Kenza eBookz

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 10

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 10

Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 10: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 10. Part din mommy yanufa bayan an idar da sallah,shida…

3,065 words

Part din mommy yanufa bayan an idar da sallah,shida sauran yan'uwansa dasuka hadu a masallaci. Babu kowa a falon duk suna daki, aunty ce tafito daga dakin dake jikin na mommy,Wanda ana take sauka idan tazo gidan. Da mamaki mustapha yake kallonta,danbesan tazoba. Shikuma su sadiq sunsan tazo harsun gaisama. Fadada fara'a aunty tayi tace, "sannunka boy seyanzu kadawo kenan agogo sarkin aiki,tunda nazo nake cikiyarka aunty atika tacemun katafi office, kai weekend dinma bazaka hutaba" shagawabe fuska yayi yace, "wai auntynah haryanzu boy dinnan baze fita daga bakinkiba, nifa bansan sunan" karasawa aunty tayi kusa dashi ta kamo hannunsa tana fadin, "sorry my son,nariga nasabane,zomuje kazauna kahuta dannasan ka kwaso gajiya" su haidar kuwa dasuke kallonsu se guntse dariya sukeyi, indai aunty tazo gidan seta tsokanesa tace masa boy, saboda dayana yaro haka akecemasa,daya girmane yayi cancel din sunan. Zama sukayi akan kujera,yana gaisheta. Aunty macece,me kirki da saukin hali,gashi tana jansu ajiki,musammanma mustapha, haka kawai takejin wani Abu agame dashi me kamar tausayi,Wanda batasan dalilin hakanba. Mommy ce tadawo falon itama. Daga baya kuma suhailat tashigo, se satar kallon mustapha takeyi, shikuma daga gaisuwar daya amsa mata,bekara mata maganaba, cigaba da hirarsu sukayi da aunty.

Adakina mukayi sallah,da muka idarma hira Aliya tacigaba damun, araina mamakinta kawai nakeyi yanda bata gajiya da magana,gaskiya Allah yahore mata baiwar surutu. Aunty ce dakanta tashigo dakin da sallama, amsa mata mukayi ta Dora da fadin, "sannu Aliya,kinzo kincikata da surutu, narasa irinki aliya kogajiya da magana bakyayi" murmushi nayi nace, "babu komai aunty hirafa mukeyi" "kai aunty, nifa bani da surutu,kawaidai banaso inga nazauna shirune" "naji nidai,kitaso kigaisa da yan'uwanki kowa ya hallara afalo." Zunbur aliya ta mike tayi bakin kofa, nikuma ina zaune ko motsawa banyiba. Juyowa aliya tayi tana kallona, "kitaso muje mana tare maryam" "A'a aliya kije kawai zanfito anjima" takuramun aliya tayi,dole na mike muka fita tare. dashi nafarayin tozali,hakan yahaddasamun wata faduwar gaba,bantaba ganinshi yana murmushi ba seyau naga yanayiwa aunty,dimples dinsa duka kumatu biyu sun lotsa abun sha'awa,akodayaushe idan na kallesa karamun kyau yakeyi,yanzumma hakance ta kasance. "Oyoyo yaya.....muryar aliya ta katsemun tunani, sekuma naji itama tayi shiru,kallonta nayi naga ta wani nutsu harta da tafiyartama ta canza. Dariya naga su yaya sadiq sunsaka mata,ashesu sunsan dawar garin, ganin mustapha ne yasata nutsuwa ba jiri,ta wani koma salihar gaske,dantasan halinsa farinsani. Shikuwa ya wani tsare gida, yana latsa waya. Akasa muka zauna,kusa da aunty muka gaishesu.

Daga gaisuwar bankara cewa komaiba,na sunkuyar da kaina kasa, zuciyata na luguden bugu kamar kodayaushe idan mukayi close dashi,ga daddadan mayen kamshinsa gaba daya ya mamaye falon,se lumshe ido nakeyi ina sauke ajiyar zuciya akai_akai saboda dadin kamshinnasa .itama Aliya duk shegen surutunta shiru tayi,su yaya sadiq ne suketa hirarsu shidasu aunty,shima ogan shiru yayi yacigaba da latsa waya. Suhailat se kallonsa takeyi tamkar zata hadiyesa. Kiran sallar isha'ine ya tarwatsa taron,dama a takure nake da zaman,nina fara mikewa nashige daki,ina kallon suhailat tana bina da wani mugun kallo. Aliyama biyo bayana tayi tana fadin, "nida dodo" dariya na tsuntsire mata saboda yanda tayi maganar tamkar taga dodon gaske. "Allah kuwa maryam,bakiga nayi tsitba aitun watarana a gidannan Inata zuba,shikuma yana zaune kawai yana kallona, sedaga bayane yakirani gabansa ya murdemun baki,harkuka nayi saboda azaba,tundaga ranar idan yana guri kodogon numfashi banasonyi" murmushi nayi ina nufar toilet nace, "maganinki yayi ai" "hmmm,danshirunnan danayi bakina haryafaramun tsami yasin" "kai aliya banda sharri" "bawani sharri gaskiyace, ai gaskiya aunty suhailat zatayi kokari, danzama da yaya musty se hakuri, kodayake shine maganinta ai,tunda itama bata da kirki" alwalata nafara ina fadin,"kekadai dai".

Koda muka idar da sallah bamukoma faloba, aliya tamakure akarshen gado sekashe murya take tana waya da saurinta,kamar ba itace me karadinnanba. Nidai kayana nahau kwasowa daga toilet na dinke nasasu a cikin cover. Ganin har 9 tayi nafita domin musu serving abinci,dannaga wayar aliya bata kare bace. Aikuwa Ina fita kuku,nata jera abincin akan dinning,sukuma dukansu kamar dazu suna zaune a falon.

Yana gamawa mommy ta umarci kowa dayataso suci abincin. Dukansu suka hallara amma banda oga dayaketa aikin latsa waya, aunty ce ta dubeshi tace, "Muhammad yanaga baka tasoba" satar kallonsa nayi,tasowa yayi kawai becemata komaiba. Ajiyar zuciya nasauke,nafara serving dinsu,dauriya kawai nakeyi amma nikadai nasan halin da zuciyata take ciki, gawani mahaukacin bugu da takemun. Aliyace tafito daga daki, tayani serving din tayi mukarasa,aunty da yaya sadiq ne kawai suke mana sannu. Juyawa nayi zantafi,aliya dake kokarin zama tace,"A'a maryam ina zakije kuma?" "daki zankoma" "wanne irin daki kuma maryam,kizo kici abinci" cewar aunty data karbe zancen. Babu Wanda yayi ko tari acikinsu,harnadawo na zauna,se suhailat daketa kallonmu tana tabe baki nida aliya. zuba abincinnayi,jujjayashi kawai nakeyi amma nakasa ci, saboda bansababa duk senaji natakura,gashi duk dagowar dazanyi idon yaya sadiq nakaina. Aunty ce tamun magana akan naci abincin mana,dole nadaure nafara tura abincin tamkar inacin magani. Mustapha ne yafara tashi aunty namasa tsiyar haryanzu yananandai da rashin son cin abincinsa. Murmushi kawai yamata yafice,daga falon gabadaya. Daya bayan daya suka dinga tashi,nikuma atare muka tashi nida aliya. Dakina nakoma toilet nashiga nayi fitsari nadawo na kwanta,dan yanayin danakejin kaina baze misaltuba,inajin aliya ta shigo tanamun magana,wai ita anan zata kwana,shiru na mata dan ina fama da zuciyatane, har gwanin iya sata yasaceni bansan sanda ta kwantaba........

Washegari gari lahadi,yau ma basu tashi da wuriba,nima danayi sallah komawa bacci nayi,se wajen 10 natashi,aikina nayi kamar kullum danasaba tare da taimakon aliya. Yanayin dana kwana dashi yabarni,sedaifa duk abunda nakeyi tunanin mustapha ne,manne acikin raina. Yauma acikinsu nayi Karin kumallo,bisa umarnin aunty kamar jiya,amma yau naga ogan bezoba. Abunda yake bani mamaki,duk abunda aunty tace,mommy bata musu kota hana,balle sauran yayangidan. Suhailat kam na lura tafi kowa jin haushin hakan,danbanda harara babu abunda take aikamun dashi harmuka tashi. Namaci sa'a banmaci zagiba,itama naga kwana 2 duk tayi wani sukuku da ita. Munagamawa na tattara kayan,nakai kitchen mukayi wanke_wanke sannan mukayi wanka. Bayan munshirya aliya tatakuramun wai dole senazo munje garden din gidan,hijabina na zunbula muka fito. Mommy ce zaune afalo tayi bakuwa,bakuwar irin manyan matannanne, masu ji da gayu kamar mommy, taci kwalliya da gwalagwalai se tashin kamshi takeyi. tunda muka fito takafeni da ido,gaisuwar damuke matama seda mommy ta tabota sannan ta amsa,mudai ficewarmu mukayi. Maida kallonta bakuwar tayi akan mommy tana zauke ajiyar zuciya bayan su maryam su fita, gyara zama tayi tace. "Kekuwa atika ina kika samo wannan dankwaleliyar yarinya haka,gaskiya yarinyarnan tamun wlh, nidazakimun wani taimakoma dakin bani ita natafi da ita,tamun koda 2 weeks ne namaida maitata........✍️

````kuyi hakuri da dogon jira, amma yanzu insha Allah zakudinga jina yanda ya kamata````

Meson complete Whatsapp 08166674823

*ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_

*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*

*Bismillahirrahmanirrahim*

1️⃣6️⃣

...........Bata fuska mommy tayi tace,"haba baraka wannan yar yarinyar nawa take, kedai wlh maitarki tacika yawa." Murmushi bakuwar da mommy takira da baraka tayi tace, "hmmm,ninasan menagani atika,irin wadannan yaran,sunfi dadin harka" tabe baki mommy tayi ta kawar da kanta gefe batace komaiba. Ganin haka yasa baraka sako wata hirar daban, amma ta kudirce aranta kotayayane seta lashi zumar maryama,dan yarinyar ta mata, daga ganin farko data mata....

Garden din gidan da tafiya, danni gurin dayakema bantaba zuwaba,banmasan dashi agidanma. Gurin ya matukar yimun kyau, da burgeni. Ga wata ni'imar iska dake kadawa ahankali,me kwantar da zuciya. Kujerun roba, aliya ta kwaso mana, domin mu zauna. Amma kafin na zaune seda nadan zagaya naga gurin, gaskiya masu kudi sun huta,iya kanshi gurinma ya isa yadaukewa mutum kewa. Zama nayi ina sauke ajiyar zuciya. "Kyan zaman gurinnan ace mutum yana tare da masoyinsa, susha soyayyarsu seyafi dadi." Cewar aliya. Murmushi namata,kawai na lumshe idona, narasa meyasa fuskar mustapha takemun gizo a acikin idona,hotonta kuma yayi tsaye kyam acikin zuciyata. Cikin dariyar keta aliya tace, "um'um,kaga su maryam manya kintafi tunanin naki masoyinkenan" numfashi na sauke tare da bude idona,ahankali ina hararar aliya nace, "banson iskanci,ni ina naga wani masoyi" dariya takara kwashewa da ita tace, "fadanma ko kyau bemikiba, gwaramadai hararar" banza na mata. Ita kuma tashiga bani labarin saurayinta, korar duk wani tunani nayi daga zuciyata mukasha hirarmu da aliya. Kiran sallar azharne yatadamu muka koma cikin gida...

Suhailat ce, zaune a falon sama na part din mustapha, shima yana zaune, se latse_latsen waya yakeyi. yauda kanta ta kaimasa breakfast dinsa. tazone ta kara bashi hakuri, dan har yanzu be sakko mataba.yanuna mata dai ya hakura,amma yaki sakar mata fuska. Se satar kallonsa takeyi tana hadiyar yawu, sotake tajita kwance akan faffadan kirjinnasa tana shafa lallausar fatarsa amma ba dama, danbataga fuskar hakanba. Kwana biyunnan duk atakure take, sotakema ta fita anjima gurin kamal amma kuma tana tsoron wani sabon fushinnasa. "Pls my love am sorry again" ta fadi haka cikin marairaicewa, tamkar zata fashe da kuka. kallonta yayi, sekuma ta bashi tausayi. Sakin fuskarsa yayi daga dauren datake. Amma bece mata komaiba. Ajiyar zuciya suhailat ta sauke, ganin ya hakura duk da bece mata komaiba amma tasan ya hakura. Hira tashiga yimasa, irinta masoya tare da kalailameshi da kalaman soyayya,hardai tasamu suka shirya suka koma kamar da.....

Aunty kuwa bayan sungama breakfast part din masu aiki ta wuce gurin talatu,domin itace abokiyar hirarta idan tazo gidan, amma basa wata doguwar hira da mommy. Bayan sungaisa aunty ta dubi talatu tace, "talatu,naga wata sabuwar yarinya a gidannan ita kuma daga ina, aka samota,naga batayi kala da sauran masu aikin gidannanba?" gyara zama talatu tayi,tabawa aunty labarin maryam atakaice. Cike da tausayawa aunty tace, "kai wasu mutanen son zuciyarsu yayi yawa, bandahaka aikamata yayi ace kamar wannan yarinyar tana makaranta tana karatu yanzu,amma shine aka turota aikatau,gata yarinya me hankali da nutsuwa, itama aunty atika narasa meyasa take kaunar yara kananu a aikatau, dan wani abu yataba faruwa dakai can abaya, shikenan kuma yanzuma seyakara faruwa, gata da yara samari bafata dai akeba amma bata tunanin wani Abu ya faru, musamman yanzu da zamani ya lalace ga kuma sharrin shedan" "Allah dai ya kyauta" kawai baba talatu tace, Aranta kuma cewa tayi, "danma bakisan meyake faruwa agidan bane" wata hirar suka kama daban...

Lokacin damuka koma part din duka yaran gidan,suna zaune a falo,bakuwar mommynma ta tatafi,yaya musty ne kawai babu a falon se suhailat da aunty. Aliyama zama tayi sukasha hira, dan jiya bata samu damar hira dasuba,nidai daki na wuce nayi sallah ta, sedaga baya aliya tashigo itama tayi. Haka muka karasa wunin yau cikin farin ciki nida aliya. nidai zuwansu aliya gidan yamun dadi,aunty ma data dawo part dinmu, ta kirani tamun tambayoyi akan rayuwata, tare da mun nasiha. Godiya na mata sosai,seta tunamun da ummansu salima. Dan itama kullum cikin yimun nasiha takeyi. Yau kam kwata_kwata banga ogaba, kuma kosaudaya mommy bata aikeni part dinsaba,senaji dadin hakan saboda maganar rigarsa tananan daram araina. Amma kuma a wani bangaren na zuciyata,senaji ina kwadayin ganinsa.😳🤤

Washegari tun asuba dana tashi,bankoma bacciba nayi ayyukana,saboda yaya sadiq yacemun kafin yawuce office zamuje school, kamar yadda yamun alkawarin. murna da farincikin danake ciki yau baze misaltuba, waiyau nice zankoma makaranta da sunan cigaba da karatu, gaskiya yaya sadiq yataimakeni, Allah ya biyasa kawai. Kafin 8 munje makarantar office din principal mukaje, akamun tambayoyi akan karatuna. Alhamdulillah na amsa yanda yakamata, Matsalata kawai rashin iya turanci,hakan yasa yaya sadiq yace zedaukar mini me lesson yadingamun da yamma. Kudin duk da aka bukata yaya sadiq, yabiya. Atake aka bani, uniform da littafan karatu. Ss2, aka kaini, amma bazan fara zuwa yauba, se gobe idan Allah yakaimu, nace zanfara zuwa.

Da murnata nashigo daki, bayan yaya sadiq ya saukeni agida ya wuce aiki, aikuwa yau yasha addu'a da godiya me tarin yawa agurina. Rukunkume, aliya nayi saboda murna. Itama tayani tayi mukayi tayin murnar tare. Seda muka gama murna sannan na dubeta nace, "Aliya gaskiya yau ina cikin farin ciki sosai, gashi makarantar ta burgeni da'alama kuma ana karatu sosai" "ai gaskiya makaranta da dadi maryam, zaman gidan haka badadi, seki dage kiyi karatu karkibawa yaya sadiq kunya" murmushi nayi cikin jindadi nace, "insha Allah aliya zanyi karatu sosai" "haka akeso Allah yataimaka." "Ameen" auntyma tatayani murna sosai, takuma mun addu'ar nasara. Hakama baaba talatu danaje nasanar mata. Mommy kam, danaje nanunamata karba tayi itama tasamun albarka, dana mata maganar aikin gidan, seta kafin natafi nayi abunda zan iya kawai, idannadawo na karasa, godiya na mata, nakoma naciga da shirye_shiryen fara zuwa school gobe........

*______________* *MUSTAPHA* *______________*

Tunda yadawo daga sallar asuba shima be koma bacciba,abubuwansa ya karasa ya shirya cikin kananun kaya,wadanda suka matukar amsarsa. Yayi kyau sosai,kamalarsa da cikar zatinsa sunkara fitowa. Karfe 7/15 kamar kodayaushe yagama shirinsa tsaf, ko breakfast beyiba, yadau briefcase dinsa, seda yabiya part din mommy yaymata sallama ita da aunty, sanna yafito. Direbensa yana tsaye abakin mota yana jiransa, yana hangoshi ya taho cikin girmamawa yana gaisheshi tare da amsar briefcase din hannunsa, ya bude masa mota yashiga,shima yazagaya ya shige, yatada motar suka fice, bayan ya gaisa damasu gadin gidan.

Yau kam ma'akaitar duk ma'aikatan sunzo da wuri,sabanin sati dayan dabayanan kowa kashin kansa yakeci. Cikin takunsa nakasaita ya fito daga motar,direbansa na biye dashi abaya rike da briefcase dinsa. Ma'aikatan dake kaikawo,aharabar ma'aikatar se kwasar gaisuwa sukeyi. Mikewa sakatariyarsa tayi cikin girmamawa tana kwasar gaisuwa,tare da amsar briefcase dinsa daga hannu direba takai masa cikin office dinsa. Bayan yazauna akan kujerane yatura sakatariyarsa ta kira masa P.A. tare suka dawo office din. P.A sewata karairaya takeyi da yauki, amma kobitakanta beyiba,bayan sallamar daya amsa mata. hankalinsa yana kan duba wani files dayakeyi. Tari P.A takamayi ba kakkautawa, dagowa yayi yana kallonta, tare da yimata sannu. Kanta kawai ta iya daga masa, har tarin ya lafa, sekuma yakara turniketa ba kakkautawa. Hankali atashe mustapha ya mike zaune, atunaninsa asmartace tatashi, nuni take masa da hannu ga fridge din dake office din, alamun yabata ruwa. Dasauri cikin tausayawa ya nufi fridge din, ya dakko mata ruwan yabude yakawo mata ya kafa mata abaki. Seda tasha kusan Rabin, robar sannan ta janye bakinta tana sauke ajiyar zuciya, tare da maida numfashi. Yunkurin tashi tayi, sekuma tayi luuu zata fadi kasa, dasauri mustapha yatarota jikinsa, cikin azama,yana jera mata sannu. wal_wal haske ya bayyana a office din, nadaukar hoto......✍️ Meson complete Whatsapp 08166674823

ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_

*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*

*Bismillahirrahmanirrahim*

1️⃣7️⃣

...........Hankalin mustapha gaba daya yana kan P.A, hakan yasa be lura da abunda ke faruwaba. bubbuga bayanta yahauyi ahankali,saboda tarin daya kara sarketa harta samu ta dawo nutsuwarta,tarin ya tsaya. Taimaka mata yayi takoma kan kujera, se lumshe ido takeyi, tanajin dama su dawwama tana kwance a kirjinsa, tana shakar daddadan kamshinsa. wani sonsa da kaunarsane yakara ninkuwa aranta, harzuciyarta ta fara kokwanto akan anya kuwa ta kyauta masa, mutumin daya tsamota daga duhun talauci, daga rana zuwa inuwa, amma yau da ita aka haka baki domin cutar dashi, anya kuwa tayi wa kanta adalci....daddadar muryarsa me cike da kasaita takatse mata tunaninta. "Dama kinsan bakida lafiya kika fito aiki,?" Ya fadi haka yana kallonta. Cikin muryarta data dan dashe tace, "lafiya kalau natashi, yanzune kawai naji tarin" "ohk, bari nakira doctor yadubaki" "no, sir, base kakira doctor ba, yamatsayamun tarin" ta fadi haka cikin sauri. Kallonta yayi nawasu sakanni, yadan tabe baki yace, "Alright, Allah yakara sauki" "Ameen, thank u so much sir" be'amsa mataba sewata takarda daya mika mata, karba tayi taduba, sannan ta mike ta masa sallama ta fice, tana tafe tana waigensa.........

Kafin yamma nagama shirina tsaf na zuwan school gobe, nagoge uniform dina, najera books dina a school bag dita. Jinake kamar na zuko gobe tadawo yau saboda zumudi, aliya se dariya takemun tana tsokanata. Tunda nazo gidannan babu abunda yasani farin ciki kamar wannan, yanzu saurana islamiyya, itama inason komawa. Allah sarki, yar'uwata salima,nasan itama idan taji wannan labarin zatayi farin ciki sosai, umma ma haka. Kewarsu naji tacikamun zuciya, masoyan kwarai kenan. Kaina dake tsefe, aliya tasani wankewa, aunty ta rangadamin kitso, dama nayi kwanaki dakan atsefe. Godiya nayiwa aunty sosai bayan tagamamun. "Wow mairo, kinga yanda kitsonnan yayi kyau, gaskiya kina da kyan kitso gaki da gashi, ga tsawo da cika,gashi baki sidik, kedai kinji dadinki komai naki mekyaune." Cewar aliya tana shafa kitson. Murmushi nayi kawai mekama dana yake, kamar yadda aliya take yabona haka kullum salima ma takemun. Tabbas nikaina nasan Allah yayimun baiwa ta kyawu, amma idannatuna bani da kyawun nasaba, senaji wani kunci da daci yaziyarci zuciyata. kyau ko dukiya bashine cikar kamalar mutumba, *ASALI* shine abun tunkaho da alfahari ga kowanne dan Adam, amma ni bansan nawa asalinba, banmasan ina zannemesuba. Kwalla ce ta jikamun ido, kasa nayi da kaina ina kokarin mayar da ita dan karsu aunty sugani, Amma hakan beyiyuba seda wani hawaye ne dumi ya ziraromun. arikice aliya ta hau tambayata "lafiya maryam, meyafaru meya saki kuka, ko baki da lafiya ne?" shiru namata ina share hawayen fuskata, nikadai nasan halin danake shiga idannatuna wacece ni. Cike da tausayawa aunty take kallon maryam, daga ganin yarinyar akwai abunda ke damunta acikin zuciyarta. Ganin aliya ta matsamata da tambaya, ita kuma tayi shiru se aunty ta dubi aliya tace, "Aliya kowanne dan'adam yanada sirri nasa nakansa arayuwa, sanin abunda kedamunta ayanzu bashine abun bukataba, addu'a kawai zaki tayata da ita, akan Allah yayaye mata koma menene" gyadawa aunty kai, aliya tayi cikin gamsuwa. dafa kafadar maryam aunty tayi tace, "kiyi hakuri maryam da rayuwa, a duk yadda tazo miki, kikuma godewa Allah. kowadakika ganshi datasa irin kaddarar, kuma komai me wuce wane arayuwa, na dadine kona wuya." Nasiha sosai, aunty tayiwa maryam me kwantar da hankali dasanya nutsuwa. sosai naji dadin tunasarwar da aunty tamun, har radadin da zuciyata kemun naji ya ragu,sakar jikina nayi muka koma kamar da, muka cigaba da nishadinmu nida aliya........

*_________________* *HAJ.GWAGGO* *_________________*

Tun tafiyar maryam, haryau datafi sati ba'asamomata me aikinba, ansamo mata wata yarinya dai, tana zuwa taji lissafin ayyukan gwaggo tace bazata iya jaki work ba, aiki babu hutu. gwaggo taita mata masifa tace karta iya din, aikin da'ake nemansa ido rufe danma ita tasamu za'a dauketa, taje dubunta zasuzo. Kamar kodayaushe yauma se rana tatashi daga asararren barcinta, bakinta kawai ta kuskuro ta dawo ta hada tea tahau sha, tana Karin kumallon tana mitar maryam taki zuwa, balle ta kawo mata abun duniya, dan bakin hali irinnata. Sallama taji ana kwadawa abakin kofar gidanta, banza tayi tacigaba da cin abincin ta, cigaba akayi da kwada sallamar, hakura tayi ta mike ta zari mayafinta,ta nufi kofar gidan tana fadin, "jaraba da masifar duniya, ko ubanwaye zezo mata gida wannan farar safiyar ya takura mata oho, itadai tasan ba bashin uban wanda take ci.....

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull