Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 11
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 11: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 11. Tsayawa tayi cak, bayan ta karaso kofar gidannata cike da…
3,186 words
Tsayawa tayi cak, bayan ta karaso kofar gidannata cike da mamakin ganin Wanda batayi zaton ganinsaba. "Malam audu!" Gwaggo ta ambata cikin mamaki. "Na'am ladi, kinyi mamakin ganina ko?" "Sosaima malam audu, Ashe rai kanga rai, shigo_shigo maraba lale marhabun" gwaggo tayi gaba yana binta abaya, se kallon gidan yake, yana mamakin yanda gidan duk yabi ya mutu, ga tarin ledodi da abubuwa na rashin shara. Rabonsa da gidan tun mutuwar inna. (Malam audu, dan'uwan mijin innane, wato kakan maryam, kani yake agurinsa, inafatan kun gane) atsakar gida cikin datti gwaggo ta masa shimfidar tabarma, zama yayi adarare. Gwaggo ta dakko kujerar tsuguno ta zauna,ko tunanin kawo masa ruwa batayiba. Suka gaisa, gwaggo se washe masa baki takeyi, saboda tasan malam audu, shime alkhairi ne, ko lokacin da inna take raye shikadai yake waiwayarta ayan uwan mijinta. Gyara zama malam audu yayi yace, "ladi ina jikartawane, banga gilmawartaba kotana makarantane." Cikin kaudi inna tace, "eh, tana makaranta aidayake bata wasa da karatu akwaita da himma" "ai hakan yanada kyau, Dama zuwa nayi ince tashirya ta hada kayanta, idan zan koma gobe Lagos dim, mutafi tare ta koma hannuna da zama, tunda kinga ke macece, ita kuma yarinyarnan........ "Malam Audu, mekake nufi maryam din zaka rabani da ita?" Gwaggo ta katsesa cikin karaji, fara'ar dake fuskata gaba daya ta dauke. Batajira amsarsaba, cikin makirci ta fashe da kukan munafurci, tana fadin. "Yanzu maryam din danake gani inji dadima, ita kake kokarin rabani da ita, ko tausayina bakaji, tunda ni Allah bebani haihuwaba, ita kadai nake kalla inji dadi,shine kake kokarin rabani da ita" Tausasa murya malam audu yayi yace, "bahaka bane ladi, rayuwafa yanzu ta sauya, rikon maryam da namiji yadace ba maceba, yarinyarnan yanzu koda aurantane ya tashi a misali, bata da kowa wani namiji tsayayye daze tsaya mata, nikuma kinga kafinnazo garinnanma senadauki shekaru,shiyasa naga gwara ace tana hannuna" kafewa gwaggo tayi ita bazata bada maryamba, shikuma malam audu yasan halin gwaggo sarai, babu Allah aranta, shiyasa yakeson yadauke maryam daga hannunta, dan yarinyar tana matukar bashi tausayi.
Ganin inna ta kafe se malam audu yace, "shikenan ladi tunda kinkafe bazakibada maryam ba, insha Allah zandinga kokarin wajen ganin ina ziyartarku akai_akai, yanzu bari najira tadawo daga makarantar naganta sena wuce." Cike da rashin gaskiya, inna tace, "ai ba makarantar jeka kadawo takeba, makarantar kwana takeyi" "haba ladi, kanki daya kuwa zakidau yarinya marainiyar Allah, kikaita wata makarantar kwana?" Malam audu yafadi haka cikin dan fada. "To, malam audu itafa yarinyarnan ita tace tanason makarantarnan" "to kuma dantace tanaso seki biye mata kikaita, ai ita yarinyace kuriciya nadamunta, ke kuma......"Haba malam audu, kazo se masifa kakemun, nimafa maryam dinnan jininace bazan cutar da itaba, kuma makarantar ba ita kadai tatafiba, harda kawarta tanan gidan saleemat, kuma shi alh. Adon shiya kaisu da kansa" ajiyar zuciya malam audu, yasauke domin yasan mahaifin saleemat, mutumin kirkine. "Shikenan ladi, wacce makarantarce sena biya naga maryam din" sosa kai gwaggo tahauyi cikin in'ina tace, "um..um, kajima sunan makarantar ya kwantamun, kasanni dake ba bokonnayiba barikewa nakeba" cikin takaici malam audu, yafarawa gwaggo fada, danta fara kaishi bango, ganin sakacinnata yayi yawa, banda haka kadauki yarinya kakaita makaranta,amma kace kamanta sunan makarantar. Gwaggo datasan bata da gaskiya anan, kuma tana tsoron yaganota setahau bashi hakuri, tace masa bari taje gidansu saleeman tatambayo.....
Saleemat yau bataje school ba saboda ciwon marar daya addaba mata tun cikin dare, seyanzu datasha magani tasamu ya sarara mata. Fitowa tsakar gida tayi, ta kama shara, umma nahanata, amma tace ta barshi zata iya taji sauki. "Suwaiba, suwaiba!" Abunda gwaggo tashigo gidan tana fada kenan ko sallama babu. Umma dake hura wuta tafito daga kitchen din tana fadin. "Na'am gwaggo lafiya?" "Inafa lafiya suwaiba, wannan jarababben dan ka'idar yazomun,zedaga mun hankali" "wakenan gwaggo?" "Malam audu na Lagos mana...labarin abunda yafaru tsakaninsu gwaggo ta bata atakaice, ta kara da fadin, "suwaiba kitaimakeni kifadamun sunan wata makarantar kwana ta gwamnati da kika sani, infada masa. Idanyaje yagama bulayinsa ba'asametaba,aiya hakura." Cike da mamakin halin gwaggo umma take kallonta, cikin sauke numfashi tace mata, "kice masa nannan shekara take" "yawwa suwaiba nagode" gwaggo ta fadi haka, tare da juyawa ta fice." Saleemat dake tsaye rike da tsintsiya tace, "haba umma, yazaki fada mata, kenan kina goyon bayan karyar datayi?" "Bagoyon bayan karyar gwaggo nakeba, saleemat, kinsan halin gwaggo yanzu idan banfada mataba, seta hauni da tsinuwa ta tataramun jama'a, kibarta kawai kome tayi ita da Allah, insha Allahu aikatau din data tura maryam, seya zamo mata alkhairi." "Shikenan umma, Allah yasa" cike da kewa da begen kawar kirki, kuma yar'uwa, saleemat tacigaba da shararta. Itama umma, komawa kitchen tayi tacigaba da aikinta. Malam audu, bejira komaiba yashuri takalminsa bayan gwaggo ta fada masa sunan makarantar, yafice domin zuwa dubata,gwaggo tana ala raka taki a zuciyarta.........
*___________________________* *ALH. MENASARA HOUSE* *____________________________*
Bayan sallar magriba mommy ta aiko kirana, danaje setacemun induba kitchen ta hadawa son dinta abinci, inkaimasa,amsa mata nayi nafito. Dakina nadawo,domin neman rakiyar aliya zuciyata cike da tsoro. Amma senaga bata dakin, dakin aunty na nufa, tanacan kuwa. Dubanta nayi bayan nayi sallama sun amsa nace, "Aliya dan Allah zokirakani nakaiwa yaya mustapha abinci part dinsa" zaro ido waje aliya tayi tace, "cabdijan, rufamun asiri, inkin ganni a lahira kaini akai, aini nan dakika ganni bana kaunar abunda zehadani da yaya, kinga dadin danakeji kuwa,dabaya zama a part dinnan sosai" "haba aliyata dan Allah kizo kirakani kinga darene tsoron hanya nakeji" "mene hakane aliya, kitashi ki rakata mana" cewar aunty. "Nifa yanzu ina zuwa, zefara hararata yanacemun parrot ko turkartive." "To karya yayi, bahaka kikeba, kitashi kuje,aidama ba tsari tatafi ita kadai,part dinnasa." gwalo nayiwa aliya, ina kunshe dariya nafice, tashi tayi tana babbata rai ta biyoni abaya. Dundu tadakamun abaya, bayan munfito. Dariya na mata nashige kitchen nadakko basket din da'aka hada masa abincin. Tunkafin musauka kasama muka shirya da aliya, tafaramun surutu. Tunda muka tunkaro part din gabana yake dukan tara_tara, nikam narasa wannan bawan Allah, meyaymun nake tsoronsa haka. Aliyama tsit tayi daga hirar datakemun, dataga munhau falon sama. Ahankali na murda handle din kofar falon, dama nice agaba, dan aliyama dacewa tayi bazata shigaba a waje zata tsaya,seda naroketa sannan ta yarda zata bini har ciki.
Mustapha yau bedawo dawuriba daga office, saboda meeting din dasukayi bayan antashi daga aiki. A matukar gajiye, yadawo ga kuma yunwa datake nukurkusarsa, dan yau dabinone kawai acikinsa dayaci a office, sekuma coffee dayasha. Yana dawowa wanka kawai yayi, yaje yayi sallar magriba, seyanzu kuma daya dawo, shine yakira mommy tasa akawo masa abinci. Yana zaune a kujerar dake pacing kofar shigowa falon, suhailat tana gefensa, wai tazo ganinsa yau gaba daya bata ganshiba, tayi kewarsa. Da sallama dauke a bakina nashiga, ina sauke wata boyayyiyar ajiyar zuciyata, saboda daddadan kamshinsa daya ziyarci hancina. wata irin bugawa zuciyata tayi saboda ganin suhailat a falon, tawani kura masa ido se kallonsa take. Sekace ta samu TV, shikuma yanata sana'ar tasa latsa waya. Tunda nazo gidan nasan da labarin auransu, amma bantaba ganinsu tare irin hakaba, wani Abu naji yaziyarci zuciyata. Karasawa nayi cikin falon, gaishesu nayi, shidai naga sanda ya amsamun, ta hanyar motsin da kyawawan labbansa sukai, lokacin dana saci kallonsa. ita kuwa suhailat wani banzan kallo ta bini dashi. Ajiye kayan nayi, akan dinning da Sauri, na juyo da niyyar fita, haka kawai naji banji dadin ganinsu tareba, komeyasa oho?, kumama banmanta da rikicinmu na riga dashiba.. Se'a lokacin na lura Ashe aliya bata shigo falonba, makalewa tayi a corridor. "Ke!" Naji muryar aunty suhailat, nasan dani take dan haka natsaya cak. "Ke wacce irin mahaukaciyace, kuma dabba, jaka Mara lissafi." Cikin jin zafin kalamanta na juyo ina kallonta amma bance mata komaiba. Kawai jinayi ta tsinkamun mari, batare dana mata lefin komaiba, dafe kuncina nayi, idona na cikowa da kwalla dama kwana 2, bansha wulakancintaba. Cigaba da magana tayi cikin karaji, "matsiyacin ubanki ne zezo yazuba masa abincin, dazaki fice baki zuba masaba, banza me kamada alade, har ina miki magana kinamun shiru, kinwani tsareni da wadannan idanunnaki tamkar na mujiya" muryana na rawa ina shirin fashewa da kuka, nace, "kiyi hakuri aunty suhailat, bansan yanzu zeci abincinbane, shiyasa banzuba masaba" "aidama tunda ke jakace baki da kwakwalwa, kwakwalwarki ta kifice,bazaki saniba, stupid kawai idiot,m"........Marin da mustapha yasakarmata a kuncine, yasata hadiye maganarta, batare data shiryaba ba.........✍️
JUMA'AT MUBARAK*_
Gaskia bakuma LITTAFIN nan COMMENTS ko baku sone a daina yinsa😒🥴 Meson complete Whatsapp 08166674823
ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_
*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*
*Bismillahirrahmanirrahim*
1️⃣8️⃣
.........Ba suhailat kadaiba, nikaina na matukar firgita da Marin daya mata. Cike da tsantsar mamaki tare da al'ajabi suhailat ta dafe kuncinta, tare da dago kanta ta zuba masa idanuwanta cikin son tabbatar da shidinne take gani agabanta, kuma haryadaga hannu ya mareta, abunda koda tana karama betaba mataba, anya kuwa ba mafarki takeba. Mustapha dake tsaye yana jifanta da wani kallo shima cikin tsantasar bacin rai, jikinsa har tsuma yakeyi, idanunnan sunkada sunyi jajur. Yariga yasan halin suhailat na rashin da'a da mutunci, amma betaba tunanin abunnata yakai hakaba. cikin tsananin bakin da takaici suhailat tace, "yanzu yaya akan wannan...... "shut up!, stupid. Get out"!!!!!! Yafadi haka cikin tsawa da karaji, tare da nuna mata kofa da hannunsa. baya naja dasauri saboda matukar tsorata jikina harya fara tsuma,tsawar tasa har cikin tsakiyar kaina najita. Juyawa tayi tafara tafiya fuuuu tamkar zata tashi sama har bangaje maryam tayi, ta fice daga falon,hawayen bakin ciki nazirara daga idonta,tasan halinsa idan taki fita,seyayimata abunda yafi mari agaban wannan banzar yarinyar. Maida kallonsa yayi ga maryam, ya galla mata wata uwar harara. Cikin kakkausar murya yacemata. "what are you waiting for?" Aikafinma yakarasa najuya nafice dagudu, zuciyata na luguden bugu. Komawa kan kujera yayi yazauna, yana maida numfashi. Kansa dake saramasa, saboda yar hayaniyarnan yadafe, zuciyarsa na masa zafi. Kokadan bayason yaga anacin zarafin dan'adam da Allah yabasa daraja, da kima,irin haka. Lumshe kyawawan idanunsa yayi tare da kwantar da kansa ajikin kujera,cikin kunar zuci......
A corridor mukayi kicibus da aliya,kankameta nayi inasakin kuka me tsuma zuciya,Wanda bansan dalilinsaba,kalaman suhailat dai,nasaba dajinsu,marinma bayau tafara munba,kawaidai hoton yanda nashigo nagansu yaki bacemun daga idona. Rungumeta aliya tayi tsam ajikinta tana dan bubbuga bayanta, cikin tsananin tausayawa, duk da batasan meyafaruba, amma tasan halin suhailat, gashi kuma taga itama ta fito a fusace tana hawaye. Kusan 2 minutes sannan tazareta daga jikinta, tare da kama hannunta suka fara tafiya batare datacemata komaiba.
Mommy da aunty dasu haidar ne zaune a falo, amma banda yaya sadiq. Tamkar ancillota sukaga tafado falon dagudu tana kuka. Dasauri mommy ta mike tatareta cikin rudewa take tambayar, "lafiya,meyafaru?" Kowa na falon zuba mata ido yayi yana kallonta. Bata bata amsaba, se kankameta datayi tana sakin kukan banza. Girgizata mommy tahauyi, cikin dimuwa tana fadin, "daughter wai menene, kinsa hankalina yatashi kowani abunne yasamu my son,pls tell me what happen?" Cikin kuka suhailat tace, "mommy wlh yau sewaccan bakar yarinyar yar matsiyata tabar gidannan,tunda bagidan ubanta bane." "Wacce yarinyar kenan daughter?" Mommy tatambayi suhailat tana dagota daga jikinta. Gabadaya hankalin mommy idan yayi dubu yatashi, saboda ganin yartata na kuka, Wanda tamanta rabon dataga tana kuka irin haka, ba mommy kadaiba sukansu su haidar hankalinsu atashe yake, duk sunyo kanta suna mata tambayoyi,cikin rudewa. Aunty dai kawai tsayawa tayi tana kallon ikon Allah,duk da itama hankalinnata yadan tashi,danda farko da suhailat tashigo tadauka wani mummunan abunne yafaru. tsagaita kukan suhailat tayi cikin shan majina tace, "mommy yaya nefa yamareni akan na mari waccan banzar me aikin" zaro ido waje mommy tayi tace, "shi son dinne ya mareki dakansa, akanme to, akan wanne dalili?" hada karya da gaskiya suhailat tayi tafadawa mommy, wai maryam dince tamata rashin kunya,kuma tahada mata makirci har yayan ya mareta. Jinjina kai mommy tahauyi cikin bacin rai, tace. "Aidama talaka be iya samun guriba, tana gidan ubanki tanacin arziki shine zata miki haka, lallai kan mage yawaye." Haidar ne ya amshe zancen dacewa, "kyaleta mommy, zata shigo tasameni, zatasan akanta aka mari suhailat, sena rama mata Marin akanta" zama mommy tayi tare da dora suhailat akan cinyarta, tafara rarrashinta tare da share mata hawaye.
Adaidai lokacin mukashigo falon, wata mahaukaciyar faduwar gabace ta ziyarceni, ganinsu duka a falon, zannurain da haidar sunyi tsaye cirko_cirko, fuskarsu na nuna tsantsar bacin rai. yaya faruq kuma yana zaune, yana latsa wayar sa, tamkarma besan abunda ke faruwaba. Idonane yasauka akan mommy, tsantsar bacin rai da fushi na hango afuskarta, Wanda tunda nazo gidan bantaba ganiba, wani mugun kallo take jehomun. Kasa nayi dakaina dasauri zuciyata na bugawa da sauri_sauri dama nasan alhakalin marinnan akaina ze kare. Aunty kuwa kallonsu kawai takeyi baki bude, yanda duk suka wani rude, suna tada jijiyoyin wuya akan anmari suhailat. Tasan mustapha, tasan halinsa akan dan karamin Abu baze mari suhailat ba. Cikin sanyin jiki nake taka kafata har tsakiyar falon a matukar tsorace. aliya dake gaba tsayawa tayi ganinsu ahaka, tamkar Wanda aka aiko musu sakon mutuwa. Cikin zafin rai haidar yayi kan maryam danufin yarufeta da duka.
fahimtar hakan yasa aunty mikewa da sauri, ta kare maryam, tare da tsaida haidar da fadin, "haba haidar mekake shirinyine dukanta zakayi kome, aiba itace da lefiba tunda ba ita ta mari suhailat dinba" tsayawa haidar yayi, jikinsa na tsuma se huci yakeyi, yana jifan maryam da wani mugun kallo,amma bece komaiba. "Haba aunty,kibarshi mana ya hukuntata,bakiji me suhailat tace bane, aikome meyafaru itace sila" cewar zannurain. Hararsa aunty tayi tace, "kai kazo kahukuntata dinmana" nidai ina bayan aunty na boye, ina zubar da hawayen bakin ciki. Cikin fusata mommy tasauke suhailat daka kan cinyarta ta mike tsaye tana duban aunty tace, "menene hakane saudart, yazakihana yara su hukuntata, wato kinzabi bare akan yar,dan'uwanki kenanan, gaskiya ni kidenamun irin wannan,tunda kikazo gidannan sewani jajjan yarinyarnan kikeyi ajiki, sekace kekika kawota, ina ni nakawota gidannan,dan haka dani da yayana, muna dadamar yimata duk abunda mukaga dama." Masifa sosai mommy tahauyi, mamakintane yacikamun zuciya dama masifaffiyace haka, wani matsanancin tsoronta ne yashigeni, danni arayuwata banason masifa da fada. Girgiza kai kawai aunty tayi, amma batace mata komaiba, hartakai aya. Yanda ta wani hakikance tana bala'i, duk maganganu na rashin tarbiyya da da'a, dayarta ta fada,tare da muggan kalamai akan yarwani bata kwabetaba, sema goyon bayanta datayi. "Allah yabaki hakuri, aunty atika, nibanyi haka da wata manufaba,banyi kuma danna bata miki raiba" aunty tafadi haka, tare da kama hannuna, tajani zuwa dakinta. Aliya dakebin kowa da kallo, tamkar TV tasauke numfashi tare da juyawa tabi bayan uwarta. Da harara suhailat ta bisu duka, cikin jin takaicin hana dukan maryam da aunty tayi tace, "yanzu mommy kina kallo ta janyeta,amma bazaki hanaba, nidai gaskiya mommy yarinyarnan tabar gidannan kawai, hakanne zesa hankalina ya kwanta,danni gaskiya nafara tunanin mayyace" cikin rarrashi mommy tace, "kiyi hakuri daughter, nikadai nasan matakin dazan dauka akanta, ai saudat din zata bar gidan ba dawwama zatayiba, seta gwammace kida da karatu," lallaba yayanta mommy tahauyi, musammanma suhailat da haydar, harta samu suka sakko, takuma cewa suhailat ta kwantar da hankalinta zataje ta samu mustapha har part dinnasa da kanta,ta masa magana,takuma basa hakurin fushin dayayi da ita.
Adakin aunty kuwa, maryam sekuka takeyi ita setabar gidan, saboda ta matukar tsorata dasu mommy, tasan daba aunty yau, kashinta ya gama bushewa, gashi shima yaya sadiq bayanan, dama shikadaine me kaunarta agidan. Aunty ce, tahau lallacinta tare da lallabata akan ta kwantar da hankalinta babu abunda zasu mata, masifar iya yauce kawai daga yanzu angama. Aliya tambayar aunty tahauyi wai meyafaru?" Dubanta aunty tayi tace, "bansaniba sarkin son zance, naga ai tare kuka je, komai agabanki yafaru" shiru aliya tayi, dantasan idan tacewa aunty batashiga ba fada zata mata. Ajiyar zuciya kawai nake saukewa, saboda kukan danaci. Kaina nakan cinyar aunty, itakuma tana shafa kaina cikin tausayawa. Kiran sallar, isha'i ne yatadamu, aunty tashige toilet din dake dakinta, nikuma nida aliya muka fice zuwa dakina. Suna zaune a falon dukansu har yanzu, sunkuyar da kaina kasa nayi banyarda nahada ido da kowannensuba. Suhailat kuwa bin maryam take da wani mugun kallo, cikin tsana, tanajin wata matsananciyar tsanar maryam nakara mamaye zuciyarta. Nidai banmasan tanayiba, daki muka shige. Muna alwala ina bawa aliya labarin abunda yafaru apart din yaya, saboda addabamun din datayi da tambaya, tun shigowarmu dakin......
Tunda yazauna bayan fitarsu ko motsawa beyiba, ko abincinma be kallaba, duk da yunwar dake nukurkusarsa. kiran sallar isha'inne shima ya mikar dashi, dakinshi ya shiga yadauro alwala yafito yanufi masallacin dake manne da gidannasu. Ana idar da sallah, yataso ko gaisawar dayasabayi da mutane yau betsayaba, saboda ciwon dakansa kemasa,burinsa kawai yaje ya kwanta ya huta. A palonsa na sama yatarar da mommy, hakimce akan kujera, cikin mamaki yake kallonta. Fadada fara'a mommy tayi akan fuskarta, cikin tausasa lafazi,da nuna tsantsar kulawa tace, "welcome my son" tamkar ba itace, tagama zuba masifa dazuba. sakin fuskarsa yayi daga tsuken datake, yazauna agefen mommy yana sauke numfashi tare da daga mata kai alamar amsawa. Shafa fuskarsa mommy tayi cikin tsantsar kulawa tace, "meyafarune son naganka cikin damuwa" kallon mommy yayi bece mata komaiba, yasan suhailat tasanar da ita komai,shiyasama tazo part dinnasa. "Nothing mom" yafada cikin sanyin murya, yana lumshe idonsa. Matsawa jikinsa mommy tayi, ta kwanto dashi jikinta,cikin so da kauna. Ahankali takai hannunta tana shafa bayansa,tasan halinsa idan ransa yabaci befiyason doguwar maganaba. Ajiyar zuciya yahau saukewa,yayi luf ajikin mommy,yanajin kaunar mahaifiyarsa harcikin ransa. Yanason mommy fiye da kowa a duniyarnan. "Son meyasa ka mari daughter akan waccan yarinyar kuma agabanta.?" Mommy tajeho masa wannan tambayar. Taune lips dinsa nakasa yayi, sannan yace, "mom, suhailat bataji, yarinyarnan babu abunda tamata amma tahau zaginta,da marinta. tare da siffantata da dabbobi, dan'adam da Allah yayishi da daraja,da kima, amma tadinga kamantata da dabbobi,shine abunda yafi komai konamun rai mom, banmasan sanda natashi na maretanba." cikin bacin rai yayi maganar. Shafa kwantacciyar sumar kansa mommy tahauyi tace, "kasan suhailat fa yarinyace, sekana hakuri da ita, kuma zanjamata kunne akan takiyayi hakan anan gaba, naga ranka ya baci, kasan banason abunda zebata maka rai kokadan, ayi mana hakuri nasan munyi lefi." Mommy ta karasa zancen tana sakin murmushi. Kaikawai yagyada mata, ya lumshe idonsa tare da gyara kwanciyarsa ajikin mommy. Kallon dinning mommy tayi, taga babu alamun antaba abincin dake kan dinning din. cikin dan kaduwa tace, "yasalam, my son, haryanzu bakaci abincinnanba, haba son dan Allah kadena zama da yunwarnan seta maka illa,pls son kadinga kokarin cin abinci akan lokaci" kama hannayenta yayi cikin tsananin kaunarta, yana murmushi yace, "insha Allah mom" murmushi itama mom tamasa, tare masa kiss agoshinsa. Rabashi tayi daga jikinta, ta mike. Dakanta ta shiga kitchen dinsa ta dakko plate da serving spoon, ta zuba masa abincin ta kawo masa hargabansa takuma bashi abaki. Mommy na matukar sonsa fiye da tunanin me tunani, Wanda shikansa yana mamakin hakan, musamman dayakasance bashi kadai tahaifaba, bata boye sonsa ko'agaban kowaye. shikadaine yake taba mata suhailat dinta yazauna lafiya, amma da wanine ya mari suhailat yau, dabataza kyaleshiba koda kuwa acikin sauran yayantane. Seda tatabbatar dayaci yakoshi sannan tabarsa, ta masa sallama tatafi. Dakinsa yashige ya kwanta akan makeken royal bed dinsa, haryanzu yanajin zafi da haushin abunda suhailat tayi, amma taci darajar mom dinsa, daseya kara hukuntata. Yanajin karar shigowar sakonni, amma yayi banza da wayar yasan baze wuce suhailat dinbace.......