Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 33
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 33: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 33. Tafa hannuwa mama takeyi tana sallallami tace, "yanzu…
3,226 words
ABUNDA KA SHUKA
By* *zeey kumurya*
*4️⃣9️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
..........A razane Maryam ta dago ta kalli daddy zuciyarta na tsananta bugu tamkar zata faso kirjinta ta fito. gabadaya yawun bakinta kafewa yayi,kallon daddy take a matukar razane, kana ganinta kasan a matukar rude take dajin al'amarin. shiko mustapha lumshe idonsa yayi cikin yanayin da baze misaltuba. cikin tsananin farin ciki ammi tace. "Kaii, Masha Allah Alhaji, Allah yasanya albarka Allah yasa hadinnan yazame mana alkhairi, kai Masha Allah, amma naji dadi sosai Ubangiji ya tabbatar da alkhairi yabasu zaman lafiya da zuri'a dayyiba" "Ameen" Aunty ma kallon daddy kawai takeyi cike da dunbin mamakinsa bata taɓa tunanin abunda ze fadaba, kenan. amma kuma taji dadin wannan hadin da yayi sosai, dama kalar matar data dace da Mustapha'n kenan ba kalar su suhalat ba. tasan Maryam bazata taɓa bawa daddy kunyaba da yardar Allah. Aliya kam se murmushi take saki, najin dadi dakuma na shakiyanci ganin yanda Maryam duk tabi ta firgice. gashi kuma sun bala'in dacewa seyanzuma take ganin haka. sotake su hada ido da Maryam,amma ta sunkuyar dakanta. Maryam Sarkin kuka, se hawaye takeyi tarasa na farinciki ne, kona me?... gashi dai zuciyarta ta jima da kamuwa da kaunarsa, amma kuma hada aurensu da dady yayi yazo mata a wani irin yanayi na fargaba da tsoro. Daddy kam, nazarin Maryam kawai yakeyi yasan ya mata katsalandan acikin rayuwarta, shikansa yasan be kyauta mataba. besaniba kotana da wanda takeso. Amma shi yanada dalilin dayasa ya aura mata Mustapha'n, kuma yana fatan aurennasu yazamo musu alkhairi gabadayansu. cikin sanyin murya me nuni da rarrashin wanda akewa maganar daddy yafara mata magana. "Maryam! Bansan da kalmomin dazanyi amfani dasu gurin baki hakuriba akan wannan auren dana miki batare da yardarkiba, a matsayina na wanda bakomai bane a gurinki, amma duk da haka lokaci bekure mikiba, idan har kinga zaki cutu, kokuma kina ganin natauye miki wani hakki na rayuwar ki, karkiji komai ko wani nauyi ko kunya, tunda rayuwarkice. kifadamun idan bakyason aurennan, kamar yadda nasa aka daura yanzu senasa a warwaresa." Ajiyar zuciya nasauke, kaina na kasa bandagoba. kukan dake kokarin kufcemun na danne nace. "Babu komai daddy, aikaima ka isa dani, insha Allahu zanmaka biyayya gwargwadon iyawata bazan baka kunyaba" daga haka nayi shiru a raina ina fadin, "tayaya zan yarda a warware wannan auren da....." "Masha Allah, haka nakeson ji Allah yamiki albarka, yabaki yaya masu biyayya kamar yanda kikamun" daddy yakatsemun tunani da fadin haka. Addu'a sosai daddy yaita kwararawa mustapha da Maryam. kowa nagurin sesawa auren albarka yakeyi. nikuwa nayi shiru ina saurarensu jinakeyi tamkar mafarki nake zan farka wani lokaci. sonake na kalli fuskar gogannawa naga a wanne yanayi yake ciki amma nakasa. Ammi ko se kara rungumeni take ajikinta. Mustapha kuwa ko kwakkwaran motsi beyiba, miskilancinsa kuwa baze bari kagane yanayin dayake cikiba game da maganar aurannashi.....
Sallar da aka shiga a masallaci ta tarwatsa zaman, dady da Mustapha suka nufi masallaci. Aunty tana da alwalarta,dadduma kawai zuhura ta kawo mata tatada sallah a falon. Maryam da aliya ne suka shiga daki domin yin Sallah. zaune suke akan darduma bayan sun idar da Sallah. "Mairota how market?" Aliya tafadi haka tana kwashewa da Maryam da dariya, ganin yadda take komai jikinta asanyaye. banza Maryam tamata bata kulataba, dan ita haryanzu zuciyarta takasa yarda wai yanzu aure yashiga yatsakaninta da *heart beat* dinta. matsowa jikinta Aliya tayi ta fara mata magana seriously. "Wlh Maryam, kinyi dace da miji bakadanba domin yaya Mustapha irin mijin dakowacce mace zataso ta mallakeshine, amma ke nasan mene damuwarki akan wanan aurennaku. abu na farko dake damunki saboda kina da wanda kikeso wato yaya Sadiq, na biyu kuma kina tunanin yanda zakiyi rayuwa da wanda baya sonki" da mamaki Maryam ta kalli aliya, tamkar ta shiga zuciyarta dan abunda aliyan tace shine abinda take ta tunani tun dazu. daga mata gira aliya tayi tace, "koba haka bane" numfashi na sauke nace. "Hakane aliya, ni namafi tunanin yaya Sadik, dan yana matukar sona nasan bakaramin tashin hankali ze shigaba idan yaji wannan abun" "gaskiya abun babu daɗi rana daya arabaka da masoyinka dake da yaya Sadik dole zaku shiga damuwa, daman, amma kuma hakuri zakuyi dan bamusan alkhairin dake cikin wannan aurennakuba. shikuma yaya Mustapha kisha kuruminki, dan idan ana kuka akan soyayya seya miki shaɓe_shaɓe har da gunji, nina fada miki kuma." "Hmmm, aliya kenan bana tunanin haka agurinsa tunda shima kinsan yana da wadda yakeso,kawai babu yanda zeyine" tabe baki aliya tayi tace. "Wai ant suhalat kike nufi, tabb aiba wani sonta yakeba,kawai biyayya yayiwa mommy yake kulata, banda haka mezeyi da wata suhalat mace ba kamun kai" shiru namata domin nikadai nasan halin da zuciyata take ciki. baki aliya taita bani akan aurennan da dady yamun tana tausata. batasan nafi kowa murna da aurannanba kawai dai fargabata daya yanda zamuyi tarayya matsayin miji da mata dashi,nasan akwai ja. daga karshe kuma seta koma tsokatana wai zanyi fama da miskilancinsa. Ammi ce dakanta tazo takiramu domin Muci abinci. Da kyar daddy yayarda su tsaya suci abincin dan da cewa yayi tafiya zasuyi, mama ta masa magiyar yabari su kwana da safe sesu wuce, amma yace mata hakan baze yiyuba. Domin bakaramin ayyuka ne agabansaba, dan missed called din dake wayarsama kadai ya ishe sa, ga harkar kasuwancinsa yanaso gobe yakoma acigaba da daga inda aka tsaya. kadan sukaci abincin kowa yace yakoshi, Maryam kam batafi lauma biyuba tace takoshi. Mustapha kam beciba, Aunty ce tacewa ammi haka yake, bedamu dacin abinciba sedai coffee ko tea. ammi bata bata lokaciba ta shiga kitchen ta dafa masa hadadden shayi dayaji kayan hadi, ta kawo masa. tamkar zata bashi a baki saboda kauna. kafin isha'i su dady sungama shirinsu na tafiya. ammi tacikasu da kayan su bagaruwa da dabino datazo dasu daga Saudiyya, suna kewar juna sukayi sallama,bayan sunyi musayar numbobin juna. Maryam se kwakube Aunty take, batasan anan za'a bartaba tunda mijinta bandashi za'a tafi ze zauna gurin mahaifiyarsane. Afarfajiyar gidan Aunty ta tsaidata da fadin. "To, Maryam saduwar alkhairi, insha Allahu gobe kafin na koma kd, zanje gidan gwaggonki na mata bayani, inda halima har kauyennaku semuje da yaya suma mumusu bayani" Maryam bata amsawa Aunty ba, se kuka data fashe dashi tare da riketa. tausayintane yacika Aunty, aliyama se hawaye na tausayin maironta. rungumeta Aunty tayi tana bubbuga bayanta alamun lallashi. cikin kuka tace. "Aunty dan Allah nidai zan biki mutafi" duk dauriyar Aunty seda kwalla ta cika mata ido, domin itama bakaramin missing Maryam zatayiba. maida kwallar data cika mata idon tayi tadago da Maryam daga jikinta. cikin lallami tace mata. "Kiyi hakuri diyata, ai zandawo nanbada jimawaba, kuma aikinyi sabuwar mommy, gaki ga amminki zata miki fiyema da abunda zanmiki, kikwantar da hankalinki kidena damuwa, idan kuma mukayi waya da ammi tacemun kina damuwa tobazanzo intafi dakeba." Aunty ta karashe zancen tana sharemun hawayen fuskata. gyada mata kai nayi alamun gamsuwa. Addu'ar fatan nasara ta mun. rungume juna mukayi da aliya cikin shaukin juna muna kuka, da kyar Aunty ta rarrashemu muka yi shiru. harta juya zata tafi nace mata. "Aunty yaya Sadik fa, inajin tausayinsa." maganar Maryam karaf a kunnen Mustapha daya baro gurin daddy, yazo sukara yin sallama da Aunty. "Karki damu Maryam, nasan mezance masa dabaze damuba" Aunty tafadamun haka tana kallon Mustapha. cikin karayar zuci najuya nakoma cikin gidan dazan fara sabuwar rayuwa a cikinsa,jikina a matukar sanyaye. a zaune nataddasu dukansu a falon sunata maida zance. kaina na kasa na musu sallama, gefen Aunty zuhura datake bawa yaronta nono na zauna. jana ammi da mama suka shigayi da hira duk dan insaki jiki dasu musammanma ammi. seda kusan mintuna 20, suka shude sannan ya shigo falon, bakinsa dauke da sallama. amsa masa mukayi gaba-daya, ammi fuskarta dauke da fara'a ta nunawa mustapha gefenta yaje ya zauna. kallo daya zakayiwa ammi katabbarta da tana cikin tsananin farin ciki. fuskarta cike take da annuri, tarasa ina zata tsoma kanta saboda jindadi da murna. harta kira mahaifiyarta da kaninta tasanar musu. kaninta yace ze kirata anjima ta video call suga mustapha. muna zaune a falon Saddam da mijin A'isha suka shigo. suna zama mama tafara rattaba musu bayanin abunda yafaru...........
*KANO*
Yau suhailat da wani matsananci ciwon kai da zazzaɓi tatashi. jikinta gaba-daya rawar dari kawai yakeyi. misalin ƙarfe 11 na safe mommy tashigo dakin datake tana fadin. "kinanan kina wannan shegen baccinnaki na jaraba ko? kinsandai nan bagida bane babu masu aiki, kitashi kifito kimun shara." Wasu hawayene masu zafi suka zubowa suhailat, ita kadai tasan azabar datakeji ajikinta amma mommy tashigo tana mata masifa, duk mommy tabi ta canza mata yanzu kullum se fada da masifa, kamar ita tadora mata damuwar dake damunta. kan gadon datake mommy ta karasa da nufin tatasheta. tana dora hannu ajikinta taji zafi zau. "suhailat bakida da lafiya ne?" suhailat bata bata amsaba, hawa gadon mommy tayi ta janyota jikinta. da sauri suhailat ta janye jikinta daga na mommy, saboda kamshin turarenta data shaka bemata dadiba. kafin tayi wani yunkuri tuni wani amai yataho mata, kokarin sakkowa tayi daga kan gadon kafafuwanta kawai ta zuru aman ya kufce mata, ta fara kelayashi a nan bakin gadon, tamkar zata amayar da kayan cikinta saboda azabar aman, se haki takeyi tana kelayashi. kallonta mommy tayi cikin wani irin yanayi na alamar tambaya. gaba-daya suhailat din ta canza mata, jikinta har wani yalo yakeyi tsabar fari, ga cika data kara sekace wata matar aure, seyanzu ta lura da hakan. jan jiki tayi takoma kan gadon ta kwanta tana sauke numfashi,bayan aman ya tsaya mata. "Sannu" mommy tace mata adakile. dole ta mike tahau gyara gurin tanayi tana tsaki, bayan tagama gyara dakin ta gogeshi tass. ta dakko room freshener ta hau fesawa. suhailat na shaka wani aman yakara taso mata, da gudu tatashi tanufi toilet ta fara kakari. tsayawa mommy tayi cak tana kallonta zuciyarta cike da fargaba gami da wasiwasin meke damun suhailat din take ta kwara amai haka. wani tunani tayi dasauri tafice daga dakin taje dakin datake taɗauki wayarta takira likitanta ta mata bayani atakaice. Address din gidannata ta tura mata. da rarrafe suhailat ta fito daga toilet din, jikinta gabadaya ya mutu babu kwari kokadan a bakin toilet din ta kwanta, domin ko kan gadon bazata iya karasawaba. mommy data shigo taganka a haka tana numfarfashi se tausayinta ya tsirga mata. dagata tayi ta kaita kan gado ta kwantar, suhailat kam se toshe hanci take dan batason turaren mommy kokadan daga mata hankali yakeyi bakadanba. yanda jikinta yayi zafi zau se mommy ta rage mata kayan jikinta, towel ta dakko da ruwa ta daddanna mata ajikinta, se zafin jikinnata yaragu,amma se rawar sanyi take. lulluba mata blanket mommy tayi bajimawa bacci yadauketa. fita mommy tayi tafara rage ayyukan gidan. wajen 12/30 doctor din tazo. Bayan sungaisa mommy tamata jagora zuwa dakin, har lokacin suhailat baccinta takesha. duddubata ta shigayi, tanayi tana tambayar mommy yanayin yanda taga jikinnata. jininta ta diba tace, zataje asibiti ta auna seta dawowa da mommy da result din. godiya mommy ta mata, sukayi sallama ta tafi...........✍️
Meson complete Whatsapp 08166674823
ABUNDA KA SHUKA
By* *zeey kumurya*
*5️⃣0️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
.........A ɓangaren Sadik kuwa yau da wani matsanancin ciwon kai yatashi wanda ko idansa yakasa budewa saboda azabar ciwon kan, hakanne yasa besamu yafito ganin Maryam ba, kamar yadda yaci alwashi jiya. daga ciwon kai jikinshi gaba-daya yaɗauki wani irin zafi, da kyarma. tun yana iya sanin duniyar dayake ciki harya fice daga hayyacinsa........
********************
*DARMANAWA*
Saleemat ce zaune adakinta da waya a hannunta yau wurin sati guda kenan tana trying number'n Maryam amma a kashe. cikin takaici tafito daga dakinnata ta nufi dakin umma. ''umma wlh haryanzu wayartata a kashe, kuma su ba matsalar NEPA ba, bare nace caji ne babu a wayartata." saleemat ta fadi haka bayan ta daga labulen dakin. umma tana dubanta tace, "toko matsalar network ne, saleema?" "gaskiya umma bana jin network ne, wayarce dai a kashe" "to Allah yasa dai lafiya" "lafiya kalauma insha Allah, nafi tunanin wayarce ta samu matsala" "to Allah yasa muji Alkhairi" "Ameen, umma bari nakarasa ninkin danakeyi naje gidan gwaggo nasanar mata dakaina" murmushi umma tayi tace, "saleemat ba kunya, kawo kayan lefennaki zaki fada mata da kanki" dariya saleemat tayi tace, "Aiso nake na kunnota kwana biyu shiruma banjitaba" umma tace, "nimun hadu da ita jiya, dana fita, naga tanata sauri ne, shiyasa banfada mata kawo kayan ba."....
Gwaggo tana zaune adakinta tanata lissafe kudinta na adashi dana aikatau din Maryam. tanayi tana mitar sabon wata yashiga amma shiru bataji alert na aikatau din Maryam ba, gashi tanata kiran number'n lami bata shiga. sabuwar me aikin datayi me suna laure ce tashigo dakin ko sallama babu. zabura gwaggo tayi tashiga boye kudin akasanta. tana fadin, "ubanme yashigo dake dakina babu sallama, kinga laure kikiyayeni" tabe baki lauren tayi tana jijjiga kafa tana jifan gwaggo da kallon raini tace. "Kekika sani dai, uwar mako da rowa, wannan uban tumulin kudin ina kikasamoshi gwaggo?" cikin harzuka gwaggo tace, "bansaniba uwata, nace bansaniba, kujimun yarinya da fitsara haifata kikayi dazakizo ki titsiyeni da tambaya, to a gidan uwarki nasamo" "badai uwataba gaskiya" laure ta fada tana kauda kai gefe. "bazan kulakiba dannasan uwarki bata baki cikakkiyar tarbiyyaba, ina fatan kingamamun ayyukana. "Cabb, wannan uban ayyukan sekace wata jaka, nayidai iya abinda zan iya" rike haba gwaggo tayi tace, "aa..lallai laure rashin kunyartaki kullum kara gaba take to wlh baki isaba sekinmun duka ayyukan gidannan, zandinga biyanki kudin aikine a banza bakyamun aiki yanda Yakamata. wani kallon banza laure tayiwa gwaggo sannan tace. "Nawane kudinnaki da har kikemun iko akansa, akan 20,000 din dako kayan kwalliya bata isata na siya" "kinsan da haka meyasa kikazo mun aikin, Ai da sekiyi zamanki uwarki ta dinga baki" laure zatayi magana wayarta dake kan cinyarta tayi kara, fita tayi domin ta daga wayar. gwaggo ta bita da harara. kullum sesunyi sa'insa da laure, yarinyar da inda ta haihu setayi jika da ita. amma ta rainata laure bata da tarbiyya kokadan, duk fadan gwaggo da masifarta laure tafi karfinta, duk iskancin dataga dama shitakeyi kuma gwaggo bata isa ta hanataba sedai kallo da ido. kullum se gwaggo tashiwa Maryam albarka tana cewa, "yarinya me biyayya da hakuri bakamarkiba laure" a duk sanda gwaggo ta fadi haka se laure tatabe baki tace da gwaggo. "To kinsan da itan kika daukeni, kije ki dawo da ita mana" a kauye lami tasamowa gwaggo laure, dududu batafi wata da zuwaba amma ta gallabi gwaggo, ga yawon bin samari. gwaggo tanata cigaba da lissafinta na kudadenta, zuciyarta fari kal kamar takadda tatara kudin komawa Saudiyya. Ashe fitar da laure tayi tana waya, wani saurayinta ɗan daba ne yakirata wanda sukayi magana tun jiya zasuzo da abokansa suyiwa gwaggo fashi. tunda ta kyallara ido taga kudin gwaggon takirasa ta fada masa, amma da sharadin bayan sun kwaci kudin itama zebata nata kason. Bayan befi 40 minutes ba, suka karaso unguwar. Laure ce tafita dakanta ta tarosu ta musu jagora har kofar dakin gwaggo.(fashi da ranar Allah🤔)
Gwaggo kawai jitayi an banko mata daki anfado babu ko neman izni, susu biyarne. suka tsaya mata cirko_cirko ai. zabura tayi, ta mike tsaye tare fadin. "Subhanallahi suwaye ku, wadannan samudawa daku zaku shigomun gida har daki. lafiya?" daya daga cikinsune yace, "lafiyar ce takawo haka" wuka da yafito da ita daga aljihunsa tare da karbar wani mulmulallen karfe a hannu wani yana muzurai yacewa gwaggo. "Ki bamu kudin dake cikin gidannan ta lallami kokuma na fardeki na kwata" "wanne kudi kuma, uwarku ta bani ajiyan...." "Ke!" wani daga cikinsu yadaka mata da tsawa yana zaro wuka shima daga aljihunsa yana nuna gwaggo da ita. duk da gwaggo ta tsorata amma bakinta be mutu ba, kuma tace kome zesu mata bazata basu dukinba. ganin tana bata musu lokaci, wanda ya mata magana da farko ya kwada mata ƙarfen hannunsa akafa sau biyu, gwaggo ta hau ihu tana neman taimako. Toshe mata baki sukayi sannan suka datsa mata wuka agefen kafadarta, ga azabar yanka gata rufe mata baki da hanci da sukaimata, nanfa numfashinta yafara sarkewa daga karshema se numfashin ya dauke dif. Kasan gadonta kawai suka daga sukaga kuɗin acikin leda babba sekuma wani a cikin tarkacen kwanukanta, seda suka kwace kuɗin gwaggo kaf, ko sisi basu barmataba sannan suka tsallaketa suka fice. suna fita laure tabi bayansu da kunshin kayanta dama tagama hada komai nata.
Chapter notes and social links
Tafa hannuwa mama takeyi tana sallallami tace, "yanzu Alhaji macece ta aikata wannan abubuwan itama akan dukiyar, kai duniya ina zaki damune?.. wannan wanne irin masiface da bala'i, kadaukarwa kanka hakkin mutane saboda wani banzan burinka na duniya" "Gaskiya matarnan tacika shu'uma, kuma makira, Allah wadaran halinta" cewar nafisa. Maryam da aliya kuwa suman zaune sukayi dajin abunda mommy ta aikata, yanzu sungano dalilin dayasa mommy bata gida. Rungume Aunty ammi tayi ajikinta tana hawaye tace, "nagode sosai da yanda kika kula da ɗana, kika tsaya tsayin daka wajen ganin rayuwarsa ta inganta, Allah yasaka da alkhairi." kara rungume ta, Aunty tayi itama ajikinta tace. "Babu komai ai yiwa kaine, kuma Ni haryanzu Muhammad, kallon ɗana nake masa, babu abunda yacanza." sakin Aunty ammi tayi tana murmushi tace, "bazan gaji da miki godiyaba, Allah yaraya miki zuri'a ya kare gabanki da bayanki" "ameen" kallon Maryam ammi tayi, tundaga kallon farko data mata, taji kaunar yarinyar tashiga ranta. yarinyar ta burgeta ga nutsuwa a tattare da ita. yanzu kuma dataji abunda tayiwa ɗanta setaji kaunar tata ta karu aranta. "Zonan diyata yar albarka" ammi tacewa Maryam. A hankali ta mike cikin matukar sanyin jiki, ta nufi gurin ammi. rungumeta ammin tayi ajikinta, tana saka mata albarka, lokaci daya Maryam taji kaunar matar ta shiga ranta. Duban Zuhura mama tayi tace. "Zuhura, kije kidakko Abul mana magriba ta gabato." "Toh, mama" zuhura ta amsa mata cikin girmamawa sannan ta mike tashiga wani daki ta dakko ɗanta, mesuna Nasir amma ana masa lakabi da Abul. Jaririne dan befi wata uku ba. Sosai su mama suka jimanta halin mommy, dana yayyin baban Mustapha, ga kuma mamakin yanda Allah, yasakawa dukiyar Mustapha albarka. Ammi ma tayi mamaki sosai, dataji wai dukiyar Mustapha ce, tazama haka, gashi Allah yasa mata albarka, mutane da dama sun amfana da ita. duban daddy tayi tace. "Yanzu ina matar taka, inason ganinta itama namata godiya, ko bakomai ta rikemun yarona, bazan gazaba zanta mata addu'ar shiriya, Allah yasa tatuba takoma ga Allah" kasa kawai daddy yayi da kansa yana jinjina kyawun hali irinna ammi, duk abunda akace mommy tayiwa yaronta amma bata zagetaba, kota aibatataba se fatan shiriyama data mata. kallon Mustapha wanda yayi shiru tamkar baya falon daddy yayi yakira sunansa. "Son!" A hankali ya juyo lumsheshshun idanunsa ya kalli daddy, tare da motsa labbansa ya amsa masa. "Ina son sanar dakai wani abune, duk da nasan namaka karfa_karfa a cikin rayuwarka, amma inafatan zaka yafeni kakuma fahimci manufata" kallon daddy kawai Mustapha yakeyi amma be fuskanci meyake nufiba. fahimtar hakan daddy yayi. a gogon hannunsa ya kalla a karo na biyu. dagowa yayi yadubi kowa sannan yace. "Lokaci na kurewa, gashi a yau nakeson mukoma Kano, amma akwai abu guda daya danakeson sanar daku. A ranar da Mustapha ya warke daga ciwon dayayi, naje masallaci bayan an idar da Sallah nasamu liman mukayi magana akan wata bukatata,liman ya amincemun. batare da wani bata lokaciba nasa aka daura auren *MUSTAPHA da MARYAM* ni nayi waliccin mustapha,liman yayi na Maryam, tsirarun mutanen dasuka rage a masallaci suka zamto shaida"...........✍️ Meson complete Whatsapp 08166674823