Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 24
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 24: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 24. Watarana ina zaune a kasuwa bayan anyi sallar la'asar…
3,285 words
Watarana ina zaune a kasuwa bayan anyi sallar la'asar naji ankira sunana,cike da mamaki najuya jin muryar abokina sa'idu,cikin mamaki nace, "sa'idu dama rai kanga rai" danrabona dashi tunda yasamarmun aiki agurin megidana. "Gashi kuwa munhadu sulaiman, tun dazu nashigo kasuwar inata nemanka se nura yace inzonan zansameka" gaisawa mukayi cikin farincikin ganin juna, se kallon sa'idu nakeyi yanda yacanza daga gani kudi sunzauna masa, tambayata yayi menakeyi yanzu nace masa buga_buga ce kawai tunda alh, yarasu har yau bansamu wata kwakkwarar sana'aba. jimantamun sa'idu yayi sosai, yace idan zan iya zuwa *NIJER* indinga saida takalma zebani jari narasa nadinga kaiwa can, danshima sana'ar dayakeyi kenan acan shiyasama yabarnan, kuma harkar akwai samu sosai acikinta. shiru nayi ina nazari dagacan kuma nace masa, "toyazanyi da iyalina tunda idannace zantafi dasu candinma bani da masauki kuma bani da kudi balle inkama mana haya" murmushi sa'idu yayi yace, "wannan duk ba matsala bace, zakabar iyalinnaka anan gidane, kafara zuwa kaikadai kafin muga abunda Allah zeyi, zuwa lokacin dazaka samu abunda ake fata seka dauketa kukoma can gabadaya, idankatashi sarar kaya sekazo kaikadai kakoma." godiya nayiwa sa'idu sosai nace masa zanje gida nayi shawara tukunna, yacemun ba matsala idannayi shawarar abunda nayanke zezo gobe mu hadu, seyaji. Koda nakoma gida sena nemi shawarar isma'il akan abunda sa'idu yazomun dashi,aiko isma'il yayi murna sosai, kuma yacemun na amince damace Allah yabani,nanemi albarka abun kawai natafi nafara. banfadawa atikaba seda mukagama magana da sa'idu muka shirya komai yanda abun zekasance, har Lagos mukaje muka saro takalman, nanfa atika tatubure sedai mutafi tare dakyar nasamu na lallabata bayan na cikata da kudi, dannasan mutuniyar tawa akwai son kudi, nakuma ajiye musu komai dazasu bukata itada isma'il ishashshe, alokacin nayi niyyar dakko saudart domin tataya atika zama, amma marikiyartata taki bada ita, dansunsan halin atika ba mutunci garetaba.
Cikin ikon Allah,mukaje nijer lafiya nida sa'idu nakuma fara sana'ata itama da taimakon sa'idu. Naji dadin zama akasar nijer sosai, inda cikin dan kankanin lokaci nasaba da mutane, nakai kusan wata biyu sannan nazo ganin gida, anan na tarar da wani mummunan labari na barewar cikin danabar atika dashi, gashi atika tazama jarababbiya kullum se fada da makota da yawon gantali, isma'il yacemun yana iyakacin yinsa wajen ganin yahanata amma taki hanuwa, banyi kasa a gwiwaba nazaunar da ita namata nasiha takuma nunamun tadauka. Tundaga wannan lokacin nakoma safarar takalma daganan gida Nigeria zuwa kasar nijer, kuma alhamdulillah Allah yadafamun ina samun alkhairi sosai acikin sana'ata. Banfi shekara da fara zuwaba nadauke atika muka komacan Inda nakama mana haya a can din mukacigaba da rayuwarmu, tunda zamana acan yafi yawa gwara ace matata tana kusa dani, yan'uwana kuwa ina musu aiken kudi yanda yakamata. tundaga wannan barin cikin da atika tayi bata kara koda batan wataba, gashi ni kuma Allah ya halicceni mutum ne meson yara, kullum cikin addu'a nake, Allah ya'azurtamu da samun yaya. Atika taso dakko kanwarta jamila tadawo hannunta da zama lokacin dazamu koma nijer,amma kanin mahaifinta yace baze bataba.
Rayuwa tasauyamun sosai nasamu budi da nasara aharkar kasuwancina sosai, nasamu rufin asirina daidai gwargwado. abokina sa'idu shine yasamun sunan *menasara* daganan sunan yabini wasuma idan kace musu sulaiman bazasu sugane nikake nufiba sekace musu *menasara* watanmu shida dakomawa nijer dazama nida atika, Allah ya'aiko mana da wani iftila'i, kayana na shago sunkare kaf, natattara kudadena a buhu, zanzo gida nayi siyayya, lokacin account beyi yawaba, dama tafiyar dare mukayi yan fashi da makami suka tare motarmu akan hanya,suka kwace komai namu dagamu se tufafin jikinmu sukabarmu, se juyo damu driven yayi domin dama yawancinmu sare_sare zamu kuma gashi ankwace kudin sarin, dayawa daga cikin wadanda muke a motar kusan zaucewa sukayi,manyan maza magidanta segamu da kuka shabe_shabe da hawaye. wannan fashin da'aka mana bakaramin talautamu akayiba, danseda takai ta kawo naira biyarma gagararmu takeyi, dan abincin da sauran kudin da'akabarwa mata agida duk ancinyesu. Nashiga cikin tsananin tashin hankali bakanba a wannan lokacin narasa ina zantsoma kaina, gashi ko kudin motarma dazan mana mudawo gida Nigeria nida atika kozan samu abunyi anan babu. Alokacinne kuma atika ta fitomun da ainihin halinta na rashin imani da tausayi, kullum cikin yimun tijara da rashin mutunci take, akan rashin da Allah yadoramun, bata ganin nima bayin kaina bane. Kaddarace Allah yadoramun dakuma jarrabawar rayuwa. Watarana da daddare ina zaune a tsakar gidanmu ranar munwuni bamuciba nayi tagumi ina tunanin yanda rayuwa tazomun atika tafito daga daki ta tsayamun aka cikin masifa tafaramun magana, "sulaiman yanaganka anan kazauna, wato bazakaje kasamomun abunda zanciba, mekake nufine, sedai inyi tazama da yunwa ta takasheni" janye tagumin danayi, nayi cikin rarrashi nafara mata magana da fadin, "dan Allah atika kiyi hakuri, kinga yanzu dare yayi bansan inda zannufa insamo miki abunda zakiciba,amma kibari zuwa safiya insha Allahu zannemi koda wankaune domin inbaki abunda zakici" rike kugu atika tayi tace, "wlh baka isaba sulaiman yau bazaka kwana agidannanba seka nemomun abunda zanci, danbazan zauna yunwa tamun lahani abanzaba" cikin takaicin halin atika na rashin tausayi nace, "haba atika amma kinsan nima babuce Allah yadoromun lokacin da ina dashi aina baki abincin" "kaga sulaiman nifa babu ruwana da wani babunka nidai kawai kanemomun abunda zanci, tunda kai kakawoni nan ka'ajiyeni danhaka dole kasamarmin abunda zanci, dankasan shi ciki besan wani babuba ehe" bancemata komaiba namike nafice daga gidan, lokacin goman darema ta kusa. Duk inda nasan zanje insamo wa atika koda biscuit ne amma naje bansamoba, haka nadawo gida jikina asabule lokacin dare yafarayi dan 12 saura, atika harta rufe gida, kwankwasamata nayi ta bude, koda taga hannuna babu komai seta maida kofar gidan tarufe tana fadin wlh bazan shigoba matukar bansamo mata abunda zataciba. wani bakin cikine yaziyarceni nida gidana amma ahanani shiga, meyasa atika bata tausayinane nimafa yunwarnan nakeji amma tunsafe nake yawon nema mata abunda zataji amma bata gani. Wata shawara zuciyata tabani akan naje unguwar masu kudi mana, inrokesu su sanmun koda danyen abincine inkawowa atika tadafa, ko tunanin dare banyiba nakama hanya natafi dukda nisan dake tsakaninmu dasu. ina tafe nakadai tunkis tunkis harna shigo wata unguwa dako sunanta bansaniba amma dai ta masu kudice, kowanne layima da gate dinsa kuma duk an rurrufesu,tsayawa nayi ajikin wata bishiya ina maida numfashin wahala, tunaninma tayanda zan iya komawa gida nakeyi dannagaji likis ga kishirwa dake damuna. ahankali nafarajin taku daga bayana alamar ana gudu, cikin tsoro najuya ina karanta addu'a acikin raina, mutum na hanyo yana gudu da dukkan karfinsa, seda ya matso kusa naga Ashe macece goye da yaro hannunta kuma dauke da wata jaka. Cike da mamaki da tsoro nake kallonta kamar yadda itama ta tsaya cak tana kallona. Cikin karfi hali nace, "baiwar Allah mutum ko aljan?" Cikin hausarta dabata fita sosai tana haki tacemun. "bawan Allah mutum ce ni kamarka" bata jira mezancemataba ta hau kici_kicin kunce dan bayanta bayan ta ajiye jakar hannunta akasa. niko tsayawa nayi kawai ina kallonta cike da mamakin meya fito da ita daga gida cikin darennan, gata yarinya karama danko atika batayiba gata fara jajur kyakkyawa da ita kana ganinta kaga cikakkiyar buzuw..... Katsemun tunani tayi ta hanyar mikomun jaririn hannunta tana kuka tana fadin, "bawan Allah, dan Allah kataimakeni kagudarmun da jaririnnannawa,wlh kashemunshi zasuyi,kuma yanzu suna dubawa basu ganniba zasu biyo bayanane, nikuma dasu kashemun dana gwara ni sukasheni shiya rayu, kataimakeni kagudarmun dashi shikadai Allah yabani, banaso narasashi,wlh dana dan halak ne da ubansa, shima babannasa sun kasheshi shine shima yanzu sukeson kasheshi" takarasa zancen tana fashewa da kuka, tsayawa nayi kawai ina kallonta zuciyata namun wasi_wasi akan abunda tace. "Kataimakeni, sunkusa karasowa, karikemun dana da amana dan Allah,kagudarmun dashi karsu karaso su kashemunshiiiiiiii!..............✍️
Meson complete Whatsapp 08166674823
ABUNDA KA SHUKA.........* _*(shizaka girba)*_
*3️⃣6️⃣*
...........Tsayawa nayi kawai ina kallonta cikin kura ido, domin tabbatar da abunda take fada har cikin zuciyarta gaskiyane. Kasancewar gurin da wadatar hasken kwayayan gidan mutane ina ganin yanda hawaye yake zuba daga idanunta tamkar ankunna fanfo se shatata yakeyi. Cikin tsananin tausayawa nakai hannu nakarbi yaron daketa bacci abunsa, duk wannan uban gudun da mahaifiyarsa tasha amma be farkaba. "Suwaye zasu kashe miki danki, kuma akanme?" Na tambayeta ina kallonta bayan na karbi yaron. girgizamun kai tahauyi cikin kuka tace, "babu ishashshen lokaci dazan makama bayanin kosu suwaye,amma dai su mugayene azzalumai wadanda san duniyarsu yamantar dasu Allah, sun kashemun mijina, nima basu kyaleniba Neman rayuwata sukeyi data dana,duk akan abun duniya." wani numfashi taja tare da runtse idanunta tace, "kagudu karsu karaso,domin ni nasan duk inda nashigama agarinnan,sesun nemoni sunkasheni,kadauki wannan jakar zata taimakeka arayuwa" batajira amsataba ta bude idonta takurawa danta idanunta dasuke zubar hawaye, sumbatar goshinsa tayi gami dayin magana da yarensu cikin kuka me karya zuciyar mesaurare. Har cikin zuciyata nakejin kukan matarnan, tsabar tausayinta ita da danta nama kasa magana, se kwalla data cikamun idona. Ina shirin kara mata magana najiyo taku alamun ana tahowa inda muke, dasauri muka juya dukanmu nida matar daga inda ta bullo daganan takun yake tahowa, nikaina ba itaba bakaramin tsorata nayiba domin ga dukkan alamu wadanda take fadane suka biyo bayanta bisa ga yadda naga duk ta firgice. Rungume yaron nayi a kirjina da hannun haguna, hannun damana kuma na rarrafa nahaye kan bishiyar damuke tsaye akasanta, domin nanne kadai gurin dazan iya buya bazasu ganniba. cikin ikon Allah kuwa nahaye bishiyar tamkar dan biri ina maida numfashi, ninama manta da jakar datacemun indauka seda naga tadauketa ta ziramun acikin wani kurmin bishiyar. Sannan ta ruga da gudu ta miki wata hanya, ko minti 4 bata cika da tafiyaba wasu mutane guda hudu suka karaso gurin, hannayensu dauke da fitilu hanyar da matar tabi nan suka mika suma da gudu, naji sunyi magana cikin yarensu na buzaye amma banfahimci mesukaceba ga dukkan alamudai hango matar sukayi.
wata nannauyar ajiyar zuciya nasauke bayan sunbar gurin,wani matsanancin tausayin matarne yakamani,lallai mahaifiya, mahaifiyace tazabi danta yarayu ahannun wanda bata saniba,batasan daga inda yakeba akan akashemata shi, tazabi ita tarasa rayuwarta danta yarayu. wasu zafafan hawayene suka shiga kwaranyomun inajin dama zan iya danaje nataimaki matarnan daga hannun azzaluman mutanen data ambata. rokon Allah nashigayi akan Allah ya kubutar da ita, insha Allahu bazasu samu nasara akantaba. Nakai kusan minti talatin akan bishiyarnan ina sakawa da kwancewa sannan nadiro jikina asanyaye. Jakar data ajiyemun nadauka senaji jakar da nauyi,mamakine yakamani ganin yanda matarnan ta iya gudu da ita ga kuma goyon yaro abayanta, kodayake gudun ceton rai bazataji nauyin komaiba. Goyo yaron nayi abayana nadauki jakar naruga da gudu zuwa gida, domin nima a matukar tsorace nake, gani nake kamar mutanennan zasu iya dawowa su riskeni. yunwa da gajiyar danakeji ada gabadaya yanzu sunbar jikina,burina kawai inganni acikin gidana na tseratarwa da matarnan da danta.
Cikin ikon Allah, nakarasa gida lafiya alokacin tsakiyar darene gari yayi shiru, se haushin karnuka da kukan tsuntsaye. Nadade ina kwankwasa kofa kafin atika tazo tabudemun kofar. nasan bacci tafara, aiko ko tsayawa batayiba ta juya takoma dakinta, ni dadin hakanma naji,danbansan yanda zamu kareba idan taga yaron bayana. Dakina nashiga na kunce yaron nashimfideshi akan tabarmar dake dakin bayan na kunna light haske ya gauraye dakin. kurawa yaron ido nayi cikin tsananin tausayinsa, gashi kyakkyawa dashi fari kal harwani pink_pink yake tsabar fari. hannuna nakai nashafa kwantacciyar sumar kansa baka sidik, so da kaunar yaron nashiga cikin raina afili na furta. "Ya Allah, karaya wannan bawannaka, kabani abunda zan iya rikeshi,kakuma bani ikon rikeshi bisa amana batare dana cutar dashiba" badon nagaji da kallonsaba na mike nabude wata tsohuwar jakata danake ajiye abubuwa nasaka jakar da matarnan tabani aciki na mayar na zuge na ajiye. kamar ance injuyo naga yaronnan ya bude idonsa yana wawure_wawure da hannunsa yana kaiwa baki dasauri nanufeshi nadaukeshi, aikuwa yabude baki yacanyara kuka, jijjigashi nahauyi cikin son yayi shiru amma ina tamkar kara zugashi nayi se ihu yake da dukkan karfinsa abun tausayi. Se'alokacin nayi tunanin watakila yunwace take damunsa,nanfa hankalina idan yayi dubu yatashi domin banda abunda zanbashi acikin gidannan. Yana hannuna nafita dashi domin nabashi ruwa ko Allah zesa yayi shiru kafin safiya nanemo abunda zanbasa. Atsakar gidan nayi kicibus da atika tafito a hargitse. Gabanane yayanke yafadi danbansan yanda atika zata dauki maganar yaronnanba, tsayawa tayi cak tana kallona cike da tsananin mamaki kafin naji ta lailayo wani uban ashar gami dacewa, "sulaiman mezan gani haka, jariri ahannunaka ina kasamoshi, ina cikin baccina naji kukan yaro yacikamun kunne kamar amafarki, shine nafito inleka waje inga tsinannen yaro daya hanani bacci, kuma se'inganshi acikin gidana" bance mata komaiba harna debo ruwan akofi nazauna nakafawa yaron abaki, nandanan kuwa yakama wawurar kofin da baki abun tausayi yahau kukkutar ruwan, sedayasha kusan rabin kofin sannan nacire kofin daga bakinsa kuka yasaka alamun ruwan be'isheshiba. kara mayarmasa nayi yakarasha, atikadai tana tsaye tana kallon ikon Allah.
seda yakarashan ruwan sosai sannan na'ajiye guntun ruwan. bekarayin kukanba hakanyasa na kwantar dashi akan kafadata ina shafa bayansa, abunda yakara burgeni da yaron yanda yake tsaf sewani daddadan kamshi dake tashi ajikinsa. Kallon atika nayi nace tabiyoni dakinta muyi magana, masifa tahauyi wai maganar mezamuyi ita kawai nafada mata inda nasamo yaro, maimakon nakawo mata abinci sedai kawai taga nashigo mata gida da yaro. Juyin duniya atika tashiga daki muyi magana amma taki, dole haka namata bayani atsakar gida. Bala'i da masifar da atika tamun adarennan baze misaltuba tijira kala_kala akan sena fita da yaron daga gidan,kilama wata naje nayiwa cikin shege ta haifamun dan shine zanzo inhada karyata gata wacca batasan metakeba akawomata rainon shege gida. maganganunta sunbatan rai amma dai haka nadaure naki kulata nashige dakina nabarta atsakar gida tanata hayagaga makota najinta.
dakinma bantsiraba haka tabiyoni taitamun tijara. Halaccin da atika tamunne kawai yasa adarennan bantsige igiyar aurena akantaba,amma raina yabaci matuka danne zuciyata kawai nayi bankulataba. Ranar yanda naga dare haka naga rana,ga kukan dayaron yashigayi shima tamkar ana zarar numfashinsa nasan yunwace take damunsa. Seda asuba nasamu yayi bacci, harnaje masallaci nadawo betashiba. Alokacin banhakuraba nakara zuwa dakin atika nabata hakuri dannasan kowacce macece rana tsaka mijinta yakawo mata jariri gida da tunanin dazatayi, da kyar nashawo kan atika tahakura zamu rike yaronnan,amma seda namata uwar magiya daban baki gami da rantse_rantse akan abunda nafada mata shine gaskiyar al'amari. Aranar da duku_duku nafita Neman abunda zamuci, cikin kudurar Allah wani makocinmu yakaini wani guri nayi aikin safiya nasamo dan abunda ba'asaraba. Cikin tsananin farinciki na auno abunda zamuci da kayan hadi na kawo gida, shikuma yaron na auno masa madara gwangwani daya. Koda nakoma gida yanda nabar yaron adakina haka nashigo nasamesa yanata tsala kuka, atika ko kallon inda yake batayiba, cikin sauri nanufeshi nadaukeshi nahau jijjigashi dama ina wajene amma gabadaya hankalina yana kansa. danayiwa atika maganar tanajinsa yana kuka amma ko daukarsane aitayi. Seta kada baki tacemun ita bata haifi daba bazatayiwa wata bautaba, itakuma tanacan tana hutawa. bankulataba nadama madarar danashigowa da yaron da ita nabasa yasha, dannasan yunwace ke dawainiya dashi. bansaniba ko yunwar dake damunsace kokuma danda ruwan sanyi nadama masa yana gamasha se amai. hankalinafa yatashi danbansan mezan kuma bashiba. Ruwa nabashi yasha sannan na masa wanka nagoyeshi abayana bajimawa bacci yadaukeshi. Atikadai sedai ta kalleni tatabe baki. Intakaice muku zance, nikadai nayita wahala da yaronnan inda nasa masa suna *Muhammad mustapha* nayita wahala sosai dashi, dan dafarkoma har rashin lafiya yayi kamar baze rayuba, sedaga baya yasamu lafiya. banfi wata dafara rikonshiba nasamu aiki a wani guri, shinema hankalina yadan kwanta dannasamu sana'ar dazamu dinga kaiwa bakin salati. atika tsana kururu take nunawa mustapha, tun yana yaro haka zatayi ta daka masa tsawa shiko bemasan metakeba. nine wankansa, inbashi abinci, tsarkin kashi da fitsari duk nine tare muke kwana tashi. Sedai innafita atika taga yadameta da kuka sannan zata bashi abinci, tana bashi tana zaginshi wataranma hardasu dungure masa kai. Nikuma Allah yadoramun matsanancin so da kaunar mustapha, bana gajiya da daukarsa inta masa wasa, wannan abun yana kara bakanta ran atika gami da kara mata tsanar mustapha aranta.
Watarana ina daki inayin karatun alkur'ani da sassafene, lokacin mustapha yayi kusan wata takwas ahannunmu, yanata rarrafensa atsakar gida yana wasansa. Atika kuma tanata kokarin hada mana abunkari domin fitar wuri nakeyi zuwa gurin aiki, shayi ta sauke atukunya kafin tajuye a flaks, abunka da yaro yana ganin ta ajiye tukunyar ya rarrafa gurin da gudunsa, ina daga daki ina hangoshi banyi tunanin komaiba dannaga atika tana gurin nasan bazata barshi yataba tukunyarba, sunkuyar dakaina nayi nacigaba da karatuna. Ihun da mustapha ya kwallane yasani dagowa dasauri, hangoshi nayi yabude murfin tukunyar yatsoma hannunshi acikin ruwan shayin atika na kallonshi tacigaba da aikinta. dasauri nafito daga daki nadaukeshi cike da tsananin tausayawa, gabadaya ya gigice se kuka yakeyi da dukkan karfinsa. ruwa nadebo nashiga kwara masa ahannunnasa seda nazuba masa ruwan sosai, sannan nadakko gishiri na barbada masa natottofamasa addu'oi. dakyar nasamu bacci yadaukeshi bayan yaci kuka yagode Allah, muryarshi hardashewa tayi, se faman ajiyar zuciya yake saukewa. Har hawaye seda namasa alokacin tsabar tausayawa. bayan naje na kwantar dashi adaki nafito nasamu atika datake ta aikinta hankali kwance nace mata. "Kin kyauta atika, yau nakara tabbatar da imaninki ragaggene kina kallon yaron harya bude tukunya da ruwan zafi aciki amma kigagara daukeshi. Toya kone hankalinki ya kwanta, zanfita idan kintashi duk abunda kikaga dama kimasa kokasheshinema kiyi,amma kisani Allah baze barkiba, *Abunda kikashuka shizaki girba* kema bakisan ahannun wanda danki ze rayuba nangaba, zaki iya haihuwa kimutu kibar dan, domin babu wanda yasan zeyaru da dansa har abada, itama uwarsa batasan wannan kaddarar zata sametaba aduniya, kuma ki sani zalintar marayan Allah kikeyi,kikiyayi gamuwarki da ubangiji" inagama fada mata haka najuya nafice daga gidan raina a tsananin bace.
Hakadai mukacigaba da rayuwa a garin nijer ina rainon mustapha, yaro me tsananin hakuri idan kaji kukansa tobakaramin abubane, atika tamasa mugunta kala_kala duk abunda zecutar dashi koda tana gani bazata hanaba, yasha zuba yaji a idonsa kokuma yaji ciwo da wani abun. Amma duk da haka yaron Kallon mahaifiya yakewa atika, danyana ganinta sefara wangale mata baki yana mikamata hannu alamun tadaukeshi. Ko yarane suka shigo namakota idan kiwarsa tatashi seyaki zuwa gurinsu yayita binta,ita kuma intaga dama ta daukeshi tana dungure masa kai, idanbatagadamaba kuwa ko kallonsa batayi sedai yayi abinsa shikadai yagama. Mustapha befi shekara dayaba ahannunmu atika tafara laulayin ciki, murna da farincikin danaji bazata misaltuba, duk da ina kallon mustapha amatsayin dana amma nima inason naga dana nacikina, atika tayi murna sosai taita yada habaici ga yaron dabemasan me duniya take Cikiba, dan ita a ganinta danbani da dane yasa nakeson mustapha yanzu kuwa tunda zansamu nakaina sena rage sonsa. batasan abunbahaka bane soyayyar mustapha acikin jinina take, ina kaunarsa sosai gami da matsanancin tausayinsa. Alhamdulillah zuwa wannan lokacin nasamu rufin asirin kaina, natara kudadena. Harna fara tunanin dawowa kasata dazama gabadaya kodan yawan Aiken danakesha daga gurin yan'uwana musammanma Isma'il kanina.
Wataranar juma'a dabazan taba mantawa da itaba arayuwata, bayan ansakko daga masallaci dama ranar juma'a bama fita aiki. Lokacin cikin jikin atika yayi wata hudu, ina zaune adakina ina ware kayana masu amfani damarasa amfani danbanajin zankara sati biyu a nijer. Jakar danake ajiye abubuwa nasauko senajita da nauyi sosai, mamakine yakamani domin ni namamanta da batun jakar da babar mustapha ta bani, tun ranar kuma bankara dakko jakarba. cike da mamaki na ajiye jakar na budeta, tozali nayi da jakar se'alokacin natunata,to jarabar atika kadaima ta isa tasa tamanta da ita. Banyi kasa agwiwaba na dakkota, yarkaramar jakace me gurare ajikinta. Kananun zip din nafara budewa, a wani naga azurfa babba bata danyatasaba ta tsintsiyar hannu, sekuma wani abu kaman tambarin gidan sarauta kona wani abu dai, anyi rubutu da yaren French ajiki, ajiyesu nayi agefe na bude babban zip din jakar, abunda nayi tozali dashi acikin jakarne yakusa zautar dani............✍️ Meson complete Whatsapp 08166674823
A daure a ringa Comments update 12pm
*ABUNDA KASHUKA....* _*(shizaka girba)*_
*3️⃣7️⃣*
*INAWA DAUKACIN AL'UMMAR MUSULMI BARKA DA SALLAH, DAFATAN ANYI SALLAH LAFIYA. ALLAH YA MAIMAITA MANA YA AMSHI IBADUNMU,AMEEN*🙏🥰
*Bismillahirrahmanirrahim*