Kenza eBookz

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 16

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 16

Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 16: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 16. washegari yaya sadiq asubanci yayi yatafi,hakan yasa bamu…

3,363 words

washegari yaya sadiq asubanci yayi yatafi,hakan yasa bamu haduba. Drivern dayake dakkoni shine yakaini school yau. Duk senaji kewar yaya sadiq ta lullubeni, dama shi sabo haka yake. Yau laraba kwanan yaya sadiq biyu da tafiya, gaskiya nayi kewarshi sosai gidan duk badadi. A kwana biyunnan haidar yasakarmun fuska sosai, wani lokacinma idan muna zaune yayita jana da hira. Abunna matukar bani mamaki,haidar daya tsaneni sosai yanzu kuma shikemun haka. Bankawo komai arainaba na canzamun din dayayi. Suhailat ce dai jiya i yau, tamkarma kara mata tsanata akeyi. Yanzu kullum bayan magriba senaje gaida daddy har part dinsa bisa umarnin mommy, anannema nake ganin mustapha nake samun nutsuwa. Nadage ina karatu sosai saboda banaso nabawa yaya sadiq kunya. Yau tunda nadawo daga school naketa faman solving di maths da zee ta kara koyamun, danyanzu yafi bani wahala akan duka sauran subjects din da mukeyi. Alhamdulillah yanzu ina fuskantar turanci ba lefi, dan malamin lesson dina yadagemun sosai, kuma a school kwata_kwata ba'a Hausa se turanci shiyasa. Satina na uku kenan a school din, amma munyi text yakai 7. Gobe zamuyi ta maths din shiyasa na dukufa akanshi.

Bayan magriba ina zaune a falo ina kallo nikadaice duk suna part din daddy, tunda yadawo ba kullum suke zaman part dinba. Nima banjima da dawowa daga gaisheshiba. Jinayi kawai ansa hannu an rufemun ido, a matukar tsorace nafara kokarin banbare hannun, amma na kasa. Sedayaga dama dankansa sannan ya sakarmun idon yana dariya. Dasauri na juyo ina kallonsa, haidar ne. Ajiyar zuciya nasauke na juyar dakaina bance masa komaiba. Zagayowa yayi yazauna akusa dani yana fadin, "matsoraciya jibi yadda duk kikabi kika wani firgice se sauke numfashi kike" nibesanma haushi najiba, dominni tsoratanin dayayi bedameniba kamar tabamun fuska dayayi, duk senaji raina ya baci. Danne bacin raina nayi nace. "Ai dole In tsorata yaya haidar, bansan da shigowarkabafa kawai jinka nayi." "Tom shikenan Allah yabaki hakuri yar kanwata" yafadi haka yana hade hannunsa guri daya alamar roko.🙏gyada masa kai kawai nayi, namaida hankalina akan kallon danakeyi. Jana ya shigayi da hira, nikuma ina kakkaucewa danse naji zuciyata bataso kasancewa dashiba. Ko fahimtar hakan yayi daga baya daya gaji dan kansa yatashi ya tafi. Nina matsuma gobe tayi yaya sadiq yadawo. Yau a part dinmu sukayi dinner, amma banda daddy da mustapha. A gurin serving dinnasuma haidar se magana yakemun ina basarwa,harda cewa nima nazauna naci abincin tare dasu mana nace masa aini nakoshi. Dasuka gamama ina wanke_wanke a kitchen seda yakara shigowa ya takuramun. Besan banason wannan kusancinnamu dashiba, dan haka kawai naji zuciyata bata yarda da wannan canjinnasaba.

Misalin karfe biyu na dare na tashi domin yin sallar nafila, ina toilet ina alwala naji kamar motsi adakina, dif nayi domin natabbatarwa. amma se naji shiru,cikin tsananin tsorata naja kafata ina sanda nafito zuciyata na dukan uku_uku. Dama kofar toilet din abude nabarta saboda bankunnan hasken dakinba, na toilet dinne kawai a kunne. Cikin dan hasken dake dakin, naga kamar gilmawar mutum yafita tare da jan kofa. Jikina har rawa yakeyi saboda tsoro, dama gani sarkin tsoron. hannuna na karkarwa na kunnan light din dakin haske ya gauraye. Bin dakin nahauyi da kallo cikin faduwar gaba, tabbas anshigomun daki, saboda wani irin kamshin turare Mara dadi danaji yana tashi adakin,bugun zuciyatane ya karu,saboda razani. _la'ilaha'illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin_ nashiga maimaitawa araina ina tunkarar kofar dakin, inajan kofar kuwa ta bude, alamun babu key ajikinta,kuma ni nasan akulle nabarta. Wani matsanancin tsorone ya kara lullubeni addu'a nashiga karantowa a fili, jinake kamar na leka falon naga kowaye amma kuma tsananin tsoro yahanani lekawar..ahankali namaida kofar na rufe tare dasanya mata key. Zama nayi abakin gado hawaye na zuba daga idona, abun yazo kaina kenan. afili na fara magana. *ya Allah kakareni daga dukkan me nufina da sharri , ya Allah kada kabawa koma waye damar ketamun haddi, Allah narokeka, Allah kakawomun dauki, acikin wannan al'amari* kuka nafashe dashi meban tausayi, bantaba tsorata da abunda baaba talatu tacemun irinna yauba, takurewa nayi akan gado, tsoro da razani duk sun baibayeni, gani nakeyi tamkar mutumin zedawo. gashi bani dame taimakona a wannan Daren, idan mutumin dayawo, mommy yanzu a part din daddy take kwana daga ni se suhailat asaman yanzu. Kalaman innata data taba fadamun sune suka dawomun arai. _*maryam, wani baya karewa wani abunda Allah yakaddara seya samesa, duk abunda yasameki na kunci kona damuwa, kada kinemi taimakon kowa se Allah, shikadaine ze iya kareki daga sharrin me sharri, kisawa ranki Allah yana tare dake aduk inda kike, kuma shine zekareki akan komai, kikasance memikawa ALLAH kukanki daneman taimakonsa akodayaushe.*_ wasu hawaye masu dumine suka shiga kwaranyomun saboda tunawa da innata. nadade a dunkule nikadai ina faman rera kuka da addu'a araina. Dakyardai na rarrashi zuciyata na mike nakoma toilet nasake dauro alwala nafito nasaka hijabina na tada sallah domin kaiwa Allah kukana. har ketowar alfijir ina gaban ubangiji,seda aka kira sallah natsagaita. zama nayi tare da rafka uban tagumi ina tunane_tunane, tunanin hanyar kawai dazanbar gidannan nakeyi,tunda ankawomun hari nafarko gobema za'a iya kawomun na biyu gwara kawai nabar gidan na huta. sallar da'aka tayarne yasani mikewa nabi limamamin nima. Bayan an idar na dakko alkur'ani me girma nashiga karantawa, izu biyu nayi nadakko addu'ar da aunty tabani itama na karanta. Seda gari yayi haske tangararau sannan na mike daga kan dadduma nafita nafara ayyukana. Jikina asanyaye yau nakeyin komai tamkar wacca kwai yafashewa aciki, kuku naganina yafara tambayata meke damuna ko banda lafiyane, babu komai kawai nace masa,danni yau maganaba banaso nikadai nasan halin da zuciyata take ciki nafargabar zaman gidannan.

Ina gama ayyukana nakoma daki nayi wanka nashirya cikin uniform dina. Kotunanin abinci banba nazumbula hijabina nafito domin tafiya school. Mommy nagani a falo taci kwalliya da'alama turakar miji zata koma. Gaisheta nayi ta'amsa tana bina da kallonta, yaukam ta kuramun ido sosai. Harna fara tafiya ta tsaidani da fadin. "Maryam lafiya kike kuwa,naganki haka?" "Lafiya kalau mommy, kainane kedanmun ciwo" nabata amsa kwalla nataruwa a idona ta tausayin kaina. "Ayya sannu, Allah yasawwake dafatandai kinsha magani ko?" Kaina gyada mata alamar eh. Sannu ta karamun nikuma nafice. Kodanaje makarantarma su zee da salma setambayata suke lafiya nake, nace musu marata kemun ciwo kawai dansu barni. Sannu sukamun dafatan samun sauki. Dakyar na iya zana text din damukayi, danni yau komai ya kuncemun tsoro da fargabane kawai acikin raina. Gashi yau bamu tafi gida da wuriba saboda munyi practical din biology. Seda 4 tawucema nadawo gida. Abun mamaki ina shiga falo naga yaya sadiq zaune, dama ina school Inata addu'ar Allah yasa yadawo. Jinayi gabadaya Rabin damuwata tatafi, wani farincikine ya lullubeni kamar naje narungumesa haka naji. Murnar danakeyi taganinsa kasa boyuwa tayi, zama nayi ina jera masa sannu da zuwa da tambayarsa ya hanya. Shikuwa sadiq ganin yanda maryam tayi murnar ganinsa alamun tayi kewarsa seyaji tamkar anmasa albishir da aljannah, domin hakan nanuni da cewa itama tafara damuwa dashi. hira muka dan taba yana tambayata ya karatu da komai da komai nace masa komai lafiya. daga karshe yacewa maryam taje ta kimtsa tafito tasamesa afalo. saboda sadiq yakudiri niyyar yau zesanar da maryam abunda ke ransa,koyahuta.

Wanka nayi tare dayin sallah sannan naci abinci, dan yunwa tafara nukurkusata. Kamar yadda yaya sadiq yace nasamesa afalo anan naje nasamesa. Shikadaine a falon ya kwantar da jikinsa ajikin kujera idanunsa a lumshe. Zama nayi agefensa inafadin "sannu yaya sadiq ya gajiyar" bude idonsa yayi yasaukesu akan maryam sannan yace, "yawwa maryama be babban suna, kema sannunki, yakaratunne" "alhamdulillah yaya" gyadamun kai yayi tare da janyo ledar dake gefensa ya mikomun yana fadin ga tsarabarki tunda kinki fadamun abunda kikeso" cikin jin kunya nace, "yaya sadiq mekuma kasiyomun kaibaka gajiya dan Allah dayimun hidima, abun yayi yawa wl.... "Shiiiiii" yaya sadiq yakatseni yana Dora danyatsansa abaki yace, "babu wata hidima maryam anan, kuma banason wata doguwar godiya rike kawai" karbar ledar nayi tare da fadin ''nagode" hararata yayi saboda godiyar dana masa, murmusawa nayi ina kallonsa. Gabadaya yarame yayi wani iri, kamar bashiba. Kasa daurewa nayi nace, "yaya lafiya kuwa naganka wani iri kokayi cutane a tafiyar dakayi" girgizamun kai yayi alamun a'a tare da fadin, "wani abu ke damuna maryam, gabadaya yahanani sukuni dajin dadin rayuwa" "subhanallah wanne irin abune wannan yaya sadiq?" natambayeshi cikin yanayin damuwa. "Idan kinjima bazaki iya magancemunba kitayi da addu'a kawai" marairaicewa nayi nace, "karkace haka yaya, kafadamun mana koda da shawarace se'inbaka da kuma addu'ar" harga Allah nadamu da damuwar yaya sadiq,senaji duk babu dadi dayace wani abu nadamunsa. Sadiq kuwa juya abunda zecewa maryam yakeyi aransa, besan yazataji abunba kokuma ta daukesa. Ganin yayi shiru yana tunani sena cemasa. "Shikenan yaya, Allah yayayemaka koma meke damunka tunda bazaka fadamunba." Kallona yajuyo yayi nawasu sakanni,kamar yadda nima nake kallonsa, zuciyata nadan harbawa. wani gwauran numfashi yasauke. Ya dauke kansa daga kallona yace, *MARYAM! CIWON SONKI KEDAMUNA!!*..........✍️

Meson complete Whatsapp 08166674823

*ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_

*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*

*FARIN JINI WRITERS ASSO.....*📚

~*Free novel*~

*Bismillahirrahmanirrahim*

2️⃣5️⃣

*DEDICATED TO👇* *MEERAH* *NANA* *Xeey* *abjamila824* *Jidderh m Ahmad* *Maman jani* *pheenar_Abdallah* *Aseeyah*

*Comments dunku nasani nishadi masoyan asali,nagode sosai Allah yabar kauna*❤️🥰

...........Cikin tsananin dimuwa dajin kalaman yaya sadiq nake kallonsa baki bude cikin rashin abunyi, tabbas ayanda yayi maganar babu alamar wasa acikinta,balle ince wasa yakemun. Wani yawu na hadiye cikin rawar murya nace, "yaya sadiq kasan me kake fada kuwa, kokamanta maryam ce agabanka yar aikin gidanku?" Juyowa yayi yana kallona da idanunsa da suka sauya launi,cikin wata kasalalliyar murya yace, "nasani maryam, nasan kece agabana,kuma gaskiyar abunda ke zuciyata nake fadamiki *INA TSANANIN SONKI DA KAUNARKI MARYAM*" yakarasa zancen yana taune lips dinsa gami da runtse idonsa. Tashin hankali Wanda ba'asamasa rana, wacce irin fitina yaya sadiq yakeson kunnomun agidansu dazece yana sona. Wani gwauron numfashi nasauke zuciyata na dokawa nace, "yaya sadiq!" bude idonsa yayi yazubamun amma bece komaiba. Kasa nayi dakaina narasama mezance masa, ganin abunnake tamkar mafarki nakeyi yauni yaya sadiq yace yana sona, *"SO FA!"* girgiza kaina nahauyi ahankali nafara magana batare dana dago kainaba. "Yaya sadiq wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa babu........ "Look maryam banason jin wadannan kalamanki, please and please maryam, ki amincewa soyayyata, zuciyata nagab da bugawa. idan har kikaki amsar soyyata zanshiga mummunan hali. Maryam na miki alkawarin bazaki kuka daniba insha Allah, zanzame miki bangon rayuwa, zanshayar dake zallar kauna da tsantasar soyayya azamanmu" dagowa nayi na kallesa da sauri yanda yaketa rokona,gabadaya ya marairaice duk yabi yabani tausayi. Kaina gabadaya ya kulle narasa abunyi, wannan shine karon farko arayuwata da wani danamiji yace yana sona, kuma mutum me kima da daraja a idanuna. Kawar dakaina nayi daga kallonsa nace, "dole nafadi abunda bakasan ji yaya sadiq, nifa mutum ce talaka ba yarkowaba, kaikuma fa,da akwai bambamci sosai atsakanina dakai kuma ni gaskiya ayanzu babu soyayya atsarina domin banshirya mataba, kayi hakuri idan kalamaina sun bata maka rai." Runtse idonsa yayi cikin takaicin kalamanta zuciyarsa na masa zafi yace, "maryam bakisan soba, bakisan zafinsa da radadinsaba. So baya duba cancanta ko kamata balle kuma matsayi. So baya shawara a lokacin daze shige zuciyar mutum. kisani inasonki a duk yanda kike koda kece karshen talauci a duniya, da talaka dame kudi duk dayane agurin Allah, nima haka yake agurina, dan haka kicire batun matsayi a soyayyata dake. Bazan miki doleba kokuma na tursasaki akan dole sekin soniba, kuma dan Allah banason kiduba abubuwan dana miki kice zaki soni dan haka, nafison kisoni dan karan kanki. amma zanbaki nanda kwana 3 kije kiyi shawara,akan haka, kuma kada ki cuci kanki,wajen bani amsa. nabarki lafiya" yakarasa zancen yana Mikewa tsaye. Bejira amsar da maryam zata bashiba yafara tafiya, cikin daci da kunar zuciya,kallona daya mutum zewa sadiq yagane yana cikin tsananin damuwa.

Daskarewa nayi a zaune tamkar mutum mutumi ina binsa da kallo amma nakasa magana, harya fice daga falon. Lumshe idona nayi ina sauke dogon numfashi. "Anya kuwa nayiwa kaina adalci, yaya sadiq be cancanci nakishiba, yamun halacci arayuwa, amma inda matsalar take mahaifiyarsa, koda na amince masa munfara soyyya ba yarda zatayi da auranmu, musamman da abun yahadarmun biyu ga rashin asali ga kuma talauci." Nafadi hakan araina. Nakasa tabuka komai, kwakwalwata ta tsaya tunaninma nakasa, inadai zaune ni kadai afalon. Addu'a nakeyi Allah yasa mafarki nakeyi bagaskiya bane wannan al'amari. Kiran sallar magriba ne yasani motsawa na mike tare da daukar ledar da yaya sadiq ya bani nayi dakina, zuciyata cike fal da damuwar bakon al'amarin daya tunkaro rayuwata Wanda bantaba tunaninshiba koda nan gaba.cikin sanyin jiki nayi alawala nayi sallah, nadade ina addu'a acikin sujjadata akan Allah ya warwaremun duk wata matsala ta rayuwata yakuma tabbatarmun da abunda yake na alkahairi agareni. Ga matsalar jiya bangama fita daga cikiba yau ga yaya sadiq ya kara shigomun da wata. Koda na idar da sallarma zama nayi Inata tunane_tunane. Da kyar na iya yunkurawa domin zuwa nagaida daddy. Ledar da yaya sadiq yabanima ko budeta banma na'ajiye acikin loka. Mommy da daddy da suhailat sukadai na tarar a falonnasa. Tunda maryam tashigo daddy ya kura mata ido yana kallonta, yarinyar tana matukar bashi sha'awa hankali da nutsuwarta, yanaso yamata tambayoyi akan rayuwarta, musamman yanzu daya gano da Wanda kallonnasu yake iri daya ga kuma muryarta datake masa........."ina wuni daddy" muryar maryam ta katse masa tunani, da gaisuwarta. Cikin fara'a yace, "lafiya kalau maryama, ya karatunnaki" "Alhamdulillah" "to masha Allah, Allah yataimaka yayi albarka" "ameen daddy nagode" nafadi haka cikin jindadi ina mikewa domin komawa. Inajin dadin addu'ar daddy akodayaushe kullum nazo seya samun albarka. Sallama nayi musu na fice...

Daren yau gabadaya a wani irin yanayi nayishi, tunanin abunda yaya sadiq yafadamun yamun tsaye a zuciya. Ga kuma tsananin tsoro na abunda yafaru jiya, I najin tsoron karyauma a kara shigomun. Addu'a makamin mumini ita nakama inatayi afili da cikin zuciyata. Abunda yakara tadamun da hankali danazo serving dinsu na dinner babu yaya sadiq, da mommy ta tambayi su haidar sesukace yace bayajin dadine. Shiru naga mommy tayi bata kara cewa komaiba. Senaji duk babu dadi, yanzu akaina yaya sadiq ko abinci yakici, akaina ze shiga damuwa irin haka, gaskiya yakamata nayi tunani kada nazama me saka alkhairi da sharri. Nima kasa cin abincinnayi se sakawa da kwancewa nakeyi, idannayi tunanin amincewa yaya sadiq se kuma intuno badakalar daza'asha alokacin dazancen yafito. Karshedai na yanke shawarar zanyi shawara da zee gobe idan Allah yakaimu naje school. Baccina nayau rabi da rabine ga tsoro ga damuwa, danaga abun bana kare bane sena tashi na nahauyin sallar nafila...........

Washegari, kamar kodayaushe 7/30 nagama shirina, nasaba yaya sadiq kafin wannan time din yazo falo yana jirana, amma yau dana fito senaga wayam babushi. fita nayi koyana mota yana jirana amma nanma se driver nagani, yacemun tundazu yake jirana oga yace shize kaini. Hankalinafa idan yayi dubu yakara tashi, me yaya sadiq yake nufi, jikinnasane kokuma me? bani dame bani wadannan amsoshin seshi.

Da'aka fita break yau banfitaba, dama ni ba kullum nake fitaba, balle yau danake cikin damuwa. Su zee dai sun fita. bata jimaba ta dawo ita kadai. Zama tayi agefena tace, "maryam Ahmad lafiya, yau naganki sukuku dake, kodai jikinnakine.?" Girgiza mata kai nayi alamun a'a sannan nace, "zee yau wata matsalace dani nake Neman shawararki amma dan Allah inaso abun yazama sirri tsakanina dake." Cikin mamaki zee take duban maryam, tace. "Matsala kuma maryam wacce iri" numfashi nasauke. "nabawa zee labarin abunda yake faruwa atakaice." Cike da tsantsar mamaki zee take kallon maryam, domin bata taba tunanin maryam aiki takeyi agidan alh menasaraba. dan batayi kala da masu aikiba. Gyara zama zee tayi tare da dafa kafadar maryam tace, "kamar yadda kikafadamun sadiq ya miki abubuwa arayuwa na alkhairi yakamata kema kisaka masa da alkhairi. Kicire tunanin wai mahaifiayarsa ko yan'uwansa baza susokiba, wannan duk ba matsala bace, domin badasu zaki zaunaba, kuma babu wanda ya isa yahana abunda Allah yarubuta faruwa, duk bala'i da masifar mutum kuwa,idan Allah yayi ke matarsace babu Wanda ya isa ya hana. Maryam zanbaki shawara wadda nasan zakiji dadinta, bazan taba fada miki abunda ze cutar dakeba, danko nice bakebama haka zanyi. Ki amshi soyayyar yaya sadiq hannu, bibbiyu natabbata bazakiyi danasaniba nangaba. Yaya sadiq yakai asoshi, gashi kyakkyawa, ga kirki ga saukin hali, gadai abubuwa na qualities dayawa yana dashi wanda kowacce mace zataso mijinta yakasance haka. Kuma koda yanzu bakyajin sonsa azuciyarki nangaba zaki sosa. Yarinya kisaki jiki kawai Ku kwashi romon soyayya, gashi kun bala'in dacewa dashi kuwa" takarashe zancen da murmushi a fuskarta. Shiru nayi ina juya maganganunta araina, tabbas duk abunda zee tafada gaskiyane, kuma insha Allah zanyi amfani da shawararta duk da haryanzu wani bari na zuciyata cike yake da tsoron yau nice da soyayya, nida banmasan menene sonba, balle harna iya wata soyayya. Ajiyar zuciya nasauke nace, "nagode sosai kawata, Allah yabarmu tare insha Allahu zanyi amfani da shawararki." "Yawwa tawan kokefa, Allah ya kade muku fitina da sharrin shedan atsakaninku yakuma tabbatar mana da alkhairi musha biki" ta fadi haka tana rungumoni ajikinta. "Ameen" nafada cikin jin kunya. "Inyeee, yanmata masoya harna hangoki kinawa yaya sadiq kallon luv, dan wannan idanunnaki masu kyau nasan zasu bada wuta wajen kara hargitsashi." Zee tafadi haka cikin shakiyanci. Dariya namata kawai cikin jin dadi, senaji tamkar ansauken wani katon dutse daga kirjina, duk senaji na matsu a tashi injewa yaya sadiq dina da daddadan albishir. Amma duk wannan abun dake faruwa daga jiya zuwa yau, tunanin yaya mustapha nanan daram araina kamar kodayaushe, amaimakon idanuna su dinga haskomun hoton yaya sadiq senashi kawai nake gani. "Wannan bawan Allah, bansan sanda zandena tunaninshiba, tare dajin faduwar gaba idan na tunoshi" nafadi haka araina ina lumshe ido😳🤐..........

Yau din senajita wata tadaban arayuwata inajin tamkar ancanzani. Ina dawowa gida natarar da yaya sadiq shikadai a falon mommy, da alama beje office ba. Wata sassanyar ajiyar zuciya nasauke na shiga falon da sallama. Sadiq dake kwance akan kujera 3 star tunanin maryam yahanashi sukuni, daga yammacin jiya zuwa yanzu dabe gantaba gaba daya yakasa samun nutsuwa. Amsa mata yayi yana binta da kallo, duk yanda yaso dauke idonsa daga ganta amma yakasa,wani garin ciki yaji sanda yaganta ajiyar zuciyarsa yahausaukewa akai akai dama dawowar tata yake jira. Nikuwa ganin yaya sadiq yana kallonta senayi kasa da kaina cikin jin kunya, zuciyata na bugawa. Ahankali nakarasa garesa naxauna aka can carpet nace, "yaya sadiq sannu da gida yajikinnaka" "dasauki maryam ya makarantar?" Yafadi haka yana tashi zaune, cikin sanyin murya me tattare da damuwa. "Alhamdulillah" daganan nayi shiru ina wasa da yanyatsun hannuna, nama rasa ta ina zanfara masa maganar, kalmomun bakina duk sun gudu. Fahimtar hakan sadiq yayi yace, "maryam kamar da magana abakinki ina fatandai lafiya ko" tattaro duk wata nutsuwata da juriyata nayi na daure nace, "yaya sadiq na'amince da soyayyarka." Nafadi haka cikin rawar murya. farincikin da sadiq yaji alokacin da maryam tafadi haka baze misaltuba, hannu yadaga sama yace, "Alhamdulillah" har sau uku. Fuskarsa dauke da fara'a bakinsa yaki rufuwa,betaba tunanin zata amince masa haka da wuriba,tsareta yayi da idanunsa cikin tsananin farin ciki,yakasa dauke idonsa daga ganta. Mikewa nayi da sauri nafara tafiya cikin sassarfa saboda matsananciyar kunyarsa data lullubeni. "Kije ki shirya, kifito zamuyi magana" natsinkayi muryar yayasadiq yana fadar haka, banjuyoba nidai nashige daki. Tsayawa nayi ajikin kofa ina sauke numfashi tamkar wadda tayi tseren gudu, gani nakeyi kamar nayi gaggawar amincewa yaya sadiq, amma idannatuna kalaman zee se inji hankalina ya kwanta.nadade atsaye ina jimantawa kaina, dakyar naja jiki nashiga toilet na watsa ruwa tare da dauro alwala nafito natada sallah. Ina sallah tunanin tsarabar yaya sadiq ta fadomum arai, aiko ina idarwa na dakko ledar na bude danganin menene aciki. Waro idona nayi waje duka saboda abunda nafara tozali dashi, wayar hannuce kirar android yar madaidaiciya. Bansan takan wayaba balle nasan matsayinta kawaidai tun a jikin kwalin naga anrubuta _Samsung_ ajikin wayarma haka. Ajiyeta nayi agefe, domin gaskiya mayar masa da wayar zanyi, abun yayi yawa dawainiyar tayi yawa gaskiya. Se abu nabiyu dana gani agoguna guda 6 na karfe masu matukar kyau da daukar ido. Gaskiya na jinjinawa yaya sadiq a wajen kyauta, shiko gajiya bayayi nihar kunyar amsar abu nakeyi ahannunsa. Wata takardace ta karshe anannade, se tashin kamshi takeyi. warwarewa nayi naga rubutune amma typed akayi. Gyara zama nayi nafara karantawa kamar haka:

*________________________________________*

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ _*SAKON ZUCIYATA ZUWA GAREKI MARYAMA SARAUNIYAR MATA, TAURARUWATA SANYIN IDANIYATA*_❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull