Kenza eBookz

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 35

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 35

Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 35: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 35. Ammi na zaune a bakin gado tana waya da wata cousin dinta…

3,370 words

Ammi na zaune a bakin gado tana waya da wata cousin dinta datake Niger mustapha ya shigo dakin da sallama, zama yayi a gefenta yana jiran ta gama wayar, befi 1 minute da zamaba sukayi sallama ammi ta aje wayar. tana dubanshi tace."NOOR, yanaga kadawo daga kasuwar dafatan dai lafiya?" lips dinshi na kasa yaɗan lasa sannan yace. "Lafiya kalau Amminah, daddy ne yakirani akan karatun waccan" tsareshi ammi tayi da ido tace wace waccan kuma batasa suna ne?" shafa kansa yayi tare da lumshe idonsa a hankali kamar bayasonyin magana yace, "me sunanki" ita ammi ma dariya yaso ya bata, yanda ya wani basarwa, tace. "Uhm, inajinka meyafaru da karatunnata?" yana latsa wayarsa yace. "Daddy yace, anemi PRIVATE SCHOOL abiya mata tayi NECO, tunda WAEC lokaci ya kure, ran monday zasu fara. Idan Allah yakaimu November_december setayi PRIVATE WAEC" ammi tace. "Hakanma yayi Allah yataimaka yabada sa'a, kayiwa Saddam magana seya samo mata makarantar dazatayi" amsa mata yayi cikin girmamawa sannan ya mike yayiwa ammi sallama ya fice. daya dawo ze fitama bandago na kalleshiba, inaji dai Aunty zuhura ta masa Allah yakiyaye hanya. Lekowa ammi tayi takirani, da Abul a hannuna na mike nanufi dakinnata. Bayan na zauna ta bani abu a kofi kamar magani, tun washegari garin ranar danazo kullum seta bani nasha sau uku a rana. da daddare kuma kafin na kwanta tasani inci fruits. karbar abul tayi daga hannuna dayaketa bingira mata dariya. Seda na shanye tass sannan na ajiye cup din ina yamutsa fuska saboda rashin dadi. wani abu ta mikomun daban tace in lasa, maganine na gari aka kwabashi da zuma, shikam nasha sosai ta dadin rai saboda zaki_zakin zuma, a kunyace nakesha duk da ammi hankalinta nakan Abul. da farko data fara bani bansan amfaninsaba, seda ta hanani tsarki da ruwan sanyi saidai na dumi sannan na gane. kuma kullum kafin nayi bacci setasa na shiga ruwan zafi wanda ta tafasashi da lalle da wasu ganyayyaki masu amfani. da safe kuma ina tashi zata samun turaren tsugunno a kasko. inna gama dashi tasamun na turare jiki. banshanyeba na ajiye saboda cikar danaji cikina yamun, akan mudubi na ajiye robar bayan na rufe da murfinta. Ammi tace, "yawwa ɗiyata kinsha sosai ko?" A mutukar kunyace na dagawa ammi kai, kaina na kasa. kwantar da Abul tayi a kan gado sannan ta dakko wayarta tana fadin, "bari nakira antinku takirani tun dazu tace na baki wayar kina wanka, nace idan kinfito zankirata kuma na sha'afa" komawa bakin gado nayi nazauna ammi ta mikomun wayar bayan ta shiga, daukar Abul tayi suka fita parlour. "Assalamu alaikum" Aunty ta fada bayan ta daga wayar. amsa mata nayi na kara da faɗin, "ina kwana Aunty" tace. "Lafiya kalau, ya Jos din, ina fatan komaidai lafiya" nace, "lafiya kalau Aunty, yajikin yaya Sadik" tace, "jiki Alhamdulillah za'ace Maryam, dan yanzuma haka suna hanyar zuwa saudiyya shida yaya da zannurain, tunda nandin kullum ciwon kara gaba yake." cike da tausayawa gami da jimantawa nace. "Allah ya bashi lafiya, yasa karshen wahalar kenan" Aunty tace, "Ameen Maryam, yau insha Allah zanje gidan gwaggonki saboda zirga_zirgar asibiti yasa bansamu najeba" "bakomai Aunty aikina kokarima sosai wlh" "to yaza'ayi Maryam girman kenan" "hakane ina aliya fa?" "Tanacan tana ta shiri kinsan yau zamu wuce kd" "kigaidamun da ita Aunty" "zataji insha Allah, ya angonki?" Murmushi nayi cikin jin kunya nace, "yananan kalau aunty" "amminku tacemun yau zaku koma bangarenku ko" "ehh Aunty" fada Aunty tashiga yiwa Maryam sosai, akan aure da yanda zata kula da mijinta da hikimomi da dabaru da kissa na zaman aure. mun dade muna waya da Aunty, dan munfi awa ɗaya, har aliya tafito itama Aunty tabata wayar muka gaisa sannan mukayi sallama, na koma falo. A kitchen na tarar da ammi da Aunty zuhura sunata aiki, nima tayasu nayi duk da ammi taso hanani amma nadage senayu........

*KANO*

Aunty bayan sungama waya da Maryam ta kira layin suhailat, suhailat tana zaune abun duniya duk ya isheta, ga zaman kadaici dan har yanzu tananan da bakin girman kanta tafi ƙarfin tayi hira da matar da tazo tana yi mata aiki. gashi mommy ta hanata fita, ta hanata hawa online tana ganin kiransu faruq amma bazata iya dagawaba saboda tsoron masifar mommy. seyanzu kuma cikin yake damunta, ta matsu mommy ta dawo aje a zubar dashi gashi kullum cikin ciwo take babu lafiya. tanasoma ta sanar da kamal maganar cikin. a hankali ta kai hannu ta dakko wayarta jin tana vibrate alamar shigowar kira, ajiyar zuciya ta sauke me karfi ganin sunan Aunty yana yawo akan screen ɗin wayar, hannunta har rawa yakeyi wajen picking dantasan zata samu information akan Mustapha. jinta daga Aunty tace, "suhailat!" cikin mamaki. "Na'am Aunty" "meyake faruwa ne, in'ankiraki bakya dagawa, wayar Aunty Atika kuma bata shiga" rasa abun cewa suhailat tayi,tayiwa Aunty shiru kawai. "Bakya jinane suhailat" "inajinki Aunty, mommy'n batananne tayi tafiya Niger" "Niger kuma? To ke kina ina?" "Ina gidanta" "kekadai?" "Eh, sekuma mai aiki da maigadi" shiru Aunty tayi tana girmama rashin hankali irinna mommy, banda haka yazakayi tafiya me nisa irin haka, kabar yarinya budurwa ita kadai a gida" numfasawa Aunty tayi tace, "kituromun address din gidan zanzo nadaukeki anjima" "toh Aunty" suhailat ta amsa cikin jindadi zata koma gida kusa da masoyinta. kafin tatambayi Aunty ina mustapha Aunty ta kashe wayarta. Duban aliya dake danna waya Aunty tayi cikin bacin rai tace, "taso muje" kallon Aunty aliya tayi ganin yanda ta sauya lokacin ɗaya tace. "Lafiya Aunty? Meyafaru?" "Bansaniba kinsan bansan yawan tambaya ko?" shiru aliya tayi ta dakko hijabinta suka fita. batasha wahalaba wajen gane gidan gwaggo da kwatancen da Maryam ta mata, suna ɗan tattambaya har sukazo gidan. A kofar gidan gwaggo Aunty tayi parking, bayan sun fito daga motar taga gidan a kulle, Aunty bataji dadiba ganin gidan a rufe. Aranta tace, "sun rafka sabani kenan da gwaggo" har zata cewa aliya su koma gida kawai, se kuma tayi shawarar shiga makota kobatayi nisaba, dan ita yanzu idan tabar Kaduna batasan ranar dawowartaba. Gidan umma suka shiga. Umma tana daki tayi baki yan ganin lefe, saleemat kuma tana kitchen tana girki.

Da sallama suka shiga, saleemat dake kitchen ta amsa musu, tsayawa sukayi a tsakar gida bayan kamar 2 minutes saleemat ta fito. Da fara'a dauke akan fuskarta tace, "sannunku da zuwa" duk da bata wayesuba. "Ku shigo tana ciki" Aunty tace, " barshi nanma yayi muna sauri ne" "to bari namata magana" saleemat ta fadi haka tana nufar dakin umma, sanar mata tayi tayi baƙi kuma sunce suna saurine. Biyo bayan saleemat umma tayi, da fara'a itama tayiwa su aunty sannu da zuwa, tare da kaisu falo. Bayan sun zauna sun gaisa umma tace. "Saidai banganekuba" murmushi Aunty tayi tace, "dama bakisanmu, nazo nanne makotanku naga gidan a kulle, shine nace bari nazo natambaya ko kwatancenne banganeba" umma tace, "gidanwa kuke nema" "gidan wata gwaggo wadda take rikon yarinya Maryam" umma na mamakin abunda yakawo wadannan kyawawan mutane, masu tattare da kamala gidan gwaggo, duk da sunsha hijabansu amma kallo ɗaya zakasamu kasan a daga gidan hutu suke, tace. "Eh, nanne kuwa bakuyi batan kaiba, saidai yanzu haka tana asibiti batada lafiya" "subhanallahi meyasameta" Aunty tatambaya cikin razani. atakaice umma ta musu bayani. Cikin jimantawa Aunty tace, "Allah Sarki, Allah yabata lafiya, yakiyaye gaba, sukuma wadanda sukayi Allah yatoni asirinsu" "Ameen" umma da aliya suka amsa a tare. "Tana wanne asibitin yanzu" Aunty ta tambaya. "Aminu Kano" daidai lokacin saleemat ta shigo dakin hannunta dauke da ruwa, godiya su Aunty suka mata, sannan suka kara gaisawa. Aunty ce tayiwa umma bayanin abunda ke tafe dasu atakaice. kafin umma tayi magana, saleemat cike da mamaki tace. "Maryam ditace take da aure yanzu?" "Ehh ita, kinsan iko na Ubangiji babu yadda baya canza al'amari, mu mutane muna namune Allah natasa, rabon aurennasune yakai Maryam aikatau gidan yaya" ganin yanda suka cika da mamaki, umma takara musu bayani sosai yanda zasu fuskanta karsu dauki abun da wata manufa. sun dan jima a gidan suna tattaunawa akan al'amarin seda sukayi sallar azahar sannan aunty suka tafi da saleemat asibiti dubo gwaggo. Lokacin dasukaje gwaggo tana duniyar bacci. wadda ke zaune a gurinta Aunty tayiwa bayaninsu kansu takuma tabbatar mata zasu dawo nan bada jimawaba harda Maryam din, seda Aunty ta cikasu da Alkhairi sannan suka musu sallama suka tafi. seda ta biya ta dauko suhailat bayan ta sallami matar dake zaune da ita, se bayan la'asar dai ta komo gidan daddy........

*JOS*

Girke_girke mukayi, munsha aiki gaskiya. duk wannan hidimar akan yarinyar gidan dazata dawone wadda kullum senaji ammi da Aunty zuhura, da mama sunyi zancenta wai ita umaimah. daga jin yadda suke zancenta suna matukar ji da ita. Bayan mungama aikin nayi wanka na shirya cikin wata doguwar riga kalar dark pink, anmata adon baki da wasu fulawoyi a gaban rigar. faka gashin kaina dayasha gyara nayi ya sauka har gadon bayana, tattareshi nayi na cusa a cikin ribbom sannan na dakko wata bakar hula nasaka. dankunne fashion masu kyau nasaka tare da agogo da zobe. kwalli kawai nasaka a idona se white lipstick danasawa lips dina. humra me dadin kamshi na shafa a jikina, se wani turare na fesawa me sanyi da dadin kamshi. seya hadu yabada wani kamshi me dadin gaske. Kallon kaina nayi a mudubin dakin ammi, nikaina nasan nayi kyau, fatata tayi haske sosai jikina kuma ya murmure, tona samu kwanciyar hankalin zuciya tunda na mallaki *heartbeat* dina.

Maryam tana daki tana shiryawa umaimah ta dawo gidan, cike da farin ciki ahalin gidan suka tarbeta kowa na murna da farincikin dawowarta musamman ammi. Itama anata bangaren umaimah cike take da murnar dawowarta gida tayi missing dinsu sosai musammanma amminta, harsuka gama tarbe_tarbenta Maryam tana daki batamasan sunayiba. lokacin da Maryam ta gama shirinta ta shigo umaimah tana daki tana wanka. kusa da ammi naje na zauna bayan na musu sannu da gida. wayar Aunty na dauka nafarayin game, ita kuma suna hira da Aunty zuhura da mama. Bayan kamar 20 minutes umaimah ta fito daga dakinta karaf idonta yasauka akan Maryam, da dunbin mamaki take kallonta, danbatasan da zaman Maryam a gidanba. Aranta tace, "to wannan yarinyarfa, kodai daga Saudiyyan da Ammi taje tataho da ita?" a wani bangaren na zuciyarta kuwa kishi ne da kyashi ya turniketa na ganin kyawun Maryam, ita macece dabatasan taga anfita kyau, sekuma gashi yau taga wadda tafita komai da komai a cikin gidansu. hade rai tayi cike da hassada ta dauke kallonta daga kan maryam, kusa da mama taje ta zauna tana wani narke mata ajiki tana zuba mata shagwaba. se'alokacin Maryam tasan da zuwanta falon, dago kai tayi ta kalleta, mamakine yacikata ganinta katuwace amma take wannan sangartar, kallo daya Maryam ta mata ta dauke kanta tacigaba da game dinta. Ammi ce ta dubi Maryam tace, "ɗiyata ga autatah fa, danace miki tayi tafiya Abuja. kakaro fara'a Maryam tayi cikin sanyin muryarta tace, "sannu yakike" fuskarta babu fara'a tace. "Lafiya kalau" bankara cemata komaiba itama haka, a gani ɗaya dana mata naji ni sam batamunba, ita kam umaimah bakin ciki ne yakara turniketa dataji Muryar Maryam me sanyi da zaki, "yarinyar komai ta hada ga kyau ga zakin murya, salon yanda take maganama kawai abun burgewane" umaimah ta fadi haka a ranta cikin kyashi. Daidai lokacin Saddam da Mustapha suka shigo falon bayan sunyi sallama, kasancewar yau juma'a da wuri suke dawowa daga kasuwa. kamar ance ta kalli kofa idanunta ya sauka akan Mustapha. wani mayen kallo tabi mustapha'n dashi without control her self, kallonsa take tamkar zata lashesa............✍️

Meson complete Whatsapp 08166674823

ABUNDA KA SHUKA

By* *zeey kumurya*

*5️⃣3️⃣*

*Bismillahirrahmanirrahim*

............. Umaimah har wani zunkuɗowa take daga kan kujera tana sakin baki da hanci tana binshi da mayen kallo, Saddam da zuhura tare da Maryam ne suka lura da kallon da take masan, ammi kuwa hankalinta yana kan ɗanta bata luraba. wani kishine yazo ya turnikemun zuciya irin me dacinnan, nibanmasan haka kishin yakeba dan bantaba jin na Aunty suhailat irin hakaba, yanda take kallonsa kamar idonta ze cire, tabe Bakina nayi nadauke kaina daga kallonta zuciyata namun kuna. Ita kuwa zuhura murmushi tayi dantasan za'ayi haka. Saddam ma murmushin yayi yakau da kansa daga kallon Umaimah. Mustapha seda yagaida amminsa da mama sannan ya zauna a kusa da Maryam, dan babu wani gurin zama da yay saura a falon senan, kuma shima ya lura da kallon da umaimah take masa. Lumshe idonsa yayi saboda kamshin Maryam daya shaka kamshin ya masa daɗi sosai. Ita kuwa Maryam bata rai tayi hartana turo dan karamin bakinta gaba batasaniba saboda zafin kishi. A hankali ya bude idanunnasa ya kalli Maryam ta gefen ido. Umaimah wadda takasa dauke idonta daga kansa sekara sakar baki da hanci take tana kallonsa, a ranta tace. "Wowww, wowww amma guy dinnan ya haɗu iya haɗuwa, yatafi da imanina, amma daga gani brother din yarinyarnanne" dan ita kama taga Maryam da Mustapha sun mata. danna wayar ammi kawai nake amma bansan menake dannawaba tunda yazauna a kusa dani nanemi nutsuwata na rasa, kawai daurewa nake ga kamshinsa gaba-daya ya cikani.

kara kallonta nayi naga har lokacin bata dauke idonta daga kansaba, sonake na kalleshi naga ko shima ita yake kallo amma nakasa. Mamace tatabo umaimah tana cemata. "Ke! Mekike kallo hakane?" Ajiyar zuciya umaimah ta saki ta juyo ta kalli mama a hankali tace, "mama suwaye wadannan wai? daga ina suke?" mama tace. "Bakin amminki ne" umaimah na far da ido tace, "amma suna da kyau sosai kamar ammin, musammanma namijin yafi kyau ga muryarsa me dadi" cikin tsokana mama tace, "yau wacce rana umaimah ta yabi wani ɗa namiji arayuwarta" tana satar kallon Mustapha tace, "mama ai yakai a yabeshinne, wlh bantaba ganin namijin daya mun kyau kamarshifa, guy ɗinfa yayi mama" murmushi kawai mama tayi batace komaiba. Maida kallonta tayi ga yayanta tace. "Yaya Saddam ina yini" "lafiya kalau sisina, aitunda nashigo nakeson na miki magana naga kunata sirri da mama senace bari najira ku gama." Dariya tayi tace, "kasan tsakanina da tsohuwarnan da amana" "hakane yar lelen mama, kindawo lafiya" "lafiya kalau yayana" maida kallonta tayi ga Mustapha tana wani fari a kokarinta nata dauki hankalinsa tace, "ina yini" sarai yasan dashi take amma ya mata banza tamkar bejiba. Ammice tace dashi, "NOOR ana gaisheka" batare daya kalletaba yace. "Lafiya" atakaice. hira suka shiga yi dukansu amma banda Maryam da Mustapha dasukayi dif tamkar basa falon, umaimah se wani iyayi take idan zatayi magana tana wani fari da ido, wanda takeyi danshi bemasan tana yiba. Bayan sunyi sallar la'asar ammi zata kaiwa Mustapha abinci, umaimah ta karba ta kai masa har daki tana wani yaya NOOR, gabadaya tabi ta susuce dataga mustapha. Shiko mustapha haka kawai yaji yarinyar bata masaba dan daga ganinta zatayi rawar kai, data kawo masa abincinma hade ransa yayi, a niyyar umaimah ta zauna suyi hira dashi amma ganin ba fuska seta fice badan tasoba. Yana gama cin abincin ya fice daga gidan.

Misalin ƙarfe biyar da yan'mintuna bayan nagama haɗa komai nawa kamar yadda ammi tace, ina zaune adakinta akan gado nikadai, ammi da Aunty zuhura suna part dinmu suna kara gyarawa. Ammi tace ta shigo dakin da sallama, amsa mata nayi cikin girmamawa. Ammi tana kallona tace, "yawwa Maryam kingama haɗa komai, har su turarukan da mayukan?" cikin sanyin murya kamar yadda jikinama yake a sanyaye nace, "ehh ammi nagama" wayarta ta mikomun tana fadin, "yanzu aka kirani da wata number wai ana nemanki" nace "ba Aunty bace kuma" ammi tace, "ehh ba ita bace wannan ma kamar yarinya" cikin mamaki na karbi wayar na duba number senaga kamar nasan number'n. danna kira nayi nakara a kunnena. Ammi ta dauki jakar da Maryam tahada kaya tafice. seda wayar takusa katsewa sannan aka daga da sallama. wayyo daɗi, wani farinciki naji ya lullubeni danaji Muryar sahibata kawar asali, kawar rufin asiri saleemat. cikin ɗoki nace, "saleemat!" itama tana dariyar jindadi tace, "na'am kawata nayi kewarki sosai wlh" "hmmm, kedai bari saleemat dazunnan nagama zancenki acikin raina, ya gida yasu umma da baba da kowa da kowa" "duk lafiya kalau Maryam" "Masha Allah, ina Habibi Adam?" "Habibi yananan kalau, ke ankawo lefenafa tun waccen satin" "kai haba, shine ba labari" "wlh Maryam nakai wata ina neman wayarki bata shiga" "wayar ta fadine, wai dagaske kike ankawo lefennaki saleemat" "dagaske mana, zan miki wasane dakina chat ma dana turo miki kingani" "kaii, amma naji dadi kawata Allah yasanya Alkhairi, Allah yasa damu za'ayi." "Ameen" hira muka shigayi irinta amininan juna, harna tambayeta inata samu numbar ammi tacemun aunty ce ta bata. muna cikin hirarne nace mata, "ina gwaggo kuwa saleemat? Aunty tacemun idan tazo zata hadani da ita inata jiranta naji shiru" saleemat tace, "gwaggo tananan lafiya kalau" (dayake Aunty tarokesu karsu sanar da Maryam ciwon gwaggon dantasan halinta tada hankalinta zatayi tayita koke_koke, tafison idan tazo kafin azumi seta taho da ita ta duba gwaggon.) nace, "kigaidamun da ita sosai, kikarbomun number'n tama kituromun nakirata" "toh" kawai saleemat tace, ta kawar da zancen da fadin. "Yanaji wai muryarki kasa_kasa, kodai angonnaki ya tumurmushekine a gado" ta karasa zancen tana dariya. Cikin jin haushi nace. "Bansaniba yar iska, ni kaiwa umma wayar mugaisa" dariya tacigaba dayi harta kaiwa umma wayar, mungaisa sosai da umma na mata Allah yasanya Alkhairin lefen saleemat. Umma tamun yar nasiha akan aure na mata godiya mukayi sallama. banbari saleemat ta karbi wayarba na kashe dannasan tsokanata zata cigaba dayi. Haka kawai naji ina hawaye, dama jikina duk a sanyaye yake yau. goge hawayena nayi da sauri jin tafiya a falo, dan kofar dakin abude take. Ammi ce kuwa ta shigo dakin, bata lura da halin da Maryam take cikiba dan tayi kokarin boye damuwarta. Ammi tace, "Maryam kungama wayar" nace "ehh, wata kawatacema ashe Aunty ce ta bata number'n ki" tace. "ayya, kema Yakamata ace kina da waya a hannunki, bari NOOR yashigo sena masa zancen yasiyo miki" ban iya cewa mata komaiba dan kuka ze iya kufcemun" zama ammi tayi akan gado tana fadin "washh" araina nace. "Ai dole kigaji" saboda ammi kwata_kwata bata zama, koyaushe cikin dawainiya take damu nida yaya Mustapha, har tausayi take bani. "Sannu ammi" na furta a hankali. "Yawwa Maryam" mikewa nayi nace "ko in miki tausane" muryar ammi na nuni da gajiya tace, "dakuwa kin kyauta ɗiyata" kwanciya tayi akan gado nikuma nashiga yimata tausar............

*KANO*

Suhailat tunda suka dawo gida taketa baza ido taga ta inda zata ga Mustapha, amma ko alamarsa bata ganiba. kasa hakura tayi taje har part dinsa, amma setaga a kulle. Da hanzarinta ta dawo bako kunya tatambayi aunty. Aunty kawai tace mata yayi tafiya ne. bataji dadiba kuma bataso hakaba, ta koma daki ta ɗauki wayarta taita kiransa amma wayar bata shiga, haka ta hakura zuciyarta babu daɗi kokaɗan. Aunty sunyi waya dasu daddy sun isa lafiya. wajen karfe biyar tasa suhailat ta hada kayanta danda ita zata wuce Kaduna, suhailat bata iya hada kayanba saboda batajin dadin jikinta. Se aliyace tana kunkuni ta hada mata, bisa tursasawar Aunty. Aunty kallon suhailat kawai take tunda ta dakkota yanda gabadaya ta zabge ta rame, se uban fari kamar zabiya. gashi sebin tiles take tana kwanciya, Aunty dai takasa hakuri tatambayeta meke damunta. setace mata wai malaria ce. Aunty baiwar Allah babu tunanin komai aranta seta yarda ta mata fatan samun sauƙi.......

*JOS*

Duk da part din dazamu zauna yana jikin na ammine,dan amminma tacemun anan ta zauna kafin mamansu Saddam ta rasu, seda ta rasu ta dawo inda take yanzu. Amma wlh jinake kamar wani garin za'akaini me nisa gashi zuciyata cike take da fargabar yadda zamannamu ze kasance, nasan dai ni ina matukar sonsa amma shi nasan baya sona. Idannatuna hakan se inji duk zuciyata ta karaya jikina yayi zanyi, musamman ma yanda yake nuna halin ko'in kula akaina. dauriya kawai nakeyi ina boye damuwata. Zuwa yanzu umaimah tasan waye mustapha a gurin ammi, kuma tasan Maryam matarsa ce, dan part din mama taje ta matsa mata da tambaya akan waye mustapha, seda mama tabata labari ta samu sa'ida. Tsana da haushin Maryam ne suka cika mata zuciya ganin ta rigata mallakar irin mijin datake mafarkin samu, amma dadinta daya dayakasance gida ɗaya zasu zauna, ita kuwa zatasan yanda zatayi tajanyo hankalinshi yadawo kanta, zatayi duk yanda zatayi ganin ta kwaceshi daga hannun wannan karamar yarinyar wato Maryam.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull