Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 30
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 30: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 30. Abangaren Sadik ma, yau tunanin Maryam ya yawaita aransa…
2,857 words
Abangaren Sadik ma, yau tunanin Maryam ya yawaita aransa fiye da kullum, kewarta ta masa katutu a zuciya, jiyakeyi tamkar zerasata ne. Idanuwansa ita kadai suke da muradin gani. kaunar Maryam na azabtar da dukkan jiki da zuciyarsa. betaba tunanin abun zejuye masa hakaba, daga soyayyar wasa da yaudara ta juye zuwa ta gaske, soyayyar Maryam tamasa bazata tamasa mugun kamun dake barazanar tarwatsa kwakwalwarsa. yazama dole gobe yafita danya ganta koyaji sauƙin abunda yake ji acikin zuciyarsa........
washegari Mustapha yatashi garau tamkar bashine yayi wannan doguwar jinyarba,dama haka Allah ke ikonsa. babu wani guri ajikinsa dayake masa ciwo. Yariga ya fawwalawa Allah al'amarinsa kuma ya amshi kaddarar datazo masa cikin rayuwarsa da hannu bibbiyu, addu'a kawai yake yi Allah yabashi juriya akan abinda ya jarrabesa dashi. babban abunda yafi komai dugunzuma hankalinsa idan yatuna shifa yanzu besan asalinsaba, besan wani jininsa. wannan abu idanyatunashi seyaji yatsani duniyarma gabadayanta. gashi yau tunda yatashi yakejin wani iri ajikinsa, haka dai yadaure yayi wanka yashirya cikin wani yadi mekyau da tsada milk colour. part din daddy yanufa jikinsa a matukar sanyaye tamkar anmasa duka. daddy nashirin fita shikuma yana shigowa, a falo sukayi kicibus. cike da tsananin farinciki daddy yake dubanshi wanda har yakasa boyuwa a fuskarsa, saboda ganin Mustapha fess dashi yana takawa da kafafunshi. fuskarsa ce, kawai tayi fayau da ita sekuma haske daya kara. "Good morning Dad" mustapha yafadi haka, cikin danne damuwar dake nukurkusar ransa. "Morning too, son. Dafatan katashi lafiya" "lafiya kalau daddy" yabashi amsa bayan ya zauna a daya daga cikin hadaddun Royal chair din dake falan. "Masha Allah, son daga gani babu tambayata jiki yayi kyau, dama yanzu nake shirin zuwa part dinnaka nadubaka, kafin na wuce asibiti, doctor yakirani tundazu zebasu sallama." "Alright, sekadawo" daddy kamar yace masa su tafi tare, sekuma dai kawai yafasa yasa kansa ya tafi. Lumshe idanunsa yayi bayan daddy yafice, mommy ce tafado masa a rai. haryau yakasa mantawa da ita, acikin ransa. Mamakintama yaki barinshi ace duk tarin kaunar data nuna masa duk ba gaskiyabane, ita kuwa mommy wacce irin mutum ce...... ahaka Aunty da daddy yaturota takawo masa abinci tazo ta samesa yanata tunane_tunane. nasiha taita masa cikin hikima kamar kodayaushe, dakanta ta bashi abincin abaki, duk dan yadena damuwa. danta hango damuwa karara acikin idanunsa. shima boye duk wata damuwarsa yayi yazage yayi break fast din, sosai yaci abincin duk dan Aunty taji dadi. Aikuwa Aunty taji dadin sosai, tata jero masa addu'oi.....
Daddy yaje asibiti yatarar harsun gama shirinsu, ciwon matar begama warkewaba bandejin kawai aka cire mata,dandai ta matsane kawai aka sallamesu. kanwartata tun sassafe suka wuce ita da driver da mamanta. megidantane kawai yazauna su tafi tare. Da niyyarsu daga asibiti su wuce Jos,amma daddy yace dole sesun biya ta gidansa. wajen 12 na rana suka karaso gidan alhaji menasara. Part din mommy daddy yakaisu, sun samu tarba sosai a gurin su Aunty. Daddy ne yacewa Aunty su shirya tare zasu tafi Jos din, suraka matar. Aikuwa Maryam da aliya se murna za'a tafi dasu. dan Aunty tace bazata tafi tabarsuba kafarta ƙafarsu. Mustapha yana kwance a falon daddy, daddy yakirasa a waya yace yazo part din mommy yagaisa dasu matar kafin su wuce, tunda basu taba haduwaba. Amsa masa yayi cikin ladabi sannan ya mike yafito yanufi part din mommy.........✍️
*kuyi manage da wannan pls*
Meson complete Whatsapp 08166674823
ABUNDA KA SHUKA
(Shi zaka girba)
*Zeey kumurya*
*4️⃣4️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
...........Cikin takunsa me cike da nutsuwa da kasaita gami da daukar hankali ya shigo falon mommy bakinsa dauke da sallama, daddadan kamshinsa mesanya nutsuwa ya mamaye falon gaba-daya. wata ajiyar zuciya daban shiryamataba nasauke, tare da maida kallona bakin kofa dasauri ina satar kallonsa. gaba-daya mutanen dake falon suka amsa masa sallamartasa a lokaci guda. akan carpet ya zauna ya fuskanci matar da megidanta ya gaishesu. matar datunda Mustapha yashigo ta kura masa ido tana kallonsa. numfashi ta sauke ta amsa masa gaisuwar batare data dauke idonta daga kallonsaba. shikuwa Mustapha kansa yana kasa bemasan tanayiba. Daddy yace, "wannan shine babban dana, sunanshi Mustapha, shine kuma mara lafiyar danace muku" mijin matarne ya amshe zancen da fadin "Allah Sarki, sannu kaji dan samari ya jikinnaka" "dasauki" ya amsa atakaice, saboda yanayin dayakejinsa yafara yawaita. "Allah yakara sauki" matar tafada still dai idanta nakan Mustapha bata dena kallonsaba saboda ita kadai tasan metagani a tattare da Mustapha'n. Aliyace ta gaisheshi cikin girmamawa, nima cikin dauriyar abunda nakeji agame dashi nagaisheshi. Daddy ne yadubemu yace, "Maryama kuje kukarasa shiryawa yanzu zamu wucefa munayin sallah,kuma a yau zamu dawo insha Allah" "to daddy" muka amsamasa cikin ladabi, tare da mikewa muka nufi dakin Aunty. duban daddy matar tayi tace, "Alhaji hardasu a yan rakiyar ne?" murmushi daddy yayi yace. "Ehhh, mamansu tace bazata tafi ta barsu sukadaiba" mijin matarne ya amshe zancen dacewa. "Amma Alhaji dasunyi zamansu har ita Hajiyan, aganina wannan ai wahalar daku zamuyi, bayan dawainiyar dakukasha damu yanzukuma harda rakiya." dubansa daddy yayi cikin tsanaki yace, "haba, wannan ba wahalar dakai bane, muda mukeso akulla zumunta, wadda zata dore har'aba. Aiko bakomai maje muga muhallinku" "Amma dai da wannan dannaka zamu tafi ko?" matar ta fadi haka tana kallon Mustapha. shima daddy kallonsa yayi yace, "A'a bandashi" "to nidai gaskiya inason yarakamu sa....." "Saboda kinga kyakkyawan saurayi ko?" mijinnata ya katse ta dafadar haka. murmusawa tayi tace. "Ehhh, najidin" "uhmm, kodai kinaso kihadashi da mummunar yarki *umaimah* ne?" dariya suka saka har daddy, amma banda Mustapha dabemasan mesukeba, yatafi can wata duniyar daban. "Nidai kawai inaso yakaramu babu ruwanka dameyasa" matar ta fadi haka tana dariya. daddy batare da tunanin komaiba yace, "to shikenan tunda kince haka, semu tafi dashi din, da dakaninsa zamu tafi, amma tunda kince haka semu tafi dashidin ba wani abu" "yawwa Alhaji godiya nake".....
Bayan anyi sallar azahar kamar yadda daddy yafada muka fito gabadayanmu domin tafiya. Ni, Aunty, Aliya, daddy sekuma matar da mijinta. bamusan da yaya Mustapha za'a tafiba seda mugaka yafito cikin shirinsa, yacanza kaya banadazu bane. yanzu wata dakakkiyar shaddace ajikinsa kalar light blue, yayi matukar kyau,amma fuskarnan tasa a tsuke take daga gani ba'ason ransa za'ayi wannan tafiyar dashi ba. Matar da daddy yabuge ita bada wata manufa tace atafi da Mustapha ba, sedan wata yar yayanta dasuke gida ɗaya ta ganshi. yarinyar sunanta umaimah, budurwace amma zatayi shekara 27. Ita umaimah ta kasance tana bala'in son kyakkyawan namiji gentle duk wanda yazo yace yana sonta setace ita bemataba, haryanzu bataga kamar namijin datakeso ta auraba, kullum cikin siffanta yanda takeso mijinta yakasance take. A lokacin da matarnan tayi arba da Mustapha, setaga babu abunda yayi saura daga yanda umaimah take siffanta yanda takeso mijinta yakasance a tattare da Mustapha. shine abun yamatukar bawa matar mamaki, dansu gani sukeyi kamar baza'a iya samuba gashi kuma kamar yadda take so dan hamshakin mekudi, harta matsu sukoma gida taga yanda umaimah zatayi idan taga Mustapha'n.
Mota muka shiga nida Aunty da Aliya da matar, yaya faruq ne zeyi driving dinmu. suma su daddy wata sukahau sukuma driver ne zeyi driving dinsu, nayi zaton a mota zamu Jos din, amma senaga muntsaya a wani guri,gurin katon filine. Fitowa daddy yace muyi. babu bata lokaci muka fita dukanmu mukabi bayan daddy zuwa cikin gurin. ashe airport ne mukazo, seda muka dan jira daddy yayi magana da wasu mutane sannan muka kara yin gaba. wajen wani abu muka tsaya, mekamar jirgin sojoji *(JET)* (kasancewar garin Jos basuda filin saukar jirage, shi yasa daddy yayanke shawarar su tafi a jet din) Gani nayi kowa a cikinmu yana shiga cikin shi babu fargabar komai, nikam senaji wani iri tunda bantaba hawaba, banma taba tunanin zanganni a airport ba balle harta kaini ga shiga jirgi. senaji kamar mafarki nake, wai yau nice zanhau jirgi har yayi shawagi dani a sama. danne duk wani kauyancina da fargabata nayi, nayi bismillah nima na hau. Bayan anyi duk abunda yakmata muka lula sama, banda ya faruq da driver su gida suka koma. Ajiyar zuciya nasauke nadubi aliya dake kusa dani kasa_kasa nace mata. "Ke kinji yanda nakejina kuwa gaba daya atsorace nake" dariya aliya tayi ahankali yanda babu mejinta seni tace, "aina lura dake tun ashigowa tamkar mekoyon tafiya" "kedai bari abunda baka saba" "kenima wannan ne hawana na uku, dama indai zakuyi tafiya da daddy, indai irin state ne haka ba wata kasarba a Jet yake zuwa" "auww, dama wannan ne jet din a wani American firlm nataba ganinsa" "ehhh, shine na dady ne yanama da wani bayan wannan" kawar da zancen jet dinnayi da fadin "kinwa Aunty zancen yaya Sadiq kuwa?" "Ehhh, na mata tacemun zamuyi maganar idan mundawo daga tafiyar yan" "Tom shikenan,Allah yadawo damu lafiya" "Ameen".....
Munsauka a garin Jos lafiya a unguwar *Rikkos.* Garin lumlumlum dashi babu zafi, bakamar kanoba da muke da tsananin rana, garin ya burgeni gasu da duwatsu. Hamdala matarnan tayi ganin sun sauka a gida lafiya, ita kam zuwa Kano bemata dadiba amma bawa baya kaucewa kaddararsa koda a gidama take idan Allah yayi setayi accident din. Gidannasu babbane me kyau daga gani suma masu haline. Amma irin family house dinnanne. wani part dake hannun dama muka nufa,muka yada zango a falo. wata mata ce tatarbemu wadda bazata haura shekara 32 ba. da fara'arta se sannu da zuwa take mana. dukkanmu muna zaune a falon harda yaya Mustapha da daddy. duban matashiyar matar A'isha tayi tace. "Zuhura ina Aunty Maryam, dasu mama?" "Mama tana part dinta, ammi kuma tana ciki, may be bataji zuwanku bane" mikewa A'isha tayi ta shiga wani daki dake falon bayan tace mana zuwa, itama matar damuka tarar mikewa tayi ta shige kitchen. Shiru falon yayi, nikam tunda muka shigo gidannan gabana yake faduwa bana wasaba, abun harya bani tsoro sosai, akwanakinnan inajin haka sosai atattare dani amma na yanzu yafi na kullum, addu'a kawai nashiga karantawa a cikin zuciyata. satar kallon yaya Mustapha nayi naganshi yajingina bayanshi da jikin kujera idanunsa a lumshe tamkar kowanne mafiya yawan lokuta danake ganinsa. maida kallona nayi ga Aliya datake danne danne waya. maman matar damuka kadece ta shigo falon da sallama ita da kanwar matar fuskokinsu dauke da fara'a. "Sannunku da zuwa" tsohuwar ta fada bayan ta zauna. daddy ne ya amsa mata da fadin. "Yawwa sannu baaba, dafatan kunzo gida lafiya, ya hanya?" "Lafiya kalau Alhaji, sannunkufa angode, Allah yasaka da alkhairi" "Ameen, ameen" gaisheta mukayi gabadayanmu amma banda yaya Mustapha dako motsawa beyiba, itama kanwar matar gaisawa mukayi ta nufi kitchen gurin zuhura. "Mustapha!" Daddy yakira sunansa ganin yanayin dayake ciki. Mustapha dayakejinshi a wata duniyar daban, saboda wani matsananci bugu da zuciyarsa take masa,kansama jinsa yakeyi tamkar ze rabe biyu. idanuwansa da suka masa nauyi yabude a hankali ya kalli daddy. amma bece komaiba. kallo daya daddy yamasa yasan da akwai matsala saboda yanayinsa gaba-daya ya sauya.ya hango tsantsar damuwa a idanun dannasa. cikin tausayawa daddy yace masa. "Ga mahaifiyarsunan kugaisa" maida dubansa yayi ga matar, zuciyarsa na kara tsananta bugu, cikin matukar dauriya yace mata. "Ina wuni?" asanyaye. matar wadda ta zuba masa ido kawai tana kallonsa tace. "Lafiya kalau, ya jikinnaka" (dayake duk sunsan bashi da lafiya) dauriyarsa ta kare hakan yasa ko harafi daya baze iya kara furtawa dan yanayin dayakejin kansa ya yawaita, dakai kawai yabata amsa. gaba-daya falon yabasu tausayi musamman Aunty da daddy dasukan damuwarsa, kawar dakai Aunty tayi daga kallonsa cike da tsananin tausayinsa. Maryam kuwa batasan daliliba kawai taji kwalla tacika mata ido. maman azatonta jikinnasane dan haka tace, "Allah yakaro sauki, aidama yayi zamansa tunda bashi da lafiya, tafiyarma seta karawa mutum ciw..." Fitowar matar da daddy ya kade ita ta katsewa mama maganar datakeyi. wata kyakkyawar macece tamkar balarabiya biye abayanta, tana sanye da abaya me matukar kyau, wadda taji adon dutsuna, ta yane kanta da mayafin abayar. tana sako kafarta cikin falon wayarta dake hannunta tayi kara alamun kira, dakatawa tayi ta daga wayar cikin wani irin bakon yanayi mewuyar fassaruwa daya risketa a lokaci daya. kafin tagama wayar su zuhura sun fito daga kitchen hannayensu dauke da farantai dake dauke da ruwa da lemuka,suka dire agabanmu. da sallama kyakkyawar matar ta karaso falon, gabadayanmu muka daga kai muka kalleta saboda dadin muryarta duk da ta manyanta. siririn farin glass din dake idonta ta zare ta rike a hannunta, kyawawan idanunta farare tass suka bayyana wanda ta saukesu akan fuskar Maryam.............✍️ _*masu complain na rage yawan typing, kuma kun rage yawan comment ne, idan kun gyara nima zan gyara*_
Meson complete Whatsapp 08166674823
ABUNDA KA SHUKA
(Shi zaka girba)
By* *zeey kumurya*
*4️⃣5️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
...........A tare zuciyoyinsu suka buga da karfin gaske, kallon cikin ido matar take yiwa Maryam. Ita kuwa Maryam dasauri tayi kasa da idonta bugun zuciyarta na tsananta. a ranta tana fadin, "tsarki ya tabbata ga Ubangijin da yayi wannan kyakkyawar halitta." ita kuwa matar kara kafe Maryam tayi da ido, zuciyarta nacigaba da bugawa saboda mamakin abunda tagani a tare da Maryam. mama dabata lura da halin da Maryam da matar suke cikiba ta fadada fara'a tana duban matar tace. "Wannan matar yayansu ce daya rasu, shine babban dana, lokacin da akayi hatsarin tana Saudiya ne ta kaiwa mahaifiyarta da kaninta ziyara se jiya ta dawo" kallon matar daddy yayi a karo na biyu zuciyarsa na kissima masa wani abu akanta, muryarta ta masa dadi bakadanba, yayi mamaki daya kalli fuskarta yaga ta manyanta dan muryartata tamkar ta wata matashiyar saboda dadinta da sanyinta. ga muryartata ta sanya masa wani abu a cikin zuciyarsa wanda yakasa gane ko menene, hakan yasa yaji yanakuma son yakarajin muryartata. numfashi matar ta sauke, tana kokarin daidaita nutsuwarta. maida kallonta tayi ga Aunty datake gaisheta. Amsa mata tayi cikin sakin fuska. tana kokarin zama akan hannun kujerar da mama take, tamkar ance ta dago kanta idanunta yasauka akan Mustapha,daya kafeta da ido yana kallonta. wata mahaukaciyar bugawa zuciyarta tayi cikin tsananin razani tafasa zaman datake kokarinyi, ilahirin jikinta ne yadauki rawa tamkar mazari, hannunta na rawa take nuna Mustapha tanason tayi magana amma takasa, wani dimmm taji kanta yayi juwace ta kwasheta kawai segani akayi tayi kasa zata fadi. Dasauri matar da daddy yakade da mama sukayi kanta saboda sunfi kusa da ita, gaba-daya mutanen falon sukayi kanta, banda Mustapha dayakasa koda motsi, da Maryam. "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un" abun bakunansu kawai suke iya furtawa kenan. "Zuhura kikira Saddam, maza yazo mukaita asibiti jibifa jikinta yashika ko numfashi batayi" cewar matar da dady kayade cikin tsananin tashin hankali. "Nashiga uku, ni salamatu, dan Allah kutaimakamun mukaita mota, base munjira wani Saddam ba, semunje ta mace mana" mama tafadi haka tana hawaye. Aunty ce tace, "dama tanayin haka, kotana da wani ciwonne" "wlh bata da ciwon komai yarnan, bamu taɓa ganin tayi haka ba, seyau" mama tabawa Aunty amsa da fadin haka. "Ina ganinfa kamar suma tayi, a kawo ruwa mugwada watsa mata,zata farfaɗo insha Allah" daddy yafadi haka cikin son ya kwantar musu da hankali, ganin yadda gaba-daya hankulansu yatashi, zuhura da kanwar matar da daddy yakade harsun fara kuka. zuhurance tayi sauri taje ta dakko ruwa a fridge ta kawo, zuba mata ruwan aka shigayi a fuskarta zuwa kirjinta. kusan mintuna biyu ana zuba mata ruwan kafin taja wata doguwar ajiyar zuciya. Numfargashi tafara saukewa akai,akai. ganin ta farfaɗo sukayo kanta da mata sannu zukatansu cike da Murna. "Babu shakka familinnan suna matukar son matarnan" Aunty ta fadi haka a cikin ranta.
A hankali ta bude idanunta tana kallon mutanen dake zagaye da ita, hannun matar da daddy yakade ta kama, cikin sanyin murya me cike da rudani tace mata. "A'isha bani ruwa insha, guntun ruwan da'aka tsiyaya mata, A'ishan ta taimaka mata ta bata tasha. Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon mama tace, "mama wani mafarki nayi me rikitarwa" "wanne irin mafarki kuma diyar kirki" maman tatambayeta cike da mamaki. "Mama tunda natashi yau, nakejin wata irin faduwar gaba, jikina duk babu dadi kamar wadda wani mugun abun zesama, sekuma yanzu nayi mafarki A'isha tashigo dakina tasameni wai inzo mugaisa da mutanen dasuka bugeta, shine naga wani a zaune a falonnan, wlh yanda kikasan mijina na farko daya rasu babu abun daya banbantasu nakamanni, shine abun ya matukar firgitani" dammmm! Zuciyar daddy ta buga, jin muryar matar, a yanayin datayi magana yanzu babu banbanci da muryar matar data bashi Mustapha, shikanshi yana mamakin yanda amon muryar matar yakasa bacewa daga kwanyarsa duk kuwa da tsayin shekarunnan da aka dauka, a lokuta da dama idan yana zaune shikadai kalaman matar suna masa amsa kuwwa a cikin kwakwalwarsa. gabadaya falon tsit yayi dama Mustapha da Maryam basusan me'akeba. Sukuwa su mama, basu wani dauki zancen matar da mahimmanciba sun dauka zafin ciwon daya sametane lokaci daya ya firgitata. Aunty kuwa kallon matar kawai takeyi, ta kalli Mustapha ta kalli maryam. nuna Mustapha tayi tana kallon matar tace, "ko wancanne wanda kika gani ɗin?" dasauri matar ta kalli inda Aunty ta nuna mata, tozali idanunta suka mata da Mustapha wanda idanunsa suke a lumshe yanzu saɓanin dazu dayakafeta da tsumammun idanunsa shiyasama ta tsorata sosai harta sume. gani kawai sukayi ta mike tsaye zumbur, kura masa ido tayi na wasu sakanni kafin ta fara murza idonta dan tabbatar da ba gizo yake mataba. cikin karaji da matsananciyar rudewa muryarta na rawa tace, "sh...sh..shi..ne wlh, shineeeee!." takarashe zancen da jan maganar.