Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 13
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 13: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 13. Bayan mungaisa aunty tace, "toh maryam sedai ince Allah…
3,339 words
Bayan mungaisa aunty tace, "toh maryam sedai ince Allah yakaddara saduwarmu,dan yau zamu tafi, kafin kidawo daga school ma muntafi" cikin matsananciyar faduwar gaba nake kallon aunty, zuciyata na bugawa, yanxu su auntyn danake kallo nakejin dadi agidannan suma tafiya zasuyi. Cikin rawar murya nace, "aunty tun yau zaku tafi naga baku dade da zuwaba?" Murmushi aunty tayi tace, "Abbansu aliya yanata kirana indawo, ga kuma makarantar aliya,nima banso tafiyarba naso jiran dawowar yaya, danyacemun yakusa dawowa amma tafiyar tazamarmun dolene" shiru nayi bance komaiba. Janyoni aunty tayi ta kwantar da kaina akan kafadarta, cikin lallami ta fara mun magana. "Karki damu kanki maryam, nanbada jimawaba zakiga nadawo, bana jimawa nake dawowa, kinji maryam tah" gyada mata kai nayi ina kokarin maida kwallar data cikamun idona nace, "shikenan aunty kugaida gida, Allah yakiyaye hanya, amma zanyi kewarku sosai" shafa fuskata aunty tayi tace, "ameen maryama muma zamuyi kewarki, kedai kawai abunda nakeso dake kidage da karatunki kikuma kula da kanki, kikara hakuri akan Wanda kikeyi agidannan, duk abunda kike bukata kuma kitambayi sadiq kinji" "tom aunty nagode sosai da kulawarki agareni." Bakomai maryam, Allah yamiki albarka, kije kikarasa shirinki karkiyi latti, kafin kitafi kibiyo tanan zan baki sako, karki bari aliya ta tsaidaki da surutunta dannasan halinta,sarai.,seta makarantar dake" Murmushi nayi na mike nafice, zuciyata babu dadi kokadan.
Aliya nazaune a bakin hado ta rafka tagumi nashigo dakin da sallama ciki_ciki, tsayawa nayi kawai ina kallonta daga ganinta itama jikinta yayi week. Ahankali tadago da kanta ta zubamun ido, karasawa nayi bakin gadon nazauna agefenta dafa kafardarta nayi nace, "aliya Ashe yau zakutafi shine baki sanarmunba, seyanzu aunty take sanarmun" numfashi aliya tasauke tace, "kiyi hakuri maryam,aunty ce tace karna fada miki seyau,dantasan seki tashi hankalinki kikasa bacci." "Yanxu idan kuka tafi seyaushe?" Natambayeta idona nacikowa da kwalla, kwanaki ukunnan damukayi tare dasu jinta nake tamkar mundau wasu shekaru tare, yanzu idan suka tafi shikenan rayuwar kuncin danake agidannan zata dawo,tunda sukazo ko kallon banza babu Wanda yamun agidan se ranar da abunnan yafaru saboda ganin idon aunty. Na lura duka yaran gidan suna Shakkar aunty. Banmasan hawaye yafara zuba daga idonaba seda naji hannun aliya tana sharemun, itama idonta duk yayi kwal_kwal kamar zatayi kukan. gabadaya tausayin maryam yacika mata zuciya,tasan halin yan'uwanta sarai ba kirkine dasuba,tasan maryam zaman hakuri kawai takeyi agidannan. Rungumeta tayi tsam ajikinta ganin taki dena kukan, cikin rarrashi take bubbuga bayanta. Magana tafara mata cikin rarrashi da lallami akan tayi hakuri, insha Allahu dazarar anmusu hutun school zatazonan tayi hutunnata gabadaya tare da ita. Dakyar aliya tasamu maryam ta hakura tadena kukan. Toilet nashiga nakara wanke fuskata,sannan nadawo nakarasa shirina, aliya nata bani labaran bandariya duk dan nasaki jikina. Nikuma se nuku_nuku nakeyi naki tafiya, harseda yaya sadiq yakira wayar aliya akan yana waje yana jirana. Dakin mommy naje, namata sallama,yau dakantama tace intafi karnayi latti base nayi serving dinsu ba. Kuku harya gama hada breakfast yau da wuri, diddibarmun aliya tayi na tafi dashi, dakin aunty na koma kamar yadda tace. Wani littafin addu'oi ta dakko ta bani har guda biyu, tace nadaure nadinga karantawa arana koda saudayane. Godiya na kara mata sosai, itakuma tanata kwararamun addu'oi. Har bakin motar da yaya sadiq yake ciki aliya ta rakani. Abincin dake hannunta ta mikomun tare da fadin, "to maryam segani nabiyu" karba nayi cikin sanyin jiki nace, "nagode aliya,kugaida gida Allah yakiyaye hanya" "ameen" cewar aliya tana maida hankalinta akan yaya sadiq dake zaune acikin mota amma ya bude murfin, kafafunsama suna waje. yatsaya kawai yana kallonmu da sauraronmu. "Yaya sadiq ga maryam nan, dan Allah kakularmun da ita amana karka bari ko kuda yatabata, balle kuma wani Abu yabata mata rai." Murmushi mukayi nidashi saboda yanda aliya take maganar, yace, "baki da damuwa yarkanwata indai maryam ce zankula miki da ita fiye da yanda kike tunani." "Yawwa yayana, maryam bye bye, semunyi waya, insha Allah zandinga kiran wayar yaya sadiq muna gaisawa, I will miss u over" da kai kawai nabata amsa, saboda ina bude baki tsaf zan iya saka kuka, daurewa kawai nakeyi. Zagayawa nayi na shige cikin motar, daga mun hannu aliya tayi ta juya tatafi,ina binta da kallo. Tada motar danaji yaya sadiq yayi yasani dauke ido daga kanta,ina sauke ajiyar zuciya. Kallona yayi dasauri sekuma yadauke kansa yayi yaja motar muka tafi. Hawayen dake makale a idonane yasamu damar zirarowa, nikuma haka kaddarata take arayuwa, duk Wanda nakejin dadin zama dashi, sena rabu dashi..... "Yasalam, maryam! Kuka kuma, kiyi hakuri pls nasan kunyi sabo da aliya Wanda dole zakiji zafin rabuwarku, amma kukan bashine mafitaba, kidena kinji" murya yaya sadiq ta katsemun tunani. Daga masa kainayi ina share hawayena. "Yawwa kokefa, duk sanda kikeson ganin aliya na miki alkawari zankaiki, ammafa idan kindena kuka" dasauri nace, "nadena yaya sadiq Allah" murmushi yayi yace toh shikenan kyakkyawa" shiru nayi bance masa komaiba, shima yaya sadiq shirun yayi har muka karasa school din. Yau kam sukuku nayi a makarantar har zee seda tatambayeni ko bani da lafiya, nace mata lpy ta klu. Koda aka tashi nadawo gida, duk senaji gidan babu dadi, saboda su aliya suntafi kamar yadda aunty tace, zama nayi bayan nayi sallah na rafka tagumi ina tunanin rayuwata, ganin tunanin babu abunda ze karamun se damuna sena tashi na dakko littafin addu'ar da aunty ta bani, na karanta, cikin ikon Allah se zuciyata tayi sanyi,damuwata duk ta ragu. Haka rayuwa take Allah baya barin wani Dan wani yaji dadi. Bayan na gama karantawa na tashi naci gaba da ayyukana.........
*BAYAN KWANA UKU*
Rayuwata ta koma kamar tada agidan alh. Menasara,rayuwar kadaici da kunci da tsangwama agurin yaran gidan, a gurin yaya sadiq kawai nake samun sauki, bayan tafiyar su aliya munyi waya da ita har sau biyu, a wayar yaya sadiq, aunty ma haka. Harda yayantama mungaisa, yacemun aliya tanata damunsa da zancena. Dadin abunma ina zuwa makaranta, tanadaukemun kewa sosai, nasaba da zee sosai da sauran kawayenta, su salma da humaira. Kullum yaya sadiq ne yake kaini, driver kuma ya dakkoni. Yanzuma bana gamuwa da yaran gidan sosai, dan dasafe kafinma su fito natafi makaranta da rana idannadawo basanan sai dare muke haduwa.
Abangaren suhailat kuma, cin karanta take babu babbaka tunda aunty tatafi, kullum setaje gurin kamal sun sheke ayarsu, kuma ta dawo zuwa part din mustapha, danma yanzu kotaje bawani kulata yakeyi sosaiba sedai tagaji da zama da tatafi, babban abun dayake kara tada hankalinta yanzu ko hannunsa baya bari tataba. Ko zuwa tayi da niyyar tabashi kamar da, bata iyawa saboda babu fuska. Shikuma mustapha ayan kwanakinnan aiki yakeyi tukuru, gashi a week dinnan zeyi promotion na ma'aikata a companynsu dole ne ya nutsu yamaida hankali danganin yayi adalci ya'ajiye kowa a inda yadace dashi.
Yanzu kam yagane babban kuskuren daya tafka arayuwarsa na barin suhailat tana hugging dinshi da abubuwan dabasu daceba,ada baya daukar hakan amatsayin lefi saboda ganin suhailat cousin dinsace. Zuwannan da aunty tayi shiya kara tunatar dashi abunda yamanta, nasiha aunty tamasa sosai akan illar hakan,yasan aunty bata taba ganinsu a hakanba, kawaidai ta masa wa'azinne akan tunatarwa irinta da da uwa. shine dalilin dayasa yayiwa kansa alkawari idan ba aure sukayiba insha Allahu hakan bazata kara faruwa atsakaninsuba,sedai bisa kuskure. Mommy amatsayinta na uwarsu yakamata ace ita tafara nuna musu illar hakan, tunda sometimes agabanta suhailat din take hugging dinsa. Amma sedai tanuna jindadin hakan. Yana matukar son mommynsa amma bayason wasu halayennata, da first halinta dabayaso shine kyamar talaka, tana nuna musu takala bakowa bane, tana nuna musu talaka tamkar ba cikakken mutum bane. Alhalin Allah dakansa yafada shiyake bada wadata da arziki ga wanda yaso. Kuma badon yafisansa yabasaba, sedon ganin damarsa. kuma aduk sanda yaso ze iya kwacewa. To meyasa ita mommy bata tunanin wata rana suma zasu iya rasa tasu dukiyar, kokuma talakan datake rainawa yamusu ranar wani abun, domin kowa da irin baiwar da Allah yamasa. Sekuma hali na biyu na mahaifiyarsa dabayaso,macece ita me mugun son kanta da yayanta, kome yayanta zasuyi badaidaiba bazata musu maganaba, balle ta kwabesu. Komai sukayi nuna musu take daidaine, gashu kuma batadamu da musu wata kyakyakkyawar tarbiyyaba, ilimin addini kuwa duk basu dashi yanda yakamata, shima dan ya taba zama agurin auntyne lokacin su mommy dukansu suna america, shikadaine a naija, shiyasa yasamu ilimin addine sosai. Sekuma abu na uku, yanda mommy take juya mahaifinsu sekace wani danta, se'abunda tace yayi sannan zeyi, bayajin maganar kowa setata. Wadannan halaye na mahaifiyarsa bayasonsu kokadan, dandai babu yanda zeyine uwa, uwace tafi karfin wasa, sedai addu'a dabaya gajiyawa dayi mata akodayaushe akan Allah yaganar da ita gaskiya.....✍️
Meson complete Whatsapp 08166674823
*ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_
*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*
*Bismillahirrahmanirrahim*
2️⃣1️⃣
*BA EDITING YAU🤤😎*
........Yau asabar babu school hakan yasa bantashi da wuriba se wajen goma na tashi, ayyukana nayi duka, saboda yau ina gida. Amma kwanakin da suka shude bakomai nakeba nake tafiya school cikin abunda banayi harda gyaran dakin suhailat da mommy, senadawo nakeyi. Yau time din dana shiga dakinta bacci takeyi bata tashiba, ko agurin break ma banga tafitoba. Se bayan la'asar nagama aikina, saboda har wanki nayi. Ina gamawa nayi wanka nashirya cikin wata doguwar riga mara nauyi da hijabi karami irinna makannan, acikin siyayyar kayan da yaya sadiq yasiyomun jiyane. Duk wani Abu na amfanin mata seda yasiyomun jiya har kayan unders yasiyomun dasu pad, siyayya yamun sosai ta bajinta, duk a kokarinsa na ganin narage damuwa, ga wani tattali da kulawa dayake bani na musamman. nikam nikadai nasan halin danake ciki saboda rashin ganin mustapha, zuwa yanzukam nafara tunanin akwai wani Abu dayake faruka dani akansa, tunaninsa da wani abu dabansa komeneba ya yawaita araina, kullum bana iya bacci sena dauko rigarsa dake gurina nashaki kamshinsa sannan nake samun nutsuwa. Yau kwanana biyar banganshiba tun ranar da abunnan yafaru, wata mahaukaciyar kewarsa naji tacikamun zuciya. Duk wannan abun dake damun maryam akan mustapha kokadan batayi tunanin so bane, dan ita bama tasan menesodinba, anata shirmen kawai burgeta yakeyi. Bayan na idar da sallane, nadakko addu'ar da aunty tabani nakaranta.
Wajen 2/30 mommy ta aiko wata me aiki kirana, a kitchen naje nasameta tanata hada kayan snacks tana package dinsu, sannu da aiki namata,amsawa tayi takara da fadin, "maryam Ku kwashi kayannan dakeda jummai kukai part din my son yanada bakine.'' Cikin faduwar gaba na'amsa da to. Ambatarsa da mommy tayi kawai yajefani cikin wani irin yanayi na doki da zumudin ganinsa, a wasu kwanduna masu kyau madaidaita guda biyu mommy tajera kayan, daya na dauka itama jumman tadauki daya, mukanufi part dinnasa zuciyata na bugawa kadan_kadan. Sama_sama muke dan hira da jummai, har muka karasa part dinnasa. Wata bugawa zuciyata tayi lokacin damukasha part dinnasa, dan banyi zaton ganinsa a falon kasaba, amma muna shiga dashi nafara cin karo, se sauran abokannasa da sunkai su six, wata boyayyiyar ajiyar zuciya nasauke, daddadan kamshinsa gabadaya ya mamayemun hancina. Gaishesu muka hauyi daya bayan daya, suna amsawa cikin sakin fuska, shine na karshen gaisuwar saboda yanacan gefene yanata faman latsa waya, tun shigowarmu ko motsawa beyiba balle yadago ya kallemu, gaisuwarma da muka masa hannu kawai yadaga mana, batare daya dagoba. Kananun kayane ajikinsa, Wanda suka matukar yimasa kyau, idanunsa sanye da wani siririn glass baki, tsintsiyar hannunsa nadauke da wata azurfa, tunda nazo gidan duk sanda zangansa da ita nake ganinsa, se kuma wani zobe na azurfa me kyau shima, yasa adanyatsansa na tsakiya,dayan hannunnasa kuma agogene shima me kyau. Acikin yan sakanni nakaremasa kallo, jinakeyi dama karna dena kallonnasa, sefaman sauke ajiyar zuciya nakeyi ahankali. Cikin tsananin farin cikin ganinsa na karasa dinning na ajiye kayan hannuna, senajini nadawo daidai dana gansa. "Oh Allah ni maryam me nakeji haka akan wannan bawan Allan ne?" Nafadi haka araina cikin mamakin wannan bakon al'amari agareni. Daya daga cikin abokan musty mesuna fahad se kallon maryam yakeyi tunda tashigo yarinyar ta masa kyau matuka, nakusa dashine yazunguresa tare da fadin, "fahad kaga wata yar baby, mekyau ko?" Sauke numfashi fahad yayi yace, "hmmm kaidai bari faruq bakaga nasaki baki ina kallontaba" "wlh aboki babyn tayifa" cewar faruq dayakebin maryam da kallo dasuke kokarin fita. Dakatar da ita fahad yayi da fadin, "yan mata yazaki tafi baki gama aikinkiba?" jin maganar mutum kamar dani yake sena juyo ina kallonsa amma bance komai ba, dagemun gira yayi tare da fadin, "eh mana baki zuba mana abunda kika kawo manaba, gashi naga kina kokarin fita, danni nan dakika ganni bakaramar yunwa nakejiba, dan zuwa gurin dinning dinma wahala ze bani" lukman dasuke hira da sauran abokannasu yayi murmushi me sauti danya gano inda fahad yadosa akan maryam. Shikam tunranda yafara ganin yarinyar yaji ta burgeshi amma bawai sonta yakeba, dan yana da budurwarsa bikinsama saura 2 weeks dalilin bikinnema yahadasu anan dansu tattauna. Nima murmushi nayi ganin yanda yayi maganar na juya da nufin zubo musu. Mustapha dake zaune yana saurarensu yadago yace, "ke!" Cak na tsaya cikin matukar tsorata saboda cikin kakkausar murya yayi maganar, bejira amsataba yanunamun kofa alamun na fice. Sum_sum naja kafata nafice dama jummai tayi gaba abinta.
Galala su lukman suka tsaya suna kallonsa, shikuwa yawani maze tamkar bashi yayi maganarba yacigaba da latsawayarsa hankalinsa kwance. "Haba musty bayan muguntar daka mana, kaki fadamana kanada kanwa kamar wannan,sannan yanzu kuma naganta dakaina shine zaka korarmun ita, bamugama magana da itaba" cewar fahad yana hararar mustapha, a tunaninsa maryam cousin din mustapha ce, danbata masa kala da me aikiba,kuma harwata kama yaga sunayi. Banza mustapha yamasa danyasan halin fahad dama, shiyasa ya kora maryam, danyanzu seyace yana sonta. "To namamajo, aidama tunda naga kallonta nagane inda kadosa" cewar lukman yana dariya, suma sauran dariya sukasa ganin yanda fahad ya wani kebe fuska. "Ah, karna kalleta tamunne ai, idan kasamu wannan amata ai kagama dacewa, ga kyau ga nutsuwa da kamala ga hankali, nidai gaskiya tamun zanje nasamu mommy mugana,aknta" "irinkune maso jawa mutum raini, yanzu wannan yarinyar karama zakace kanaso, to tun wurima kacireta daga ranka dan ammata miji" mustapha yafadi haka batare daya dagoba. Kallonsa suke gabadayansu yanda ya wani maze tamkar bashi yayi maganarba. Faruq ne ya amshe zancen dacewa, "mene abun raini aciki, ai irin wadannan matan inkasamesu kagama morewa" "bari kaidai abokina, katayani da addu'a kawai Allah yasa nadace agurinta, koma wane mijin da'aka mata kwaf daya zanmasa na kwacemasa ita, yan bakin ciki kuma sedai suga anayi ehe!" cewar fahad yana mikewa zuwa dinning danya debo kayan da kansa. Banza musty yamasa bece kalaba, shifa dagaske yake har cikin zuciyarsa gani yake rainine kace kanason mata kananu kamar maryam, mema zasu iya yimaka, sedai suta maka shirme,da shiririta.🤤🥺
Ina tafe ina gulmarsa acikin zuciyata, haushi duk ya isheni nikadai nasan dadin danaji sanda abokinshi yakirani, ko banza zanta kallonsa amma yanzu yamun bukulu ya koroni. A kofar part dinmu naga yaya sadiq tsaye yazubamun ido kawai yana kallona harna karaso kusa dashi. "Yaya sadiq barka da warhaka" muryar maryam ta katse masa tunanin daya tafi akanta, firgigit yadawo daga duniyar daya lula yace, "yawwa maryam ya gida ya weekend?" "Lafiya kalau yaya" "to masha Allah, anjimafa bayan la'asar me lesson dinnaki zefara zuwa" "eh yaya banmantaba aina zamuyine?" Juyawa yaya sadiq yayi yanunamun wata yar rumfa dake dan nesa damu, yace, "acan zakuyi" "toh yaya nagode sosai da dawainiyar da kakemun, Allah yakara budi yabiyaka da aljannah" "ameen, maryam,kinyi kyaufa" rufe fuskata nayi cikin jin kunya nace, "nagode" murmusawa yayi yana binta da kallo. Maryam tana matukar burgesa komai tayi kyau take masa, gawani bakon al'amari dayakeji akanta. sallama namasa na wuce ciki,bin bayanta da kallo sadiq yayi harta shige, ajiyar zuciya yasauke ya juya yatafi. A falo natarar da mommy da suhailat, araina nace, "seyanzu tatashi kenan" gaisheta nayi bata amsamunba sedai uwar harara tare da mugun kallo data bini dashi, dama jiya kafin natafi school bamu rabu ta dadiba, masifa tayitayi akan ina tafiya ina barin aiki, wai dole sedai idannagama aikin natafi makarantar ko karfe nawane, mommy ce ta tausheta shine ta hakura da kyar. Ko dakina banshigaba nanufi dakinta, na gyara mata. Gyaran dakinta yana daukarmun lokaci saboda kodayaushe kaca_kaca yake, kamar me yara kanana dabata gyara dakin. Bata kintsa komai, komai taci kota cire atsakar dakin zata barbarzar, kuma haryanzu ninake wanke mata kayan unders dinta. Bayan nagama na koma dakina nayi sallar la'asar sannan na tattara duk abunda zan bukata nanufi gurin lesson dinmu. Me lesson din haryazo, gaisawa mukayi babu bata lokaci, yafaramun. Me lesson din yana da kirki sosai, gashi da faran faran, kuma alhamdulillah nagane sosai, da kananun sentence na turanci yafaramun, yakuma rubutamun sunan wasu littattafai yace nabawa yaya sadiq yasiyomun, se wajen magriba muka gama yatafi. Danayi sallahma nayita bitar abunda yakoyamun harya zauna daram akaina.
Washegari, tun kiran farko mommy tazo tatasheni da kanta, dayake yau natashi nayi sallar dare, ina kan dadduma naji ana knocking kofata, cike da mamaki da tsoro nace, "waye?" Sai naji muryar mommy ce ta amsa, shine hankalina ya kwanta naje na bude. Sanarmun tayi na fito aikine damu yau megidan ze dawo, babu bata lokaci nabita zuwa kitchen. Aiki muka kama bakama kafar yaro, nifa har yanzu nadena mamaki, wai duk wannan kayan ciye_ciyen duk akan mutum daya akeyi, sukuma haka masu kudi suke, ina mutum zekai wannan abincin. Har gyaran gida ranar na musamman akayi, komai ankara tsaftaceshi na wanki an wanke, na gogewa an goge, gabadaya part din mommy ya kaure da kamshi, saboda turarukan da'aketa sanyawa, duk da ba'a part din ze saukaba, dannaji sanda mommy tatura aje agyara masa part dinsa. Gabadaya yan gidan kowa kaga fuskarsa cike da annuri da farin ciki take, hatta masu aiki kuwa, saboda dawowar megidan. Fara'ar dabantaba ganiba yau naganta a fuskar mommy da suhailat, se buge_bugen waya sukeyi suna fada alh. zedawo. Gaskiya mahaifi akwai dadi, yanda suke murna da rawar jiki,banga lefinsuba akan dawowarsa, inama nima zanga mahaifina, inama nima nawa mahaifin zedawo gareni, da kuwa duk wani bakin cikin dake zuciyata nasan seya yaye. Gaskiya masu iyaye araye kuma atare dasu sunji dadinsu.(Allah kabarmu da iyayenmu, kakuma rabamu dasu lafiya, Wanda suka rigamu gidan gaskiya kuma, Allah yagafarta musu. Ameen).
Se bayan azhar nasamu kaina, jikina duk yayi tubus da gajiya, ko karyawa banyiba yau,yunwa se nukurkusata takeyi, abinci nadiba naci, kadannema yasamu yashiga cikinnawa, kamshi duk yagama cikamun ciki, ruwa na watsa nafito nayi sallah, lafiyar gado nabi domin rama bashin baccin dake kaina........
Gabadaya ahalin gidan alh.menasara yau suna cike da murna da farincikin dawowarsa gida, dan gaskiya ya jima a tafiyar dayayi. Ma'aikatan gidanma ba'abarsu abayaba wajen taya murna, domin sunsan idanyadawo kakarsu ta yanke saka. Mutum ne shi me kirki, baya kyamar talaka ko kadan, gashi da kyauta sabanin mommy dabata kyauta kokadan, shiyasa yayanta duk ita suka gado, mustapha ne kadai me wannan kyautar irintashi, se sadiq dake bimasa baya. Karfe uku jirginsu ze sauka, tun karfe 2 kowa nagidan ya shirya dan tarboshi, harda mustapha dake cike da farinciki shima, sekuma abokan alh. Menasaran dasuma zasuje tarbar tasa. 2/40 a filin airport din ta musu suna jiran saukarsa......
Cikin farin ciki yake sakkowa daga matattakalar jirgin fuskarsa dauke da annuri, lumshe idonsa yayi cikin Jin dadin shakar iskar kasarsa me albarka dayayi. Alh. Menasara kenan, mutum me cikar zati da kamala hadi da kwarjini, kamarsa daya sak da sadiq kamartasu harta baci, hatta duhun fatarsu dayane. Masha Allah kyakkyawane shima, dan har yafi mommy kyau sedai kawai ta nuna masa hasken fata. Fuskarsa dauke da fara'a yake tafiya cikin nutsuwa,iyalansa da abokanansa suna ganinsa suka karaso garesa, da gudu haidar da zannurain suka fada jikinsa cikin tsananin murna. Rungumesu yayi tsam ajikinsa shima yana shafa kawunansu. "Welcome dad" suka fada atare. "Thank u dears" yabasu amsa, daidai nan su mommy suka karaso garesa, kowa narige_rigen hugging daddy. Daya bayan daya yake rungumesu suna gaisawa, mustapha ne na karshe daya tsaya kawai yana kallonsu cike da sha'awa, fuskarsa cike da annuri. Takawa daddy yayi har daf dashi yayi hugging dinsa yana fadin, "Muhammad dina, I really missed u'' lumshe idonsa yayi cikin kaunar mahaifinnasa yace, "missed u too dad'' shafa kansa daddy yayi cike da matsananciyar kaunarsa. Sannan yasakesa suka shiga gaisawa da abokanansa kuma amininansa. Dunguma sukayi duka zuwa mota.......