Kenza eBookz

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 32

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 32

Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 32: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 32. "kafin su kasheshin sunsha dambe dashi a kokarin shi na…

2,879 words

ABUNDA KA SHUKA

*zeey kumurya*

*4️⃣8️⃣*

*Bismillahirrahmanirrahim*

............Fitilar dake hannunsu na hango ta cikin glass din motar,suna tafe suna dube_dube. wata boyayyiyar ajiyar zuciya nasauke lokacin danaji me motar yaja motar mun fara tafiya. Se'alokacin naji wani gumi yana ketomun duk da motar akwai sanyin a.c amma tamkar heater haka tazamarmun. tunanin mahaifiyata da kanina ne yafadomun a cikin zuciya, "yaya zasuji idan suka wayi gari sukaga babu ni a cikin gidanmu?" natambayi kaina, wasu zafafan hawayene naji sun zubomun a kuncina. Ga wata masifaffiyar kewar ɗana data cikamun zuciya, danasan zan hado da wannan bawan Allah, da bazan bada yarona ga wani wanda bansaniba, bansaniba shima koba mutumin kirki bane, idona yarufe a lokacin dana bada ɗana ko tunanin me mutumin yakeyi cikin dare a waje banyiba na bashi dana, kuka me karfine yatahomun, da sauri na cusa kasan dankwalina na toshe bakina dan kar kukan yafito. "Kiyi hakuri, ki fawwalawa Allah dukkan lamuranki, kuma dukkan tsanani yana tare da sauki" mai motar yafadamun haka cikin sanyin murya. Ajiyar zuciya nasauke ina kokarin hadiye kukana nace masa. "Nagode" "ina kika nufa ne, acikin wannan daren" ya tambaye ni. shiru na masa dan bansan mezan kumace masa ba, danni kaɗai nasan irin azabtuwar da zuciyata takemun. kuncin danake ciki a wannan lokacin baze misaltuba, rasama tunanin dazanyi nayi, tun ina gane wasu abubuwan harna fice daga hayyaci na, saboda damuwa. farkawa kawai nayi naganni a cikin gidannan, kwance akan gado, ansanyamun drip a hannuna. mama da mutumin daya daukoni a mota tare da matarsa na gani adakin, sannu suka shiga yimun tare damun ya jiki, nidai da ido kawai nake binsu,ba bakin magana. Bayan ruwan yakare anciremun, mama tataimakamun nayi wanka, tabani tea nasha bisa dole sannan nasha magani narama sallolin da'ake bina azaune. bansan yazan fada muku halacci da karramawa irin ta mutanen gidannanba, sun rike tamkar jininsu, mama tasoni sosai, dan bata banbantani da ƴaƴanta. Alokacin su A'isha suna yanmata tare take hadamu take yimana komai. A duk lokacin da mama da *Alhaji Bashir* (wanda yaɗauki ammi a mota) suka tambayeni tarihina bana ce musu komai sedai naita kuka, hakan yasa suka kyaleni suka dena tambayata. matar alhaji Nasir, zakiyya macece me kirki tajani a jikinta sosai bata nunamun wani abu na kyara ko tsangwama. A lokacin danazo gidan Saddam yana karami danko yayeshi batayiba. seyazama kullum nice mai rainonsa yana hannuna kokuma in goyeshi, shiyake debemun kewar Muhammad dina, wanda kullum sena kulle kaina adaki nayi kukan rashinsa dana adalin mijina. Ga kewar mahaifiyata data kanina tana damina a rai. haka rayuwa taita tafiya. wasa_wasa segashi har nayi shekara biyu a NIGERIA a garin JOS. Alhaji Nasir, dan kasuwane yana sarar kaya yana kaiwa gariri, ranar daya dakkonima yakai wa wani abokin kasuwancinsa kayane, kuma dare yamasa a hanya, gashi yana da uzurin dazeyi a safiyar ranar shiyasa bebari ya kwanaba a nijer ɗin. Lokacin da alhaji Nasir yanuna yana son aurena, kin amincewa nayi saboda yadda muke da matarsa. mama tayita bani baki akan na amince da auren, indai zakiyyace bata da matsala. Itama zakiyyan a lokacin dakanta ta dinga nunamun bakomai tana bani baki. Ganin haka sena amince, dama kuma bakinshi nakeba. suda basusan asalinabama suka nemi na shiga cikin zuri'arsu seni zankisu. munyi aure da alhaji Nasir muka cigaba da rayuwarmu cikin farin ciki. Alhaji Nasir yana kwatantata adalci atsakaninmu, muma kuma muna mutunta juna nida zakiyya, hakan yasa zamanmu lafiya lau. Saddam yana shekara 6, zakiyya takuma samun ciki. ta haifi yarta mace, aka samata sunan mama ummussalma, amma umaimah ake cemata. Umaimah batafi shekara 1 ba, akayi bikin A'isha da wani abokin alhaji Nasir. umaimah nada shekara uku Allah yayiwa mahaifiyarta zakiyya rasuwa. Se rikonsu yadawo hannuna gaba-daya ita da Saddam, nikuma har zuwa wannan lokacin ko batan wata bantaba yiba. Alhaji Nasir yama fini damuwa da rashin haihuwata shida su mama. wani lokacin ma ninake bashi baki, duk da nima abun nadamuwana amma haka nake danne zuciyata bana nunawa. Kullum da tunanin Muhammad ɗana, da mahaifiyata nake kwana nake tashi. A haka rayuwa tayita tafiya, ahalin gidannan suna sona sosai, tunda nake agidannan bantaba fuskantar wata matsala ta kyara ko cin mutunciba, girmamawa da mutuntawa itace tsakanina da kowa. Bayan wasu shekaru masu yawa munje kasa me tsarki sauke farali, Allah yahadani da kanina da mahaifiyata, munyi murna mara misaltuwa sosai a lokacinnan. mahaifiyata ta sanarmun da sun shiga tashin hankali bakadanba dasuka wayi gari babu ni a cikin gidanmu. kanina yashigar da yan'uwan modibbo kara akan sufito dani da ɗana, danyasan babu me zaceni sesu. Kuma yanada kwakkwaran hujja akan hakan, ganin dasukayi zetona musu asiri, sesuka masa asiri yabar kasar gaba-daya aka nemeshi aka rasa. Se bayan wasu shekaru yakoma, ya dauke mahaifiyarmu suka koma Saudiyya da zama anan yayi aure yanzu yana da yara guda biyu, mace da namiji. Se'alokacin su mama sukasan tarihina, dama tun lokacin da alhaji Nasir ze aureni, nasanar masa na taba aure mijinnawa yarasu. Amma banfada musu inada yaroba. mahaifiyata tamun fada sosai akan meyasa nabawa wani dabansanshiba yarona. daga karshe kuma takoma addu'a akan Allah yasa yana hannu nagari, idan yana raye Allah yahadamu, idan kuma ya mutu Allah yaji kansa. Alhaji Nasir a hanyarsa ta dawowa daga Niger wata ranar Litinin yakai kaya, Allah yamasa rasuwa. Naji mutuwarsa sosai shima kamar modibbo, nayi kukan rashinsa. Gashi shikadaine dan mama namiji se kannensa gasunan mata ne guda biyu, A'isha da nafisa. yanzu shekara biyu kenan da rasuwar tasa. Kanina yaso nakoma Saudiyya da zama, amma naki amincewa saidai nadinga kaimusu ziyara. dannasan idan natafi su mama bazasuji dadiba, gakuma umaimah datake kallona a matsayin mahaifiya, bazan iya tafiya inbartaba. Zuwa yanzu nariga na fidda rai, daganin Muhammad ɗana, dan shekara 33, ba wasabace. saidai kullum cikin yimasa addu'ar alkhairi nake, a duk inda yake." numfasawa ammi tayi tace, "inafata yanzu dukkanninku kun fita daga cikin duhun da kuke" Maryam data kurawa matar ido kawai tana kallonta, kasa tayi dakanta tana hawayen dabatasan dalilinsuba. Mama ce, tace. "Gaskiya Maryama kinsha gwabarmaya, kai mutane babu Allah a ransu yanzu duk wannan abun dayafaru akan dukiyane fa, dukiyar daza'amutu abarta." Aunty ce ta amshe zancen da fadin. "Hmmm, wlh mama abun ba daɗin ji, mutane gabadaya kudi yasa sun manta da Allah, kaga mutum yayi shirka, yayi kisa duk akan kuɗi, kuma karshedai dole mutuwa mutum zeyi ya barshi, Allah yasa mudace kawai." "Ameen, suka amsa gaba-daya banda maryam da Mustapha daya amsa aransa. Kallon ammi daddy yayi yace, "angano wadanda suka kashe modibbonnaki?" kallon daddy ammi tayi itama, dasauri kuma ta dauke kanta daga kallonnasa sannan tace. "Ehhh, anganosu yan'uwansane suka sanya a kashe shi, yanzu haka suna gidan yari anmusu daurin rai da rai, dasu da wadanda sukayi kisan, amma mutumin biyu a cikinsu sun rasu, da babban su, da kuma na tsakiya yanzu saura su uku." cikin gyada kai mama tace, "kinjifa, yanzu mene ribarsu akan abinda suka aikata?.. gashi yanzu karshe sedai sukare rayuwarsu a gidan yari, gashima wasu daga cikinsu harsun je inda shi modibbon yaje" "to ai dama mama duk *ABINDA KASHUKA, SHIZAKA GIRBA* arayuwarnan" cewar Aunty. Aliya kam mamakine yakara kasheta dataji wai mommy ba ita tahaifi yaya Mustapha ba, duk tarin kaunar datake nuna masa. gyaran murya daddy yayi yace. "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah. dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah madaukakin sarki, daya nuna mana wannan ranar gabadayanmu, Allah yajikan wadanda suka rigamu gidan gaskiya mukuma intamu tazo yasa mucika da imani, Allah yarabamu dayin abin da zamuzo muna danasani akansa a rayuwarmu, Allah yaraya mana zuri'a, yashiryar dasu bisa tafarkin addinin Islama" "Ameen, ameen" suka amsa gaba-daya. duban ammi daddy yayi yace. "Nasan yanzu zuciyarki babu abunda takeson ji, sama dana baki labarin abunda yafaru bayan kinbada danki ko?" Murmushi ammi tayi tace, "kamar kashiga zuciyata kuwa, inason sanin kaina bawa ɗana, kokuma wanine yabaka riƙonsa kuma ina son sanin wacece ta raini ɗana, domin nagode mata." shiru daddy yayi na wasu sakanni, yayinda ammi taketa kallonsa. "Nifa senaga tamkar nasankama amma narasa ina nasankan" A'isha ce tatari zancen ammi da faɗin, "zakisanshi mana, ko da agidan TV ko jaridu ne, shine fa alhaji mainasara" waro ido ammi tayi waje irin na mamakinnan tace. "Alhaji mainasara, shahararren dan kasuwar nan danakeji ana fadarsa" "ehh, shifa" gyada kai ammi tayi cikin mamaki. mamace tace, "kinyi mamaki ko Maryama, kinganshidai mutumin damukejin labarinshi a duniya, yau gashi zaune tare damu. Ai mainasara mutumin kirki ne, bakigaba yanda yamana da muna asibitinnan, karramawa babu irin wadda bamuganiba hakama ahalinsa suma masu mutunta dan'adam, basu dauki rayuwar su da zafiba,sundauki duniyarsu da sauki, shiya kullum yake ganin cigaba a al'amuransa." murmushi daddy yayi ya kalli agogon hannunsa yaga har lokacin magriba yakusa, kuma yau yakeso su koma Kano, gashi yabar matukin jet dinsa a waje yana jiransu. gyara zama yayi yabasu labarin, daga lokacin da ammi tabashi Mustapha, har kawo yau atakaice. be boye musu komai ba, nadaga abunda mommy ta aikatawa Mustapha, dakuma taimakon da Maryam tayi agidansa. amma bece Sadik ne yakeyin fyaden ba.

Chapter notes and social links

"kafin su kasheshin sunsha dambe dashi a kokarin shi na kwatar ransa, dan har wasu yajiwa ciwo da naushin daya dinga kai musu, to Sarkin yawa yafi Sarkin Karfi. susu biyarne shikuma shi ɗaya, kuma su da makamai a hannunsu. ni kuwa banda ihu babu abunda nakeyi ina neman taimako, ɗaya daga cikinsune yatoshemun baki, da gwabjejen hannunsa. maimaita kalmar shahada yayitayi harsuka yankashi sekace wani dabba. kansa nayi da gudu bayan sun fice ina jijjigashi ina kururuwa ina fadin yatashi karya tafi yabarni. gaba-daya nima nayi dama_dama a cikin jinin dake fita daga jikinsa, tun ina fahimtar menakeyi harna dena. farkawa kawai nayi naga gidan a cike da mutane, ga jami'an tsaro suna jiran na farfaɗo suji karin bayanin abunda yafaru. mahaifiyatace a kaina da kanina Muhammad, gaba-daya ido yadawo kaina, masumun sannu nayi masu kallon tsegumi namun. nidai dakyar na yunkura na tashi zaune saboda nauyin da kaina yamun, ashe nadade a sume dan har anyi masa sutura. Dakin dayake mahaifiyata ta kama hannuna ta kaini, muna shiga na hangoshi a makara da gudu na kwace hannuna daga nata nanufi gurin da makarar take na kwanta akan gawartasa na fashe da kuka, surutai naitayi irin na fitar hayyaci, dakyar aka banbareni daga jikinsa, ina kallo aka fitar dashi zuwa gidansa na gaskiya. Tundaga wannan lokacin nazama ba uhmm ba um'um, saidai naitabin mutane da kallo, banaci banasha kuma bana kukan fili sena zuci, a haka har akayi sadakar uku. Nidai bazance ina cikin hayyacinaba a wannan lokacin, suma kam nayita ba adadi, ga tsohon ciki. Seda na kwanta jinya a asibiti, dannamafi wata a kwance, mahaifiyata kullum cikin kuka take, dan duk sun fitar da rai dani. Kanina Muhammad koyaushe cikin kwantarmun da hankali yake, tare da alƙawarin seya daukarmun fansar mijina akan wadanda suka kasheshi ko su waye. Mahukunta nata aikinsu na binkice akan kisan. kwana biyu da sallamoni daga asibiti yan'uwan MODIBBO sukazo akan rabon gado, nace musu suje surike komai ni banaso. banason komai na dukiyar na bar musu. Muhammad ne, yace hakan bazeyiyuba ai rabon gado Allah ne yace ayi, kuma ko badonniba, abunda ke cikinafa ai dole a fitar masa da hakkinsa. Sukuwa yan'uwansa ba hankali harsun fara hada kan kadarorinnasa suna mallakesu. Muhammad ne yaje yasamu wani yayan abokinsa lauya yafada masa, shikuma yashigar da maganar kotu. segamu har gaban alkali. Alkali yace, ai babu zancen rabon gado yanzu harse na haihu anga menahaifa. dan haka a tattaro duka abunda ya mallaka a damka masa har zuwa lokacin dazan haihu, budar bakinsu secewa sukayi ai anyi scanning anga mace ce, a cikina dan haka ayi raba kawai. mamakinsu bakadanbane ya kamani, dan duk jinyar danasha ko duniya basuzoba, amma wai anmun scanning anga macece. Alkali kuwa fatattakarsu yayi yace dole sena haihu, kar wanda yakara zuwa masa da batun harse na haihu. Ba'afi wata dayin hakaba, na haihu a asibiti bayan uwar wahalar danaci. Nahaifi yaro kyakkyawa me kama da ubansa, lafiya kalau dashi. Nakai kwana 3 bansan waye akainaba, bayan na haihu. saboda damuwa tamun yawa,jinina yahau sosai. Nafi sati a asibiti sannan aka sallamoni. yaro yaci sunan *Muhammad* nayiwa kanina takwara, saboda soyayyar dake tsakanina dashi, dakuma yanda yake son Muhammad, kodayaushe yana hannunsa, har wanka yake masa sekace mace. kullum cikin fadamun yake, idan yayi aure nabar bishi Muhammad, yarikesa. Haihuwar yaron ita taragemun kaso 50 nadamuwar danake ciki akan mutuwar adalin mijina. soyayyar uwa da danta, daga Allah ne, bansan yazan fasalta muku yanda nakejin kaunar danakewa Muhammad karami ba. Munje kotu alkali yamana rabon gado, tunda namiji aka haifa yan'uwan modibbo basu da komai a cikin gadonsa, komai nasa na yaronsane seni da'aka bawa tumunin takaba. tundaga wannan rana damukaje kotu yan'uwan modibbo suka sakomu a gaba, nida mahaifiyata da kanina. suka takura mana suka tsangwamemu. watarana bayan munyi arba'in, sukazo mun da wata fitinar akan dole sena basu dukiyar Muhammad, tunda sune danginsa na uba, zasu rike masa su juya masa kafin ya girma. harna mike zan tattaro musu kanina Muhammad yashigo gidan, dayaji abunda ke faruwa abakin mahaifiyarmu yace basu isaba baza'abasu komai na dukiyar Muhammad. fada sosai abun yazamarmusu da Muhammad duk da befi ɗan cikinsu ba, daga karshe dai dole suka hakura suka tafi. Yan'uwan mahaifin modibbo danaje musu yawon arba'in sena fada musu abunda yake faruwa, shine sukace natattaro komai nakawo musu aisu basu isa sun kwata ahannunsuba. haka kuwa akayi natattara komai nakai musu. Gwalagwalan da modibbo yasiyo a ranar daya rasu sukadaine ban bayarba. dama a cikin wata jaka yake, sena boye jakar a dakina. Akwai wata a zurfa a hannun modibbo, tunda nasanshi da ita nasanshi da ita, seda ya mutu aka cireta. itama sena jefata a cikin jakarnan dakuma tambarin gidansu modibbo, duk na hada na ajiye. Watarana da daddare muna cikin bacci, wasu mutane suka hauro mana gidanmu. basu tunkari dakin kowaba senawa. Ina rungume da Muhammad a kirjina naji ana ƙoƙarin rabani dashi ta ƙarfi. da sauri na farka, shima Muhammad din farkawa yayi yana tsandara kuka. cikin matukar tsorata naja baya, ina kara kankameshi a kirji na. tare da fadin, "suwaye ku?" wata dariyar rashin imani wani acikin su yakece da ita, sannan yace. "Wadanda suka kashe megidanki ne, yanzu kuma munzo mukashe wannan dannakine, daya hana ruwa gudu." tsoro metsanani ne yakamani, zanin goyonsa dake kan gadon, na yayiba na mike tsaye na goyeshi, suna tsaye suna kallona basucemun kalaba. cikin kuka nace musu, "wai kudin suwaye, me mijina da yarona suka muku? Kunkashe mun mijinma bazaku barmuba, sekun biyo dannawa guda daya tilo shima kunkasheshi, kuwanne irin marasa imani ne? Wlh Allah bazai barkuba ku....." Wata uwar tsawa wani a cikin su yadakamun. wadda tasani hadiye maganata, batare dana shiryaba. maganganu yashiga yimun wanda bana fuskantar komai saboda dimuwa da razani, tunanin hanyar dazanbi inkubutar da dana kawai nakeyi. A kalamannasa dai na fahimci yace, turosu akeyi kuma saboda dukiyar modibbo ne. jin haka sena fara neman inda jakarnan take domin na basu, dansu kyalemun dana. seda nagama shan wahala nanemo jakar, nace musu ga dukiya nan, indai dukiyace. Nidai dan Allah subarmun yarona karsu rabani dashi, kokuma ni su kasheni akan sukasheshi. A lokacin senaji gwara ni namutu shiya rayu. wata irin kaunarsa nakeji, tana kara mamaye zuciyata. mutanennan sukace susam Muhammad akace sukashe kuma sesun kasheshi, sannan su tafi da dukiyar. daukar jakar nayi kamar mika musu zanyi, nafaki idonsu nafada toilet na kulle, bubbuga kofar suka hauyi da nufin su ballata. ganin danayi tsaf zasu iya balla kofar su shigo su riskeni sena fara tunanin mafita. shawara zuciyata tabani akan nayi nesa da garin kawai, inda halima nabar kasar gaba daya,ta hakane kawai zan tsira daga sharrin muggan mutanennan. batare da tunanin komaiba na amince da shawarar zuciyata, window din toilet dinmu na kalla naga zan iya fita ta cikinsa, harna bar jakarnan sekumadai nadawo nadauka dannasan zatamun amfani nan gaba, na ratayata, a kafadata, na gyara goyon Muhammad tamau, na fice ta window. da wani irin gudu dabansan ina dashiba nafice daga gidanmu naita falfalashi. Banmasan inda nake jefa kafataba kawai shiga duk layin dana gani yakeyi. nasan balla kofar toilet din sukayi sukaga bananan shine suka biyo bayana, ina cikin guduna kamar ance in juya na hango kyalli fitilarsu daga can nesa. Abunda yasa nagane sune, kuma ni sukebi, duk layin dana shiga nan hasken fitilar yakebi shima. hankalinafa ya kara tashi gashi harna fara gajiya da gudun, ina shan kwanar wani layi nayi kacibus da wani mutum...........(labarin abunda yafaru tsakanin ta da dady ta basu sanna ta cigaba) bayan na bashi yaron senaji hankalina ya kwanta, koda sun cimmun bani da damuwa tunda ɗana ya tsira da yardar Allah, kuma dukiyar da'ake fadan akanta bazasu sametaba. wata mota nagani tazo ta wuce ta gabana ina cikin gudu, can kuma naga motar ta dawo ta tsaya a gabana, kokarin canza hanya nayi cikin tsananin tsorata. mai motar ne yafito da sauri cikin harshen Hausa yacemun. "Baiwar Allah, zoki shiga mota narage miki hanya, naga wasu mutane sunata gudu da muggan makamai karsu suganki suyi miki wata illar, gashi yanzu dare ya tsala" jin kalamansa yasa da sauri na bude bayan motar na shige batare da tunanin komaiba, shima ya koma cikin motar. kafin yakai ga jan motar mutafi azzaluman mutanennan sun karaso layin.........✍️ Comments update 11am MESON COMPLETE WHATSAPP 08166674823

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull