Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 38
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 38: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 38. Har aka sharuwa bansakashi a idonaba, jikina yau duk a…
3,388 words
ABUNDA KA SHUKA
By* *zeey kumurya*
*5️⃣7️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
..........Ammi ta rakasu da murmushin jin daɗi, dama ita burinta kenan taga sun haɗa kansu kuma Alhamdulillah ta lura babu wata matsala a zamannasu.... Yana gaba ina binsa abaya har muka karasa gurin motar, na zagaya na shige bayan shima ya shiga. kafin ya kai ga kunna motar wayarsa ta hau ruri cikin amo me daɗin sauti. dagawa yayi ya kara a kunne tare da yin sallama. Amsa masa akayi sannan yace, "Aunty ina kwana, ya ibadah?" Da sauri na kallesa jin ya ambaci sunan Aunty. daga can ɓangaren bayan Aunty amsa masa gaisuwar ta ƙara da faɗin, "Muhammad suhailat ce keson magana dakai, ta dameni inkira mata kai, wai ita idan takiraka baka samun wayarka." Cikin matukar mamaki yace, "suhailat kuma?" Gabanane yayanke ya fadi jin sunan Aunty suhailat daya ambata. Aunty tace, "ehh" bekara cewa komaiba duk da zuciyarsa cike take da mamakin meyakai suhailat gidan Aunty, tunda yasan ba zuwa takeba. nikuwa tsumu nayi ina saurarensu. Suhailat bayan Aunty ta mika mata wayar cikin azabarbi tace, "yayana! I missed you, dan Allah yaushe zaka dawo, wlh gaba-daya duk nabi nadamu, ganinka kawai nakesonyi" lumshe idonsa kawai yayi bece mata komaiba. suhailat taita masa magana amma kememe yaki cemata ko "kala" harda kukanta amma yayi biris abunsa karshema kashe wayar yayi dan kar Aunty ta karba ta masa faɗa akan kin kula suhailat ɗin da yayi. kallon Maryam yayi ta kasan ido, ta haɗe rai sosai an tsuke bakinnan. tabe bakinsa yayi ya tada motarsa suka wuce....yauma damuka tashi shiyazo ya ɗaukeni, Ni mamakinshi nake yanda yake barin kasuwa yadawo ya dakkoni sannan ya koma. Bayan ansha ruwa kafin sallar isha'i, su Maryam suna zaune a falon ammi dukansu suna hira. Ammi ta dubemu nida umaimah tace, "ɗiyata ku tashi kuje gurin Musa tailer, seki zabi ɗinkin da kikeso ya miki ya kuma gwadaki" a hankali nace "to ammi, da nisane gurin?" Aunty zuhurace tace, "da ɗan nisa kadan gaskiya" umaimah kuwa kallon su kawai take tana tabe baki, dan zuhuranma ba wani shiri suke da itaba. Ammi ta dubeta tace, "Autatah ki tashi kuje tare, bari nakira NOOR yakaiku idan babu abunda yake idan kuma yana wani uzurin sena kaiku da kaina." Da umaimah harzatace kanta na ciwo bazata raka maryamba, amma jin ance mustapha ne ze kaisu seta fasa. Ammi ta dakko waya takirasa ta sanar masa, yace mata su jirasa gashinan zuwa. ammi na sanar musu Umaimah ta tashi da sauri ta shige daki, turare ta bulbula har yayi yawa. Tana fitowa Aunty zuhura tace, "kai umaimah wannan turaren dakika saka yayi yawa har yana hawa kai fa" murguda baki tayi ta zauna batace komaiba. Ammi ce tace, "gaskiya autah yayi yawa" cikin sangarta tace, "ammi feshi biyu nayifa haka turaren yake" ammi zata kuma Magana wayarta tayi ƙara, dagawa tayi mustapha yace mata yana jiransu a mota. Bayan ta kashe wayar ta dubemu tace, "ku tashi kuje kunsan bayason jira" Zuhura na dariya tace, "ai da gimbiyarsa dole yajirasu" murmushi nayi kawai, na musu sallama muka tafi.
A gajiye nake tafiya yau nagaji sosai kuma azumin yaɗan kolani. ina gaba tana bina a bayana danna rigata fitowa daga falon. yana zaune acikin motar ya buɗe murfin ƙafarsa ɗaya na waje yana latsa wayarsa. zagayawa nayi na buɗe front seat na shiga da sallama ɗauke abakina. batare ɗaya dagoba ya amsamun acan ƙasan makoshi. Yana ganin umaimah tataho ya maido ƙafarsa ya rufe Kofar, kunna motar yayi, ya kuma kunna light din motar. kallon fuskar Maryam yayi yaga itama shi take kallo karaf suka haɗa ido. Hararata yayi nayi sauri na ɗauke idona daga kansa ina kebe fuska. umaimah ta buɗe bayan motar ta shiga sannan tace, "yaya NOOR ina wuni, dafatan kasha ruwa lafiya" "lafiya" yabata amsa atakaice yana tada motar. reverse yayi megadi ya buɗe mana get muka fice daga gidan. umaimah na masa hanya har muka karasa. A kofar wani shago mukayi parking, umaimah ta fito ta dubi Maryam daketa lumshe ido bacci fal cikinsu tace, "ki fito" mustapha na kallon Maryam yace, "ina zata?" Umaimah tace, "ciki zamu shiga ze aunatane ta kuma zaɓi ɗinkin datakeso" fuskarsa a tsuke yace, "bazata ta shiga cikin wannan mazanba" galala umaimah tayi tana kallonsa baƙin ciki fal ranta yanda mustapha yake nuna kishin Maryam akan komai. Maryam kam sama_sama take jinsu amma bata fahimtar mesuke cewa bacci yafara fuzgarta. umaimah batace masa komaiba ta juya ta nufi cikin shagon, bayan kamar 10 minutes suka fito tare da toilor ɗin. gaishe da mustapha yayi, Maryam kuma data wartsake dakyar ta gaisheshi. Ya dubeni yace, "Hajiya wanne irin ɗinki za'a miki?" Nace masa "style me kyau kawai" yace, "doguwar riga ko riga da skirt koda zani?" "Kamata doguwar riga" mustapha dake latsa wayarsa tamkar baya saurarensu ya fadi hakan. na kallesa kawai bance komaiba. Toilor'n yace, "angama ranka ya dade" umaimah ma ta faɗa masa irin ɗinkin takeso. Toilor'n yace to nafito ya gwadani, amma Mustapha ya hana. Toilor'n yace masa, to umaimah seta gwadani amma kememe bawan Allah nan yahana waishi baza'a gwada masa mata a titiba. Dariya kawai toilor'n yayi yacemun muje to zezo har gida ya karbi measurement ɗina. muna cikin tafiya a mota naji mutum ya janyoni jikinsa. lumshe idona nayi ina sauke ajiyar zuciya. daidai kunnena yakai bakinsa cikin wata sanyin murya yacemun "kin sakarmun nauyi fa" aiko kamar ya tunzurani nakara manne masa a jiki. umaimah dake baya ta hadiye wani yawu me daci a ranta tana faɗin. "Tsabar jaraba yana tukinma amma seya wani rungumeta, gashi se wani rada_rada yake mata, kamar sun manta da ni a motar" mtss taja siririn tsaki tana hararar bayan Maryam. Mustapha sarai yaji tsakin da umaimah tayi kawai sharewa yayi. kafin suje gida Maryam tayi bacci ajikinsa. yanayin parking umaimah ta buɗe kofa ta fice. Kallon Maryam yayi yaga baccinta take hankali kwance, se numfashi take saukewa a hankali. Kurawa fuskarta ido yayi a karo na biyu a rayuwarsa bekuma san dalilin kallonnata dayakeba. tabe bakinsa yayi bayan yagama ƙare mata kallon, a hankali yafara ƙoƙarin rabata da jikinsa. Maryam kuma ta ƙara kankameshi. Lumshe idonsa yayi ya ƙara rabata da jikinnasa. Maryam ta buɗe idonta a hankali tana jingina jikinta da kujera, buɗe murfin motar yayi ya fice abinsa, bekara koda kallon inda nakeba . da kyar nima na daure na fito, wani irin bacci nakeji. Kulle motarsa yayi yanufi masallaci dan har anyi isha'i anfara asham. Ban koma part din ammi ba, na koma namu......
Kwanci tashi asarar mai rai. Yau 23 ga watan Ramadan yau kuma muka gama exam dinmu ta NECO, dayake babu wani interval sosai. A 'yan kwanakinnan wata shakuwace ta shiga tsakanin Maryam da Mustapha, wanda su kansu basu gane hakanba. Mustapha matukar da umaimah a guri ze nunawa Maryam kulawa da tattali koda a gaban ammi ne kuwa. Hakan kuwa bakaramin kona ran umaimah yakeba. gashi kullum son mustapha karuwa yake a ranta tarasa yadda zatayi, zuciyarta nabata shawarar ta sanar masa kawai koze amshi tayinta, amma kawarta ta hanata tace ta bari a gama azumi tasan mezasuyi dole mustapha yasota. Maryam kam ta fara gwada abubuwan da taji zuhura na fadawa kawarta a waya, ta kuma dage da addu'a akan Allah ya waiwayo mata da hankalin mustapha gareta. Mustapha kuwa yanzun baya gane kansa dan kwata_kwata bayajin daɗin jikinsa, yakuma rasa meke damunsa. Gashi yanzu babu abunda yaji yanaso sama daya dinga jin Maryam ajikinsa yana shaƙar daddaɗan kamshinta, yanason kamshin jikinta sosai. kullum seya ayyana ya rungumeta ba'adadi amma seya kasa. saboda yana ganin Maryam zata rainashi gata yarinya ƙarama ai girmansa seya zube. Ya lura kuma yarinyar itama miskikar kantace.
Yau exam din rana sukayi 2_4 daya dakkota be koma kasuwaba ya kwanta a dakinsa. ita kuma Maryam tana part din ammi sunata aikin girki. tunani yakeyi kawai ta yanda za'ayi su kwana tare, badan ya mata komaiba sedan kawai soyake yajita a jikinsa suna bacci tare. mikewa yayi ya fice bayan yasamo mafita. yau nasha wahalar azumi sosai, dama gashi har yau bansha a zumiba. kafin asha ruwa kamar kullum zandebo abincinsa in ajiye masa akan dinning, mukuma dama a part din ammi muke shanruwa. Bayan na jera masa komai akan dinning na koma part din ammi na sheme akan carpet kafin akira sallah. Aunty zuhura se tsokanata take. Ammi kuwa se sannu takemun tana faɗin, "wannan megidannawa yana wahalarmun dake ɗiyata" duk a zaton ammi karamin ciki ne dani, kullum seta dinga cemun Yakamata insha azumi in dan huta saboda lafiyarmu. Idan ta fadi haka senaita mamaki araina ince. "Dududu yaushe muka tare da har suke tunanin inada ciki, inma ha hakaba nida ko wata mu'amalar aure bata taɓa shiga tsakaninmuba ta ina za'a samu cikin." Da'aka sha ruwa kunun aya kawai nasha yacikamun ciki. Aiko jikina ya mutu murus kamar anmun shegen duka, dakyar na lallaba na koma part dinmu nayi Sallah, ina idarwa na baje akan gado se bacci. Ban tashi farkawaba se wajen 9:30. sallar isha'i nayi na fito falo domin na samarwa kaina abunda zanci. yana zaune a falo yana kallon labarai. "Sannu da zuwa" na masa ya amsamun dakai. kan dinning na nufa na dibi sauran abincin daya rage naci na koshi sannan na koma daki. Mustapha daketa satar kallon Maryam harta gama ta koma daki. Bayan kamar 10 minutes da shigarta dakin, ya dauki wata leda dake gefenshi yabi bayanta. A hankali ya taɓa handle din dakin yaji kofar a buɗe take, ajiyar zuciya yasauke ya tura kofar a hankali. kamar yadda yazata Maryam tana toilet tana wanka, murmushin mugunta yayi ya aiwatar da abunda zeyi ya fice. Yana fita ba jimawa Maryam ta fito daga toilet tana daure da towel. gaban mudubi na nufa na zauna akan stool nafara shafa tsadaddadun lotions masu kamshi ajikina. seda na mulke jikina tass dasu sannan nabi kowanne lungu da sako na jikina na shafeshi da daddaɗar humrar da Aunty zuhura ta bani gami da body spray me sanyin kamshi. lokar mudubi na janyo na dakko alawata da kullum senasha kafin na kwanta, itama Aunty zuhura ce ta bani tace nadinga sha kafin na kwanta bacci. kokaɗan banajin bacci a idona tunda banjima da tashiba. Addu'a nafarayi Allah yasa kafin nagama shiryawa yabar falon, intafi part ɗin ammi musha hira, dan wataran hanani zuwa yake yace dare yayi, shiyasa kafin yadawo nake guduwa harse yagaji da kansa yazo yakirani. white lipstick na shafa kawai a lips ɗina na Mike da nufin na dakko kaya. Abunda nagani a kan gadone yasani kwalla wata gigiciyar ƙara a matuƙar firgice nayi baya na manne da bango ina runtse ido tare da karanto duk addu'ar datazo bakina. A hankali na buɗe idona kaɗan cikin tsoro na ƙara kallon kan gadon. abunda nagani dai shi nakara gani, kadangarene jangwala gwada katoto kamar ma yana motsi yanzu. da gudu na nufi kofa na buɗe nafice daga dakin nama manta babu kaya a jikina se ɗan guntun towel........✍️ COMMENTS MESON COMPLETE WHATSAPP 08166674823
* *ABINDA KASHUKA...*
_*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_
*5️⃣8️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
........... Mustapha dake zauna a falo yana kallonsa hankali kwance tamkar beji ƙarar da Maryam ta kwallaba. A matukar tsorace na fito falon jikina na wata irin kyarma karasawa nayi na faɗa jikinshi cikin fitar hayyaci sosai na tsorata saboda arayuwata ina bala'in tsoron kadangare. lumshe idonsa yayi jinta ajikinshi yana sakin boyayyiyar ajiyar zuciya, Maryam kam ta kankameshi rawa kawai jikinta yakeyi idanunta a runtse. A hankali yasa hannunsa yana ƙoƙarin rabata da jikinsa, cikin basarwa yace, "mene haka?" hannunta na rawa ta nuna masa Kofar dakinta. Lips dinshi na kasa ya lasa wannan yace, "what happened?" Maryam da idanunta babu abunda yake hangomata se kadangarennan ta kasa masa bayani, tsigar jikinta se tashi take tanajin tamkar kadangarenne a jikinta. rikeshi tayi sosai tana sakin kuka tama kasa masa bayani. Lumshe idonsa ya kumayi cikin jin bakon yanayi na ziyartarsa saboda yanda sulbin fatar jikinta yake goguwa ajikinsa. yanajin kukan datake har cikin ransa bakuma ya tunanin ze iya jurar cigaba dajin kukannata. Tausayintane ya tsirga masa ganin yadda duk tabi ta tsorata jikinta se ɓari yake, beyi tunanin zata tsorata hakaba. a hankali ya ƙara saka hannunsa ya dago fuskarta daga jikinshi zuciyarsa na ɗan bugawa ya kura mata tsumammun idanunsa. Maryam da har yanzu ta kasa buɗe idonta se ƙara runtse idanta take, ta kudundune jikinta tanajin yanda idanuwansa ke yawo ajikinta. cikin kasalalliyar murya ya ƙara tambayarta. "Meyafaru a dakinnaki" "lizard🦎" ta bashi amsa hawaye na zubo mata. Yana nuna so surprise yace, "lizard?" Gyada masa kai tayi har lokacin idonta a rufe yake. ƙoƙarin sauke yayi daga jikinsa yana faɗin, "bari na duba dakin" kuka Maryam ta saka tana ƙara kankameshi gani takeyi yana barinta kadangaren ze kara biyota. lips dinsa ya lasa tare da fesar da numfashi yace, "zan cire miki ne daga dakin" girgiza kai Maryam ta hauyi cikin kuka tace "Ni kar katafi ka barni tsoro nakeji" cikin sanyin murya yace, "to muje tare, seki nunamun inda yake" nanma Maryam kin yarda tayi domin kome za'a mata bazata ƙara komawa dakinta a yauba. Be kuma cewa komaiba, jikinta yabi da kallo, musamman ma gashin kanta daya bazu a gadon bayanta. a hankali yakai hannunsa yana tattare mata gashin ya haɗe shi guri guda shafashi ya shiga a hankali yana lumshe ido. ƙara cusa kanta tayi cikin kirjinsa tana shaƙar daddaɗan kamshinsa gami da sassauke ajiyar zuciya, ta rike shi gam ga dukkan alamu har lokacin a matukar tsorace take. A hankali yayi ƙasa da hannunsa yafara shafa wuyanta zuwa bayanta cikin wani sabon yanayi dayake fizgarsa. wani abu naji ya tsirgamun a gabadayan jikina lokacin danaji lallausan tafin hannunsa akan fatar bayana, wani irin tsorone ya ƙara dirarmun, zuciyata ta fara bugawa. mutsu_mutsu na farayi ajikinsa hawaye na zubomun wanda bansan dalilinsuba. jin tana mutsu_mutsu mustapha ya fara bubbuga bayanta a hankali irin yanda akewa yara, bakinsa yakai saitin kunnenta yafara hura mata iskar bakinsa. tsit nayi nadena mutsu_mutsun cikin jin daɗin abinda yakemun, a hankali wani bacci me daɗi yafara fizgata bansan sanda baccin ya ɗaukeni ba gaba-daya. Jikintane yaji ya saki rigon data masama ta cika, hakan ya tabbatar masa da bacci ne ya ɗauketa, ya fuskanci tana da saurin bacci. a hankali ya dago da fuskarta daga jikinsa ya kura mata ido, a duk lokacin daya kalleta yana ganin wani abu dayake daure masa kai a tattare da ita. ɗan karamin bakinta ya kalla data ɗan turoshi gaba, pink lips dinnan nata se kyalli suke, ajiyar zuciya ya sauke yayi ƙasa da idonsa, towel jin jikinta ya kunce yanda ta kudundune jikinta ne yasa be zameba daga jikinnata, amma gaba-daya rabin kirjinta a waje yake. "jikinta me kyau ko ina bul_bul" ya furta hakan a ransa batare daya saniba. sosai jikinsa ya sauya masa ganin maryam a haka, kasalace take ƙara lullubeshi,wani irin sanyi jikinsa yayi. duk yanda zuciyarsa ke tunzurashi yayiwa Maryam wani abu amma yakasa, lips dinta yabashi burgeshi yanaso yamata koda kiss ne amma yakasa aiwatar da komai, daya daga hannunsa da nufin ya shafa kirjinta seyaji jikinsa ya kama rawa, kansa na sara masa. Rungumeta kawai yayi tsam ajikinsa cikin wani irin yanayi yana shaƙar kamshinta dayake ƙara saukar masa da kasala. kusan 30 minutes suna haka, Maryam tanata baccinta cikin kwanciyar hankali, saɓanin mustapha dayake cikin wani irin yanayi na rashin jin dadi me wuyar fassaruwa, duk da yanajin wata nutsuwa nabin jikinshi amma yarasa meyake masa daɗi ga mararsa data daure masa. da kyar ya iya ƙoƙartawa ya kashe TV ya dauki maryam sukayi dakinsa, dakyar yake iya taka kafarshi danma maryam ɗin bata da wani nauyi. a hankali yake ƙoƙarin shinfideta akan makeken gadonsa, kamar wata jaririya haka ya lallaba ya a jiyeta yana cize lips dinsa. yana ƙoƙarin zame hannunsa daga jikinta ta zabura a tsorace ta kankameshi ajiyar zuciya ta sauke tana ƙara lafewa ajikinsa. runtse idonsa yayi tsigar jikinsa na tashi, wani yarrrr yakeji ajikinsa. idanunsa a lumshe batare daya buɗe ba, yakai hannunsa ya fara gyara mata towel ɗin jikinta dake ƙoƙarin barin jikinnata gaba-daya, idanuwansa bazasu iya jurar kallon jikintaba a yanayin dayakejinsa a yanzu. Seda ya tabbatar yarufe duk wani abu daze iya tayar masa da hankali a jikinta, sannan ya buɗe idanunsa da suka kada sukayi jajur ya sauke akanta. Cinyoyinta ya kurawa ido, yanajin tamkar yakai hannu ya shafasu amma yakasa koda daga danyatsansa ɗaya da niyyar hakan, blanket ya jawo ya lullubeta. zare hannun damansa yayi daga jikinta ya dafe kansa dake sara masa. "Me yake shirin faruwa dashine?" ya tambayi kansa cikin dacin zuciya. shi mutum ne meson yaga ya haifi ya'ya a rayuwarsa amma baya tunanin zega wannan ranar, tunda gashi ya ƙara tabbatarwa da kansa bashi da lafiya kamar kowanne ɗanamiji. ada canbaya abun baya damunsa kokaɗan, amma yau yaji yana bukatar shima yazama mutum kamar kowa, yana bukatar samun nutsuwa ajikinsa, yanajin feeling sosai a yanzu, amma baze iya tabuka komaiba. numfashi ya fesar daga bakinsa yafara kiran sunayen Allah aransa koyaji sauƙin abunda yake damunsa. A hankali nutsuwa ta fara zuwar masa, zuciyarsa ta fara sanyi daga kunar datake masa. cikin kwarin zuciya ya lallaba ya zame maryam daga jikinsa domin yaje ya watsa ruwa ko yaji sanyi ajikinsa. A hankali ya mike ya nufi toilet amma kafin yakai ga shiga yaji muryar Maryam a firgice tana kiran "yaya,Yaya, lizard!"
Chapter notes and social links
Har aka sharuwa bansakashi a idonaba, jikina yau duk a sanyaye. Maganganun Aunty zuhura se yawo suke a kwanyata. "Tabbas duk abubuwan data faɗa hakane, karnaje natsaya kallon ruwa kwado yamun kafa, yazama dole nima nadage dan ganin na jawo hankalinsa gareni, tunda ina tsananin sonsa, ga kuma masu kawo masa farmaki daga waje, amma matsalar bansan ta ina zan faraba, ko shawarar Aunty zuhura zannema, takaramun haske da dabarun yanda zanjawo hankalinnasa.".... Haka dai naita tunane_tunane nikadai. Be shigo gidanba seda aka idar da da sallar asham, ina jinshi ya kunna kallo a falo amma nakasa fita falon, duk da zuciyata na azalzalata naje nafara aiwatar da abunda naji aunty zuhura nafadawa kawarta amma nakasa, hakura nayi na kwanta bacci saboda tashin dare..... Washegari bantashi daga barci da wuriba saboda yau se 11 mukeda exam, kafinma na tashi daga barci ya fita. seda na gyara gidan tsaf nayi wanka na shirya cikin Uniform dina sannan na nufi part din ammi domin na gaisheta. Suna zaune a falon ita da umaimah nayi sallama na shiga, ammi ta amsamun amma umaimah se bina datayi da kallon banza. muka gaisa da ammi cikin fara'a. duban umaimah nayi dan kar ammi ta zargi wani abu nace mata "Aunty umaimah ina kwana?" Umaimah da tunda Maryam ta shigo taji wani baƙin ciki ya turniketa, saboda ganin Maryam yanzu ya kara tuno mata da abunda yafaru jiya. maimakon ta amsawa Maryam gaisuwarta seta faki idon Aunty ta galla mata harara tare binta da wani wulakantaccen kallo, ran Maryam ya ɓaci taji babu daɗi sosai, amma ta daure ta dubi ammi tace. "Ammi zan wuce naga 10:20 tay..." Bangama rufe bakina sassanyan kamshinsa ya ziyarci hancina. Lumshe idona nayi cikin jin daɗi ina sauraren daddadar muryarsa yana sallama. Rabona dana ganshi tun jiya daya dakkoni daga school, da asubama daya tasheni sahur ban wani ganshiba ina buɗe kofa ya juya ya tafi.. muryarsa naji yana faɗin, "taso mu wuce" mikewa nayi cikin jin daɗi dannasan dani yake. Ammi tana murmushi tace, "har ina zanyiwa yiwa Ali driver magana yakaita, ashema kana tafe" kallon Umaimah data kura masa ido da mayen kallonta yayi, sannan ya maida kallonsa kan Maryam, yana wani kankanne ido irin kallon luv dinnan yace. "Nafison na kaita da kaina ammi, karnaje amun gudu da ita a mota a wahalarmun da ƴar matata." yana gama faɗin haka ya juya ya fice abunsa. Naji daɗin abinda yafada sosai ko ba komai ya wankemun bacin ran da umaimah ta samun, duk da nasan ba har zuciyarsa haka bane, dan umaiman yayi, kamar jiya daya ɗaukeni amma farincikin danaji baze misaltuba, dandai ammi tana gurinne dase na faɗa masa magana nima wanda zata kara kular da umaimah'n. Cikin jin kunya nayiwa ammi sallama nabi bayanshi. Aiko Umaimah ta shaka ba kadanba. Amma duk da haka ba gudu ba ja da baya a son mustapha yanzuma ta fara, wannan soyyayar dayake nunawa Maryam setayi duk yadda tayi ta dawo kanta seta jawo hankalinsa gareta kota yayane.......✍️ MESON COMPLETE WHATSAPP 08166674823