Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 17
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 17: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 17. _*maryam, kisani sonki yamun babbar illa acikin zuciyata…
3,293 words
_*maryam, kisani sonki yamun babbar illa acikin zuciyata nagane hakanne ta hanyoyi kamar haka, akowanne second dayake shudewa tunaninki na manne acikin zuciyata, aduk lokacin dana dau wasu awanni bangankiba senaji gabadaya nutsuwata tatafi, harse naganki nake samun nutsuwa. Idanuwana basa gajiya da kallon kyakkyawar fuskarki, aduk.lokacin dana ganki inajin farin ciki Mara misaltuwa acikin zuciyata, inajin wata nutsuwa me tattare da nishadi tana bin gabban jikina, ianjin dama in dawwama ina kallonki,zuciyata na bugawa aduk lokacin dana tunaki. Komai naki na burgeni, maganarki, nutsuwarki, tafiyarki,tattausan murmushinki. Akodayaushe hoton kyakkyawar fuskarki na manne acikin idona da zuciyata, mar.........*_
Wani yawu me daci na hadiye makut, zuciyata na mahaukacin bugu, jikina gabadaya yakama rawa takardar ta fadi kasa batare dana karasa karantawaba, wani uban gumine yahau tsatstsafomun ta ko ina ajikina. dakyar na'iya furta Kalmar "innalillahi,wa'inna ilaihirraji'un." Meyake shirin faruwa da rayuwatane, duka abunda yaya sadiq yarubuta amatsayin soyyayya agareni, sunakeji akan yaya mustapha, kenan hakan yana nufin nima nakamu da son yayamustapha, *sonsa nakeyi.* Tashin hankali!.............✍️
_kuyi manage da wannan pls,tun shekaran jiya naso Baku sekuma nafita,jiya kuma naje school bansamu kainaba se dare,nafara typing bacci yadaukeni seyanzu nasamu na muku. kuyi hakuri da typing error banyi editing ba ina saurine zani school_
*BY* *zeey kumurya*
*ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_
*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*
*Bismillahirrahmanirrahim*
2️⃣6️⃣
..........."innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, allahummma ajirni fil masibati, wa'aklifni khairan minha" naita maimaitawa a fili, cikin dimuwa da razanin kwakwalwa, zuciyata na tsananta bugu. Tabbas babu tantama son mustapha nakeyi, nashiga uku ni maryam wacce kaddarace ta kawoni gidannan ta wahala kota azabar rayuwa zankirata. Mikewa tsaye nayi ina goge gumin dake tsatstsafowa asaman goshina. zarya nafarayi ina kaiwa da komowa,cikin mawuyacin halin dabansan yazan misalta muku shiba. Sonake hawaye yasilalomun ko zanji dadin abunda nakeji acikin zuciyata na damuwa. "Yazama dole nacire soyayyar mustapha daga cikin zuciyata, to tayaya? Natambayi kaina, tunanin maganar damukayi da saleemat na tuno. Babu shakka saleemat tagane son yamustapha nakeyi shiyasa tace nayi nesa dashi. Tahakane kawai sonsa zebar cikin zuciyata, kuma sannan zanyi kokarin ganin na cusa son yayasadiq acikin zuciyata tare kuma dadagewa da addu'a, ta hakanne kawai wannan *kaddararren son* zefita daga zuciyata, wannan wanne irin jarabtace, son Wanda besan kanayiba, bemasan dazamanaba, banda haukan so ta bakin yaya sadiq inani inason yayamustapha. mutumin dabe Masan inayiba, besan daniba. zama nayi ina sauke ajiyar zuciya, aganina nasamu mafitar cire son yaya mustapha acikin zuciyata. tunane tunane nayi tayi har akayi sallar isha'i amma nakasa mikewa nayi, yau tsabar firgici kogaida da daddy banjeba, nama manta. dakyar na lallaba naje nayi alwala nadawo nayi sallar. Acikin sallahta addu'a natayi akan Allah yaciremun son yaya mustapha acikin raina,nama godewa Allah dasonnasa beyi mugun tasiri azuciyata. Ina zaune na rafka uban tagumi, naji ana knocking kofata. Ahankali na mike naje nabude, yaya sadiq nagani tsaye,nishaf namamanta yace zamuyi magana. Kasa nayi dakaina saboda kallon daya tastareni dashi, banason yagano wani abu nadamuwa kokadan. Juyawa yayi yana cewa, "kikaraso muyi magana" cikin sanyin jiki nabi bayanshi batare dana amsaba, na zauna agefensa. Yau samannamu shiru, duk basanan, tunda nadawoma ko mommy banganiba nasan suna part din daddy. Satar kallon yaya sadiq yayi, shima duk ya rame kamar baya cikin nutsuwarsa, duk yayi wani iri. Ko duk sonnawane yamaidashi...... "Maryam naji dadin amincewa soyayyata dakikayi, nayi farin ciki Mara misaltuwa, harna rasa bakin miki godiya. Amma dan Allah inason kifadamun gaskiya, har zuciyarki abunda kike fadamun gaskiyane, kokuma kin amincewa soyayyata dan wani abu, kokuma dan kina ganin idan kikaki amincemun kamar bakiyi halarciba. nibanason natursasaki balle namiki dole akan soyyata, kuma banaso ki cutu, inafatan kingane menake nufi. Gyada masa kai nayi cikin danne damuwata nace. "duk abunda nafada maka yaya, har cikin zuciyata yake, cancantarka da kamatarkace yasa na amince maka. Kowacce mace datasan kanta, zatayi alfahari dakai idan ta sameka amatsayin mijinta, shiyasa nima bazanso damarnan ta subcemunba." Daga haka nayi shiru danbansan mekuma zankara cewa, wadannan dinma dakyar na iya furtasu burina a yanzu kawai insamu kadaici. Cikin jin dadin maganganun maryam sadiq yace, "gaskiya bazance nataba jin kalamai masu dadin wannan arayuwataba,idanma naji toh gaskiya namanta, yau kam maryam kinwarkamun da ciwon dake damuna acikin zuciyata, yau zanyi kwanan farinciki dana dade banyi irinsaba, nagode,nagode, nagode sosai, maryam da amsar tayin soyayyata dakikayi, ubangiji yamiki sakayya da gidan aljanna" "amin" na'amsa ina sauke numfashi nakara da fadin, "ammafa yaya sadiq akwai matsala a soyayyarmu" dasauri yajuyo cikin mamaki yana kallona, yace. "Matsala kuma wacce iri kenan" gyara zama nayi cikin jin dacin abunda zanfada nace,"Yaya sadiq koda ahalinka basu hana soyyarmu saboda talaucinaba zasu hana saboda rashin asalina, ninan dakake ganina bansan mahaifinaba kuma bansan kowa nasaba, dangin mahaifiya kawai gare..." Nakasa karasa zancena saboda kukan dayake kokarin kufcemun. Cikin tsananin tausayawa yaya sadiq yace, "kada kidamu maryam dan wannan, ni sadiq ina sonki ahaka kuma zan iya rayuwa dake ahaka, insha Allahu kuma zantayaki da addu'ar Allah ya bayyana miki dangin mahaifinki. Kuma indai maganar iyayenane, daddy bashi da matsala, shi mutum ne me fuskantar abu da kuma masa duba na fahimta, nasan insha Allahu ze fahimcemu. Ita kuma mommy nasan ta yanda zan shawo kanta,harta amince, kikwantar da hankalinki banason ganin kina damuwa." Ajiyar zuciya nakara saukewa akaro na babu adadi, nace. "Shikenan insha Allah zandena damuwar, sannan kuma yaya ina neman wata alfarma dakai guda daya a soyayyarmu dan Allah kamun ita" "uhm, inajinki fadamun wacce irin alfarmace." Cewar sadiq yana maida hankalinsa duka akan maryam. "Yaya sonake ka boye soyayyata dakai,tayanda babu Wanda ze fuskanta" cikin sauri sadiq yace, "banganeba mekike nufiba?" "Ina nufin midunga soyayyarmu aboye kada kowa nagidannan yasani ko kuma wani awaje har zuwa wani lokaci nan gaba." "To maryam mene fa'idar hakan, akwai wani abu aibune a soyayyar tamu, nikam nafison nanuna miki soyayya agaban kowa ta yanda zaki tabbatar da har zuciyata ina sonki" "kayi hakuri yaya, dan Allah kamun wannan alfarma, ina da dalilin haka, idan lokaci yayi zanfada maka dalili. Shiru yaya sadiq yayi na wasu sakanni, sannan yace. "Shikenan maryam namiki wannan alfarmar, inafatan lokacin bame tsaho bane." "Bawani me tsaho bane insha Allah" "tom shikenan kikoma ciki ki huta naga kamar duk agajiye kike, da safe zamu karasa magana" kai kawai na gyada masa na mike na koma daki, dama nagaji da zaman. Shiko sadiq binta yayi da kallo, cikin so da kaunarta gami da tausayinta, ya lura tabbas akwai abunda yake damunta, a yanzu amma ze tambayeta da safe yaji. Ina shiga daki na kwanta saboda nemawa kaina nutsuwa dan har wani jiri_jiri nakeji yana dibata.
**********
Apart din daddy kuwa, yau yaran gidan duk basu je canba, mustapha yana part dinsa suhailat kuma taje gurinsa,dama sune suka fiya zama a part dinnasa. Mommy ce kawai tare da daddy suke hira. Daddy yana lura da lokacin da maryam take zuwa gaishesa, yauseyaga har lokacin ya wuce bata zoba, har an fara kiran sallar isha'i a wasu masallatan. Duban mommy yayi danyakasa hakuri, domin aduk lokacin dayaga maryam zuciyarsa na kokarin tuno masa wani abu daya manta. Yace, "hajiya yau kinga yarinyarnan shiru batazo gaidaniba ko lafiya" takaicine yaturnike mommy, bedamu da yayansa nacikinsa dabasu zoba sewatacan daban, danne rashin jindadin hakan tayi tace, "kasan jiki da jini, kilan tadawo daga makaranta ta gajine, amma innakoma part din zantambayeta dalili." "Hakane, ai yarinyarma tana da kokari gata da hankali da nutsuwa daga ganinta daga gidan tarbiyya tafito" daddy yafadi haka yana mikewa domin zuwa yayi alwala yatafi masallaci. Wani kallo mommy tabishi dashi batace komaiba, se abubuwan datake kissimawa aranta. Shidai daddy toilet yanufa yayi alwalarsa yafice.
*_________________________________________* *MUSTAPHA* *_________________________________________*
Komai na tafiyar masa yanda yakamata, musamman agurin aiki, dasukayi promotion din dazasuyi, amma duk da haka yanzu basosai yake samun kansaba, tunda daddy yana gari. Kullum bayan magriba seyaje sun tattaunawa akan harkar kasuwancinnasu, se can dare yake samun kansa. Yau kam daya dawo akwai aikin dazeyi shiyasa beje part din daddyba sedai waya da sukayi, yana dawowa daga masallaci yadukufa akan system. Suhailat bayan ta dawo daga school da yamma likis kamar kodayaushe. Wanka tayi ta shirya cikin wasu hadaddun kaya riga da skirt yan kanti. Tayi kyau sosai, ta bulbule jikinta da turaruka se tashin kamshi takeyi. Yau sotakeyi ta gigita yayannata, tayanda zata samo yayarda ta tabashi, tayi matukar kewar lallausar fatarsa. Cikin takunta na kasaita da isa ta fito tanufi part dinnasa. Kamar kodayaushe kofarsa abude take, shi mutumne ba'abocin yawan rufe kofaba, saboda yatsani ayi knocking yataso yabude, shiyasa yake barinsu a bude, se can dare yake rufewa. bedroom dinsane kawai idan yana ciki yake kullewa. Afalonsa na kasa tatarar dashi, wata dagowar ajiyar zuciya ta sauke tafara binsa da kallo tamkar zata lashesa. Singlet ce ajikinsa da wando three quarter, kasancewar lokacin zafi yashigo yanzu, danshi Allah yahalicceshi mutum ne mejin zafi ajikinsa, shiyasa baya kaunar zafi kokakan. Sallama ta masa,dagowa yayi da sauri yana kallonta dan besan da shigowartaba, kallonta yayi na wasu sakanni, sannan yamaida kansa kan abunda yakeyi bayan ya amsa mata sallamar. Zama suhailat tayi a gefensa cikin faduwar gaba, domin taga daya ganta maimakon yayi murna sema bata rai dayayi. Kurawa damtsensa da kirjinsa ido tayi, tana hadiyar yawu. Sotake takai hannu tatabasa kotaji dadi amma babu fuska, tarasa meyasa yake mata haka yanzu, baya bata duk wata kulawa data dace ta soyayya. Magana tayi masa amma yashareta, batasan haushinta yake jiba saboda shigar datayi, duk da ita suhailat aganinta tayi shigar mutunci,dan tasan halinsa. Cikin raunin murya suhailat ta kara masa magana da fadin, "haba yaya meyasa kakemun hakane yanzu, baka nemana karage duk wata kulawa da kake bani, idannazo gurinkama kokuma inmun hadu, sedai kaita batamun rai, baka sakarmun fuska, pls yaya idan wani abunnamaka kayi hakuri mu koma kamar da, zuciyata baza ta iya jurar wannan yanayinba, kasan ina tsananin sonka da kaunarka." Takarashe maganar da sakin kuka, domin harga ALLAH soyayyarsa na azabatar da ita. Runtse idanunsa yayi, cikin tausayinta. Shikansa bazece ga dalilin dayasa yake mata hakaba. Suhailat tana bukatar kulawarshi, tunda tana tsananin sonsa kuma itace matar daze aura, shi halayentane bayaso amma idan yatuna ba itace babbar me lefiba, lefin mommy ne, tunda itace bata tsawatarmata seyaji haushinta dayakeji yaragu. Ahankali yakai hannu, ya kwantar da kanta akan kafadarsa batare dayace mata komaiba, yaci gaba da aikinsa. Wasu ajiyar zuciya suhailat tahau saukewa, dama abunda takeso kenan, tasan hakan daya mata alamun rarrashine. Lumshe idonta tayi cikin jin dadi tana shakar kamshinsa. Can kuma ta bude idonta ta kurawa kyakkyawar fuskarsa ido, gaskiya tayi dace da masoyi, abunda yake kara rikitata kenan akansa kyawunsa, tarasa ina yasamo wannan kyannasa, tunda mommy da daddy basu kaisa kyauba, a familynsuma kaf tana tunanin babu me kyawunsa. Badon yagama aikinba ya ture system din yace ta bashi labari,bayan yarabata da jikinsa. Aiko suhailat ansamu abunyi nantaita masa zuba, cikin jin dadi, danma yarage mata jin dadin, daya rabata da jikinsa. seda aka kira sallar isha'i tatafi, shima badon tasoba danma dai yace ze kirata anjimane.
**********
Yau a part dinmu sukayi dinner,danaje serving dinsu mommy tatambayeni meyasa banje nagaida daddy ba nace mata baccine yadaukeni. bansaniba. Yaya sadiq kam yaubezo gurin dinner dinba, bankuma San daliliba. Haidar nata kwasata da hira, suhailat kuwa sedai harare harare dataketa wullomun, batasan bata ita nakeba abunda ke kainama yafi karfina,dakyar ma na iya serving dinnasu na koma daki. Saboda bana hayyacina ko yunwa banaji, kokari kawai nakeyi nacire tunanin yaya mustapha daga zuciyata, amma abun yaci tura, fuskarsa kawai nake gani a idona, ga wata jarababbebiyar kewarsa data addabeni amma na kudurcewa raina kozan mutu bazanbari mukara haduwa dashiba saidai bisa tsautsayi. Dama tunda daddy yadawo mommy ba sosai take aikena part dinsaba kamarda. Haka naita juye, juye akan gado ina tunane_tunane, gashi cikina ciwo yakemun nasan lokacin yin al'adatane yayi, namamanta banyiwa yaya sadiq zancen wayar daya baniba, seda nadawo naganta natuna,killaceta nayi dasafe inzan wuce school nabasa. Ana wata ga wata, gadamuwa nacimun rai, gakuma azababben ciwon ciki, daya addabamun kamar kodayaushe idan zanyi period. Ko motsawa nakasayi balle nayi yunkurin fita karbo magani agurin mommy, gashi dare yana karayi. Dafe cikin kawai nayi ina salati, gabadaya nahada uban gumi, se murkukusu nakeyi. Secan zuwa dare nasamu yalafamun bayan nafarajin alamun digar jinin daga jikina, bankaiga yunkurin mikewaba wani wahalallen bacci yadaukeni.
Ban farkaba se cikin dare, jikina duk yamun tsami, kirjina har wani nauyi yakemun saboda damuwa, ga wani azababben ciwon kai. haka na daure nashiga toilet na tsafatace jikina nadawo na kwanta jikina sam babu kwari kasala duk ta lullubeni ga wani sanyi danake ji yana ratsa jikina, kuma nakasa tashi inkashe koda fankane, se lulluba nayi da bargo. a wahalcedai nakarasa daren yau.
Washegari, da zazzabi natashi mezafi ajikina, hakan yasa nakasa koda tashi daga kwancen danake. Mommy dakanta taje har dakin maryam danganin shiru bata fitoba, ganin halin datake ciki mommy ta kira family doctor dinsu yazo ya duba maryam. Dan taga maryam din najin jiki se rawar dari takeyi. Allura doctor din yamun tare da bani magunguna. Baba talatu mommy takira tazo ta kula dani, baccine yakara daukeni. Baba talatu ita ta fanshi maryam tayi ayyukan part din. Se wajen 1 na farka, alhamdulillah naji dadin jikina sedai kasalar jiki. Yau kam ba batun zuwa school dama Friday ce. Tea me kauri baba talatu ta hadamun nasha tanata jeramun sannu, anan take sanarmun sadiq yazo har sau biyu bantashiba. Danasha tea din kuma senaji dadi sosai, wanka nayi nadawo nakara kwanciya.
Alhamdulillah,kafin yamma na wartsake zazzabin yasauka,kodan nasha maganine. yaya sadiq yakara dawowa yamun sannu. Amma suhailat mun hadu kotamun sannu, kuma nasan tasan bani da lafiya. Hakan bedameniba tunda gashi Allah ya bani lafiya. Littafin literature nadauka, naduba saboda ta kansa zamu fara exam ran Monday. Da daddare danaje gaida daddy, yayitamun sannu haryana cewa dahar part dinma zezo yadubani da kansa sekuma gani nazo. Bayan nadawo muka hadu sa yaya sadiq,namasa zancen maido masa da waya, seya nunamun bacin ransa akan hakan, yakuma ce inada bukatar rike waya nima kodan karatu da sauran abubuwa, nakuma dinga gaisawa da kawaye da yan'uwana,nace masa mommy bazatayi fadaba, yacemun ba'abun da zatace, dan yasaimun waya. Dakko wayar nayi ya kunnata, dama acike take yacazamun ita, nunamun duk yanda zanyi amfani da ita yayi, yakuma bude mun abubuwa. Godiya na masa sosai, muka cigaba da hirarmu cikin nishadi, ammafa duk abunda ke faruwa ayinin yau tunanin yaya mustapha nanan daram araina kamar kodayaushe, babu abunda yaragu daurewa kawai nakeyi a kokarina nason cireshi daga raina,dan ma naganshi dazu a part din daddy kewarsa ta ragu daga raina...........✍️
Meson complete Whatsapp 08166674823
ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_
*Bismillahirrahmanirrahim*
2️⃣7️⃣
*_________________________________________* *AFTER SIX MONTHS* *_________________________________________*
..........Rayuwa nata tafiya tamkar gudun ruwa, (Allah yasa mudace) yau gashi harnayi kusan wata takwas agidan alh, menasara. Nasamu cigaba agidan sosai ta fannin ilimi, dan yanzu gashi harmun shiga ss3. Azaman danayi na watanninan agidan bakaramin canzawa nayiba, nakara kyau da fari, dama bakin na wahalane da hayaki. Canzawar danayi bata wasa bace, naxama kalar yayan masu kudinnan, fatata tacanza tayi kyau tayi sumul_sumul,hatta gashin kaina yacanza yakara baki da tsawo saboda gyara. Komai na gayu da amfanin ya mace yayasadiq yana saimun, har yawa sukemun nake bayarwa,kuma ba'amun iyaka da duk wani abunci kosha agidan,yanda yayan gidan zasuci nima haka zanci komene son raina . Zuwa yanzun kaina ya waye sosai, amma ba irin wayewa wacca ba'asoba wayewa tasanin rayuwa. Zuwa yanzu turanci yazauna sosai abakina, littattafan addinima nasansu sosai, kur'ani me girmama nakusa saukeshi. Gaskiya babu abunda zancewa yaya sadiq domin shine silar zamana komai arayuwa. Zuwa yanzun shakuwa me karfi tashiga tsakanina da yaya sadiq,duk wata damuwata yasani nima nasan tasa, shine abokin shawarata. sedaifa har yanzu babu digon sonsa acikin zuciyata, son mustapha ne zaune daram araina, nayi ina yina da kokarin ganin nacire sonnasa amma nakasa, amma duk da haka ina iyakar kokarina wajen ganin nabawa yaya sadiq kulawa yanda kamata, kamar yadda yake bani. Soyayya mukeyi me tsafta da tsari, koda hannuna yaya sadiq betaba rikewaba. Kuma har wannan lokacin aboye mukeyin soyayyartamu,babu Wanda yasani sedai zee dana fada mata tun farko. danko saleemah banfadawaba haryanzu. Aliya tadawo har sau biyu, amma aunty sau daya takara dawowa,nima naje har kadunan na musu wuni guda, tarema mukaje da yaya sadiq. Naje unguwarmu wajen gwaggo dasu saleemat sosai, dan yanzu duk sanda nakeson fita yaya sadiq yana kaini, har gidan kawayena. Saleemat tataba zuwa gurina sau daya, shima dakyar umma tabarta. Gwaggo kuwa tasha cemun zatabiyoni idannaje sena mata wayo nagud,do,dannasan idan tazo kunyatani zatayi.
Zaman danayi ayanzu nagane halin kowa nagidan dakuma yanayin gidan. Shidai megidan yana da kirki sosai, gashi bashida fariya ko karya, Allah yabashi kudin daze iyayin abubuwa na jindadin rayuwa, amma kuma yanayin komai nasa daidai misali baya zafafawa. Yanada gidajen mai, da makarantu na boko dana islamiyya, da kamfanunnuka na sarrafa abubuwa, sannan gashi mutum ne meyawan sadaka da kyauta. sabanin mommy datake komai nata cikin fariya da nuna isa gami da gadara, amma haryau nakasa gane halinta,wani lokacin tamaka kirki, wani lokacin kuma rashin kirki. gidan alh, menasara basayin baki kwata_kwata, kawayen mommy ne kadai suke zuwa se su aunty. Amma ko yan'uwan ta bantaba ganiba agidan tunda nazo. Suhailat halin mommy ne da ita Sak, babu ta Inda tabarta, kamar yadda suke tsananin kama. Har yanzu tsakanina da ita kyara da hantara,narasa meyasa ta tsaneni haka. Su zannurain da haidar kuwa, yanzu nasamu lafiya musammanma haidar shiri muke dashi sosai har karatun boko yana koyamun abunda banganeba. Sai *heartbeat* (mustapha) sunan danasa masa kenan. Shima na fuskanci wasu daga cikin halayennasa.Shi mutum ne miskili,irin miskilancinnan me cin rai nashariya. amma gaskiya yanada kirki sosai, kuma sam baya shiga sabgar mutane, kuma bayason raini akwai tsare gida, shiyasa kannensa suke masifar tsoronsa, last kuma shi masifaffene,nakarshe idan aka tabosa. Daddy mutum ne metafiye_tafiye, amma idan yaxo gida yana jimawa kafin yakoma. Yaya sadiq ma yanzu baya wata agida seyayi tafiya,harkar kasuwancinsu. Yau laraba, sakaliyar yammace, zaune nake nikadai a garden ina tunanin rayuwa. Yaya sadiq bayanan yayi tafiya tun shekaran jiya. Kewarsa gaba daya tacikamun zuciya, shiyasama nazo garden din na zauna, kullum anan muke tadinmu nudashi. Nikam haryanzu hankalina yakasa kwanciya akan soyayyarmu dashi nasan zeyi wahala su mommy su amince masa ya aureni, dandai yadagene. aduk lokacin dana fada masa haka, seyayta lallabani yana bani baki akan zasu amince. Tunani nakeyi akan maganarmu dashi last kafin yatafi, yacemun dazarar yadawo zefadawa daddy abunda ke tsakaninmu shiyagaji da wannan boye_boyen damukeyi. inda naji dadima daddyn bayanan kuma bedade dayin tafiyarba. Ganin magriba tagabato sena nabar garden din. Ina cikin tafiya kafinnakarasa part dinmu, nahango motar tashigo. Haka kawai naji gabada yafadi bankuma san daliliba. tsayawa nayi danganin waze fito daga motar. Wata sassanyar ajiyar zuciya na sauke ganin Wanda yafito bayan drivernsa yabude masa murfin motar, yaya mustapha ne ashe shiyasa zuciya ta tahau luguden bugun data saba aduk sanda naganshi, lumshe ido nayi cikin wani irin yanayi. "Oh ni maryam, bansan sanda zandena son wannan bawan Allahn ba." Nafadi haka afili cikin tsananin damuwa. Nayi iyakar yina wajen ganin nacire sonsa daga zuciyata amma abu yafaskara, narasa wannan wacce irin kaddara ce. Gashi wani irin zazzafan so nake masa, wanda idan nawuni bangansaba gabadaya fita nake daga hayyacina,narasa mekemun dadi aduniya,harse nagansa nake samun nutsuwa. Yanzunma dana gansa bakaramin dadi najiba, gaskiya so bemun adalciba nikadai nasan irin wahalar da zuciyata takesha akan bawan Allah nan, mutumin da nasan yamun nisa nahar abada, bazantaba samunsaba, domin nikaina nasan niba kalarsa bace, yawuce ajina. idanma na samesa ina zan iya kishi da suhailat? Yanda take tsananin sonsa, bata iya boye soyyayar datake masa agaban kowa manuna masa kauna takeyi,tsaf zata iya wa mutum illa akansa. Anma fara zancen bikinsu tunda suhailat din tana level 4 ne yanzu, tana kammalawa kuma za'asha bikinsu. Cikin sanyin jiki naja kafata datamun sanyi nacigaba da tafiya.