Kenza eBookz

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 15

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 15

Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 15: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 15. ..........Salimat yau wanki sukesha ita da umma, tana…

3,352 words

..........Salimat yau wanki sukesha ita da umma, tana sabawa umma na tishi da dauraya. dan'autansu me suna hanifne ya shigo da gudu yana kwalawa saleemat kira,tun daga soro. "Yaya saleema,yaya saleema!" "Na'am, autan umma ya'akayine irin wannan kira haka" "yanzu naga yamaryam ansauketa a wata mota me kyau" saleemat dabatayi tunanin ganin maryam yanzuba tace, "autan umma banason karya, ina kaga yamaryam din, sedai idan wata kagani." "Allah yasaleemat yamaryam nagani itafa da wani mutum me mota" murmushi umma tayi tace, "mutanen dake zuwa gidan gwaggo ai yawa garesu, yadaiga wata yake tunanin maryam dince, danyaga kullum cikin zancenta muke" "gaskiya dai, amma banda haka maryam meze hadata da wani harda za'akawota a mota, bama na tunanin zuwan maryam unguwarnan yanzu" cewar saleemat tana mikewa domin shanya kayan da umma ta dauraye. Turo baki hanif yayi ganin sun karyatashi ya juya ze fita. Hanashi fita saleemat tayi dan yanzu idan yafita se lokacin islamiyya yayi bedawoba. Harsuka gama wankin hirar maryam sukeyi, abunda ya kara tabbatar musu ba maryam ce tazoba,jin gudar gwaggo dansunsa gwaggo bazatayiwa zuwan maryam wannan murnarba. wanka saleemat tayiwa kannenta biyu ta shiryasu suka tafi islamiyya. Cike da murna da doki nanufi gidansu saleemat bayan nadau kayan dana boye adakina. Saleemat na bakin rijiya tanajan ruwan wanka bayan tayi sallah taci abinci na shigo gidan da sallama. Da matukar mamaki saleemat ta juyo tana kallon bakin kofa tare da sakin gugan hannunta a lokaci guda tana waro idanunta waje. Fuskata dauke da murmushi nacigaba da tunkararta mamakin ganin maryam yahana saleemat ko motsi balle ta amsa sallamar data mata. Cikin ihun murna kuma, ta kwasa da gudu ta rukunkume maryam, nima rungumeta nayi ajikina cikin jindadin ganinta,atare muka sauke ajiyar zuciya ni da ita. Umma ce tafito daga daki tana fadin lafiyarki kuwa salima kikasaki guda haka, wannan aise kifadarwada mutum gaba ga Ku.....maganar umma ce ta tsaya ganin salimat rungume da wata. Sakin maryam salimat tayi cikin tsananin murna da farincikinganin maryam mara misaltuwa tace, "umma she dagaske hanif yake maryam tazo" kafin umma tayi magana nanufeta da gudu na rungumeta itama ina fadin, "ummata nayi kewarki sosai" umma dake cike da dinbun mamaki da farincikin ganin maryam tace, "maryama dagaske kece agidannamu yau" "nice umma" nafadi haka ina sakinta. "Maraba lale marhabun diyata, kai amma naji dadin ganinki,shigo, shigo, shigo" umma ta kama hannuna muka shiga daki. saleemat dake tabun maryam da kallo ganin cikin kwanaki kadan ta sauya tabi bayansu zuwa dakin. Farin cikin datake ciki yau baze misaltuba naganin kawa,aminiya,kuma yar'uwarta da kulkum take kwana take tashi da ita aranta. Gaishe da umma maryam tayi tare da dan taba hirar yaushe gamo, salimat dai tatasa maryam agaba kawai tana kallonta. Fita umma tayi da kanta domin takawowa maryam abinci da ruwa. Hararar salimat nayi bayan umma tafita nace, "wannan kallonfa, kintasani agaba ko kewatama bakiyiba ko" matsowa kusa da maryam suhailat tayi ta rungumuta a jikinta tace, "haba tawan, aike ko fada miki akayi banyi kewarkiba nasan zaki karyata, naga kinkaramun wani kyaune da fresh ga wani daddadan kamshi dake tashi ajikinki, kuma ta ummanki kike bataniba,shiyasa namiki shiru" "hmmm,ainazo zaki fara, ya kwana 2 ya makaranta?" "Alhamdulillah muna shirin farama waec" "masha Allah,Allah ya taimaka yabada sa'a, kinsan nima nakoma school da islamiyya" cikin mamaki salimat take duban maryam,amma batace komaiba. "Dagaske kawata,nakoma makaranta,nima" nafadi haka ina murmushi. rukunkumeni salimat tayi cikin tsananin murna tana murmushi tace, "wayyo dadi, amma gaskiya maryam naji dadin wannan labarin, amma gaskiya mutanen gidan suna da kirki dasuka saki a school" daidainan umma ta dawo da ruwa da abinci ahannunta harda lemo, dasauri muka tashi muka karbeta ina mata sannu tare da godiya. Cikin tsananin farin ciki salimat ta mata bayanin na koma makaranta, tayani murna umma tayi sosai tare damun addu'ar samun nasara. Abinci umma tace na sakko naci, jallop din taliyace da zafinta taji kayan hadi daidai misali, wanka salimat ta shiga kafin nagama cin abincin, umma kuwa tarasa inda zatasaka maryam don farincikin ganinta fess,batayi zaton zasu ganta hakaba, ga kuma daddadan labarin ta koma karatu, umma setaji wata nutsuwa hankalinta ya kwanta akan aikatau din maryam. Bayan nagama cin abincine umma ta dubeni tace, "maryama ya gidan aikinnaki babu dai wata matsala ko?" Ajiyar zuciya nasauke nace. "Gashinandai umma kinsan masu kudi, inadai dan fuskantar matsala daga wasu yayan gidan,amma matar gidankam babu wata matsala, bata shiga sabgata idan ba aiki zanmataba. Sauran ma'aikatan gidanma muna zaune lafiya, kuma kome zasuci agidan nima zan iyaci, ba'amun iyaka da abinci ko sha kowanne irine,megidan dabayananma danaje gidan yayi tafiya, sati biyu dasuka wuce yadawo kuma shima gaskiyadai bashi da matsala................

Labarin komai na gidan maryam tabawa umma, harda kirkin da sadiq da baaba talatu suke mata da zuwan su aunty, labarin fyaden da'akewa yan aikin gidan kawai bata fadawa ummaba dan kar hankalinta yatashi,tadaice tatayata da addu'a akan Allah yakareta daga duk wani sharri nagidan. Numfashi umma tasauke tace, "Dama ba duka hali yazama dayaba, " Allah yasakawa wannan yaro dayake dawainiya dake da alkhairi, Allah yabiyasa da aljannah, sukuma sauran yaran gidan sekiyi takatsantsan da bacin ransu, kikuma kama kanki tunda kince yaran gidan duk samarine. kikara hakuri maryam komai lokacine, kuma komai me wucewane kinji" "insha Allah umma nagode sosai" salimat ce ta dawo dakin umma kuma tafita domin karasa aikin gida. Labarin gidan alh. Menasara nabawa maryam atakaice itama, addu'a taitaiwa yaya sadiq itama dakuma kara bani baki. Sallar la'asar mukayi sannan mukacigaba da hirarmu cikin jindadin ganin juna dakuma kewa. Farincikin kasancewa da salimat ayau yaragemun tunanin mustapha araina, amma duk da haka yana fadomun arai lokaci zuwa lokaci.

Muna cikin hira naga salimat tayi shiru tana kallona. cikin mamakinta nace, "Menene naga kintsaya kina kallona?" Numfashi salimat ta sauke tace, kamar akwai abunda kedamunki Wanda kike kokarin boyemun amma fuskarki tagaza boyewa seda ta nuna" nuna kaina nayi da hannu nace, "nikuma gaskiya babu abunda yake damuna" kama hannun maryam salimat tayi tace, "bekamata ayanda Muke dake kiboyemun wani abu dake damunkiba, muna zaunannen senaga kinyi shiru harda lumshe ido, kina sauke numfashi, tabbas hakan alamace ta akwai abunda yake damunki acikin ranki" "gaskiya babu komai, sedai ko tunanin exam dazamu fara next week" "hmmm, maryam kenan maganar dakikeyi yanzu tana kara fallasa abunda ke ranki,kinsan maryam nasanki nasan duk wani moment dinki, kifadamun abunda ke damunki kona samu kwanciyar hankali, domin kuwa tabbas idan kika tafi ahaka, zaki barni cikin damuwane, kifadamun koda wata matsala dakike fuskanta agidan aikin,nikuma zanbaki shawarar dazata amfaneki tare da tayaki da addu'a da yardar Allah" shiru nayi ina sauke numfashi, tabbas salimat tayi gaskiya, aduk lokacin da mustapha yafadomun araine nake shiga yanayin data fada, kuma salimat bata cancanci na boye mata komai na rayuwataba,kuma dama ina son tambaya akan abunda nakeji akan mustapha. Wata doguwar ajiyar zuciya nasauke ina duban salimat nace, "nima bansan meke damunaba kawata, amma na tsinci kaina acikin wani irin yanayi a kwanakin dasuka shude, zuciyata ta kasance kullum cikin tunanin wani bawan Allah take, dakuma kwadayin ganinsa akodayaushe, aduk lokacin dana gansa inajin zuciyata na wata irin bugawa tare da samun nutsuwa araina, inajin dazan wuni ina kallonsa bazan gajiba, bansan yanda zan kwatanta miki yanda nake jinsa arainaba, ada nayi tunanin tsoronsa danakeji seda daga baya kuma naga abun yawuce akirashi da tsoro" "waye shi?" Salimat ta jehomun wannan tambayar. Labarin musty na bata atakaice. Shiru salimat tayi, domin tagane maryam ta kamo da son mustapha ne, batare data saniba, amma bazata fada mataba dankar tatada mata da hankali, zata tayata dai da addu'a Allah yayaye mata, domin abunda baze yiyubane wannan, soyayyar maryam da danmekudi irin alh. menasara, bata mata fatan hakan koda nangaba, domin ayanda maryam tabata labarin yaran gidan zasu zangwametane kawai su kyareta, koda ta auresa bazataji dadin danginsaba. to idanma bahakaba shi Wanda takeso din yamasan tanayi, inma yasan tanayi zesotane,mutumin da tasan ko kallo maryam bata ishesaba. Addu'a salimat tacewa maryam tadage da ita, tare kuma da nisanta kanta da haduwarsu da mustapha zataji saukin abun aranta,kuma dantariga tasawa ranta tsoronsane yiyasa takejin hakan akansa. Godiya na mata,cikin yarda da abunda tacemun batare da tunanin komaiba. Hirarmu muka cigaba dayi......

Se wajen magriba nabar gidansu salimat,bayan nabata kayan dana kawo mata taitamun godiya kuwa ita da umma, har gidan gwaggo salimat ta rakani,bayan umma ta karamun nasiha akan na tsare mutuncina. Koda na koma gida, gwaggo batanan ta fita, dama nayi mamakin yanda akayi har nayi wannan dadewar gwaggo bataje ta kiraniba, ashe batananne,amma da alamun ba nisa tayiba dannaga janyo kofar gidan kawai tayi bata rufe da kwadoba. Hajiya gwaggo anatafi kai kudi gidan adashi. Nanma seda muka kara wata sabuwar hirar sannan tatafi. se ana sallar magriba gwaggo ta dawo, time din data shigoma ni sallah nakeyi. "Sannu da zuwa gwaggo" nafada bayan na idar da sallah. "Uhm, aikece za'aiwa sannu kinje gidan uwartaki kinyi zamanki tana doraki akan hudubar banza ko" zanyi magana gwaggo ta hanani. "Rufemun baki ni, bansan jin komai daga gareki, gobe inkika zo base nakara barinki zuwaba, sannan abu nagaba danakeson fada miki, karki kara zuwamun batare da kudi masu yawa ko kayan masarufiba" "to ni inna ina zansamu kudi balle harna siyo miki wani abu, kudin aikatau dinma ko ganinsa banba, kawaidai matar gidan tacemun tabada ankawo miki lokacin danayi wata guda agidan" cikin fada gwaggo tace, "kajimun sakarar yarinya se'anbaki zaki kawomun, fakar idonta zakiyi ki dakko, kayanma kidinga sata da kadan_kadan kina boyewa idan yataru seki sato hanya kikawomun" dasauri na kalli gwaggo cikin matukar mamakinta ina maimaita Kalmar _Hasbunallahuwani'imalwakil_ araina, narasa hali nasan abun duniya irin na gwaggo,yanzu ita danake kallo amatsayin uwa ita take umartata danayi sata. Cikin takaici nace, "gwaggo satafa kikace, idan wataran aka kamanifa,koba hakabama gaskiya bazan iya sataba, sedai na dinga tara miki kudin makarantata" "to yar bakin ciki, me shegen bakin hali, kar Allah yasa ki iya din" bala'i gwaggo tashigamun tana zagida da tsinemun, nidai shiru na mata bakin ciki cunkushe azuciyata, har hawayen bakin ciki seda nayi. Sallamar wani yaroce tasa nasamu salamar bala'innata. Yaya sadiq ne yazo zamu wuce gida, kafin nayi wani yunkuri gwaggo harta fice gurinsa. Jakata nadauka nafito nima. Gwaggo nata masa banbadancinta a son zuciya irinnata yakara bata kudi, sadiq ganin maryam tafito yayiwa gwaggo sallama ya nufi mota. Tsayawa nayi inayiwa gwaggo sallama, akokarina nasan takoma gida, dan idan tana tsaye agurin bazata barni nakoma nayiwa su umma sallamaba, kuma nasan baba yadawo yanzu inason shima nagaisheshi. Gwaggo kuwa tasan nufin maryam shiyasa taki komawa gida, wai ita kar sadiq yace zegaida umma balle yabata wani abun. Seda taga nashiga mota haryakunnan munfara tafiya sannan ta koma ciki,tana cewa sadiq setazo gidan. Nikuma ina ganin haka nace masa nayi mantuwa banwa umma sallamaba, kashe motar yayi yace muje shima seya gaidata. Abakin kofar gidan ya tsaya nikuma nashiga, gaisawa mukayi da baba nayiwa umma da salimat sallama nakuma sanar mata da sakon sadiq, hijabi umma tasaka ta leko soro suka gaisa cikin girmamawa, godiya sosai umma ta masa akan dawainiyar dayakeyi akan maryam. Kudi sadiq yadakko yabawa umma, amma umma Sam taki karba karshema tashi tayi ta koma ciki. Saleemat data rakoni yabawa kudin, itama kin karba tayi, dakyardai ta karba ahakanma seda nasaka baki, sallama mukayi cike da kewa da begen juna muka rabu.

Muna cikin tafiyane, yaya sadiq yadubeni yace, "wato zuwa kikayi kinata yayatani na miki abu ko?" Murmushi nayi nace, "a'a yaya kawaifa cemata nayi kamaidani makaranta,shine ta maka godiya" "Shikenan" yace atakaice.dubansa nayi dakyau nace, "yaya sadiq naga kamar wani abu nadamunka tundazu dazamu tafi, da'alamunma bakaje bikinba?" Numfashi sadiq yasauke yace, "banajin dadi ne maryam kuma gobe zanyi tafiya, daddy ya aikeni Abuja." "ayya yayana sannu mekedamunka" nafadi haka cikin tausayawa. _"cutar sonki"_ yafadi hakan aransa,amma a fili seyace, "ciwon Kaine da kuma gajiya" "sannu, Allah yakara sauki, kuma ahaka zakayi tafiyar,kadaga mana zuwa wani lolacin" girgiza kai yayi alamar a'a yace, "baze yiyuba abunda zanyi yana da mahimmanci." "Tom shikenan yaya, Allah yakiyaye hanya yakuma kara sauki" "ameen" yafada cikin sanyin murna. Shiru sukayi na wasu mintuna kowa da tunanin dayakeyi aransa, ni ina tunanin halin dazan shiga idan baya gidan, domin shine garkuwata,acikin gidan. Shikuma sadiq yana tunanin tayanda zefadawa maryam yana sonta. Candai na katse shirunnamu dacewa, "kuma kwana nawa zakayi a abujan?" "Zakiyi kewatane idannatafi" sadiq yatambayeta yana kallonta. Batare da tunanin komaiba, nace, "sosaima yaya" wani murmushi yayi yace, "kozaki binine mu tafi tare" "ai mommy bazata bariba" "Injiwa zata bari mana" "tom shikenan zanbika" nafadi haka ina murmushi. Daidai nan muka karaso gida. Seda yayi parking sannan yadubeni yace, "tun yamma aliya take kirana nabaki waya zaku gaisa, kishiga ciki kihuta kiyi sallah kici abinci, zanzo muyi magana,sekuma nakira miki aliyan" "tom yaya nagode sosai, se'anjiman" nafadi haka ina bude motar na fice. Dai dai lokacin da maryam tafito haidar yakaraso parking space din, zedau mota ze fita. Tsayawa yayi yana kallon maryam cike da mamaki, shida farkoma beganetaba sedaga baya,takara masa kyau. "dama haka yarinyarnan take da kyawun sura, shiyasa kullum cikin zunbula hijabi take, gatadai yar karama amma akwai kayan aiki, lalle zeso ya more wannan kyakkyawan jikinnata" yafadi haka aransa yana lasar lips dinsa..........✍️

*BY* *zeey kumurya*

*ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_

*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*

*Bismillahirrahmanirrahim*

2️⃣4️⃣

.........Tunda nafito daga motar na hango haidar,sanin danayi bawani shiri mukeba sena dauke kaina ina kokarin wucewa batare dana masa maganaba, kamar daga sama naji muryarsa cikin tattausan lafazi yana cewa. "Yanmata babu magana" cak na tsaya cike da mamakinsa da wanine yacemun koda a mafarki haidar zemun magana irin haka zan karyatashi domin tsakanina dashi magana cikin tsawa da masiface take hadamu. Murmushi na kirkiro nace, "ayya yahaidar bangankaba ina wuni" "lafiya kalau" ya amsa yana bina da wani shu'umin kallo, nidai daga haka bankara maganaba nayi gaba danse naji abun wani banbarakwai. Shiko haidar binta yayi da kallo yana ayyana mummunan kudirinsa akanta harta kulewa ganinsa. Ahankali nake tafiya ina zancen zuci harna karasa part dinmu, su mommy basu dawoba, me'aikin danake gani kullum tana zaune a falo tana kallo, gaisawa mukayi na wuce sama. Jakata na ajiye a daki nashiga kitchen nadibo abinci domin wata yunwa nakeji, a falo na zauna naci bayan na kunna kallo. Inagama cin abincin na shige daki, domin yin sallar isha'i. Bansan sanda su mommy suka dawoba, seda nagama duk abunda zanyi adaki na fito falo naga mommy ta fito daga kitchen. "Sannu da dawowa mommy" "yawwa maryam yakika baro mutan gidan" "lafiya kalu sunata agaisheku" "toh muna amsawa, yawwa maryam shiga kitchen zakiga nahada wa alh, abinci bari na dakko mayafi kibini part dinshi, dashi" cikin ladabi na amsa mata sannan na shige kitchen din na dakko, seda nadan jira sannan mommy tafito muka tafi. Daddy yana zaune a falonsa na tsakiya,yana karatun jarida yana kurbar ruwan shayi muka shigo falon. Wani sassanyan kamshine yadaki hancina, seyau nasamu damar bawa idona abinci a part din daddy. Gaskiya part din yahadu iya haduwa, danhar yafi na mommy kyau, amma nakasa gane wanne yafi kyau shida na mustapha, kawaidai abunda nagane yafi na mustapha girma. Masha Allah gaskiya kudi yana inda yake, komai najin dadin rayuwa akwai a part din daddy, duk da iya faluka biyu nagani a part din. Har kan hadadden dinning dinsa naje na'ajiye abincin, sannan na dawo gabansa na durkusa na gaishe sa. Amsamun yayi kamar kodayaushe cikin fara'arsa. Mikewa nayi namusu sallama nafice. Ina fita na hango yaya mustapha yana tahowa,ya kara waya a kunnensa,alamun waya yakeyi. Nandanan zuciyata tahau aikinta a duk lokacin data gansa, wata boyayyiyar ajiyar zuciya nasauke ina satar kallonsa ta gefen ido. Yayi kyau sosai yau shigar manyan kaya yayi, kansa harda hula. fitinanne kamshinsa yacikamun hanci,tun kafin yakaraso. Cikin takunsa nakasaita da daukar hankali yake tafiya. Wata nutsuwace naji ta lullubeni, dana gansa se ajiyar zuciya nake saukewa akai akai. Ahankali nake tafiya har mukayi clash, dakyar na harhado kalmomi abakina nace, "ina yini" ina dan rissinawa batare daya kalleniba yadagamun hannu ya wuce abinsa, yabarni da mayen kamshinsa. Lumshe idona nayi wani murmushin daban shirya masaba ya subcemun. Yanayin dana tsinci kaina na farin ciki baze misaltuba a wannan lokacin. Tunaninsa manne acikin zuciyata nakoma part dinmu, a falo na tarar da yaya sadiq yana kallon news shikadai azaune.

Sallama namasa batare daya juyoba ya amsamun zama nayi a kujerar dake pacing dinsa nace, "yaya ya kannaka" "yayisauki sosai maryamaaaa" yaja karshen sunan yana kallonta. Nima shiru nayi ina kallonsa gabadaya duk ya canza yayi wani iri,kamar baya cikin nutsuwarsa, inajindai ko tafiyar dazeyice bayaso dole aka masa.ajiyar zuciya sadiq yasauke tare da dauke kansa daga kallon maryam, wayarsa yazaro daga aljihu ya lalubu number aliya ya danna mata kira. Alama yayimun da hannu alamun nazo na karba, tasowa nayi ahankali na karba na koma mazaunina tare da kara wayar akunnena. "Hello, yasadiq tadawo?" Murmushi nayi me sauti nace, "ehh nadawo" daga daya bangaren aliya cikin farin ciki tace, "mairota, ykk ya gida ya school ya samari?" "Komai da kowa lafiya kalau, samari kuma seku manya ai" nabata amsa fuskata dauke da murmushi har lokacin. "Hmmm zama kifadi gaskiya, nasan yanzu kinyi baby's irin ten dinnan a school idannazo zaki bani labarine" "nikuma sekace wata ke,dazanyi samari har 10, ya aunty?" Nakawar da wancan zancen da tambayar aunty. Aunty tananan klu, dafazamuzo muyiwa daddy sannu da zuwa to kuma munfara exam ne, sedai wani lokacin" "ohk, Allah ya kaimu, nifa ince nayi mamaki dabaku zoba naga anata zuwa gaishesa" "zamuzo nan kusa insha Allah" "Allah yakawoku lafiya" "ameen maryam, se anjima, zanyi karatune dama kira nayi naji ykk" "toh aliya nagode sosai kigaidamun da aunty pls" "zataji insha Allah, nima kigaidamun da nakarfen kafin nazo mugaisa" "Allah yashiryeki" nafadi haka ina dariya tare da kashe wayar. Mikawa yaya sadiq wayar nayi, daya tsaya kawai yana kallon maryam, ita batamasan yanayiba. Shiko ya kura mata ido yanda take magana cikin siririyar muryarta bakaramin kyau take kara masaba. Hira mukadanyi da yaya sadiq kadan akan makaranta, sannan mukayi sallama ya tafi, bayan yayi_yayi nafada masa menakeso yakawomun a tsaraba naki. Yauma a part din daddy zasuyi dinner, secan anjima zasu dawo. dakina nakoma nacigaba da al'amurana.

A part din daddy kuwa, bayan maryam ta fita daddy ya juyo yana kallon mommy yace, "wai ko atika a ina kika samo wannan yarinyar?" "Meyafaru dear kake tambaya?" "Naganta batayi kalar yaran da'ake kawowa aikatau bane, kuma ni yanayin kallonta yanamun kamar nasan me irin kallon, kuma namijine" shiru mommy tayi cikin faduwar gaba, tabbas itama tadade tana kallon hakan agurin maryam din tun randa tafara ganinta, kuma ita tagane me irin kallon maryam din,amma bazata tunawa daddy ba danbataso ya tuna, yanzu seya ballo mata wani ruwan. Kuma abunda yake bawa mommy mamaki, kwata_kwata maryam bata kama da Wanda kallonnasu yake daya, amma yanda take dago idonta tana dan lumsheshi shima haka yake, musammanma dayana yaro, idan maryam tayi kallon se mommy taga tamkar shine dayana yaro. Numfashi ta sauke tace, "haba dear har akwai wani kallo nadaban da wani yakeyi,kallodai ai duk kallone, kawai kaikake ganin haka" kafin daddy yabawa mommy amsar maganarta mustapha ya shigo falon da sallama. Cikin tsantsar kulawa da kauna. suka amsa masa, zama yayi atsakiyarsu yana musu sannu da gida. Hular kansa yacire ya ajiye, dukta takura masa ga gajiya sosai ajikinsa. Tsokanarsa daddy yahauyi ganin yanda yaketa faman yamutsa fuska. Mommy kuwa kwantar dakansa tayi akan kafadarta tare da shafa lallausar sumar kansa. Cikin tattausan lafazi tace, "son ya taro da gajiyar biki" lumshe idonsa kawai yayi tare da daga mata kai alamar amsawa. Wayarsa dake hannunsa aketa kira, kindagawa yayi danyasan abokansane suke Neman caza masa kai, sunga basu gansaba. dan yanzuma sulalowa yayi ya gudo, da'ana zancen kai amarya, shikam baze iya wani kai amaryaba, sabgar mata ai ciwon kai zasu kara masa akan Wanda yake damunsa. Fahimtar da mommy tayi da gajiya atattareshi seta mike ta dakko masa ruwa da lemo me sanyi ta bashi yasha. Yakwaji sanyi aransa dandama da kishirwar atattare dashi. Mommy dakanta tayi masa tausa, tanayi tana jera masa sannu. Daddy kuwa nagefe yana kallonsu cike da ban sha'awa da burgewa, yanajin dadin yanda mommy take kula da mustapha yanda yakamata..........

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull