Kenza eBookz

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 31

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 31

Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 31: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 31. "shine wa Aunty Maryam" Aisha tatambayeta tana riketa…

3,365 words

ABUNDA KA SHUKA

(Shi zaka girba)

Zeey kumurya*

*4️⃣6️⃣*

*Bismillahirrahmanirrahim*

.............Yarasa a wacce duniya yake saboda, dadi,al'ajabi da mamaki. Tamkar ansauke masa wani abu mai nauyi a cikin zuciyarsa haka yaji. farinciki mara misaltuwa ne yamamaye dukkan baƙin cikin dake cikin zuciyarsa. jikinsane yayi wani irin sanyi tubus hakan yasa yakasa tabuka komai, koda danyatsa daya yakasa motsawa. falon yayi tsit bakajin komai se sheshshekar kukan *ammi* wadda take kara manne Mustapha akirjinta, tanajin tamkar ta maidashi ciki saboda tsabar kauna. lumshe idonsa yayi yakara kwantar da kansa ajikinta yana shaƙar sassanyan kamshinta,wani dumi yaji yana shiga jikinsa, ajiyar zuciya yake sassaukewa akai_akai. Aliya da tsaiwa ta gagareta ta zube akan kujera cikin rawar murya ta dubi daddy dayaketa murmushi me nuni da yana cikin tsananin farin ciki tace. "Da..daddy.. tayaya tazama mom dinsa?..mommy fa?.." taku daddy yayi yazauna a kusa da ita har lokacin fuskarsa nadauke da murmushi, gefen kuncinta yashafa yace, "bazaki fuskanci komaiba, autar Aunty amma very soon nasan zakigane yanda abun yake nanbada jimawaba" yanda aliya ta kurawa daddy ido tana kallonshine yagane bata fuskantar meyake nufi. Aunty ma zama tayi a kusa da Maryam wadda ta kurawa su Mustapha ido, ko kiftawa batayi. share hawayen fuskarta Aunty tayi tare da kauda kanta daga kallon su Mustapha. Sosai tausayinsu yake ratsa zukatan kowa dake falon musamman ma ammi. A hankali mama tafara jan kafarta data mata nauyi tazo gaban daddy, cikin daukewar tunani tace masa. "Alhaji, dan Allah, kafitar damu daga cikin duhun dakuka samu, gabadaya kunsa zuciyoyinmu cikin tararrabi, tayaya danku dakukazo dashi zezama dan Maryama.?" "Labarine metsaho mama, dole semun zauna mun nutsu sanna zamu warware muku zare da abawa" "daddy yabata amsa cikin girmamawa. numfashi kawai ta fesar taja kafarta, ta karasa inda su Mustapha suke, tafarawa ammi magana cikin lallami danta fuskanci tahakane kawai zata iya barin wannan kukannata. "Haba, Maryam kukan na menene haka,kiyi hakuri kiyi shiru kibar kukan haka, kizo ki fitar damu daga cikin duhun dakika sanyamu" a hankali taraba jikinta dana Mustapha wanda ya wani manne mata, sekace karamin yaro. Kukan datakeyi ta dena se ajiyar zuciya take saukewa. Mustapha kuwa kasa yayi dakansa idanunsa a lumshe, beso tsohuwar ta katse masa samun nutsuwa da jindadin dayakeji dalilin jinsa a jikin mahaifiyarsaba sedai tsananin miskilancinsa baze bari kagane yanayin dayake cikiba. kama hannun ammi, mama tayi tazaunar da ita akan kujera ta fara share mata hawayen fuskarta cikin tsananin so da kaunarta. Tun ba yauba, ta fuskanci akwai wani abu dake damun zuciyar ammin, tana dannewane kawai, domin lokuta da dama tana taddata cikin zurfaffen tunani ko kuma cikin yanayi nadamuwa. kallon Mustapha kawai ammai takeyi takasa dauke idonta daga kansa, wani sanyi takeji yana ratsa zuciyarta. maida kallonta tayi ga mama tare da kama hannunta cikin sanyin murya tace, "mama dan Allah abunda yake faruwa gaske ne ba mafarki nake ba, wlh nakasa tabbatarwa da kaina." cikin tausayawa mama tace. "Gaske ne Maryama ba mafarki kikeba, azahiri komai dakika gani yake faruw...." Ai ammi bata bari mama takarashe zancen taba ta zube a kasa tana sujjada domin nuna godiyarta ga Ubangiji. "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah" daddy, aunty, mustapha, ammi suke furtawa a cikin zukatansu tamkar hadin baki cike da tsananin farin ciki. A'isha da kanwarta mesuna Halima tare da surukarsu wato zuhura, mazauni sukayiwa kansu dan sunga abun bana ƙarau bane, ga ƙafafuwansu duk sun sage saboda tsaiwa.............

farincikin da dady da Mustapha da ammi suka nuna akan haɗuwar Mustapha da mahaifiyarsa a wannan lokacin baze misaltuba, duk miskilancin Mustapha kasa jurewa yayi yaje ya rungume mahaifiyarsa cikin tsananin shaukinta da kaunarta mara misaltuwa a cikin ransa, tabbas ya yarda mahaifiya daban take, dan yanayin dayake jin kansa akan bayyanarta baze misaltuba. ita kuwa ammi se shafa kansa takeyi tana sumbatarsa, takasa dauke ido daga kallonsa ko kunyar surukartata yau bataji. babu abunda yaraba Mustapha da mahaifinsa hatta tafiyarsu kuwa, har miskilanci data fahimci Mustapha'n dashi duk na mahaifinsa ne, yanayin yanda yake kallon abu dakuma lumshe ido shine kawai irinnata, amma komai na mahaifinsa ne. mama ganin kamar sun manta dasu agurin ta junansu kawai sukeyi tace sudai, ammi tazo ta fitar dasu daga cikin duhun dasuke. badan ammi tasoba taraba jikinta dana danta, abin kaunarta tace kowa yaje yayi Sallah don har anyi la'asar sannan ta basu labarin. Bayan kowa ya idar da sallar suka kara hallara a falon dukansu kowa yazaku yaji yanda abun yakasance, dan abun yarikitar dasu bakadanba musamman Maryam da aliya dasukasan mommy ce ta haifi Mustapha. Gyara zama ammi tayi tafara bada labarinta kamar haka...

"Sunana MARYAM IBRAHIM, mu yan ƙasar NIGER ne, anhaifeni a garin NIAMEY. Anan natashi anan na girma anan nayi makarantata anan nayi aure. mahaifina ba wani mekudi bane saidai yanada rufun asiri daidai gwargwado. mahaifiyarmuce kaɗai matarsa kuma mu biyu ta haifa, nice babba se kanina MUHAMMAD. muntaso cikin son junanmu, iyayenmu sunbamu tarbiyya wadda kowa yake yabanmu. inada shekara goma sha biyu kanina kuma tara, Allah yayiwa mahaifinmu rasuwa. Tun daga wannan lokacin rayuwa ta fara sauya mana,muka fara rayuwar maraici. Muhammad yakasance yaro me kwazo da zuciya. Tun baifi shekara goma sha biyuba, yake ƙoƙarin neman nakansa. Akwai wata makociyarmu matar tana da kirki sosai, kuma tsohuwace ta manyanta. mijinta itama yarasu yabarta da yaya maza guda biyar, tasake aure ta haifi yaro ɗaya shima mijinnata yarasu, se yan'uwan baban yaronnata suka daukeshi. Saboda masu kuɗi ne sosai, mahaifin yaron yamutu yabar masa dukiya me tarin yawa. Duk kafin a haifeni akayi haka, tsohuwar dakanta take bani labari. saboda Allah yahada jinina da ita. nibanmasan tana da wani ɗa ba, bayan biyar ɗin data haifa da mijinta na farko, dan da mijinta na biyun yarasu seta dawo gurin ƴaƴanta suka cigaba da zama tare. Tumunin takabar da'aka bata na gadon mijinta shitake juyawa take saide_saide. matar tana sona sosai kasancewar bata ƴa mace, haka zata saimun kayan kwalliya na mata da abubuwan buƙata. Seda dannata ya girma yazama saurayi sannan yadawo gurin ta, a lokacinma duka yayannata biyar ɗin sunyi aure. Sanda yadawo gurinta inada shekara 16. Kyakkyawane shi, dominshi ruwa biyu ne, mamansa buzuwace kamar mu, mahaifinsa kuma bafulatanine. Haka kawai Allah yadoramun tsoronsa dan gaskiya yana da kwarjini, gashi miskili, kuma baya sakarmun fuska, amma fa akwai shi da kyauta. Abun hannunsa betsone masa idoba. amma suna shiri sosai da kanina Muhammad saɓanin Ni, hakama mahaifiyarmu kullum seya shiga yagaisheta yamata abun arziki. sana'ar saida gwala-gwalai yakeyi yana zuwa Dubai da Saudiya yana sarowa, Allah kuma yabuda masa sosai. sauran yan'uwansa sesuka hade kansu suke nuna basa kaunarsa, afili karara suke nunu masa kiyayya. Amma shi babu ruwan shi haka yake girmamasu kuma komai suka ce yamusu yana musu, yasai musu gidaje yabasu jari, kuma idan suka zo da bukata haka zemusu. mahaifiyarsu da kanta take masa faɗa, akan yadena yawan basu kudi tunda suma barasawa sukayiba. Aduk lokacin da tamasa zancen haka, sedai yayi murmushi yace mata "idan be musuba wazewa bashifa da wasu yan'uwa sesu, tunda mahaifinsa shikadai yahaifa shima. ai bashida kamarsu.

Watarana dabazan taɓa mantawa da itaba a rayuwata. Ranar juma'a da safe. Nashiga gidansu domin duba mahaifiyarsa a lokacin bata da lafiya tana zazzaɓi, ina shiga gidan naci karo dashi a harabar gidan yana tsaye. seda gabana yafadi dana gansa bansan kuma meyasa ba, kuma seyamun kyau sosai tamkar wani Balarabe, satar kallonsa naitayi harnazo giftawa tagabansa seda na lumshe idona saboda kamshinsa dana shaka me dadin gaske. kaina na kasa nagaisheshi. me mamakon ya amsamun seyace mene ne kallonsa. dasauri na dago nasaci kallonsa senaga yahade rai, tsorone yakamani nafara bashi hakuri, ganin duk na firgice seyayi murmushi kawai ya wuce abinsa, nima jikina ba kwari nakarasa ciki. Ranar agidan na wuni inata aikece aikece, shikuma yazo yazauna yasamun ido yana kallona, duk motsin danayi idansa na kaina. duk se naji na takura. In takaicemuku zancedai a daren ranar yacemun yana sona. nayi matukar mamakinsa danni banyardabama,tun daga ranar nafara wasan buya dashi duk hanyar danasan zata hadamu seda na kauce mata, har gidansuma nadena zuwa. har gida mamansu tazo ta sameni tace kotamun wani lefinne nadauke mata kafa, nace mata wlh babu komai. babu yadda na iya haka naci gaba da zuwa gidansu dankar mahaifiyar sa tayi tunanin wani abu.

Aiko watarana yaritsani yace sena fada masa, shi dodo ne danake gudunsa, nace masa a'a. yace to idannakara gudunsa seya fadawa mahaifiyarsa yana sona. dasauri nace masa a'a karya fada mata nadena insha Allah. Tun daga ranar kullum semunyi tadi, dannima gaskiya inason sa. Dan duk inda ake neman namijin da mace zatayi alfahari dashi MODIBBOnah yakai. tun inajin kunyarsa harna rage. munsaba dashi sosai mun kuma shaku iya shakuwa. Tun munayin soyayyar a boye harta fito fili kowa yasani. mahaifiyarsa tafi kowa murna dajin labarin soyayyar mu, saɓanin mahaifiyarmu dabatayi murnaba, bansan kuma meyasa ba dan alokacin bata fadamunba. munkai kusan shekara muna soyayya dashi sannan akayi zancen aurenmu, aka saka ranar aurentamu. ba'awani saka lokaci me tsahoba na bikin. Tun daga lokacin yan'uwansa suka dora mana karon tsana nida mahaifiyata da kanina, wai kwadayine zesa na auresa badon Allah ba. nikuma ina matukar sonsa shiyasa tsanar dasuke mana ko'ajikina mahaifiyarmucema take damuwa. Rana bata karya, segashi lokacin da'aka saka na bikinmu yazo. Ansha shagali sosai anyi taro lafiya angama lafiya, muka tare a gidanmu dake cikin unguwartamu dai, amma da ɗan tafiya daga gidanmu. munyi rayuwarmu ta farinciki da jindadi da kwanciyar hankali, soyayyar damukasha da megidana *ALHASSAN MODIBBO* bazata faduba, yasoni ya tattalani kamar kwai, nima kuma ina matukar sonsa. yabani farinciki arayuwata duk abunda nakeso shiyakemun. Nandanan na murje nakara fari nayi haske, ana ganina anga ina cikin kwanciyar hankali Alhamdulillah. Nanfa tsanar da yan'uwansa sukemun ta karo, waina mallake musu dan'uwa se'abunda nace yayi shiyake. Shifa sesuka fara masa zagon kasa, suna masa wayo suna cin dukiyarsa a boye batare da saninsa ba. Aurenmu befi da wata biyar ba, Allah yayiwa mahaifiyarsa rasuwa, alokacin ina dauke da karamin ciki. Munji mutuwarnan sosai, mutuwar tadakeni nayi kuka tamkar raina ze fita, daga karshema shiya komo yana rarrashina. A hankali mutuwar tabi jikinmu muka hakura muka koma yimata addu'a. Tundaga lokacin yan'uwansa suka fara nuna masa wayonsu a fili, suka dinga binsa suna yabasu kadarorinsa. Shima dake yaganesu seya k',i basu. Mubamu saniba ashe sunacan suna haɗa masa gadar zare. watarana muna zaune a falo da daddare, ranar yadawo daga Dubai yayi sarin gwalagwalai masu yawa, ko inda ake narka masa su a maidasu dankunnaye da sarka bekaiba, ya a jiyesu a gida, yace dasafe zekai dan lokacin yagaji. a lokacin cikina yakai wata 7. Muna zaune naga yakuramun ido yana kallona, tafin hannuna nasa narufe masa idon nace. "Wannan kallonfa" hannuna yacire daga fuskarsa yana bina da wani kallo dayasa jikina duk yayi sanyi yace. "Nasone!" murmusawa nayi cikin jindadi duk da faduwar gaban danakeji amma haka nadaure nace. "Mijina, ina sonka sosai,ina addu'ar Allah yabarmu tare harkarshen rayuwarmu..." kalamai masu dad'i da sanyaya zuciya mukaita fadawa junanmu a wannan daren, a ranar MODIBBO yanunamun soyayyar dabetaba nunamun irintaba, soyayya me tsayawa arai dasanya nishadi a duk sanda aka tunata" shiru ammi tayi tana sauke numfashi, lokaci daya yanayinta yasauya idanunta yakawo ruwa. wani yawu medaci tahadiye sannan ta cigaba da magana. "Amma duk da haka jikina a sanyaye yake kamar wata mara lafiya, shima kuma haka na lura danashi'karfin hali kawai yakeyi. kaina na bisa cinyarsa bacci yasaceni, a falon ya kwantar dani ya tada sallar nafila kamar yadda yakeyi kowanne dare. Bansan mekefaruwaba se farkawa kawai nayi naji suna magana da wasu mutane a falon. bude idona nayi da sauri kokarin mikewa zaune nayi najini rungume ajikinsa. Abunda naji yana fadane ya matukar dagamun hankali. "Kome zakumin kumun,amma karku taɓamun lafiyar matata da abunda ke cikinta" ai bansan sanda na kwace daga rikon dayamunba, ina kallon mutane. Fuskokinsu duk a rufe da wani bakin kyalle. cikin tsorata nace musu. "Suwaye ku,? mekukazoyi gidanmu? mekuke bukata?" Wani me ƙatuwar muryane a cikinsu naji yace. "Ran mijin ki mukazo dauka" cikin zafin rai nace masa, "ƙarya kakeyi, baka isa ka kashe shiba matukar kwanansa bekareba. Ai rannasa ba'a hannunka yake......" kafin na karasa maganata naji daya a cikinsu yadagi yacillar gefe, cikin zafin naka da karfin zuciya namike zankoma gun mijina, suka karayin gefe dani. Intakaice muke zance, ina kallo a gabana, mutanennan marasa imani da tausayi masu zuciyar kafirai suka yankamun mijina, duk da uwar magiyar daya musu akan su kyaleshi karsu maida masa da ɗa/ya Maraya tun kafin suzo duniya, su fadi ko nawa sukeso,kome sukeso zebasu,amma sukace su sam basa bukatar komai. ransa kawai suke da bukata. Inaji ina gani suka masa yankan rago" kuka me karya zuciyar me saurarensa ammi tafashe dashi tamkar a lokacin abun yafaru.......✍️ Indai nayi posting kuna Comments toh zaku dinga samin update akan lokaci Meson complete Whatsapp 08166674823

ABUNDA KA SHUKA

BY* *zeey kumurya*

*4️⃣7️⃣*

*Bismillahirrahmanirrahim*

...........Babu wanda bezubar da hawayeba a falon se dady da Mustapha. shikam Mustapha zuciyarsace take tafarfasa tsabar bakin ciki da tausayin mahaifansa, jiyayi dama shima kukan zesamu yazo masa, koyaji sauƙin radadin dake damunsa a zuci. Farararen idanunnan nasa sun kada sunyi jajur, jijiyoyin kansa gaba daya sun mike sunyi rudu_rudu. kasa kawai yayi dakansa yana fesar da zazzzafan huci daga cikin bakinsa. daddy ma dauriyace kawai domin karya kara karyarmusu da zuciya, lallaminsu yafarayi duka da fadin. "Kuka bashine maganiba, duk da nasan tausayine yasaku kukan, amma yakamata kuyi hakuri kuyi shiru, kar kukan yajanyo muku wata matsalar, musammanma ke dakike kukan tun dazu" yakarashe zancen yana kallon ammi. shiru suka masa babu wanda yace masa kala, dakyar dai dady yashawo kan ammi tayi shiru tacigaba da bada labarin cikin raunin murya.

Chapter notes and social links

"shine wa Aunty Maryam" Aisha tatambayeta tana riketa ganin yadda duk ta burkice lokaci daya, mama baki sake take kallonta, danko sanda mijinta dan maman yarasu batayi irin wannan birkicewarba da gigicewa. "Dan Allah A'isha wanene shi wannan din danake ganinsa, koku bakwa ganinshine, kikalleshi zakiga kamarshi da miji na *MODIBBO*" "Danane" muryar daddy ta doki dodon kunnenta, dasauri ta kwace daga rikon da A'isha ta mata, taje gaban daddy cikin kuka tafara masa magana da fadin. "Danka, kuma?" To meyasa yake kama da mijina, hatta azurfar hannunsa irintace a hannun mijina harya mutu" "wai MARYAM, meke damunki ne, wanne mijinnaki kike magana akai, mufa bamugane mekike nufiba,gabadaya duk kinbi kin firgitamu" mama tatambayeta cikin dunbin al'ajabi, dan ita abun matar yafara bata tsoro harta fara tunanin ko matar tayi gamone. hannunta Aunty takama ganin duk falon sunkasa aiwatar da komai, hatta daddy kuwa daya tsaya kawai yana kallon matar. cikin lallami Aunty tafara mata magana. "Baiwar Allah, nasan ke musulmace kuma kinsan babu ta yadda za'ayi wanda yamutu yadawo, a kalamanki kuma naji kina fadin mijinnaki yarasu, kuma wannan danmune dashi mukazo garinnan, kinga babu tayanda za'ayi yazama mijin ki" "tabbas mijinannawa yarasu tun shekara fiye da talatin dasuka wuce, Amma kuma yau gashi naga wani me matukar kama dashi ai dole na shiga rudu" "baku da dane tare da mijinnaki?" Aunty tatambayeta cikin son tabbatar da abunda take zargi. kasa matar tayi dakanta idanunta na shatatatar da hawaye, tausayintane yacika su mama da iyalanta. cikin matsanancin kuka tace, "bani da ɗa ko ɗaya a duniyar nan" hawayene yaciko idanun Aunty, wani matsanancin tausayinta ne taji yashigeta lokaci ɗaya. shikanshi daddy seda kwallar tacika masa ido saboda yanda matar take kuka tamkar ranta zefita, ga dukkan alamu an sosa mata wani mikine a cikin ranta. Lokaci daya Mustapha daya kurawa matar ido kawai yana kallonta tun sanda tafara magana, yaji wani matsananci tausayinta gami da zazzafar kaunarta ta cika masa zuciya. rungume matar Aunty tayi tsam ajikinta, sedai batayi yunkurin rarrashintaba dan ta hanata kukan datakeyiba. tasan kukanne kadai ze rage mata radadin datakeji a cikin zuciyarta dan rashin haihuwa ba karamin abu tawaya bane ga dan adam. Maryam da aliyama hawayene kawai yake zuba a fuskarsa na tausayin matar, dan duk wani me imani idan yaga yadda matar take kuka seya zubar mata da hawaye. su mama kuwa mamakine yakamasu na matar, dan bata taɓa shiga irin wannan yanayinba akan rashin haihuwartata, saboda macece ita me tsananin tawakkali akan duk yadda rayuwa tazo mata,lokuta da damama mijinta yafita nuna damuwa akan rashin haihuwar tata. Daddy dayakejinsa tamkar mafarki yake, saboda duk wata alama dazata nuna masa matarnan mahaifiyar Mustapha ce ta bayyana agareshi. Saboda hujjojin dayake dasu kwarara guda biyu. Nafarko zancen azurfar dake hannun Mustapha datayi, na biyu kuma kukanta datakeyi yanzu yayi iri daya sak da wanda tayi lokacin data bashi Mustapha. sunayen Allah kawai yake kira danshima nutsuwarsa kokarin barinshi takeyi, haryanzu yakasa tabbatarwa da kansa ba mafarki yakeba, matar data bashi Mustapha itace tsaye agabansa. tattaro duk wata dauriyarsa yayi ya sarrafa harshensa dakyar yace, "kin taɓa haihuwa ne?" barin jikin Aunty tayi da sauri saboda yanda tambayar ta daki zuciyarta batare data dena kukan datakeba tace. "Ehhh!" tamkar mekoyan magana. mamakine yakama su mama domin su bata taɓa ce musu tataba haihuwaba, sun sandai tataba aure kafin ta auri baban Saddam. dauke kukan datakeyi tayi dif tamkar ba itaba, taci gaba da magana. "Nataba haihuwa na haifi yaro namiji amma yanzu bansaniba koyana raye koya mutu dan......" "Yazakiji idan nace miki wannan shine dannaki dakika taɓa haifa?" Daddy yakatseta da fadin haka cikin karfin zuciya yana nuna mata Mustapha. Ba ita kadaiba babu wanda kalaman daddy basu daki zuciyarsaba a falon, hatta Aunty kuwa da take da haske akan hakan. Maryam da aliya sunfi kowa shiga rudu, dama aliya itacan arude take banda zare idanu tana kallon mutane babu abunda takeyi. Maryam kuwa bata fahimtar komai, cikin duhu kawai kalaman daddy suke kara sanyata. Shikuwa gogan wato Mustapha wata muguwar faduwar gabace ta riskeshi shifa gani yakeyi abubuwan dasuke faruwa duka mafarki yakeyi ze iya farkawa wani lokacin. batasan sanda ta kama hannun daddy ba duka biyu tana maimaita kalmar. "daaanaaa...daaanaaa..." Tamkar wata mara fahimta. Abin gwanin ban tausayi. daddy danne wani abu daya darsu a zuciyarsa yayi yace, "ehh, dankine, duk da banji wani bayani akan kiba amma wasu hujjojina masu karfi sun tabbatar mun da kece matar dakika bani jariri, a wani dare akasar *Niger* a garin *Niamey*?" ilahirin jikintane yaɗauki kyarma gami da ɗauke war numfashinta na wasu sakanni a lokaci guda. Tabbas bazata taba manta wannan ranar data bayar da danta gudan jinintaba harta koma ga mahaliccinta. "Kidena mamaki, akan ikon Allah, domin buwayarsa ta wuce tunanin me tunani, shine me sauya al'amari a duk sanda yaso kuma a lokacin dayaso,kije ga danki da Ubangiji ya hadaku a lokacin da bakuyi tsammaniba dukanku." murmusawa daddy yayi yamaida kallo nsa ga Mustapha daya zama tamkar mutun mutumi yace. *"Son, come to your real mom"* A matukar firgici ta juya ta kalli su mama, da mamaki yahanasu koda kwakkwaran motsi idanuwansu kawai suke bawa abinci suna ganin abun tamkar wasan kwaikwayo, banda haka daga mutane sun rakosu sekuma dansu yazama na wata. cikin sauri ta juya ta nufi inda Mustapha yake wanda ko motsawa beyiba daga zaunen dayake, zuciyarta na tsananin bugawa tasa hannunta dake rawa tafara balle botiran gaban rigar Mustapha, lumshe idansa yayi shima tasa zuciyar natsananta bugu tamkar zata faso kirjinsa ta fito, wanda har mahaifiyartasa tanajin bugun zuciyar tasa. singlet fara kar itace ta bayyana bayan ta gama balle botiran gaban rigar tasa, cikin zafinnama da karfin dabatasan tana dashiba ta yaga singlet din gida biyu, faffadan kirjinsa fari tass dashi me dauke da kwantaccen bakin gashi yabayyana. a kirjinsa daga ɓangaren dama ta kurawa ido, wani abune asaman nononsa baki. (rowa) abunka da farin mutum tafito tayi dodar. cikin fitar hayyaci saboda tsabar farinciki tarungume Mustapha ajikinta tana me fashewa da kukan murna. "babu shakka, kai danane nacikina, dukda nasan mafarki nakeyi,zan iya farkawa a kowanne lokaci amma hakan baze hanani nuna farincikinaba akan ganinka......." Zantuka tayi ta saki na farinciki cikin matsanancin kuka tamkar zata shide tana shafa sumar kansa. shikuwa Mustapha lokacin data rungumeshi wata doguwar ajiyar zuciya yasauke, yanajin wani shauki nabin dukkan jiki da ruhinsa, wata nutsuwa saya rasa a rayuwarsace yaji ta lullubeshi lokaci guda, ga tsananin kaunar matar data cika dukkan zuciyarsa. wasu sanyayan hawayene suka fara zuba akan kuncinsa..........✍️ Na dazun naga kunyi Comments da yawa shiiyya sa kuka samu update da huri Meson complete Whatsapp 08166674823

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull