Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 7
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 7: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 7. Dafe zuciyarsa yayi saboda tsananta bugu datake masa,Wanda…
3,224 words
Dafe zuciyarsa yayi saboda tsananta bugu datake masa,Wanda besan daliliba, ahankali yake sakkowa daga matattakalar jirgin janye fa trolly ɗinsa,idanuwansa ya lumshe saboda shakar iskar garin mahaifarsa da yayi,yana jin farin ciki sosai aransa,na dawowarsa gida *kano ta dabo tumbin gwiwa* tafiya ya farayi cikin gentle dinsa,fuskarsa babu fara'a kamar koda yaushe.su mommy suna tsaye suna baza ido ganin anata fitowa.suhailat ce ta fara hangoshi. Taɓo mommy tayi,"laaa mommy kinganshi ya fito." Kamar yaji metace shima ya kalli inda suke,bazasu iya jira yaƙarasoba,hakan yasasu nufar inda yake.tunda yafito yan matan dake gurin suke binsa da kallo,cike da burgewa kowacce tanaji aranta dama wannan hadaddan guy din yazama mallakinta.murmushi yasaki kadan,saboda hango yan'uwansa kuma guɗan jininsa sun nufo garesa.da gudu suhailat ta karasa garesa ta fada ƙirjinsa,cikin tsananin murna da doki.shima beyi ƙasa a gwiwaba,ya mata masauki a faffadan kirjinsa,tare dasa tausasan hannayesan yazagane bayanta. Wata nannauyar ajiyar zuciya suhailat ta sauke,lumshe idanuwanta tayi Tana shakar daddadan kamshinsa. Saboda tsabar jaraba,har yanayinta ya fara sauyawa,shafa bayansa tafarayi tama manta a inda suke. Daidai lokacin su mommy suka karaso,raba suhailat yayi daga jikinsa wadda ta kasa magana, da hannu yake amsawa yan uwansa,welcoming din dasuke masa,hugging dinsa sukayi one,by one. Mommy kamar ta maidashi ciki,haka takeji. Duk da baifaɗaba,amma fuskarsa ta bayyana yana cikin farin ciki,sadiq ne ya karbi trolly dinsa suka nufi mota.hannun suhailat ya kama,wadda taketa kallonsa tamkar zata cinyesa,ya matukar yi mata kyau,ya kara wani fresh. duk da fuskarsa tayi fayau alamun ya ɗan ji jiki.Hannunta ya murza,tare da ɗage mata gira,yayi mata alama da hannunsa alamun yadai yaga tayi shiru. Lumshe idanta taƙari tare da lasar lips dinta. Kwantar da kanta tayi ajikinsa,batare da tayi maganaba.saboda itakaɗai tasan metakeji jinta datayi,ajikinsa.ahaka suka ƙarasa motar, front seat yashiga sukuma suna baya kamar yadda sukazo.mommy se tambayoyi take masa,akan ciwonsa,da'abunda yake damunsa. Atakaice yace mata zazzabine....
Direct part ɗinsa ya nufa,duk da mommy taso yaje part ɗinta amma yace mata seya huta zezo.dole haka tasa ƴan aiki suka kwashi kayan data shirya masa zuwa part ɗinsa. Mommy dakanta ta haɗa masa ruwan wanka yashiga.kafin ya fito duk sun fice daga part ɗin,domin sunsan halinsa bayason hayaniya,musammanma daya kasance yau ya dawo.bayan ya ɗauki wasu mintuna ya fito,shiryawa yayi cikin ƙananan kaya,wayarsa ya dauka ya fito falonsa. dinning ya nufa koze samu abunda yake buƙata,amma beganshiba.tsaki yaja,kobi takan liyafar da aka shiryamasa beyiba,ya koma ɗakinsa,text yayiwa mommy akan yana bukatar coffee....
Wata mahaukaciyar yunwace tatasheni ɗaga bacci,toilet na shiga na wanke bakina sannan na fito zuwa kitchen, ina addu'ar Allah yasa babu kowa a falo. Amma kash!,addu'ata bata karɓuba dukansu suna falon amma banda mommy. Suhailat tana ta tsokanar su yahaydar akan yayanta ya dawo, su kuma sunata kukkumbura. Kamar na juya na koma,sekuma naga rashin dacewar hakan tunda sun Riga dasun ganni. Kaina akasa na fara tafiya cikina na kiran chiroma.sannu na musu,amma ko kallo ban ishesuba,yayasadiq ne kawai ya amsamun. Ina shiga kitchen mommy tana fitowa hannunta ɗauke da wani basket me matuƙar kyau,ban kalli mene acikiba,saboda hankalina yanaga aɗɗa'ami. Kafin nayi magana,mommy tarigani. "Yawwa maryam dan kaiwa my son wannan,part dinshi yana gaban namu daga right side dinki,idan kin fita.kiyi sauri dan Allah Dan bayason jira, dama tunanin me kaimasa nakeyi su salame duk sunyi part ɗinsu, su suhailat kuma duk sun gaji......✍️
*BY* *zeey kumurya*
*ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_
*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*
*Bismillahirrahmanirrahim*
1️⃣1️⃣
.............Wani magidancine Wanda zekai kimanin shekara 40. zaune a wani hadaddan restaurent,waya yakeyi.daga bisani kuma yasauke wayar yana wani munafukin murmushi.wata matashiyar budurwace ta shigo restaurant din tana sanye da wani red din Less,da adon baki ajikinsa.ta yafa mayafi black,hang bag din hannuntama black ce.black beauty ce tana dan kiba.gurin magidancinnan ta nufa,sallama ta masa tare da zama akujerar dake fuskantarsa.murmushi dauke a fuskarta. "Barka da zuwa *P.A* "barkanka da warhaka me girma *MD* dadina dake P.A bakya jinkiri idan ankiraki shiyasa nakeson aiki dake.dariya P.A tayi,ai dole kaganni da hanzari me girma,MD. Kasan ance idan kaji kira samune. mikewa tsaye yayi tare da zura hannunsa duka acikin aljihunsa. Maimunatu! Yakira ainihin sunanta. "Na'am MD" kinsan meyasa na kiraki wajannan,girgiza masa kai tayi alamun a'a. Murmushi yakarayi yace" ayanzu kiran gaggawa ya riskeni oga mustapha yadawo garinnan,ayau sabanin da dayace zeyi sati biyu.bamusan dalilin dawowarsaba amma munsa a bincika mana.matsowa yayi daf da ita,wani aiki mukeso ki mana akan oga mustapha,maimuna karki sake wannan damar ta wuceki idan kika yarda zaki yimana wannan aikin,kinada babban rabo na makudan muliyoyin kudi,idan kuwa akayi nasara a aikin,zaki samu ninkin abunda muka baki a farko. Cikin Neman Karin bayani tace"wanne irin aikine wannan me girma MD. dariya yayi yace. "P.A kenan bazan fada miki aikinba sekin yarjemun zakiyi. Shiru P.A tayi na wasu mintuna kafin ta numfasa ta fara magana. "Me girma MD,bazan ki tatakaba,amma a gaskiya banason nayi abunda ze cutar da oga mustapha, saboda tsananin son da nake masa,da kuma halaccinsa agareni. Kafin yazo wannan ma'aikatar lokacin mu yarane na can kasa,kuma shuwagabannin wannan kamfanin alokacin azzalumaine,mun azabtu a wajensu. Amma zuwan oga mustapha, yacanza mana matuka,mutum ne shi me adalci,dakuma tsaiwa akan aikinsa.tasanadinsa yanzu gani a matsayin P.A dinsa. Dariya MD,ya kyalkyale da ita. "Haba P.A, kada garin Neman gira kirasa ido,kada kizo daga baya kiyi bawan ba kanin. Sanin kankine oga mustapha yana da mata agida,yar uwarsace kuma kowa yasan ita ze aura.sannan kuma duk bayanin da kikeyi na oga,ya miki halacci karki manta duk tare yamana,amma ki sani a rayuwar nan ta yanzu kowa kansa yasani,dan haka kibar batun wani oga,kawai ki kama aiki,Wanda ta sanadinsa zakiyi arziki Mara yankewa. Aikinnan ba nawa bane shima nasakani akai. Kallonsa takeyi tamkar meson karanto wani Abu a fuskarsa. "Nima MD banason tufkar dana dade inayi shekara da shekaru nayi kuskuren dazata warware gaba daya. Gashi kuma naji na kwadaitu da son wadannan makudan kudi daka ambata. Zama yayi ya tsiyaya lemon dake kan table din gabansa. Kurba yayi yace. "Ina mai tabbatar miki bazakitaba dana saniba a wanna aikin,aikine daya kunshi manyan kasarnan,dayan kasuw.,kekuma naga ke amintacciyar oga ce shiyasa nasakoki aciki.kedaice zaki mana abunda muke bukata. Kada kiyiwa kanki azanci,idan kingama shawara ki sameni gobe a office idan antashi,sena jiki. Yana gama fadar haka ya mike ya dauki mukullin motarsa da wayarsa yayi gaba.binsa kawai P.A tayi da kallo harya bacewa ganinta.......
*************
Ai Jinayi tamkar nadora hannu aka na kurma ihu,saboda yunwar danakeji harwani jiri_jiri nake gani.gashi kuma mommy ta hadani da aiki,kuma bani da damar bijirewa.cikin sanyin jiki na karba basket din,na juya nayi waje.suhailat na ganina ta mike,"mommy yazakibawa wannan abar ta kaiwa yaya coffee,kinsanfa yaya da kyankyami,idan takai masa dakyar idan zesha.kuma kinsanshi befiyason karikican kowanne irin mutaneba,balle ita dabata san tsarinsaba.bari na kaimasa da kaina.mommy dake bina abaya tace. "Kiyi zamanki my daughter nasan ze karba,banason kina wahala da yawa yanzufa kika gama korafin kingaji.badan tasoba ta koma ta zauna.tana zabgamun uwar harara. Cigaba nayi da tafiya zuciyata na kuna,kafata har hardewa takeyi,se hada hanya nakeyi.tunda nazo gidan yaune nafara fitowa farfajiyar gidan.tsayawa nayi ina bawa idanuwa abinci,nama manta da wani sauri da'akace inyi.wasu shuke_shuke da fulawoyi da suka zagane gidan sunfi komai burgeni.ahankali nake tafiya ina kallon ko'ina,nayi tafiyar 5 minutes na iso wani part kamar yadda hajiya tace daga part dinta seshi. "Ya Allahu" na furta a fili saboda tunkafin na shiga part din nasan ankashe masa dukiya,yaci uwar na hajiya a kyau da tsaruwa. Tamkar da zinare aka ginasa,saboda wani sheki da gininsa yakeyi. Kamar part din hajiya,shima seda nahau step me matattakala 4. Nanfa ake yinta,wata irin koface wadda bantaba ganin irintaba,banmasan ta ina zan budeba.in komane in sanar da hajiya kokuma inyi yaya? Na tambayi kaina.kusan 2 minutes,ina tsaye ina sakawa da kwancewa. se Allah yajehomun da wani bawan Allah,danaga ya tunkaro inda nake.dama tunda nazo gurin naganshi zaune akan kujerar roba daga gefen part din.
Murmushi yamun nima na mayar masa. "Yan mata da alama gurin oga kikazo ko? "Ehhh na amsa masa. "Ohk,nine babba acikin yaransa na gidannan,bejira mezanceba kawai naga yatsaya agaban kofar,kawai gani nayi kofar ta bude da kanta,bin bayansa nayi da sauri nima nashige,muna shiga falon naga ta rufe kanta. "Yawwa yanmata,nasan abunda ya tsayar dake kenan daga yanzu idan kikazo haka zaki dingayi zakiga ta bude,ki hau kan steps dinnan zakiga falo yana ciki,idan kuma bayanan kiyi knocking dakin dakika gani na farko a falon.godiya na masa sosai yasakai ya fice. Suman tsaye nayi saboda se lokacin nagama karewa falon kallo. Banyasan yazan misalta muku tsaruwa da kyawun falonba,kokuma kayan ciki,kawai Ku kissima da kanku.wannan wane irin mutum ne da komai nasa na dabanne a gidannan, wani kugi da cikina yayi yasani yin azamar hawa benen domin nayi sauri na kaimasa sakon nakoma naci abinci,ga lokacin sallar magriba ya gabato. Tasbihi kawai nafarayi araina lokacin dana shiga falon saman,ga wani sassanyan kamshi dayake tashi,Wanda ya mun kamar nasanshi,ko kuma na taba jinsa. Aradu aka barni a falonnan akace in zauna,ko abinci bazan nema,kallonsa zantayi yana debemun kewa,saboda tsaruwarsa. Wani lumtsumeman center carpet na taka,Wanda ya mamaye tsakiyar falon.baya cikin falon hakan yasa nanufi dakin da Adam yace na kwankwasa.tunda natashi daga bacci naji zuciyata tana dan harbawa,amma ina kusantar dakinnasa senaji bugun ya tsananta.
Tunda yayiwa mommy text ya koma bakin gado ya zauna,zaman jira. 5 minutes yajira yaji shiru, dafe mararsa yayi datake dan masa ciwo kadan_kadan.shiru shiru bega ankawo masa coffee dinma,gashi yariga ya saba idan beshaba bayajinsa daidai.har mintuna ashirin suka shude baga ankawo masa.shi mutum ne dabaya maimaita Abu idan yafada yafada kenan,hakan yasa be kira mommy ma, yaji dalilin dayasa ba'akawo masaba. Ammafa ransa harya fara baci.lumshe idonsa yayi tare da cize lips dinsa na kasa. Ahankali nafara knocking kofar dakin. Tsaki yaji jin ana knocking, abunda abude yabar kofar,kuma kofar idan tana key mutum yana ganewa.(😂😂😂sorry guy,ta babangidan batasan wannan tsarinba,tukunna dai senan gaba) ko motsawa beyiba balle yayi tunanin tashi,saitin zuciyarsa datake ta bugawa kawai ya dafe. Tun inayi kadan_kadan harna farayi da karfi,saboda nafara gajiya ga yunwa na kwakular cikina.ga wannan bugun da zuciyata takemun, Wanda na alakantashi da na tsorone kawai,domin ni kaina nasanni da shegen tsoro tamkar farar kura,ga kuma abunda akacemun akansa.dafe kansa yayi cikin tsananin bacin ran,wanne shashashanne yake buga masa kofa haka,tamkar ze ballata,ko kuma yasa masa ciwon kai. Cikin zafin rai ya mike ya nufi kofar,jin anki dena bugun,zuciyarsa na bugawa tamkar zata fasa kirjinsa ta fito. Bude kofar yayi. _"Hasbunallu wanimal wakil, ya hayyu ya kayyumu._ t nafara karantowa a fili saboda arba danayi da wani kyakkyawan halitta,bugun zuciyatane ya tsananta,runtse idanuwana nayi atunanina gamo nayi,amma ina kara budewa nakara ganinshi,ya kuramun wasu fitinannun idanuwansa wadanda sukasa jinin jikina tsinkewa.kasa nayi da idona,ina tasbihi ga ubangijin dayayi wannan kyakkyawar halitta. Nandanan jikina yafara rawa,basket din dake hannunane ya subuce ya fadi kasa,jikake tasss! flaks din ya fashe ruwan coffee din ya fara malala akasa,se turiri yakeyi,da sauri yayi baya saboda jin ruwan coffee din akafarsa.........✍️ Meson complete Whatsapp 08166674823
*ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_
*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*
*Bismillahirrahmanirrahim*
1️⃣2️⃣
..............Tashin hankali da rudani da matsanancin tsorone suka ziyarceni a lokaci guda. "Nashiga uku, na furta a fili saboda ganin ya kone bayan zubar masa da coofee harda konasa nayi,nasan yau mommy idan ta kamani sedai wata baniba.ganin yanda ya zauna abakin gado,amma kunar tamkar ba'ajikinsaba kawai dai ya lumshe idansa.tunanin inda zan samu ruwa na farayi.dan karamin fridge me kyau na hango a dakin,da sauri na nufeshi na dakko ruwan roba me sanyi a ciki. Kafin na karasa garesa kawai naga cikin azama ya janyoni na fado saman gadon,duk da kan gado na fada amma naji jiki.saboda yanda ya warbar dani.wani matsanancin tsorene ya kara rufeni,nandanan jikina ya kama rawa.da sauri na mike daga kwancen danake,saboda tunawa da inda nake.kokarin sakkowa nayi,senaga Ashe kwalbar flaks dince data tarwatse a gabana na kusa takawa shiyasa ya janyoni. Ajiyar zuciya na sauke nadan saci kallonsa.kokarin zuba masa ruwan nayi a kafarsa,amma wata uwar harara ya jefomun. Dasauri nayi kasa da idona,cikin rauni na fara magana,kwalla harta taru a idona. "Dan Allah,kayi hakuri wlh bansan haka zata faruba kayi hakuri dan Allah.nakarasa maganar da fashewa da wani matsanancin kuka,saboda na rasa mafita,bansan hukuncin daze dauka akainaba.
Dafe kansa yayi cikin tsananin takaicin wannan yar kauyen yarinyar.tazo ta dameshi,sannan kuma ta zubar masa da cofee harda konasa.yanzu kuma tazo ta dameshi da wani banzan kukanta.ita kuwa mommy ina ta samu wannan *yar shilar yarinyar.* duk maganar dana masa kodagowa beyi ya kalleniba,balle nasakaran zemun magana,araina nace kodai kurmane,babu shakka ma kurmane, afili nace," Allah sarki ga kyau ga kudi amma Allah ya tauyeshi ta wani fannin.cikin sanyin jiki na tashi,na dakko abun share daki,domin su bada tsintsiya suke amfaniba nikuma bansan sunan abunba. Flaks din daya tarwatse na fara sharewa,a wani Dan basket me kyau na zuba,Wanda nake kyautata zaton shine na zuba sharar dakin,saboda kowanne daki na gidan da akwaisa. Hadadden toilet dinsa na nufa Wanda kyawunsa da tsaruwarsa ya zarce duk wani toilet dana gani agidan. moffer na dakko na goge coffee din daya zube Tass,na kara yayyafa ruwa na goge. Ajiyar zuciya na sauke bayan naga dakin ya koma need kamar da.satar kallonsa nayi,naga shima niyake kallo,Wanda na kasa fassara kallon kona menene.
Kiran sallar magriba da ladanin masallacin gidan ya kwalla ne yasani nufar kofa daniyyar fita,amma kamar saukar aradu naji wata daddadar murya,amma a dan kaurare take. "Ki hadomun wani" tsayawa nayi cak nibanyi gababa ni banyi bayaba,saboda matukar firgita "Ashe dama yana magana na tambayi kaina,ga zahiri nan kuma,wata zuciyar ta bani amsa. too!, shiko wannan wanne irin mutum ne,daga ganinsa zeyi murdadden hali,da muskilanci bana wasaba. Motsin bude kofar toilet yasani juyowa da sauri,harya shige toilet dinsa.da sauri nima na juya na fice daga dakin.cikin sauri_sauri, gudu_gudu na fice daga part dinnasa gaba daya. Ina kokarin shiga part din mommy yaya sadiq yana fitowa da alama masallaci zashi. "Maryam.lafiya naganki a firgice kuma kin Dade,tundazu naketa zaman jiranki zamuyi wata magana.tattaro nutsuwata nayi ina murmushin yake nace babu komai yasadiq kawaidai ina saurine zanyi sallah. "Anya kuwa maryam? Yakara tambayata yana tsareni da idanuwansa. "Dagaske yaasadiq babu komai. "Toh shikenan ni zan tafi masallaci idannadawo zamuyi magana.kai kawai na gyada masa na wuce ciki. Babu kowa a falon duk sun fice.ajiyar zuciya na sauke ina godiya ga Allah. Cikin mintuna kalilan na tafasa masa coffee din,Allah yasoma bansha wahalar ganinsaba. A wani flaks din na zuba masa. Acikin hijabina na zura,ina addu'ar kar Allah ya hadani da kowa harnaje na dawo.
Cikin ikon Allah kuwa bangamu da kowaba,se tsirarrun masu aiki.wlh na matukar gajiya,zaryarnan danayi ga yunwa jinake tamkar zanci babu,ga nauyin sallah akaina dan har an idar. Baya dakin,alamun bedawo daga masallaciba. Ajiyar zuciya na sauke,ajiye masa flkas din nayi. Se'a lokacin na samu nutsuwar karewa dakin kallo. Bansan yazan misalta muku kyawu da tsaruwar dakinba,amma fa ya bala'in haduwa. Juyawa nayi dan karyazo ya sameni,na fice daga dakin. Ina sauka falon kasa naci karo dashi wani na biye dashi abaya,nandanan zuciyata ta hau luguden bugu,tafiya nafara yi tamkar kazar da kwai ya fashewa aciki,cikin matsanancin tsoronsa. Ko kallon inda nakema beyiba yayi hayewarsa sama. Na bayannasane kawai yamun magana.gaishesa nayi muryarsa namun kamar na Santa,ko kuma nataba jin irinta,amma nakasa tuno inda nasantan.
Kawar da tunanin nayi daga raina na koma part dinmu. Seda nafara cin abinci sannan nayi sallah,abincinma kadan naci saboda yunwar taci ta cinyeni.falo na dawo na tarar da yaa sadiq,shikadai a zaune. Yana latsa wayarsa. Zama nayi a kusa dashi akan kujera,saboda yanzu nariga na saba dashi. ina maida numfashi. Kallona yayi, "anya kuwa lafiya kike maryam naga gaba daya dukkin canza. "Bakomai fa yaasadiq da gaske,gajiyace kawai Kasan yau munsha aiki. Gyada kai yayi yace. "Hakane dama maganar danakeso muyi akan karatunkine,a ina kika tsaya,akaratunki kinga zaman gidan haka babu dadi sekicigaba ko? Dasauri na dago ina kallonsa saboda jin yasosomun inda yakemun kaikayi. Cikin matukar murna nace,"yaya! Makaranta kuma,kana tunanin hajiya zata bari. Murmushi yayi yace "indai mommy ce bata da matsala,zata bari. Dafe kirjina nayi cikin matukar murna,Ashe inada rabon cigaba da karatu a duniya,Ashe idan Allah yaso zan iya cika burina na duniy...katsemun tunani sadiq yayi, "ki shirya zuwa Monday zamuje school din se'asan yanda za'ayi. ina shirin magana mommy ta fito daga dakin ta. Sallama tayi mana ta zauna akan kujera. Dubanta yaasadiq yayi. "Mommy ina mata maganane akan zanmaidata school zaman haka babu dadi. Kamar daga sama naji muryarta tana tambayata. "A wanne class ta tsaya,akaratun?. Satar kallonta nayi nace "ss 1,amma yanzu yan mate dinmu this year zasuyi candy.gyada kai kawai tayi batacemun komaiba.tana bina da kallon data saba bina dashi,Wanda bansan kona meneneba. Yaasadiq ne yace. "Babu matsala idan mukaje za'asan yanda za'ayi. Godiya na masa,hajiyama na mata na tashi na koma daki.kamar na taka rawa dan murna. "Gaskiya yaasadiq yamun komai arayuwa,idan yamaidani makaranta,yataka babbar gudunmawa arayuwata.bazan taba mantawa dashiba,na bashi babban matsayi a zuciyata.gashi dadin abun hajiya bata hanaba. Wazanwa wannan daddadan albishirdin. Saleemat ce ta fadomun arai. Allah sarki yar'uwata me kaunata,gaskiya gobe zangwada tambayar hajiya kozata barni naje unguwarmu.ko minti talatinne nayi na dawo,Allah yasa ta barni.........
Dauriya kawai yakeyi amma kafarsa tana masa zafi kadan_kadan. A falo suka yada zango shida lukman.dubansa lukman yayi yace. "Abokina wai meyake damun Kane naga gabadaya ka canza. Lumshe idansa kawai yayi bece komaiba, wani Abu yake tunani aransa,game da yarinyar dazu. Mikewa yayi ya shiga dakinsa ya dakko flaks din data kawo masa. Dakansa ya dakko musu cup,ya tsiyaya musu.shi mutum ne me tsantsani,da kyankyami.amma kwata_kwata seyaji baya kyankyamin yarinyar. Kodan bega wata kazanta a tattare da ita bane. yafison shan coffee da zafinsa,kurba daya ya masa. yaji kamar ba kalar Wanda yasabasha kullum ba, ya masa dadi sosai.haka yaita kurba yana lumshe ido se cup din kawai ya dire.hira sukayi sosai da amininsa,amma karfin hirar lukman ne yakeyi......
Danazo serving dinsu banganshiba, hamdala nayi araina danbansan da idon dazan kallesaba.gani daya dana masa wani mugun tsoronsa yakamani.ga wasu idanuwansa dayake tsare mutum dashi,duk subi su rikirkitaka.inajin suhailat tana tambayar mommy shi,mommy tace,yace zeyi dinner sa a part dinsa.nidai ina gama abunda zanyi na wuce dakina.yau kam bansamu rabon zagi daga kowaba kuma bansan daliliba......
Suhailat, suna gama dinner ta nufi part dinsa.yana zaune a bakin gado ya tasa laptop agaba,yanata latsawa. Da sallama ta shiga bedroom dinnasa,dan tasan halinsa idan batayi sallama cin ubanta zeyi.a saman lebbansa kawai ya amsa batare da dago ya kalletaba.zama tayi agefensa tana masa wani shu'umin kallo tamkar zata cinyesa.
Tana matukar son mustapha arayuwarta,ta matsu ta karasa karatu asha bikinsu,yazama mallakinta ita kadai.bata fuska tayi cikin shagwaba tace."yaya baka ganni bane.dagowa yayi ya kalleta yana sakar mata tsadadden murmushinsa me zautar da ita.ido daya yakashe mata bece mata komaiba.ya maida hankalinsa kan aikinsa.kwantar da kanta tayi a kafadarsa tana shakar daddadan kamshinsa. Ya dauki tsawon 15 minutes sannan yakashe laptop din.hira sukayi sama_sama.tana fada masa yanda tayi missing dinsa,murmushi kawai yake mata.ita kadai taketa masa surutu. Seda yace mata yau agajiye yake,yanason yayi bacci. sannan ta barshi badon tasoba ta tafi.
Missed call din kamal ta gani har 5,bin bayan kirannasa tayi amma shima bedaukaba. ajiye wayar tayi ta shige toilet tayi wanka.kayan bacci tasa,ta haye luntsumeman gadonta. tafara sana'artata wato chatting. Kullum seta raba dare sannan take bacci,banda chat da samari babu abunda takeyi, suyi ta hirar batsa.kokuma video call da kamal.kiranta kamal yayi sukasha hira,akarshe yasanar mata da zezo gobe ya gaida mum dinta.batare da tunanin komaiba ta amince masa yazo gidannasu......