Kenza eBookz

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 9

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 9

Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 9: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 9. Ajiyar zuciya nasauke ganin yanzu mun rabu lafiya, part din…

3,371 words

Ajiyar zuciya nasauke ganin yanzu mun rabu lafiya, part din da baaba talatu ta kwatantamun naje, karamin part ne, yana dauke da babban falo da se dakuna. Gasu salame nan zaune da sauran 'yan aiki, kowa yana sabgar gabansa gaishesu nayi na tambayesu baaba talatu,wani daki suka nunamun godiya na musu nashiga da sallama. Baaba talatu zaune take akan dadduma tana lazimi, zama nayi agefen katifar dake dakin ina jiran ta karasa. "Maryama, ashedai zakizo Aida nayi tunanin bazakizoba" baaba talatu tafada bayan kammala laziminta. "tun dazu nakeson zuwa baaba sekuma nayi wani aiki danagama kuma bacci yadaukeni" "ayya sannunki, aikina da kokari ya aikin,kinadai jin dadinsa" "eh baaba, ai aikinma babu yawa nariga nasaba fiye da haka agida." Gyara zama nayi sosai nace "baaba talatu, dan Allah kikaramun Karin haske akan abunda kikafadamun wlh kullum cikin zullumi nake, da tsoro acikin gidannan" "maryama ki kwantar da hankalinki insha Allah, babu abunda ze faru dake, kedai kawai kidage da addu'a kuma kiyi takatsantsan da kowa na gidannan." Numfashi nasauke nace, "to baaba talatu kincemun lokacin da'akeyin wannan mummunan abun duka yaran gidan basanan towa kike zargi kenan?" "Bawai ina nufin dukansu basananbane kawata_kwata, a'a,lokacin daza'ayi idan wannan yananan to wannan bayanan, zakiga wani lokacin da'akayi mutum ukun sunanan kokuma hudu kokuma biyu,inafatan kingane." Jinjina kai nayi nace, "eh nagane baaba amma ni abunda yafi tsoratar dani dakikace duk wadda akayiwa fyaden mutuwa takeyi" "Eh to gaskiya kuskuren danayi kenan dana fada miki haka, saboda bansan na sauranba,ammadai tabbas na jikata hakance ta kasance." "To shi megidan baaba meyasa bazedau matakiba, kodan gudan bacin sunansa a idon jama'a, musamman dayakasance ana fadar alkhairinsa sosai agarinnan" "bansaniba gaskiya maryam, domin tabbas alh mutumin kirkine" ajiyar zuciya nasauke, nidai har ga Allah zaman gidannan a tsorace nakeyinsa. "Amma baaba da lefin hajiyama, kuma ni tana aikena part din danta ko tunanin wani Abu yafaru batayi. Murmusawa tayi tace, " Aishi wannan gaskiya bana zarginsa saboda kafinma kiganshi a part din hajiya ana jimawa, kuma wannan abunda akeyi adakin masu aikin akeyi harnan akebinsu, shikuwa daga gurin aiki se part dinsa,befiya zuwa nanba gaskiya,amma ai bata aikenkipart din sauran yarannata?" "Ehh,baaba bata aikena." "Yawwa" Munsha hira da baaba talatu sosai, takuma kwantarmun da hankali, Allah yanaji yana gani, kuma baya barci shize kareni,babu wayo ko dabarata. Seda nayi sallar magriba nabar part dinnasu, har kofar part din hajiya ta rakoni. Tambayarta nayi akan zan iya tambayar hajiya zuwa ganin gida, tatabbatarmun dazan iya kuma hajiya zata barni.

Babu kowa a falo yanzu, dakina nashige, rigar yaya dana wanke nadakko harta bushe, dama bata dawani nauyi. Tunda nazo gidan naga iron sabo adakina, bantaba guga dashiba seyau nace bara nagoge masa rigar. Jonawa nayi nafara gogewa, ina gugar ina tunanin maganarmu da baaba talatu, ban'ankaraba tsautsayi ya afkamun iron din yakwashe wani guri agaban rigar kuma dayawa ya kwashe. Wani gumine yafara tsatstsafomun duk da a.c da fankar dake dakin, "nashiga uku ni maryam, meyakaini goge rigarnan, tsautsayi ko karambani yanzu gashi na kona masa, nasan idan yaji lefin dana aikata masa sedai wata baniba" wata hautsinawa cikina yayi, matsanancin tsorone ya lullubeni. Ninke rigar nayi cikin rashin sanin mafita, addu'a nakeyi araina Allah yasaukakamun duk hukuncin dazemun. Adaren yau kam abincima kadan natsakura naci, saboda zullumi. Inayin serving dinsu na kwanta dama nayi sallah ta, addu'a nashigayi araina ga tsoron zaman gidannan ga tsoron gamuwata da oga kwata_kwata,baccinakam adaren ragaggene, dandaima baccin barawone,bansan sanda yasaceniba.

washegari, inayin sallar asuba nafara gyaran dakina,yau sonake nagama aikina da wuri domin inason zuwa unguwarmu. Harna gyara falo na koma dakina na kwanta, babu Wanda yafito,har kuku kuwa. Tunawa nayi yau Saturday, may be weekend basa tashi da wuri. Se wurin karfe goma da wasu mintuna suka fito,nima fitowa nayi danyin aikina. Serving dinsu nayi ina gaishesu,wasu suna amsawa wasu kuwa ko kallo ban ishesuba, ninama Riga nasaba da hakan,kamar kullum yauma duk sun hallara amma babu oga. Harna juya zantafi mommy ta tsaidani da fadin na shiga kitchen madauki breakfast dinsa nakai masa. Seda zuciyata ta buga sosai, saboda tsoro. Amsa mata nayi nakoma dakina nadakko rigartasa na boyota acikin hijabi. Basket din kayan Karin kumallonnasa na dauka, zuciyata na dukan tara_tara, ina tafe Inayin addu'a. Da sallama nashiga falon kasa, babu kowa se mayen kamshin turarensa,sama na haura, yana zaune akan kujera 2siter yanata fama aiki a computer. Dukda bugun da zuciyata takemun haka nadaure nashiga da sallama, labbensane kawai ya motsa alamar ya amsa. Tsugunnawa nayi cikin girmamawa nace, "ina kwana" batare daya dagoba yadagamun hannunsa, karasa wa nayi najere kayan akan dinning, gabansa na dawo na durkusa akaro na biyu, cikin matukar tsoro na mika masa rigarsa. Dagowa yayi yakalleni na wasu y'an sakanni sannan yadauke kansa karbar rigar yayi ya budata. Kallona yakeyi yana kallon rigar, nandanan jikina yafara rawa, saboda babu wasa kokadan a fuskarsa. "Dan Allah kayi hakuri, wlh bada sanina na konaba,tsautsayine" nafadi haka cikin rawar murya inashirin fashewa da kuka. "Meyasa kika konamun Riga?" Yajehomun wannan tambayar cikin tsawa,fuskarsa a hade. Cikin in'ina nace, "ba....ba.ko..mai." Daradaran idanunsa yazubamun, kasa nayi dakaina hawaye yafara zuba a idona,saboda tsoro. Cillomun rigar yayi becemun komaiba,yamaida hankalinsa akan abunda yakeyi. Ahankali nadago kaina na kura masa ido, duk yanda naso dauke idona daga kallonsa amma nakasa, yana sanyene cikin farar jallabiya. Gaskiya ada gaba daya kallon tsoro nake masa, seyanzu nakara ganin tsantsar kyawunsa, ada inaganin kamarsa da mommy, amma yaunagane yafita kyau nesa bakusaba, babuma hadi, kuma ba mommy kadaiba dukama mutanen gidan duk ya fisu kyau,farar fatarsuce kawai daya. Mintuna goma, suka shude, amma beko kara kallonaba, nikuma aikin kallonsa kawai nakeyi ina tasbihi ga ubangijin dayayishi,wani Abu naji yana shigata akansa, Wanda bansan yazan fasalta mukuba, domin bantaba Jinhakan akan waniba. Kafata ta sagemun saboda tsugunnon danayi, gyarata nayi ina sauke doguwar ajiyar zuciya. Kallona yayi ya nunamun hanyar kofa, tare da fadin, "kisan yanda zakiyi kikawomun wata rigar,bakonanniyaba, tunda ke bakyajin magana,kokuma na babballaki agidannan" waro idona nayi waje cikin tsorata nace, "dan All....." "Go out!" Yakatseni cikin tsawa. mikewa nayi ina kara sauke nannauyar ajiyar zuciya, ajiye rigartasa nayi ina satar kallonsa, wata uwar harara ya wurgamun dasauri na dauki rigar nafara tafiya, Ina tafe ina waiwayensa harna fice. Tsaki yaja bayan ta fice, yalura yarinyar akwai yarinta sosai atattare da ita, ga kuma abunda yatsana wato saurin kuka,ga kuma rashin ji. Yarasa meyasa mommy takeson irin wadannan yaran a matsayin y'an aiki,wadanda babu abunda suka iya banda shirme, dasawa mutum ciwon kai. tabe bakinsa yayi yacigaba da aikinsa..... (Kaikadai dai🤤)

Ina tafe ina gulmarsa araina, hoton fuskarsa yaki bacememun daga idona,gadai tsoronsa daya cikamun zuciya,amma jinakeyi dama bekoreniba inzauna inta kallon fuskarsa me kyau,niyau fadannasama burgeni yayi. Seda nafara ajiye rigar adakina, sannan nafara gyaran dakunan su mommy. Abun mamaki mommy bata tambayeni mena tsaya yiba harna dade. Se suhailat cema naji tana magana tana hararata, nibanmaji metaceba, hankalina yana wani gurin daban. Bayan nagamane na tambayeni mommy, inason zuwa gida, tace nabari senakara kwanaki yanzu yayi kusa, dududu satina dayafa. Haka na hakura na koma dakina, bayan na dibi abincin Karin kumallona, inagama ci na kwanta, Inata tunanin yanda zan iya biyansa rigarsa, niba kudiba idanma inada kudin inazansamu rigar insai masa, Allah ka sassauta zuciyar bawannanka ya hakura, dan tun jiya danakaimasa lemo na fuskanci ransa abace yake. bansan sanda bacci yayi awongaba daniba Inata tunane_tunanena..........

Suhailat ce tashiga falon mustapha da sallama, duk da sallama ba dabi'arta bace, amma shi tana masa dantasan idan batayiba casata zeyi. Bedago ya kalletaba ya'amsa mata akan labbansa. Zama tayi agefensa tana fadin, "yayana ina kwana?" Dagowa yayi yajefeta da wani kallo be amsa mataba,yamaida kansa, yacigaba aikinsa. Marairaicewa suhailat tayi ta fara magana cikin shagwaba. "Haba yaya ina maka magana kaki kulani, meyafarune jiyama da daddare nakiraka da yawa amma bakayi picking ba, pls yaya I'm sorry idan na maka lefi" Wata uwar harara yadago ya zabga mata, wadda tasa yayan cikinta hautsinawa. "Waye Wanda yazo gurinki jiya?" Yajefo mata wannan tambayar cikin kakkausar murya. Rasss! Gabanta yayanke yafadi, dama yasan kamal yazo, nashiga uku ni suhailat, Ashe duk boyon danakeyi yasan da zuwannansa. Cikin alamun rashin gaskiya tace, "am... Cla..ss ma..te dinane" "kifadamun gaskiya, kinsan banason karya ko?" Yafadi haka yana tsareta da idanunsa, kasa tayi da kanta cikin matukar tsoro, batason fushinsa ko bacin ransa, saboda be iya fushiba. "Dagaske nake yaya" bekara cemata komaiba yacigaba da aikinsa. Gajiya tayi da zama ta mike jiki asabule ta fice, dankarta kara wani lefin. mommy ce kawai zata iya shawo mata kansa, yanda taga tsananin bacin rai atattare dashi.......

Seda akayi sallar azhar na tashi wanka nayi tare da dauro alwala. Ina idar da sallah nafita falo domin yin kallo, dannagaji da zaman da kwanciya kuma nasan yanzu babu kowa a falon. Ina shiga falon naga yaya sadiq, shikadai azaune. Da mamaki nake kallonsa. "Yaya sadiq, ina wuni?" Nagaisheshi bayan nazauna. "Lafiya kalau, maryama ya gidan?" "Alhamdulillah yau lafiya naga baka fita aikiba?" Murmushi yayi yace, "kinmanta yau weekend ne" "eh hakanefa bamanta" tasowa yayi yadawo kusa dani yazauna. "Meke damunkine maryam, naga kamar da damuwa akan fuskarki?" "Bakomai yaya, amma meyasa kullum.kake tambayata haka." Murmusawa yayi yace, "saboda inaganin hakan atattare dakene, amma senaji kinje bakomai, ko bakyajin dadin zaman gidannamune?" "A'a kokadan bahaka bane kawaidai kai kake ganin haka" bebani amsaba yazira hannunsa acikin aljihun wandonsa, wani zobe na azurfa me kyau ya mikomun yana fadin, "saka wannan ahannunki, naga hannunki ko ring daya babu" cike da mamaki nake kallonsa, "kaii yaya sadiq, amma yayi kyau sosai, nagode Allah yasaka da alkhairi." "Babu komai kanwata ni dake da suhailat duk daya nadaukeku agurina,duk abunda zangani insai mata kema zansiya miki" murmushi nayi inasaka azurfan a danyatsana na tsakiya,naji dadin kalamansa sosai, kaf gidannan bayan baaba talatu babu Wanda nakejin dadin kasancewa dashi tamkar yaya sadiq, yanada kirki sosai bakamar yan'uwansaba,shiyasa nasaki jikina dashi. Azurfar tamun kyau ahannuna kuma tamun dadidai tamkara angwadani. Godiya namasa sosai, harseda yacemun godiyar ta isa haka. labari ya shiga bani na'abun bandariya, daga baya muka koma hira. gaskiya yadebemun kewa sosai, wadda harta mantar dani rikicinmu da oga. Muna cikin hirarne mommy tashigo falon. Tunda tashigo namata sannu, naja bakina nayi gum. Hira suka farayi da danta, nikuma na maida hankalina akan kallo.

Zannurainne yashigo falon, zama yayi agefen mahaifiyarsa, gaishesa nayi, bayare daya kalleniba ya'amsamun, yau kam naci sa'a ya'amsamun amma duk da haka gwarashi akan haidar. "Mommy yaufa ba'a gyaramun dakiba, yanacan yayi kaca_kaca." "Meyasa my son, su salame basuzobane?" "Sunzo ina bacci, that is the why" "ohk bari nakirasu yanzu su gyara maka" "no, mommy leave them, wannan yarinyar taje ta gyaramun kawai". Bansan meyasaba naji gabana yayanke yafadi, duka maganar dasukeyi inajinsu, Allah yasa kar mommy ta yarda naje na gyara masa, nifa harga Allah bansan zuwa dakin maza, sukuma naga hakan bakomai bane agurins......."maryam kije kigyarawa zannurain dakinshi yanzu" muryar mommy takatsemun tunani. Cikin ladabi na'amsa mata. "Toh mommy, amma bansan inane dakinba" kwatantamun part dinnasu mommy tayi, mikewa nayi zuciyata babu dadi, nafice. Ina kallon fuskar yaya sadiq nagane Sam beji dadin hakanba. Da tafiya daga part din mommy zuwa nasu, suma part dinnasu babbane kuma shima yayi kyau. Sama nahau kamar yadda mommy tacemun, dakin dake left side, nashiga. Banwani tsaya karewa dakin kalloba, saboda burina inyi ingama gyaran. Filallika nasauke kasa nafara karkade zanin gadon, wani abune karami naga yafado daga kan gadon, dauka nayi ina dubawa. Zaro idonayi nayi waje, domin bazantaba mantawa da abunnanba, saboda asanadinsa aka taba zanemu lokacin muna j.s 3, wata kawarmu aka kamashi, ni'a time dinma bansan ko meneba, sedaga baya salimat takemun bayani wai sunansa *condom*, da kuma dalilin dayasa ake amfani dashi. Ajiyewa nayi zuciyata cike da mamaki, tome zannurain yakeyi dashi shida ba mataba. Ajiyewa nayi tare da Tabe baki, nacigaba da gyaran dakin, nagama gyaran gado ina kokarin share dakin, naji anturo kofar dakin. Dasauri nadago dan ganin meshigowa, zannurain dinne, yana kokarin maida kofar yarufe........✍️

Meson complete Whatsapp 08166674823

*ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_

*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*

*Bismillahirrahmanirrahim*

1️⃣5️⃣

..........maida kofar yayi ya rufe,hakan yayi daidai da buguwar da zuciyata tayi, cak na tsaya rike da tsintsiyar ahannuna,ina kallonsa, hade fuskarsa yayi yana bina da wani mugun kallo tamkar yaga kashi, wayar hannunsa ya ajiye akan mudubi,toilet naga ya nufa,becemun komaiba. Wata sassanyar ajiyar zuciya nasauke,bayan ya shiga toilet din. Sunkuyawa nayi nafara sharar,cikin sauri,sonake kafin ya fito nakarasa saboda kasancewarmu a daki daya bedaceba. Ko Rabin dakin banyiba,naji ana knocking kofar dakin,ajiye tsintsiyar hannuna nayi naje na bude,zuciyata nadan bugawa. Yaya sadiq nagani tsaye fuskarsa ahade, kallona yayi na wasu sakanni,sannan yace, "wuce mu tafi" da mamaki nake kallonsa,zanyi magana yadagamun hannu,jiki asanyaye nabiyo bayanshi muka fice. Tafiya mukeyi amma babu Wanda yayiwa dan'uwansa magana,nalura ransa abace yake sosai,danni tunda nazo gidanma bantaba ganinsa cikin irin wannan bacin ranba,domin shi mutum ne ma'abocin fara'a da raha. Har kofar part dinmu yarakani, satar kallonsa nayi naga shima ni yake kallo,duk senaji na tsargu, ahankali na juya na fara tafiya, na shige part dinnamu. Wata sassanyar ajiyar zuciya sadiq yasauke bayan tashige,shima juyawa yayi ya koma part dinnasu..........

Turus zannurain ya tsaya bayan yafito daga toilet din,ganin babu maryam adakin, ga shara ta fara kuma bata karasaba. Cikin dacin rai ya fita domin ganin iskancin daya hanata karasa masa gyaran dakin,ga toilet dinma bata wankeshiba. A falon kasa yaci karo da yaya sadiq,daya shigo part din,zagaye shi yayi yana kokarin fita sadiq ya rukosa. Tsayawa yayi batare daya juyoba, "kama dena wani sauri,kana tafiya fuuu kamar zaka tashi sama,nasan mekake shirinyi,toni nace ta koma,ka gyara dakin da kanka,kokuma Wanda suka saba gyara maka su gyarama,aidama ita banda gyaran dakinku aka dauketa aiki a gidannan,danhaka daga yau karka kara sata gyaran daki,nafada maka,kuma karka kuskura kace zaka mata wani abun!" Yakarasa zancen dadan daga murya, zannurain bashi dadamar musawa sadiq abunda yace,domin duk fitsararsu basayiwa yayyensu,dan daddy bebasu wannan tarbiyyarba,ga kuma oga kwata_kwata mustapha yanajin labarin kayiwa nagaba dakai rashin kunya seya sabarmaka. Juyawa yayi,yakoma sama yana kunkuni aransa amma bece komaiba........

Seda gabana yafadi danashiga falo,ganin suhailat kwance akan cinyar mommy ita kuma mommy tana waya,ni indai ba tsautsayiba bana kaunar abunda zehadani da suhailat. Sallama nayi batako kalkeniba balle ta amsamun,mommy cema kawai tadagamun hannu tana bina da kallon dabana ganemasa, narasa meyasa indai muna guri daya duk dagowar dazanyi senaga mommy tana bina da wani irin kallo,araina nakance ko dabi'arta kenan kalllon mutane oho,danni kallonnata yafara isata. Dakina nashige.

Mommy bayan tagama wayar datakeyi ta shafa kan suhailat Wanda ko dankwali babu,tana fadin, "yadai daughter naga kamar ranki abace,meke damarmunkene.?" Cikin tabara tace, "mum, yayanefa daga naje part dinsa dazu yayitamun fada yanamun tsawa,karshema koroni yayi wai duk akan kamal yazo gidannan,kuma nafada masa abokin karatunane" murmushi mommy tayi tace, "aidama nasani,toki kwantar da hankalinki kidena damuwa bari nakirasa awaya nabashi hakuri" "yawwa mommy ta thanks" pick mommy tamata agoshi. ta dakko wayarta ta yi diarling number shi, har 2 missed call tamasa amma bedagaba. "Kinga daughter, beyi picking call dinba,amma mubari zuwa later idanma bekiraniba senaje har part dinnasa,natausheshi" "tom shikenan mum,bari naje na kwanta bacci nakeji" suhailat ta fadi haka tana tashi daga jikin mommy. "Ohk daughter sekin tashi"......

Bayan sallar sala'ar ina toilet ina wanke kayan dana cire naji,ana knocking kofar dakina,tsane hannuna nayi na dauraye na fito na bude. Daya daga cikin masu aikin gidan ce, gaisawa mukayi tacemun infito falo hajiya tana nemana. Amsa mata nayi nakoma na dakko hijabina nasaka,ina mamakin mommy,yanda idan tana nemana bazata iya zuwa takiraniba da kanta, dukda muna part daya,sedai ta turo wasu dasukecan da nisa,aganina ai wannan wahalace. Da sallama abakina na karasa falon,ina bin bakin masu kamala dake falon da kallo. Wata dattijuwace,sekuma wata yar budurwa dako zata girmemun kadanne. Tsugunnawa nayi na gaishe da dattijuwar cikin ladabi, ta amsamun fuskarta dauke da fara'a,ita kuwa matashiyar se kallona takeyi. Sannu namata,amsawa tayi ta kara da fadin, "aunty,kinga nasaki baki se kallonta nakeyi,naganta kyakkyawa masha Allah,mommy ina kika samu wannan me aikin kyakkyawa da ita,gata kuma......"kai aliya badai danbanzan surutuba,daga ganin yarmutane zaki fara cikata da surutu." Wadda sukazo taren ta fadi haka,da alama kuma mahaifiyartace saboda tsananin kamar dasukeyi. Nidai murmushi kawai nayi,mommy ma murmushin tayi tana kallona. "Maryam baki mukayi,kije kihado musu abinci" cewar mommy tana mikewa. Cikin ladabi na amsa mata ina tashi. "Bari inzo intayaki" cewar budurwar itama tana mikewa,Murmushi nakara mata akaro na biyu. Tare muka Shiga kitchen din, muka hado kayan muka jera akan dinning, mamakinta ya cikani,daga ganinta itama daga gidan kudi ta fito,amma jibi yanda takemun babu kyama kokuma nuna banbanci,ashe dai masu kudin akwai masu kirki. dakina na koma,bayan mun kammala. "Gaskiya aunty me aikin gidan daddy menasara,ta burgeni zanso ta zama frnd dita,bari nagama cin abincin nan naje musha hira." cewar aliya tana kokarin kai abinci baki. Harararta aunty tayi tace, "zadai kije cikata da shegen surutunnan naki, Mara kan gado,to itadai kinga yanda take, daga ganinta bameson hayaniya bace,karkije ki takura mata."

Tura baki gaba,Aliya tayi tafara cin abinta. (Hajiya saudart kanwar alh menarasace,uwarsu daya ubansu daya,dama su uku iyayensu suka haifa,daga alh menasara,se baban suhailat sekuma auta hajiya saudart,wadda suke kiranta da aunty. ) ita kanta aunty,maryam ta burgeta, gani daya data mata tagane yarinyar tana da nutsuwa, da hankali. ina cikin shanya kayana najitashigo dakin da sallama,dama abude nabar kofar. Har bakin toilet din takaraso rike haba tayi tace, "sannunki da aiki, dakanki kike wankin,bada masu wanki agidanba kidinga basu mana" "ai wankin babu yawa,kayan dana cirenefa" "lallai agaisheki,nikuwa kinganninan na tsani wanki da wanke wanke arayuwata." Murmurshi na mata kawai,ina mopping toilet din bayan nagama shanyar. Aliya bata damu da shirun da maryam tamataba, tace. "Nikuma. Maryam aunty suhailat tananan tunda mukazo banji duriyartaba" "tananandai dazuma kafin kuzo tana falo,ammadai yanzu bansaniba kota fita" nabata amsa ina fitowa daga toilet din. Zama mukayi abakin gado,tabe baki aliya tayi tace, "hmmm,kilanma tana jinmu taki fitowa,shiyasafa dakyar na biyo aunty gidannan, saboda kwata_kwata bama shiri da ita, kingadai babanta da auntynmu uwarsu daya ubansu daya,amma seta dinga daddaga mun kai,gata da masifa,amma ina zuwa naganki senaji dadi dannasamu abokiyar hira." Dariya nayi danyadda take magana ta matukar bani dariya,"wow kinga yadda kika kara kyau kuwa,dakikayi dariyar nan,ga dimples dinki sunkara lotsawa,dama nice ke." Murmushi kawai namata, nace. "Kemafa kyakkyawace amma.kindage seyabon kyauna kikeyi" "hmm,mekyau inda babu kyawawa irinkuba." nanma murmusawa kawai nayi.Hira tashiga yimun tana bani labarai, harta fadamun daga kaduna suke,tanata bani labarin kawayenta dana school, lokaci daya naji tashiga raina, baburuwanta gaskiya, tamkar wadda muka Dade da sanin juna, nalura daga ganinta bazatayi wulakanciba,bata duba matsayina agidanba,tasaki jikinta dani tanatamun hira,nima naji dadin haka,kobakomai zata debemun kewa kafin suntafi.......

*___________________* *MUSTAPHA* *___________________*

Har sallar azhar yanata faman aiki, sallah ce tasheshi dama kuma ya kammala, abunda yakeyi. Yunwace yaji tana nukurkusarsa,dinning ya nufa inda maryam tajere masa abinci, yahada tea yasha sannan yatsakuri sauran kayan break din,dahar time din dazafinsu basuyi sanyiba,saboda flaks din dasuke ciki masu rikon zafine sosai, yaci. Sedayaje sallah yadawo sannan yayi wanka ya shirya cikin kananun kaya, Wanda suka matukar yimasa kyau. Direbansa yakira,yazo ya daukesa zuwa kamfanin dayake aiki,domin yanason yaduba wasu ayyukane. Time din da mommy takirashima yanacan,shiyasa beyi picking call dintaba, sedaga baya yaga missed call dinta,text ya turamata,akan yaje office ne,yana sauri shiyasa beshigo yamata sallamaba sedai idan yadawo. Dama ka'idane kullum idan yadawo daga sallar asuba,baya komawa part dinsa seya fara zuwa yagaida mommy,yaga kuma yatatashi,sannan yakoma part dinsa. Yanaganin text din da suhailat ta masa kala_kala naban hakuri,karantawa kawai yayi amma bemata reply ba. Shifa Sam bayajin son suhailat aransa,bayan na yan'uwantaka, saboda shi sam bakalar macen dayakeso bace suhailat. Suhailat tanada rawar kai,da hayaniya. Shikuma yafison mace silent Mara hayaniya. Kawai yana tausayin suhailat ne yanda take tsananin sonsa, shiya shima yake nunamata yana sonta, kuma sannan iyayensuma suna farin ciki da soyayyartasu. A'da Sometimes yana tunanin anya kuwa yanada lafiya,kamar kowanne namiji, saboda bayajin wani feeling kokadan ajikinsa, amma kuma segashi yanzu harciwo feeling yake samasa,tundaga ranar da accident yahadasu da yarinyar dabesan ina zegantaba, gashi asanadiyyarta komai nasa yana kokarin canzawa,danma yadage da shan magunguna yanzu, dabesan halin dazeshigaba. Watsar da tunanin komai yayi daga ransa yacigaba da abunda yakawosa. Se kusan magriba yabaro office din,sanda ya shigo gida ana kiraye_kirayen sallar magriba, beko shiga cikin gidanba,ya nufi masallaci.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull