Kenza eBookz

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 21

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 21

Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 21: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 21. Dana dawo daga school yau senaga aunty suhailat bata…

2,972 words

Dana dawo daga school yau senaga aunty suhailat bata dawoba, kuma yanzu da wuri take dawowa bata kaiwa yammannan kamar da, abun mamaki harnayi aikina nagama suhailat bata dawoba, nikuma gani nikadai a part gashi duhu yafarayi tsoroma nakeji, haka nazauna nikadai tsuru a falo, se kunna kallo nayi danya debemun kewa. Suhailat tasha bacci sosai se dafda magriba ta farka, mamakin dadewar datayi tana bacci tayi. Dasauri ta mike tashiga toilet jikinta duk ya mata tsami se zugi datakeji kadan_kadan akasanta, wanka takarayi tare da gasa jikinta tafito tashirya ta dauki jakarta tafito falo inda kamal yake. cikin yaudararsa yatareta,ya kama tarairayarta yana lallabata,itadai kawai cemasa tayi yakaita gida,cikin tsananin farin ciki kamal yadauketa cak a hannu har bakin mota yakaita yadireta,sannan ya bude mata motar tashiga shima yazagaya yashiga driver seat yajasu zuwa gida. shiru suhailat tayi a motar ko uffan bataceba,duk kuwa da kokarin janta hira da kamal yakeyi, wani iri takejinta kamar ba itaba, duniyar gabadaya ta sauya mata,gashi tasan su mommy sunata nemanta basu sameta a wayaba danta kashe wayar gabadaya. har cikin gida kamal yakai suhailat ya'ajeta,yayi kokarin kara rarrashinta amma tafito dasauri tashige gida. Ina zaune a falo nikadai tsuru naga taga shigo tamkar ancillota ko sallama babu, gabanane yayanke yafadi ganin yanayinta kamar Mara lafiya duktayi wani iri, senayi tunanin ko wani abune yasamu yaya mustapha. Kasa hakuri nayi nace mata, "aunty suhailat lafiya kuwa naga yau kindade baki dawoba ko baki da lafiyane?" Cak suhailat ta tsaya daga kokarin shiga dakin datakeyi, juyowa tayi ta gallawa maryam harara tayi wucewarta,daki. bandamu da abunda tamunba,hasalima ni wani matsanancin tausayintane naji yakamani,batare danasan daliliba,cigaba nayi da kallona har akayi sallar isha'i sannan na tashi nakoma dakina. Suhailat kuwa tana shiga daki ta zube akan gado tana maida numfashi, wayarta ta zaro acikin Jakarta ta kunnata,bayan ta kunnu ta kunna data tahau online. tana hawa taga mommy online dasauri ta danna mata voice call,danbataso takirata video call taga halin datake ciki. Mommy tana kwance a masaukinsu tana hutawa tana chatting dinta,bama ta asibin a wannan lokacin, kiran suhailat yashigo wayar ta, dasauri ta daga dama tanata nemanta tundazu bata shigaba. "Hello mom'nah" "na'am, daughter ina kika boyene yau tun dazu nake nemanki a waya bansamekiba" cikin son boye damuwarta tace, "mom yau bandawo da wuriba kuma dana dawo bacci yadaukeni seyanzu natashi nayi wanka na kunna wayar" "ayya,daughter sannu,inafatandai bakyashan wahala a school din" "um,banasha mom, kewarkuce dai kawai tadameni data yayana" murmushi mommy tayi tace, "muma munyi kewarki sosai,kodayaushe daddy cikin zancenki yake." "Yawwa mom,kirokarmunshima dan Allah inason zuwa a week dinnan." "kibari next weekend su haidar zasuzo sekibiyosu kuzo tare" wani irin dadine ya lullube suhailat zataje taga life dinta nankusa, hira sukacigaba dayi da mommy tanata tambayarta abubuwan gida dayanda abubuwa suke tafiya,kafin daga bisani sukayi sallama. kwanciya suhailat tayi bayan sungama waya da mom tana tunani akan abunda yafaru da ita yau ita da kamal, tana ganin yanata kiranta amma taki dagawa, ko abinci bata nemaba balle tayi tunanin yin sallah tacigaba da kwanciyarta..............

Kwanci tashi babu wuya agurin Allah, yausu mustapha sunfi wata daya a India,amma dai jikinnasa gashinan gashinanne,har wanna lokacin besan wake kansaba bashi da aiki se bacci kuma komai sedai a masa,sedai a kwantar a tayar gashi memakon yarame sewata irin kumbura yakeyi. Yaya sadiq yazo gida sau biyu, daddyma yazazzo gida su suhailatma sunje can Indian saudaya sunduba jikinnasa. Aunty tazo kano itama taga yanda muke nida suhailat, mommy ce dai bata taba zuwa tunda suka tafi. Suhailat daa abunda yafaru tsakaninta da kamal yadameta, amma daga baya kuwa seta ware tamaida komai bakomaiba,kuma sukacigaba da mu'amalarsu da kamal. Munyi hutu a school na jaranawar second term da mukayi, yanzu saurana term daya nayi candy, a islamiyyaba munsauke alkur'ani amma a biye, bikin sauka kawai yarage mana shima ankusa samana rana. Acan India kuwa daddy ganin jikin mustapha yakiyin yanda akeso yace gaskiya gida za'adawo amma mommy taki yarda, seda aunty taje taga jikindai basauki sannan ta matsawa daddy dole badon mommy tasoba ta bari adawo gidan. yau talata yaune kuma su mommy zasu dawo, farin cikin danake ciki baze misaltuba yau zanga *heartbeat* tun safe muka gyare masa a part dinsa saboda acan zeyi jinyartasa. Aunty ma tazo kanon amma banda aliya. wani malami a Zaria,daya shahara a karya sihiri da cire jinnu daga jikin mutum,da maganin mayu dadai sauran lalurori, aunty tayi tattaki dakanta harzuwa kauyen dayake ta masa bayani akan ciwon mustapha, domin taji ana fadar kyan maganinsa sosai. dafarko cewa yayi akawo masa mustaphan har inda yake, sekuma aunty ta rokesa akan idan babu damuwa sutafi kano tare dashi, saboda yanayin da mustapha yake ciki, idan akace za'azo dashi garin wahala kawai za'asha saboda kauyen dayake basuda titi me kyau hanyoyin duk a rube suke. beyi wata doguwar gardama ya amince yabiyo aunty kano, amma da sharadin baze kwanaba aranar zejuyo gida saboda masu zuwa karbar magani, aunty tace babu komai ahakanma sungode.

Karfe biyu na yamma a naija taiwa su mommy, haidar ne yaje ya dakkosu a airport zuwa gida. ina zaune ina karatun alkur'ani aunty tashigo dakin danake da sallama,amsa mata nayi bayan na kai aya narufe alkur'anin. "Maryam karatu akene" murmushi nayi nace "eh aunty" "masha Allah, yagajiyar aikin da kukasha" "babu gajiya aunty" gyara zama aunty tayi tace, "dama zuwa nayi nace miki,kije part din baki kitahoda malaminnan damuka zo tare,kirakashi part din Muhammad,nizan karasa kisameni acan" amsa mata nayi ta mike tafice, nima ajiye kur'anin nayi a ma'ajiyarsa nafito, na nufi part din bakin. Malamine me cike da kamala da nutsuwa,yanata lazimunsa naje nasameta. gaishesa nayi cikin mutuntuwa, sannan na isar masa da sakon aunty. biyoni yayi a bayana har zuwa part din *heartbeat* gabana sefaduwa yakeyi, ga farincikin zanganshi gakuma fargabar halin dazanje in riskeshi aciki. A falon sama na tarar da mommy, da aunty da daddy harda yaya mustapha. kallon mommy nakeyi kamar yadda itama take kallona irin kallon data sabamun, nikuma ina mata kallon mamakin yanda naganta,tamkar bame cinyaba, babu wata alamar damuwa a tattare da ita,amma fa aganina. cikin fara'a nakarasa gareta ina gaisheta dan itace acikinsu nadade bangantaba,amsamun tayi itama da fara'ar dauke a fuskarta takara da fadin, "maryama, ya gidan ya karatu?" "Alhamdulillah mommy, yame jiki" "jiki sai godiyar Allah" "Allah, yakara sauki yasa kaffarace" "ameen, duka dakin suka hada baki gurin amsawa" gaishe da daddy nayi dasuke magana da malam,shima ya amsamun da fara'arsa. Daddy nema kanaganinsa kasan yana cikin damuwa,dan har yar rama yayi. inason na tambaya ina mara lafiyar amma na kasa, haka na mike nafice nabasu guri. jagora daddy da yaya sadiq suka yiwa malam har dakin mustapha inda yake a kwance akan gado yana bacci. itadai mommy ba'ason rantaba aka dauko malaminnanba shiyasama bata wani bashi mahimmanciba. sadiq ne yakara yiwa malam bayanin abunda yake damun mustapha dalla_dalla, duddubashi malam yayi da baiwar da Allah yabasa. Shikansa malam yayi mamakin ciwon mustapha amma ko tantama bayayi aikin sihirine ko jinnu a ciwon mustapha. jakar magungunansa ya dakko yabawa daddy wani kullin magani, na karya sihiri. Za'a kwabashi da man habbatussauda se'adinga shafe masa jiki dashi safe da dare, se kuma ruwan jarka dayace abashi yayi tofi aciki shima yace kullum adinga diga masa abaki, atabbatar yana shiga cikinsa,insha Allahu ko wanne irin sihirine ajikinsa seya karye. godiya sosai daddy da aunty suka masa, kudi masu kauri daddy yabashi a matsayin sadaka danyaki fadar abunda za'a bashin. Bayan anyi sallar la'asar daddy yasa driver ya maidashi gida........

Mommy ce zaune a dakinta ita da daddy da aunty suna tattunawa akan abunda malam yace. "Nifa gaskiya sam banyarda da abunda malaminnan yaceba, kawaidai yazo yafadi abunda yagadamane, amma acikin awanni biyu harya gane sihiri akawa son" cewar mommy tana tabe baki. "Aunty atika kenan, aisu irin wadannan malaman baiwace Allah yabasu, kuma ni nayarda da abunda yace, saboda wlh ciwon Muhammad yayi kama da sihiri, idan kikayi la'akari yanayin ciwonnasa. Duk ciwon dakikaga anrasa gane kansa balle gindinsa, kuma ankasa gano meke damun mutum, tobaya wuce jinnu, kokuma asiri ko mayu" cewar aunty. kara tabe baki mommy tayi tace, "to saudart shiko mustapha, waye zemasa wani asiri, me yaywa wani, shida ko harkar mutane baya shiga" "hmmmm,aunty atika kenan, bar mutum kawai yanda kika gansa,zakiga kina rayuwarki baruwanki da mutum amma shi akwai mugun nufinsa akanki, mudai kawai muyi addu'a Allah yarabamu da sharrin makiya da mahassada" "amin, amma ni banso akayiwa mustapha wani maganin hausaba, dandai kundagene shiyasa na bari, danni gaskiya banyarda da wani ingancinsaba" daddy dayake saurarensu yace, "yanzu duk wannan zancen bashi bane, addu'a kawai itace mafita,kuma mu jarraba amfani da maganin malam din muga abunda Allah zeyi. Ita ko,aunty shiru tayi kawai tana kallon mommy, yanda taga yanzu hankalinta ya kwanta ba kamar farko da mustapha yafara cutaba, duk wannan muguwar damuwar datakeyi akan ciwonnasa yanzu tadena.......

Kamar yadda malam yace adingawa mustapha amfani da magani haka ake masa, kullum babu fashi, yan dubiya kuwa kullum cikin zuwa sukeyi kota ina, duk da ba'a bari aganshi saboda bakin mutane, kowa da abunda zece. yau tsawon sati guda kenan anayiwa mustapha amfani da maganin, yaya sadiq ne yake jigilar shafa masa maganin da diga masa ruwan kodayaushe, amma jikin mustapha tamkar ba'a magani babu abunda yakaru nasauki sema karin ciwo, zuwa yanzu daddy yafara sarewa da ciwon mustapha ganin yakijin magani, mommy kuwa se masifa take tana cewa dama seda tace kar'ayi wani maganin hausa gashi babu abunda yayi sema karin ciwo. Aunty ce take kara tausarsu akan akara gwadawa zuwa nanda sati daya idan beyiba se'acanza wani malamin kokuma a fitar dashi kasar saudiyan kawai.

*MARYAM*

Har yau bansamu naga mustapha ba duk kuwa da matukar gwadayin ganinsa danake sonyi, yaudai nakasa hakuri seda nacewa yaya sadiq inason ganinsa dan tunda yafara ciwo banganshiba, shine yace dasafe nazo shine agurinsa sena shiga naganshi. da misalin karfe goma na safe bayan nagama aikina nanufi part dinnasa, babu kowa kuwa kamar yadda yaya sadiq yace seshi dayake kula dashi, seda najirashi a falo yagama kimtsashi sannan yafito yace nashiga naganshi. da mamaki na kalli yaya sadiq nace, "yaya nikadai zanshiga bandakai" "haba maryam,kemafa yar gidace kishiga kawai babu matsala zanyi wayane tun dazu ake kirana da ina ciki" gyada masa kai nayi. Ahankali na mike nafara tafiya zuciyata na luguden bugun datasaba aduk lokacin danayi kusanshi dashi. ahankali na murda handle din kofar dakin nashiga da sallama, dukda nasan babu me amsamun. Faduwar gaba da karuwar bugun zuciyatane suka dirarmu alokaci daya sanda nayi arba dashi kwance idanunsa a lumshe. jankafata nayi data faramun nauyi nakarasa gaban gadon ina mai kura masa ido. Jallabiyace ajikinsa wadda babu alamar datti a tattare da ita. "Ya Allah muntuba,Allah ka iya mana" nafada acikin zuciyata ina kara girmama ikon Allah, mutum me kwazo da kasaita,shine acikin wannan yanayin kwance komai sedai a masa,lallai muji tsoron Allah domin duniya abar banzace. Lumshe idona nayi ina tuno yanda yake abaya da lafayarsa amma yanzu gashi a kwance ko hannunsa baze iya dagawaba. ahankali nabude idona nasauke akan kyakkyawar fuskarsa da ita kadaice bata kumburaba ajikinsa. Hawaye ya shiga kwaranyomun a fuskata na tsananin tausayinsa, ga wani gumi dayaketa tsatstsafo masa na azabar ciwo, kawai jinayi nakai hannuna kan goshinsa ina ina share masa gumin kansa batare dana shirya yin hakanba, dukda wani zafi da huci danakeji a tafin hannunnawa amma nakasa cirewa daga goshinsa, sema kara kamasa kandanayi da danyatsuna biyu kamar yadda akeyi idan za'a kamawa me ciwon kai, kai. nafara karanto abunda ake karantawa nakamun kai acikin zuciyata, jikinane kawai yabani yanda kannannasa yake zuba uban gumi yana masa ciwo, seda na kammala karanta duk abunda ake karantawa sannan nasakar masa kannasa. Rankwafowa nayi daidai fuskarsa har ina jiyo hucin numfashinsa a fuskata,lumshe idona nayi,bugun zuciyata kuma ya karu, hannuna na rawa nakaishi daidai bakinsa naraba kananun lips dinsa nasama dana kasa, nafara karanto ayoyin rokiyya a fili yana shigarsa tacikin kunnensa kuma ina tofawa acikin bakinsa, dan idannatsaya debo ruwa nace zantofa aciki zanbatawa kaina lokacine, kuma yaya sadiq yana falo yana jirana. naji abakin aunty ciwon dake damunsa ana tunanin jinnune, duk da tsananin tsoron danakeji akan abunda nake aikatawa,amma haka na daure zuciyata, nacigaba da karanto masa domin wannan shine kadai taimakon dazan iya masa,kuma nasan bazan kara samun wata damar dazan masa irin wannanba.........✍️

*kuyi manage da wannan*

*By* *zeey kumurya*

ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_

*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*

*Bismillahirrahmanirrahim*

3️⃣3️⃣

..........cikin ikon Allah harna gama karanta masa yaya sadiq bezo kiranaba kuma babu wanda yashigo,abunda ya bani mamaki kenan. Ammafa naji ajikina, dan naji jikina yayi mun wani iri kuma se rawa yakeyi, gabadaya na hada gumi ga wani mahaukacin bugu da zuciyata takemun. ahankali nakai hannuna dake karkarwa na taba goshinsa,senaji zafin jikinnasa ya ragu, se ajiyoyin zuciya naji yana saukewa akai_akai cikin baccinnasa, dauke hannuna nayi daga kannasa nima ina sauke ajiyar zuciyar. badon nasoba bakuma danna gaji da kallonsa naja jiki nafito zuwa falo, abun mamaki babu yaya sadiq babu dalilinsa, zama nayi akan kujera ina maida numfashi hannuna dafe dakaina dayake mugun saramun,wani irin shauki da kaunar yaya mustapha ne, yake kara ninkuwa araina gami da tsananin tausayinsa,daga gani base anfadaba kasan yana jin jiki,dakuma azabar ciwo, dama dazan iya dana maido da ciwonnasa jikina, wasu guntayen hawayene suka silalomun wanda bansan dalilinsuba,tabbas idan Allah yabaka lafiya yagama maka komai najin dadin rayuwa. nakai ten minutes azaune ina jiran yaya sadiq amma naji shiru bedawoba, mikewa nayi zanje naduba falon kasa koyacan, a kan steps mukacikaro da mommy,datake hawowa benen cikin sauri har bangazata tayi, bayanayi dasauri harna kusa faduwa dama jikina babu kwari sekuma narike karfen benen. "Maryam!" naji mommy takira sunana da alamun mamaki. Gabanane yayanke yafadi danbansan me mommy zatamunba intaga nikadaice agurin danta. "Na'am" na'amsa mata cikin rawar murya. "Mekike anan" cikin dauriyar abunda nakeji ajikina nace mata, "mommy nazo duba yayane, shine yaya sadiq yace injirashi zeje yadawo, kuma haryanzu bedawoba" mommy batakaramun magana sebina datayi da kallo, kasa nayi da kaina cikin faduwar gaba. "Yanzu sadiq son din yabarmun shikadai shikuma yakama gabansa" mommy ta fadi haka cike da bacin rai" batajira mezanceba ta raba tagefena tahaye saman. wata nannauyar ajiyar zuciya nasauke ina bin bayanta da kallo, "yanzu da'ace ina dakin mommy tazo tasameni mezance inayiwa danta,nagodewa Allah daseda nafito ita kuma tazo. Karasa sauka nayi nafice daga part din,banga yaya sadiq ba harna karasa part dinmu. Dakina nashige na kwanta akan gado,kaina na juyamun,addu'a nashiga karantowa acikin zuciyata har baccin wahala yadaukeni.

Cikin baccina naji ana kiran sunana tare da tabani, ahankali na bude idona dasuka sauya kala saboda bacci, nace. "Uhm" muryar aunty naji tana fadin, "maryam, kitashi kiyi sallah baccin ya isa haka, har 2 tawuce fa" mikewa nayi zaune cike da mamakin dadewar danayi ina baccin ina yar mika nace, "aunty har 2 fa tawuce kikace banmasan nadade hakaba" "aitun dazu nashigo naga kina tashan bacci,nima baccinnayi banjima da tashiba" "bari naje nayi sallah aunty" nafadi haka ina sauka daga kangadon har yanzu idona begama budewaba kamarma inkoma baccin haka nakeji" bakina na wanke na dauro alwala nafito nayi sallah, har lokacin aunty tana kishingide akan gadona tana danna waya. bayan na idar aunty tadubeni tana murmushi tace, "kinjini da mutuniyar taki, wai yaushe zandawo kokuma ita tabiyoni" murmushin nayi nima nace, "gaskiya dai aunty dakin taho da ita, yanzu se ita kadai agidan ko?" "Maryam makaranta shiyasa bantaho da itaba,amma jibi Friday zance yayanta yakawota seta koma ran sunday, kuma bata gidama tana gidan kanwar abbansu dayake bamu da nisa" "yawwa aunty, harnaji dadi dakikce zatazo Allah yakaimu jibin" "ameen" gyara zama nayi natambayi aunty abunda yake damuna arai dafadin"aunty yame jikin kuwa" "jiki da sauki maryam, daga gurinshi nakema nabiyo tanan,yau jikinnashi yayi kyau sosai" gyada kai nayi nace, "Allah ubangiji yakaro sauki,amma aunty meyasa ba'abashi rubutu kokuma adinga masa tofi aruwa ana shafa masa ajiki" "nima dafarko nayi wannan tunanin maryam,amma ganin malam yabashi na shafawa ajikin yasa banmaida hankali akan adinga masa hakaba, kuma shima yabada tofin ana diga masa abaki" "hakane aunty, amma ni aganina addu'a bata yawa, malaminmu na islamiyya ya turamun ayayoyin da ake karantawa na rokiyya a wayata wanda SUDAIS ne yake karantawa,kullum kafin nayi bacci sena kunna naji harna haddacema yanzu, meze hana adinga kunnamasa shima yanaji, nikuma zantofa aruwa se'abashi yasha kokuma ashafa masa ajiki." Cikin gamsuwa da bayanan maryam aunty tace,gaskiya maryam kinkawo abu me kyau,aidamu bamuyi tunanin koda karatunne adinga kunnamasaba, wannan shawarartaki tayi sosai maryam, mungode Allah yasaka da alkhairi, anjima bayan la'asar idan zani semuje tare a fara masa." "Bakomai aunty fatanmu kawai,Allah yabashi lafiya" hira mukacigaba dayi da aunty, zuciyata fess da farinciki zandinga ganin *heartbeat* kullum, kuma da izinin Allah seya samu rangawame aciwon dake damunsa dan ayar Allah bakarya bace,kuma alkur'ani warakace ga dukkan kowanne ciwo.

Kamar yadda aunty tace, dayamma mukaje na kunnamasa karatun adakinsa ita kuma takawomun ruwa a cup na tofa aka shafe masa jikinsa dashi. mommy da aunty tafada mata abunda za'adinga yiwa mustapha batace komaiba, daddy kam yayi farinciki sosai yayta sawa maryam albarka. Tundaga ranar kullum senaje namasa safe da dare,wataranma aunty tana falo nikadai take bari adakin inyi ta kallonsa. Kuma alhamdulillah jikinnasa yanasamun sassauci, dan wannan kumburin jikinnan nasa duka babu yanzu, saidaifa wani abun mamaki, duk sanda nazo nakunna masa karatun kuma akashafa masa ruwan tofin ajikinsa sejikinsa yayi sanyi kamar nakowa, amma washegari, ina kara zuwa za'a masa se'aji zafin jikinnasa yadawo zafi zau se ankuma masa yake tafiya. Su aliya sunzu sunyi kwana biyu ita da yan'uwan abbansu da yayanta,umma da saleemat ma sunzu harda gwaggo, duk sunzo dubiya, muna waya da saleemat ne nakefada mata ciwon yaya mustaphan, shine tafadawa umma, umman tace kodan kirkin sadiq zasuzo suduba yayansa,shine tayiwa gwaggo magana sukazo tare. Gwaggo anzo gidan alh.menasara hankali ya kwanta, mommy kam bata wani kulasuba daga gaisuwa shikenan, danma aunty tananan itakam ta karbesu hannu bibbiyu faran_faran.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull