Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 36
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 36: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 36. Bayan sallar magriba ammi tasani nayi wanka na shirya…
3,340 words
Bayan sallar magriba ammi tasani nayi wanka na shirya cikin wata hadaddiyar doguwar riga me kamar alkyabba yanayin jikinta. nayi kyau sosai acikinta, nafeshe jikina da daɗaɗan turaruka masu sanyi kamshi. Bayan nagama shiryawa ammi tamun faɗa akan zamantakewar aure, mama ma, tamun. nidai hawaye kawai nakeyi ina saurarensu.
Bayan sallar isha'i ammi ta kama hannuna ita da mama suka rakani har inda yake a matsayin dakina ta zaunar dani akan gado. nasha kuka sosai bayan sun tafi. Daga baya kuma na rarrashi kaina nadena kukan. A hankali na tashi nakarewa dakin kallo yayimun kyau sosai sai kamshin turaren wuta da sabon fenti yakeyi. kayana su ammi sun jeremun su a cikin cover, su turaruka da mayuka duk anjeremun akan mudubi, komaidai need abun gwanin ban sha'awa. Falo na fito shima yayi kyau sosai babu wani tarkace, yasha labulaye masu kyau. daga falo kitchen nanufa, shima yaji kaya komai na amfani akwaishi. dakina na koma bayan nagama kalle_kallennawa, dakinsane kawai banyi gigin shigaba. ina mamakin wai wannan gidanane da kayan cikinsa komai nawane, nida bantaba zaton zansami koda rabin wannan ba. Zama nayi a bakin gado nashiga sake_sake. Ƙarfe goma da yan mintuna ya shigo part dinnasu, hannunsa dauke da ledoji manya. Kitchen ya nufa ya ajiye kajin daya shigo dasu kamar yadda ammi tace yasiyo. Shima seda yagama karewa gidan kallo, shima gidan yamasa kyau sosai, kafin yashiga daki seda ya saita kayan kallo danshi mutum ne meson kallon news da kallon ball. Ina zaune tsuru naji shigowarshi ajiyar zuciya nasauke cikin jindadi,dandama a tsororace nake da zaman nikadai, nandaima da wutar NEPA ne. Dakinshi ya shiga ya ajiye sauran kayan dayashigo dasu, sabulayene da mayuka da turaruka. Nashi ya kwasa ya jera a gaban madubin dakin. sannan dauki sabulu da saban towel din daya shigo dasu ya nufi toilet. bayan kusan 30 minutes yafito yazira jallabiya yafashe jikinshi da turaruka ya kwanta. Lumshe idansa yayi yana tunanin wannan aure da daddy yamasa. shiyanzu besan yazeyi da yarinyar mutaneba, tunda bashi da lafiyar daze bata hakkinta na aure akansa, kodama yanada lafiyar baya tunanin waccan karamar yarinyar zata iya dashi, shifa yaraina Maryam a matsayin matarsa ganinta yake yar karamar yarinya, dandai baze iya bijirewa daddy bane da....... wayarsace ta katse masa tunaninsa ta hanyar yin vibrate. Ahankali ya bude idansa ya tashi ya dakkota daga kan madubi. MY UNCLE yagani yana yawo akan screen ɗin wayar. kanin ammi ne dayake saudiyya kullum sesunyi waya dashi, dagawa yayi sukasha hira har yaransa yabawa suka gaisa sannan sukayi sallama. Nasihar da daddy yamasa ranar da zasu koma kano itace ta dawo masa kwanyarsa tamkar yanzu yake masa ita. "Mustapha, karike yarinyarnan amana kaga marainiyace kuma bata da wani gata sena Allah, idan ka cutar da ita Allah baze barkaba. Kuma yazama dole kakula da cinta da shanta da kuma lafiyarta." Mikewa yayi yaɗauki ledar daya shigo da ita, bisa umarnin da zuciyarsa ta basa akan yakamata yaje yaga lafiyarta kafin ya kwanta, tunda yanzu amanace ita a hannunsa, da wannan tunanin ya nufi dakinta. Maryam dataga zaman ya isheta gashi ko digon bacci a idonta, seta tashi dama da alwalarta ta shimfida sabuwar daddumarta ta tada sallah.............✍️ COMMENTS PHAAA 🙄 MESON COMPLETE WHATSAPP 08166674823
ABUNDA KA SHUKA
*By* *Zeey kumurya*
*5️⃣4️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
............ Ahankali ya tura kofar dakin yajita a bude, bakinsa dauke da sallama ya shiga dakin. wata irin faduwar gabace ta ziyarceni duk da Sallah nake jin shigowartasa. kamshinsane yatabbatarmun da shine, gaba-daya jinayi na diririce, narasama menake karantowa a cikin sallar saboda tsabar fargaba. shiko mustapha ganin sallah Maryam take, seya ajiye ledar hannunsa ya juya ya fice. Ajiyar zuciya nasauke jin yafita na sallame sallar amma banko motsaba daga inda nake, duk da yafitan amma bandawo cikin nutsuwa taba.gani nake kamar ina juyawa zanganshi yadawo cikin dakin, kusan 16 minutes sannan na daure na tashi daga kan dardumar har lokacin daddadan kamshinsa bebar dakinba. hijabin jikina na cire na ajiye, leda nagani dabansan da itaba a dakin. cikin mamaki na dakkota nafara fito da kayan dake ciki, sabulayen wanka ne dana wanki,se MacLean da sabbin burush guda biyu da mayukan shafawa harda sosan wanka me kyau acikin ledarsa araina nace, "gaskiya wannan ya iya siyayya, komai dayasan zan bukata seda yasiyo." mayar da kayan nayi cikin ledar bayan na dauki abunda zan bukata a yanzu na ajiye a gefen gado. Toilet na fada nayi wanka, ina fitowa na zira rigar bacci nafada kan gado dan wani irin bacci naji inaji lokaci daya......
Washegari, bayan nayi sallar asuba ban koma bacciba, Alqur'ani me girma na dakko na karanta izifi uku nayi narufe na ajiye. Addu'a nayi sosai akan rayuwata, nayi mana addu'a sosai akan aurennan namu da hearbeat senaji duk wani tsoro da fargaba ya kaumun daga zuciya. Ƙarfe bakwai da yan mintuna nafito daga dakina domin na gyara gidan. babu wani datti yananan fess dinsa. kujerun na karkade nashare dan dattin dabaza'arasaba a falon, nagoge dining da tv. Kitchen na shiga shima babu wani abun datti a cikinsa, leda na hango akan karamar freezer dake kitchen din, da dan mamaki nakarasa nahau dubawa, dan jiya dana shigo babu da ita. kaza nagani a ciki har uku, se zuba kamshi takeyi. shiru nayi cikin karayar zuci, araina nace. "Kazar amarci dakowanne ango yake siyowa matarsa ya lallabata yabata taci, amma ni nawa angon saboda baya sona seyazo yadireta a kitchen" kwallace ta cikamun idona, maida ita nayi yanda naganta nafito daga kitchen din zuciyata namun kuna. "Yaushe bawan Allah'n nan zesoni? kamar yadda aliya tace, anya kuwa zanga wannan ranar ba yaudarar kaina nakeba kuwa? abun da kamar wuya" natambayi kaina hawaye na zubomun daga idona. Knocking din kofar falon akayi yasani saurin goge hawayennawa, kofar na nufa na bude batare da tambayar wayeba. Umaimah ce tsaye hannunta dauke da basket da kayan breakfast a ciki, ammi ce dazata kawo da kanta umaimah tace tabata takai musu, dan a zatonta mustapha ne ze bude kofar amma setaga Maryam. bata rai tayi sosai ta wani hade fuska, ko sannun da Maryam ta mata bata amsaba. matsa mata nayi ta wuce ciki nima nakoma na zauna akan kujera bankara kallon koda inda takeba harta fice danna lura yar rainin hankalice. tana fita na tashi na kulle kofar, inajin yunwa gaskiya dan tun jiya da rana rabona da abinci. Flates na dakko da cups nadibi abinda zanci nanufi dakina, Allah sarki ammi nasan wannan duk aikintane. koda nagamaci banfitoba wanka nayi na kwanta ina tunanin yanda zamanmu zecigaba dashi. seda goma ta wuce nafito Falour'n dauke da kwanukan danayi amfani dasu, nasan zuwa yanzu kam yafita. kan dinning na kalla naga shima kwanukan dayayi amfani dasu a gurin, da alamama bejima da fitaba danga kamshin turarensanan a falon. Tattara kwanukan nayi duka nakai kitchen na wanke na kara kimtsa wasu abubuwan. sannan naje na gaida ammi cike da jin kunyarta, a tunaninta mustapha yananan befitaba, muna gama gaisawa tace inkoma gurin mijina. Ƙarfe 12 na rana aka kawo mana wuta, dama nagaji da zama ba abunyi sena kunna kallo..... Yaran makota sun shigomun yau sosai harda yanmata kamar ni, dan su mama duk sun sanar amarya tatare. naji dadi kuwa sosai dama kewa ta isheni har bayan la'asar sannan suka tafi. kara gyara gidan nayi naturareshi da turaren wuta me dadi, Aunty zuhurace ta aikomun dashi da yawa a cikin bokiti. se kusan magriba mustapha yadawo gidan, ina zaune a falo ya shigo. Lumshe idonsa yayi saboda wani ni'imtaccen kamshi dayaji falon yanayi. shikam yanason kamshi a rayuwarsa yana kuma san tsafta. A hankali ya kalli inda yaji muryatarta data amsa masa sallamar dayayi, danbe zaci tana falonba. becemun komaiba yawuce dakinshi, ni kuma na bishi da kallo zuciyata cike da shaukinsa. Lumshe idona nayi nafada duniyar tunani, har aka kira sallar magriba inanan zaune inda yabarni. da kyar na yunkura na shiga daki nayi alwala danyin sallah. Da daddare yaya sadam yazo har part dinmu yace inshirya da safe zamuje amun passport za'akai makarantar dazanyi NECO. Wayyo daɗi kamar ze kasheni dan Murna dan da har na fiddarai da karatun......
*2 weeks later*
Munje school din dazanyi exam nida yaya Saddam angamamun komai na exam din. goma ga azumi zamu fara exam din insha Allah. Zamanmu da *heartbeat* jiya ie yau babu abunda yasauya, tsakanina dashi gaisuwa ce, ko abinci bana zuba masa da kansa yake zubawa yaci. Amma yanzu kullum kafin yafita seya duba yanda natashi kafin yayi baccima seyazo ya Dubani. bantaba shiga dakinsaba, koda da sunan gyara danbanga wannan fuskarba. Kullum yana fita ina gama ayyukana zantafi part din ammi muyita hira da Aunty zuhura. Umaimah kuwa bama magana kwata_,kwata, da ina gaisheta naga bata amsawa nadena. Inta ganni setayi ta hararata tana bata rai, niko da ita da banza duk ɗaya na daukesu gurina. duk abunda ke faruwa tsakanin Maryam da umaimah zuhura tana hankalce dasu kuma tasan Umaimah son mustapha takeyi. shima Mustapha'n zuwa yanzu yagane inda umaimah ta dosa akansa. yana zuwa part din ammi zata fara shishshige masa ta kawo masa ruwa da lemo, tana iyayi tana fadin. "Yaya NOOR inkawo maka abinci, kokuma yaya NOOR mezakaci indafa maka" haka zataita masa iyayi da neman suna, shiko yamata banza abunka da miskilin mutum, gashi yarinyar bata burgeshi kokadan. Muna waya da Aunty da saleemat akai akai a wayar ammi, dan har yau besaimun wayarba, yace sena gama exam da ammi ta kuma masa maganar.
Yau ma kamar kullum Muna zaune a falon ammi, yau nida itane kadai Aunty zuhura taje gidansu ita da umaimah ta rakata, munata hira da ammi akan azumi daya rage saura kwana uku. wayar ammi ce ta kawo haske alamar kira, dauka tayi taduba. mikomun tayi tana fadin, "gashi ke ake nema ɗiyata" tasowa nayi na karba nadaga. Saleemat ce, tace. "hello mairota" ina murmushi nace, "na'am kawata yakike" "lafiya kalau, naje asibitine gurin gwaggo tace nakira mata ke" cikin tsananin mamaki nace, "gwaggo kuma bakincemun tayi tafiyaba?" "a'a batafiya tayiba Maryam"..... Nan saleemat tabawa Maryam labarin abunda yafaru da gwaggo. Hawaye shabe_shabe a fuskata nace, "yanzu saleemat kin kyautamun kenan, ace kamar gwaggo bata da lafiya amma kiƙi fadamun seyanzu, idan da mutuwa tayifa?" cikin kwantar da murya saleemat takeson ta fahimtar da Maryam dalilinsu nayin hakan, amma Maryam taki saurararta se kuka take. Ammi dake ta tambayar Maryam a rude ganin kukan datake ta kwace wayar tunda Maryam din taki mata bayani se kuka. Tambayar saleemat tayi, saleemat tayiwa ammi bayanin komai harda boyewar da Aunty tace suyiwa Maryam. Ammi tace. "Ayya Allah yabata lafiya, amma meyasa Hajiya sauda tayi haka, aida tabari anfada semuje harmuma mudubota, amma yanzu bari na lallami Maryam ɗin, zankiraki anjima seki kaiwa gwaggonnata wayar" salimat ta amsa mata cikin girmamawa sannan ta kashe wayar. da kyar ammi ta shawo kan Maryam tayi shiru ta dena kukan. Kiran saleemat ammi tayi ita kuma ta kaiwa gwaggo. gwaggo jiki yayi sauki sosai tunda yanzu har zama tanayi da kanta, sedaifa bata magana ta zama shiru_shiru, dantafara saduda da duniyar, tasan alhakalin Maryam ne yafara kamata. jiya da Aunty takara dawowa dubata take fada mata Maryam tayi aure, da kuma yanda auren yakasance. Gwaggo seta sawa abun albarka, da dane kuwa da tuni tahau tijara tana masifar ita bazata yardaba sai'andawo mata da jikarta. Ta waya Aunty ta hada daddy da gwaggo, ya mata yajiki yakuma bata hakuri akan auran daya yiwa Maryam batare da saninsu su dangintaba. Gwaggo tace bakomai ahakanma sun gode, daddy besan dadine yacikataba na wayar datayi dashiba. se washe haƙora take kamar ba mara lafiyaba ita tayi waya da alhaji *mai nasara* Aunty ta cika gwaggo da kudi da kayan masarufi masu yawa kafin su tafi, ita da megidanta sukazo. Seda ammi suka gaisa da gwaggo sannan tabawa Maryam wayar. "Gwaggo!" Maryam ta fada cikin zumudi. cikin karaya da nadama gwaggo tace, "na'am Maryama" "gwaggo yajikinnaki?" "Dasauki Maryam" "sauki sosai, wlh gwaggo bansan baki da lafiyaba" Maryam ta fadi haka tana hawaye. "Nasani Maryam, nasan dakin sani datuni kinzo dubani, aike yarinyar arziki ce yar albarka" tsananin mamaki ne yacika Maryam dajin abunda gwaggo tace, kodai mafarki take kokuma tsananin ciwo ne yasa gwaggo saduda, har take kiranta da yar albarka, abunda bata taɓa ji gwaggon ta faɗa mataba tunda suke. Numfashi Maryam tasauke tace, "gwaggo zanzo kafin azumi insha Allah, nadubaki." "A'a Maryama kizauna tunda kinga ba gari ɗaya mukeba, bayan sallah in Allah yakaimu sekizo, tunda naji sauki yanzu" dagewa Maryam tayi setazo amma gwaggo tahanata, tace ta bari ko cikin azumi ne tazo. Ammi ma ta roki gwaggo suzo koda a gobene, amma gwaggo tace suyi zamansu. Suna gama wayar ammi ta dubi Maryam tace, "ki kwantar da hankalinki gobe insha Allahu zamu sedai kawai su ganmu kwatsam." Daɗine yacika Maryam gobe zata je taga gwaggon ta da saleemat dinta,kuma hankalinta ya kwanta dasukayi waya da gwaggo taji jikinnata da sauki, dan da saleemat ta fada mata ta dauka gwaggo magashiyyan take a kwance. domin Maryam bazataso gwaggo tamutuba, dan ita kadai gareta yar uwa ta jini sosai, shinema abunda yasata kuka dan idan gwaggo ta mutu bata da wani sauran dangi najiki dazata bugi kirji ta nuna. Da yamma bayan nagama aikina nadawo part din ammi. Kitso zatamun danbansan zuwa Kano kaina babu kitso, namanta rabon danayi kitso ma. Manya_manya nace ammi tamun dan tundaga tazar gashin nafara jin zafi. Aiko gaba-daya kannawa yaɗaure se zafi yakemun saboda nadade ba kitso. se tauna lips nake ina runtse ido. kafin magriba muka gama na mata godiya sosai nakoma part dinmu. Ina zuwa dakina na lambace mai akan kozanji sauƙin radadin dakan yakemun amma a banza. falo na dawo na zauna a kasa, ko dankwali bandauraba balle nasa ribbom nasaki jelar kitson har gadon bayana, dama shukune kitson. dafe kan nayi saboda ciwon dayakemun, nayi dana sanin yin kitsonnan ni banma taɓa yin kitso yamun zafi kamar hakaba. Da sallama dauke a bakinshi ya shigo falon, tsayawa yayi cak yana kallon gashin kan Maryam cikin mamaki. jin kamshin turarensa yasani dago da kaina dasauri dan bansan yashigoba, Banji sallamarsaba. kasa nayi da kaina gabana na faduwa ganin ya nufo inda nake. Fuskarsa a daure yace, "waya miki kitsonnan?" Kaina nakasa bandagoba nace, "ammi ce" "ammi?" Ya maimaita da alamun mamaki. gyada masa kai nayi. Yana kallon gashin yace, "ammin ce ta miki kitso da attachment?" dasauri nadago na kallesa. "Attachment kuma?" Namaimaita araina. A hankali nace, "A'a ba attachment bane" harararta yayi ganin ta raina masa hankali duk wannan tulin gashin tana nufin tace masa gashintane. zama yayi akan kujerar dake fuskantar ta, yadora kafa ɗaya kan ɗaya. Babu wasa a fuskarsa yace. "Dakkomun abun da ake kitso dashi" kallonsa nayi nace, "wanne abun kitson?" Banza yamata bekuma mata maganaba, shi bayason ayita jan magana shiyasa bekuma tambayarta me aka kara mata a kitsonba, amma yasan mezeyi yagane da kansa, kuma idan har karya ta masa seyayi maganinta, danshi baya kaunar musu. toni bangane meyake nufiba, "abun da ake kitso? Kibiya kenan yake nufi watakila" nafadi haka araina. batare da tunanin komaiba na mike nashiga daki nadakko masa kibiyar bayan nasaka dankwalina na rufe kaina. tsugunnawa nayi sannan na mika masa kibiyar, ina kokarin tashi kawai naji yasa hannunshi ya mikar dani tare da jawoni nafada jikinsa.........✍️ Comments Meson complete Whatsapp 08166674823
ABUNDA KA SHUKA
*zeey kumurya
*5️⃣5️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
...........Wata irin bugawa zuciyata tayi da ƙarfi lokacin dana jini ajikinsa batare da zato ko tsammaninaba. shiko mustapha lumshe idonsa yayi cikin wani irin yanayi dabeyi zatoba, zuciyarsace ta hau bugawa da sauri_sauri. kara firgicewa nayi ganin yana gyaramun kwanciyata akirjinshi, gaba-daya na tsorata jikina ya kama rawa saboda bansan mezemunba. runtse idona nayi kawai ina kara shigewa jikinsa batare danasaniba, ajiyar zuciya nahau saukewa ahankali cikin wani irin yanayi, luf nayi ajikinsa ina shaƙar daddaɗan kamshinsa me saukarmun da nutsuwa,wani dumin ni'ima naji yana ratsa jikina, har wani bacci_ bacci me daɗi naji yana fizgata. shiko mustapha kasa aiwatar da komai yayi, wata irin kasalace take baibaye dukkan gaban jikinsa. A hankali ya buɗe lumshashshun idanunsa, cikin matukar dauriya da yanayin daya tsinci kanshi yakai hannunsa dake ɗan rawa yacire ɗankwalin kan Maryam, jedar kitson data tusa a cikin ɗankwalin ta zubo a gadon bayanta. kansa yadora akannata yana shaƙar kamshin kanta daya matuƙar yimasa daɗi, batare dayasan yayi hakanba. A haka yakama jelar kitson ƙeya guda ɗaya yafara warwareshi da kibiya, be iya tsifarba hakan yasa se cisgar mata gashi yake, amma Maryam ko zafi daya batajiba batamasan meyakeba tatafi duniyar shauki, sekara manne masa take tamkar wata mage, da alama ta manta ajikin wanda take. Yayi 12 minutes kafin yagama tsefe kitson guda ɗaya jal, amma dakyar yakarasa saboda baƙon yanayin dayake kara dabaibayeshi mara misaltuwa. A hankali ya ajiye kibiyar akan kujera Zuciyarshi cike da tsananin mamakin ganin tabbas gashintane bata masa karyaba. Yaga mata masu gashi da yawa amma be taɓa ganin kamar na Maryam akan Hausa Fulaninmuba, yasan aunty da mommy da suhailat suna da gashi sosai amma be kama kafar na Maryam ba, kallon kannata kawai yake cike da shauki, shi mutum ne meson yaga gashi akan mace, yana kaunar yaga yana shafashi. A hankali yakai hannunsa yana shafa kitsonnata tamkar me mata tafiyar tsutsa. Wata nannauyar ajiyar zuciya Maryam ta sauke tana kara gyara kwanciyarta ajikinsa. Da sauri ya dago da fuskarta daga kirjinsa yabi fuskarta kallo. Bacci takeyi hankalinta kwance, numfashin datake saukewa a hankali ne, yasa yagane bacci takeyi. Kurawa kyakkyawar fuskarta ido yayi zuciyarsa na bugawa. Cikakkiyar girarta da kwantaccen gashin dake goshinta zuwa gefen kunnenta gami da zara_zaran eyelashes dinta, yasa isa shaida idan ka kalleta kasan zatayi gashi. Kara maida kanta tayi cikin jikinshi tana kara kankameshi. Wata irin kasalace take kara baibayeshi, tsigar jikinsa gaba-daya tatashi. Lumshe idonsa yayi cikin rashin sanin abunyi, yanaji ana kwada kiran Sallah amma yakasa motsa koda danyatsansane. "To meyake shirin faruwa dashi haka ne?" Yatambayi kansa, betaba tsintar kansa a irin wannan yanayinba seyau, yanayine me wuyar fassaruwa ga zuciyarsa dake ta aikin bugawa, kansane yaji yasara masa. tsawon 5 minutes suna zaune a haka, ita Maryam baccinta takeyi cikin kwanciyar hankali, baccin da bata masan sanda yadauketaba. Dakyar ya iya bude idanunsa dasuka masa matukar nauyi, tattaro duk wata dauriyarsa yayi yafara ƙoƙarin rabata da jikinsa a hankali dankarta tashi. Daukarta yayi cak kamar wata baby ya kwantar da ita akan doguwar kujera. A hankali yake kokarin zare hannunsa daga jikinta cikin lallabawa dan karta farka. Mikewa yayi ya kalleta na wasu sakanni, sannan ya fara tafiya yanufi dakinshi jikinshi a matukar sanyaye. kafin yayi alwala har an tada sallah anyi raka'a ɗaya. dakyar yake iya ɗaga kafafunshi yake tafiya. duk da yayi alwala amma yanayin dayakeji bebarshiba, bayan kasala har wani yammmm...yakeji ajikinsa,Tsigar jikinsa har lokacin batabar tashi ba. a haka dai yadaure yaje masallacin yayi Sallah. koda yadawo gidan part din ammi yawuce kamar yadda yasaba kullum, babu kowa a parlon dakinta yashiga bakinsa dauke da sallama. Ammi tana zaune akan darduma tana lazimi ya shigo. zama yayi a gefen gado tare da dafe kansa dayake cigaba da sara masa. seda ammi ta shafa sannan ta juyo ta dubesa tare da fadin, "NOOR an dawo?" Dago kansa yayi cikin dauriya da abunda yakeji yace. "Ehh ammi ya gida" bata amsa masaba se kafeshi datayi da ido kafin tace. "NOOR lafiya kake kuwa naganka wani iri?" "Lafiya kalau ammi" yabata amsa yana zaro wayarsa daga aljihunsa dan karta kuma masa wata tambayar. kallonsa ammi take sosai kamar meson tagano wani abu a tattare dashi, taga kamar wani abu nadamunsa amma tasan halinsa tunda yace mata babu komai koma da akwai ɗin ba fada mata zeyiba. Nisawa tayi tace, "Maryam ta faɗa maka gobe zamu kano ko?" Da sauri yadago yadubi ammi so surprise yace, "Kano kuma?'' ammi tace "ehh, zamuje dubo gwaggon tane bata da lafiya"...ammi tabashi labarin abunda yasamu gwaggo. Cikin tausayawa yace, "Ayya, Allah yabata lafiya" "Ameen" "amma a goben zaku dawo ko?" "A'a sedai jibi" "ok, Allah yakaimu lafiya." wata hirar suka cigaba duk da shi daurewa kawai yake dan kar ammi tagane wani abu, amma shikadai yasan meyakeji ajikinsa da zuciyarsa......