Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 12
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 12: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 12. Tunda muka idar da sallah aliya taketa mita da…
3,271 words
Tunda muka idar da sallah aliya taketa mita da masifa,akan abunda yafaru, nidai shiru namata na kwanta, saboda matsanancin ciwon dakaina yakemun. Seda aka kirata awayane nasamu sa'idar mitartata. Dukda matsanancin ciwon dakaina yakemun haka na yunkura, nafito falo saboda ganin 9 harta gota, nasan ni suke jira inyi serving nasu. Ilai kuwa, dukansu suna zaune a kan dinning din harda yaya sadiq. Kuramun ido yayi yana kallona, amma becemun komaiba,harna karasa garesu, inadan jin tsoro ganin babu aunty a falon, karnaje sumin wani abun dadintama da yaya sadiq. Amma senaga babu yakoda kalleni, ajiyar zuciya nasauke. Cikin sanyin jiki nafara serving dinnasu, inayi ina taune lips dina saboda azabar ciwon kai. Takan yaya faruq nafara, inakan yaya sadiq,aunty tafito. Kallon maryam kawai aunty tayi, tagane batajin dadi, dama tasan kukan datasha seya samata ciwon kai. "Maryam, kibarshi kikoma daki kikwanta, aliya tazo ta karasa,tunda naga bakyajin dadi." cewar aunty, bayan taja kujera tazauna agefen mommy. Dama hutunnakeda bukata, dan harwani jiri_jiri nakeji. Kai nagyadawa aunty kawai najuya, aliyanma harta fito, sannu tamun takarasa dinning din,nikuma nashige daki. Ajiyar zuciya sadiq yasauke, bayan maryam tabar falon yadubi aunty yace, "aunty meke damuntane wai, nagama idanunta kamar kuka tayi" "ciwon kai" aunty tabashi amsa atakaice. Aliya ta bude baki zatayi magana aunty ta harareta, dauke kanta tayi tafara rattabowa yaya sadiq bayanin abunda yafaru, duk hararar da aunty take aika mata kuwa, seda takai aya, ta tsaya. Suhailat ma cike da jin haushinta take harararta, itafa shiyasa batason yarinyarnan shegen surutu gareta da shishshigi. Jinjina kai kawai sadiq yake cikin takaicin halin mahaifiyarsa da yan'uwansa. Shiyasa tunda yashigo yaga fuskokinsu babu walwala, kamar ko yaushe. Hakadai sukayi dinner yau kowa zuciyarsa babudadi.
Ina kwance bacci yaki daukata,aunty tashigo dakin hannunta dauke da plate da ruwa. Ajiyewa tayi tahau tashina atunaninta bacci nakeyi. Tashi zaune nayi, tace nasakko naci abinci nasha magani, senafi jin dadin baccin. Banmata musuba na sakkowa naci abincin kadan, aunty taitai nakara nace mata nakoshi, maganin tabani nasha nakoma na kwanta, itakuma tafice tanamun addu'ar samun sauki. Har bacci yafara daukata Aliya tashigo dakin, wayarta tasamu a kunnena wai yaya sadiq zemun magana. Karba nayi na rike, sallamar dayamun na amsa. Cikin murayata dako fita batayi saboda baccin danakeji. Sannu yamun, yakuma bani hakuri akan abunda yafaru, nuna masa nayi babu komai, mukayi sallama nabawa aliya wayarta, nagyara kwanciyata,nakoma baccina.........✍️ Meson complete Whatsapp 08166674823
*ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_
*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*
*Bismillahirrahmanirrahim*
1️⃣9️⃣
..........Da matukar bakin ciki suhailat tayi daren yau, gashi ita babbar damuwarta fushin mustapha, idanunta kawai hasko mata sanda abunda yafaru sukeyi,yanda taga ransa ya matukar baci, ita bataga wani abun bacin rai acikin abunda tayiwa maryam ba, kuma koma metayi mata aiduk akansane. Juyi tayi akan makeken gadonta datake kwance, kusan 12 nadare Amma babu bacci Sam a idonta, tun dazu take kiran wayarasa taki shiga,gashi texts take tura masa naban hakuri tare da kalaman soyayya, amma shiru babu reply. Tafin hannunta takai ta shafi kuncinta, haryanxu tanajin wani dimmm akunnenta na Marin datasha. Mikewa zaune tayi saboda wani kunci dayaziyarci zuciyarta. "Wai yanzu akan wannan kucakar yarinyar ya mareni" ta fadi haka a fili cikin tsananin takaici, kwafa tayi aranta tana kissima irin muguntar dazatayiwa maryam kala kala a gidannan. Kiran wayarta da'akayine ya katse mata tunanin ta, koda bata dubaba tasan kowaye, kamal ne. Banza tayi da wayar, shikuma yayi ta nacin kira, tsaki taja a fili. Sannan ta tashi ta dakko wayar, tayi picking, suka fara hirarsu wadda rabi duk batsace,wayartasu da kamal dinnema tadan rage mata damuwa......
Abangaren mustapha kuwa besan sanda bacci yayi awongaba dashiba. Wajen 1 na dare, yafarka a matukar firgice bakinsa dauke da addu'a saboda wani mugun mafarki dayayi,wanda yakasa fahimtar me mafarkin yake nufi. Gaba daya yahada wata uwar zufa, duk da fankar dake kadawa a dakin, danya kashe a.c tun kafin yakwanta. Sosai mafarkin ya firgitashi amma yakasa tuno komai acikin mafarkin. Ajiyar zuciya yake saukewa akai_akai, abunda kwakwalwarsa ta iya tuno masa shine yaga wata yarinya a mafarkin, da wasu mata da wani namiji, kuma duk kamar yasansu a mafarkin,amma yakasa tunosu azahiri. Korar tunanin mafarkin yayi daga ransa, dan mafarki ba gaskiya bane. Mikewa yayi cikin sanyin jiki ya nufi toilet yadauro alwala,yadawo yafara jero nafilfili kamar yadda yasaba a kowanne daren Allah........
Abangaren sadiq kuwa, tausayin maryam gabadaya yacika masa zuciya, baya kaunar halin mahaifiyarsa dana yan'uwansa kokadan,dandai babu yanda zeyine. Da tunanin maryam ya kwana aransa cikin wani irin bakon yanayi me wuyar fassaruwa agareshi........
*WASHEGARI*
Mustapha kamar yadda yasaba, kullum bayan yafito daga masallaci ya nufi part din mommy, dakin mommy yafara shiga suka gaisa sannan ya nufi dakin aunty. Aunty na zaune akan darduma tana lazimi yashigo dakin, zama yayi agefenta. Yana fadin, "asamu a addu'a aunty" murmushi aunty tayi tace, "insha Allah, addu'a ai kullum cikin ymuku ita mukeyi." Cike da kaunar kanwar mahaifinnasa yagaisheta. Amsawa aunty tayi tare da gyara zama tace, "dama tun jiya inason magana dakai, sekuma bamu haduba" maida hankalinsa yayi duka ga auntyn amma bece komaiba. Cigaba da magana aunty tayi. "Mustapha meyasa jiya ka mari suhailat, nayi mamaki gaskiya dan nasan hakan ba halinka bane?" "Aunty nikaina bansan sanda na maretanba,Abunda tayine ya matukar konamun rai shiyasa" yafadi ahaka muryasa adakile. "Shikenan mustapha amma adai, kiyaye gaba, dan wataran ma'aurata zaku zama kaida ita, jirama nake yaya yadawo kasarnan, ayi maganar aurenku, shekarunku sunja,karatun ta karasa adakinta. Danyanzu ko su haidar da zannurain sun isa aure, balle kuma kai." Kwantar da kansa yayi ajikin aunty yace, "duk yanda kikace haka za'ayi little mom, Allah yatabbatar mana da alkhairinsa." Shafa kansa aunty tayi, tace "ameen" cike da tsananin kaunarsa da tausayinsa, tarasa meyasa takejin tausayinsa aranta, kuma tun yana karami takejin hakan akansa, alhalin babu abunda yanema yarasa arayuwarsa. shiyasa duk miskilancinsa seda tajawoshi jikinta sosai, haryayi matukar sabo da ita, yake kuma sanar mata da duk wata matsalarsa. Hira suka dan taba akan kasuwanci da kuma halin rayuwa, duk da karfin hirar aunty cekeyi. Sannan yatafi....
Duk murna da dokin danakeyi na zuwa school, duk babu dana tashi saboda da bacin rai na kwanta. Ciwon kan dake damuna yasauka sosai, yanayin danake jima kafin na kwanta duk babu, amma zuciyata ce sam babu dadi. Ina idar da sallar asuba, nafara ayyukana, sharar falo nayi da mopping sekuma wanke_wanken kayan da'aci abinci dadaddare. Inagama wanke_wanken nashirya komai tsaf, tare da shareshi shima nayi mopping. Ina kokarin fita daga kitchen din, kuku yashigo, sama_sama muka gaisa dashi bakamar kullumba dayake tsayar dani da surutunsa, duk da hausarsa ko fita batayi,amma munashan hira dashi. harna koma dakina aliya baccintatake, dama tana idar da sallah ta koma. Toilet na nufa na wanke, sannan nayi wanka. Uniform din makarantar na dakko da nufin shiryawa, riga da wadone rigar har gwiwa, se wani karamin hijabi iya kafada.
Tsayawa kawai nayi ina kallon kayan, ina tunanin tayanda zansakasu, harna iya fita dasu ahaka. Ganin lokaci yana kuremunne yasa kawai na daure nasaka, sunkoyi dass ajikina, tsayawa nayi agaban mudubi ina karewa kaina kallo, kayan sunyimun kyau sosai,sedai rigarce ta kamani daga kirjina. Dankwali na daura,nadakko hijabin danayi sallah nafito falo. Kuku begama breakfast ba, gashi har 7/30 tayi. Babuma Wanda yafito acikin gidan. Dakin aunty nanufa, knocking nayi tabani izinin shiga. Da sallama nashiga. Zama nayi akan carpet din dake gaban gadon, ita kuma aunty tana kan dadduma da'alama karatun alkur'ani takeyi, saboda kur'anin dana gani agabanta. Gaisheta nayi ta amsamun cikin fara'arta. Bayan mungama gaisawarne, cikin ladabi nadubeta nace, "Aunty dama nashiryane zamu tafi makarantar, kuma naga haryanzu ko abincin kuku begama hadawa balle nayi serving dinku, kuma yaya sadiq 7/40 yacemun zamu tafi." "Badamuwa maryam, kije kutafi schl din, tunda kinga yau zaki fara zuwa karki fara da latti, aliya tayi serving dinnamu, amma kafin ki tafi kishiga kisanar da aunty atika" "tom aunty nagode senadawo" "yawwa maryam, Allah yakiyaye yabada sa'a, kikula sosai kinji, banda kawaye barkatai,kiyi karatunki kawai" "insha Allah aunty zankiyaye" nafadi haka ina mikewa, tsaidani aunty tayi, hang bag dinta naga ta dakko, kudi ta dakko naira 500 ta mikomun. Girgiza kainayi nace, "kibarshi kawai aunty" batarai aunty tayi tace, "bansan musu maryam, bakici komaiba zaki tafi sannan kuma kiki karbar kudi, kiduba inda ake ajiye kayan snacks a kitchen kidauka kihada da yoghurt wannan kudin kuma kyayi break dashi" amsa nayi namata godiya nafice, cike da kaunarta dakuma yabon halinta. Cikin tsoro nanufi dakin mommy danbansan da fuskar dazata tarbeniba, amma abun mamaki senaganta kamar babu abunda yafaru, takarbeni kamar kullum fuskarta babu yabo ba fallasa, dana fada mata abunda kefaruwama tace muje bakomai, Allah yabada sa'a. Kitchen nashiga na dakko cake da yoghurt kamar yadda aunty ta umarceni, dakina na koma domin dakko school bag dina. Aliya natar tana waya.
Murmushi kawai na mata, cike da mamakinta ko gajiya batayi da waya. cire hijabin jikina nayi, na dakko karamun na makarantar nasaka. "Wow maryam, wlh bakiga yadda uniform dinnan ya miki kyauaba" "aike dama komai kyau yake mun" nabata amsa ina rataya jakata. "Allah dagaske nake maryam, yamiki bala'in kyau, karkijefa ki tadawa malaman makarantar hankali" hararta nayi na dauki hijab din dana cire nakara mayarwa, dangaskiya bazan iya fita hakaba, inajin kunya. Idannaje bakin get nacire naninke nasa ajaka. "Yaya sadiq nefa yakirani yanzu shinema yatasheni daga bacci, yace yana waje yana kiranki,tun dazu." "Ohk,bari nakarasa, sena dawo, bye" "Allah yakiyaye I will miss u wlh" cewar aliya tana marairaicewa. murmushi namata nace, "nima zanyi kewarki sosai da surutunki" dariya mukasa dukanmu namata sallama, na tafi. A bakin part dinmu, naci karo da yaya sadiq, yana kokarin shiga. Cikin mutuntawa mukagaisa, yana sanarmun dama yanzu yake shirin shiga yakirani yaji shiru. Duk da hijabin dake jikina,amma seda yaya sadiq yace kayan sunmun kyau sosai. Godiya na masa cikin jin kunya. Muna tafe muna hirarmu akan makarantar, harmuka karasa parking space. Damuka shiga motane yake kara bani hakuri, akan abunda yafaru jiya, nuna masa nayi bakomai ninama manta. Duk da abun yana raina, musammanma yanayin dana baro yaya mustapha, haka kawai tun jiyan naji badadi saboda fushin dayayi, yauma da kwadayin son ganinsa natashi, inason naganshi naga halin dayake ciki. Harmukaje makarantar tunaninshi kawai nakeyi. Seda muka fara zuwa office din principle sannan akasa wata tarakani class dinmu. Yaya sadiq ma yabani kudi,tun a mota. Duk dagewar danayi bazan karbaba, nakuma sanar masa aunty tabani, amma yabata rai yace dole sena karba. Ganin ransa ya baci sena karba namasa godiya. Bansan yazan misaltamuku yanda nakejin zuciyataba ahalin yanzu, wani irin yanayi take ciki kamar nadamuwa. Amma hakan behanani yin farin cikiba, saboda ganina a makaranta a kuma aji. Ajin yankadan natarar time din dana shiga, kuma mata da mazane a ajin, duk senaji kunya ta lullubeni danni nasaba makarantarmu matane zalla,gashi nacire hijab dina, sekarami na makarantar kawai. Sallama naiwa matan dana tarar a ajin, se bina sukeyi da kallo, duk senaji na tsargu. Watace tamun magana da fara'arta ta kuma nunamun kusa da ita, tace nazo na zauna. Godiya na mata nazauna, tambayata tayi sunana nafada mata. *MARYAM AHMAD* ita kuma tacemun sunanta, *ZAINAB ILYAS MIJINYAWA* banfi 5 minutes dazamaba, malami yashigo ajin..........
Gaskiya makarantar ana karatu sosai, gashi ajin babu yawa. Wani abunnagane wani kuma banganeba, saboda matsalar turanci daba komai nake jiba. Zee mijinyawa tana da kirki sosai, da'aka fito break duk abunda banganeba ita takaramun bayaninsa da hausa,nakuwa gane sosai. Ban fita ko'inaba cake dindanazo dashi naci, itadai zee tafita. Naji dadin makarantar sosai gaskiya, banfuskanci wata matsalaba kodaga gurin sauran yan aji. Malamaima kowa yashigo seya tambayeni sunana, tare damun welcoming. Karfe 2/15 ake tashi daga makarantar. Da'aka tashi tare muka fito da zee da wasu kawayenta, bayan tabani aron books dinta nayi copy note a gida. Kamar yadda yaya sadiq yacemun direba zezo yadaukeni, hakance ta kasance kuwa. Ta gurin number motar nagane shi, saboda duka motocin gidan anrubuta *MENASARA* .yana bakin gate yana jirana kuwa, sallama naiwa su zee nashige muka tafi gida, zuciyata cike da farincikin yau gani na koma karatu,da yardar Allah zancika burina,dana innata.
Mintuna kalililan muka karasa gidan,dama makarantar babu nisa,koda kafama zan iya dawowa. A parking space nakara maida hijabina, danga masu aikin gidan sunata kaikawo, a makarantar ma dan babu yanda zanyine. Aunty da mommy da aliyane, zaune a falon sama. Da sallama nashiga. Atare duk suka amsamun suna kallona, dagudu aliya tataho ta rungume ni, aunty na mata fadan kardai ta kadani. Nima rungumeta nayi cikin murnar ganinta. Jakata ta karba, sannu da gida naiwa su aunty, aunty tamun sannu da zuwa da tambayata ya karatun, mommy kuwa sedai kallonnanta muka shige daki. Aliya kamar ta lasheni, dan murnar dawowata waidama tagaji da zaman kadaici. Kozama banba nashige toilet na watsa ruwa tare da dauro alwala nafito nayi sallah. Kafin na idar aliya harta kawomun abinci,da ruwa. Allah sarki aliya masoyiyar asali, komai nata idan tayi tana tunamun da salimat ne, itama haka take nunamun irin wannan kaunar. Ina cin abinci ina bata labarin school din. Bayan nagama cin abincin na dakko jakata, kudin da aunty da yaya sadiq suka bani nanunawa aliya, cewa tayi na ajiye watara zasumun amfani. Rabawa nayi nabata rabi, amma tacemun wlh bazata karbaba. Cikin jin haushinta na'ajiye kudin, na dakko littafaina na fara kwafar note, itama aliya wani ta dakko tana tayani. Rubutun dayawa, dan anyi nisa a term din. Har bayan magriba muna note din, sallah ce kawai ketadamu. Badon mungamaba,sedon hannunmu dasuka gaji muka bar note din haka gobe nakarasa. Tun dayamma yaya sadiq yakira aliya, wai yaji kona dawo gida. Banima wayartayi mukayi magana, ya tambayeni ya school din da kuma karatu. Nace masa komai lpy klu,sai godiyar Allah.....
Suhailat yau bata dawo gidaba se daf da magriba, kuma tun 9 ta fice. Saboda tabiya ta gurin kamal sunyi badakalarsu, ahakanma daurewa tayi tadawo badon sungaji,dajunaba. Tanata yamutsa fuska tashigo gidan ita adole ta gaji. Mommy sewani lallabata takeyi ita kuma tana wani narkewa. Aunty datun yamma tafara mitar dadewar suhailat din, batayi shiruba data dawo seda tatambayeta dalilin dadewarta. Cemata tayi practical suka tsayayi. Seda tayi wanka ta shirya, da nufin zuwa part din mustapha, amma aunty tahanata zuwa. Aganin aunty hakan bedaceba,yarinya budurwa taringa zuwa part din namiji, aiko uwa daya uba daya kuke bedaceba, balle su da'akwai soyayya atsakaninsu. Ran,suhailat a matukar bace ta koma dakinta, ita tamatsu aunty ta tafi saboda tagaji da takurarta, dama ita takurane da ita, a cewar suhailat fa......✍️
Meson complete Whatsapp 08166674823
*ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_
*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*
*Bismillahirrahmanirrahim*
2️⃣0️⃣
............Zama tayi abakin gadonta cike da takaicin hanata zuwa ganin masoyinta da aunty tayi, gashi tun tana school takirashi bedagaba kuma bebiyo bayan kirannataba, datace bazata kara kiransaba itama zatayi zuciya dashi, amma takasa zuciyarta bazata iyaba. Wayarta dake hannunta ta kunna ta kara dialing number sa akaro naba adadi,daga jiya zuwa yau. Mustapha yana zaune a falonsa yana kallon news a TV, kiran waya yashigo wayarsa, dakko wayar yayi yaga suhailat ce, dafe kansa yayi, yaga missed calls dinta dayawa kuma yace zekirata amma shaf yamanta. Rejecting yayi ya kirata. Cikin zumudi suhailat tadaga wayar danda tayi tunanin rejecting yayi badon yakirataba. Wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke jin daddadar muryarsa ta doki kunnenta da sallama. Maimakon ta amsa sallamartasa seta samasa kukan shagwaba, lumshe idonsa yayi tare da taune lips dinsa, bayason kuka kokadan arayuwarsa kona yara bayasonji balle na mace, kukan mace yana taba masa zuciya. Fesar da iska yayi daga bakinsa yace, "autar mommyyyy"! Yanda yaja sunannata seda taji wani yarrrr ajikinta, itafa ko muryarsa taji tada mata da sha'awa take, balle kuma taganta agabansa,ita kadai tasan metakeji. Cikin kukan tace, "na'am" "menene?" Yatambayeta cikin sigar rarrashi,tausayinta gabadaya yacika masa zuciya, shima ba'asonranta yake mata abubuwa kodan tsananin sonda take masa, amma suhailat dince idan baya mata haka bazatana shiga taitayintaba. Cikin shagwaba ta fara masa korafin kira da texts datayita masa,ganin ya sakko,haryana mata magana cikin sanyin rai. Rarrashinta yafarayi, tare da mata nasiha akan abunda tayi. Hakuri tabashi tace masa tadena. Cigaba ta masa da surutu cikin jin dadi, da farincikin sun shirya, shikuma sedai kawai yabita da um, ko um'um. Hakan baya damun suhailat danta riga tasaba da wannan halinnasa. Itadai burinta yacika tundadai yasakko daga fushin dayake da ita. Damashi haka yake, wani lokacin yanada saurin sauka, wani lokacin kuma seda kyar.......
Falo muka fito nida aliya, yau kam tanacemun mu fita muyi hira bamusu nafito. dukansu samarin gidan da aunty da mommy suna zaune a falon, amma banda oga da suhailat,da yaya sadiq. Wani tunanine ya darsu a zuciyata, na maybe suna tare a part dinsa, wani iri naji, zuciyata babu dadi, Tambayar kaina nayi araina. "Wai ma mene ruwana acikin rayuwarsu danake damunkaina?" Musammanma shi mustapha danake yawan tunaninshi, kuma aduk lokacin dana tunashi se gaba ya fadi. Nakan alakanta hakan da matsanancin tsoronsa danakeji, danshi mutum ne me kwarjini, kuma ni a sanin dana masa masifaffene, gashi ya iya daka tsawa,me hautsina yayan cikin mutum. Lumshe idona nayi ina fasalto kyakkyawar fuskarshi acikin zuciyata, Wanda bansan yazan fasalta muku shiba azahiri. Narasa ina yagado wannan kyawun nasa, dan mommy dai da sauran yan gidan duka basu kaishi kyauba, amma nafi inatunanin a wurin mahaifinsa yagada, tunda shikadaine bantaba ganiba agidan. Wata doguwar ajiyar zuciya nasauke, aliya dake gefena suna hirarsu ta juyo ta kalleni da Sauri, ahankali naji tace, "lafiyarki kuwa maryam?" Bude idona nayi nakalleta nace, "lafiya ta kalau,me kika gani" girgizamun kai tayi alamun ba komai, ta juya sukacigaba da hirarsu. Hira sukeyi amma hankalina gabadaya baya kan hirar tasu, addu'a kawai nakeyi araina. Allah yakawo abunda zesa mommy ta aikeni part din yaya mustapha, dalilin fitowatama daga daki kenan,amma naji shiru yau bata aikeniba. Har ka kira sallar isha'i muna falon, ayanda nakeji araina jinake kamar nacewa mommy bata da aikene yau gurin yaya mustapha, wani irin azalzala zuciyata takemun nason ganinsa. Cikin sanyin jiki natashi nanufi dakina donyin sallah, adakinma seda aliya tatambayeni wai meke damuna,nace mata babu komai domin ni kaina bansan mezance mataba, banmasan abunda ke damuna dinba. Haka nakarasa daren yau jikina duk asanyaye, gashi bansamu damar ganinnasaba. Abincima kadan natsakura naci, yaya sadiq ma harkiran aliya yakarayi awaya ta bani, yahau tambayata wai meke damuna yaganni kamar mara lafiya, amasar dai dayace bakomai, gajiyar school ce kawai, nace masa. yanzu yaya sadiq yaragemun magana acikin yan'uwansa,tsakanina dashi gaisuwace kawai, tunda aliya tazo gidan sedai yakirata awaya Muyi magana.
Bayan mungama dinner na kwashi kayan da'aka bata na wanke. Aliya yau bata tayaniba tana dakin aunty time din danayima. Ina gamawa nadawo dakina nashiga toilet fitsari nayi tare da dauro alwala nadawo nahaye gadona nakwanta, bajimawa bacci yadaukeni dan gaskiya banajin dadin jikina, kuma jikinnawa da yar gajiya. Wajen 11 saura aliya tadawo dakin, kallon maryam tayi cikin jimami da tausayinta, danyanda ta lura da maryam irin mutanennanne da damuwa take wahalar dasu sosai. Gobe zasu koma k.d shine dalilinma dayasa ta dade adakin aunty har wannan lokacin suna hada kayansu, dukda kayannasu bawani yawane dasuba, tsabaracema meyawa saboda kowa nagidan yakawowa aunty tasa shine suka tsaya shirya kayan,dama da niyyar kwana uku sukazo, aunty tazone kawai taga yanda suke. Aliya jitayi kamar tafasa bin aunty gobe, setaji batason barin maryam ita kadai,jikinta gabadaya yayi la'asar. Cikin sanyin jiki ta tattara duk wani nata dake dakin maryam ta hade guri guda, a hang bag dinta. Dama su agogontane da abun hannunta. Kashemusu light din dakin tayi ta kwanta agefen maryam,zuciyarta babu dadi.......
Washegari tare mukayi aiki da aliya yau itama bata koma bacciba. Dayake mu biyune kafin 7 mungama komai, wanka nayi nashirya cikin uniform dina sabo, dan set biyu aka bani a makarantar. Kamar jiya yauma hijabi nadora akai nanufi dakin aunty,danna gaisheta.