Kenza eBookz

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 29

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 29

Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 29: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 29. Maryam, tadade tana bacci sosai dantayi fiye da awa uku,…

3,305 words

Maryam, tadade tana bacci sosai dantayi fiye da awa uku, sebayan la'asar tatashi. Ahankali ta sakko daga kan gadon aunty ta nufi toilet, alwala ta dauro tadawo tatada sallah ganin har lokacin ta yana kokarin kurewa. bayan ta idar tazauna tana addu'a, Alhamdulillah taji saukin jikinta sosai, zugi da radadin da hannunta shima se kadan yanzu. tunani nashigayi akan abunda yafaru dani jiya, amma nakasa tunawa, gaba daya kaina ya kulle. kawar da tunanin hakan nayi nashiga wanda yazamarmun jiki wato tunanin mahaifina, koyana raye koya mace se Allah. A fili na furta "ya Allah kabayyamun mahaifina,kowani dan'uwansa kafin na mutu." nima naga dangina kamar kowa. hawayen daban shirya musubane naji sunabin kuncina, koyaushe zandena kukan rashin mahaifi da danginsa se Allah. mikewa nayi naninke dardumar danai sallah akai na ajiye. bakin kofa nanufa na bude nafita. Falon babu kowa bakamar yadda nazataba, kitchen nanufa nanma babu kowa, dakin mommy naje nayi knocking nanma shiru. gabanane naji yafadi kawai senaji ina tsoron zaman kadaicin, danna fuskanci babu kowa asaman. harna nufi dakina sekuma nafasa nasauka kasa. Ajiyar zuciya nasauke saboda ganin asabe me aiki. Cikin jindadi nace. "Aunty asabe, sannu da gida" "yawwa maryama kintashi" "eh" "yajikinnaki" "dasauki, inasu mommy ne da aunty naji gidan tsit" "wlh duk basanan maryam, dan hajiya babbama yaubansata a idonaba, se hajiya karamace tacemun idan kintashi nafada miki sun fita" jikina asanyaye nace, "to aunty asabe nagode, bari nakoma sama" ina tafe ina tunanin ina su aunty da mommy suka tafi, kodai jikin yaya mustapha ne yayi tsamari suka tafi gurin magani.?" bani dame bani amsa, hakan yasa nace. "Allah yasa alkhairi ne fitar tasu" kitchen na shiga nahada tea, nasha sannan nasha maganina da doctor yabani. zama nayi afalo cikin rashin sanin abunyi nahau karanta wasikar jaki........

Daddy ne zaune agaban gadon da mustapha yake kwance yakura masa ido cikin tausayawa, yaro mejuriya da dauriya akan dukkan abunda yasamesa amma wannan yakasa jure masa, se faman shan wahalar ciwo yakeyi. gaskiya atika ta cutar dashi, amma sakamakonta yanaga ubangiji shiyasan meze mata. Ahankali yabude lumsheshshun idanunsa yana bin saman dakin dayake da kallo. beyi yunkurin koda motsiba face silik din dakin daya kurawa ido kawai yana kallo, daddy yanacan duniyar tunani bemasan yatashiba. aunty dake zaune akan darduma tana lazimi kamar ance tadago takalleshi taga yafarka. mikewa tayi tana fadin, "yaya kaga yatashi" maganar aunty tadawo da daddy daga duniyar tunanin daya tafi. "Masha Allah" daddy yafadi haka cikin farin ciki yana kallon mustapha daya juyo yakura musu ido baya ko kiftawa. "Sannu, son yajikinnaka bari nakira doctor" cewar aunty tana kokarin juyawa tafita. da hannu yamata alama alamun karta fita tazo garesa. aunty bata musaba takarasa gareshi. kama hannunta yayi, cikin tsananin kaunarta dabayajin yanawa kowacce diya mace aduniya bayan mahaifiyarsa se ita. girgiza mata kai yahauyi kafin yayi karfin hali fara mata magana da muryarsa dabata fita sosai saboda ciwo da fadin. "Kada kiwahalar da kanki aunty wajen kiran doctor,domin nasan wannan ciwonnawa bana tashi bane inaji ajikina shine zezama ajalina" yakarashe zancen yana taune lips dinsa,saboda azaba da zugi da zuciyarsa kemasa. kwallace tatararwa aunty a idonta, kokarin maidata tayi tace. "haba Muhammad, kadena irin wannan zancen ba lokacin yinsu bane,insha Allahu zaka samu lafiya kawarke kakoma kamar da" kara damke hannun aunty yayi tare da runtse idanunsa, dago hannun aunty yayi yadora adaidai saitin zuciyarsa yafara magana a wahalce. "Aunty kinjifa yanda zuciyata take bugawa, inajin wani irin radadi acikinta dama dukkan jikina, aunty inaji tamkar ana zarar numfashi nane" bude idonsa yayi yadorashi akan na aunty wadda hawaye keta kwarara akan kuncinta yacigaba da magana. "Aunty nikam gwara mutuwa da wannan"....... hannu aunty tasa tatoshe masa bakinsa da sauri ta hau girgiza masa kai, Cikin kuka tafara magana. "Haba Muhammad, kaifa musulmine kazama me yarda da kaddara aduk yadda tazo maka. kada kazama me butulcewa Allah, duk abunda hakuri bebakaba rashinsama baze bakaba, kayi hakuri insha Allahu duk wannan abunda ze faruwa wataran seya zama tarihi, kaji tamkar ba'ayiba. Very soon zaka koma rayuwar farinciki da jindadi fiye da da." lumshe idonsa yayi yanajin ninkin kaunar aunty nakara ratsa zuciyarsa. ahankali yakai hannu yana share mata hawayen dake fuskarta batare daya bude idontasaba,dan har cikin ransa yakejin kukannata. murmushi aunty tayi Cikin tsananin kaunarsa ta rike hannunnasa ta sumbata. Ahankali tace, "bakaso kaganni ina kukane son?" daga mata kai yayi alamun eh. "To idan kanaso indena se kamun alkawarin zaka dena damuwa, zaka mikawa Allah dukkan lamuranka, kuma zaka dena tunane_tunane. domin shine yajanyo maka wannan ciwon dakakeyi." bude idonsa yayi yana murmushi yace, "nadena uwa tagari, kuma alkawari namiki insha Allah zandena tunanin komai, indai zakiji dadi" murmushi aunty tayi Cikin jindadi tace. "Nagode sosai, son,Allah yabaka lafiya." takarashe zancen dakai hannu tana shafa lallausar sumar kansa. Daddy dake tsaye yana kallonsu cike da bansha'awa da tausayawa, duk dauriyarsa amma seda kwalla tacika masa ido, amma bebarta tazuboba yamaidata. Yana mamakin yanda sauda take kaunar mustapha, fiye da yayan cikinta a yanda take nunawa. itama ayanxu tausayi take bashi, duk hankalinta ba'a kwanceba, tabaro yayanta da mijinta duk dan akan takula da mustapha, gaskiya ya jinjina kaunar datake masa. cike da kauna mustapha ke binta da kallo harta fice domin kiran doctor. sannu daddy yakarayiwa mustapha cike da tsananin kulawa. Aunty tare suka dawo da doctor ya duddubashi bayan yamasa sannu da addu'ar samun sauki. bayan fitar doctor bajimawa su faruq suka dawo dakin, alokacin mustapha yana zaune yajingina bayansa da filo, aunty tana bashi tea a baki. Sunyi matukar farincikin ganinsa ahaka, cike da dunbin farinciki suka karasa garesa suna jera masa sannu. dakai kawai yake amsa musu, yanamejin tarin kaunarsu acikin zuciyarsa. mustapha yatabbatarwa kansa duk duniya bashida kamar daddy da ahalinsa, yanajin koda yayi katarin ganin mahaifiyarsa ko wani nashi, baze iya barin su daddy ba, sedai sucigaba da kasancewa tare. yanda yaga kowa yana nuna jindadinsa da farincikinsa akan yanda sukaga yasamu lafiya, seyaji wani dadi da sanyi yana ratsa zuciyarsa, ahankali damuwar dake cunkushe acikin ruhinsa tafara gushewa, Cikin ransa amabaton sunan Allah kawai yakeyi.

Aunty ce, ta umarci faruq idan yayi sallah yaje yadakko maryam, yakawota asibitin tasan yanzu tamacan tanata zullumi dama ita ba cikakkiyar lafiyaba, gashi tabarta ita kadai a gida. ina zaune a falo bayan na idar da sallar magariba naji ana kokarin bude kofar falon. Ajiyar zuciya nasauke domin duk a tunanina aunty ce tadawo, amma senaga ya faruq. da sallama yashigo falon, amsa masa nayi Cikin girmamawa tare da gaisheshi. bayabo babu fallasa ya amsamun, yakara da fadin. "Ki shirya, aunty tace nazo nadaukeki nakaiki gurinta" aida sauri namike domin zaman kadaicin ya isheni, dama yanzu nake tunanin zuwa part din su baaba talatu idan su aunty basu dawoba. dadduma kawai nakai daki nakulle dakin sannan nafito muka tafi, bayan na kulle kofar falon gabadaya. Bamuyi wata tafiya menisaba naga munkaraso wani guri, nibanma gane ina bane seda muka fara tafiya na fahimci asibitine. gabanane yayanke yafadi dannasan baze wuce yaya mustaphane, bashida lafiyaba. yana tafe ina binshi abaya, zuciyata na luguden bugu har muka karasa bakin kofar dakin, inda bugun zuciyata yakaro fiye dana da. jikina asanyaye nashiga dakin da sallama, cike da fargabar halin dazan riskeshi aciki na rashin lafiya. Ina dago kaina karaf muka hada ido dashi bayan nashiga dakin, dan gadon dayake kai yana fuskantar kofar ne. wata mummunar faduwar gabace ta ziyarceni bugun zuciyata ya karo, tamkar wadda akayiwa dole nakasa dauke idona daga cikin nasa, duk da tsananin kwarjinin dayamun, dauriya kawai nakeyi. yanda maryam taji faduwar gaba dasuka hada ido da mustapha haka shima yaji, haka kawai kuma yaji yakasa dauke idonsa daga kanta. kallon maryam Aunty tayi, ta kalli mustapha, da sauri tajuyo takara kallon maryam Cikin tsananin mamakin abunda tagani, kara maida kallonta tayi akan mustapha, abunda tagani dai shita kara gani babu canji, bakamar yadda tazataba ko idontane kemata gizo............✍️

Meson complete Whatsapp 08166674823

* *ABUNDA KA SHUKA*

(shi zaka girba)

*BY* *zeey kumurya*

*4️⃣2️⃣*

*Bismillahirrahmanirrahim*

.........Sosai abunda aunty tagani ya matukar bata mamaki ba kadanba, kuma wani Ikon Allah bata taba luraba seyau kodan yau tataba ganinsu suna kallonne alokaci guda? kasa nayi da nawa idon saboda juriyar tawa ta kare, ahakanma nikadai nasan yanda nakejin zuciya na kallon kwayar idonsa danayi akaron farko arayuwata, jikina gabadaya jinsa nake a matukar sanyaye. "Maryam kikaraso mana" muryar aunty ta katsemun tunanin danake. Ajiyar zuciya nasauke cikin dauriya nakarasa ciki, daddy nafara gaisawar wanda yaketa murmushi a boye wanda shikadai yasan ma'anarsa. cikin fara'a da kulawa ya amsamun ya tambayeni Jikina nace masa da Sauki. jikin aunty na matsa nace, "aunty nah, ina wuni?" "Lafiya kalau, diyata ya Jikinnaki?" Aunty ta amsamun da murmushi dauke akan fuskarta. "Naji sauki aunty, dan yanzuma babu abunda nakeji na ciwo ajikina" "Masha Allah, haka mukeson ji, Allah yakaro sauki" "Ameen, yajikin yaya" "Alhamdulillah" aunty ta fada tana maida dubanta garesa. ya lumshe idonsa kawai yanajinsu. shiru dakin yy kowa da abunda yake tunani acikin zuciyarsa,inaso namasa ya jiki, amma kuma nakasa kwarjininsa dayakemun duk ya cikani. nayi tunanin ina zuwa zanga mommy da suhalat amma kuma sebangansuba, kamar na tambayi aunty sekuma na kyale tunda ba hurumina bane. Daddy ne yakatse shirunnamu da fadin, "saudart, bari naleka candin nakara dubasu." aunty tagane asibitin da mara lafiyarsa take yake nufi. "Tom, yaya kagaishesu kafin muzo" "zasuji insha Allah, yanzuma ai dasu Aliyu zamu koma, kekuma ko gobe da safene sekuje" "toh, sekun dawo" Maryam da mustapha dai basu gane inda maganarsu daddy da aunty ta dosaba, dan mustapha besan daddy sunyi accident ba, aunty tace kar afada masa seya kara samun sauki. faruq dake zauna yana danna waya yabi bayan daddy suka fita tare, kujerar da daddy ya tashi nan Maryam ta koma ta zauna. tunanin yaya Sadiq ne yafadomun arai, bansan nadamu dashi hakaba seyau dabanji duriyarsaba gaba daya, duk senaji kewarsa ta cikamun zuciya. tunanika kala_kala nahauyi akansa, nasan duk inda yake ba kalau yakeba, tunda har wuni guda benemeniba, amma bansaniba ko wani aikinne yadauke masa hankali. kasa daurewa nayi nadubi aunty nace, ''Aunty yau kuwa kunyi waya da yaya Sadiq?" cikin son basar da zancen aunty tace, "ehh, yacema yana gaisheki" ajiyar zuciya nasauke cikin jindadi tunda sunyi waya da aunty nasan yana lafiya kenan. "Ina amsawa" nafadi haka ina maida kallona kan tv dake dakin. har gurin mota faruq yaraka daddy inda su haidar suke jiransa sannan yakoma ciki. Wannan ciwon na mustapha babu wanda yasani dan aunty tace kar'asanar da kowa saboda kar sirrin boye yafito fili.......

Bayan tafiyar daddy bajimawa matar ta farfado, Alhamdulillah ta farko cikin hayyacinta sedai babu bakin magana se ido datakebin kowa dashi. "Sannu Aisha" cewar kawarta tana kara matsawa jikin gadon. ido kawai ta bita dashi dankokanta bazata iya motsawa, saboda wani dimmm dataji yamata. yamata wani irin nauyi kamar andora mata dutse. Duban daya daga cikin yayannata matar tayi tace. "Rasheedah, jeki kirawo doctor kice masa ta farka" "toh, umma" wadda aka kira da rasheedah ta amsa tare da fita daga dakin. cike da jimantawa kawartata take kallonta, kana taka Allah na tashi, lafiya lafiya fa sukayi waya tace mata sunshigo Kano, amma ba'afi minti talatinba segashi ta riski wannan mummunan labari. yanda Aisha taci burin zuwa Kano da bikinnan amma gashi zuwan bezo mata da dadiba,Allah karabamu da mummunar kaddara, Allah ma yatakaita batayi wani rauni meyawa...dawowar doctor da rasheedah yakatse mata tunaninta. gaisawa sukayi da doctor yamusu yame jiki, sannan yaduba matar. Tambayar matar yayi inane yake mata ciwo bayan yatambayeta jikinnata. Kanta ta nuna masa da hannunta sekuma kafadarta ta barin dama. mammatsa mata kafadar yayi, ita kuwa se runtse ido takeyi, sannu yake mata, dama yasan dole zataji ciwo agurin tunda tanan ta fadi, danma Allah yatakaita amma dazata iya samun karaya akafadar. gefen fuskartama duk ta kukkurje. Seda yamata duk abinda yadace sannan yafita. kawartatama sallama tamata tatafi akan zata dawo Anjima, danse kiranta akeyi a waya. babbar yarta rasheedah ta bari, sekuma direban matar. harsu daddy suka karaso yan'uwan matar basuzoba, dama se cikin dare daddy yayi tsammanin zuwansu dan hanyar bata da kyau. sun mata sannu, kuma sundan jima sebayan isha'i suka bar asibitin........

Wajen 8:30 su aliya sukazo asibitin, zuwansu kenan ko gida basu jeba. naji dadin ganin aliya sosai itama haka. basu wani jimaba, aunty tatasamu agaba muka koma gida, harda ita. daddy da faruq aka bari agurin mustapha, Maryam jitayi tamkar karsu tafi don bata gaji da kallon heartbeat dintaba. hankalin ahalin alhaji mainasara yafara dawowa jikinsu, tunda Jikin mustapha Alhamdulillah, yayi kyau, dasu Maryam ma suka tafi sunbarshi yana ta baccine.......

*BAYAN SATI DAYA*

jikin mustapha yayi kyau sosai yanda akeso, jininnasa yadaidaita. Yacire komai na damuwa daga cikin ransa, dan kullum daddy da aunty cikin yimasa nasiha sukeyi. Maryam ma taji sauki sosai, yankewar datayi ahannu ya warke dama bawani yanka sosai mudubin yamataba. Zuwa wannan lokacin Maryam tagane, gidan babu lafiya, tunda gashi sati guda cur batasaka yaya Sadiq da mommy da suhalat a idontaba. kuma batakara tambayar aunty komai game dasuba, tunda ta lura bataso tasani. Ammafa abun yana matukar daure mata kai, ace kamar mustapha babu lafiya, amma mommy tatafi tabarshi, tunda ita haryau batasan meyake faruwaba. Aunty tanaso ta tambayi Maryam taji tayaya wannan tukunyar sirihin da mommy tayiwa mustapha asiri tazo dakinta amma basu samu sun kebeba, saboda zirga_zirgar asibiti, gana mustapha gana matar da daddy yabuge. Mommy tasamu information din su daddy suna gari, harma da accident da ciwon mustapha, duk taji labari. sungama shirinsu da kawarta binta zata rakata gurin wani hamshakin boka a garin Niger acan wani kauye. Nanda kwana 3 masu zuwa zasuyi tafiyar, danma binta ta tsaya yin wani uzurinta datuni suntafi. Suhalat kam,gabadaya kwanakinnan tayisune cikin tsananin damuwa na rashin kasancewa da mustapha dakuma rashin sanin matsayinta agurinsa,taso zuwa gida amma mommy tahanata. Abangaren Sadiq kuwa gabadaya ya boye kansa daga idon mutane, kodayaushe yana dakinsa a kulle, yarame yayi baki, ga kewar Maryam data addabeshi, mommy kullum seta kirashi a waya, amma baya picking. kullum cikin zullumi da tsammanin kamuwa da ciwo yake kamar yadda boka yafada. ko abinci baya iyaci, seyaji tamkar ze mutu yake iya jefa wani abu acikinsa. daddy kam yana sane, amma yayi banza da lamarinsa. Aunty cema takewa daddy zancensa akan yakamata su jawoshi ajiki tunda yayi nadama, amma daddy yayi biris yace tabarshi nadamama aitana gaba bega komaiba har yanzu,tunda shi yasiya da kudinsa......

Yau zamuje dubo matar da daddy yabuge nida aliya da aunty, dan tun washegarin ranar bamu kara komawaba, ranar damukajema bacci takeyi. misalin karfe hudu na yamma muka fito cikin shirunmu, bansan daliliba bankuma san meyasaba gabana yaketa faduwa tunda akayi zancen zuwanmu dubiyar, yanzumma da muka fito hakance ta kasance. muna cikin tafiya aliya tadubi aunty tace, "aunty pls kibani key nayi driving dinnan" harararta aunty tayi tace. "Aizaki iya zuwa ki kwata, uwar rawar kai kawai" duk da yanayin danakejin kaina seda na murmusa, aliya kuwa tsit tayi bata kara maganaba,se baki data turo gaba. Aunty da aliya suna matukar burgeni, suna kuma bani nishadi, har inji dama nice da mahaifiyata. "Allah kajikan mahaifiyata da innata, dama dukkan musulmi baki daya. Ameen" nafadi haka araina Aunty ce tayi driving dinmu har asibitin.........✍️ Babu dadi novel din shiyya sa baku Comments koh Meson complete Whatsapp 08166674823

ABUNDA KA SHUKA* (shi zaka girba)

*4️⃣3️⃣*

*Bismillahirrahmanirrahim*

..........Da bismillah na fito daga motar saboda gani nake tamkar wani abu ne zesameni saboda yanda nakejin zuciyata. Aunty nagaba aliya nabinta abaya seni kuma ta karshe har muka karasa dakin da matar take. matar tana zaune akan gadonta, mahaifiyarta da kanwarta sune ke kwana tare da ita, suna zaune suma akan wani gado dake dakin, se megidanta shima dayazo yana zaune akan wata kujera dake fuskantar matar. da sallama aunty ta yaye labulen dakin ta shiga. a tare suka amsa mata gaba-dayansu harda marar lafiya. dasauri kanwar matar ta mike tanawa aunty sannu da zuwa tare da nuna mata gurin zama. Kafin aunty tagai ga zama muma munshigo dakin, bakunanmu dauke da sallama. kaina na kasa na shiga dakin, gefen aunty muka karasa muka zauna. Duban mahaifiyar matar wadda ta manyata sosai aunty tayi tace, "ina wuni baaba" "lafiya kalau, yarnan ya hidima damu?" Murmushi aunty tayi tace, "haba baaba aiba wata hidima, Yamejikin?" "Jiki da sauki, Alhamdulillah" "Masha Allah, Allah yakara sauki" kanwar matar ce tagaida aunty, muma muka gaishesu duka mukayiwa mejiki sannu. har lokacin kaina na kasa. Muryar dattijuwar naji tana fadin, "ai likitanma yace insha Allahu, gobe ko jibi za'a iya sallamarta, tunda jikinnata ya warware. Tun shekaran jiyama take cewa a sallameta ita ta koma gida, likitanne yace ta dad'a hakuri zuwa gobe." "Allah Sarki, ai zamanne guri daya babu dadi, duk se mutum yaji yatakura" cewar aunty. "Hakane kuma da wannan dan wannan, to ita kaddarace bawa be'isa ya kauce mataba, yanda Aisha taci burin zuwa bikinnan tanata murna zatazo Kano taga ya Kano take, ashe rabon wahala ne ke kiranta" "To Allah ya takaita yakiye gaba, Allah yasa kaffarane" wayar kanwar matar ce tayi kara alamun shigowar kira. kafin wani a dakin yakara magana. dakkowa tayi taduba tace, "Mama kinga, aunty Maryam ce take kira, kuma naga da number dinta ta naija ce, ko sun saukane?" "watakil Asiya daga kiji dai" wayar harta katse se Asiyan ce tabi bayan kiran. dadokinta ta amsa sallama kafin tace, "Aunty Maryam, saukar yaushe?" daga daya bangaren matar tace, "saukar yanzunnan Asiya, ko gida bamu karasaba muna hanya nadora sim dina nace bari nasanar muku ya jikin A'ishan?" "Dasauki bari na bata wayar" ta karashe zancen tana mikawa mara lafiyar wayar. basu wani jima suna wayarba ta mikawa mahaifiyartasu, ita sundan jima suna magana sannan ta mikawa mijin matar shima sukayi magana. daga gani wadda sukeyin wayar da ita suna ji da ita, yanda kowannensu yake farinciki da hakan, su Aunty sungane hakane ta fuskokinsu data bayyana tsantsar farincikin da suke ciki. mundan jima sannan muka musu sallama muka tafi. Kafin mutafi seda Aunty taje office din doctor suka kara tattaunawa akan ciwon matar sannan muka nufo gida. hamdala nayi ga Ubangiji da muka dawo gida lafiya babu abunda yafaro, dan yanda zuciyata taitamun rawa nayi tunanin wani abunne ze faru dani. Adaren yau aka sallamo yaya Mustapha daga asibiti, itama matar da daddy yaje da daddare likita yatabbatar masa gobe insha Allahu zasu sallameta...

Tunanin yaya Sadiq ya yawaita acikin zuciyata a daren yau, jikina duk ya sanyaya komai cikin rashin kuzari nayisa, har Aunty take tambayata koda matsalane nace mata babu komai. Bayan mungama komai munzo kwanciya nakasa daurewa nadubi aliya nace. "Aliya niko dan Allah Intambayeki mana" inajinki matar yayana?" harararta nayi nace, "banson iskanci se'inma fasa tambayartaki" "yihakuri tawan ta abubakari kwandon sukari" ta fadi haka tana dariya. numfashi nasauke nace, "kamar kuwa kinsan akanshi zantambayeki, aliya yau kimanin fiye da sati guda kenan bansashi a idonaba, nasan dai yacemun zeyi tafiya amma baze jimaba zedawo, gashi wayata batanan bare nakirashi naji ko lafiya, nikuma ina kunyar na tambayi aunty" "hmm,wlh bake kadaiba nima nayi mamaki dabanga yaya Sadiq ba har tsawon sati guda,shida su mommyba. Dana tambayi aunty nace mata suna ina, setacemun bata sani ba. amma nifa nafi kyautata zaton bakalauba,akwai abunda ke faruwa agidannan" shiru nayi, domin nima nadade ina tunanin da akwai wani abu dake faruwa a gidan, banda haka ace duk ciwon da Mustapha yayi babu mommy ba yaya Sadiq ba suhalat, kuma ko zancensu banji Aunty tanayiba ko waya banga sunayiba gas... "Kinyi shiru Maryam" aliya ta katsemun tunanin danakeyi. Ajiyar zuciya nasauke nadago nadubeta nace, "narasa abun cewane Aliya, amma inason sanin halin dayake ciki, zuciyata cike take da kewarsa, dan Allah kitambayarmun Aunty halin dayake ciki" "shikenan kawata karki damu, kikwanta kiyi baccinki, zan tambayarmiki ita insha Allahu, dasafe" kwanciya nayi ina fadin, "nagode" atakaice, dan yanda nakejina doguwar maganama bazan iya taba. inajin Aliya na tsokanata wai soyayya dadi, nidai namata banza, harta gaji ta kwanta itama.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull