Kenza eBookz

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 23

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 23

Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 23: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 23. Mommy bayan fitar aunty da maryam takai hannu da nufin…

3,522 words

Mommy bayan fitar aunty da maryam takai hannu da nufin daukar abunda yafashedin sekuma tayi wani tunani tafasa ta fice daga dakin dasauri cikin wani irin yanayi mewuyar fassaruwa. hankalin aunty a matukar tashe take shafawa maryam ruwa ajikinta, suhailat kuma namata firfita bisa umarnin aunty. gashi hankalin aunty ya rabu biyu, sotake taje taga menene adakin maryam dayake hayaki, tabbas kotantama batayi akwai wata kulallaliya akarkashin kasa da kuma kitimurmura dake faruwa,sannan kuma ga tunanin wanda tagani yafice daga falon. hannun maryam aunty ta wanke mata jinin tare da daure matashi da kyalle. Kusan 20 minutes sannan maryam taja dogon numfashi gami da mikewa zaune a firgice tana kokarin guduwa tare da fadin, "waye kai, meyasa kakeson cutar dani kayi hakuri dan Allah karka rabani da martabata, aunty, mommy kutaimakeni,karku bari yabatamun rayuwa!" Kalaman da maryam takeyi kenan cikin kuka. Fahimtar da aunty tayi bata cikin hayyacinta seta riketa gam ajikinta tahau shafa bayanta.tare da karanto addu'a tana tofa mata. Luf maryam tayi ajikin aunty, tana sauke ajiyar zuciya. Can kuma cikin wahalalliyar murya tace, "ruwa,ruwa" suhailat ce tatashi tadakko takawo mata, domin ita kanta jikinta yayi sanyi da yanda abubuwan suke faruwa ta kuma fahimci wanine yazo domin ya cutar da maryam din a kalamanata. Ruwan aunty tabawa maryam tasha sannan ta kwantar da ita akan gado tana cigaba da tofa mata addu'a, bajimawa bacci menauyi yayi awon gaba da ita. ganin maryam tasamu bacci aunty tadubi suhailat tace, "kikwanta kema kinga tsakiyar darene zanje naduba dakin maryam din" gyada mata kai suhailat tayi, sotake tatambayi aunty meke faruwa amma takasa magana. ficewa aunty tayi ta nufi dakin maryam zuciyarta namata sake_sake, kalaman maryam sunkara sata acikin duhu,kenan wanda tagani ya fita farmaki yakaiwa maryam. "tabbas akwai abunda ake kullawa maryam, tunda naga wani yafita da gudu daga falonnan sannan kuma ga abunda nagani adakinta, ga kuma kalaman datakeyi. amma insha Allahu koma waye sedai mugun nufinsa yakoma kansa" aunty ta fadi haka afili, sanda tashiga dakin maryam din, bin dakin tahauyi da kallo daga gani ansha artabo tsakanin koma waye da maryam, ganin yanda dakin yake duk a hargitse. Tsugunnawa tayi agaban abunnan tana karanto ayatul kursiyyu a fili sannan tasa hannu tadauki abun, dasauri aunty tasakeshi saboda zafin dataji ahannunta yana shirin konata. Kurawa abun ido tayi danganin menene aciki, abunda kawai ta fahimta wata yarkaramar layace sekuma gashi dake saman layar, har lokacin kuma hayaki nafita daga cikin abun kadan_kadan. aunty macece dabata tsoro kokadan akan irin wadannan abubuwan, tunani barkataine sukazo mata cikin kwanyarta akan abunda yafaru. Daddy seda ya idar da sallah yake tambayar zannurain ina faruq, yace masa shima tashi yayi yaga begansaba. duddubawa daddy yace yayi ko yana wani dakin, amma zannurain yaduba ko'ina a part din begansaba har kasa begansaba. Daddy beyi tunanin komaiba danyasan halin faruq, may be abunnasane ya motsa ya koma part dinsu......

Mommy tana komawa dakinta cikin tsananin tashin hankali ta daukko wayarta missed call din zannurain tagani, dama tasan za'ayi haka dantasan zuwa yanzu mustapha ya mike. wata Number ta lalulubo takira takara wayar a kunnenta, ringing biyu aka daga cikin kunar zuciya gami da tsananin bakin ciki mommy tafara magana. "Dan' albarkana, ya'akayi haka ta faru meyasa al'amuran suka lalace yauma bakayi nasara akannata bane?" Daga daya bangaren akace, "hmmmm, mommy yarinyar tana wahalar damu gashi gabadaya ta dagula mana lissafi tadawo mana da hannun agogo baya, muna gabda cimma nasara akan abunda mukayi shekaru muna nema, amma rana daya tazo ta ruguza mana komai. waiyama akayi wannan kaskon yazo dakinta?" "bansaniba nima wlh, shine abunda yafi komai dagamun hankali dasani dimuwa" cewar mommy cikin tsananin bacin rai. "Mommy, akwai matsalafa domin *boka tsidau* yacemun aikinmu yana gab da lalacewa,matukar bamu dageba" wata mahaukaciyar dariya mommy takece da ita, kafin daga baya ta hade rai tace, "karyane dana, aikina baze taba lalacewaba nicefa atika, kaidai kazuba ido kaga abunda zanyi, itama yarinyar datake batamun shirina sena kasheta da hannuna,.!,domin tunda tazo gidannan komai nawa yakeyin baya" mommy takarasa zancen cikin Karaji,zuciyarta na tafarfasa. "Amma mo.... " karkace komai dana, kaidai kawai katabbatar kabar gidannan adarennan kafin wani yaganka" mommy tana gama fadar haka ta katse kiran tare da bin bayan kiran zannurain,amma harta katse shima bedagaba, time din yaje duban faruq wayartasa kuma tana silent shiyasa daddy beji kiranba. Aunty ta jima durkushe agaban abunnan tana karanto addu'a tana tofawa acikinsa, sannan tasamu hayakin dake fita daga cikinsa yadena fita. ahankali takai hannu akaro na biyu ta dauki abun setaji babu zafinnan, dakinta ta nufa dashi dauke ahannunta......

*AFTER SOME HOURS*

Har safiya su aunty basusan halin da'ake cikiba game da farfadowar mustapha, kuma haryanzu maryam bata tashiba aunty ma bata tashetaba,duk da zuciyarta a kwadaice take dajin ina maryam ta samo abunnan. zannurain bega missed call din mommy ba sebayan daya dawo daga masallacin sallar asuba,yabi bayan kirannata kuma bata dagaba. A masallaci daddy haidar kawai yagani bega faruq ba, ya tambayi haidar koya baroshi a part dinsune yace masa besaniba koyana cikin dakinshi. tare da haidar suka dunguma duka zuwa part din mustapha, dan tun kafin a tada sallah zannurain ya guntsa masa yaya ya mike. Aunty takira daddy danta sanar masa abunda yake faruwa yace mata tazo part din mustapha shima akwai abunda yakeson sanar mata, takuma biya tataho da mommy dansuna ta sabanin kira da ita. Koda aunty tazo dakin mommy, seta tarar mommy tana cikin toilet hakan yasata ficewa tafadawa suhailat idan mommy tafito tasamesu a part din mustaphan. Mustapha yana kwance akan gado, idanunsa a lumshe amma ba bacci yakeba, su haidar suna zagaye dashi, sun rasa inda zasu tsoma kansu dan farinciki, ahaka aunty tashigo ta samesu bakinta dauke da sallama, amsa mata sukayi atare fuskokinsu dauke da murmushi. da mamaki aunty take kallonsu kafin tace wani abu haidar yay caraf yace, "auntynmu kibani goron albishir dan albishir din dazan miki yacancanta kibani goro me daraja, yayanmu ya warke harya mike zaune dakans......"dagaske kake haidar" aunty tafadi haka cikin tsananin farin ciki tana nufar inda mustapha yake. "Dagaske yake saudart" cewar daddy yana murmushi. "Godiya ta tabbata ga Allah, me rahama dajin kai ga bayinsa,Allah kakara sassauta mana, ka kara mana lafiya, Allah duk wanda yake cikin hali na jinya Allah shima kabashi lafiya" aunty tafadi haka tana shafa fuskar mustapha, gabadaya suka amsa mata da "ameen", banda mustapha dako bude idonsa beyiba. "Yaya yaushe ya farfado dinne?" aunty tatambayi daddy. "Tun jiya cikin dare zannurain yakirani yasanarmun wai ya tashi a firgice,amma yanzu komai yayi daidai danhar wanka usman yataimaka masa yayi gami da sallah, amma maganacefa haryanzu beyiba" "kai, masha Allah, jiki yayi kyau, ai maganar se'ahankali zeyine da yardar Allah,ahakanma angodewa Allah, sannu kaji Muhammad Allah yakara sauki" "ameen,ameen" duban zannurain aunty tayi tace, "amma zannurain a wani irin firgici ya farka?" Numfashi zannurain yasauke yace, "aunty nidai ina bacci naji wata irin kara daganan kuma senaji muryarsa yatashi yana kiran sunan Allah" "kara kuma harnan kunjiyo wannan karar?" Aunty tatambayeshi cike da mamaki, "aunty nima ai naji" cewar haidar, daddy ma cike da mamaki yace, "aiko nima naso naji wata kara cikin baccina, karar mene" shiru aunty tayi batace komaiba, se gyada kai kawai takeyi,cikin ranta tace. "Tabbas babu tantama abunda tadakko daga dakin maryam shine abunda yafashe kuma yayi wannan karar, kuma yanada nasaba da ciwon mustapha, to amma meyakaishi dakin maryam, ko wanda tagani yafita daga dakin shine ajiye abun" bata dame bata wannan amsar se maryam, itace zata fayyacemata zare da abawa tunda adakinta abun yafaru, daddy yabude baki danufin yakara tambayar aunty akan wai meke faruwane ganin tayi shiru, amma shigowar mommy da suhailat ta hanashi maganar. Su haidar naganin mommy suka ruga gareta suna rige_rigen sanar mata yaya yatashi, dansunsa setafi kowa farin ciki da tashin mustapha, atare suka sanar mata, pretending na murnar da mommy tayi akan tashin mustapha baze misaltuba, harda kukanta na murna, suhailat ma tayi murna sosai, kokunyar su aunty batajiba taje ta rungumeshi tana shashshafashi. mommy cikin tsananin murnar datake nunawa ta karasa gabanshi, ta kama hannunsa ta rike tana fadin, "my son, tashi kaga mommynka, bude idonka naganka naji dadi araina, yau ranar farin cikin muce son, tunda Allah yabaka lafiya" a matukar firgice mustapha ya bude idonsa gami da tashi zaune yafara ja baya daga kusa da mommy,jin muryarta yana fadin, "pls mommy kiyi hakuri idan wani lefinna miki kidenamun abunda kikemun kullum pls mom,inajin azaba sosai ajikina..!" cikin raunananniyar yayi maganar yana sakin numfarfashi,alamun dakyarma ya iya yin maganar. dafe kirji mommy tayi tace, "son kasan mekake cewa kuwa, nicefa mommynka koka manta nine" girgiza kai mustapha yahauyi yana kara jabaya, rikeshi haidar yayi ganin kamar baya cikin hayyacinsa. cikin tashin hankali mommy ta juyo tana kallon daddy, idanunta na zubar da hawayen munafurci tace, "daddy kaji me son dina yake cewa, yau nice son bayason narabeshi, wai ina masa wani abu, wlh anshiga tsakanina da dana, anmasa mugun asirin daya manta kansa pls daddy kayi wani abu akai,wlh angamamun da dana" ta karasa zancen tana fashewa da kuka. wani irin kallo aunty takebin mommy dashi na tuhuma, kafin daddy yayi magana, sukaji daga bakin kofar dakin anacewa, "babu wanda yayi masa asiri danya rabaku, face ke dakikayi masa asirin dakanki akokarinki na ganin ya mutu, danki cika wani banzan burinki,saboda bake kika haifesaba. sekuma Allah bebaki nasaraba gashi ya warke a lokacin dabakiyi tsammaniba...........✍️ Baku Comments Gaskia

Meson complete Whatsapp 08166674823

*ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_

*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*

*Bismillahirrahmanirrahim*

3️⃣5️⃣

...........Gaba daya suka juya atare cikin tsananin mamakin jin muryar me maganar gami da abunda yafada, mutumin dasuka manta rabon dasuji yayi doguwar magana irin haka. "Faruq! ni mahaifiyarka kake jifa da wadannan muggan kalaman, nikake cewa nayiwa dana nacikina asiri kuma bani na haifesaba,kana cikin hayyacinka kuwa faruq!?" mommy tafadi haka cikin tsawa da matsanancin tashin hankali. murmushi faruq yayi, gami da yin taku yakaraso har gaban mommy yace, "ina cikin hayyacina mommy nake fada miki wadannan maganganun,kidena wani borin kunya,kina nuna kamar bakisan abunda kinfi kowa sanin saba,yau ranar tonan asirinki ce tazo keda wanda kuke shirya komai tare, kisani asirin dakikamun na shekara da shekaru ya karye hakama wanda kikayiwa daddy ya karye" kafin mommy tayi magana aunty tatari numfashin faruq tana duban daddy tace, "yaya kanajin me faruq yake cewa akan mahaifiyarsa amma kayi shiru kana kallonsa, menene gaskiyar al'amarin yaya?" Shiru daddy yayi bece komaiba amma fuskarsa tana nuni da tsantsar damuwa, da tashin hankali,kusan 50 second sannan ya numfasa yace, "tabbas atika ba'ita ta haifi mustapha b..." wata hantsilowa mustapha yayi daga kan gado jikinsa gabadaya yadauki wata irin kyarma hannunsa narawa yahau nuna mommy yana kallon daddy, magana yakeson yayi amma yakasa se bakinsa dake motsi alamar yanason yace wani abu. aunty, haidar,zannurain atare suka mike tsaye cikin tsananin dimuwa jin abunda daddy yace,aunty hartana yarda wayarta kasa batare data saniba, baya mustapha yayi luuu,ze fadi kasa,dasauri daddy yataro jikinsa,suka zauna abakin gado, dama jikinnashi babu kwari gakuwa wani bakin zance dayakeji wanda yake kokarin saka zuciyarsa ta buga, wanda yajishi tamkar saukar ruwan narkakkiyar dalma atsakiyar kansa. kallon mommy aunty takeyi amma itama takasa magana se girgiza kai kawai takeyi, aranta tana cewa, "wanne irin burine wannan da mommy takeson cikawa wanda har tayiwa danta na cikinta da kuma mijinta asiri,kuma take kokarin kashe mustapha" mommy kuwa jitayi gabadaya yawun bakinta ya kafe kaf, zuciyarta tahau harbawa dasauri cikin tsananin tashin hankali bata taba tunanin abun zezo mata ahakaba, "nashiga uku ni atika,yanzu kenan sulaiman ze iya tuno komai daya faru ada" mommy ta fadi haka atunaninta azuci tayi maganar, amma seta tsinkayi muryar daddy yana fadin, "tabbas tunanina yadawo akan abunda kika gusarmun da hankali akansa, kuma ranar wanka ba'aboyen cibi yau zansanar da mustapha abunda nake da burin sanar masa shekara da shekaru,amma kika rufe mun baki ruf namanta nakasa sanar masa." wani irin murmushi mommy tayi me ciwo cikin karfin hali tace, "to seme, sulaiman idan kafada masa, kadade baka sanar da mustapha gaskiyaba, to bari kaji insanar maka fadar abunda kake kokarin yi, daidai yake da tonawa mustapha asirin dani dakai muka rufa masa arayuwarsa" shima daddy murmushin yayi yace, "insha Allahu, fadata saidai tazamo masa alkhairi arayuwarsa" mommy tana kokarin sake magana sadiq dake falo tundazu yashigo dakin asukwane fuskarsa murtuk babu alamun fara'a yana bin kowa da kallo dai_dai, zaro ido aunty tayi cikin tsananin razani ganin rigar dataga mutumin jiya datagani yafita da ita ajikin sadiq,ga kuma kansa yane da hirami, hannunsa duka biyun da safunan hannu, alhalin ba lokacin sanyi bane. dafe kanta tayi tana furta Kalmar hazbunallau wa'inimal wakil afili. tana addu'a aranta,Allah yasa abunda take zargi karya tabbata kokuma fatan idonta beganin mata daidaiba,kai bamata tunanin haka sediq ze aikata abunda take tunani,kilan jiyanne idonta beganinmata daidaiba. "Sadiq meyadawo dakai yau kuma?" Mommy tatambayeshi cikin tsananin firgici tana kallonsa. be'iya bata amsaba se faruq daya nuna mata da hannunsa. zama aunty tayi dabas akasa tamarasa mezata kira wannan bakon al'amarin me cike da rudu da tashin hankali acikinsa. Mommy ma zama tayi a gefen gado gumi na tsatstsafoma mata ako'ina najikinta, domin bata taba tunanin abun zejuye mata hakaba, bata taba tunanin wannan ranar tonan asirin zata zomataba arayuwarta, tarasa wanne sakaci tayi dakomai nata ya lalace, amma duk da haka zuciyarta bata sadudaba, takudircewa ranta agama wannan rikicin dakanta zata koma gurin boka tsidau,yasake mata sabon aiki. Faruq ma zama yayi akasa agefen aunty, haidar da zannurain kuwa basa gane komai akan abunda yake faruwa,kwakwalensu gabadaya sun toshe tsabar tararrabi sunma kasa magana, yanzu dama ba mommynsuce ta haifi mustapha ba, "to wacece ta haifesa?" tambayar da suhailat data daskare a tsugunne itama takeyiwa kanta kenan, shiru dakin yadauka kowa da tunanin dayakeyi acikin ransa,babu wanda yadamu da yanda sukaga sadiq,dominsu basusan komaiba akan fyaden da akeyi agidanba,hatta da daddy kuwa, mommy ce kadai tasani seshi meyin da faruq.

aunty ce tanisa cikin tsananin damuwa ta katse shirun tana duban daddy tace, "yaya kafada mana abunda yake faruwa kunsamu acikin duhu kaida faruq da aunty atika,kasanarma menene kuke boyewa da kuma gaskiyar al'amari akan abunda mu bamu saniba,sannan kuma tayaya Muhammad yazama badan aunty atikaba, wacece mahaifiyarsa to?." numfasawa daddy yayi yakalli su haidar da sadiq yace su zauna labarine me tsaho, babu musu dukansu suka yiwa kansu mazauni cikin son jin yanda daddy ze warwaremusu yanda abun yake, daddy ma raba mustapha yayi da jikinsa ya zaunar dashi akan gadon bayan yasamasa filo abayansa,cikin tsananin tausayawa ganin yanda numfashinsa yake fita dakyar tsabar tashin hankali. gyara zama daddy yayi yafara magana kamar haka:

Kamar yadda kuka sani, sunana sulaiman Abdullahi, iyayenmu mu uku kacal suka haifa, nine babba se mebimun isma'il se auta saudart. Mu cikakkun yan kanone muna zaune a unguwar gwammaja. Mahaifinmu tun muna yara Allah yayi masa rasuwa, lokacin banfi shekara 12 ba,shikuma isma'il shekara 8,yayinda saudart take karama sosai danko yayeta ba'ayiba. Mutuwar mahaifinmu bakaramin girgizamu tayiba nida innarmu,tashin hankalin da muka shiga baze faduba, haka mahaifiyarmu ta rungumemo ta cigaba da rainonmu ta kuma tashi tsaye da neman kudi domin ta rufa mana asiri. Nima tun lokacin banzaunaba nafara yan bugegene domin na dinga taimakawa mahaifiyata, dan babu metaimakonta se Allah, kunsan yanda zumuncin yanzu ya lalace, babu mekulaka sekana dashi, yan'uwan mahaifinmu ba wani kula sukeyi damuba,amma duk da haka bamu yada suba muna zuwa mugaishesu nida isma'il. haka muka cigaba da rayuwarmu cikin rufin asirin Allah, harnakai munzalin zama saurayi, lokacin nagama degree na farko,saboda halin rayuwa sena tsaya da karatun haka nacigaba da yan buge_bugena,dan mahaifiyarmu girma yakamata wasu sana'oin duk bata iyasu. Ina da shekara ashirin da hudu, itama mahaifiyarmu Allah yamata rasuwa bayan gajeriyar jinya datayi, A wannan lokacin munshiga tashin hankali fiye da mutuwar mahaifinmu, danni kusan zaucewa nayi seda aka hadamun da rokon Allah sannan nadawo nutsuwata,haka mukacigaba da rayuwa cikin maraici da kuncin rayuwa, wata cousin din innarmu itace tadauki saudart, domin innarmu bata da yan'uwa dasuke uwa daya ko uba daya. Gidanmu yazama daga ni se isma'il muke rayuwa aciki, bani da wasu abokanai hakama isma'il, mune abokan junanmu komai tare mukeyi mu nemi shawarar juna, muhaka mu binne tare. bayan rasuwar innata da watanni nafara zuwa kasuwa da taimakon wani Dan ajinmu damukai makaranta tare me suna sa'idu. wani alh, yahadani dashi nake masa jiran shago anan kasuwar wanbai,Wanda da shi sa'idunne yake masa,sekuma yanzu yasamu wani kasuwancin shine yakaini na maye gurbinsa. cikin ikon Allah tunda nakoma shagon se cinikin shagon ya ninku fiye dana baya, kullum idan aka tashi daga kasuwa sena biya gidan alhajin munyi lissafe lissafenmu sannan nake komawa gida, to a wannan zuwa gidan alhajin danakeyi anan nahadu da atika (mommy) gidansu makotane da gidan alhajin, kullum naje da yamma zanganta ita kuma tadawo daga islamiyya ita da kawayenta, amma fa kullum cikin yin fada take, wataranma harda dambe, danni kaina nasha rabasu. Kuma a lokacin ba yarinya bace, da girmanta danta zama cikakkiyar budurwa zama tayi shekara 19,sedai tana da karamin jiki. Kullum idan ta ganni setayi ta kallona, nikuma bansan meyasaba dariya take bani saboda tsiwarta,se'inta tsokanarta. Watarana bayan nazo mungama abunda zamuyi da alh, nafito zantafi gida segata da gudunta tatareni tabani wata takarda,nace mata ta mecece, tacemun idannaje gida nakaranta nagani. Banyi tunanin komaiba nakarba nazira a aljihu na wuce gida. Ninama manta da wani batun takardar data bani, seda nazo bacci zancire riga najita acikin aljihuna, dakkowa nayi ina mamakin menene, seda naganta kuma sena tuna, warwarewa nayi nakaranta, gabadaya abunda takardar ta kunsa wai atika tana sonane, dariyama ni abun yabani nazauna nayita kyakyatawa danni a lokacin ko tunanin wata soyayya banayi, tunanin yanda zansamu rufin asirin kaina na tallafi rayuwar yan'uwana kawai nakeyi. Isma'il ne yatambayeni mene yasani dariya haka, takardar hannuna nabasa ina basa labarin atika, tsaki yayi bayan yagama karantawa yakada baki yace, "yaya niko zakayi soyayyama bana fatan kayi da irin wadannan marasa kunyar, dandaga ganinta bata da tarbiyya tunda har tana mace ta iya furta maka kalmarso" bance masa komaiba,saboda bandauki zancen gabadaya da wani mahimmanciba nayi kwanciyata bacci. washegari kamar kodayaushe bayan nabaro kasuwa nazo unguwar su atika, ina fitowa kamar kullum muka kara haduwa da ita, ba kunya tatambayeni kona karanta takardar data bani, nace mata eh, seta tambayeni kona amince da soyayyarta, dariya kawai namata nawuce dan a tunanina wasa kawai takeyi itama. Intakaice muku zance,kullum se atika tatareni ta jaddadamun itafa sona takeyi dagaske, tun ina daukar abun wasa harnima naji nafara tausayinta dan wataran har kuka take sanyamun akan insota, batare danayi shawara da kowaba na amincewa soyayyar atika muka fara soyayya, dukda ni jikina yana bani bazamuyi aureba, danni talakane sukuma su atika suna da kudinsu, seda soyayyarmu tayi nisa nakejin labarin ashe atika itama marainiyace babu uwa ba uba, agurin kanin mahaifinta take, kuma anrigaya da anmata miji, yana kasar waje yana karatune shiyasa ba'ayi aurannasuba. banyi kasa a gwiwaba nasanarwada atika akan muhakura da juna tunda anrigaya anmata miji, amma atika tace sam ita batasan wannan zanceba ni takeso kuma ni zata aura. kanin mahaifinta yafatattakeni yace karna kara zuwa gurin yarsa, idanba hakaba seyasa andaureni, tundaga ranar dayamun hakan koda nazo unguwar bana sauraren atika, amma atika taki hakura dani har kasuwa take biyoni shagona, nayi mata rarrashin duniya akan muhakura da juna,amma atika takiji. Atika irin matannanne masu kafiya da taurinkai, rikicin da'aki da atika agidansu akan tahakura dani baze misaltuba,karshema kanin mahaifinta cewa yayi ta zaba koni koshi tace tazabeni, haka yatattaro mata kayanta yakoreta, tana kuka kanwarta na kuka, dayake su biyu iyayensu suka haifa, kafin su rasu, yan'uwa da abokan arziki suka dinga rokon marikin atika akan yayi hakuri tacigaba da zama agurinsa, amma yace yarantse matukar bata canza ra'ayintaba shima bazata cigaba da zaunar masa agidaba, tunda tace be'isa da itaba. itama atika ta kafe akan bakanta. cikin masu bawa kawun atika baki harda wannan alhajin danake zuwa gurinsa, toni kuma ganin atika ta guji kowa nata saboda ni, senayanke shawarar auranta a wannan lokacin, duk da nasan bawani karfi gareniba amma auranta shine kadai halarcin dazanmata akan abunda tamun. bansamu matsalaba agurin magabatanaba danaje musu da zancen zanyi aure, sudai tunda ficikarsu bazatayi ciwoba basu da damuwa, isma'il nema yanunamun kin amincewarsa danshifa atika bata masaba, dakyar nasamu na rarrasheshi ya amince. Ubangidana shine yatsayamana nida atika a aurenmu, ita yay mata kayan daki da kayan amfanin gida, nikuma yahadamun lefe. Gidanmu damuke ciki dama daki ukune kuma bawasu masu girmaba, guda biyu nagyarawa atika dayan kuma na hanyar kofar gida isma'il yacigaba da zama aciki, ubangidana shine yazama waliyyin atika aka daura mana aure atika tatare agidana, gaskiya babu karya atika tanunamun soyayya, tasoni kamarme azamanmu, dafarko bamu samu wata matsala da itaba,seda Allah yayiwa megidana rasuwa magada suka amshe shagonsu. Nashiga tashin hankali bakaramiba, domin bansan wacce Sana'a zankamaba wadda zan rufawa kaina asiriba. Isma'il shima alokacin baya sana'ar komai, hasalima karatu yakeyi ninake daukar nauyinsa, rayuwafa ta sauyamana gabadaya ga atika nadauke da dankaramin ciki a lokacin, abincin dazamucima wataran gagararmu yakeyi, ga atika bata hakuri kokadan akan rashi, kullum cikin mita da masifa takemun akan nafita nasamota abunda zataci, haka nake fita nayi yan buge_bugena daga bayama senakoma yin dako akasuwa, duk dan asamu abun kaiwa bakin salati.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull