Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 34
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 34: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 34. Saleemat bayan tagama abunda take tayi wanka ta nufi…
3,222 words
Saleemat bayan tagama abunda take tayi wanka ta nufi gidan gwaggo. tundaga soro take zuba sallama amma taji shiru, tsayawa tayi a tsakar gida dan basa shiga dakin gwaggo. sallamar tacigaba dayi amma taji shiru. kofar banɗaki ta kalla taganta abude babu kowa a ciki. "Ko gwaggo batananne?" Saleemat ta tambayi kanta. amma kuma ai ko fita zatayi tana rufe dakinta koda tabar gidan abude. dakinnata ta shiga da sallama dauke abakinta, atunaninta ko gwaggo bacci take. yanayin dataga gwaggo bakaramin firgitata yayiba, kwance taganta baki a daure cikin jini, ga dakinta duk a birkice. cikin kidima ta fice da sauri taje ta sanar da umma, tare suka dawo gidan da umma. bakaramin gigita ummantayiba itama, fita tayi tasamu wani makocinsu ta masa bayani, saboda suna ganin girman umma mazan unguwar shiyasa ya yarda ya shiga gidan gwaggo amma badan itaba. hankalinsu umma a tashe ta kira baban saleema ta fada masa halin da'ake ciki. Napep aka samu akasaka gwaggo aka nufi asibin AMINU KANO da ita.............
Likitar mommy bata dawo kawo mata result dinba seda yamma bayan ta tashi daga aiki, kafin tazo suhailat tayi amai yakai sau hudu, kuma taki cin komai, amma zazzaɓin jikinnata yasauka, se Rashin kwarin jiki kawai kedamunta, har wanka ta iya yi da kanta. likitan ta girgiza dataga abun dake damun suhailat din. Jiki a sanyaye ta nufo gidan mommy, gaisawa sukayi da mommy dake zaune a falo tana waya, sannan tatambayeta ina suhailat ta nuna mata dakin datake da hannu. suhailat na kwance, Dr ta shigo dakin da sallama. Amsa mata tayi tare da yunkurin tashi zaune. "Sannu patient ya jikinnaki? cewar Dr, bayan ta zauna akan stool din mudubi. tace "Da sauki Dr," "Masha Allah, yanzu i nane yake miki ciwo?" Dr, tatambayeta tana tsareta da ido. Tana yamutsa fuska tace, "kaina sekuma jikina da babu kwari inajin kasala sosai, sekuma jiri da tashin zuciya" Dr, tace. "Sannu, yaushe rabon dakiga period ɗinki?" dan jimm suhailat tayi tace. "Gaskiya namanta" "ohk, bari nasa Miki drip dinnan" Dr, ta fadi haka tana janyo jakar kayan aikin datazo dasu. Allurai taiwa suhailat na tsaida aman, sannan tasa mata karin ruwa. magunguna ta rubuta tabawa suhailat. addu'ar Neman sauki tamata sannan ta fice daga dakin cewa zuciyarta cike da tausayinta. Har lokacin mommy bata gama wayar datakeba. zama tayi taɗan jira mommy'n. katse wayar mommy tayi badan ta gamaba sedan ganin Dr ta fito. tace "Sannu Dr, harkun gama?" Dr, tace "Ehh, Hajiya namata allurar tsaida aman nakuma samata ruwa" "ok, babu magungunan daza'a siya?" "Akwai na rubuta nabata" "yawwa Dr, Nagode, amma babu kuɗi cash a hannuna, amma insha Allah anjima zanmiki transfer" "babu komai Hajiya, nizan wuce, ga result ɗin abunda ke damunnata" Dr, ta fadi haka tana mikewa. karba mommy tayi ta'ajiye akan kujera batare data dubaba, kokuma tatambayi Dr, abunda ke damun suhailat dinba, hankalinta nakan wayar dasukeyi ita da Binta akan zuwansu gurin boka gobe. sallama sukayi da Dr, tafice. daukar wayarta mommy tayi takira Binta suka cigaba da maganarsu........
Su dadddy sun sauka a garin Kano lafiya. daddy zuciyarsa fess yakejinta yau yasauke dakon dake kansa na shekaru masu dama. Aunty a part din su baaba talatu ta sauka, anan sukayi sallah itada Aliya,baaba talatu ta kawo musu abinci sukaci sannan Aunty tatara ma'aikatan gidan mata tace musu za'a sallamesu gobe, badon sunyi lefin komaiba. amma za'acigaba da biyansu albashinsu, godiya sukayiwa Aunty duk da basusan dalilin hakan ba. abunda yasa Aunty tayi haka, a ganinta bedace suci gaba da zama agidanba tunda babu mata a gidan, bazeyiyu su zauna daga su se ya'yan gida da megidaba. seda suka kebe a daki sannan Aunty tayiwa baaba talatu bayanin abunda yake faruwa atakaice kamar yadda ta bukata. sosai baaba talatu tacika da rudu, da al'ajabin wannan abu. Amma batayi mamakiba dantasan halin mommy ciki dabai. amma bata taɓa zaton ba ita tahaifi Mustapha ba.
Aunty tana fitowa daga part din su baaba talatu ta nufi part din su Sadik, dan yau ta kudurcewa ranta seta ganshi taga halin dayake ciki, ai hannunka baya taba rubewa ka yanke kayar. su faruq duk suna part din daddy. knocking din dakinnasa ta shigayi, data murda handle din tajita a rufe. bubbuga dakin taitayi amma bebudeba, dole ta hakura ta kyaleshi. part din daddy ta zarce, nan suka hadu sukaita hira dasu faruq cikin nishadi, daddy da Aunty nabasu labarin abunda yafaru a jos. sunyi farin ciki sosai dajin yayansu yahadu da mahaifiyarsa. Amma fa zasuyi missing yayansu sosai............✍️
MESON COMPLETE WHATSAPP 08166674823
ABUNDA KA SHUKA
*By* *zeey kumurya*
*5️⃣1️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
...........Mommy bata tashi duba result din da Dr, ta kawo mataba se bayan magriba. wani irin zabura tayi ta mike tsaye daga zaunen datake lokacin da taga abunda ke rubuce a jikin takardar. gani tayi kamar idontane benuna mata daidaiba, dakinta ta nufa da sauri ta dauki glass dinta ta saka sannan ta kara duba takardar abunda tagani da farko dai shita kara gani, da sauri ta fito falo hartana tuntube ta dauki wayarta tayi Dialing number doctor, ringing uku Dr, ta daga da sallamarta. batare da mommy ta amsa mataba tace: "Dr, Rahila yanaga wani result daban gane masaba, kodai bana suhailat din bane?" Cikin girmamawa Dr, tace. "Hajiya shine mana, natane" mommy na haki tace, "to ai bangane meke damunnatabane kimun bayani yanda zangane" numfashi Dr, taja tace: "Hajiya am sorry to say suhailat na dauke da ciki na tsawon sati shid......" "What" mommy ta katseta cikin karaji tare da yarda takardar hannunta. "Dr, kinsan mekike fadamun kuwa, suhailat din tawace take da ciki?" "Yes mah" abinda Rahila kawai tace mata kenan dan ta san duk bayanin dazatayiwa mommy a yanzu baza ta taɓa fuskantartaba.
batare da mommy ta kashe wayarba ta cillar da ita akan kujera tanufi dakin suhailat da saurinta. suhailat tana kwance tana tunanin Mustapha wanda kewarsa ta cika mata zuciya ta hanata sukuni. turo kofar dakin da mommy tayi da karfi yasata tashi zaune a firgice, gabantane yayanke yafadi ganin yanayin mommy'n. cikin tsananin bacin rai mommy tafara magana, "suhailat! nizaki kunyata, ki tozartani a idon duniya, ubanwa ya miki ciki?" Rasssss gaban suhailat yayanke yafadi cikin rawar murya tace. "Mo..mo..mmy cik..ciki kuma?" wani mugun kallo mommy'n ta watsa mata sannan tace. "Rahila zata miki karya ne, kuma yanayin ciwonkima kadai ya isa ya zama shaidar kina da shigar ciki, kifadamun ubanda ya miki ciki kafin na illataki yanzunnan" runtse ido suhailat tayi cikin tsananin tashin hankali, wata mahaukaciyar bugawa kirjinta yashiga yi. "Nashiga uku, yanzu idan yaya naji labarin cewa nayi ciki ze aureni kuwa?" ta fadi haka hawaye na zubo mata. cikin tsawa mommy tace. "Ina tambayarki uban da ya miki ciki, keta wani banzama can kike ko?" cikin kuka suhailat tace. "Kamal ne" "kamal" mommy ta maimaita cikin tsananin mamaki. jijjiga kai kawai mommy takeyi kafin tayi kwafa ta fice daga dakin. kuka sosai suhailat ta fashe dashi, ita zancen ciki betada mata hankaliba kamar yadda take tunanin rasa Mustapha, domin idan har yaji wannan labarin tasan maganar auransu ta rushe, danyasha fada mata yatsani zina kuma yatsani mazinaci!..........
mommy tana zaune a falo ta rafka tagumi abun duniya duk ya isheta, kullum seta Kira layin Sadik amma bata samunsa. gashi gobe da sassafe zasu tafi Niger ita da Binta, tana son neman shawarar Binta akan cikin dake jikin suhailat amma kuma batason tonawa kanta asiri dantasan binta bata da sirri, zuwa zatayi tayita yamadidi da ita a cikin kawayensu. shawara ta yanke kawai suna dawowa daga Nijar din zata kai suhailat a zubar mata da cikin, tunda Binta tace baza su wuce sati daya ba zasu dawo. da wannan tunanin taji zuciyarta ta dan mata sanyi akan damuwar datake ciki..........
kusan raba dare su Aunty sukayi suna shan hirarsu cikin nishadi, kokadan su haidar basuyi zancen mommy ba. se Aunty cema tace musu yakamata zuwa yanzu ace sunnemeta sunji halin datake ciki, dan kome mommy ta aikata mahaifiyarsuce matsayinta baze taba canzuwa a gurinsuba. sukace mata da safe insha Allah, zasu kirata........
*JOS*
Sallar isha'i ce ta ta tashemu, bayan an idar muka dawo aka cigaba da hira. se kusan karfe biyu na dare sannan kowa ya nufi part dinsa, ashe part din da muke zaune na ammi ne. falo ne da dakuna uku, kowanne da toilet a ciki. Dakinta ammi tace naje na kwanta a kan gado. shikuma Mustapha ta bude masa wani dakin, da kanta ta share masa ta gogeshi tass, sannan ta sakamasa turaren wuta me dadin kamshi, a darennan seda ta wanke masa har toilet, duk da yana cewa tabarshi dare yayi da safe a gyara amma ammi tace a'a baze kwana A cikin dattiba. wanka nayi a toilet din ammi, kafin na fito ammi ta'ajiyemun wata rigar bacci sabuwa mara nauyi. rigar kawai nasaka kawai na kwanta saboda ciwon kan dake damuna, ga wani irin bacci danakeji. Mustapha yau yana cikin tsananin farin ciki, mara misaltuwa yanda ammi takeyin nan_nan dashi yafi komai yimasa dadi. dakin ya shiga da sallama bayan ammi tagama gyareshi, tsaf dashi dakin setashin kamshi kawai yakeyi. kayan jikinsa ya fara ragewa sannan ya shige toilet yayi wanka tare da dauro alwala. idanuwansa yau a bushe suke ko baccinma bayaji saboda farinciki, a gefe guda kuma zuciyarsa cike take da kewar yan'uwansa. dan yasan ammi bazata barshi yakoma Kano nan kusaba. tsayawa yayi a gaban madubin dakin yana tsane sumar kansa, tunanin abunda zesa a jikinsa yayi, dan gaskiya baze iya maida kayan daya cireba. Kwankwasa kofar dakin da'akayi ya katse masa tunaninsa. batare da yayi maganaba yaje ya bude kofar, ammi ce tsaye hannunta dauke da wata leda, dama yasan itace, murmushi yamata kamar yadda itama shine dauke akan fuskarta. "Sannu ammi, yakamata kije ki huta haka dare fa ya raba" yafada mata cikin sanyin murya. murmushi ta masa tace, "to shikenan Muhammad, baka bukatar wani abu?" Yace, "saidai abun sallah" mika masa ledar hannunta tayi tana fadin, "bari na dakko maka" karba yayi yajuya ya koma ciki. ledar ya bude ya duba, jallabiyace guda uku masu kyau, se tashin kamshi suke ammi ta feshesu da turare. murmushi yayi cikin tsananin jin kaunar ammi a ransa ya dauka guda daya ash colour yazira a jikinsa. ammi ce tashigo dakin da sallama ta ajiye masa daddumar a gefen gado. "Thank you real mom" murmushi ammi tayi me sauti dajin abunda yace. tana murmushin tace, "kana da fake mom ne?" murmushi yayi shima amma bebata amsaba, ya zauna a gefen ta tare da kwantar da kansa akan kafadarta. shikadai yasan irin dadin dayakeji idan ya rabi jikin ammi, yanajin dama karta tafi ta zauna su kwana tare, itama ammin hakanne anata bangaren bataso tabar gudan jininnata a halin yanzu shiyasa tun dazu takasa zuwa ta kwanta. tana shafa lallausar sumar kansa tana masa tambayoyi akan wasu abubuwa na rayuwarsa da suka shude, tun yana bata amsa har bacci ya daukeshi ajikinta, bacci me cike da nutsuwa daya manta rabon dayayi kamarsa. a hankali kamar wani jariri ammi ta lallaba ta kwantar dashi tare gyara masa kwanciya. kana kallon yanda yake baccin kasan cikin kwanciyar hankali da jindadi yake yinsa. Addu'a ta tofa masa, sannan tayi kissing goshinsa da kumatunta. seda ta rage masa hasken dakin sannan ta fice cikin shaukin dannata. sanda ta koma dakinta Maryam ta jima dayin bacci, wanka tayi itama sannan tafito tafara jero sallah domin nuna godiyarta ga Allah......
Har aka fara kiraye_kirayen sallah ammi bata runtsaba tana kan sallaya tana rokarwa danta addu'oin samun dacewa duniya da lahira. seda akayi kiran assalatu sannan ta mike. kan gado ta nufa inda Maryam take a kwance tanata sharar baccinta tafara tashinta a hankal tana kiran sunanta. A hankali Maryam ta bude idanta dake cike da bacci. "Diyata ki tashi lokacin sallah yayi" daga mata kai Maryam tayi tana kara lumshe ido kamar zata koma baccin. falo ammi tafita domin tatashi Mustapha shima, tana tura kofar dakin taga bayanan se motsin ruwa dataji a toilet, juyowa tayi takoma daki tunda yatashi. da kyar na iya tashi zaune, saboda baccin be isheniba. nina manta a inda nake, seda na watstsake na tuna, hakan yatabbatarmun da abunda yafaru jiya ba mafarki bane gaske ne, dan da kokwanto a raina na kwanta bacci musammanma aurenmu da *heartbeat* nafijin abun tamkar almara. toilet na shiga nadauro alwala, hijabi ammi tabani na zira na tada sallar. Bayan mun idar nadanyi lazimina nadubi ammi nace, "ina kwana ammi" da fara'a tace. "Lafiya kalau, ya kwanan bakunta?" "Lafiya kalau" na'amsa cikin jin kunyarta. hira ammi tashigamun tare mun tambayoyi akan rayuwata cikin hikima nikuma ina bata amsa. seda gari yafara haske sannan ta tashi ta fita. Tana fita nima na mike nashiga gyaran dakin, duk da babu wani datti a cikinsa se tashin kamshi dayake, bayan nagama na wanke toilet tass sannan nafita falo. Ammi bata falon kuma bata kitchen tanacan sunashan hira da danta. (Allah Sarki uwa mai dadi, Allah kajikan iyayenmu😥🙏.) nariga nasaba da aiki idan na tashi da safe shiyasa duk randa banyiba se injini wani iri. kitchen din na shiga, dan babbane komai tsaf an killakeshi a mahallinsa, kayan da akaci abinci jiya da daddare su nahada na shiga wankewa, dan jiya hira bata bari anyi wanke_wankenba. Ina cikin yi ammi ta shigo ta sameni, kama baki tayi tare da fadin. "Diyata wayasaki aiki, na shiga dakima naga kin gyara shi fess, yanzu kuma shine kikazo kika kama wanke_wanke, aida kinbarshi nima zanyine kokuma zuhura idan tashigo setayi, dan ma umaimah batananne amma ita takeyi base kin wahalar da kanki ba." murmushi nayi amma bance mata komaiba, danni banga abun wahalarwaba. da kyar ta barni na karasa amma da cewa tayi sedai na barshi ta karasa. Wajen karfe tara Aunty zuhura ta kawo mana lafiyayyen abinci na breakfast ammi da kanta ta zubamun ta dibarwa danta nasa takai masa daki, nidai har lokacin bamu hadu dashiba, inason inje ingaisheshi amma kuma nakasa.
Ammi abayoyi da jallabiyoyi take saidawa, kaninta yana turo mata daga Makkah kokuma intaje ta taho da wasu. Dilar datazo da ita a wannan zuwan datayi ita ta kunce, ta dibarwa Maryam abayoyi da yawa kafin a aiko mata da kayanta. shima Mustapha ta dibar masa jallabiyoyi. bayan nagama cin abinci nayi wanka na shirya cikin wata abaya me kyau a cikin wanda ammi ta kawomun, na yane kaina da mayafinta. ammi tace in fito muje mugaida mutanen gidan. se'alokacin muka hadu dashi, kaina a kasa nagaisheshi bayabo bafallasa ya amsamun. Part din mama muka fara zuwa mukagaisheta sannan part dinsu aunty zuhura, nasu matar da daddy yakadene na karshe. Bayan mundawo part din ammi, mukayi waya da Aunty tatambayeni babu matsalar komai nace mata babu, ta kara jaddadamun anjima zataje gidan gwaggo ta fada mata, nace dan Allah idan taje ta hadani da ita a waya. daga baya Aunty tabawa Aliya wayar mukasha hira tanatamun shakiyancinta da barkwancinta..........
*KANO*
Mommy tun sassafe suka doka sammako suka wuce nijer, bayan ta dokawa suhailat uban warning akan ko kofar gida kartayi gigin lekawa, kuma karta fadawa kowa tana ciki koda wasa, tasa asamo mata wadda zata dinga kula da ita, anjima zatazo. mommy ta a jiyewa suhailat ishashshen kudi da kayan abinci daze isheta kafin ta dawo.
Likitoci basu karbi gwaggo ba, seda aka kira dan sanda sannan suka karbeta. inda suka kwada mata karfe a kafa ta samu karaya a gurin, sun mata dori sannan kuma suka mata ɗinki a kafadarta inda suka yanketa da wuka, anmata karin jini kuma saboda jinin data zubar. Duk abinda aka bukata na kuɗi kona wani abun, baban saleemat da umma ne sukeyi. Allah yatakaita barayin basu tafi da wayar gwaggo ba, da ita aka kira yan'uwanta na kauye aka sanar musu....
Bayan Aunty sungama waya dasu Maryam dan har Mustapha ma takira sungaisa. wayar faruq takira tace yazo ya sameta a falon mommy. Da sallama ya shiga yazauna a gefen Aunty Bayan ta amsa masa. Aunty ce kadai a falon Aliya tana daki tana hada musu kayansu. "Ina kwana Aunty" "lafiya kalau faruq, yau baka fita aikin bane?" "Ehh, Aunty yanzu nake shirin fita, dan tun safe daddy yamun magana to nadanyi wani aikine a system" "ok, Allah yataimaka" "ameen" "dama maganar Sadiq zan maka, yakamata zuwa yanzu mudubashi musan halin dayake ciki, danbazeyiyu a barshi hakaba, ace mutum ya kulle kansa a daki babu ci da sha na kirki, jiya damuka dawo naje nadubashi naji kofarshi a rufe, idan kana da extra key na dakinsa ka bude muga halin dayake ciki, hankalina ya kasa kwanciya. Ai hannunka baya rubewa kayanke kayar. Dazu danayiwa yaya maganar seyace in kyaleshi, amma yanzu tunda yafito kaje kadubomunshi." numfashi faruq yasauke yace, "shikenan Aunty, Bari naje naduboshi" "yawwa faruq ina jiranka." Mikewa yayi yakoma part dinsu, dakinshi ya shiga ya binkico key din dakin Sadiq dayake dashi. A mawuyacin hali yasamu Sadiq jikinshi ya wani sandare kamar gawa, gashi ko numfashi bayayi. Hankalin faruq a tashe yasanar da yan'uwansa da Aunty, babu bata lokaci suka daukeshi zuwa asibiti..........
*Bayan sati daya*
Har yau mommy bata dawoba kamar yadda tacewa suhailat, suhailat ta kira wayarta amma bata sametaba. Su faruq ma sunkikkira mommy dansu sanar mata ciwon Sadiq suma basu sametaba, suhailat kuma idan suka kirata bata dagawa. Su Hajiya gwaggo an farfaɗo amma batasan wake kantaba, sesunbatu take tana kiran "kudadenta,kudadenta." An kawo lefen saleemat Masha Allah kaya sunyi kyau sosai, ansaka bikinta bayan karamar sallah da sati hudu.
Abangaren su Maryam kuwa komai natafiya yadda yakamata, gidan kowa haba_haba yakeyi dasu. Ammi tayiwa Maryam da Mustapha siyayya ta kaya sosai. Mustapha tun kwanansu uku a Jos din, yakebin Saddam kasuwa domin yacewa Ammi baze iya zaman gidaba kamar wata mace. Motarta ammi tabasa yake zirga_zirga da ita. Tsakaninsa da Maryam gaisuwace kawai take hadasu. Part din mijin ammi, nan ammin tasa aka gyara musu aka yimasa fenti da dan gyare_gyare. Falone da 2 bedrooms a part din se kitchen da ɗan karamin store. komai sabo dal ammi tasa aka samusu, amma Mustapha ne yabiya kudin. danda tace ita zata biya yahanata. Kullum suna waya dasu Aunty, mustapha yaso zuwa yaduba jikin Sadiq, amma daddy yahana. Danyace idan yataho Maryam bazataji dadiba, idan ya barta ita kadai. Yau juma'a, kuma yaune ango da amarya zasu koma part dinsu subar na ammi, yau kuma *umaimah* zata dawo daga hutun dataje gidan kakanninta na wajen uwa...........✍️
MESON COMPLETE WHATSAPP 08166674823
ABUNDA KA SHUKA
Zeey kumurya*
*5️⃣2️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
..........Da misalin ƙarfe 11 na safe muna zaune a falon ammi nida Aunty zuhura, yaronta yana hannuna ina masa wasa muna hira jefi_jefi. kamar a mafarki naji kamshin turarensa, nidai nasan yana kasuwa kuma baya dawowa a irin wannan lokacin. dago kaina nayi da sauri yayi daidai da shigowarsa falon bakinsa dauke da sallama. maida kaina kasa nayi zuciyata na ɗan bugawa, a hankali na amsa masa sallamar dan dakyarma inyaji, saɓanin Aunty zuhura da har gaisawa sukayi ta masa sannu da zuwa, nidai daga amsa masa sallamar bankara koda kallon inda yakeba nacigaba da yiwa Abul wasa. yanda Maryam bata kalli Mustaphaba, haka shima ko kallon inda take beba yashige dakin ammi bayan sungama gaisawa da zuhura. kallon Maryam zuhura tayi tana sakin murmushi, miskilancinsu na bata dariya, yanda idan suka haɗu suke wani basarwa tamkar ba ma'aurataba, zataso taga wanda zefara aje miskilancinsa tsakanin Maryam da Mustapha. Nikam banmasan tana kallonnawaba natafi duniyar tunanin yanda zamanmu ze kasance ni da shi a mahalli ɗaya.