Kenza eBookz

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 19

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 19

Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 19: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 19. Gwaggo ce, tsaye a gidansu su saleemat rike da kugu…

3,113 words

Gwaggo ce, tsaye a gidansu su saleemat rike da kugu tazone akan dole se saleemat ta rakata gidan alh,menasara tunda tataba zuwa, ita tasan unguwar gidanne bata saniba. saleemat dai nazaune tana danna wayarta hankali kwance, dama umma batanan tafita taje asibiti ganin likita tun safe, kannenta kuma sun tafi school se ita kadai agida. Kara cokalo harbatsatstsen daurinta gwaggo tayi gaba,cikin masifa tace, "kefa dama yarinyarnan bakida kirki da mutunci kokadan, banda haka nazo tundazu ina miki magana amma kinmaidani yar iska kinki kulani, da suwaibace zaki mata haka." Kallon gwaggo saleemat tayi tace, "amma gwaggo kina kallo dai umma batanan, nikadaice kuma maryam koda munjema batanan tana school" "Toni dama nace miki gurin wata maryam zani meruwana da wata maryam,gurin mutanen gidan zani ingaishesu" kafin saleemat tabawa gwaggo amsa wani almajiri yashigo yacewa gwaggo tazo tayi bakuwa tana kofar gida atsaye. Wani dogon tsaki gwaggo taja tana fadin, "wacce gantalalliyarce kuma tazomun ina shirin fita, amma mujedai ingani" takarashe zancen dabin bayan yaron. Itadai saleemat hamdala tayiwa Allah tasamu salama.

Gwaggo nafita taga wata tsohuwar kawarta dasuka fi shekara basu haduba. irin matannanne masu zaman saudiya, gatanan fess da ita taci gayunta. wangale baki gwaggo tayi cikin mamaki tace, "hajja gana,dama rai kanga rai" murmushi matar tayi tace, "gashi kuwa ladi mun hadu" makullin dake hannun gwaggo tasa tabude gidan tana zubawa hajja gana maraba cikin muryar ganinta. Bayan sun shiga gidan, hajja gana tazauna agefen gadon gwaggo adarare saboda kyankyami tace, "wato haryanzu Ladi halinkidai besauyaba na kazanta" bata fuska gwaggo tayi tace, "nifa matsalata dake kenan hajja,shegen tsantsaini iyayin tsiya,kinsaba da saudiya ko'ina fess,aibaza kihada nan da canba,kuma ni gaskiya aiki wahalar dani yakeyi,bazan iya wani bautar gidaba,barinshi nake yaci dattinshi yagama" "Gyada kai hajja, tayi tace. "Amma kin iya fita tun farar safiya gidan makota,ana jiyo muryarki har kwararo kinata kwakwazo" "badole kijini har kwararoba hajja,yarinyace naje nace tarakani gidan da maryam take aikatau amma taki,saboda tsabar bakin hali" "ladi!, wacce maryam din ce take aikatau kuma, badai takiba.?" "Ita mana, ai aikatau nakaita" cike da takaici hajja tace, "amma wlh ladi, Allah wadaran halinki yanzu duk abunda maryam take miki a gidannan shine kika dauketa kikakaita aikatau,saboda zalinci" cikin rashin damuwa gwaggo tace, "yoo duk abunda takemun yafi kudin dazansamune" "hmmm, ladi tsinannen son kudinkine ze kasheki, banda haka dudu nawane kudin aikin da ake biyan masu aiki,nasan bekai ribarki ta sana'ar da yarinyarnan take mikiba" dariya gwaggo tayi tace, "wannan dayawa ne hajja, gidan alh. Menasaranefa take aikin, 200,000 duk wata haka nake jinsu dumus yanzu takai kusan wata tara tana aikin, kudina sunanan a ninke ina tarawa" galala hajja tayi tana kallon gwaggo, tsabar takaicima takasa magana.

Secan ta numfasa tace, "ladi, wlh wlh wlh idan bakiyi wasaba son kudinkine ze kasheki. Tsabar masifa kidauki yarinya kikaita aikatau,ke bakirasa ciba baki rasa shaba, yarinyarnan duk irin bautar datake miki amma be ishekiba sekin cutar da ita h...... "dakata hajja, wai meyasa kowa yazo seya dinga bankyautaba,bankyataba, danna kai maryam aikatau. Yarinyarnan fa tawace, duk wanda zesota abayana yake, kuma aikinnan data tafi, hutantane dacigabanta itama. Bakiga yanda ta canzaba tayi bul_bul abunta tayi fari kal kamar kya tsaga jini yafito ajikinta, kuma sunsata a makaranta to kuma mene faduwa anan,aganinama aise riba data samu" gwaggo takatse hajja dafadin haka cikin masifa. "Ladi,yakamata kidinga tunani akan abubuwan dazaki aikata kafin ki aikata, 200,000 yayi yawa a kudin aiki, ko aikin gwamanati sekana babban aiki zaka samu 200,000" dariya gwaggo tayi tace, "kinmanta kudin mutuminne hajja, kuma gashi da kyauta ance,koda maryam bata masu aiki ayanda ake fadar halinsu ze iya bamu kyauta"Hararar gwaggo hajja tayi tace, "gaskiya ladi haryanzu bakisan duniyaba, to bari kiji infada miki,masu kudi sunfiki son kudinsu, idanma zaki dawo cikin hankalinki kidawo kinsan inda yake miki ciwo. Haka kawai baza'adinga daukar makudan kudi ana baki amatsayin iya na aikin maryam, ninasan halin masu kudi,nazauna da manyan masu kudi, dan haka ina baki shawara kije kidakko maryam tunkafin kiyi danasani, kada kiyi sanadin abunda za'a cutar da marainiyar Allah. Ladi, kinsan illar cutar da maraya kuwa, kiji tsoron Allah mana ladi, duk abunda kikayiwa yarinyarnan abaya be isaba kiba sekin kaita inda........... "kinga dan Allah hajja, dakata. Niba wa'azai nace kizo kimunba, ku mutane bakwason fadar alkhairi sedai kuyita munana zato, maryam dai bazan dakkota daga gidan aikatauba, sena tara kudin zuwa saudiya da siyen makeken gida, dan haka ki sauraramun. Dan'uwan mijin innama yazo yayi nasa nagaji, dan haka kema kisauraramun,kibarni inyi abunda naso,daga zuwanki karki batan rai." Kallon gwaggo kawai hajja takeyi cike da mamakin shegen son kudi irinnata, gashi kuma kudinnata baya ciyuwa, tana dai danci acikinta, amma ko suturar arziki bata iya daurawa, kullum ita kenan bin gidajen masu adashi tana zubi. Sanin halin gwaggo na kafiya da naci akan abunda tasa agaba yasa hajja, ta kyaleta da maganar maryama,amma ta kudircewa ranta insha Allah setaje ta dakko maryam dakanta, danyanda duniyarnan ta lalace, ta safarar yara kanana yan mata zuwa kasar waje. itama sam hankalinta beyarda da wannan aikinba,ga uban kudin da'akace ana bayarwa,akan dan aikin gida. abunda mamaki sosai,dama can ita rayuwar yarinyar nabata tausayi. (Gwaggo, yakamata kiyi hankali mana, ayanda kawayenki da suke zugaki akan abunda kikeyiwa maryam ada, amma yanzu duk abunsu su suke kara tunatar dake,abunda kikayi badai_dai bane,amma kinkasa ganewa.)..........

********************

Awanni biyu sun shude,amma har lokacin su mommy basusan halinda mustapha yake cikiba,likitocin dai suna kansa har wannan lokacin. Haidar dakanshi yaje makaranta yadakko suhailat, aiko tana zuwa taji abunda yafaru ta haukata gurin da kuka, tana kiran abarta taje taga mustapha. Wata nurse ce ta tausheta tare da bata baki, aka samu tayi shiru da gunjin datakeyi, mommy kam zuwa yanzu ko magana bata iyayi. Daddyma yakirasu yakai sau biyar domin yaji yanayin jikinnasa, shima yanacan yanata cuku_cukun tahowa naija.

Se wajen daya saura likitocin suka fito gabadaya su mommy sukayi kansu da tambayar yaya jikinnasa. Dr, musaddiq wanda shine babba acikin likitocin ya dubi su mommy yace. "Hajiya ku kwantar da hankalinku munsamu numfashinnasa yadaidaita munma daura masa drip, tare dayimasa allurori,yasamu bacci yanzu" "to yanzu doctor zamu iya shiga muganshi" mommy ta fadi haka da saurinta. "Ehh, zaku iya shiga ku ganshi" ai ko gama rufe bakinsa Dr, beyiba suka nufi dakin dukansu. Duban yaya sadiq Dr, yayi ganin duk yafisu tawakkali yace, "abokina idan badamuwa kasameni a office mana, muyi magana" "ohk badamuwa" yaya sadiq yabashi amsa, tare da bin bayansa zuwa office dinnasa. Mustapha na kwance, akan gadon asibitin dakin dayake, shikadaine adakin se wani gado dake gefennasa. Kusa dashi su mommy suka kasara suka kura masa ido cike da jimami. Gaba daya jikinsu haidar yayi sanyi da ganin halin da yayannasu yake ciki. Duk'abun mutum idan yaga mustapha ahalin dayake ciki seya tausaya masa, lokaci daya ya zabge yayi wata uwar rama, ga numfashinsa dake fita a wahalce, bawan Allah shikadai yasan azabar dayake ji ajikinsa. Kuka suhailat ta fashe dashi tana fadin, "mommy yanzu yayane kwance ahaka kamar gawa, mom dubeshifa yanda yakoma,sekuma karasa gaban gadonnasa tana fashewa da kuka. "mommy kam takasa magana se girgiza kai kawai takeyi hawaye na malala a fuskarta.

Acan office din Dr, kuwa bayan sun shiga sun zauna. Dr yadubi sadiq yace, "sadiq! Agaskiya dan'uwanku yana cikin wani yanayi na mawuyacin hali, numfashinsa gaba daya yayi sama, dakyar muka samu muka shawo kan matsalar, saidaifa wata matsalar daban, duk binkicenmun munkasa gano meke damunshi takamaimai daya yashi a wannan halin,naso ace mahaifiyarku nayiwa wannan bayanin amma naga gaba daya naga a rude take, bazama ta fuskanci me nake cewaba, shiyasa nakiraka kai kazo domin na maka bayani." Numfasawa yaya sadiq yayi, cikin tsananin damuwa data kasa boyuwa har a fuskarsa yace, "doctor kaina gabadaya ya kulle narasama mezance akan wannan al'amarin,saboda jiya lafiya kalau muka rabu dashi, yau fa kawai akaga yatashi da wannan ciwon metayar da hankali,da sanya rudu a zuciya." "Haka dama ikon Allah yake yawuce gaban komai, wannan kadanne daga cikin ikonnasa. Fatanmu kawai Allah yabashi lafiya, yanzudai mun dibi jininshi zamu auna, insha Allah zamu gano inda matsalar take semusan abunyi" "tom shikenan Dr, mungode sosai bari naje naga jikinnashi." Musabaha sukayi sadiq yafice daga office din zuciyarsa Sam babu dadi.........

******************

Kasancewar yau Friday, 12:30 ake tashinmu, kuma duk ran Friday yaya sadiq ne yake zuwa daukata idan yana gari. Idan yadawo daga gurin aiki seya biyo mutafi kafin ya wuce masallacin juma'a. Jiransa natsayi a bakin gate din makaranta, amma shiru_shiru bezoba, babu shi babu driver,nasan wani babban uzurine yatsaidashi. Ganin nayi kusan mintuna 20 atsaye dalibai duk sun tafi, su zeema sunjima da tafiya,ga lokacin masallaci yakusato, nasan yanzu ankusa kashe hanya. Adaidaita sahu na yanke shawarar hawa kawai yakaini gida. dama makarantar tamu akan titi take. Guda daya na tare yace nakawo 100 babu bata lokaci na haye muka nufi gida. Har kofar gida yakaini na ya saukeni nabiyashi hakkinshi. Gaba daya jikina babu dadi kokadan, knocking nayi megadi yazo ya budemun, gaishesa nayi nawuce ciki. Maimakon nayi hanyar part dinmu, sena nufi part din yaya mustapha sonake kawai naganshi, naji dadi azuciyata. Harna kusa zuwa wata zuciyar ta tunatar dani yanzu hakafa yana masallaci saboda lokacin sallah yayi,tokodama bahakaba idannaje mezance masa? Juyawa nayi cikin sanyin jiki nakoma nanufi part dinmu. banci karo da kowaba a part din kasa hakama nasama. gaba daya part dinma tsit najishi. Dakina na wuce nayi wanka tare da dauro alwala, nayi sallah. Ina idarwa bayan nayi lazimi nakaranta khahfi. Kwanciya nayi saboda wani bacci dayake cina, inason naje nacewa mommy nadawo nakuma kunna wayata nakira yaya sadiq nasan yanzu shima yakirani yaji kona dawo gida,amma wani irin bacci nakeji, bari nayi nadan runtsa idan natahi nayi duk abunda zanyi.............

Karfe biyu na rana,a garin kano tayiwa aunty, danma a motor driver dinta yakawota, taso biyo jirgi sekuma taga ze bata mata lokacine kawai. Itakadaima tataho aliya tana school batamasan tatahoba se sallahu tabar mata gurin masu aikinta. Wayar sadiq takira yasanar mata asibitin dasuke suka nufi can. Su mommy ansha kuka ita da suhailat sun hakura sunyi shiru. Se tasashi dasukayi agama suna kallonshi. Su haidar kuwa dakyar sadiq ya taushesu suka nufi masallaci. Daddy ma yakirasu yace jirgin karfe uku zebiyo. Su aunty nashigowa asibitin suka hadu dasu yaya sadiq sundawo daga masallaci. Tunda aunty tagansu taji gabanta yafadi yanda taga fuskokinsu babu walwala kokadan kamar mustaphan mutuwa yayi, tatabbatar bakaramin jiki yake jiba. Ahanzarce ta fito bayan driver yayi parking, tabi bayansu yaya sadiq dasukayi gaba dansu basu gantaba. "Sadiq, sadiq" aunty ta kwalla masa kira lokacin data kusa cimmusu. Gabadaya suka juyo suna kallonta. "Aunty harkin karaso, sannu da zuwa" cewar sadiq. "Nakaraso sadiq yajikinnasa,ina fatan da sauki dai ko" "jiki alhamdulillah za'ace,sauki kam sena Allah." shiru aunty tayi jin abunda sadiq yace, hankalinta ya kara tashi,dama kwana 2 se mafarkinsa takeyi cikin mawuyacin hali. Gaisheta su zannurain sukayi asanyaye, itama ahakan ta amsa musu suka dunguma zuwa dakin dayake. Mommy nazaune ta rafka uban tagumi,kana ganinta kasan hankalinta sam ba'a kwance yakeba duk ta wani burkice. Doctor ne tsaye akan mustapha yana dubasa, bisa takurawar mommy,ganin mustapha yaki farkawa har yanzu. Da sallama dauke abakunansu duka suka dakin. Doctor ne kawai ya amsa musu amma mommy kodagowa ta kasayi, suhailat kam tatasashi agaba takasa motsawa daga inda ta zauna,se sauke ajiyar zuciya take saukewa akai_akai............ ALLAH baku Comments sosai

Meson complete Whatsapp 08166674823

*ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_

*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*

*Bismillahirrahmanirrahim*

3️⃣0️⃣

.........Karasawa kusa da mommy aunty tayi tagaisheta tare da tambayarta me jiki, cikin dashashshiya gami da sanyin murya mommy ta amsa mata. Tausayin mommy gaba daya yacika aunty, lokaci daya harta rame tayi zuru_zuru,kamar me jinyar itama. Gaisawa aunty sukayi da doctor dayake kokarin fita. "Doctor me'ake ciki ne, dan Allah kafadamun halin da dana yake ciki tun safe amma haryanzu kunkasa gano meke damunshi" mommy ta tsaida Dr, dake kokarin fita da fadin haka idonta na zubar hawaye. Asanyaye Dr yajuyo,shikansa jikinsa yayi sanyi da lamarin, sunyi kwajin jininma amma benuna musu akwai wani abu dake damunsaba, cikin son kwantarwada mommy hankali yace, "hajiya kikara hakuri munakan aikine, insha Allahu kafin dare zamu gano abunda kedamunsa" "to yaushe ze farfado" "shima nanbada jimawaba insha Allah,ciki gaba da masa addu'a kawai." shiru mommy tayi tana ayyana matukar mustapha be farfado ayauba sesuncanza asibiti, ita barima daddy yazo, kasar gaba daya za'a bari dashi. Gwara suje wata kasar aduba mata lafiyar danta. Cike da tausayawa aunty takebin mustapha da kallo, ita kanta bakaramin tsorata tayiba daganin yanda mustaphan yakomab lokaci daya, ahankali ta karasa daf da dashi takai hannu tataba goshinsa, zafin datajine yasata sauke hannunta dasauri, wannan wanne irin ciwone yake damun sa, zafin jikinsa ba irinna zafin ciwo bane data sani, nasa tamkar ana rura garwashin wuta, ga kuma bayanin dataji Dr,yanayiwa mommy na ba'asanma meke damunsaba. bin jikinsa tacigaba dayi da kallo,gaba daya jikinnasa ya shika ga numfashinsa dake fita dakyar. wani wahalallen numfashi aunty ta sauke afili ta furta. "Ya Allah,kabawa wannan yaro lafiya, kakawo masa sassauci da rangwame acikin wannan ciwon" gaba daya suka hada baki gurin cewa "ameen" jikin aunty gabadaya yayi sanyi, itakam wannan ciwo na mustapha ya firgitata ba kadanba, bata tunanin wannan ciwon na tashine. Kafadar suhailat dake gefenta ta dafa cikin rarrashi tafara mata magana. "Kiyi hakuri suhailat ba kukane mafitaba ahalin yanzu, addu'arki kawai yake bukata" aunty ta karashe zancen da share mata hawaye, ganin tunda tashigo dakin suhailat kuka kawai takeyi. Duk sesukabawa aunty tausayi, tabbas dole duka hankulansu ya tashi domin mustapha tamkar uba yake agurinsu duka, da daddy yana gari dabaya gari, shine ke musu komai, kuma duk da baya sakar musu fuska amma yajasu ajiki sosai, koyaya yaga wani sauyi atattare dasu ze tambayesu menene matsalarsu kuma ya magance musu ita,gwargwadon iyawarsa. mazauni aunty tayiwa kanta, sadiq yana bata bayanin ciwon mustaphan dakuma bayanin da likita ya masa.......

Seda uku na rana ta wuce natashi daga bacci, nayi mamakin dadewar danayi ina baccin, duk da sam baccin bayamun dadi kawaidai yinshi nayi. cikin sauri na sakko daga kangadona nashiga toilet na kuskure baki, dannasan yanzu haka mommy tanacan tana jirana, ga girki zanyi. Nayi zaton ganin yaran gidan a falo kasancewar yau Friday,amma senaga babu kowa. Kofar dakin mommy naje nayi knocking naji shiru, komawa kan kujera nayi nazauna, atunanina tana wani uzurinne,mintuna biyar suka shude naji shiru. Yanke shawara nayi kawai bari naje naduba may be bacci takeyi. Koda nashiga dakin senaga batanan, mamakine yakamani dan gaskiya da wuya kaga mommy batanan a irin wannan lokacin, kuma babu alamun tana toilet,amma nasan banisa tayiba tunda har tabar dakinta abude. Fitowa nayi nanufi kitchen nafara wanke_wanken dabanyiba. Harna gama nakoma dakina nayi sallar la'asar ko motsin bera banjiba a part dinba balle na mutum.

Se a lokacin nadakko wayata na kunna, ina kunnawa sakon yaya sadiq na shigowa,karantawa nafarayi acikin zuciyata kamar haka. _*my love,am sorry yau banzo na dakkokiba wani babban uzurine yatsaidani, dafatan kina lafiya,tun dazu naketa kiran wayarki akashe. need your du'a sweet*_ murmushi nayi tare da lumshe idona, aduk lokacin danaga wani sako na yaya sadiq koyamun kalamai na soyayya se'inji dama daga gurin yaya mustapha nake jinsu, tausayin yaya sadiq ne yakamani, ganinshi kullum cikin yin abunda zesani farinciki yakeyi amma ni kuma zuciyata naga wani can daban dabemasan ina yiba, aduk lokacin dana tuna haka se inji wani kunci yaziyarci zuciyata, da ina da yanda zanyi dana sauya sonda nakewa yaya mustapha zuwa ga yaya sadiq domin shiya cancanta zuciyata taso, amma kash nayi iya yina amma nakasa yin hakan, kullum son mustapha kara ta'azzara yakeyi acikin zuciyata.

bude idona nayi ina sauke numfashi, nanemo number yaya sadiq na danna masa kira. Sadiq dawowarsa kenan daga restaurant yaje yasiyo musu abinci bisa takurawar aunty, dataga alamar babu me niyyar cin abinci, shine tace yaje yayo musu take away, ba'azauna haka ba'aciba. fita yayi daga dakin rejecting yayi sannan yakara kiranta. dama nasan baze dagaba sedai ya katse, kullum yaya sadiq cikin sakamun kati yakeyi amma baya taba daga kirana, sedai nakira aliya ko salimat musha hirarmu. dagawa nayi tare dayin sallama, amsamun yayi. Senaji muryarsa kamar bashi da lafiya. "Yayana lafiya kuwa, naji muryarkar haka?" Natambayeshi cikin kulawa. Numfasawa sadiq yayi yace, "lafiya kalau maryam, ina kikashiga naita kiran wayarki akashe?" Batare dana yarda da amsar daya baniba, nace. "Agajiye nadawo daga school ne, kuma ina dawowa bacci yadaukeni bandade datashiba" "ohk" kawai yace yayi shiru. nima shirunnayi na wasu sakanni kafin na katse shirunnamu dacewa, "anya kuwa yaya lafiya kake, naji muryarkafa akwai damuwa acikinta,pls dan Allah kafadamun meke damunka" wani zazzafan huci ya fesar yace, "maryam gaskiya da akwai matsala,yaya ne yau aka wayi gari bashi da lafiya,cuta me tsanani yanzuma muna asibi.....wata muguwar faduwar gabace ta ziyarceni, cikin gigita na katse yaya sadiq da fadin" wanne yayan kuma?" "yaya mustapha mana" shima yabani amsa. cikin sauri nace, "meke damunshi" bayanin halin da mustapha yake ciki sadiq yayiwa maryam atakaice. Kasa magana nayi saboda tsabar tashin hankalin jin *heartbeat* bashida lafiya. wani uban gumine yahau karyomun ta ko'ina ajikina, dukda banganshiba amma gabadaya tausayinsa yagama cikamun zuciya, naji babu abunda nake da bukata duk duniyarnan sama danaje nagansa naga halin dayake ciki. "Hello,maryam" muryar yaya sadiq tadawo dani cikin nutsuwata. wani yawu me daci na hadiye dakyar cikin tattaro nutsuwata, da sanyin murya nace, "na'am yaya, yanzu yajikinnasa" "dasauki za'ace maryam" "Allah yakara sauki,yabashi lafiya" "Ameen maryam,bari nakoma ciki." Sallama mukayi yadatse wayar. Tagumi na rafka cikin matukar damuwa, Ashe dama bashi da lafiya shiyasa yau befitoba har rana. Wayatace tahau vibrate alamun kira. Ahankali nakai hannu nadakko, ganin aliyace nadauka dasauri. "Hello maryam Ashe yayan kano bashi da lafiya" "wlh aliya nima yanzu yaya sadiq yake sanarmun" "nima naje school ne nadawo natarar aunty batanan shine masu aikinmu suke sanarmun tataho kanone yaya bashi da lafiya,inata kiran wayarta taki shiga,shine nace bari nakiraki" hankali nane yakara tashi jin abunda,aliya tace. Kenan ciwonnashi ya tsananta matuka tunda har aunty dake wani garin tazo. bamuyi wata hirar kirkiba mukayi sallama, dukanmu zuciyoyinmu babu dadi,tadaicemun gobe zasuzo ita da abbansu. Zarya nafarayi adaki ina tunanin hanyar dazanbi inje asibiti ayau ingano yaya mustapha, dan inbanganshiba akwai matsala. yunwar danake jima tuni nanemeta narasa,hankalina gaba daya yanaga inje inga jikin *heartbeat* .........

Acan asibiti kuwa jikin mustapha ne yakara rikicewa numfashin nasa dayake fita dakyar dinma yadauke dif, hankalinfa su mommy gabadaya inyayi dubu yatashi, mommy ma faduwa tayi sedaukarta akayi itama aka bata gado, aka mata allura tasamu bacci. Suhailat kam kuka takeyi sosai iya karfinta, tana sumbatu tana fadin, "dan Allah yaya katashi karka mutu katafi kabarni" ire_iren wadannan kalamai kawai takeyi. Aunty kuwa babu kuka na ido sena zuci. Fitowa sukayi gabadayansu daga dakin dayake, sukuma likitocin suka dukufa akansa domin ceto numfashinsa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull