Kenza eBookz

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 28

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 28

Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 28: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 28. Daddy akokarinsa nason tafiyarsu takance da wuri, yadauki…

3,123 words

Daddy akokarinsa nason tafiyarsu takance da wuri, yadauki mota yafita dakansa domin yimusu cuku_cukun tafiyar, ga wayarsa dake Cikin aljihunsa sekiransa akeyi ga tarin damuwar dake addabar ransa. tukin kawai yakeyi amma hankalinsa baya jikinsa yanacan duniyar tunane_tunane. be'ankaraba sekawai jiyayi ya gwabzi wata mota adaidai dangi. Cikin tsananin firgici daddy yafara ambaton "subhanallah" a fili, dasauri yayi parking motar tasa yafito ko rufewa kofar beyiba. mutane harsun fara taruwa saboda motar ta jirkicene anata kokarin dago da ita. shima daddy karasawa yayi akafara kiciniyar daga motor dashi. direban dake tuka motar yafito babu wani rauni ajikinsa sedai juya dake dibansa sakamakon jirkicewar da motar tayi, dan motar ta barin dama ta jirkita. Anyi nasarar juyar da motar har'aka fito da matar da direban yake tukawa, sedai matar babu alamar numfashi atattare da ita. tashin hankali wanda ba'asamasa rana. "Ana wata ga wata" daddy yafurta hakan azuciyarsa. "Ya Allah kasa ba kisan kai nayiba" yakara furta haka lokacin da'aka dakko matar a hannu rai ahannun Allah,babu inda yake motsi ajikinta. hankalin direban idan yayi dubu yatashi. Se kiran "innalillahi'wa'inna'ilahirraji'un" yakeyi kamar yadda daukacin mutanen wajen keyi. Cikin sauri daddy yayi gaba zuwa wajen motarsa aka Sanya matar abayan motar. Kasancewar daddy ba boyayyen mutum bane, mutane se fadin. "Yallabai Allah yakiyaye gaba sukeyi" driver seat daddy yashiga direban motar kuma yashiga front seat daddy yaja motar yanufi asibitin aminu kano. wayarsa yazaro yakira bakanikensa yasanarmasa yazo ya dauki motar dayabugedin yatafi da ita, tare da kiran asibitin yasanar musu da zuwansu. Cikin mintuna kalilan suka karasa asibitin abakin emergency yayi parking motar yafito dasauri yabude bayan, ma'akaitan asibin suka kama matad suka sanyata akan abun tura marasa lafiya suka nufi ciki da ita dasaurinsu, suma su daddy rufa musu baya sukayi.........

Doctor yazo yaduba hannun maryam yasa mata maganin,yakuma bata wasu dazata dinga sha. har Aunty tagama hada yan abubuwan datasan zasu bukata atafiyarsu sukayi sallar azhar amma daddy shiru_shiru bedawoba bekuma kirataba. part din mustapha takoma domin tagano halin dayake ciki, tana zuwa tatarar dashi cikin mummunan yanayi. cikin kidima mommy takira daddy danta sanar masa. "Hello, yaya ina katsayane?" numfashi daddy yasauke yace, "saudart ina hanyata tatafiya na bugi wata motane, yanzu haka muna asibiti" "innalillahi'wa'inna'ilaihirraji'un, subhanallah Allah yasadai babu wanda yayi mummunan rauni" "to, su biyune dai acikin motar, da driver da wata mata, direban yar buguwa yayi, sunma samasa ruwa, matar cedai kwance haryanzu likitoci nakanta" "ya Allah, Allah katakaitamana" "ameen" "yanzu kuna wanne asibitinne" "Aminu kano" "OK, bari muzo nida su faruq, Allah yakiyaye gaba" bayan sunyi sallama mommy takira faruq tace yadakko mota yazo bakin part din mustapha. taboyewa daddy halin da mustapha yake cikine saboda kar abun yamasa yawa,wannan tashin hankali har ina, dama haka rayuwatake,watarana dole se Allah ya jarrabeka. koda faruq yazo yaga halin da mustapha yake ciki hankalinshi yatashi sosai shima, batare da bata lokaciba yakira su haidar suka kamashi sukasashi a mota suka nufi asibiti dashi. aunty ce, tafadawa asabe me aiki sunfita, idan maryam tatashi tasanar mata, dantunda tasha maganin da doctor yabata sekuma bacci yadauketa. Asibiti mafi kusa dasu suka kaishi wanda yakasance private ne, suna zuwa aka karbeshi likitoci suka rufa akansa,domin ceto rayuwarsa........

mommy cikin mintuna kalilan takarasa gidanta dake lamido, wanda babu kowa aciki se megadi. horn tahau dannawa ba kakkautawa megadi dake kwance adakinsa yana bacci yaji horn din tamkar a mafarki. ahankali yabude idonsa yajidai azahiri yakejin horn din, dasauri yatashi yasuri rigarsa yasaka yafito danyaga waye a wannan lokacin yakatse masa baccinsa. karamar kofar gidan yabude ya leka, ganin motar mommy ce yasashi komawa da sauri ya bude mata get din, zuciyarsa cike da mamakin ganinnata domin tunda yazo gadi gidan bata taba zuwa a irin wannan lokacin ba, tafi zuwa da yamma koda daddare. A fili ya furta "banda abuna,ita da gidanta mene nawa aciki." gudu_gudu, sauri_sauri, yakarasa inda mommy take bayan yarufe gida. "Hajiya sannu da zuwa dafatan kin iso lafiya" yafadi haka yana kokarin karbar jakar hannunta kamar yadda yasaba a kodayaushe idan tazo yakai mata har cikin falo. Amma yau ga mamakinsa seyaga tadaga masa hannu bata bashi jakarba, bakuma ta amsa masa sannun dayake mataba tayi wucewarta ciki. kallonta kawai yatsaya yanayi harta bacewa ganinsa, zuciyarsa cike da mamakin ta, dan duk da bata da sakin fuska amma yau yaga abun yafi na kullum, yana tunanindai akwai matsala tunda gashima ita kadai tazo, sabanin da datake zuwa da driver wani lokacin ma, harda danta. komawa dakinsa yayi domin cigaba da baccinsa.

Momy tana shiga falo ta ajiye jakarta gami da mayafinta akan kujera, zuciyarta sam babu dadi, zarya tafarayi afalon cike da tsananin damuwa, se'alokacin wani gumi yafara keto mata. tanunawa su daddy warkewar mustapha bedaga mata hankalibane dankarsuga gazawarta da wuri. Amma bakaramin dimuwa gami da tashin hankali tashigaba, musamman datasan boka yace, idan aiki ya lalace komai zekoma kan sadiq ne. Tarasa meyasa tun mustapha yana karami kome tamasa na sharri sedai taganshi akan yayanta, taso mustapha ya lalace yazama mebin mata kuma takadirin dan shaye_shaye amma kuma sebezamaba, seyayantane sukeyi. lokacin da mustapha suka fara soyayya da suhailat agabanta suhailat zata dane kan cinyarsa kotayi huging dinsa amma bata hanata, duk dan mustaphan yalalace amma kuma belalace dinba. "tabbas! yazama dole natafi Neman mafita ayau ba gobeba, yanzu_yanzu ma kuwa!" mommy ta fadi haka a fili,tana cizon yatsa. (Hmmm, momy kenan, aishi sharri dan aikene.) wayarta dake cikin jaka ta dakko ta lalubo number wata kawarta takirata. tayi sa'a wayar tashiga amma harta katse bata dagaba,kara kira tayi nanma bata dagaba. Tsaki mommy taja afili ta furta. "ko'ina binta tashiga tabar wayartata oho,Inata kiranta amma taki dagawa" kara kiranta tayi akaro na uku, harta kusa katsewa sekuma ta daga. "Hello kawata, uwargida agidan alh mai nas".......... "kinga dalla ni badogon zance nanemaba, ina kika shiga inata kiranki baki dagaba" mommy ta katseta da fadin haka. "ina falone ina hutawa wayar kuma na daki" "ohk, idan babu damuwa inason ganinki yanzu domin akwai wata matsala babba" "matsala kuma atika, tame?" binta tatambayeta cikin kidima. "Kedai kawai idan da hali kizo, maganar bazata yiyu a wayaba, amma bana gida zanturo miki address din inda nake sekizo kisameni." "Tom, shikenan ba matsala ganinan zuwa yanzunnan" "yawwa binta sekin karaso" mommy nagama fadar haka ta katse wayar, address din inda take ta turawa binta kawarta. jefar da wayar tayi akan kujera bayan text din yaje, zama tayi itama akan kujerar ta rafka uban tagumi da hannu biyu tana tunane_tunane.

Bayan 40 minutes binta ta karaso gidan da mommy take, bayan tafito daga motarta sungaisa da megadi take tambayarsa ina mommy, dantaga gidan part 2 ne. jagora megadi yamata har bakin part din da mommy take, godiya ta masa ta karasa bakin falon tayi knocking. Ajiyar zuciya mommy ta sauke jin ana knocking, dantasan bintace ta karaso. "A shigo" tafada atakaice domin kofar abude take. turowa binta tayi tashigo taname bin falon da kallo, kafin tace, "atika wannan gidanfa,gidan waye?" mikewa tsaye mommy tayi tace, "bashine abun damuwaba binta ahalin yanzu. Ina cikin matsala kikaraso muyi magana ina bukatar shawararki." binta batayi musuba ta karasa cikin falon tazauna akan kujera ta fuskanci mommy tace, "Atika inajinki wacce irin matsalace gareki, kinsa hankalina gabadaya ya tashi" shiru mommy tayi nakusan mintuna uku kafin tafara magana kamar haka."binta inason ganin bayan mustaphanah, da sulaiman mijina, inason ayau ba gobebe nashafe labarinsu a doron duniya, ke atakaicedai inason nakashesune.!" cikin tsananin mamaki binta take duban mommy baki bude, kafin tayi karfin halin fadin, "atika! Kinsan mekike fada kuwa, kokinfara haukane, danki da mijinki kikeson ganin bayansu,kikeson kashesu kuma akanme to?" "Akan kudi" mommy tabata amsa agadarance. "Kudi kuma atika, kudinme to?" gyara zama mommy tayi tace, "labarine me tsaho amma zantakaita miki shi nabaki" ........... Labari mommy tabawa binta tundaga ranar dasuka samu mustapha har kawo yau. baki hangame binta take kallon mommy, tama kasa magana saboda dinbun mamaki, gani takeyi tamkar mommy kirkirar labarin tayi kawai tabata, yaron datake matukar sonsa fiye da komai a duniya amma ita take fadin ta masa mugayen abubuwa irinka,gaskiya ta jinjinawa hali irinna mommy, domin duk shedanancinta bazata iya abunda mommy tayiba. Jikinta a sanyaye tace, "Atika!, dagaske kike wannan labarinnaki,nifa kwanyata ta kasa dauka,amma tayaya kika gudanar da duk wadannan ayyuka batare da sanin kowaba tsahon shekaru?" taune lips mommy tayi tace, "kinga alamar wasa akan fuskata dazan miki karya. dagaske nake mustapha badana bane nacikina, kuma ina gudanar da aikinane cikin sirri a wannan gidan nida sadiq, abunda yasa babu wanda ya'ankare tsawon lokacin dana dauka inayi, saboda sadiq nake aikawa gurin boka tsidau, ninayi shekaru banje gurinsaba sedai idan sadiq yaje ya hadamu a waya. ko zuwa gidannan damukeyi babu wanda yasani, danse yamma lis nake zuwa kuma ta get din baya muke fita. Abundai da kawai yarana da megidana suka sani inada wannan gidan kuma ina zuwa lokaci zuwa lokaci ina dubashi." wani dogon numfashi binta taja sannan tace, "yanzu ke Atika duk daular dakike ciki, gamida kudaden da kike juyawa wanda har karshen rayuwarki zasu isheki, amma shine kika aikata haka, gashi yanzu asirinki yatonu, batare da kincinma kudirinkiba. mene amfanin hakan, gaskiya Atika duk tsagerancina gamida son duniyata da shu'umancina amma nasara miki gami da jinjina miki" wani murmushi mommy tayi tace. "Lallai binta haryanzu bakigama sanin Atikaba, tokisani nawuce duk yanda kike tunani indai akan cikar burinane babu abunda bazanyiba arayuwarnan. Dakike maganar kuma duk dukiyar danake ciki, amma senayi hankorin wata. Namiki uzuri, bakisan tarin dukiyar da golds din mustapha sukayibane shiyasa zakice haka"...... "Amm"....."dakata binta" mommy ta katse binta ta hanyar daga mata hannu kamar yadda itama ta katseta. "Bana kirakibane muyita ja'inja kokuma jan maganaba, nakirakine kawai kibani shawara domin kaina gabadaya ya kulle, narasa mafita. gashi kuma boka yamana gargadin dazarar aiki ya lalace karmu koma gurinsa" Ajiyar zuciya binta tasauke tace, "yanzu yakikeso ayi?" mikewa mommy tayi tsaye tadanyi taku sannan ta tsaya tace, "sonake mustapha, menasara da wannan tsinanniyar yarinyar maryam su mutu ayau. Shiru binta tayi kafin yadago kai ta dubi mommy dake kallonta tace. "Kidawo kizauna sena fada miki yanda za'ayi" babu musu mommy tadawo tazauna suka fuskanci juna binta tafara bata shawara.....

suhailat bayan taci kukanta ta koshi bacci yadauketa adakin mommy batare data shirya masaba. se wajen 2 tafarka. tashi tayi dasauri tafito falo,tana mamakin baccin datayi. tsit taji falon babu alamar mutum acikin part din. Dakin aunty ta nufa tana kwala mata kira, amma taji shiru. handle din dakin ta murda tajishi a rufe, tayi knocking ma taji shiru. maryam dake ciki tana bacci batamasan metakeba. duddubawata tayi har kitchen batagantaba, har dakin maryam ta leka. "To ina aunty tatafi, ko itama tatafi tabartane?" tatambayi kanta. kasa ta sauko inda tatarar da daya daga cikin masu aikin gidan a falo. Tambayarta tayi ina aunty, tace mata sunfita ita da su faruq. mamakine yakama suhailat akan ina kuma suka tafi suka barta ita daya agida.sama takoma dasauri ta shiga dakinta tadakko wayarta, number mommy tayi dialing. mommy suna zaune ita da binta sunata sakawa da kwancewa har lokacin kiran suhailat yashigo wayarta. dakkowa tayi taduba ganin sunan Sweet daughter nayawo akan screen din wayar yasata dagawa dasauri. cikin kuka suhailat tace, "mommy, kintafi kinbarni suma gashi suma sunfita dukansu seni kadai agidan" mikewa tsaye mommy tayi tace, "what? daughter banganeba suwaye suka tafi?" "Daddy, da aunty da yaya, dasu yafaruq da wannan yarinyar" muryar mommy narawa tace, "ina suka tafi?" "Bansaniba mom, danbasu fadaminba, nima asabe ce takefadamun" yawun bakin mommy ne ya kafe kaf, murnarta ta koma ciki, dafe kanta tayi, dakyar ta iya kokarin cewa. "Kihada kayanki yanzu zansa adakkoki akawoki inda nake" "to mommy" jefar da wayar mommy tayi, batare data katse kiranba, kotaba suhailat amsaba. "Lafiya Atika mekefaruwa kuma?" binta tatambayi mommy cikin mamakin ganin yanda yanayinta yasauya lokaci daya, harta fara zufa. wani numfashi mommy taja mehade da huci tace, "wai su sulaimanne sukayi tafiya yanzu basa gidan, se suhailat kadai,kenan hakan nanufin zasubar garinne kokuma yaya?" "tafiya kuma, zuwa ina?" binta ta tambayi mommy. "Oho, inazansani inanan" mommy tafadi haka akufule tana share zufar data tsatstsafo mata a goshinta. shiru binta tayi ganin mommy a kidime take. ita kuwa mommy zarya tahauyi a falon tsahon wasu mintuna, kafin ta dauki wayarta dasauri. number sadiq ta lalubo takira, tayi sa'a kuwa tashiga sedai bedagaba harta katse. tamai missed call yakai 5,amma yakidagawa. dole ta hakura takira driver dinta, akan yadakko suhailat yakawota gidan da take.........✍️

MESON COMPLETE WHATSAPP 08166674823

*ABUNDA KASHUKA*

_*(shizaka girba)*_

*4️⃣1️⃣*

*Bismillahirrahmanirrahim*

.........Daddy ne zaune a office din wani doctor yana masa bayanin abunda kedamun matar dayaka buge. "Yallabai ka kwantar da hankalinka ba wata matsala bace babba, buguwa kawai tayi a kanta, kuma alhamdulillah munshawo kan matsalar,fatanmu kawai Allah yasa ta farka cikin hayyacinta. sekuma dogon suma datayi. yanzu zaka iya shiga kaganta, da yardar Allah zata farka zuwa nanda awanni biyu munmata allaurar baccine" wata doguwar ajiyar zuciya daddy yasauke bayan doctor yagama masa bayani. se'alokacin hankalinsa yafara kwanciya yawu ya hadiya dakyar yace. "Shikenan doctor nagode sosai" "babu komai, yallabai. fatanmu kawai Allah yabata lafiya yakuma kiyaye gaba" "ameen,ameen" daddy ya amsa. Paper doctor yamikawa daddy ta magungunan daza'asiyane. sallama daddy yamasa yafita bayan ya karbi paper. dakin da'aka kwantar da direban nan daddy yanufa, yayi sa'a kuwa ya farka har nurses sun cire masa karin ruwan da'aka masa. da sallama daddy yashiga dakin, amsa masa direban yayi yana kokarin mikewa zaune. taimaka masa daddy yayi yazauna yana jera masa sannu. shidai direban mamakin daddy kawai yakeyi yanda yake nuna damuwa da kulawa agaresu tamkar ba shahararren me kudiba,da wanine sedai yabiya kudi yace amsusu dukkan abunda yadace tunda yana da halin yin hakan, shikuma yakama gabansa. Kuma ga dukkan alamu shima yana saurine ze gudanar da wani uzurinnasa. daga ganinsa rayuwarsa bashida damuwa,ko girman kai irinna wasu masu kudin. lallai samun kamar alh, mai nasara se"..... "Sannu, yajikinnaka" daddy yakatse masa tunaninsa da tambayarsa. ajiyar zuciya yasauke yace "dasauki Alhaji" zama daddy yayi akan kujerar dake fuskantarsa yace, "Allah yakaro sauki, yasa kaffarane" "Ameen Alhaji" "yawwa, zuwa yanzu yakamata ace kakira gida kasanar dasu halin da'ake ciki" "nayi yunkurin yin hakan tun dazu, amma Inata kiran number maigidanta ita hajiyar bata shigaba" "Allah, sarki, tokuma babu wani dazaka kira seshi, kota yayantafa" dan jimmm, direban yayi kafin yace. "Ai bata da yaya ranka yadade, sedai yayan yayanta dasuke zaune gida daya, sukuma gaskiya bani da number dinsu" jinjina kai daddy yayi yace. "To ita ina wayarta semunemi number mukira, kaga ai baze yiyu ace haryanzu wani nata besaniba" "hakane, Alhaji, wayartata tana cikin Jakarta, kuma ina tunanin mun barota a cikin motar mu" daddy bekara cewa komaiba se wayarsa daya dakko daga aljihun gaban rigarsa yakira bakaniken daya tura yadauki motartasu, yace masa yaduba motar idan yaga jaka aciki yadakkota yabada akawo masa asibitin aminu kano yanzu. Amsa masa bakaniken yayi cikin girmamawa sannan yaduba, yana dubawa kuwa yaga jakar, a take yabada aka kawowa daddy. Number da matar tayi waya da ita last, ita daddy yakira. wata kawartace dazatayi bikin yarta, bikinma matar tataho, kuma wannan shine karonta na farko zuwa kano daga garin *jos*. kawartata ta rude sosai, dama tanata kiran wayarta taji kota karaso bata shiga, cikin hanzari suka kimtsa ita da wasu yayanta suka nufo asibitin. ansamu number maigidannata ta shiga shima ansanar masa. masallaci daddy yanufa domin yin sallah, bayan yagama kiraye_kirayen wayar zuciyarsa cike da mamakin abunda yatsaida su aunty karasowa asibitin haryanzu..........

Abangaren su aunty ma, ansamu anshawo kan ciwon mustapha, dama damuwace kawai ta masa yawa, wanda hakan yasa jininsa yahau sosai. dukansu sunsashi agaba sunyi tagumi jigum_jigum, su haidar harda kuka dasukaji daddy sunyi accident. wannan wacce irin jarrabawace daga wannan se wannan, to Allah yatsayar haka,shine addu'ar dasukayi kawai. Numfashi aunty ta sauke cikin karayar zuci, na wannan bakon al'amari daya samesu. wayartace tayi kara. Ahankali tasa hannu ta daukkota, Abban aliyane ke kiranta dagawa tayi dayin sallama cikin sanyin murya. "Wa'alaikumussalam, hajiya sauda yajikin mustaphan?" (Dayake takirasa tafada masa) "dasauki Abbansu, gashinanma yanata bacci" cikin tausayawa abbansu aliya yace, "Allah yakara sauki, Allah yayankewa yaronnan wannan wahala haka" "Ameen, abbansu, kuntahone?" "A'a, yanzudai zamu taho, dan auta bata jima da dawowa daga islamiyyaba" "shikenan, Abbansu sekun karaso" sukayi sallama aunty ta kashe wayar. number daddy takira, har 3 missed call tamasa bedagaba, time din yana sallah ne, seda ya idar yabiyo bayan kiran. bayan tadaga yace, "hello saudart" "na'am, yaya yamasu jikin" "dasauki Alhamdulillah, danshi direbanma ya warware matarcedai haryanzu tana kwance tana bacci" "Allah yakara sauki yakiyaye gaba" "Ameen, sauda. Najiku shiru kuma baku zoba haryanzu, gashi su ashema ba'a garinnan sukeba, daga jos sukataho biki, babu wanda yazo haryanzu danbanma jima dasanar musuba, sedai gidan dasukazo bikin sunce gasunan zuwa." shiru aunty tayi gabanta nadan faduwa, tana tsoron ta fada masa mustapha babu lafiya yakara shiga wani tashin hankalin. "Hello, sauda naji kinyi shiru, ina mustapha fa?" wata boyayyiyar ajiyar zuciya aunty ta sauke tace, "yaya mustapha, gashi kwance babu lafiya muna asibitima yanzu haka, shine dalilinma dayasa kajimu shiru" "innalillahi, meke damunsa kuma?" "damuwace kawai yaya, hartasa jininsa yahau, naki fada makane saboda kar hankalinka yatashi, ga wancan ga wannan" "ya salaammm, ya subhanallah" daddya yafadi haka cikin tsananin damuwa yana fesar da numfashi. "hakuri zamuyi yaya, haka Allah yakaddaro mana babu yanda zamuyi, amma insha Allahu, komai zedaidaita, banason katada hankalinka yaya, kacigaba da juriya da addu'a, da yardar Allah komai zezama tarihi kamar ba'ayiba" jinjina kai daddy yayi yace, "hakane sauda, yanzu kuna wanne asibitin?" Asibitin aunty tafada masa, yace gashinan zuwa. Daddy bebar asibitinba seda kawar matarnan tazo, yakuma siyo dukkan magungun da'aka bukata gami da duk wani dayasan zasu bukata, se wajen karfe biyar yabar asibitin....

Direban mommy yakai mata suhailat kamar yadda ta bukata, suhailat tana shiga falon gidan taga mommy zaune ta rafka uban tagumi. dagudu tatafi tafada jikinta ta rungumeta tana kuka. "Cikin takaicin dake nukurkusar mommy tace, "Meyafaru daughter?" "Mom, meyasa kikayi haka, gashi yanzu duk suntafi sunbar gidan, mom dan Allah kiyi hakuri kijanye kudirinki kibawa daddy hakuri kidawo gida, mucigaba da rayuwarmu medadi kamar da." janye suhailat mommy tayi daga jikinta tana fadin. "Yaro man kaza!". daga haka bata kara cewa komaiba ta mike tanufi daya daga cikin dakunan dake falon. suhailat kuwa kuka tacigaba tayi, domin ita damuwarta daya a yanzu maganar auranta da mustapha batasan ina maganar ta kwanaba, tana matukar kaunarsa bazataso ta rasashiba. wayarta dake cikin jaka ta dakko saboda kiran da'ake tamata tuntana mota. kamal ne yake kirannata, cillar da wayar tayi akan kujera danbatashi takeba a yanzu. Binta kuwa dama tunda taga mommy ahaka, tamata sallama tayi tafiyarta. Abun duniyafa yataro yayiwa mommy yawa, takasa zaune takasa tsaye, ita burinta a yanzu kawai tasan ina su daddy suke, idan tasan haka to komai zezo mata da sauki aganinta...........

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull