Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 25
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 25: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 25. ..........Gwalagwalaine a duddunk'ule tamkar duwatsu se…
2,685 words
..........Gwalagwalaine a duddunk'ule tamkar duwatsu se daukar ido da kyalli gami da walwali sukeyi. jikina na rawa nasaka hannu nadakko curi daya ina dubawa dannakara tabbatarwa. dan gani nake tamkar idonane kemun gizo,babu tantama gwalagwalaine acikin jakarnan. ahankali nadago ina kallon mustapha dake kwance yana bacci, ina tunanin wanne irin kudine da mahaifiyarsa haka dahar tabani wannan irin kayan dukiya haka, kamar kuma antsikareni sena mike dasauri nafice ina kwadawa atika kira domin tazo tatayani ganin abunda nagani ko idonane yake mun gizo. "Lafiya sulaiman kake kwadamun irin wannan kira haka sekace sabon makaho?" cewar atika tana yamutsa fuska. cikin rudu nace mata, "atika abun mamaki nagani, kema zokiga abunda nagani" banjira amsartaba najuya nakoma dakina tana biye dani abaya, da hannu nanuna mata jakar batare danace mata komaiba. tsugunnawa tayi tadakko *gold* din daya ahannunta tana dubawa. Zaro ido atika tayi waje cikin gigita tace, "sulaiman wannan ai gold ne ina kasamo su,waya baka,ko satowa kayi?" banbata amsaba se zama danayi agefenta ina kara fito da sauran ina dubawa. kara tambayata atika tayi akaro nabiyu da fadin"sulaiman tambayarkafa nake kamun shuru,kuma kana jina". Cikin daukewar tunani daga kwanyata nace mata. "Ranar da mahaifiyar mustapha ta bani shi aranar tabani acikin wannan jakar, ninama manta da ita seyau ina duba kaya naganta shine na dakko naga menene aciki senaga wannan abun nida farkoma nadauka nine bangani daidaiba,shiyasa nakiraki kitayani gan...." gani kawai nayi atika ta washe baki tatashi ta rangada guda gami da juyi tana rawa tana waka cikin tsananin farin ciki,batare data bari nakarasa zancenaba. sakin baki nayi kawai ina kallon ikon Allah. Surar mustapha tayi daketa baccinsa tahau yimasa rawa tana fadin. "Yaro ashe da arzikinka kake tafe, Ashe ta sanadinka mafarkina zecika inzama matar attajiri,kai amma Allah yayiwa mahaifiyarka albarka, nikam tagamamun komai arayuwata databawa sulaiman wannan irin dukiya metarin yawa" cikin tsananin mamaki nake dubanta baki bude, dakyar nayi dauriyar cemata, "atika mekikeyi hakane?" Bata kulaniba secigaba da juyi da mustapha datayi, aiko mustapha yace besan zanceba, yaji ana wujijjigashi tuni yafarka da kukansa. zama tayi tana lallashinsa abunda atika bata taba yimasaba tunda nakawoshi gidan. seda yayi shiru ta dubeni tace, "yanzu sulaiman semu dawo da tafiyarmu gida nankusa muje musaida wadannanan gwalagwalan muwataya mu fancakala muyi wadaka da dukiyar datazo mana, tsuntsu daga sama gashashshe" kallon mahaukaciya nayiwa atika sannan nace mata, "haba atika yadaga ganin dukiya hankalinki yabar jikinki gabadaya duk kinbi kin burkice, wannan dukiyar dakike gani bazan taba komai daga cikintaba, dukiyar marayan Allah ce, zan ajiye masa harzuwa sanda ze girma ya juya abarsa,kuma ni bana cire ran bazankara ganin mahaifiyar mustapha ba, ko wani nata, lokaci kawai nake jira dazannemomasa danginsa insha Allahu, kinga kuwa dazarar munhadu dole nabasu dansu da dukiyarsa" gabadaya fara'ar dake fuskar atika daukewa tayi hartana kokarin yarda mustapha dake kan cinyarta. Cikin takaici tace, "lallaikuwa sulaiman daka cika me bakin hali, mu raini yaron sannan kuma kace bazamuci dukiyarsaba salon inya girman yajuya mana baya, bayan mungama cin wahalarsa,wlh baka isaba abunda bazeyiyuba kenan,aka'idama wannan dukiyar tazama tamu tunda yanzu mune uwarsa mune ubansa,mune shansa da suturarsa"
Bankulataba saboda na fuskanci ganin dukiyarnan yana kokarin sakata maida haram halak agaremu. maganganu atika tayita fadamun akan dama bangaji arzikiba dole ince haka, tayi hakuri dani alokacin da babu yanzu kuma Allah yakawo mana hanyar arziki bazan toshetaba, dan haka dole muci dukiyarnan . nidai bankulataba namayardasu cikin jakar narufe na ajiye. tundaga wannan lokaci atika takoma nunawa mustapha kauna da kulawa da tarairaya fiye da tunanin me tunani, abunnata seya dinga bani mamaki, dama shi abun duniya yafi komai saukin canza halin mutum. Kwana biyu daganin wannan gwalagwalai mukayi sallama da mutanen garin niger muka dawo kasarmu me tarin albarka Nigeria tare da wannan dumbin kayan dukiyar. Munsauka lafiya agarinmu kano,agidanmu da muke kafin mutafi anan muka sauka, isma'il yakara gyara gidan saboda alokacin yasamu sana'a yanayi anan gando suke aikin kafintanci, anan muka tarar da saudart (aunty) tazo itama domin tarbarmu. Mustapha fa yasha dauka ranar agurin mutane, dama tun lokacin da mahaifiyar mustapha tabanishi bajimawa na musu aiken cewa atika tahaihu, shiyasa duk daukarsu mustapha dan cikinmune. Kowa se yaba kyawun da Allah yayiwa mustapha yakeyi, itadai atika sedai kawai ta kalli mutum amma badamar magana, dan tun lokacin danaga tana bobbotsarewa akan rikon mustapha nace mata duk ranar data sanar da wani mustapha badanmu bane a bakin aurenta, wannan daliline yasa taboye sirrin har kawo yau danake baku labarinnan bata taba fadawa waniba, domin babu karya atika tana tsananin sona batason rabuwarmu. anan gidan muka cigaba da zama, kullum atika tadinga damuna kenan da maganar dukiyarnan, nikuma gaskiya ina tsoron tabata danbansan ya matsayin hakan yake a musulunciba. danaga ta isheni sena nemi shawarar dan'uwana rabin jiki isma'eel nakuma fada masa yanda muka samu mustapha, isma'il yasha mamaki sosai yakuma tausayawa mustapha tare da yiwa mahaifiyarsa addu'ar Allah ya kubutar da ita yakuma kaddara saduwarta da danta. Shawara yabani akan muje gurin wani malamin addini kawai mutambayesa. Haka kuwa akayi mukashirya mukaje gurin wani babban malami namasa bayanin abunda yake faruwa,seyacemun. Zan iya juya dukiyar mustapha tunda mahaifiyarsa Lokacin data bayar cewa tayi nadauka zata taimakamun amma fa da sharadi tunda wata kila gadon mustaphanne idan yagirma zanbashi ragamar dukiyarsa gaba daya. Godiya nayiwa malam nace za'akiyaye insha Allah. Kodanadawo gida nafadawa atika abunda malam yace, seta tubure tace ita sam batayarda idan mustapha ya girmaba ace masa dukiya tasaceba, kawai nabarta amatsayin tawa. nikuma nacewa atika bata isaba maganar Allah zanbi batataba, akan hakan harfada mukayi da atika. Isma'eel ne yahadani da wani baban abokinsa dayake sana'ar saida gwalagwalai, acikin gold din ko rabi bandibaba amma danaji kudinsu seda na girgiza domin milliyoyi aka siya tun a wancan zamaninma. danaga harkar gold din ana samu sosai senace bari kawai nima nakoma harkar saida gold din. Sauran na dakko aka narkamun zuwa sarka da dankunnaye gami da zobuna,wannan shine farkon silar arzikina a duniya. cikin watanni kadan cinikifa yabude kudi se zuwa sukemun kota ina, nikaina har tsorata nayi kar'a zargeni domin gwalagwalannan kudi suke kawowa bana wasaba. nanfa yan'uwa sukamun caa da tambaya ina nasamu wannan uban jarin haka dare daya, nanna sanar musu, ubangidane dani agarin Niger shiya dorani akan dukiyarsa, dayake bawani damuwa sukayi da lamarinmuba sebasu wani tsananta binkiceba. Ganin arziki yasamu atika tatada balli akan ita bazata haihu agidan damukeba sena sake mana gida mekyau na yangayu. Naso ki,amma isma'eel yace namata babu komai ai. Anan unguwar tarauni nasai wani katon fili natamfatsa ginina me matukar kyau nazamani muka koma. Burin atika yacika tafara shiga sahun matan attajirai. Ko kwana goma bamuyi da komawaba atika tahaifi danta namiji nasa masa suna *abubakar sadiq.* bayan haihuwar abubakar bajimawa Allah yayiwa marikin atika rasuwa, bayan yasha doguwar jinya. kafin yarasu seda atika tanemi gafararsa bisa takurawata akan abunda tamasa a lokacin auranmu. Munji mutuwar tasa sosai,bayan sadakar bakwai atika ta dakko kanwarta jamila tadawo hannunta da zama. Arzikina kara habaka yakeyi abun har mamaki yake bani. hakan yasa nafara saro kaya daga kasashen waje ina saidawa. kafin wani lokaci arzikina yahabaka sunana yafara kewaya sassa na garin kano a jerun masu kudi, nakasarwa atika bakin aljihu tana wadaka da kudi son ranta. tasa abunda takeso taci abunda takeso. Cikin ikon Allah kuma se atika take ta haihuwa akufai_akufai, dan sadiq beyi shekara biyuba tahaifi faruq, shima befi shekara biyuba ta haifi yan biyu haidar da zannurain daganan kuma haihuwar ta tsaya mata. atika macece me matukar son yayanta bata kaunar lefinsu kokadan, amma soyayyar datake nunawa mustapha daban take, nikuma banyi tunanin komaiba dadin hakanma nakeji dannayi tunanin sauyin rayuwar da muka samune yasata sassauta masa. soyayya ce ta kullu tsakanin isma'eel da jamila kanwar atika, munji dadin hakan sosai dan gaskiya atika ba halinsu daya da jamilaba, jamila yarinyace me hakuri da hankali babu ruwanta. tana gama makaranta akayi bikinsu tare aka hada dana saudart. ansha shagali sosai,lokacin su zannurain basufi shekara ukuba a duniya. Zuwa lokacin nashahara akudi sosai nashiga sahun attajiran kasarnan sunana ya yado a birni da kauyuka. Samun kudina besani girmankai ko kyamatar talakaba. har lokacin kowa nawane kuma abun hannuna berufemun idoba base nafadaba kunsan kyautata ba yabon kaiba. Sabanin atika data dauki girmankai da izza gamida kasaita ta dorawa kanta, matan yan siyasa da manyan masu kudi sune abokan huldarta, yan'uwanta kuwa danawa ko kallo basu ishetaba. ta raina arzikinsu tafi karfin ta kulasu. Nagina masallatai da makarantu da kamfanunnuka nadora abokanaina akai da yan'uwa. na hakawa iyayena dasuka rigamu gidan gaskiya rijiyoyi da fanfuna akauyuka da gurararen da suke bukatar ruwa. har saudart tayi haihuwar fari jamila bata haihuba, nanfa tatada hankalinta harda koke_koke domin ita macece meson yaya, nida kaina nabata hakuri da banbaki nace bataga yanda atika tayibane yanzu kuma da Allah yabata haihuwar gashi hartayi yaya biyar. takara hakuri komai lokacine. cikin ikon Allah ba'afi shekara biyu da zancen haihuwarba itama Allah yabata haihuwar diya mace. Zokuga murna gurin ahalinmu domin dukkanmu bamu da diya mace, saudart ma namiji ta Haifa. Ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyarmu Ummukulsum amma ana kiranta da *suhailat* suhailat tataso cikin soyayyar yan'uwa da iyaye kasancewarta ita kadaice mace, kowa sonta da riritata yakeyi amma babu kamar atika. Mustapha nema baya nuna mata wata kauna, domin shi damacan tun yana yaro miskiline nakarshe kuma bayason hayaniya ita kuma suhailat akwai kuka da tabara shiyasa sam basa shiri. Bayan arba'in dintane muka dawo wannan gidan dana tamfatsashi, part din da mustapha yake yanzu anan isma'eel yazauna shida medakinsa jamila. hakan yasa kullum suhailat tana gurinmu shan nonone kawai ke maidata gurin mahaifiyarta. Arziki nadada bunkasa yayin da burukan atika nadada yawaita, munjejje saudiya munsauke farali gami da umra akaro dayawa. Akullum cikin fadawa atika da isma'eel nake kobayan raina idan mustapha ya mallaki hankalin kansa su damkamasa dukiyarsa gabadaya a hannunsa. domin ko mutuwa nayi yayana basu da gado acikinta. Wannan magana tawa bakaramin bakanta ran atika takeba a duk sanda nafada mata haka. Haka rayuwa tayita tafiya kullum samuna kara gaba yakeyi kamar yadda nima kullum cikin sadaka da bada kyauta nake, domin banmanta halin danashigaba lokacin ina halin talauci. Mustapha primary school kawai yayi anan kasar atika ta matsa sedai afita dashi waje yakarasa karatunnasa, kin amuncewa nayi amma nacin atika yasa nabarsa yaje yayi,shima ba'ason ransaba umarnin mahaifiyarsa kawai yabi yatafi. Ranar bakin ciki arayuwata ranar dabazan taba mantawa da itaba itace ranar da isma'eel yayi hatsari ya mutu shida medakinsa ahanyarsu ta zuwa abuja, fadar irin tashin hankalin damuka shiga a lokacin rasuwar su isma'eel baze faduba. mutuwar ta shigeni sosai nayi rashin dan'uwa Rabin jiki abokin shawara gakuma tsananin tausayin suhailat da maraici yasameta tuntana yar karamarta. danma karfin rikonta ahannunmu yake dantamafi shakuwa da atika fiye da mahaifiyarta. daga gaisuwar isma'il da mustapha yazo yace baze koma karatu wajeba, alokacin saboda atika bata son bacin ransa tahakura badon tasoba yadawo gida dazama. Bayan mutuwar su isma'il atika suka tafi kasar turkey ita da yara duka mustapha ne kadai bandashi yace baze busuba, se yakoma gurin saudart da zama. anan yakarasa Senior class dinsa, saboda su atika sundade a turkey dansunyi kusan shekara 4 sannan suka dawo, nima se zamana yafi karfi a can tunda iyalina sunacan,nan kuma da masu kularmun da dukiyata. bayan sun dawo mustapha yakoma america domin cigaba da karatunsa anan yayi degree dinsa nafarko dana biyu har *PHD* dinsa.
Tundaga lokacin da isma'il yarasu abubuwa suka fara tabarbarewa, nazama tamkar uwargijiya da baiwarta tsakanina da atika se'abunda tace nayi shinakeyi, kuma duk abunda zatayi nabadaidaiba ban isa na tsawatarmataba. Tarabani da yan'uwana dama ita nata bawani damunta sukayiba. yarama kowa abunda yakeso shiyakeyi babu me kwabarsu,bankuma isa natsawatar musuba. Alokacin ne kuma namanta da batun dukiyar mustapha cefa a hannuna ina juyata, senaji kawai tamkar damacan dukiyar tawace. Burin danake dashi na insanar da mustapha dukiyarsace da kuma burin komawa garin Niger domin nemomasa danginsa duk yakau daga kwakwalwata nama manta dashi gabadaya, sabanin da da kullum da tunanin hakan nake kwana nake tashi araina. kawaidai abunda nasan nayi duk wani harka ta kasuwancina ina saka mustapha akan gaba, sauran yayanama kowa yagama karatu zandorashi akan harkar kasuwancina. Wannan shine takaitaccen labarin dazan Baku, dakuma yanda muka samu mustapha." shiru dakin yadauka bakajin motsin komai se karar fanka da sassauke numfarfashi da kowa yakeyi. Gabadaya bakunansu sun musu nauyi sunkasa sarrafa harshensu balle susamu damar koda furta harafi dayane, saboda tsabar mamaki gami da al'ajabi da jimami. Mustapha kawai kallon daddy yakeyi tunda yafara bada labarin, wani irin yanayi yakeji ajikinsa me wuyar fassaruwa,yanda yakejin zuciyarsa tamkar ana rura masa wutar garwashi acikinta, gani yakeyi tamkar daddy kirkirar labarin yayi kawai ya basu. tayaya ze iya daukar wannan bakon al'amarin ace mominshi me kaunarsa meson ganin farincikinsa akodayaushe ba'ita ta haifesaba. ahankali ya yunkura idanunsa a lumshe tsabar damuwa ko gani bayayi ya mike yana layi ya karasa gaban mommy yadurkusa yakama hannunta, cikin wahalalliyar murya menuni da me ita shikadai yasan azabar dayakeji yace, "mommynah, nike nasani amatsayin mahaifiya kuma kenaso nacigaba da kallo amatsayin uwata dan Allah kimusantamun abunda daddy yafada konaji sanyin tafarfasar da zuciyata takemun,wlh kwakwalwata bazata iya daukar wannan lamarinba" wani irin kallo mommy tamasa me wuyar fassaruwa tana murmushin mugunta tace, "mustapha kada ka bata bakinka gami da wahalar dakanka akan abunda yake na gaskiya zuwa wanda bashi bane. ninan atika dakaganni banasonka bana kaunarka mesonkama bana sonshi imfact madai duk duniyarnan babu wanda na tsana sama dakai mustapha, saboda haryau zuciyata bata yarda da zancen sulaimanba, nafi yarda da ciki yayiwa wata a waje ta haifeka" mommy tafadi haka babu alamar nadama a tatattare da ita. Gabadaya yarannata ido suka zuba mata suna kallonta yanda take magana babu alamun rahama akan fuskarta. Aunty kuwa kanta nakasa tana karanto addu'ar samun nutsuwa domin kuwa yanda taji al'amarin a baibai waiba mommy ce tahaifi mustapha ba, kuma duk irin tarin soyyayar datake nuna masa ashe duk na muguntane,lallai mommy ta iya zagon kasa,kuma ta cika cikakkiyar makira. mustapha cikin fitar hayyaci yakara damke hannun mommy idanunsa nazubar da hawaye yace, "mommy meyasa bakya sona wanne lefi namiki arayuwa, please and please mommy kisoni sona gaskiya nike kadai nasani amatsayin uwata kome zakimun kuwa bazantaba canza matsayinkiba,domin banida kamarki" dagowa aunty tayi tana kallonsa cike da tausayawa idanunta nazubar da hawaye, yanda yake kuka yana rokon mommy, abunda ta manta rabon dataga kukansa, domin shi mutum ne mejuriya akan komai. tabbas akwai tashin hankalin da idan yazowa mutum duk jarumtarsa be isa ya jure masaba. daddy ma cike da tausayawa yake kallon dannasa abun kaunarsa, duk da daddy yasamu wasu yayan amma bayajin kaunarsu kamar yadda yakejin ta mustapha,kaunar mustapha daban take acikin zuciyarsa. Faruqne ya matso yakama mustapha yarungumeshi ajikinsa. shima idanunsa nazubar da hawaye yace, "yaya mustapha dama nine kai, domin kai kayi sa'ar mahaifiya sabaninmu dabayi sa'artaba, mahaifiyarka tazabi mutuwa kaikuma karayu saboda tsananin kaunar datake maka,amma mu mommy da kanta take cutar damu duk dan akan duniya tabbas nasan idan kaji irin abubuwan da mommy tamaka na cutarwa zaka tsaneta, kuma bakaikadai ta cutarba harda wasu bayin Allah dabasujiba basu ganiba duk domin dukiyarka ta zamo mallakinta ita yayanta,inama ana canza uwa dase nazanca mommy wlh, domin bata da imani kokadan" yakarashe zancen yana fashewa da kuka meban tausayi. mommy ce ta amshe zancennasa da fadin, "bana nadama kodanasani arayuwata tunda nafarata, kuma ayanzuma banyiba kuma bana fiddaran zanci nasara akan abunda nasa gaba,domin duk abunda na kudura arayuwata sena cimma nasara akansa komeneshi kuma komun wuyarsa ko....." "ba'aiwa Allah izgili kada kiga kinsamu nasara abaya kiyi zaton zaki kara samu nangaba, insha Allahu alkadarinki ya karye daga yanzu, kuma da sannu zaki girbi *abunda kika shuka* da hannunki" daddy yakatse mommy da fadin haka cikin tsananin bacin rai gamida takaicinta tare da danasanin kasancewarta matarsa. Mommy batabi takan maganar daddyba. tadubesu duka tace, "bari na baku kadan daga cikin labarin irin abubuwan dana aikata duk domin nasamu biyan bukatar raina" gabadaya ido suka zuba mata akaro nababu adadi amma banda sadiq dakansa yake a sunkuye tunsanda daddy yafara bada labari. Mikewa mommy tayi tai taku uku sannan ta fara magana kamar haka:..........✍️
*BY* *zeey kumurya*
*ABUNDA KASHUKA* _*(shizaka girba)*_
*3️⃣8️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*