Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 18
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 18: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 18. Mommy natarar zaune afalo ita kadai, sannu namata ina…
3,291 words
Mommy natarar zaune afalo ita kadai, sannu namata ina kokarin shiga dakina ta kirani. Dawowa nayi na tsugunna agabanta. "Yawwa maryam, tundazu nake nemanki,binta tacemun kinfita garden, kinsan saura kwana 3 Christmas gobe su kuku zasu tafi garinsu se bayan 2 week zasu dawo, yanzu aikinki yadadu a gidannan harda girki kezaki fanshesa, inafatan kin iya girkin ai" dagamata kai nayi alamar eh. "Ohk, sannan kuma se gyaran part din son shima duk masu masa aikin dasuke masa zasu tafi tarene, zaki dinga zuwa kina masa tun sassafe kafin kitafi school danshi yafison kafin yafito yaga angama masa komai,." Damma kirjina ya buga, gabana yayanke yafadi, yanzu part dinsa zandinga zuwa gyarawa, meyasa mommy bazata tura waniba seni, nifa adole nake barin muna haduwa dashi, danba yanda zanyine,amma gashi mommy takara kusantamu, dan babu tayanda za'ayi nagama gyara part dinsa duka ace bamu hadu b..."maryam!" Mommy takatsemun tunani da kiran sunana. "Na'am" na'amsa ina sauke numfashi. "Dafatan kinji duka abunda nace miki kuma zaki kiyaye." "Insha Allah mommy" "yawwa daga gobe zaki fara, zaki iya tashi ki tafi" ahankali na mike nafara tafiya tamkar wadda kwai yafashewa aciki.
bani da zabi banda bin umarnin mommy tunda aikinta nakeyi agidan. Da wuri nayanke shawarar zan kwanta yau, saboda karnayi latti gurin tashi da wuri gobe,tunda aikina ya ninku akannada. bayan nayi serving dinsu nima naci abincin na kwanta. Ina kwanciya naji wayata na vibrate nasan yaya sadiq ne. Janyota nayi nadaga tare yin sallama,cikin danne abunda kedamuna. Daga daya bangaren yaya sadiq yace,
"Wa'alaikissalam tauraruwar zuciyata, harnaji dadi danaji wannan daddadar muryartaki, wata nutsuwace ta lullubeni, dako gaba daya nakasa aiwatar da komai"
Murmushi nayi nace, "Nima inanan kewarka ta hanani sukuni,yayana"
"Uhm, shine kokikirani balle kimun dan text ko?"
"Sorry yayana, nasan kana aikine shiyasa amma ai namaka sakon zuciya da zuciya, shi'ai nasan ya'iso gareka"
Murmushi yayi me sauti cikin jin dadin kalamanta yace, "Naganshi indai wannanne, dafatan nima kibiyar dana harbo miki ta reply ta karaso gareki"
"Ehhh, mana tunyaushe shiyasama kaga ai nakai haryanzu kalau, dabata karasoba datuni katawo jinya ai,danda bazankai yanzu lafiya kalauba"....
Hira muka cigaba dayi irinta ta masoya, duk da ni karfin hali kawai nakeyi, dakyar yaya sadiq yabarni shima danyaji nafara masa shiru alamun bacci yafara Cina. Munagama wayar kuwa bacci yadaukeni bajimawa. Cikin baccina naji ana tabani, dafarko nayi tunanin a baccine sedaga baya naji abun ya girmama,kuma kamar azahiri. Bude idona nayi ahankali, tacikin duhu naga kamar inuwar mutum akaina, wata mahaukaciyar bugu zuciyata tayi tamkar zata faso kirjina tafito, cikin tsananin firgici da tsorata nayi yunkurin mikewa zaune, amma aka mayar dani kwancen danake aka danneni da karfi tamkar za'a ballani,numfashinama dakyar yake fita. Wani irin kamshi me kamar kaurine yake tashi daga jikin mutumin, irin wanda naji randa aka taba shigomun daki. runtse idona nayi jikina gaba daya yahau kyarma, addu'ar neman tsari daga Allah nafara karantowa araina, domin shikadai gareni ahalin yanzu kuma shine kadai ze iya kubutar dani. Cikin wata irin dashashshiyar murya mutumin yafara magana. "Yarinya yau babu me kwatarki ahannuna, yau sena cika burina na karshe arayuwa akanki, yau mafarkin dana dade Inayi ze tabbata agaskiya, kece cikar burina na karshe arayuwa,dan haka dole nacikawa kaina burinaaaa!!!!..........✍️ Meson complete Whatsapp 08166674823
*ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_
*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*
*Bismillahirrahmanirrahim*
2️⃣8️⃣
.............Cikin wani irin karfi danaji yaziyarceni na hankade mutumin daga kaina tare da mikewa zaune da Sauri ina maida numfashi,da sauri da sauri. jabaya nafarayi cikin tsananin tsorata gami da razani, bakina nacigaba da karanto addu'ar neman tsarin daga ubangiji ,kafin na kara wani yunkuri mutumin yakara yowa kaina, cikin azama naja baya sosai harnakai karshen gado, sonake na kurma ihu,kozan samu dauki amma nakasa tamkar ansa super glue anrufemun baki,nakasa koda motsashi,ga wani kauri_kauri dake tashi daga jikin mutumin dayake kokarin tarwatsamun kaina. saboda tsabar tsorata cikina se har wani kugi yakemun. Hannunsa yakuma sawa yadamki gashin kaina da karfi yana kokarin maidani kasa, saboda tsananin azabar data ziyarceni, bansan sanda nadankara masa cizo a gefen wuyansaba. Wata yar siririyar kara yasaki tare da sakina yasauka daga kan gadon da sauri,ya fice daga dakin da gudu. Nima cikin fitar hayyaci nasakko,nabi bayansa numfashina nafita dakyar, banmasan inda nake jefa kafataba,hannuna dafe da kaina dayake mugun saramun gami da juyamun, ina fita falo naga wayam babu kowa harya fece, kuma falon akawai haske balle ince buya yayi, daidai lokacin mommy tafito daga dakinta cikin firgici ta fara fadin, "maryam lafiya meke faruwa, naji anbuga kofar falo da karfi" ban iya bata amsaba saboda wani jiri daya kwasheni nayi kasa luuuu zanfadi, dasauri mommy tataho tatarota jikinta, girgiza maryam tahauyi tana tambayarta lafiya,maryam batamasan tana yiba tatafi duniyar suma. Daukar maryam mommy tayi takaita dakinta ta kwantar da ita akan gado. Ruwa me sanyi ta debo tahau shafawa maryam a fuskarta zuwa wuyanta,kusan 12 minutes tana mata haka, kafin maryam taja wani dogon numfashi, ajiyar zuciya mommy tasauke ganin maryam ta farfado, hartaji sanyi aranta kar yar mutane, ta mace mata. "Maryam,maryam,maryam!" Naji muryar mommy asama tana kiran sunana, ahankali na bude idona dayaymun nauyi ina kallonta dishi_dishi, sonake namata magana amma nakasa harshena yamun nauyi, tunanin abunda yafaru nake kokarin yi, amma nakasa,ga wata sarawa da kaina yakemun tamkar ze rabe biyu. Duk da bana cikin nutsuwata amma yanayin mommy dana fuskanta, gaba daya arude take, har wani gumi naga tana hadawa. Mayar da idona nayi na lumshe,cikin karfin hali nafara karanto addu'a acikin raina, cikin ikon Allah bansan sanda bacci ya daukeniba....
Ahankali na bude idona Wanda hakan yayi daidai da kiran sallar asuba da'ake kwadawa. Ahankali na yunkura na tashi zaune ina karewa dakin mommy kallo, jikina rass najishi babu ciwon komai kamar jiya. tunanin abunda yafaru har ganni adakin mommy nake kokarin yi amma nakasa, hakura nayi da tunanin na sakko daga kan gadon nanufi toilet domin yin alwala, abunda ya bani mamaki mommy bata dakin. Koda nafito daga toilet din sena ga mommy zaune akan dadduma da hijabi ajikinta. Kallon maryam mommy tahauyi cikin kura mata ido, nidai kasa nayi da kaina ina kokarin gaisheta naji tace, "maryam harkin tashi, yakikejin kannaki yanzu?" cikin sanyin murya nace mata, "dasauki mommy,yama tafi duka" "masha Allah haka akeso, ga dardumacan dakko sekiyi sallar" dakai na amsa mata na dakko dardumar na shimfida, kaina gaba daya ya kulle narasa tuno mekefaruwa. Jam'i mukabi dukanmu nida mommy, ana idarwa nayi lazimina na mike naiwa mommy sallama nakoma dakina. Dakin na tsaya ina karewa kallo, babu wata alama data nunamun wani abu yafaru, dakin fess dashi setashin kamshin room freshener yakeyi da turaren wuta. Toilet nafada nayo wanka nadawo shap_shap nasaka uniform dina na zunbula hijabi,dakina na tattare kafin gari yayi haske intafi gyaran part din *heartbeart.*
6:18,am. Nafito daga part dinmu nanufi nashi, ma'aikatan gidan burjik kowa nata aikinshi a farfajiyar gidan, masu shara nayi masu bawa flower ruwa nayi gasunandai sunata fama. Ahankali nabude kofar part dinnasa bakina dauke da sallama, tsayawa nayi ina karewa falon kasan kallo, namanta rabona dana shigo part dinnan, ancanza komai na falon,tundaga kan kujeru labulaye center carpet komaidai ancanza daga Wanda nasani. Falon fess naganshi babu datti, ga wani daddadan kamshi dayake tashi, toni banmaga abun datti daza'a gyaraba ananba. Ganin zanbatawa kaina lokaci, sena shiga inda mommy tacemun nadakko abun shara, nashare falon, bayan na kwashe yar kurar dana tara nayi mopping din falon, da goge_gogen su TV da dinning. Kafin nagama duk senaji nagaji dan falon yafi na mommy girma. Kitchen din kasan nashiga shima na gyara cikin Sauri danna kusa latti, dama kasannasa babu bedrooms, daga falo se toilet se kitchen, shima toilet din, wankeshi nayi tass,tsaf dai nagyara kasan nanufi sama ganin har 7 ta wuce. Sauri_sauri na fara gyara falon saman,ina cikin goge kan dinning naji wani irin yanayi ajikina, zuciyata ta fara bugawa, da sauri na juyo bayana. Ido hudu mukayi dashi yana tsaye yana kallona, daddadan kamshinsa gaba daya ya mamaye falon, cikin shirinsa na zuwa office yake tsaf harda briefcase dinsa a hannunsa. Shi mustapha mamakin ganin maryam yayi, duk da mommy tafada masa zata turo masu aiki su gyara masa part dinsa beyi tunanin wannan yarinyar zata turo masaba, gashi kuwa abunda bayaso harya fito bata gama aikinba,dama banda abun mommy wannan yar mutsilar yarinyar ina zata iya wani aiki. "Ina kwana" nagaisheshi cikin faduwar gaban kallon danaga yana mini fuskarsa a tsuke, gyadamun kai yayi har lokacin bedena kallonaba, nidai tsaye nayi kaina a kasa nakasa cigaba da aikin, sedanaga yajuya ya fara tafiya sannan na dago ina kallon bayansa harya fice. Ajiyar zuciya nasauke, nahau gulmarsa araina. Yarame, amma bakaramin kyau yakaramunba, nadade banganshi close to close hakaba, sedai gani daga nesa. Wani irin nishadi naji acikin zuciyata dana gansa, gaskiya so bala'ine,senaji dama ya zauna inta kallonsa. Cikin jindadi nakarasa aikin part din nasa. makullin daya ajiye akan kujera nadauka narufe duka kofofi biyun nasama dana kasan part din, sannan na koma part dinmu.mommy dasu binta masu aiki sunata kokarin hada breakfast a kitchen,mukullin part dinnasa nabawa mommy,namusu sannu da aiki na wuce dakina. Karasa shiryawa nayi. Nadakko wayata zan kashe naga missed call din yaya sadiq, dama munsaba kullum kafin natafi school semunyi waya. Banbi bayan kiranba saboda nayi latti, text kawai namasa nakashe wayar, cikin kudin da yaya sadiq yake bani, nadauki 500 nafito natafi. Koda nadawo daga school nasha aiki sosai, har dare ina fama, ga girkin rana gana dare. Aiko jikina yayi tubus da gajiya.......
***********************
Yau kwana 8 dafara aikin gyara part din yaya mustapha,da duka aikin gidan. Yaya sadiq kuma kwanansa biyu da dawowa daga tafiyar da yayi. karfe 6,nagama shirina na nufi part dinshi. cikin tsananin farinciki, inajin dadin wannan aikin,saboda kullum ina ganin *heartbeat* yanda yakamata,koda naje da wuri nagama aikin, idan befitoba se inta lakai_lakai harse yafito nagansa. Aiko yanzu kullum da murmushi dauke a fuskata nake wuni,yaya sadiq har yakasa hakuri yatambayeni meyake sani farin ciki haka, nace masa duk murnar dawowarsace. Kafin 30 minutes nagama gyaran kasansa, nanufi sama. Inayi ina waigen koze fito amma harna gama ko motsinsa babu, kin tafiya nayi koze fito amma naji shiru mintuna fiye da 15 sun shude befitoba, haka na taso jiki a sabule cikin takaicin rashin ganinsa na fito daga part din,jinake kamar na koma kozan tarar yafito. Abakin part dinmu nayi kicibus da yaya sadiq, cike da mamaki ya tsaya yana kallona. ''Maryam, daga ina haka tundazu Inata jiranki kizo mu wuce na saukeki harna gaji dajira na biyo bayanki." "Yihakuri yayana, mommy ce ta aikeni nakaiwa yaya mustapha abu" "what!,me kuma mommy ta aikeki kai masa da sassafennan" yafadi haka cikin karaji haryaso ya bani tsoro. Dama banfada masa ina zuwa part din mustapha yimasa aikiba,dannasan seya hanani,nikuma bazanzo hakaba kodan karna dena ganin kyakkyawar fuskar *heart beat* ina jindadi. "tea nefa tabani nakaimasa" nabashi amsa ina dan bata fuska. Ajiyar zuciya sadiq yasauke yace, "shikenan nizan wuce naga 8 ta kusa, karnayi latti a office driver ya kaiki" yakarashe zancen yana duba agogon hannunsa. "Tom,Adawo lafiya, Allah yakiyaye" "ameen, matar sena dawo kikulamun dakanki. "Insha Allah byeee" nakarashe zancen ina daga masa hannu alamar bye_bye fuskata dauke da murmushi. Adaidai lokacin aunty suhailat tafito daga part dinmu, dasauri kuma naga tajuya takoma ciki. Nima juyawa nayi nashige domin naje nakarasa shirina. "Mom,mom,mom" suhailat take ta kwalawa mommy kira tundaga falo harta shiga dakinta. "Na'am, my daughter irin wannan kira haka" zama suhailat tayi agefen mommy tana fadin, "mom, nifa wani abu nake zargi a gidannan mara yiyuwa" cike da mamaki mommy tace, "banganeba suhailat wanne abune haka" tabe baki suhailat tayi tace, "mom nifa ina zargin waccan kujakar yarinyar yaya sadiq yake soyayya da ita" "wacce yarinya kenan daughter" "hmm,mom kenan. Wacce yarinya garemu banda house girl din gidannan, maryam take kowa,ohi mata" murmushi mommy tayi tace, "haba suhailat,tayaya za'ayi sadiq yayi soyyaya da maryam, kawaidai kinsanshi shina kowane." "Kai,mom banda irin wannan, tunda ake kawo yara gidannan aikatau wakika taba ganin yayima haka, yanafa kula da yarinyar sosai, yana kashe mata kudi mom kamar bakya ganine" "Ina gani daughter kuma ina sane dashi,amma bandauki hakan da wata manufaba gaskiya,dankinsan sadiq dina damacan shi mutum ne me kyauta da tausayawa mutane." "Mommy kenan, amma yanda yakeyiwa maryam din hidimane yayi yawa, kulawar dayake bata ta wuce ace iya tausayawace kawai." Dafa kafadar suhailat mommy tayi tace, "karki damu kanki akan haka daughter zan bincika nagani koma menene zansan tayanda zan bullo masa" "yadai kamata mom,dankaryaje yadakko mana abun kunya,da Allah wadai a idanun jama'a" suhailat ta fadi haka tana mikewa, sallama tayiwa mom ta fice, dama school zata tsegumi yadawo da ita. Zuciyata cike da tunanin yaya mustapha gami da kewarsa, nakarasa shirina nafito nayiwa mommy sallama nafice. Harna nufi gurin danasan driver yana jirana senaji ina, bazan iya barin gidaba batare dana ganshiba nariga dana sabarwa idona da zuciyata da ganinsa kullum, ahankali na juya nanufi part dinnashi,haka kawai naji zuciyata na bugawa, gashi kuma ina danjin tsoron bansan mezance masaba,idannakoma. Ahankali na tura kofar falon kasa senajita abude, ajiyar zuciya nasauke cikin farin ciki ganin yananan befitaba. Sama na haye cikin sauri, shima ina tura kofar najita abude. Anan na tsaya kuma ina sake_sake araina,wata zuciyar tanacemun nashiga bedroom dinsa wata zuciyar tana gargadina ga aikata hakan, domin aka'idama hakan bekamataba, kuma shima idan yakamanifa nasan sena yabawa aya zakinta. harjuya kuma senaga ina bazan iya komawa batare dana ganshiba tunda nazo kuma sedai komai zefaru yafaru ta fanjama fanjam,so ya rufemun ido,burina kawai ingansa. Cikin kwarin zuciya na juyo na dawo, duk da bugun da zuciyata takemun haka na runtse ido na bude dakin danasan yana ciki, cikin ikon Allah kuwa kofar dakin abude take, ahankali na tura zuciyata na tsananta bugu, tsayawa nayi ina kallonsa yanda yake kwance akan makeken gadonsa,tamkar gawa. Jikinsa gabadaya alullube yake da bargo, fuskarsa ce kawai a bude, idanunsa a lumshe da'alama bacci yakeyi. Cikin sanda nafara taku, harnaje gaban gadon natsaya ina kallonsa, ina sauke ajiyar zuciya akai_akai. Ina tunanin intasheshi amma kuma inajin tsoro, atunanina baccine yadaukesa batare dayasan lokaci yayi hakaba. "Maryam,karkiyi kuskuren haka,tunda dai kinganshi hankakinki ya kwanta kitafi kawai,kar tsautsayi yasashi farkawa yaganki tsaye akansa,mezakice masa yakawoki dakinsa" wata zuciyar ta gargadeni da aikata haka. Badon nasoba sedan tsorandanakeji najuya nafara tafiya,ina tafe ina waigensa harna fice daga dakin. Senajini duk wani iri,zuciyata sam babu dadi,kamar wani abu mara dadi nashirin faruwa dani. Haka kawai naji hankalina sam yakasa kwanciya bankuma san daliliba. Inda driver yake jirana naje nasamesa, nasanma harya gaji da jirana..........
Mommy ganin har wajen 10 son dinta bezo yagaishetaba setaji hankalinta yakasa kwanciya, shida yake zuwa gaisheta tun bayan sallar asuba amma yau haryanxu shiru, gashi tanata kiran wayarsa no respond,gashi maryam yau bata kawo mata key din part dinshiba,ita kuma tamanta bata tambayetaba. Yanke shawara kawai tayi gwara taje taduba taga ko lafiya yake. wayarta kawai ta dauka ta nufi part dinnashi,tanata addu'ar Allah yasa lafiya yake, dantasan bakaramin abune zehanashi fitaba. Kamar yadda maryam tabarshi haka mommy taje tasamesa, a kwance tamkar gawa. Cikin sauri mommy takarasa kan gadon dayake, tana kiran sunansa,cikin dan daga murya. "Son,son,son" amma taji shiru,zare bargon daya lulluba dashi tayi, ganin yanda yake hada uban gumi, wani irin huci mom taji yana tashi saga jikinsa, numfashinsa na fita da sauri da sauri. Cikin tsananin firgita da yanayin data ganshi takai hannu, tataba goshinsa. Dasauri tajanye hannunta saboda zafin dataji kannasa yayi, tamkar anzuba masa garwashi,gashi babu inda yake motsi ajikinsa, numfashin dayake fitarwane kawai zesa kagane yanada rai,abunda ya kara firgita Mommy kenan. Cikin tsananin gigita dayanayin da mommy taganshi, ta kwalla kara tahau jijjigashi tana kiran sunansa da karfi,tana fadin. "My son, meke damunka haka, pls d katashi dan Allah! Son,son!" dasauri kuma ta mike tamkar wadda aka tsiraka tafice da gudu daga part din cikin tsananin tashin hankali, farfajiyar gidan tanufa tana kiran ma'aikatan gidan akan suzo dasauri su taimakamata takai mustapha asibiti. Wani daga cikin ma'aikatan gidan me suna Adam, shiyafara zuwa. "Hajiya lafiya kuwa, meke faruwa?" Yatambayi mommy cikin mamaki saboda betaba ganinta a irin wannan yanayinaba. "Inafa lafiya Adam, nazo nasami son dina cikin mawuyacin hali na rashin lafiya,kutaimakamun nakaishi asibiti karya mutu narasashi" mom takarasa zancen cikin tsananin damuwa tamkar zata fashe da kuka. "subhanallah muje hajiya,muje, muje" juyawa mommy tayi cikin sauri da tsananin tashin hankali cikin part dinnasa,Adam na biye da ita abaya. wasu ma'aikatan dasuka karaso gurin yanzu suma suka rufa musu baya cikin sauri,ganin alamun babu lafiya..........✍️
Meson complete Whatsapp 08166674823
ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_
*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*
*Bismillahirrahmanirrahim*
2️⃣9️⃣
.........Hankali atashe mommy take nunamusu mustapha,dake kwance yanda ta barshi bayan sun isa har cikin dakinsa, babu bata lokaci suka nufeshi suka cuccuboshi kamar yadda mommy tace, suka fito dashi zuwa mota. Mommy da jikinta keta rawa saboda tsabar firgici, ta dauki wayarta data ajiye agefen gadon tun shigowarta dakin, tafara Neman number daddy domin kiransa tasanar masa halin da'ake ciki,sannan itama tabi bayansu adam da sauri. Tana tafe tana kiransa amma bedagaba harta katse, cigaba tayi da kiransa amma harta shiga mota bedagaba,driver nagaba, mommy kuma tana zaune akan kujerar mezaman banza, se mustapha da'aka kwantar abayan kujera. Cikin sauri driver yafigi motar, mommy kam gabadaya baya tajuya tana kallon mustapha,gani takeyi tamkar kafin wani lokaci kankani ze iya mutuwa, basuyi nisa da tafiyarba wayarta ta fara kara. Jikinta narawa ta dakko tadaga da sauri ganin daddy ne, sallama daddy yayiwa mommy, batare data amsa masaba, cikin tsananin rudu tace, "alhaji, my son naje natarar kwance a part dinsa babu lafiya, kuma babu Inda yake motsi ajikinsa senumfashinsa dake fita kadan_kadan,yanzuma munakan hanya zamu kaisa asibiti." Takarashe zancen da fashewa da kuka. Abangaren daddy cikin kidima yace, "Subhanallah, dama bashi da lafiyane" cikin shashsheka mommy tace, "lafiyarsa kalau muka rabu jiya" numfashi daddy yasauke yace, "ohk, kukarasa general hospital dashi bari nakirasu nasanar musu zuwanku, kujirayi zuwana nanda dare, ganinan zantaho nima insha Allah" da "to" kawai mommy ta amsa masa ta kashe wayar, number yan'uwansa tafara laluba tana kiransu daya bayan daya tana sanarmusu,suhailat ce kawai bata kiraba. Hankalinsu gabadaya yayi matukar tashi, kowa barin inda yake yayi cikin gaggawa yanufi asibitin. Driver shima kara gudu ganin yadda mommy ta gigice tanata kuka tamkar ance mata mustaphan ya mutune. Cikin 18 minutes suka karasa asibitin, ma'aikatan asibitin harsun fito da gadon tura mara lafiya suna jiransu. Acan mommy tatarar da sadiq shi haryaje yana jiransu. Cikin sauri ma'aikatan suka karasa gaban motar su mommy da gadon daukar marasa lafiya suka kama mustapha suka dorashi akai suka fara turashi da gudu zuwa cikin asibitin. Mommy ma rufa musu baya tayi,tana tafe tana saba mayafi, ita da yaya sadiq, datashin hankalinsa ya ninku fiye dana da, dayaga halin da dan'uwansa yake ciki, beyi tunanin ciwon yayi tsanani hakaba. Emergency aka nufa da mustapha, cikin wani daki likitotin suka shiga dashi, suka dukufa dubashi domin ceto numfashinsa dake barazaranar karewa. Mommy se kaiwa da komowa take aharabar gurin,yayin da sadiq yatsaya jingine da bango dafe da kansa, cikin tsananin tashin hankali, kafin 20 minutes su haidar duk sun halla a asibitin, cikin damuwa suka hau tambayar mommy meyafaru amma mommy takasa basu amsa, ita burinta likitocin su fito suce mata danta yafarfado. Abangaren daddy kuwa suna gama waya da mommy yakira aunty yasanar mata. Nandanan aunty ta rude tafara shirin tahowa kano babu bata lokaci.....
**************
Ina school ne,amma gabadaya hankalina yana gida. Zuciyata takasa samun nutsuwa. Karatunma yau ba fuskantarshi nakeba. zee dake hankalce da maryam tundazu ta zungureta,cikin rada_rada tace, "mairota lafiyarki kuwa,naga gaba daya bakya cikin nutsuwarki,se tagumi kikeyi" ajiyar zuciya nasauke nace, "babu komai kawata" "hmmm,kifadamun gaskiya kokunsamu matsalane da yaya sadiq" girgiza mata kai nayi alamun a'a. Shiru zee tayi batakara cewa komaiba, tamaida hankalinta ga karatun da'ake musu. nikam na matsu atashi hankalina gaba daya yayi gida......
**************