Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 8
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 8: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 8. Washegari,ta kama juma'atu babbar rana. tunda na tashi…
2,976 words
Washegari,ta kama juma'atu babbar rana. tunda na tashi sallar asuba bankomaba,sonake nayi aikina da wuri naje gida.karfe 8 nagama shara da moping gyaran dakinsune kawai banyiba da wanke_wanke. Kukune ya fito daga kitchen yana jera kulolin abinci akan dinning.gaisawa mukayi dashi,hira yafaramun cikin gurbatacciyar hausarsa. Na lura shi mutum ne me shegen surutu ni kuma bana shiri dame surutu. Amma shi yana bani nishadi saboda hausarsa dariya take bani. Wajen 8:30,samarin gidan suka shigo falon,mikewa tsaye nayi na gaishesu,kamar kodayaushe babu Wanda ya amsamun se yaya sadiq. direct kan dinning suka nufa suka zauna,nima kasa na samu na rakube. Cikin wata uwar tsawa haydar yacemun, "ke mahaukaciyar inace kina ganinmu, mun zauna amma bazaki taso kiyi serving dinmuba. Dasauri na mike ina basa hakuri,saboda naga mommy da suhailat nasu fitoba shiyasa banyi yunkurin zuba musuba. Ina cikin zuba musu mommy ta fito daga dakin ta.gaisheta nayi,kamar kodayaushe ta amsamun babu yabo babu fallasa. Itama zuba mata nayi na koma gefe ina jiran hamshakiya. Mintuna kadan ta fito itama,cikin shrinta. Bakar abayace ajikinta wadda ta matukar haska farar fatarta.tayi kyau sosai. "Ina kwana,aunty suhailat" wani mugun kallo ta watsomun "daban kwanaba,zaki ganni" kasa nayi da kaina,meye lefina a ciki kuma danna gaisheta ita komai Lefine agurinta. Tana zama itama naje na zuba mata break dinta.
Harna nufi dakin hajiya zan gyara naji muryar suhailat. "Ke!" Tsayawa nayi amma banjuyoba. "Kutmar, lallaima yarinyarnan wuyanki yayi kauri. ina miki magana kinki juyowa saboda tsabar raini ko? Juyowa nayi ina bata hakuri saboda banason tashin hankali. "Dalla ni,rufemun wani rubabben bakinki,nonsense kawai.zanyi bako anjima,kafin na dawo daga school ki hada masa drinks,sannan kuma zakuyi aikin delicious dinsa tare dasu salame.amsa mata nayi cikin girmamawa nashige dakin Hajiya.
Seda nagama aikina tsaf,nima na karya. sannan na koma nayi wanka. Shiryawa nayi cikin wata atamfa dinkin doguwar Riga.yay mun dass ajikina.turaruka masu sanyin kamshi na fesa wadanda yaasadiq ya kawomun.hijabina iya gwiwa nasaka Wanda ya shiga da kalar kayan. Tsayawa nayi agaban mudubi ina karewa kaina kallo. Nikaina nasan na canza,a yan kwanakin danayi a gidannan. To zanci me kyau,insha mekyau, sabulun wanka me kyau,man shafawa me kyau.makwanci me kyau gashi tunda nazo banga ranaba. Falo na fito da niyyar tambayar mommy, zan fita. a kitchen na tarar da ita tana shirya kaya a wani katon kwando. (Da'alama dai na dan lelentane.)"Sannu da aiki mommy" "yawwa,am maryam dan kaiwa son breakfast dinsa,idan kika dawo sekiyi aikin da daughter tasakaki. atunaninta aikin suhailat na taho yi. dammmm!! Zuciyata ta buga,yaseen ni nama manta dashi kwata_kwata agidan,dazu da safe agurin break bangansaba shiyasa bantuna dashiba. Karba nayi ina amsa mata. "Kiyi sauri maryam,yana saurine ze fita. Akwai plates a kitchen dinsa,ki duba ki dakko seki zuba masa. "Toh mommy na'amsa cikin ladabi.
Tunda na nufi part dinnasa zuciyata take luguden bugu, tundaga falon kasa sihirtaccen kamshinsa ya ziyarci hancina lumshe idanuwanayi saboda dadinsa.sama nahau,shima dai kamshinnasane yamun sannu da zuwa.kan dinning na ajiye kwandon. Kofar dake kusa dakinshi na bude cikin sa'a kuwa nanne kitchen. Tsayawa nayi ina kallon kitchen din,Wanda ko wata amaryar albarka.sekace mace komai kwai a kitchen din. Ba karya ya hadu shima.Plates din na dakko seda nadaurayesu sannan na dawo falo.rasss,gabana yayanke ya fadi ganinshi zaune akan dinning yana latsa wayarsa. Karasawa nayi cikin matukar tsoronsa na ajiye plates din,gaishesa nayi amma ko kallona beyiba.tambayarsa nayi mezan saka masa nanma shiru kamar besan ina gurinba.tsayawa nayi ina kare masa kallo.kananun kayane ajikinsa,rigar farace Tass, se bakin wando.kayan sun masa kyau sosai,se yanzu naga tsananin kamarsa da mommy.gajiya nayi da tsaiwa nafara serving dinshi,ina kunkuni kasa_kasa. Komai zuba masa nake acikin plate ina tura masa gabansa. Na dakko farfesu zan zuba masa,nadan saci kallonsa. Idanuwansa tsam akaina yana jifana da wani irin kallo.nandanan jikina yafara rawa. Allah yagani tsoron idanuwansa nakeyi,saboda suna saukarmun da wani yanayi ajikina.ban Ankara kawai gani nayi spoon din yafadi daga hannuna,ferfesunne ya zube akan table din.cikin matukar tsoro na dago ina kallon gefen dayake. Gaba daya roman farfesun ya tsatstsallu a gaban farar rigarsa........✍️
Meson complete Whatsapp 08166674823
*ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_
*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*
*Bismillahirrahmanirrahim*
1️⃣3️⃣
...............Kallonta kawai ya tsaya yanayi cike da takaici da bakin ciki,bayan ta shigo ta samesa bata masa sallamaba, sannan tana ta masa surutun banza,yanzu kuma yana sauri zeje office tazo ta bata masa Riga,dolene ya hukunta yarinyarnan yau. Nikuwa jikina rawa yakamayi saboda matsanancin tsoro da razana,wlh bansan ya'akayi ludayin ya subce daga hannunaba.batare dana bari na kallesaba,na tsugunna akasa akan gwiwata idona tab da kwalla na fara magna. "Dan Allah Dan annabi,kayi hakuri wlh bansanib".... "Shut up!" Yadakamun wata uwar tsawa,wadda najita har tsakiyar kaina,hawayen dake makale a idonane yafara zuba,akan fuskata jikina yacigaba da rawa tamkar mazari. Kallonta kawai yakeyi,gata yarinya karama amma se shegen rashin jin tsiya,ga dan banzan tsoro. Inajin yanda idanuwamsa suke yawo ajikina,amma nakasa dago kaina na kallesa. Mikewa yayi bekaracemun komaiba,ajiyar zuciya na sauke,ina bin bayansa da kallo. Tashi nayi, nafara goge inda na zubar da romon,amma fa bandena kukaba. Yayi kusan 5 minutes sannan ya fito sanye da wasu kayan ajikinsa,hannunsa dauke da rigar dana bata masa.dafe kansa yayi aransa yace. "Ko a ina mommy ta samo wannan yarinyar, ita kam Sam kuka baya mata wahala,yanzu meyamata datake ta kuka,yana zaman zamansa zatasa masa ciwon kai. Ina rakubu tamkar almajira naji ya cillomun rigartasa a jikina, yayi hanyar fita batare dayace mun komaiba. Fahimtar danayi fita zeyi kuma ko break din beyiba, senaji ba dadi saboda nice sanadiyyar hakan. Cikin marairaicewa nace masa. "Dan Allah karka fita bakaci abincinnanba,idan ka tafi haka bazanji dadiba wlh." ni kaina seda na furta hakan naji wani iri. Kamar daga sama yaji muryarta tana rokonsa,tsayawa yayi cak, zuciyarsa na masa kuna shifa bayason mutum me yawan takura, dolene yasanar da mommy karta kara aiko masa yarinyarnan. Juyowa yayi karaf muka hada ido,da sauri nayi kasa da nawa idon saboda wata uwar harara daya wurgomun. Ahankali ya fara takowa zuwa dinning din,da hannu ya nunamun kofa alamun na fice masa. Sum_sum nafara tafiya rungume da rigarsa,duk da befadamunba amma nagane nufinsa na wanke masa. A falon kasa na tsaya ina maida numfashi,tare da daidaita nutsuwata. Saboda ina fita a haka kallo daya mutum zemun yagano zallar firgici da tsoro a tattare dani. Ninke rigarsa nayi wadda sassanyan kamshinta ya mamaye ni,a hijab dina na boyeta na nufi hanyar fita daga part dinnasa........
Kamar amafarki na hangi baaba talatu da'alamun fita zatayi saboda naga ta nufi get din tsakiya.wani sanyi naji araina, tafiya na farayi cikin sauri_sauri saboda na cimmata. "Baaba talatu" nakira sunanta bayan na matso kusa da ita. Juyowa tayi itama cikin mamaki tace, "maryam!" "Na'am baaba talatu ina kwana, kamo hannuna tayi batare data amsamun gaisuwataba,fara'a fal fuskarta. Tace, "maryam dake nake kwana nake tashi araina,kullum,inaso naganki amma badama." "Baaba to meyasa yanzu kikadena zuwa part din hajiya,nima inason ganinki amma bansan inda zansamekiba. "Hmmm,maryam,kenan ai se hajiya ta kiramu muke da damar shiga part dinta,amma ke kina da ikon dazaki iya fitowa kije ko'ina agidannan, kinga wancan dan karamin part din idan kika wuce na hajiya,to nanne part dinmu na yan'aiki idan kikazo zaki ganni." "Kai amma naji dadin ganinki baaba,insha Allah idannagama aikina zanzo anjima,nifa nayi tunanin ma bakya gidannan." Murmushi baaba talatu tayi tace, "banda abunki maryam,ina zani ai nanne gurin Neman abincina,yanzudai sauri nakeyi zanje dubiya, wata yar garinmuce datayi aure anan jiya tayi bari,shine zanje na dubota banason a shiga masallaci bandawoba. "Toh,shikenan baaba,sekin dawo,ki mata sannu,Allah yakiyaye." "Ameen maryam sena dawo" part dinmu nanufa zuciyata cike da murnar ganin baaba talatu dama akwai tambayoyin danakeson nayi mata.
Mommy bata falo,may be tana dakin ta. abunda yake kara dauremun kai da gidannan tunda nazo banga bako ko daya yazoba,kodayake bandade da zuwaba kila shiyasaka. Dakina nashiga na'ajiye masa rigarsa acikin cover da nufin idannaga aikin dazanyi sena wanke masa. Kitchen na shiga, kuku na tarar yana kokarin Dora lunch tun yanzu,dariya nayi masa nace, "kai emeka tun yanzu zaka Dora girki?" Cikin hausarsa yacemun madam karamace tasakashi aiki kafin ta fita. Jinjina kaina nayi,dannagane aunty suhailat yake nufi. Tsayawa nayi ina karewa kitchen din kallo narasama wanne kalan drinks zan hada, na iya drinks kala_kala,tunda shine sana'ar innata. amma bansaniba koze musu dadi. Yanke shawara nayi bari kawai na mata zobo,da kunun aya da lemon kwakwa. tunda na kware wajen yinsu,dan da azumi munayi a gidan umma nida saleemat. Cikin freezer na duba,naga akwai duk abunda zan bukata. Sedai banga aya da zobo ba a kitchen din,amma naga kwakwa da dabino da madara da sugar, dasu flavour. Tambayar emeka nayi amma yakasa gane me nake nufi, dole se dakin hajiya na shiga na tambayeta. Tacemun inje kitchen injirata zata saka akawomun,godiya na mata na koma kitchen na fara gogo kwakwar da zanyi lemo da ita. Mintuna kadan wata mata ta kawomun aya da zobon dayawa, wanke ayar nayi na jikata...... ( typing da wahala danayi muku yanda tayi lemon,da kunun ayar.)
Ina cikin aikina naji fitinannen kamshinsa ya mamayemun hancina, nandanan naji zuciyata ta hau luguden bugu Wanda narasa na menene aduk lokacin damukayi kusanci dashi senaji hakan a tattare dani,lekawa nayi ta window ina kallonsa,yana sanye cikin manyan kaya yanzu sabanin sanda na baroshi kananane,kayan sun matukar yimasa kyau,amma ba hula akansa, dakin mahaifiyarsa ya shiga. Ajiyar zuciya na sauke na dawo na cigaba da aikina,araina ina tunanin tome yahanasa zuwa gurin aiki,kodai haryaje ya dawone? Babu amsa,wata zuciyar ta fadamun hakan. Se kusan karfe 2,nagama aikin drinks din saboda nayishi da yawa ko wanima zesha. A fridge nasakasu duka. Bayan na zubawa emeka nasa, ai kuwa nasha santi a gurinsa. Nidai dariya kawai natayi masa.
Daki na koma saboda inatajiran wadanda aunty suhailat tace,zamuyi aiki tare amma shiru_shiru basu zoba,ashe ni bansaniba a part dinsu sukayi aikin,dama kayan snacks ne,sukayi mata. Wanka nayi tare da dauro alwala nayi sallah. kwanciya nayi da nufin nadan huta. banmasan sanda bacci ya daukeniba.....
Tunda ta fice daga falon ya bita da kallo ta gefen ido,besan sanda murmushi ya subce masaba saboda yanda takeyin komai nata a tsorace,kuma da yarinta. Kadan ya taba breakfast din ya mike ya koma dakinsa,fasa zuwa office dinma yayi gaba daya saboda lokaci ya kure,gashi yau Friday, 12 yake baro office saboda masallacin juma'a. Aiki yayi a laptop dinsa,sannan ya mike yayi wanka yayi shirin zuwa masallaci. Seya fara zuwa ya gaida mommy sannan zewuce masallacin. Lokacin dayashiga part din mommy,yana kallonta ta gefen ido tana lekensa ta window, wani murmushi yayi Wanda shikadai yasan ma'anarsa,ya shige dakin mahaifiyarsa.......
Suhailat se da 2 ta wuce,ta dawo gida. A matukar gajiye ta dawo dama ita langwaice batason aikin wahala,zaman lectures ma wahala ne agurinta. wanka tayi ta shirya cikin wani hadadden Dubai less.dinkin Riga da skirt ne,yamata dass a jikinta. Ta kafa daurinta tayi kyau sosai,tamkar ka saceta. Suhailat irin matannanne dakana ganinsu zakaga tsantsar kyawunsu. Taci turaruka kala_kala setashin kamshi takeyi. Waya sukayi da kamal yasanar mata yana kan hanya. Abinci taci kadan kafin yakaraso. Amma zuciyartarfa cike take da tsoron yayanta. A kan zuwan kamal Tasan dai idan tace masa abokin karatuntane,ze yarda. Dakin mommy ta nufa tasanar mata kamal yanakan hanya. Mommy macece me son ra'ayin yayanta dabin abunda sukeso. Hakan yasa batayi yunkurin hana kamal zuwaba, koda yakema hakan bakomai bane agurinsu,dan abokin yarka yakawo mata ziyara gida.kuma tayarda da abunda suhailat tace mata akan,kamal abokin karatuntane.....
Kamal shikadai yazo gidan su suhailat,kuma wannan shine zuwansa na farko gidan. Bin gidan yakeyi da kallo yana jinjina yanda aka kashewa gidan kudi, tabbas dolene, yabi shawarar abokinsa, yasan yanda yayi ya auri suhailat kodan yaci kudin babanta. Sema yanzu dayazo gidannasu,yakara jin kwadayin aurannata. Murmushi yayi yana kissima abubuwa da yawa aransa,kafin yafara Neman auran suhailat dolene yafara kawar da *almustapha sulaiman menasara* daga doron duniya,domin idan har yana raye suhailat baza tataba auransaba. Yadade da sanin tarihin soyayyar mustapha azuciyar suhailat, wani murmushin yakara saki,akaro na biyu........
Tarba sosai kamal yasamu daga gurin suhailat,babban falon bakin daddy suhailat ta kaishi bayan ta taryoshi da kanta.
Ina cikin baccina naji andakamun duka abaya,da sauri na bude idona saboda dukan ya shigeni. Tozali nayi da aunty suhailat dataketa zabgamun uwar harara. "Sannu hamshakiya kinzo kin kwanta kina bacci,ina abunda nace miki kihadamun?." "Kiyi hakuri aunty suhailat banmasan baccin yadaukeniba,nahada miki drinks din yana fridge." Wani banzan kallo ta jefeni dashi,tace, "to kina nufin dakaina zan dakko drinks din nakaimasa koyaya?." Sakkowa nayi daga kan gadon ina girgizamata kai,hijabina na dauka nasaka nabi bayanta zuwa kitchen. Acikin wasu hadaddun jug na zuzzuba masa drinks din. Bayan su salame tace nabi zuwa inda ta saukeshi,sukuma suna dauke da kayan abincine zasu kaimasa,suna gaba ina binsu abaya. Da nisa gaskiya daga part dinmu zuwa part din da'aka saukeshi. Nidai har yanzu mamakin girman gidannan nake, gida kamar unguwa,gashi part part din gidan yayi yawa. Kamal yana zaune yana latsa wayarsa suka shiga suka ajiye masa kayan abincin,nice ta karshen shiga. araina nace,ji uban kayan da'aka shiryamasa shikadai, kuma idan yatashidai kadan zeci iya cikinsa. wani talakan kuwa yanacan abunda zecima bashi dashi.Tunda na shiga naga yadago ya kuramun ido, yana kallona. Tsaki naja kasa_kasa domin ni natsani kallo arayuwata. Gaishesa nayi ina ajiye masa kayan akan center table din gabansa, amsawa yayi yana bina da wani mayen kallo. Harna juya zanfita yatsayar dani da fadin, "Yan mata baki karasa ladankiba,baki zubamun drinks dinba." Dawowa nayi zan zuba masa, amma bance komaiba, Karamin Kofi nadauka nafara tsiyaya masa,raina yafara baci da kallon dayake bina dashi,duk nabi na tsargu. Shiko kamal se lasar lips dinsa yake tundaga ta shigo falon yaganta yajita masa,aransa yanacewa ina suhailat ta samo wannan yarinyar kyakkyawa, danya shakaf da ita,duk da acikin hijabi take amma daga gani tana da manyan kayan aiki. Yanzu kuwa data tsugunna seya kurawa fuskarta ido,yana ganin yanda taturo dan karamin pink lips dinta gaba, aijiyayi tamkar ya janyota jikinsa ya tsotseshi,daga gani zeyi taushi da dadi. Tundazu nake mika masa cup din,bayan na tsiyaya masa lemon kwakwar amma naji yaki karba,dago kaina nayi dannaga meyahanashi karba,senaga kallona kawai yakeyi sekace ze cinyeni. Kara bata rai nayi nace, "Karbi" adakile nayi maganar. Kamar Wanda ya firgita ya miko hannu da niyyar karba, kawai jinayi ya hada da hannuna ya damke da cup din. Kokarin kwace hannuna nayi amma yaki sakarmun se wani murmushi yake jifana dashi. Kawai jinayi kwalla ta cikamun idona,saboda bakin ciki da takaici,na bude baki zanyi magana aunty suhailat ta shigo falon..............✍️
Meson complete Whatsapp 08166674823
*ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_
*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*
*Bismillahirrahmanirrahim*
1️⃣4️⃣
...........Da sauri na saki cup din dake hannuna bayan yacikamun hannun, cup din ya fadi kasa ya tarwatse cikin tsananin tsorata na mike tsaye, shima mikewar yayi da sauri saboda kar lemon yabatasa. Wani mugun kallo aunty suhailat take bina dashi, cikin tsana dajin haushi. Tana karasowa gabanmu ta daga hannu da nufin ta kwadamun mari, runtse idona nayi cikin tsammanin jin saukar mari, amma har wasu sakanni suka wuce banjiba. Ahankali na bude idona, senaga Ashe bakonnatane ya rike hannunnata yana girgiza mata, kai.cikin tsananin bacin rai ta fara magana. "Haba kamal yazaka hanani hukunta wannan matsiyaciyar yarinyar, baka ganin abunda tayine, sekace mahaukaciya zata wani sakar maka cup, idan da yabata maka jikinkafa" ta karasa maganar cikin karaji da daga murya. "look baby, ai itama tsautasayine batasan hakan zata faruba, haba bakiga yarinya bace kidena mata magana haka mana" wani kallo ta watsama masa batace komaiba, Nidai ajiyar zuciya kawai nake saukewa, cikin hanzari na nufi kofar fita, saboda ganin yana kokarin janyota jikinsa. Zama kamal yayi yadora suhailat akan cinyarsa, yace. "Haba baby bagirmanki bane kidinga daga murya akan abunda bekaiyakawoba." "Hmm, bazakaganebane kamal natsani yarinyarnan over, haushinta nakeji" murmushi kamal yayi aransa yace, "dole kitsaneta mata tunda tafiki komai da komai." Amma a fili seyashiga lallashinta yana tattabeta.......
Da sauri nake tafiya tamkar zantashi sama, tsayawa nayi abakin kofar falo ina daidaita nutsuwata. Ahankali na bude kofar falon na shiga, mommy ce kadai zaune a falon. Sallama na mata kawai na shige dakina. kan gado na fada ina maida numfashi tunanika kala_kala araina, ga haushin wannan dan akuyar yacikamun zuciya,haka kawai ze rikemun hannu wlh, Allah ya isana. Arayuwata na tsani namiji dan iska. Agefe guda kuma ina mamakin aunty suhailat,yanda take mu'amala da dan iska, haryana tabata. Mtss naja tsaki a fili cikin takaici,nakawar da tunaninsu daga araina. Mikewa nayi na dakko rigar *oga* dankarna manta,nakara wani lefin dannaga ya kulu akan rigarnan. Tasss na wanke masa ita a toilet dina, natisa wankinta yakai sau biyar, sedanaga tayi kal sannan na barta. A toilet din nashanya masa.Alwalar sallar la'asar na dauro na fito, dan anyi sallar tun dazu.
Bayan na idar da sallar nafito domin zuwa part din su baaba talatu. Mommy nagani zaune afalo, da suhailat da bakonta. Bata fuska nayi sosai sabida kallon gefen idon dayake bina dashi. Aunty suhailat kuwa se uwar harara take zabgamun, kusa da mommy na durkusa nace, "mommy zanje gurin baaba talatu" kallona tayi na wasu sakanni, batacemun komaiba,harnayi tunanin bazata barniba senaji tace, "ki dauki lemon kwakwa a kitchen zaki ganshi na zuba a jug,kikaiwa my son,seki wuce daganan" "toh mommy nagode." Na'amsa mata cikin ladabi. Kitchen din nashige na dauka, zuciyata nadan bugawa nanufi part dinnasa, harga Allah tsoron bawan Allah nan nake,tsoroma kuwa bana wasaba. A falon kasa na tarar dashi yanada aiki a system dinsa,yacanza kaya zuwa kanana. Sannu namasa, batare daya dagoba ya amsamun dakai, harzankai lemon kan dinning, sekuma naga dacewar na ajiye masa agabansa, akan center table din gabansa na ajiye masa, ina satar kallonsa. Harna juya zantafi yatsaidani da fadin, "exucuse me pls" juyowa nayi ina kallonsa, da hannunsa yanunamun wata kofa a falon yana fadin, "help me with cup" "ohk sir" na'amsa masa cikin ladabi. Kofar dayanunamun na nufa na bude, kitchen din hadadden shima, bantsaya wani kare masa kalloba na nufi inda naga kofinan, seda na daurayesu sannan na kawomasa na fice daga part din.