BACK TO STORY)

Bayan ya dawo daga shopping mall din, madam Gloria ta kara taran sa da maganar yan aiki inda yace ta tsara komai yanda ya dace kawai, kana ya sanar da ita tafiyar sa zuwa dubai gobe zai kuma yi kwana biyu domin zai je ya duba company'n sa na turare dake can, inda an sake yin wasu designer's perfume, murna tayi masa duk da bai kai zuciyar ta ba, a kullum tana jin zafin cewa ba Dan cikin ta ke sabon wanna nasarar ba, a kullum tana bakinciki rashin haihuwar da bata yi da Patrick ba, da ta sani taje tayi adopting yaro ko da a gidan marayu ne a zuwan it's ta haifeshi, domin ta kara samun tarin dukiyar, kuma tasan cewa zai yarda tunda yana jin maganar ta, amma inaaaa bazai yu ba yanzu, tunda wanda za ta ce shine yayi mata ciki baya duniya, bare ta hada karyan ta, tabbas madam Gloria zata yin duk abinda take so, kuma ya tsaru kamar gaske, domin ta shahara a fannin iya tuggu....

Bayan sati daya aka kawo mata yan aikin inda ta raba wa kowa aikin sa, sai dai bata bawa kowa daman shiga kitchen ba, saboda a cewar ta bata yarda da tsabtar su ba.

*Gombe State* _Bayan wata biyar_

Bangaren su Innah kuwa suna cikin matsin rayuwa, domin Abinci da innah ta siya ya kare, Dan sana'ar da take a cikin gida ma sun cinye jari, ga su ammar har Dan rama suka yi saboda rashin ingantaccen Abinci da babu, kullum inna cikin tagumi take, da gari ya waye zata fara fargaban dame zasu yi karin kumallo? bama ta kanta take ba, ta yaran take, gashi Sam batason fara dorawa Indo talla, domin tun baffa yana raye ya tsani wanna dabi'ar ta dora wa y'ay'a mata talla domin ba karamin lalata tarbiyar yaran take ba, kullum addu'ar ta shine Allah ya kawo musu mafita...

Ajiyar zuciya ta sauke, Bayan ta gama tunanin halin da suke ciki, wanda hakan yayi daidai da kwad'a sallamar wata matashiyar mata cikin gidan.....

Share fisabilillah

Comment for more typing✍️

Noor🦋 07082281566

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 0806626851 [10/7, 2:41 PM] 💖NoorEemaan💖: #NoorEemaan

🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇 ABRAHAM 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇

*First edition*

*WATTPAD* @NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚✍️

*I dedicated this page to my anty, Anty hawwa(TM@shoprite ) a very nice woman with a heart of gold, duk da girman matsayin ta bata da pride, much luv 😘*💞

https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din

Chapter 17-18

Wa'alaikumu Salam Inna ta amsa tana leken mai shigowar kana tace "a'a wa nake gani kamar Bintu?"

"Nice Inna wuro" matar ta fada da murmurshi saman fuskar ta.

Lale maraba, sannu da zuwa karaso ki zauna, idanki Kenan?" Inna ta fada tana k'akk'abe saman tabarman wa bintu domin ta zauna...

Zama bintu tayi kana suka gaisa da Inna cikin yaran fillanci, Jim suka yi babu wanda yayi magana tsawon mintuna uku kana bintu ta muskuta tace "ya muka ji da hakurin rashin baffa? Ashe baffa ya Riga mu gidan gaskiya, zuwa na gida jiya na samu labari, Kin San wannan aikin namu Bamu ba lokaci gashi ba a kusa ba, Allah ya masa rahama"

Murmurshi mai ciwo Innah tayi kana ta amsa da ameen tana kokarin mayar da kwallar daya cika idanun ta, tsaf bintu ta lura da ita, amma bata ce komai ba, domin wani kukan ma rahama ne, gashi kuma ta ga alamun sauyin Rayuwa a tare dasu Inna, girgiza kai tayi cikin tausayin su, yayinda hirar da suka yi da matar da ta tace ta nema mata yar budurwa mai tsafta domin gyara dakunan su da yin girki, ko da bata iya girki ba za a kawo k'wararriya domin koya mata, burin matar dai yarinya mai tsananin tsafta take so.

Hakan nan Indon ta fado mata a rai, kallon Innah tayi tace " kiyi hakuri Inna wuro idan na yi miki shishigi naga kamar kuna cikin wani hali na rashin babu, gashi kuma can kaduna kusa da gidan da nake aiki ana neman 'yar budurwa irin su Indo, duk da dai na kwana biyu ban gan ta ba, amma nasan ta kara girma. Da' yar gidan garko zan kai, amma na fasa, domin ban ma sanar musu ba, ya kika ce innah wuro? Kinga kudin zai taimaka muku kwarai wurin sauyin Rayuwar ku fiye Dana baya" bintu ta karasa tana kallon innah, tare da fatan samun amincewar ta.

Bata rai Inna tayi kana ta girgiza kai tace "a'a bintu bazan iya ba, bazan iya tura 'yata kwalli daya aikatau ba, me mutanen gari da yan'uwan mahaifin ta zasu ce? Baz....."

"innah!" Indo dake tsaye tun dazu a gefen su ba tare da sun lura bata ta fada.

A tare suka mayar da duban su daga inda amon muryan indo ya fito, karasawa Indo tayi gaban Inna ta tsugunna, riko hannun ta tayi, hawayen zallan tausayin kansu ya zubo mata tace "innah ta! ki amince dan Allah, ki amince, kinji? zan iya yin komai matuk'ar halal ne domin mu samu sauyin Rayuwa, meye amfani na idan ban taimaka miki ba Inna? Alhalin zan iya yin hakan? A Rayuwar nan idan mutum zai yi abu kar ya duba abinda mutane zasu ce? Sati daya kacal ya ishe su yin duk wani surutun su da gulma su hakura, da Muke shan wahalar mu waya tallafa mana?, ki bani umarnin yin aikin nan Innah, ina ji a jikina cewa akwai alkhairi a tafiya ta aikatau dinan, dan Allah Innah" ta karasa cikin Sanyi murya mai cakude da Kuka wanda ya sanya innah yin laushi"

"tabbas Inna wuro abinda Indo ta fada gaskiya ne, kuma sanin kanki ki ne Inna cewa bazan taba bari tarbiyyar indo ya lalace ba, zan dinga shiga ina duba ta, tun fa ina karama Muke a amatsayin makotan juna, kin San halina, banda mutuwar Ashiru mijina da yanzu ina tare daku a kauyen nan, amma gashi yanzu da kudin aikatau din nake kula da yarana da kuma iyayena, dan Allah innah ki amince in sha Allah baza kiyi nadama ba.

Numfashi Innah ta ja, gabadaya jikin ta ya mutu, a sanyaye kana cikin mutuwar jiki tace "na amince Allah yasa hakan shine mafi alkhairi Nagode miki bintu"

"ameen Innah wuro, ai yi wa kaine Karki damu" bintu ta fada cikin farinciki da sakin fuska kamar yadda ya kasance nature dinta ne yawan fara'a.

"gobe zan wuce in sha Allah sai ki hada kayanki mu tafi ko indo"

"anya zata biki goben kuwa bintu, ina tunanin sai ga ta gaskiya"

Murmushi bintu tayi tace "ho hoo hooo Inna ta fara kewar Indon ta, toh bari na rubuta address din a takarda, sunan garin dai kaduna ne , amma bari na rubuta sunan unguwar sai ta nuna wa mai adaidaita sahu, unguwar sananene, sannan ga lambar waya ta idan kin sauka sai ki fadawa mai adaidaita ya kira miki lambar ni kuma sai na fito na mika ki gidan da zaki yi aikin kinji ko" ta fada tana kallon Indo bayan ta gama rubutun a takarda.

Murmushi kawai innah tayi bata ce komai ba, bintu ta kara awa daya a gidan suna shan hirar duniya kana ta Mike domin tafiya, jakar ta ta Bude ta zaro duhu uku ta bawa Inna, ta kyar Inna ta karba, kara zaro dubu goma bintu tayi ta bawa Indo kudin mota, Inna tace Sam ta barshi duk da cewa ba kudin garesu ba, Murmushi bintu tayi halin innar na matukar burgeta, Sam Abin duniya bai dame ta, sai da ta rantse wa Innah cewa Wacce zata dauke ta aiki ce ta bayar da kudin kana Inna ta amince, har soro lnna ta rakata tana godiya kana ta dawo cikin gidan tana addu'ar Allah yasa tafiyar Indo alkhairi ce .

************************

Indo kuwa sosai ta fara kewar yan biyu da Innar ta, sai ta shige dakinta tayi kuka sosai, amma bata bari Innah ta gani, domin ta San zata iya cewa ta fasa zuwa kaduna aikatau din.

*BAYAN KWANA UKU*

A gurguje ta fito daga wanka ta shirya domin inna tace ta hazantar su isa tasha da wuri kada motocin safiya su tashi, kayan ta take hadawa cikin sauri inda idanun ta suka sauka kan jakar data ciro sarkar dake wuyanta, shaf ta manta cewa bata mayar da jakar ba kamar yadda ta aiyana a ranar, take ta tuno da baffan ta wanda hakan yasa wasu hawaye masu dumi suka zubo mata, wanda hakan yayi daidai da kwala mata Kira da Inna tayi, cikin duburbucewa ta saka jakar cikin Ghana most go dinta, zuge zip din tayi ta fito, bayan ta share hawayen ta.

Da su ammar dake tsaye suna mata bangala mata dariya a tunanin su tare zasu tafi ta fara sauke idanun ta, murmushin ta mayar musu yayinda take jin zuciyar na karyewa, kewar su mai tsanani na ratsa ta, rungumosu tayi gabadaya da hannayen ta biyu kana ta sumbace su a goshi.

Maganar da Inna ta yi mata ne ya sanya ta Mike rike da hannun su Anwar, yayinda Inna ta dauki Ghana most go dinta suka fito, machine biyu hau inda ya fito dasu bakin titi, kana suka sake hawa wani daya kai su tasha, saukar su a tasha ke da wuya suka ji wani driver yana fadin "Kaduna! Kaduna!! Kaduna!!!" sauran mutum daya...

Cikin sauri Inna tace "Ayshatu ki kula sosai da tarbiyyar ki, Karki manta duk abinda na fada miki, Allah ya tsare ya kiyaye, ga wannan ki rike a hannunki innah ta fada tana mika mata dubu biyu, sannan ki rike takardan nan da bintu ta baki da kyau" karasawa gaban driver Inna ta, biya wa Indo kudin kujera tayi, amsar jakar ghanan driver yayi ya saka a booth, lokacin ne wani kuka mai ciwo ya kufce wa Indo, tunda aka haifeta yau ne rana ta farko da zata tafi wani gari, ganin haka yasa Inna kama hannun yan biyu suka bar wajen domin zuciyar bazata juri ganin Indo na kuka haka ba, su Ammar ihun kuka suka saka ganin da gaske Ammuh dinsu(Indo) zata tafi ba tare da su ba, haka suke kiranta da Ammuh.

Sosai suke kuka suna tirjewa alamun suna son dawowa wajen Indo, kasa juran kallon su Indo tayi ta shige motar hadi da kifa kanta kan cinyoyinta tana sakin kuka...

2:30 daidai suka sauka a tashar kaduna, kalle² Indo ta shiga yi domin ta rasa wani waje zata nufa, driver daya kawo su ne ya lura da ita yace "yarinya lafiya dai? Ko wani kike jira?" ya tambaya, yana goga aswaki a bakin sa daya dan rine, wanda hakan zai tabbatar wa mutum cewa shi din ma'abocin cin goro ne.

"hmmm uhmmm, wajen na cikin takardan nan" ta fada tana nuna masa takardan, domin ita ba karatun boko ta iya ba. Sai dai a fagen karatun addini ba baya bace.

Kallon takardan yayi yace "ai can zaki tsallaka sai ki samu a daidai ta sahu ki bashi takardan zai kai ki har wajen domin ba boyayyen waje bane.

Godiya tayi mishi kana to dora Ghana most go dinta a kai ta tsallaka dayan bangaren...

********

Saukar sa Kenan a airport, Cikin takun kasaita ya bar filin jirgi rike da wani jaka karami irin ta matafiya, tun tafiyar sa dubai bai dawo ba sai yau, ba wai dan bai gama abinda ya kai shi ba, hakan nan yayi zaman sa a wani tsadadden hotel dake can kasar dubai din, burin shi kawai ya isa gida domin ya huta shiyasa ma ya kasa hakurin jiran driver ya zo, ya gwammace ya hau adaidaitasahu....

Isar sa babban titi kuwa sai ya fara Jin wani irin, ta yanda zai tarar mai adaidaitasahu, domin abu ne wanda bai taba yi ba, bai taba hawa motar haya ba, bema San abinda zai ce ba, yana cikin wannan tunanin yaji tsayuwar mai keke a gabansa yana tambayar sa tafiya ne? Ajiyar zuciya ya sauke kana ya fada ciki, juyowa mai keke yayi yace "oga wani area zamu je? " duk da kasancewar Abraham baya jin hausa amma ambatar AREA da Dan sahun yayi ya sashi fahimtar abinda yake nufi, motsa cute lips din sa yayi yace "barnawa" kana ya fito da bakin sunscreen dinsa ya manna a fuskar sa wanda ya kara masa kyau ainun.

*****

Tun daga nesa Indo da ta gaji da tsayuwa, fuskar ta har wani jaa yayi kamar na tumatir gwanin tausayi saboda rana da ta jima tsaye a ciki, abinka da farar mace, ta hango wani keken da alaman mutum daya ne a ciki ya sanya ta fara tsayar dashi tun kafin ya karaso, domin yawanci masu wucewa a cike take...

Mai Dan sahu kuwa hango yarinya daga nesa ya Sanyi shi yin slow kadan da kadan , kana ya juyo ga Abraham yace "oga drop ne ko a dau passenger?"

Shiru Abraham yayi, ba tare da yace uffan ba, kara maimaitawa mai keke yayi still ba amsa sai kawai yayi wa Indo alaman ta taho, cikin sauri ta taho tana me mika masa takardan, karba yayi ya karanta yace "kudin ki dari biyar hau muje"

Cikin sauri ta hau tana sauke numfashi, yayin da taji bugun zuciyar ta ya karu, runtse idanun ta tayi da karfi tana kara k'amk'ame Ghana most go dinta.

Ta bangaren Abraham kuwa fiye da abinda indo taji yake ji, amma kasancewar shi namijin gaske yasa mutum zai yi tunanin bai San da zaman ta kusa dashi ba, Abin ya bashi mamaki kwarai, ta yanda yake jin kirjin sa na bugawa da sauri² daga zaman yarinyar da ko fuskar ta bai kalla ba cikin keken.

Indo kuwa ta jima idanunta a runtse kana ta ware su a hankali ta saci kallon fuskar sa, inda lafiyayyen beard din shi kadai tayi nasarar hangowa, domin ya dan juya kan sa ne, gabanta ne ya sake fad'uwa tayi sauri dauke kanta, jakar ta ta ajiye a kasa domin ta gaji, da kuma alama wajen da nisa domin sai tafiya ta ga suna yi...

Masu bada hannu ne suka tsayar dasu, wanda hakan yasa tilas duka ababben hawa dake bangaren suka tsaya, domin bawa yan dayan barin damar wuce wa...

Karan takun dokuna dake ratsa motoci suna wucewa ta fara ji, inda take ta rasa nutsuwar ta, domin tana matukar Tsoron su, daidai ta jikin adaidaitasahun su ta ga wani ya taho, saboda tsananin Tsoron da take ji ya sa ta ga kamar ita dokin ke kallo, a zabure ta manne jikinta Dana Abraham hadi da kamkame shi sosai ta boye fuskar ta a kirjin sa tace "wayyo Inna ta doki! bawan Allah kayi hakuri wallahi tsoron doki nake"

Duk da Abraham yaji wasu bakin al'amura a jikinsa amma ko gezau bai yi ba, "wacece wanna yarinyar da nake jin komai nata daban?" Ya tambayi kansa, kasancewar kuma bashi da mai bashi amsa ya sa shi kara lumshe idon sa yana jin yanda take goga masa fuskar ta a jikin sa, mai Dan sahu dake kallon su ta cikin mirror dariya ma yarinyar ta bashi...

Sai da ta daina jin takun tafiyar su kana ta dago kanta, wanda yayi daidai da bada hannu da akayi domin su wuce...

A hankali ta kalli yanda ta yamutsa masa farar Rigar sa, har kwallin ta ya bata Rigar, kunya ce ta kamata, kallon gefen fuskar sa dashi kadai tayi nasarar gani har yanzu, mamaki take ta yanda ko motsi bai yi ba, kana bai yi magana ba, ko dai kurma ne? Ta tambayi kanta, kasa tayi ta kanta a sanyaye tace "bawan Allah kayi hakuri kaji, wallahi tsoro nake ji"

Shiru babu amsa, dauke kanta tayi tana tunanin dai kurma ne, mayar da idanun ta tayi ga titi tana kallon jama'ar dake ta hada- hadar su, ga gidaje masu kyau da suke ta wujewa...

Mai adaidaitasahu yana jiran yaji Abraham yace zai sauka ya ji shiru gashi sun zo unguwar barnawa, ya kuma San idan ya tambaya ba lallai ya bashi amsa ba, kawai ya shiga cikin Layin domin sauke Indo, yana jinjina miskilanci irin na Abraham.

Daidai kofar gidan da bintu ke aiki mai keke ya tsaya, yace "yarinya mun iso, ga gidan Alhaji Umaru Kwangila nan"

Sauka Indo tayi tace "Nagode sosai ga kudin ka, amma dan Allah ka kira min lambar nan" Amsar takardan yayi yayinda Indo ta shiga kallon gidajen Alfarman dake unguwar....

Bude gajiyayun idanun sa yayi, ganin har an zo gate din kusa da gidan su ya bashi mamaki, domin bai sanar da mai keke hakan ba, domin duk a tunanin sa a titi mai keken zai sauke shi, sauka yayi ya zaro kudi da bai San nawa bane ya mikawa mai Dan sahu ya tafi, galala mai keke yayi ganin uban kudin daya bashi, "wani irin passenger na dauko yau ni zubairu" ya fada a hankali yana kara kallon kudin, sosai kuma yaji dadi, ya kuma sa a ransa cewa daga nan gida zai wuce domin ya tashi daga aiki yau...

Readers Also Read