Abraham complete by nooreemaan - Chapter 6
Abraham complete by nooreemaan Chapter 6: Abraham complete by nooreemaan Chapter 6. Indo da ta gama kallon ta ta dawo da idanun ta cikin keken taga wayam…
3,375 words
Indo da ta gama kallon ta ta dawo da idanun ta cikin keken taga wayam babu bawan Allah nan, yaushe ya sauka ta fada a ranta tana mamaki...
"gashi ta daga" mai keken ya mika mata wayar sa kirar vivo, fuskar sa fess kamar gonar auduga, amsa tayi tace "Adda bintu gani a kofar gidan, Indo ce."
Tana gama fadin haka ta mikawa mai keken waya, bata ma jira taji abinda bintu zata ce....
Mai keke kuwa yaja Dan sahun shi yayi gaba cikin nishadi, mintuna biyar kacal bintu ta fito da fara'a kan fuskar ta, rungume indo tayi kana ta dauki jakar Indon suka nufi gidan su Abraham, tana yaba mata da kokarin kawo kanta da ta yi....
WASAN YA SOMA GUYS🤩
Not edited 🤒
Share fisabilillah
Comment for more typing
If you re interested in my group just chat me up with this number 👇and I will add you. 07082281566
8:06am Sunday 23, January 2022.
NoorEemaan🦋
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 0806626851 [10/7, 7:50 PM] 💖NoorEemaan💖: 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇 ABRAHAM 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇
WATTPAD @NoorEemaan
ELEGANT ONLINE WRITER'S📚✍️
EDITING IS NOT ALLOWED❌
_assalma alaikum my lovely fans, musamman wadanda basu karanta Abraham ba sanda nake typing din shi, zan kara maimaita wa Abraham ba sabon novel bane reposting nake, ban kuma buɗe masa specific group ba kasancewar ba sabon typing bane, masu min magana private kan nayi adding din su a group din Abraham wasu na basu amsa Wasu kuma ban samu basu amsa ba domin abubuwan sun min yawa, to cut it short, Ban bude wa Abraham group ba, waccan maganar dana yi cewa duk mai so tayi magana ayi addinig din ta a group nayi shi ne lokacin da nake rubuta littafin, yanzu dai kara reposting nake, fatan kun gane, sai dai normal group Dina nan novels, idan kina so kya iya shiga, Ngd sosai da kaunar da kuke nunawa littafai na, jazakallahu khair_🫶🥰
Chapter 19-20
(Not edited)
K'wank'wasa karamar kofar Bintu tayi mai gadi ya leko da kansa, ganin bintu ce ya sa shi washe hakoran sa, bude musu kofar yayi suka shigo, a mutunce suka gaisa yana tsokanar Indo kasancewar shi mutum mai faram-faram da jama'a.
Sunyi dan tafiya kafin su kara so kofar da zai sada mutum da general falo, kallon gidan Indo take amma ba ta sigar kauyan ci ba, domin duk da cewa bata taba ganin gidaje masu kyau haka ba a kafatanin rayuwar ta amma still tayi behaving kanta, a kasan ranta kuwa jinjina tarin dukiyar da aka narka wurin gina wanna had'add'en gidan take...
Wani alarm dake manne a bango bintu ta danna yayi kara.
Madam Gloria dake zaune a daya daga cikin kujerun falo ta kwala Kiran daya daga cikin masu aikin ta da gurbataciyyar hausar ta , da ta dan koya a zaman ta a kaduna tace "Hajiyayye! Hajiyayye!! Zo ki Bude kofar falon nan"
Da gudu Wacce aka kira da Hajiyayye ta fito ta nufi kofar hadi da Bude wa, bintu ce ta fara shigowa kana Aysha ta biyo bayan ta cikin Sanyi da yanayin bakunta, "ke hajiyayye! Komai ya zama neat ko? Domin banason son ya daga ko digon datti daga zuwan shi"
Cikin ladabi hajiyayye da har ta soma tafiya tace "eh madam mun gama gyara komai"
"good"
madam Gloria ta fada cikin Izza kana tayi wa hajiyayye alamar ta tafi....
Cikin isa da takama ta dago kanta, fess ta sauke su kan Indo dake manne da bintu, Wani irin mahaukacin bugu kirjin ta yayi wanda hakan har ya nuna a saman fuskar ta, take taji tsanar Indo a ranta wanda bata taba yiwa wani mahaluki shi ba baya ga Abraham, kamar tace bata son yarinya amma ta kasa, domin ta hada duk qualities din da take so ga housemaid, amma me yasa taji wani irin yanayi a kallon farkon da ta yi wa yarinyar?
"madam ina ta gaisuwa" bintu ta katse mata tunanin ta.
Dan sakin fuska tayi kana tace "yawwa lafiya, wanna ce yarinyar?"
"eh itace madam, sunan ta Aysha"
"Ok! Ku zauna mana" ta fada a gadarance, tana kokarin controlling fad'uwar gaban da ya riske ta.
Zama suka yi yayin da Indo ke shigewa bintu domin wani mugun Tsoron matar ne ya shigeta at once, yayinda take jin gaban ta na tsananta fad'uwa....
"ya ya kike ce sunan ta?"
"Aysha"
"OK, Aysha kin iya gyaran gida, komai ya zama neat?"
"eh ta iya....."
"ki bari tayi magana ko? Or is she deaf?"
Madam Gloria ta fada tana tauna chewing gum hadi da yamutsa fuskar ta.
Shiru bintu tayi kana ta zunguri Indo alamun tayi magana, "e.... eh... eh... na iya" ta fada cikin cracking voice.
"what about cooking?" ta kara tambaya tana kallon Indo, rudewa Indo tayi ta mayar ta kallon ta ga bintu, "Addah me ta ce?" indo ta fada cikin rada.
"Cewa tayi kin iya girki" kasancewar bintu na Dan fahimtar turanci duk da cewa gidan bahaushe take aiki amma yaran gidan na son Rayuwar turawa daga nan take fahimtar wasu abubuwa.
"eh.. Na iya irin namu na kauye" ta fada gwanin tausayi.
Yamutsa fuska madam gloria tayi tace "wa zai ci na kauye? Kenan baki iya ba, anyway zan kira k'warariyyar mai girki domin ta koya miki"
"toh an gode kwarai madam, zan iya tafiya ko?" Bintu ta tambaya, yayin da a ranta tana fatan Indo ta iya zama da ita domin ta lura matar ba sauki, kuma yanzu ta fahimci hakan.
"eh! Zata fara aiki gobe, aikin ta shine gyara dakin na, da na yarona, girki da gyaran kitchen that's all, sannan salary dinta 70 thousand ne duk Wata"
Jinjina kai bintu tayi cikin jin dadi domin ko ita albashin ta bai kai haka ba, ta kuma yi wa Indo murna har ranta.
"toh Indo ni zan tafi, zan dinga shigowa duba ki bayan kwana biyu-biyu ki rike halayen ki na kirki, kar naji ance kin yi wani Abu mara kyau kinji ko?"
Jinjina kai Indo tayi tana kokarin hadiye kukan ta, da haka bintu ta fita, daya daga cikin masu aikin gidan mai suna lubabatu madam gloria ta sake kira domin ta nuna Indon dakin ta.
yarinyar mai shekaru ashirin da uku ce, har da taya Indo daukar ghanan most go suka bar falon, wani huci mai zafi madam gloria ta saki, domin tun ganin da ta yiwa indo gaban ta ke ta fad'uwa, wanda ta rasa dalilin haka.
Ta bangaren su Indo kuwa saman bene suka hau, inda dak'unan Abraham ne kawai a saman , sai wani daki can karshe Inda ba kowa, inda nan madam gloria ta sa aka gyara domin indo ta zauna, saboda a amatsayin ta na mai yi musu girki da gyara dakuna boys quarter yayi nisa, a cewar ta gwara tana kusa da su ta yanda ko wani Abu ake bukata ta dafa za a fi saurin sanar mata...
Daki daya ne babba inda aka yi masa paint da pitch color wanda ya fito da kyan dakin ainun, sai toilet dake cikin dakin, babu wasu tarkace a dakin daga dan madaidaicin gado sai wardrobe, hadi da dressing mirror da babu komai a kai, sai centre carpet dake shumfud'e saman tiles din kasa, ba laifi dakin ya hadu.
"yawwa ga sif dinki nan ki jera kayan ki a ciki, amma kafin nan bari na kawo miki abinci"
lubabatu na gama fadin haka ta bar dakin....
Kallon komai indo ke yi daki_daki, duk da cewa dakin yayi kyau sosai, sannan ko a mafarki bata taba shiga irin wanna had'add'en daki ba, kana bata taba sanin cewa zata mallaki irin wanna dakin ba, amma bai burgeta ba, kasancewar babu Innar da yan biyun ta a kusa, take hawaye ya biyo kucin ta sak'amak'on tuno su da ta yi, tun ba a je ko ina ba har ta fara shiga wani hali na tsananin kewa, jin alamun mutum ya taho wanda take da tabbacin lubabatu ce yasa ta share hawayen ta da sauri...
Ajiye Abincin lubabatu tayi tace "ga abinci nan ki ci"
"Nagode sosai" Indo ta fada kanta a kasa, murmurshi lubabatu tayi domin hakan nan taji lndo ta shiga ranta duk da cewa ta girme mata. Shiru dakin ya dauka, ganin cewa indon bata ci abincin ba ya sanya ta Mikewa hadi da cewa "bari na tafi domin ki samu ki ci abincin ki, sunana lubabatu, kefa? "
"Aysha Indo" ta amsa mata a takaice.
"masha Allah suna mai dadi da daraja, toh na tafi sai anjima ko"
"toh Nagode sosai" Indon ta kara fada.
Ta dauki tsawon mintuna goma tana tunani kana ta ja ajiyar zuciya hadi da Bude kwanon abincin.
Tuwon semonvita ne hadi da miyar ganye daya ji namomi, sai lemon exotic hadi da swan water mai Sanyi.
Duk da yanda abincin ya yi dadi, loma biyar kawai tayi ta wanke hannun ta, domin tunanin su Innah ne ya cika zuciyar ta, "ko sun ci abinci?" Sanin bata da amsa ya sanya ta rufe abinci ta Mike, toilet ta shiga Inda shima ya hadu sosai bata wani tsaya kallo ba ta shiga daura alwala cikin nutsuwa....
Kallon dakin tayi taga babu alamar sallaya, can ta tuno yanayin madam gloria din babu alamar musulunci a tare da ita, gefen wajen karshen gado ta karasa, dankwallinta ta warware ta shimfud'a a kasa, in da take dogon gashin ta mai tsaho, baki, hadi da tsantsi ya bayyana, hijab dinta ta mayar kanta kana ta tada sallar azahar da la'asar da bata yi ba....
Bayan ta iddar ta zauna tayi addu'o'inta sosai, gashi bata taho da qur'anin ta ba, gashi ta saba duk bayan sallah ta kan yi tilawa, can sai ga lubabatu ta kara dawowa, abincin ta Bude ta ce
" la la la ai baki ci komai ba?"
"wallahi na koshi" Aysha ta amsa tana murmurshi
"toh yanzu kina bukatar wani Abu ne?" lubabatu ta tambayeta.
"eh ina zan samu qur'ani in fansa Dan Allah, na manta nawa a gida"
"ai kuwa ina da guda biyu, ban ma fiye amfani dasu ba" ta fada a kunyace, domin sanin cewa hakan ba kyau, gashi kanwar bayanta ta fita himma wurin karanta littafi mai sarki, domin ita wani zubin a Wata bai fi tayi sau daya ba.
"amma kina kokarin yi kullum, ko da aya biyar ce ko uku, lada zaki samu, sannan zai taimaka miki wurin rike haddar ki, bazai zube ba" Indo ta fada cikin cool voice.
"in sha Allah zan yi kokarin yi kullum, Nagode kinji kanwata? Bari na dauko miki"
Jinjina kai Indo tayi kawai hadi da zuba tagumi, Bayan mintuna shida sai ga lubabatu ta dawo dauke da qur'ani, amsa aysha tayi cikin farinciki da godiya.
Kwanukan Lubabatu ta kwashe tace "toh sai gobe idan mun sake haduwa, domin ba a bari mu hau saman nan any how, yau ma darajar ki na ci na hau kusan sau hudu madam bata min masifa ba"
Murmushi kawai Indo tayi, Bayan Lubabatu ta fita,Aysha ta Bude qur'anin ta cikin suratul maryam, Aya goma ta karanta kana ta Mike ta ajiye qur'anin saman dressing mirror.
D'an k'wallinta ta mayar kanta hadi da bud'e wardrobe ta shiga jera kayan ta da ba wani yawa ne da su ba, sannan basu cika sabun ta ba, Bayan ta gama jerawa idanun ta ya sauka kan jakar da ta dauko a dakin baffa, a hankali tasa hannu ta dauki jakar, ido ta zubawa jakar kana ta mayar cikin Ghana most go dinta, zuge zip din jakar tayi ta rufe, kana ta saka a kasan sif din inda babu komai a ciki, kofar sif din ta rufe kana ta dawo bakin gado ta zauna, haka ta wuni sukuku ba motsin kowa, har tunani take anya zata iya yin wannan aikin? Amma idan ta tuno innar ta da Rayuwar da suke ciki sai taji kwarin guiwar yin aikin...
*************
Haka ta dinga juyi da daddare ta kasa bacci, Kiran sallar farko a kunne ta, Mikewa tayi domin bata ga amfanin kwanciyar ba tunda ba baccin take ba, toilet ta shiga tayi alwala kana ta fito, nafilfili ta shiga jerawa har aka tada sallar asuba, Bayan ta iddar ta shiga rera karatun qur'ani cikin zazzak'ar muryar ta mai sanyin amo.
Shida saura mintuna biyar ta shiga toilet, wanka tayi, hadi da brush kana ta fito daure da zanin ta, kurawa kanta ido tayi ta cikin madubi inda direct kan sarkan nan idonta ya sauka, hannu ta kai ta shafa sarkan, kullum sarkan kara kyau da sheki yake duk da dashi take wanke kullum.
Pomade din stella (mai gurguwa) da ta taho dashi ta shafa a jikin ta, wanda Inna ce ta siya mata ana yi gobe zata taho kaduna.
Doguwar rigar atamfa roba-roba ta sanya, d'ankwallinta ta daura hadi da sanya hijab dinta, duk da babu Kwalliya ko digo a fuskar ta amma tayi kyau ba laifi, sai dai rashin tsad'add'en mai na gyaran fata da karancin wayewa ya tauye tarin baiwar kyawun da take dashi.
Dan gyaran dakin ta tayi duk da bai yi wani datti ba, zama tayi na almost 1hr kana ta sauko down stairs...
Da wasu yammata biyu ta fara cin karo inda suke gyaran yalwataccen General falo, gaishe su tayi suka amsa hadi da bin ta da kallo....
Madam Gloria ce ta fito cikin takun dai-dai, kallo daya tayi wa aysha ta dauke kai hadi da cewa "shiga ki gyara dakin, if you're done sai ki hau sama ki gyarawa son na shi, anjima chef din zata zo"
"toh!" Aysha ta amsa cikin ladabi, duk da bata fahimci kalmar "chef" ba.
Falon madam Gloria ta fara gyara mata, kana ta shiga bedrooms din daya kasance biyu ta gyara ta goge, sai toilet da ta wanke ta goge, komai dai fess sai gyalli yake kai baka ce this is her first time ba, inda aikin ya dauke ta tsahon awa biyu.
Bayan ta gama ta fito, ta tarar da madam gloria hakimce a dinning area da alama breakfast take son yi.
" idan kin hau sama ki kira min son ya zo yayi having breakfast"
madam Gloria ta fada da wani irin tune daya Dan tsorata Indo domin kamar da fada-fada tayi mata.
"toh!" ta amsa a sanyaye yayinda ta cigaba da taka step case din, duk da ba duka abinda madam gloria ta fada ta gane ba.
Sama ta hau inda ta ga wasu kofofi biyu d'aya na zallan glass ne, shi din ta nufa wanda take Kyautata zaton shine dakin sa...
Gabanta na bugawa ta shiga knocking shiru,... Jin shiru yayi yawa ba motsin kowa sai kawai ta tura kofar hadi da zura kafar ciki inda ya sauka kan lallausan door mat...
*kuyi hakuri sisters ban samu zama bane shiyasa kuka jini shiru, kuyi manage da wannan, sai mun hadu a next page*
Share fisabillahi
Comment for more typing
NoorEemaan 07082281566
Thank you for reading my novel 🍇Abraham🍓
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 0806626851
https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din
https://chat.whatsapp.com/JwYkGXFKcLH95WSHP9QoUg [10/8, 8:42 AM] 💖NoorEemaan💖: 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇 ABRAHAM 🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇🍓🍇
*first edition*
*WATTPAD* @NoorEemaan
*please Don't forget to vote my story and also follow me on WATTPAD @NoorEemaan* love you all guys.
https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din
Chapter 21-22
(Not edited)
Lumshe sexy lulu eyes dinta tayi sak'amak'on sanyayyar kamashin room freshener daya daki hancinta, kana a hankali ta ware idanunta ta sauke su kan kayataccen falon daya gaji da haduwa, sai dai shiru ba motsin kowa sai k'aran Ac.
Wata kofa dake kallon gabas ta sauke idanunta a kai, a hankali ta fara takawa domin isa ga kofar, a gefe daya kuwa gabanta na tsananta fad'uwa... Hannu ta dora kan handle din kofar da niyyar bud'ewa, sai kuma tayi saurin dauke hannun ta, a hankali ta fara knocking... Shiru ba amsa, sannan ba motsin kowa har na tsawon mintuna biyar, gajiya ta fara yi da tsayuwa kasancewar ta mutum mara jurar tsayawa, shahada tayi ta bud'e kofar a hankali, kana ta shiga....
Ya subhanallah! Ta fada tana runtse idanunta da karfi sakamakon hangoshi da ta yi kwance kasan tiles babu riga a jikin sa sai dogon wandon jeans kirar company'n gucci, wanda hakan ya bawa manyan six packs din sa bayyana hadi da karfaffan hayyensa daya yi mata shi dasu.
A kafatanin rayuwar ta bata taba ganin da namiji haka ba, duba da irin gidan da ta fito, ta dauki tsawon mintuna bakwai a haka, kana kamar mai tsoron ganin wani mugun abu ta shiga Bude idanunta a hankali ta sauke kan k'yak'yawar fuskar sa dake bacci a tunanin ta, wanna karon gabanta ya fi d'azu fad'uwa saboda ganin kamanin Ammar dinta da Abraham, ba tare da kuma ta san maganar ta ta fito fili ba tace "Ammarrr" cikin sautin amo dake bayyana zallan mamaki, Ji tayi idan ta cigaba da tsayuwa a dakin komai zai faru, domin k'wak'walwarta ya gaza dauk'an abinda take gani, musamman kamanin su daya firgita ta, dan dai shi babba ne da ta ce tabbas Ammar din ta ne, cikin sassarfa ta juya domin barin dakin kamar a sama taji husky voice dinsa yace "hey! what did you want?" tilas ta tsaya cak! Gashi ya sake rudata da turanci sa da bata fahimci koda kalma daya ba... Abraham kuwa duk da yana cikin bacci, amma shigowar ta dakin ya sauya bugun zuciyar sa, wanda ya tilas ta masa farkawa daga dan baccin daya dauke sa, tabbas murya yarinyar daya ji a cikin adaidaita sahu ce, ya kuma sake tabbatar da hakan ta dalilin bugun zuciyar sa da ta sauya, wanda akan ta ne ya fara Jin hakan, mamaki yake kan meya kawo yarinyar cikin gidan su har dakinsa.
Jikin ta na bari, cikin rawar murya tace "ehm... Is your, is na mahaifiyar ka ta ce kazo kasan bene" ta fada cikin duburbucewa idanunta taf da k'walla...
Yamutsa fuska yayi domin ko kalma daya bai fahimta daga abinda tace ba, a hankali ya bud'e idanunsa da suka dan rine saboda jimawa da suka yi a rufe ya sauke su a kwanta, sai dai bayan ta kadai yake hangowa, ita kuwa jin bai sake magana ba yasa ta fita da gudu, ta nufi dakinta dake da dan nisa da nashi duk da saman bene ne.
ABRAHAM kuwa da kallo yabi bayanta, kana ya tabe bakin sa hadi da mikewa tsaye, toilet ya nufa domin yin wanka, shower ya kunna inda ruwan ya shiga dukan kansa zuwa jikinsa, a hankali muryata ya amsa kuwa a kunne sa "Ammarrr" ya maimaita kalmar can kasan makoshi, duk da bai san ma'anar sa ba, kawar da tunanin yayi ya cigaba da wankan sa inda mintuna ashirin ya dauka kana ya fito daure da farin towel.
Tsad'add'en lotion din sa ya shafa, kana yayi oiling kansa hadi da tajewa, gaban wardrobe din sa ya nufa, inda wayar sa ta fara ringing... Dubawa yayi ya ga MUM ce.
Amsawa yayi hadi da karawa a kunne sa,, "Good morning Mummy"
"morning my son, I sent the house-maid to tell you breakfast is ready and.........."
"am coming mum" ya fada yana katse Kiran ba tare da ya bari ta karasa maganar ta ba, sai yanzu da mummy ta fada ya san dalilin shigowar Yarinyar nan dakin shi, wardrobe din ya bude ya fito da wani crazy Jean trouser white, sai bakin riga mai botira hadi da dogon hannu, cikin mintuna biyar ya shirya cikin su, gaban inda tarin takalman sa suke ya nufa ya dauki wani black palm sandals na company dolce and gabbana ya sanya, agogon zallan sliver ya manna a hannun sa, ba karamin kyau mai tsayawa a rai yayi ba , Bud'e kofar yayi ya sauko kasa...