Kenza eBookz

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 27

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 27

Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 27: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 27. ..............Mommy tana gama fadar haka tajuya tafice…

3,241 words

..............Mommy tana gama fadar haka tajuya tafice daga dakin gabadaya tana kissima irin muguntar dazata kara shiryawa mustapha harma da maryam da daddy nangaba. har aunty ta mike zata bita daddy ya katseta da sauri ta hanyar fadin, "ina zaki kuma saudaurt?" batare da aunty ta juyo ta kalleshiba tace "zanje naduba jikin maryam ne, nasan zuwa yanzu tatashi" daddy yasan halin aunty sarai idan aka bata mata rai idan bataje ta mayar da martaniba batajin dadi yasan gurin mommy zata suyita cacar baki. Hakan yasa yace mata tadawo ta zauna zasuyi magana. batare da aunty tasoba tadawo ta zauna tana sassauke numfashi gami da huci cikin tsanananin takaicu. duban aunty daddy yayi da kyau sannan yace, "a matsayinki na mace wadda yakamata ace kin fini saka ido akan al'amuran cikin gida ina son kifadamun gaskiya akan duk wannan mummunan aikin da'ake aikatawa acikin gidana baki saniba.?" wani gwauron numfashi aunty ta sauke tace, "wlh yaya koda wasa bantaba jin wannan zancenba kokuma naga wani abu makamancin haka, duk da ina yawan zuwa gidannan amma ai kasan nimaba mazauniyar garinnan baceba tayaya zansani" shiru daddy yayi cikin tsananin takaici gami da kunar zuci, jin abun yake tamkar almara wai a cikin gidansa, dan cikinsa yakewa yara mata fyade. "Wa'iyazubillah" yafaurta a fili idanunsa na taruwa da kwallar bakin ciki, yarasa wacce irin mace Allah yabasa, yarasa wanne irin son duniyane da mommy. Yanzu duk daular datake ciki ita da yayanta amma be ishetaba to wanne irin kudi takeso ita kuwa tayi arayuwarta. Faruq ne yakatse daddy daga tunanin dayake ta hanyar fadin, "yanzu daddy kana kallo mommy tatafi batare dakadau wani kwakkwaran mataki akantaba ai kamata yayima kamikata ga hukuma su hukuntata akan lefin datayi" wani yawu me daci daddy ya hadiye dakyar kafin ya numfasa yace. "Babu matakin dazan dauka akan atika umar, kuma bazan mikata ga hukumaba kodan darajarku ku yayanta, amma maganar aure tsakanina da ita ta kare bazan iya kuma cigaba da zama da ita ba" "haba daddy wanne bashine iya hukuncin dayakamata kamataba kawai, kamar yadda yafaruq yafada yakamata kamikata ga hukuma su hukuntata" cewar haidar dayakatse daddy cikin tsananin takaici gami da bakin cikin abunda mahaifiyarsu ta aikata. "Hakan yakamata nayi nima Aliyu, amma kasani Allah ba azzalumun bawansabane da sannu tun anan gidan duniya zenunawa atika ishara akan abunda ta aikata, domin " duk *ABUNDA KASHUKA SHIZAKA GIRBA*" shiru sukayi kowa da abunda yake sakawa acikin zuciyarsa. suhailat ce tatashi tafice daga dakin tana kuka wiwi meban tausayi, haidar ne yabi mata baya cikin tsananin tashin hankali. aunty ma batare data kalli kowaba tamike tafice domin tadubo maryam dan zuciyarta na ayyana mata tamkar mommy tanacan tana mata wani mugun abun. Zannurain da faruq ne suka bi bayanta, sadiq kam kunya tahanashi koda dagowa ne, shikansa betaba tunanin wannna ranar tonan asirin zata zo masaba arayuwarsa, dakyar ya iya mikewa shima yafice.binsa da kallo daddy yayi cikin tsananin mamakin sadiq din daya kasa barinsa har yanzu, sadiq din dayake ganinsa me hankalin dababu kamarsa kaf cikin yayansa amma shine yake aikata wannan danyen aiki. gaskiya yayi Allah wadai da auren mommy dayayi, ta cucesa ta cutar masa da yayansa tabata musu tarbiyya, yana tunanin ze sake shawarane ya mika mommy da sadiq hannun hukuma ta bakin su faruq din, domin yazama izna agaresu anan gaba. Mustapha dake zaune tamkar mutum mutumi, domin bazece ga a duniyar dayake cikiba. Saitin zuciyarsa yadafe da hannunsa saboda harbawar datakeyi gamida zafi tamkar ana watsa masa garwashi, gabadaya yadena fahimtar komai, duniya juya masa kawai takeyi. cikin tsananin dauriya idanunsa a lumshe ya sakko daga kan gadonnasa yafara takawa zuwa gurin da daddy yake a zaune. Kafafunsa tamkar ba'ajikinsaba saboda taruwar jinin da sukayi nazama guri daya, ga nauyin dasuka masa ga wani jiri dayake jibanshi abu goma da ishirin duk shi kadai. daddy dake binshi da kallo cike da tausayawa ya lumshe idonsa saboda wata kwalla data cika masa ido na tsananin tausayin mustaphan, yasan dole yafi kowa shiga tashin hankali agame da wannan al'amari domin rashin asali bakaramin tawaya bane ga rayuwar dan'adam. Ahankali ya tsugunna agaban daddy akan gwiwowinsa ya dora hannunsa akan cinyar daddy, ilahirin jikinsa rawa yakeyi saboda tashin hankali.bCikin tsananin dauriya yafara magana dakyar da muryarsa dake nuni da tsantsar damuwa yace. "Daddy bani da baki kokuma wasu kalmomi dazanyi amfani dashi gurin gode maka arayuwata, domin Kaine jigo kuma bango na rayuwartawa. tabbas kacika mutum me tsananin kirki da hali nagari da samun kamarka zeyi wuya a zamanin yanzu. Daddy alfarma daya zakamun ayanzu shine kafadamun inda mahaifiyata tabakani, nikuma ayau ba gobeba zantafi nemanta kuma da izinin Allah indai tana raye bazan dawoba harse nagamu da ita." Yakasarashe zancen yana sassauke numfashin wahala tare da zubar hawaye masu dumi akan kuncinsa. Ahankali daddy yabude idanunshi dasuka rine zuwa ja yasaukesu akan fuskar mustapha. Hannunsa yakai yafara goge masa hawayen fuskarsa cikin tsanani so da kaunarsa kafin yafara magana kamar haka. "Insha Allahu, mustapha bama fada makaba kawai zanyiba, dakaina zankaika har garin kuma natayaka Neman mahaifiyarka da danginka, dama burinane hakan tun kafin yau. mustapha be iya cewa komaiba, saboda yanayin dayakejin kansa, mikewa yayi juwa nadibansa yanufi toilet domin yasakarwa kansa ruwa kozeji dadin jikinsa. binsa da kallo daddy yayi cike da tausayawa harya shige toilet din. cikin sanyin jiki shima ya mike ya fice daga part din....

Apart din mommy kuwa, mommy cikin sauri takarasa part dinnata direct dakinta ta nufa tafara hada abubuwan datasan zasuyi mata amfani domin tasan koda daddy befurta mataba tasan zamanta agidansa yakare daga yau, kodama bekareba yau dole ta bazama Neman mafita akan wannan kuncewar al'amarinnata dayazo mata alokacin dabatayi zatoba. cikin sauri take diban abubuwanta masu amfani tana zubawa acikin wata handbag dinta. Tana cikin hada kayan suhailat ta shigo dakin da gudu da kukanta. Sororo mommy tayi tana kallonta kafin ta tabe baki tacigaba da diban kayanta. ganin kukan suhailat din yaki karewa mommy ta dubeta a kufule tace, "daughter wai lafiya kikazo kika sani agaba da kokekoke?" cikin shan majina suhailat tace, "mommy dan Allah meyasa kikayi haka, meyasa kika cutar da yaya irin haka, me yayi miki da kika masa irin wannan tsanar?" Wani murmushi mommy tayi kafin tadubi suhailat tace, "daughter haryanzu ke yarinyace bakisan me duniya take cikiba,kuma duk bayanin dazan miki bazaki gane menake nufiba, amma komai danakeyi danku nake" mommy ta karashe zancen da daukar mayafinta ta yafawa. "wai mommy mekike shirinyi, ina kuma zaki?" suhailat tatambayi mommy cikin tsananin mamakin ganin yanda take ta sauri zata fita. "Zankoma gidanane dake lamido kafin gobe kuma nabar garin gabadaya" baki sake suhailat take kallon mommy ta bude baki zatayi magana mommy takatseta ta hanyar fadin. "Banson kikara cemun komai daughter, abunda nakeso dake kawai shine ki kwantar da hankalinki zandawo nanbada jimawaba,acan dinne senafi jin dadin yin aikin dazanyi batare da wata matsalaba." Mommy tana gama fadar haka ta fice daga bedroom dinnata cikin sauri batare data jiraa msar suhailat ba. wani kuka suhailat tafashe dashi cikin tsananin jin takaicin halin mommy, duk abunta da mugun halinta bazata iya abunda mommy tayiba gaskiya mommy tabata mamaki bakadanba.

A falo mommy sukayi kicibus da aunty data shigo. Aunty danne bacin ranta tayi taki koda kallon inda mommy take tayi shigewarta dakinta inda maryam take. Mommy kuwa bin aunty tayi da kallo kafin tayi wani murmushi da ita kadai tasan ma'anarsa sannan tafice tanufi parking space, yau ko direbanta bata nemaba dakanta zatayi driving din. Har lokacin maryam tana kwance tana baccinta, sedai daga gani baccinnata bana jin dadi bane, a wahalce take yinsa. Ahankali aunty takarasa gareta tasa hannunta tana shafa fuskarta, tausayin maryam ne yakara mamaye mata zuciya yanda take fitar da numfashi kana gani kasan na wahalane.

toilet aunty ta nufa ta watso ruwa ajikinta domin taji dadi, dan yanda takejin kanta a wannan lokacin baze misaltuba, jinta take a wata duniyar databan tsabar damuwa. Tana fitowa daga toilet din taga maryam na mutsu_mutsu alamar tatashi. Da sauri aunty ta karasa gareta ta tallafota jikinta tana kiran sunan sunanta. Memakon maryam tabata amsa se kuka data saka cikin wata wahalallaiyar murya tafara fadin, "dan Allah kumaidani gida gurin gwaggo ta, gwara na zauna agurinta akan zaman gidannan da'ake son cutar da rayuwata d...... Rufe mata baki aunty tayi, ganin haryanzu bata gama dawowa cikin nutsuwartaba, daidai lokacin daddy ya murda handle din kofar dakin bakinsa dauke da sallama, yazone domin yaduba jikin maryam din, kuma yanata knocking aunty bata jiba, kalaman maryam gabadaya akunnensa tayisu, runtse idonsa yayi cikin tsananin takaicin wai yau gidansa ake neman tsarin zama acikinsa, gaskiya atika ta gama dashi. Muryar maryam da yanda tayi maganar cikin kuka yatuno masa da muryar matar dabaze taba mantawa da itaba arayuwarsa, tamkar itace ta dawo take masa magana a yanzu. cikin sanyin jiki yakarasa cikin dakin inda sautin kukan maryam ne kawai yake tashi, aunty kuma na aikin rarrashinta. "saudart jikinnatane haryanzu" aunty dabatasan da shigowarsaba ta juyo tana kallonsa idanunta cike da kwalla tace, "inajin fa yaya haryanzu bata dawo hayyacintaba,yanzu ta farka sekuma ta fara surutai" daddy bece komaiba ya mike yanufi karamin fridge din dake dakin ya dakko ruwa a roba medan sanyi, ya tsiyaya a cup sannan yatofa addu'a yamikawa aunty yace tabawa maryam din tasha. Tallafota aunty tayi takafa mata cup din a baki, aiko Tass maryam ta shanye ruwan. "Akaro miki ruwan?" Aunty ta tambayeta. Girgiza kai tayi alamar a'a tana sauke ajiyar zuciya, taimaka mata aunty tayi ta koma ta kwanta saboda jikinta sam babu kwari. "ya Jikinnaki, yanzu inane kuma yake miki ciwo?" Aunty ta jero mata wannan tambayar. kanta dake mugun sara mata ta nunawa aunty da hannunta idanunta a lumshe, se kuma hannunta inda ta yanke da madubi. "sannu Allah yakara sauki, hannunnaki kuma bari nakira doctor yazo yaduba mikishi" gyada mata kai kawai ta iyayi. tanaso tatambayeta yajikin mustapha amma maganama wahala take mata. "Maryama, sannu kinji,Allah yakara sauki" muryar daddy ta doki kunnena, bude idona nayi da sauri najuya inda najiyo sautin muryartasa. Daga masa kai nayi shima alamun da sauki. fita daddy yayi ya zauna a falo, ya rafka tagumi yanata tunane_tunane. Aunty ce ta mike ta hadowa maryam tea mekauri, taimaka mata tayi,cikin ikon Allah kuma tasha sosai. Se'alokacin naji wata nutsuwa tafara lullubeni har gumi yana tsatstsafomun ajikina. aunty ce tataimakamun takaini toilet domin nayi wanka ko zankara jin dadin jikina. Jikina Sam babu kwari haka nadaure na watsa ruwan. ga zuciyata dakemun wani irin bugu tamkar wani abu yana shirin faruwa dani. Falo aunty tadawo gurin daddy bayan maryam tashiga wanka, zama tayi agefensa tana kallonsa yanda ya rafka uban tagumi da hannu bibbiyu. danne duk wata damuwarta tayi domin ta taushi dan'uwanta danta fuskanci yana cikin tsananin damuwa. Cikin tausasa lafazi tafara masa magana. "Yaya dan Allah kayi hakuri akan abunda yafaru mudauki komai amatsayin kaddara wadda tariga fata. kuma rubutacciya haka Allah ya kadarto mana babu yanda zamuyi." wani gwauron numfashi daddy yasauke sannan yadubi aunty Cikin raunin murya yace, "saudat zuciyata cike take da tsananin bakin cikin abunda atika tayi,yanzu ace a gidana akeyin wannan danyen aikin, amma bansaniba yanzu idan duniya taji kotasan halin da'ake ciki wanne kallo za'amun, dayawan mutanema cewa zasuyi ninakeyi dan wata bukatar kaina" "kayi hakuri dai yaya, mugodewa Allah dayasa maganar bata yaduba ita kuma aunty atika kabarta ita da Allah,shikadai yasan meze mata" "hmmm, nacanza tunani saudart zankai karar atika da sadiq ga hukuma da kaina, domin a yanke musu hukunci daidai da abunda suka aikata" da sauri aunty tadago ta dubi daddy cikin mamakinsa, shida dazu_dazu yagama cewa yabarsu da halinsu amma kuma yanzu yacanza ra'ayi. kara gyara zama aunty tayi ta fuskanceshi sosai, sannan tace. "Haba yaya yakuma zakace haka, hannunka baya taba rubewa kayanke kayar, sadiq naga nadama tsantsa a idonsa, nasan yanzu yanacan yarasa ina zesaka kansa. Kuma yanzu idan kayi kararsu katonawa mustapha asirinsa dake rufe, duniya zatasan kowaye shi. kaga mukuma bazamuso hakaba, dan Allah yaya kamar yadda kace da farko kabarsu da halinsu yanzunma kajanye batun mikasu ga hukumar." "Saudat abunda atika tayifa bakadanbane ta cutar da bayin Allah dabasujiba basu ganiba, kina ganin idan muka barsu bamuso kanmu dayaba" "yaya babu batun sankai, ayanzu koda kayi karar anti atika tanada kudin dazata iya kwatar kanta, tunda kasan shari'ar yanzu bata Allah baceba, karar anti atika da sadiq daidai yake da muntonawa kanmu asiri" shiru daddy yayi bekara cewa komaiba. Ganin haka aunty tashiga rokonsa gami da bashi baki, dan ita bazataso ayi karar su mommy, batason kowa yasan mustapha badan daddy bane. badon daddy yasoba yahakura yakuma tabbatarwa da aunty ta shirya idan anyi sallar la'asar zasu tafi Niger domin nemo dangin mustapha, kuma da maryam daza'atafi. Aunty taso fahimtar dashi hakan bamafita bane, domin idanma sunje Niger din gurinwa zasu nufa ta ina zasu fara Neman wani dangin mustapha, kuma kodama sunsan inda zasu nufa yau yayi wuri su tafin, tunda mustaphan ba ishashshiyar lafiya gareshiba. Amma daddy yace mata hakan kawai shine mafita dan mustapha yatada hankalinsa sosai. Badon tasoba ta amince. batayi kuma tunanin komaiba da daddy yace, zasu tafine tare da maryam, danko befadaba bazatabar maryam dinba dankar mommy ta cutar da ita.

Daddy bayan sungama magana da aunty direct masallacin dake manne ajikin gidansa yanufa domin ya kaddamar da abunda ya kudurcewa ransa tun a lokacin dayayi arba da maryam, yadade da kudirin aransa amma yau yayi alkawarin kafin subar kasarnan seya idda nufinsa. Kamar yadda yazata kuwa liman na zaune a masallacin shida wasu tsirarun mutane. Gaisawa sukayi da kowa cikin mutunci da sakin fuska tamkar babu abunda yake damunsa,duk da karfin haline kawai yakeyi. Gefe suka koma shida malam liman yamasa bayanin bukatarsa, yakuma tabbatarmasa da a yanzu yakeson ayi. Sauran mutanen dake masallacin malam liman yahado kansu atake agurin aka daura auren da daddy yabukata akan sadaki naira dubu hamsin wanda daddynne yabada. Malam liman ne yayi waliccin amarya daddy kuma na ango.(To Allah yasanya albarka a auran, yabada zaman lafiya me dorewa, tunda daddy bebari naji daurin auren konasu wayeba😜)....

Ina fitowa daga toilet natarar aunty ta kwasomun kayan dazansa daga dakina. Amma ita bata dakin. murmushi nayi nadauki kayan nafara sawa, zuciyata cike da kaunar aunty, yanda take nunamun kulawa ko yar cikinta sehaka. Tunanin yaya sadiq ne yafadomun acikin raina, haka kawai naji gabana yayanke yafadi dana tunasan. nasan yanzu yanata nemana a waya besameniba, amma idan aunty tashigo zance ta aramun wayarta na kirasa. kayan kawai nasaka nafito falo domin naje nagaishe da mommy, aunty nagani tafito daga kitchen hannunta dauke da plate da cokali. "Sannu aunty" "yawwa maryam, yajikinnaki?" "Dasauki aunty" "Allah yakara sauki, kizo kici indomie dinnan kenadafawa sekisha magani, zamuyi wata tafiyane yanzu, nakira doctorn ma yacemun gashinan zuwa" da mamaki nake kallon aunty cikin sanyin murya nace mata. "Aunty tafiya kuma, ina zamu?" "nima dai bansaniba maryam haka dai yaya yacemun, sekiyi sauri kici abincin munayin sallah zamu tafi" cewar aunty tana ajiye mun plate din akasa. "To aunty bari naje nagaida mommy, yau antofawa yaya addu'ar kuwa?" kallona aunty tayi sannan tace, "kici abincinki kawai anti atika batanan, shikuma mustapha jikinsa yayi sauki sosai, alhamdulillah" ajiyar zuciya nasauke aboye tajin dadin aunty tace, jikin heartbeat dina yayi sauki. Zama nayi akan carpet na bude plate din da aunty takawomun nafara cusa indomien badon inajin dadintaba, saboda yanda zuciyata take bugawa inajin tamkar wani bakon al'amari nashirin faruwa dani ayau...........✍️ Meson complete Whatsapp 08166674823

Muna da group a Whatsapp masu son shiga 08166674823

*ABUNDA KASHUKA....*

_*(shizaka girba)*_

*4️⃣0️⃣*

*Bismillahirrahmanirrahim*

..........Abangaren su faruq kuwa, gabadaya part dinsu suka nufa zuciyoyinsu babu dadi, kowa dakinsa yashige ya kullo kofa domin samun kadaita. sadiq da nadama gami da kunya suka masa katutu yakasa zaune yakasa tsaye zarya kawai yakeyi a dakinsa abubuwa biyu ne suke damunsa a wannan lokacin. Na farko wata zazzafar kaunar maryam ce ta mamaye masa zuciya. na biyu kuma boka tsidau yatabbatar masa da cewa matukar aiki ya lalace to ciwon da mustapha yakeyi ze dawo kansa ne. a yau kam yayi nadamar kasancewar mommy mahaifiyarsa, ta cusa masa abunda baze taba amfanesaba arayuwarsa. Fiye da shekaru goma ta cusa masa kiyayyar mustapha me tsanani acikin ransa, ta nuna masa mustapha babban makiyinsune, alhalin bahaka abun yakeba. wani zazzafan huci ya fuzgar, hannunsa yakai ya ware hiramun dake kansa gami da cire safar hannunsa, dinkin da'aka masa yabayyana na ciwon da maryam taji masa. fadawa kan gado yayi sharab, zuciyarsa na masa kuna jiyakeyi tamkar ya kashe kansa dan bakin ciki, ga wata kewar maryam data cika masa zuciya. Da farko da yaudara yafara son maryam, amma zuwa yanzu son yarikide masa yakoma nagaske wanda yake barazanar tarwatsa masa zuciyarsa. kansa yafara bubbugawa akan gadon a fili yafara magana. "Mommy, why,..! why, dakika zabarmun wannan rayuwar, meyasa nabiye miki nakai kaina ga halaka,yanzu da wanne ido zankalli maryam wadda tabani dukkan yarda da amanarta, ta dauki a amatsayin bango na rayuwarta, koyaya zataji idan taji labarin ninake kokarin rabata da mutuncinta. Tabbas ubangiji baze barniba akan cutar da bayinsa wanda basujiba basu ganiba danayi. kansa yarike dayake kokarin tarwatsewa saboda damuwa, wannan ranar besan dame zekirataba arayuwarsa..........

naci indomie fiye da rabi, sannna na rufe plate din saboda aman dana faraji yana tasomun, ahankali na mike nanufi dakin aunty domin nace ta bani aron wayarta nakira yaya sadiq dina. Da sallama nashiga dakin, aunty dake hada kaya acikin wata yar karamar jaka ta amsamun sallamar batare data dago ta kalleniba. zama nayi akasan gado cikin sanyin murya nace, "aunty dan Allah kibani aron wayarki zankira yaya sadiq nasan yanzu yanata kirana besameniba" dagowa aunty tayi tazubawa maryam ido, cikin tausayinta domin ta dade da fuskantar soyayya sukeyi, gashi harta kasa hakuri tatambayeta Aron waya takirashi, batasan shine me kokarin bata mata rayuwaba, koda daddy befadaba dama aunty ta dukurcewa ranta bazata bar takara kwana acikin wannan gidan da'ake burin cutar da itaba. kasa nayi dakaina ganin aunty tana kallona, wata kunyartace ta lullubenu wata zuciyar tawace tacemun kodai aunty tasan muna soyayya da yaya sadiq dinne. "Maryam, nakirashi ai tundazu amma wayartasa bata shiga, akashe ake cewa" aunty tafadawa maryam haka, domin batason tasan komai tunyanzu tafison sekomai ya lafa tukunna. "Shikenan aunty" nabata amsa cikin sanyin jiki. domin bugun zuciyatane yakaro akannada...

Mustapha yadau tsahon mintuna 20 a toilet kafin yaja kafa yafito saboda matsanancin jirin dake kwasarsa amma bawai dan ruwan ya isheshiba. kan gadonsa yafada Cikin mawuyacin hali, jikinsa na wata irin kyarma, dakyar ya iya jan bargo ya lullube jikinsa saboda wani sanyi sayaji yana shigar jikinsa. tunanin abubunwa dasuka faru abayane suke dawo masa kwanyarsa, tabbas biri yayi kama da mutum, mommy tasha siyo masa kayan maye domin yadingasha, wai rayuwarce seda haka. Agaban mommy suhailat take hugged dinsa kota dane kan cinyarsa amma mommy bazata kwabetaba sema ta nuna jindadinta. Mommy bata bashi tarbiyyya tagariba kokadan tayi masa abubuwa dadama domin ya lalace amatsayin soyayyar datake masane haka, Allah ne kawai yakareshi dakuma tsaiwar dakan da daddy yayi wajen ganin rayuwarsa ta inganta. wasu hawayene masu matukar dumi suka digo masa, wanda dakyar yasamu suka zubo. har yanzu yana mamakin wai mominsa datafi kaunarsa fiye da komai da kowa a duniya ita ce take furta Kalmar tsana agaresa saboda abunda duniya. har yanzu yanajin guntun kaunar mommy acikin zuciyarsa, kobabu komai ta raineshi kuma ita yataso yake kallo amatsayin uwa. zurfaffen tunani yashiga sosai akan rayuwarsa wanda hakan yakara haddasamasa matsanancin ciwon kai dana zuciya, tun yana gane meyakeyi haryafice daga hayyacinsa,komai yadauke masa dif.......

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull