Kenza eBookz

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 37

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 37

Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 37: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 37. Maryam bayan fitarsa ba jimawa ta fara mutsu_mutsu tana…

2,915 words

Maryam bayan fitarsa ba jimawa ta fara mutsu_mutsu tana rarumar jikin kujera kozataji shi, gaba-daya baccin yadena mata daɗi se juyi take. A hankali ta buɗe idanta tunda baccin yagagara daɗi. da sauri ta tashi zaune kamar wadda aka tsikara. sosai mamaki yakamata "bacci da magarubarnan?" Tatambayi kanta, tana dafe kanta. tunaninma ya akai tayi baccin tahauyi. "Ajikinshi bacci yadaukeni kenan kokuma ya?" Maryam ta fadi haka a fili tana waro duka idonta waje. shafa kanta tayi taji babu dan kwali. mikewa tsaye tayi ta dauki dankwalinta da kibiyar dake kan kujera ta nufi dakinta zuciyarta cike da tunanika kala_kala, abunda yafi daure mata kai baccin datayi batasan sanda yadauketaba.... Bayan ta idar da sallar magriba ta fara haɗa kayan dazasuyi tafiya gobe, ita da ammi zata bartama kwana biyu zatayi a Kano, tanason ganin Aunty ma, amma Aunty tace mata bazata samu zuwaba kafin azumi kamar yadda tace, abubuwa sun mata yawa sedai cikin sallah insha Allahu zatazo..... Maryam anayin sallar isha'i tadebi abincinta tayi daki bayan ta jera masa nasa akan dinning, da wuri takeso tayi bacci danta matsu gobe tayi, kuma batason ta kara hada ido dashi danwata irin kunyarsace taji ta lullubeta. Mustapha kam daren yau gaba-daya bayajin daɗin jikinshi, kamshin jikin Maryam dana kantane kawai yake masa gizo a hanci, koda ya kwanta bacci daya rufe idansa kyakkyawar fuskarta kawai yake hangowa lokacin datana bacci ajikinshi, da kyar yasamu bacci yadaukeshi........

*KADUNA*

Aunty tun ranar data dakko suhailat ta fuskanci wani abu a game da yanayin ciwon suhailat ɗin domin bata iyacin komai, sedai taitashan drinks da kayan zaki su take wuni tana sha, idan kuwa Aunty ta matsa mata taci wani abun, to seta amayar dashi, gashi Aunty tayi_tayi suje asibiti a dubata taki yarda ita wai lafiyarta kalau ta warke. Aunty ta rabu da ita ta kyaleta, saidai duk abunda take Aunty na hanhalce da ita ta saka mata ido ne, kawai tana kallon gudun ruwanta.......

_*Agurguje*_

Su Maryam sunje Kano lafiya sundawo lafiya, gwaggo ta tarbesu faran_faran, ammi ta hadata da Mustapha a waya shima yamata yajiki, Maryam hankali ya kwanta taga jikin gwaggo da sauki sosai kuma ta hadu da aminiyarta saleemat da Ummanta... Anshiga wataran Ramadan lafiya, wata me dunbin albarka da sanya farinciki a zukatan kowanne Musulmin kwarai. komai natafiyarwa Maryam yadda yakamata a cikin wannan wata me albarka, saidaifa tsakanin ta da maigidanta babu wani sauyi na mu'amalar auratayya. kwanci tashi babu wuya a gurin Allah yau gashi har ankai azumi 10, yau ne kuma su Maryam zasu fara zana jarrabawar NECO.

Tun ƙarfe 8 tagama shirinta cikin uniform dinta. yayi das ajikinta ya mata kyau sosai. jakarta ta dakko ta dawo falo ta zauna tana jiran mustapha yafito dan shi zekaita da kansa. TV na kunna ina kallon wa'azi kafin yafito. se 8:30 yafito, nikuwa duk na zaku kafin yafito seduba time nake karna makara saboda ƙarfe 9 muke da paper. ina ganin yafito na mike nadauki jakata na rataya, sannan na dubeshi nace. "Ina kwana" be amsamunba sebina dayayi kallo, kasa nayi da kaina ina wasa da zoben azurfan hannuna da yaya Sadiq yabani. Tsawon 2 minutes yana kallonta sannan yace. "Ahala zaki makarantar?" da sauri na dago na kalleshi sannan na fara duban kaina, inason ganin menene beyi daidaiba ajikina ganin babu komai cike da confidence dina nace masa. "Ehh" fuskarsa a hade seriously yace. "Bazaki fita da wadannan kayanba" yana gama fadar haka ya juya ya fice, ya barmun kamshinsa a parlon. binsa nayi da kallo baki buɗe harya fice daga falon. dakina na koma dasauri na tsaya gaban mudumi ina karewa kaina kallo. "To me kayan jikina yayi?" nafurta haka a fili cikin raunin murya. riga da wando ne, uniform din. Rigar har kasan gwiwata kuma bata kamaniba sosai, se hijabi nasu karamine na makarantar, amma ni seda yaya sadam ya kara dinkomun wani medan girma danya rufemun duwawu ta bayana. ganin lokaci naneman kuremun sena fice nabi bayanshi nasan baze wuce part din ammiba. umaimah tana tsaye a bakin kofar falon ammi tana waya da wata kawarta tana bata labarin mustapha da irin sonda take masa. kawartata tace mata. "Kai kawata amma natayaki murna da samun masoyi zabin ranki, amma najifa kincemun shu bemasan kina yiba kuma yanada mata." Murmushi umaimah tayi tace, "wannan ba matsalata bane kawata, tunda muna gida ɗaya, zanyi ƙoƙarin naga yajanyo hankalinshi gareni, kuma indai dan ta matarshine ai basonta yakeba itama, dan daga dukkan alamu *matar cushe* cefa, tunda na fuskanci Baya sonta dan baya nuna mata wata kulawa" karaf wannan maganganun da umaimah tayi a kunnen Mustapha dake ƙoƙarin shigowa falon, kofar falon a buɗe take shiyasa yaji. duk dashi bame fuskantar abubuwan mutane bane idan badashi aka kasaba, amma wannan maganar ta umaimah kam yagane dashi da Maryam take, wani muskilin murmushi yasaki yana ayyana wani abu aransa. Ko kallon inda take beyiba daya shiga falon, Umaimah kuwa ganinsa yasa ta katse wayar da sauri tare da faɗin, "yaya NOOR ina kwana" benuna yajitaba balle yajuyo harta saran ze amsa mata. binsa tayi da kallo kamar wata mayya harya shige dakin ammi. Ajiyar zuciya ta sauke wani masifaffen sonsa na kara fisgarta, ta saba dama idan ta masa magana baya kulata indai ba'agaban ammi bane, amma ita hakan baya damunta kokaɗan, dan jikinta yana bata wataran mustapha ze kaunaceta. dakinta ta shige domin tacigaba da wayarta. Ammi ta dubeshi bayan sungama gaisawa tace, "harka kaita makarantar?" Kafin yabata amsa Maryam tashigo da ɗakin da sallamarta cikin ɗari_dari. "Ina kwana ammi" ta fadi haka kanta na ƙasa. Ammi na murmushi tace, "Lafiya kalau ɗiyata ya ibadah" kamar wata munafuka na saci kallonsa sannan nace, "Alhamdulillah" maida kallonta ammi tayi garesa tace, "katashi ku tafi dan takusa latti taran ta kusa" yana wani tsare gida yace, "wai ahaka zata makarantar?" Ammi tace, "kamarya a haka zata?.. meyafaru?" shiru yayi kamar bazeyi maganaba sekuma can yace, "kayan jikinta mana" ammi tace, "A'a mesukayi to? makarantafa zata ba wani gurin ba, uniform ne ai, dole dasu zata ai" bekara cewa komaiba ya mike yayi gaba. daɗine ya lullubeni danda harna tsorata karyace a fasa zuwan. cikin girmamawa nacewa ammi. "Sena dawo" tamun fatan nasara nabi bayanshi da sauri. murmushi ammi tayi, dantagane tsantsar kishine kawai kedamun mustapha. yana gaba ina binshi a baya, seda yarufe part dinmu da key sannan muka tafi. satar kallonsa nayi damuka shiga mota naga ransa abace yake sosai senaji duk babu daɗi. A hankali nace "kayi hakuri dan Allah" banza yamun tamkar bejiba. Arayuwata banason shariya kawai senaji hawaye yacikamun ido, ina ƙoƙarin maidashi amma seda yazubo. kallonta yayi ya tabe baki yacigaba da tukinsa. Har cikin makarantar muka shiga, parking yayi yadubeni bece komaiba, niba bance masa komaiba na bude motar nafita. Binta yayi da kallo harta shige compound din makarantar, lumshe idonsa yayi yatada motar yatafi. Ina shiga natambayi wata daliba inda ake exam din, Tacemun ita canzata inzo muje. se wajen ƙarfe goma aka kawo mana paper'n jarrabawar, bamu fara da wuriba dan haka seda 12 ta wuce muka fito. Tafiya kawai nakeyi ɗan zaman da mukayi harna fara gajiya, gashi bansan a me zankoma gidaba danbecemun zezo yadaukeniba, kuma babu ko sisi a hannuna gashi rana ta kwalle. Ina cikin tafiya kamar a mafarki na hango motarsa fake a bakin gate, wani irin farinciki naji dama rana se dukana take da sauri na karasa wajen motar na bude na shiga, sallama na masa ya amsa ciki_ciki. kwantar da kaina nayi ajikin kujera ina lumshe idona tare da sakin ajiyar zuciya saboda sanyin ac dayafara ratsani gami da shaƙar daddaɗan kamshinsa. seda naji yayi parking alamun munzo gida sannan na bude idona. A hankali nace, "Nagode" be amsamunba se kallona dayayi, kallonsa nayi nima karaf muka haɗa ido, dasauri najanye nawa zuciyata na ɗan bugawa. juyawa nayi na bude murfin motar nafita. shima budewa yayi yafito bayan ya kashe motar. daidai lokacin umaimah tafito zata fita, taci uwar kwalliya a tsakar ranarnan dayake bata azumi yau shine ammi ta aikata. Kawar da kaina nayi daga tana inda take, danzuwa yanzu nagane dalilin dayasa bata kaunata saboda tanason *hearbeat* ɗina. shiko mustapha ganin umaimah yasashi karasawa kusa da Maryam da sauri ya kama hannunta, yana wani dubanta ƙasa_kasa, duba menuni da zallar kauna ga wanda akewa, yafara magana yanda umaimah zataji cikin taushin murya menuni da zallar kaunah. "Haba hubbynah wayace kiyi tafiya aranarnan sekin wahalarmun da kanki, ga azumi gashi kinsha wuyar school, kijira Ni mana nazo nayi aikina" yakarashe zancen yana wani kannemun ido. Niko mamakinsane ya kasheni,nama kasa motsi se kallonsa kawai nake. kamar bashine yaketa haɗe rai ɗazunba. kafin nayi wani yunkuri naji yadaukeni cak..........✍️ MESON COMPLETE WHATSAPP 08166674823

*ABINDA KASHUKA...*

_*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_

*5️⃣6️⃣*

*Bismillahirrahmanirrahim*

........Taga_taga umaimah tayi kamar zata fadi saboda tsabar firgici. da kyar ta iya daidaita nutsuwarta ta tsaya da kafafunta, saboda tsabar razani da abunda tagani, wani tukuku taji ya turnike mata zuciya, bayan daukar Maryam da Mustapha yayi harda wani bin fuskarta da kisses, wannan wanne irin mugan gani tayi yau da ranar Allah. wani abu taji yatokare mata a kirji, binsu tayi da kallo kawai harsuga shige cikin gidan kamar wata sakarya. wata tsanar Maryam taji takara cika mata kowanne sashe na zuciya, takasa koda motsi mustapha da Maryam kawai take hangowa a idonta manne da jikin juna. "ita kuma shegiyar yarinyar harda kara wani kwanciya ajikinsa kamar jikin ubanta" umaimah ta fadi haka afili hawaye masu zafi nazubo mata. ita tananan tana haukanta mustapha bason Maryam yakeba, bazatasha wuyar janyo hankalinsa garetaba, ashe ita bata sanina yana son maryam irin haka. kallon da Mustapha yayiwa Maryam shi kadai ma ya isa yatada mata hankali, balle kuma ganinta rungume a jikinsa. Umaimah tayi nadamar fitowar ta a wannan lokacin babu adadi, datasani tun dazu da ammi taketa cemata tatafi aiken tatafi, dabataga wannan abun dayake kokarin tarwatsa mata zuciyaba. son mustapha kullum karuwa yake acikin zuciyarta, mijin datake mafarkin ta aura taki sauraren kowa saboda shi, yau gashi ta haɗu da wanda yafi wanda take tunanin samun ma, amma wata banzar yarinya tana kokarin kawo mata cikas, ta dade a tsaye a gurin tana sake_sake da kyar ta iya jan kafarta tatafi, da ji tayima kamar ta koma ta fasa fitar........

Idona a runtse harya saukeni, sosai kirjina ke dukan uku_uku cikin wani irin yanayi. gabadaya salon nasa yadauremun jijiyoyin jiki tamau, jinin jikina kuwa babu tantama ya daskare. Kaina naƙasa nakasa kallon koda inuwarsace har ya buɗe Kofar part dinnamu ya shige abunsa beko ƙara kallon inda nakeba. jan kafata dakyar nima nayi nabi bayansa. harnayi wanka nayi Sallah bandawo daidaiba, kwanciya nayi akan gado na lumshe idona ina tuno ni a jikinsa, wani murmushi ne na farinciki ya subcemun, kankame filo nayi a kirjina inajin dama shine.(🙄azumi ne dai mero) bansan sanda bacci me daɗi yadaukeniba.........

Ammi tana kwance akan gadonta tana bacci, sama_sama takejin wayarta na ringing. A hankali tatashi zaune, bacci fal idonta ta janyo wayar ta daga ta kara a kunnenta. "Assalamu alaikum" daga ɗaya ɓangaren aka faɗa. 'wa'alaikassalam" ammi ta amsa sallamar tana tunanin kamar tasan Muryar me maganar. gaisawa sukayi duk da ammi bata gane shiba. Daddy ganin bata gane shiba yace, "kina magana da yaronki mainasara" murmushi ammi tayi tace, "yaro kodai ubangida" cikin zolaya daddy yace, "yaro dai, tunda ke baki nemeniba nina nemeki, kodan yanzu ɗanki yazo hannunkine shiyasa kika dena neman mu" murmushi me sauti ammi tayi tace, "to ayi hakuri na tuba kaina bisa wuyana zandinga nemanka akai_akai daga yanzu insha Allah" "dakuwa kin kyauta, dan zanso hakan sosai" batare da tunanin wani abu akan maganar daddy ba ammi tace. "yame jiki kuwa" "jiki da sauki Alhamdulillah, tunda yanzu yadawo hayyacinsa yana gane abubuwa." "Masha Allah, Allah Ubangiji ya ƙara sauki yasa kaffarane" "ameen ya Allah" daddy yatambayi lafiyar su Maryam da kowa da kowa, ammi tace duk suna lafiya. Numfasawa daddy yayi yace. "Hajiya Maryam nakirakine muyi magana akan dukiyar Mustapha dake hannuna, tun kwanaki nakeson muyi maganar ciwon Sadiq yatsaidani amma yanzu tunda komai yadaidaita semusan yanda za'ayi." ammi tace. "Yallabai, aini bani da hurumi akan wannan maganar, Muhammad ai ɗankane kuma dukiyarsa takace, a ganina babu wani bukatar yaza'ayi da dukiya, kacigaba da juyata kawai agurinka, amma ni bazan karbi komaiba, kuma Muhammad haka" cike da mamakin ammi daddy yace. "Hakane Hajiya, mustapha ɗanane amma yazama dole nabashi hakkinsa dake wajena, tunda yanzu shima yakai munzalin daze iya juya ta" "to shikenan kazamu lokaci kazo semu tattauna akan hakan." godiya daddy yamata sukayi sallama.

Se kusan la'asar natashi daga bacci. Fuskata na wanke na kuskure bakina sannan na nufi part din ammi, dan anan muke aikin azumi na duka gidan. A baranda natarar da ammi da mama A'isha suna ferayar dankali. Mama kuma tana gefe tana wankin waken kosai. Bayan mun gaisa ammi ta dubeni tace, "ɗiyata har kin tashin kenan, dazu NOOR yashigo ai, yacemun harkun dawo amma kin kwanta, ya exam din.?" Kaina na ƙasa nace, "Alhamdulillah" "Masha Allah, Allah yabada sa'a" gabadaya muka amsa da "ameen" ciki na shige na nufi kitchen. Aunty zuhura ce, kadai a kitchen din tana girki. "Aunty zuhura sannu da aiki" nafada bayan na shiga kitchen din. "Yawwa Mamana, kindawo kenan" "nadawo Aunty zuhura tun kafin 1." "Sannunki ya jarrabawar?" "Lafiya kalau, Aunty zuhura. Bari nazo natayaki aikin" Aunty zuhura na murmushi tace, "dakinyi zamankima danna kusa karasawa miyace kawai tayi saura, kar a wahalar da babynmu" murmushi kawai nayi bance komaiba, nafara tayata aikin. Zuhura dama tana sane tayiwa Maryam wannan zancen, danta fuskanci har yanzu babu abunda yashiga tsakaninsu da mustapha, danta fuskanci yanada shegen miskilanci, amma zata taimakawa Maryam da dabaru ta yanda zataja hankalin mustapha zuwa gareta, Wannan miskilancinnasa duk se tayi maganinsa. fita tayi tacewa Maryam tana zuwa, bayan kamar minti goma ta dawo da waya kare a kunnenta tana faɗin. "Bangane tunda kukayi aure haryanzu babu wani abu daya tsakaninkuba." shiru tayi alamar tana sauraren wanda suke maganar na tsawon 50 seconds sannan tace. "Haba salma kekamar ba wayayyiyaba ace haryanzu kinkasa ɗaukar hankalin Tahir zuwa gareki yana mijinki kuma kuna gida ɗaya, haba salma karki bani kunya mana." Shiru ta karayi na wasu sakanni kafin tace, "wannan duk ba matsala bane, salma dan hadaku aure akayi, ai baza'ace shikenan bazakuyi soyayya kuyi rayuwar aure kamar kowaba, kuma koda baya sonki tunda ke kina sonshi sekiyi kokari kibi duk hanyoyin dazaki jawo hankalinsa zuwa gareki, kefa macece" Takarayin shiru sannan tacigaba da fadin. "Akwai hanyoyi da dama salma dazakibi kijawo hankalin mijinki zuwa gareki, batare daya gane danshi kikeba kokuma kina son shine, shifa namiji tamkar jaririne agurin matarsa duk ta yadda kikabi dashi haka ze tashi yana miki, yanzu idan kika zauna kuncigaba da rayuwa a haka kefa zaki cutu, danshi idan yana da bukatar mace aurensa ze kara, kuma yadinga bawa matarsa kulawa kekuma kina gefe ko oho, gwarama tun wuri kifarka daga nannauyar baccin dakike kibawa makiya kunya, kijawo hankalin mijinki zuwa gareki tun kafin dare ya miki kizo kina cizon yatsa" ta karayin shiru tana saurare sannan tace, "yawwa kawata yanzu naji batu, bari na baki wasu shawarwari danasan insha Allahu zasu taimaka miki. idan yana zaune a falo irin da daddarennan yana kallo, kekuma ki tsalo wankanki cikin kananun kaya, ki baza kamshi a kowanne lungu da sako na jikinki me daɗin gaske, wanda dole idan ya shaka seya dago ya kalleki, karkiji kunya ko tsoron komai, kifito falon abinki kina tafiya ta daukar hankali, kiyi kamar baki ganshiba kishige kitchen kamar zaki dauko abune, in kinfito zaki koma kice masa sannu, kiyi kamar se lokacin kika ganshi kikoma daki abinki, kiyi kamar kwana uku kinayin haka, seki dena fitowar. Nina faɗa miki da gayyama zena zaman falon danyaga fitowarki, duk randa baki fitoba kuwa ki leko ta window zaki gansa yana kallon kofar dakin ki hankalinsama gabadaya baya kan kallon, to yanaso kifito ya shaki kamshi yaga kuma abubuwan harka na juyawa. Sannan kuma kisan dabarun dazaki na yi jikinki na haɗuwa da nashi" Shiru ta ƙara yi, sannan tace. "Kai salma na rasa irinki, yanzu bakisan yanda zakiyi jikinku ya haɗu ba, to bari na baki misali ɗaya. Bayan kinyi abinda nace miki kamar na sati ɗaya ko biyu. wataran bayan kinfito falon, sekinzo kusa dashi, seki fadi da gangan ki zube a kasa, zaki ga yataso da saurinsa yana tambayarki meyafaru duk yabi ya rude, to yana tsoron kar ko kinji ciwo sosai yadena ganin gilmawarki. kekuma seki langwabe harda hawayenki ki rirrikeshi kina nuna masa kin firgitane tare da zuba masa shagwaba, duk miskilancinsa ranar zakisha mamaki nina faɗa miki, kamshin dakike zubawa kadai ya isa ya hautsina masa lissafi." Shiru ta kumayi daga can tayi dariya tace, "yawwa kawata kinfara hawa layi haka nakeso, ki dauke masa hankalin daga kan yanmata masu farautar mazajen wasu, dama gaki da kyanki da jiki na daukar hankali....."

Shawarwari da dabaru masu yawa zuhura ta lissafo sannan tayi sallama ta aje wayar. kallon Maryam tayi wadda tayi tsit tana sauraren zuhura da dukkan hankalinta tace. "Sannu mamana, na barki kinata aiki ke kadai ko, wlh wata kawatace ta kirani akan matsalar ta ita da mijinta" murmushin ƙarfin hali na kakaro nace, "bakomai Aunty zuhura ai babu ma wani aikin" murmushi kawai Aunty zuhura tayi. suna aikin tana satar kallon Maryam, yanda tayi tsumu alamun tana tunanin wani abu, tasan abubuwan data faɗane Maryam take tunani akai, dama kuma duk wayar datayi pretending ne kawai, dan Maryam din taji tayi, ai kuwa tayi nasara danta saka Maryam a zullumi da tunani...

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull