Kenza eBookz

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 22

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 22

Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 22: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 22. Yau asabar wanda yakama daidai da saura kwana 2 mukoma…

2,900 words

Yau asabar wanda yakama daidai da saura kwana 2 mukoma school, bayan nadawo daga islamiyya karfe 11/30 muka nufi part dinnasa nida aunty, dama a irin wannan lokacin kullum muke zuwa, kafin muje yaya sadiq yagama masa na malamin da'ake masa. A bakin kofa muka tarar da yaya sadiq ze fita, gaisawa mukayi aunty tayi gaba tabarni dashi. "Malamata" yaya sadiq yafada cikin sigar tsokana, batarai nayi nace, "kaganga ko, zaka kafara kenan" murmushi yayi yace, "to ba malamar bace, karya nayi" "a'a niba malama bace dalibace me koyo" "toh shikenan na yarda, gobefa zanwuce me'aza bani dazan dinga tunawa dake kullum da kullum inji kamar muna tare." "Mekakeso kafada mana se'inbaka" "kinyarda infadi koma mene zakiban" "insha Allah indai ina dashi zanbaka" "tom shikenan kibari segoben idan zamuyi sallama zanfada miki, danse yamma zan tafi," "Allah yakaimu goben lafiya" "ameen, malama sekin fito" yafadi haka yana dariya. kin kulasa nayi nayi tafiyata, inajinsa yana cigaba da dariyarsa. A falon saman na tarar da mommy, hakimce akan kujera tanata latsa waya hankalinta kwance, gaishenayi tare da mata yame jiki nashige daki. Aunty tana gaban gadon ta rafka tagumi tana kallonsa nashiga dakin da sallama,amsamun tayi batare data dauke idonta daga kallonsaba. wayata dake hannuna na kunna, nasaka karatun, dai_dai saitin kunnensa anan ake ajiyemasa nannaje nasamasa, nadawo nabude fridge din dake dakinsa na dakko ruwa nazuba a cup, nazauna inabin karatun azuciyata ina tofawa acikin ruwan, aunty ma bin karatun takeyi, karatun yanada dan yawa, munfi rabi munma kusa gamawa aunty tafita zata amsa waya, harna gama tofawa karatun yakare aunty bata dawoba, karambani nayi nadau cup din zanshafa masa ruwan ajiki, dama aunty ce take shafa masa kullum. ahankali nazauna abakin gadon bayan na ajiye cup din agabana akasa, kura masa ido nayi cikin tsananin kaunarsa, wani shaukin sansa da tausayinsa na mamaye dukkan jini da tsoka najikina, ahankali natsiyayo ruwan ahannuna nafara shafa masa a fuskarsa, zuciyata na luguden bugu tamkar zata faso kirjina tafito, wani irin bakon yanayi naji ya bakunci dukkan gabban jikina wanda bansan yazan misalta muku shiba, lumshe idona nayi lokacin danake shafa masa ruwan a wuyansa zuwa saman kirjinsa, wani irin laushine da fatarshi gata da santsi, hannayensa duka biyun nashafa masa tare da kafafunsa, dama iya inda ake shafa masa kenan. wayata dake gefensa na dauka na tsaya kawai ina kallonsa, zancen zuci nakeyi nikadai akan koyaushe bawan Allah zetashi yacigaba da rayuwa kamar kowa se Allah. hannun haguna dake rike da wayata nadafa fuskar gado dashi, hannun damana kuma nasashi asaman goshinsa ina shafe masa ruwan dayake gurin, ban'auneba kawai naji wayata tafada ta bayan fuskar gadon. da sauri na dago cikin takaicin fadawar wayar, "yanzu ni tayaya zan iya dakko wayata ana gurin." nafadi haka a fili cikin rashin sanin abunyi, niba'abun infadawa aunty wayata tafadaba tacemun meyakaini gurin, balle kuma mommy. shiru nayi inatunanin mafita, can wata dabara ta fadomun nakoma karshen fuskar gadon na leka sena hango dan kyalli kwabar wayata amma tayimun nesa bazan iya dakkowa tananba, dawowa nayi nahau kan gadon ina kallon fuskar yaya mustapha, ahankali nakai hannuna duka biyu na matsar dakansa gefe yakoma karshen filon dayake inda nacire kannasa nanna dora gwiwata na leka fuskar gadon, adaidai nan kuwa na hango kyallin wayartawa amma bazan iya daukowaba, hakura nayi nabar leken, nazo zandaga gwiwata kawai naji wani abu metudu acikin filonnasa, cike da mamaki nazare kafata duka nasaka hannuna atsakiyar filon ina ta bawa, wani abu naji nariko ahannuna ta cikin rigar filon kamar dutse. mamakine yakamani na mene kuma zekawo dutse cikin filo, Allah sarki bawan Allah yana kwance abu yanata damunsa aka amma saboda babu bakin magana baze iya fadaba. ahankali cikin lallabawa nakara saukar dakansa kasa daga kan filon gabadaya, na juya filon tabaya nazuge zip din rigar filon nazira hannu na dakko abun. ajiye abunnayi akan gadon nazuge zip din namaida filon daidai nakara kamo kannasa nadora akai ahankali. Abunda nadakko nakurawa ido, abun kamar kaskon turaren wuta yanayin shape dinshi,amma karamine sosai harda murfinsa kamar tukunyar dandankuwa da yara sukeyi da kasa. sakkowa nayi daga kan gadon nadauki abun ahannuna, wani dogon numfashi naji yaya mustapha yasauke harya kusa tsoratar dani, dasauri na kallesa naji yanata sauke ajiyar zuciya tare da numfarfashi. ahankali kuma naga fatar saman idonsa tana motsi kamar ze bude ido, dasauri nafita da gudu zuwa falo ina kwalawa aunty kira, aunty dake waya da abbansu aliya takatse wayar dasauri jin kiran da maryam take kwala mata, "lafiya maryam" aunty tatambayi maryam tana mikewa tsaye gabanta yana faduwa. cikin haki nace, "aunty zokigani naga idonsa yana motsi" ai aunty bata jira maryam takarasa abunda zatajeba tanufi dakin dasaurinta, ilaikuwa seta tararda abunda maryam tafada mata, cikin tsananin jin dadi aunty tace, "Alhamdulillah maryam, sauki yafara samuwa da yardar Allah, tunda har wani abu najikinsa yafara motsi" nima cikin tsananin farin ciki nace, "insha Allah, aunty dama naji yanata sauke ajiyar zuciya" shafa kansa aunty tayi tace, "Allah yakara baka lafiya Muhammad, Allah yasa warakarkace tazo,dakuma karshen ciwonka" "ameen aunty" "kinshafa masa tofinne" aunty tafadi haka bayan tadago tana dubana. "Eh aunty" "yawwa dama Inata addu'ar, Allah yasa kinshafa masa abban aliyane yatsaidani awaya shiyasa." "Tom aunty bakomai bari nakoma" "ohk, maryam,mungode sosai Allah yayi albarka" "ameen" nafadi haka ina juyawa nafita, haryanzu abunnan yana hannuna na damkeshi, tare da boye hannunnawa acikin hijabi. bayan fitar maryam aunty ta dauki guntun ruwan tofin tasa acikin fridge, tazauna agefen gadon tabi bayan kiranda abbansu aliya yaketa mata bayan katse kiran datayi. Cikin sauri nake tafiya saboda Allah,Allah nake nakarasa part dinmu nabude abun hannuna naga menene, Allah yasoni babu kowa a falo nayi sauri nashige dakina. ajiye abunnayi akan madubi, nafara kokarin budewa amma abun yaki buduwa tamkar ansaka gam amanne, hakura nayi ganin nayi_nayi yaki buduwa nabarshi a gurin nakama sabgar gabana,danbanyi tunanin wani abune me mahimmanciba. Se bayan sallar azahar aunty tadawo daga part din mustapha, ta baro mommy da haidar agurinsa. Bayan sallar lasa'ar nafito falo nahadu da yaya sadiq yana kokarin fita da sauri yatsaya yace, "maryam, ina kika ajiye wayarki inata kiranki akashe" "yayana ta mutune ba caji" "haba maryam duk wutarnan amma kika bari wayarki ta mutu kuma tundazu bakisa cajiba" "baccine yadaukeni kuma namanta bansaka cajinba seyanzu dana tashi" "ohk,tafiyar danace miki zanyi gobe tadawo yau" da mamaki nake kallon sa nace, "yaya yau kuma ai yamma tayi kabaridai goben" "wlh maryam, kiran gaggawane yasameni daga kamfanin daddy na abuja" cikin sanyin jiki nace, "shikenan yayana Allah yakiyaye hanya" "to mene kuma, ko bakyason natafi naga dukkinyi wani iri" kaina nagyada masa alamun eh, haka kawai naji banason yatafi jikina duk yayi sanyi. "Kiyi hakuri kinji maryam dita, aiba dadewa zanyiba zandawo befi nayi sati dayaba ki saki jikinki kinji, karki karyamun gwiwa" danne damuwata nayi ina murmushi nace, "shikenan yayana, Adawo lafiya Allah yakiyaye, ya kare hanya kakuma kulamun da kanka" murmushi sadiq yayi cikin jin kalaman maryam yace, "kokefa yar matata, nagode sosai, kikulamun dakanki kema sosai I will miss u" "miss u too dear" nafadi haka kaina akasa, cikin fadada fara'a sadiq yace. "Byeeer I love you" hannu nadaga masa alamar bye_bye nace, "love u too" sekuma najuya da sauri nakoma dakina. Murmushi sadiq yayi yanabin maryam da kallo cike bansha'awa da tsananin kaunarta, harta shige daki sannan ya juya yatafi. Wuraren karfe 5:30 muna zaune nida aunty a falo aunty suhailat tashigo falon, da alama daga unguwa take, dan taci kwalliyarta hannunta kuma nadauke da jaka. seda tazo tsakiyar falon tayi sallama shima dantaga aunty ne dabaza tayiba. "Suhailat daga ina haka dannasan yau ba school" aunty tafadi haka bayan mun amsa mata sallamar tata. "Naje gidan wata friend ditane" itama suhailat din ta bata amsa da haka. Kallon suhailat aunty takeyi cike da tuhuma ganin yanda taga gabadaya ta canza sannan tace, "wakika tambaya" cike da kosawa suhailat tace, "mom" atakaice. aunty bata kara cewa komaiba, ita kuma suhailat tashige daki tana tutturo baki gami da kunkuni. Daga gurin kamal take, yanzu kullum ta Allah sesun hadu sun sheke ayarsu, ko duba mustapha ma saudaya take zuwa a rana, yanzu tazama yar hannu, idan bataje tayi sex da kamal ba kullum bata samun nutsuwa. Aunty takanas taje har dakin mommy bayan sallar magriba tayi mata magana akan fitar suhailat, se mommy tace ita batason haka mene nadamuwa akan yawan fitar suhailat din, yar marainiyar Allah ma se'ansa mata ido,adai dinga kyautata zato. Ran aunty yayi matukar baci dajin kalaman aunty, amma ta daure batace mata komaiba tatashi tafito ta bata guri,ita bada wata manufa tafada mataba,tafada matane kawai akan amata fada ganin yawonnata yayi yawa, alhalin kuma ga wanda ake saran yazama mijinta kwance babu lafiya.

kewar wayata duk ta isheni yau, gashi nakasa fadawa kowa tafada bayan gado, seda daddare daza'asawa yaya mustapha karatu nake fadawa aunty, fada tamun akan meyasa banfadaba tundazuba har gashi dare yayi, dole yanzu sedai abari da safe adakkomun. guntun ruwan safe kawai aunty ta shafa masa, tunda babu wayar saka karatun. Yau zannurain da faruq ne zasu kwana dashi tunda sadiq bayanan. Kafin 10 nadare nayi bacci tunda babu waya ahannuna, dama ita takesa nakai 11 a online muna chat da kawayena a group dinmu na school. cikin baccina yauma naji ana lalubata gami da yamutsani da karfin gaske, a matukar firgice na farka ina kokarin kwarara ihu, naji anrufemun baki, irin kaurin danaji wancan karon yauma shinaji, "ya Allah wannan wacce irin masiface da jaraba gami da bala'i waye wannan memugun nufinne?" nafadi haka araina cikin tsananin firgici gami da razani. banyi kasa a gwiwaba gurin karanto addu'a da kokarin kwatar kaina iya iyawata, gabadaya jikina rawa yakeyi zuciyata na harbawa da sauri_da sauri, ga wani jiri_jiri danakeji yana kwasata amma haka nadaure nacigaba da kokarin kwatar kaina, harna samu na kwaci kaina natashi da mike da sauri na sauka daga kan gadon ina kokarin guduwa, dasauri mutumin yabiyo bayana yadamki gashin kaina da karfi, kara na kwalla da iyakacin karfina saboda matsananciyar azabar data ziyarceni, juyo dani mutumin yayi yafara kokarin maidani kan gadon, turjewa nayi naki tafiya, tamkar masu dambe haka mukahau kokawa ninaki yarda yakaini kasa shima yaki hakura, seja baya nakeyi duk da dakin duhune dinkim amma haka nafara laluban kan mudubin dakina kozan samu makami, cikin ikon Allah naji nataba gaban madubin, hannuna nasa nadaki ruwan madubin da karfi, jikake bassss! Yayi kara ya karye, ko zafin yankar da madubin yamun atafin hannuna banjiba na kara karyo wani, hannunsa daya da mutumin yarike hannuna yana kokarin jana nakartawa mudubin da sauri yasakarmun hannunnawa, rike katakon madubin nayi gam nakara daga madubin dayake hannuna na yankesa goshi cikin duhu batare dana masan inda na yankaba, cikin tsananin jin azaba mutumin ya janyo maryam da dukkan karfinsa, da nufin ya tumurmusata cikin tsananin zafin rai,ganin tana bata masa lokaci. gabadaya muka taho nida madubin, mutumin ya cillani akan gadon, shikuma madubin yafadi kasa, wani abune me kyalli,naga yayi tsalle daga kan madubin yafadi a acan gefe akasa jikake toshhhhhhh!! yafashe wani bakin hayaki yafara fita daga cikinsa tare da wata muguwar kara data karade part din gabadaya me barazanar toshe kunnen mutum yakoma kurma. fashewar abun yayi daidai da tashin mustapha zaune daga kwancen dayake tamkar gawa cikin wani irin yanayi yana kiran sunan ALLAH da dukkan karfin muryarsa da Allah yayi masa............✍️ Meson complete Whatsapp 08166674823

ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_

*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*

*Bismillahirrahmanirrahim*

3️⃣4️⃣

...........A matukar firgice zannurain dake gefensa a kwance ya farka daga bacci, saboda karar abunnan harnan suka jiyota, ga kuma sunan Allah da mustapha yakira tamkar acikin kunnensa, ahankali yakai hannu yana shafa inda ya'ajiye wayarsa jikinsa gabadaya na kyarma saboda tsorata, dakyar yasamu ya lalubota ya kunna fitila inda mustapha yake yahaska yaganshi a zaune, bayansa jingine da fuskar gadon amma idanunsa a rufe. Se numfarfashi dayake saukewa akai_akai. abunda ya matukar bawa zannurain mamaki kenan tamkar bashi yaji yana kiran sunan Allah yanzu ba, amma cikin abunda befi sakan gomaba har yayi shiru yakoma gidan jiya,haska kasan dakin zannurain yayi yaga babu faruq babu alamarsa kuma alhalin harya kwanta faruq yana cikin dakin. Number daddy yafara dialing domin yasanarmasa abunda yake faruwa.......

A,part din mommy kuwa, dasauri na toshe kunnuwana da duka hannayena biyu saboda muguwar karar dake tashi adakina, wani mahaukaciyar juyawa naji kaina namun tamkar numfashina zebar gangar jikina, daga nan bankara sanin inda kaina yakeba. cikin zafinnama mutumin yasaki maryam yasakko daga kan gadon yafice da gudu kamar wancan lokacin, aunty tana kan sallaya taji wannan muguwar karar itama, dasauri ta mike tana karanto sunan Allah, dakuma addu'ar neman tsari daga abunki, cikin abunda befi sakan 5 ba, taji karar ta dauke dif, ajiyar zuciya ta sauke cikin dakakkiyar zuciya ta fito falo, karaf a idanunta taga mutum yabude kofar falon yafice da sauri, kasancewar falon akwai wadatuwar haske, cike da tsananin mamaki tayi yunkurin nufar kofar dantaga waye wannan, amma fitowar suhailat a firgice da gudu ya katse mata hanzari, rukunkume aunty suhailat tayi saboda tsananin tsorata da karar dataji, jikinta se rawa yakeyi tamkar mazari tama kasa magana tsabar firgici. ganin yanda take a matukar tsorace aunty ta rungumeta ajikinta tahau tofa mata addu'a akai. Hankalin mommy a matukar tashe tafito daga dakinta, kosu aunty dake tsaye bata kalli inda sukeba tanufi dakin maryam cikin sauri tamkar zata tashi zama, janye suhailat aunty tayi daga jikinta tabi bayan mommy dasauri danse yanzu talura da wani hakayi dayake fita ta wajen key din kofar dakin maryam, suhailat ma cikin sauri tabi bayansu. azafafe mommy ta tatura kofar ta shiga dakin tana kiran sunan maryam da karfi. aunty dake bimata baya tana shiga dakin wani wari gami da kauri mara dadi yaziyarci hancinta, toshe hancinta tayi dasauri cikin tsananin dauriya takarasa shiga dakin, suhailat kuwa dasauri tayi baya tarin dabata shirya masaba ya turniketa, laluban makunnin dakin mommy tayi ta kunna light haske ya gauraye dakin. cike da mamaki gami da tsoro aunty take kallon abunda yafashe din, yanda wani bakin hayaki yake tashi daga cikinsa. Mommy kuwa cike da tsananin tashin hankali take kallon abun, nandanan jikinta yadauki kyarma idanunta sukayi jajur alamar tsananin tashin hankali. Aunty bata lura da halin da mommy take cikiba, tanufi kan gado inda maryam take kwance itama tana kiran sunan ta, amma taji shiru. Batare dawani bata lokaciba aunty ta dakko maryam tafito da ita daga dakin da saurinta cikin tsananin rudewa ganin maryam babu alamar numfashi ajikinta ga wannan hayakin ze iya cutar da ita idan akabarta acikinsa, gakuma jinin dake zuba ahannunta, direct dakinta ta nufa da ita ta shimfideta akan gado,suhailat nabiye da ita abaya a tsorace................

Daddy cikin baccinsa shima yaji wannan karar kamar a zahiri kamar a mafarki, bejima da kwanciya ba bacci nacin sa hakan yasa betashiba, amma kiran wayarsa da'ake tayine yasashi dole yatashi ya dakko wayar yaga zannurain ne, gabansane yayanke yafadi danyasan ba lafiyaba, daga wayar yayi da sauri yakara akunnensa kafin yayi magana zannurain yarigashi dafadin "daddy pls kazo part din yaya yanzu" aiko bari daddy beyi yakarasa zancenba, ya mike da sauri yafice daga part dinnasa, danyanda yaji muryar zannurain yasan bakalauba. zannurain kuwa yanata faman jijjiga mustapha gami da kiran sunansa, ahaka daddy yakaraso yazo yasamesu. "Usman lafiya meyafaru dashi" daddy yashigo dakin yana tambayar zannurain cikin tashin hankali. "Dad, inacikin bacci naji muryarsa yana kiran sunan Allah, amma kafin nayi yunkurin tashi harya koma haka, ahaka na tashi nagansa a zaune." Cikin tsananin farin ciki daddy yace, "usman! Dagaske mustapha dakansa yatashi zaunennan kuma harda magana" "eh daddy dagaske wlh, nima nayi matukar mamaki" wata nannauyar ajiyar zuciya daddy yasauke, tare da fadin. "Alhamdulillah" harsau uku, sannan yakai hannu ya kunna light din dakin. zama yayi a gefen gadon tare da janyo mustapha jikinsa, sakayau daddy yajishi babu wannan mugun nauyi dayayi sanda yana ciwo, gajikinshi normal babu zafinnan kokadan, hannunsa yakai yataba goshinsa yaji shima babu wannan zafin, umarta zannurain daddy yayi yadakko masa ruwa me sanyi a fridge, dasauri zannurain ya mike, ya dakko ruwan ya mika masa, zuba ruwan daddy yayi ahannunasa yahau shafawa mustapha afuskarsa zuwa wuyansa, wani dogon numfashi mustapha yaja, ahankali yafara bude idonsa yana sauke ajiyar zuciya. cikin tsananin farin ciki mara misaltuba daddy yakira sunansa, be amsa masaba se kallo daya bishi dashi. Zannurain dayakasa magana saboda tsananin murna yace, "yaya!" maida kallonsa mustapha yayi akan zannurain ya kura masa ido, cikin tsananin doki zannurain yafara neman layin mommy danya mata wannan daddadan albishir din danyasan setafi kowa murna da farfadowar mustapha, kiran ya shiga amma mommy bata dagaba, behakuraba yakuma kirannata. Daddy dake ta kallon mustapha cike da tsananin tausayawa ganin yanda yaketa sauke ajiyar zuciya ya dubi zannurain yace, "nasan mominku kake kira, idan bata dagaba ka kyaleta zuwa safiya, kakara kiranta" ajiye wayar zannurain yayi yadawo kusa dasu daddy yakama hannun dan'uwansa fuskarsa dauke da fara'a menuni da zallar farin cikin dayake ciki. ganin yanda mustapha yakurawa robar ruwan da haidar ya dakko se daddy ya fuskanci kamar yanason ruwanne, dakkowa yayi yakafa masa abakinsa, aiko tamakar jaririn daya dade besha nonon uwarsaba haka yakama kukkutar ruwan, sedayashanye tasss. sannu daddy yamasa, lumshe idonsa kawai yayi yana cigaba da sauke ajiyoyin zuciya. Kwantar dashi daddy yayi akan gadon, yanufi toilet din dake dakin yadauro alwala yafito yafara sallah dannuna godiyarsa ga ubangiji maji rokon bayinsa dayabawa mustapha lafiya a lokacin dabasuyi zatoba ko tsammaniba, zannurain kuwa yakasa barin kusa da yayansa se kallonsa yakeyi cike da farin cikin tashinnasa............

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull