Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 39
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 39: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 39. Tsayawa yayi cak tare da juyowa ya kalleta, idanunta a…
3,136 words
Tsayawa yayi cak tare da juyowa ya kalleta, idanunta a rufe amma se shafa gadon take tana kiran sunansa, be ankaraba yaga tazo bakin gado garin lalubenta zata fadi, kafin yayi wani yunkuri harta fado kasan gadon. da sauri ya karasa ya tallafota jikinsa a hankali yace, "sorry" yana gyara mata gashin kanta dayake ƙoƙarin rufe mata ido. buɗe idonta tayi a hankali cikin shagwaba tace, "shine zaka tafi ka barni nikadai seya ƙara biyoni" cize lips dinsa yayi, cikin gajiyawa yace. "Babu wani lizard fa" tana matso hawaye tace, "Allah akwai nafa ganshi da idona" bece mata komaiba ya maidata kan gadon ya direta ya juya. kudundunewa nayi acikin blanket, har yanzu a tsorace nake da ganin kadangaren danayi. seyanzu na tuna babu komai a jikina se towel, gabanane yafadi dana tuna shifa ya daukoni ya kawoni dakinsa tunda bada kafata nazoba. "Yanzu haka ya ganni babu kaya fa" na fadi haka a raina. ganin ze shige toilet din nayi sauri nace, "nifa Allah tsoro nakeji bazan iya zama ni kaɗaiba" akufule yajuyo yace, "toilet din zan shiga dake?" ganin yanda yayi maganar fuskarsa a hade senayi ƙasa da kaina na fara hawaye. siririn tsaki yaja sannan ya shige toilet din. yayi danasanin sakawa Maryam lizard dinnan, gashinan yanzu bayajin daɗin jikinsa kokaɗan. ya dade yana a toilet din kafin ya fito, niko na makure a karshen gado cikin blanket, duk da da haske a dakin amma a matukar tsorace nake. kuka na fara ganin yaƙi fitowa da wuri. ɗaure da towel iya kugunsa ya fito, da wani ƙarami kuma yana goge sumar kansa. Tunda yafito yajita sarai tana shashsheka amma yaki kallon inda takema. karasawa gaban mudubi yayi ya farawa shafe_shafe. Ina ganin ya fito na sauke ajiyar zuciya amma bandena kukanba, ganinshi a haka yasa na runtse idona da sauri kirjina na dukan uku_uku, bantaba ganin namiji babba haka ba rigaba. juya masa baya nayi na kwanta badon babu kaya ajikinaba tashi zanyi infice inbar masa dakin. Duk abunda takeyi yana kallonta ta cikin madubi, tabe bakinsa yayi yacigaba da shirinshi. har ya gama shiryawa cikin wata jallabiya milk colour me kyau, maryam batayi shiru da kukan tabarar datakeba. dafe kansa yayi dayake matukar sara masa, yarasa dame zeji da kukannata dayake taɓa masa zuciya kokuma da abunda ke damunsa. ganin bata da niyyar yin shiru cikin tsawa yace mata. "Ki rufemun baki ko kuma na zaneki yanzunnan" hadiye kukan nawa nayi da sauri cikin tsoronsa. Ajiyar zuciya yasauke jin tayi shiru, ya lura shagwaba ce kawai ke damunta, seya mata da zafi_zafi sannan zasu shirya. zama yayi a bakin gadon, kallonta yayi yace, "tashi ki barmun ɗaki" a hankali nace "ni tsoro nakeji" "to tashi muje na cire miki lizard din" "um'um, nidai kakaini gurin ammi" na faɗi haka kamar zan fashe da kuka. shiru ya mata be ƙara ce mata komaiba. ƙasa ya sauka ya zauna kawai ya lumshe idonsa. har kusan ƙarfe ɗaya be ƙara koda kallon inda takeba yananan a zaune cikin yanayin damuwa. Maryam kuwa tuni bacci ya ƙara daukarta bayan tagama cin kukanta. har lokacin bayajin daɗin jikinshi, a hankali ya mike ya fice dankar ta farka. dakinta ya shiga ya dauke lizard din robar daya ajiye, har ya juya ze fita sekuma ya dawo ya buɗe wardrobe dinta, dogowar riga kawai ya ɗaukar mata da hijabi saboda sallah, kashe light din dakin yayi sannan ya fice. seda ya kashe na faloma sannan ya koma dakinsa. tananan yanda yabarta, kayan ya ajiye mata a gefen gadon, ya boye lizard din sannan ya shiga toilet ya dauro alwala, cikin dauriya yakeyin komai. be kashe mata light din dakinba, dan yanda take zabuwannan idan tatashi taga duhu seta cika gidan da ihu. fita yayi zuwa Masallaci.
Ƙarfe biyu da 'yan mintuna, na dare Maryam ta farka. A hankali ta buɗe idonta tana miƙa da salati dauke abakinta. yunkurawa tayi ta tashi zaune, domin tayi sallah kamar kullum tunda goman ƙarshe ta shiga. mararta taji ta daure tamau. yatsina fuska tayi ta janye blanket din data lullube jikinta. sakkowa tayi daga kan gadon tana daura towel ɗin jikinta. ware ido ta hauyi kozata ganshi a dakin ganin bayanan ta sauke ajiyar zuciya me ƙarfi, tama manta ba dakintabane seyanzu data mike ta ƙara wartsakewa. abunda ya faru kafin baccinta ne ya dawo mata kwanyarta. dakin na fara bi da kallo, domin yau shine shigowata ta farko tun tarewarmu. komai tsaf a kintse fes_fes, mayen kamshinsane kawai yake tashi a dakin. A fili nace "ashe ya iya gyaran dakin, amma da a gida ake masa." kayana na gani akan gadon, cike da mamaki na karasa ina dubawa. daukar rigar nayi nazira na daura towel a samanta, tunda babu komai a jikina kuma rigar shara_shara ce. toilet na shiga nayo alwala, masallaci har sun kusa idarwa, ƙarfe uku suke tashi dama. tunda zanyi fitsari nasan da matsala, dan inayin fitsarin marata na ƙara daurewa. ina tada sallah naji tsaiwar ta gagareni saboda juyamun da cikina ya farayi daurewa nayi, nayi raka'a biyu. ina sallamewa na durkushe a gurin hannuna dafe da cikina ina taune lips ɗina. "Ya Allah" na furta saboda wani murdawa da cikin yamun. kwanciya nayi akan dardumar ina juyi na rasa inda zan tsoma kaina, ciwon karuwa yake. ina nan kwance ina kuka da murkususu ya shigo dakin. ganinta a haka yasan ba kalauba. karasawa yayi kusa da ita ya tsugunna batare daya taɓataba yace, "menene?" jin muryarsa yasa natashi zaune da sauri, cikin azabar ciwo nace masa. "Ci..cik...cikina" muryarta na rawa saboda kukan danakeyi. wata murdawa da cikin yamun bansan sanda na faɗa jikinshi ba, hakan yayi dai_dai da fara zubowar jini daga ƙasana..........✍️ Meson complete Whatsapp 08166674823
ABINDA KASHUKA....*
_*ZEEY KUMURYA*_
*5️⃣9️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
..........Inajin dumin jinin nabin jikina amma nakasa motsawa balle nayi yunkurin tashi domin na tsafta kaina dan gudun kar jinin ya ɓata ni. Taune lips ɗina kawai nayi saboda azabar murdawar cikin, hawaye na zuba daga idona. sannu kawai Mustapha yakewa Maryam amma bata masan yanayiba. Dagata yayi da niyyar ya dakko wayarsa ya kira likitan ammi ganin ciwon bana ƙarau bane, da sauri ya saketa ta koma kijinnasa yana yamutsa fuska ganin jini ajikin rigarta kasancewar rigar tana da haske kuma babu komai acikinta. maida kaina nayi na kwantar a kan kirjinsa ina sauke ajiyar zuciya, idona na lumshe saboda fara sararamun da cikin da yayi, runtse idonsa yayi zuciyarsa babu daɗi, hakan yasashi kasa aiwatar da komai. A hankali na buɗe idona tare da yunkurawa na sauka daga jikinsa cikin tsananin jin kunya da takaici. cize lips ɗina nayi na daure na mike na fara jan kafata cikin dauriya na fice daga dakin zuciyata cike da tsananin kunyarsa, banajin ko ido zan iya ƙara haɗawa dashi a yau, gaskiya abunnan bemun adalci ba, yarasa a inda zezomun se'agabansa. ina shiga daki na cire hijabin jikina na wuce toilet. wanka nayi da ruwa me dumi na tsaftace jikina. Bayan na fito na dauko magani nasha sannan na kwanta, nama manta da wani batun lizard din jiya, ta kaina kawai nakeyi..... Cike da kyankyami ya buɗe idonsa jin tafice daga ɗakin, waro idonsa yayi waje yana bata fuska saboda ganin jinin har jikin jallabiyarsa ya ɓata. tsaki yaja ya mike da sauri ya shige toilet ya cire jallabiyar zuciyarsa harta fara tashi. dana sani kawai yakeyi akan sakawa Maryam lizard din da yayi a daki, da duk haka bata faruba, yana zaman_zamansa yajawa kansa ganin kazanta. yana jan tsaki ya wanke jallabiyar. cike da kyankyami ya goge dakinsa duk da jinin be diga a ƙasaba, tare da saka Room freshener. koda lokacin sahur yayi beci komaiba, ko ruwan tea beshaba, saboda tashin zuciyar dake damunsa, ze iya yin aman abu idan yaci shiyasa yakicin komai. Bayan ya dawo daga masallaci ya nufi dakinta domin yaga jikinnata. A Hankali ya tura kofar dakin ya shiga, tana kwance can ƙarshen gado ta takure jikinta kamar me jin bacci. karasawa kan gadon yayi yana kallonta, bacci take hannunta dafe da mararta. "Sleeping sickness" ya furta hakan a fili. juyawa yayi ya fita bayan ya duba maganin datasha ta ajiye sauran akan madubi. Bantashiba se wajen ƙarfe 11:00 am, Alhamdulillah cikin yasararamun sedan abunda baza'arasaba. Ayyukana nayi kamar kullum dana saba. Tea kawai nasha na nufi part din ammi......
Azumi uku kawai nasha nadora aka cigaba dani. cikin kwanakin da suke shude gaba-daya wasan buya nake dashi saboda kunyarsa danake ji. bana fitowa falo sena tabbatar ya fita, kafin ya dawo kuma zan gama komai na gudu part din ammi, idan yazo kiranane kawai muke haɗuwa. yau idan munkai azumi 29 ana saka ran gobe sallah, tun safe masu kitso da jan kunshi suka zo har gida suka mana. Kananun kitso nace amun, aiko nasha zama dan munfi awa biyu a zaune. gashi andauramun lalle a ƙafata. Umaimah se hararar Maryam take cikin hassada da kyashin ganin yawan gashin maryam ɗin, ita tana fama da kanta kamar me, dan bata da gashi kokaɗan, kitsonma dana na ƙari tace ayi mata ammi ta hana. har bayan azhar ina zaune, seda aka cire lallen na samu sa'ida. Zanen lallen yayi kyau sosai a farar ƙafata, gashi lallen ya kama sosai. Bayan ansha ruwa ina kwance a falonmu a ƙasa kan carpet, jikina duk a gajiye saboda aikin da mukasha yau, sanin danayi baya dawowa se bayan sallar isha'i shiyasama nazo falon na kwanta. labarai nake kallo, saboda inji koza'ace anga wata. banji buɗewar kofarsaba, balle shigowarsa se kamshin turarensa kawai naji. kallo bakin ƙofar nayi, da sauri na tashi zaune ganinshi ina amsa sallamar yayi gabana na faɗuwa, binsa nayi da kallo ta ƙasan ido, maimakon naga ya nufi dakinshi senaga ya karaso cikin falon ya nemi guri ya zauna akan 2 seater batare daya kalli inda nakeba. "Sannu da zuwa" na furta haka cikin sanyin murya kaina na ƙasa. kamar bejiba ko motsawa beyiba da sunan amsamun sema cigaba da danna wayarsa dayayi. kusan 3 minutes sannan naji yace, "yawwa" a can ƙasan makoshi kamar wanda akawa dole, batare daya dagoba. kamar na shareshi nima amma dai na daure na ƙara ce masa, "ga abincinka can akan dinning" girgiza kai yayi srioustly yace, "banacin abincin kazamai" waro idona nayi duka waje ina kallonsa, araina nace. "Kazama kuma? nice kazamar kenan yake nufi, to menayi na kazantar?" bakina na turo gaba tare bata fuskata kamar zanyi kuka nace. " Aini ba kazamabace?" banza yamun kamar bejiba. idona nane ya duri ruwa, naji babu daɗi sosai dayacemun kazama, gashi ina masa magana yana shareni. bansan sanda hawaye ya zubomun ba, duk da kokarin da nayi dan kar hakan ya faru. A hankali ya dago kansa ya kalleta. mamakine ya cika masa zuciya ganin tana hawaye. "To me aka mata?" Ya tambayi kansa. kallonta kawai ya tsaya yanayi yanda hawaye yaketa zuba daga idonta, kamar wadda aka daka. lumshe idonsa yayi yana fesar da numfashi. A hankali ya mike ya sauka ƙasan kujera, daf da ita ya zauna yana jifanta da wani kallo dashi kansha besan yanayiba. tafin hannunta yakama a hankali, wanda hakan yasasu jin sauyi gaba-daya ajikinsu. lallen da aka mata yakurawa ldo, kunshin ya burgeshi sosai. zamansa akusa dani yasa bugun zuciyata sauyawa, wani yarrrr naji a jikina lokacin daya kama hannuna. daurewa kawai nayi na lumshe ido. a hankali ya kai hannunsa ya fara share mata hawayen fuskarta dan yanzu yagane meyasa ta kukan. bakinsa yakai saitin kunnena cikin wani irin amon murya me narkar da zuciya yace, "what are you crying?" Batare dana buɗe idonaba na nuna shi da hannuna tsigar jikina na tashi. murmushi yayi ya kwantar da kanta akan kafadarshi. ajiyar zuciya na sauke me ƙarfi, ina ƙara lafewa ajikinsa. sosai nake tsintar kaina a wani irin yanayi a duk lokacin dana jini ajikinsa, yanayine me wuyar fassaruwa amma yanamun daɗi sosai, ina jin tamkar na dawwama ajikinnasa. kitson da aka mata ya shafa yace, "shine baki nunamun kitson sallar da lallenba ko?" cikin shagwaba nace, "bakaine kacemun kazama ba" bakinta data turo gaba ya shafa da finger dinsa yace, "bakazamar bace" kamar zan fashe da kuka nace, "Allah Ni ba kazama bace" wannan karon murde bakin yayi ganin ta ƙara turoshi gaba yace, "wacce kikamun ajikinafa" shiru nayi ina ƙara runtse idona cikin jin kunya. se yanzu nagane meyasa yacemun kazama. hannunsa yakai ya fara shafa cikina slowly, yace. "Ya jikinnaki" "na warke" na faɗa a wani irin baƙon yanayi saboda shafa cikina dayake. lips dinsa ya lasa tare da sauke numfashi ya cire hannunsa daga jikinta. raba kanta yayi da kafadarsa yana faɗin, "dagani Ni karkimun bacci a jiki" badan nasoba na bar jikinnasa. wayarsa dake gefensa ya dakko ya fara latsawa, mikomun yayi yana faɗin. "Take it" karbar nayi cikin rashin fahimta. Ganin bata ganeba yace, "Antinki keson magana dake" fadada fara'a ta nayi akan fuskata cikin jin daɗi na ƙara wayar a kunnena ina faɗin "Salamu alaikum" jin antin ta ɗaga. "Wa'alaikumussalam, Maryam ya gida." nace "lafiya kalau, Aunty nah, ya kowa da kowa" "lafiya kalau suke, ya ibadah" "Alhamdulillah Aunty, yaushe zakizo nayi missing dinki sosai" "munanan tafe tafe cikin sallah insha Allah" murmushi nayi nace, "Allah ya kaimu lafiya, ina aliya" Aliya dake gefen Aunty tana jiran ta bata wayar tace, "ganinan matar yaya, tun dazu nake mata alama ta bani wayar taƙi bani" dungura mata wayar Aunty tayi. Dariya nayi nace, "Aliya kina jin azuminnan kuwa, naji muryarki radau da karadinta" aliya tace, "hmmm idan ana sallah ba'a magana mairo, wlh azuminnan ya garani, Allah ya karba kawai. "Ameen ya Allah, ya skull?" "Skul Alhamdulillah munma yi hutu" hira muka shigayi da Aliya, aiko Aliya ta dage tanata zuba. Mustapha daya kurawa Maryam ido yana kallonta yanda take motsa ɗan karamin lips dinta bakaramin daukar hankalinsa yayiba. kawai jinayi ya kwace wayar. kallonsa nayi cikin mamaki, a hankali nace. "Meyasa ka kwace? bamu gama hirarmubafa" yana danna wayarsa yace, "kunsamu kati ne?" girgiza kai nayi alamar A'a. ina dubansa kamar zanyi kuka. dagowa yayi yamun kallon cikin ido, da sauri na lumshe idona dan bazan juri kallon kwayar idonshiba. numfashi ya sauke a hankali ya mike tsaye. bude idona nayi na sauke akansa a hankali ganin ya nufi kofa nace. "Fita zakayi?" juyowa yayi ya kalleni ya gyadamun kai. "Zan bika" na faɗa cikin sanyin murya, batare danasan sanda maganar ta fitoba. "Masallaci zani" ya fadi haka yana ficewa daga falon. murmushi nayi bayan ya fita, zuciyata cike da tsananin farinciki ganin ya fara sakemun yanzu, ba kamar farkon aurenmu ba. Mikewa nayi nima na shiga daki jin anfara kiran sallah, zuciyata cike da nishadi. ina idar da Sallah na yafa mayafin abayar dake jikina nanufi part din ammi. Suna zaune Dukansu matan gidan kowacce tana duba ɗinkin da tela yakawo ɗazu. da sallama nashiga. suka amsamun dukansu cikin fara'a, amma banda umaimah data haɗe rai tacigaba da duba kayanta. guri na samu na zauna ina gaishesu. Ammi ta dubeni tace, "Maryam kayanki suna dakina ki shiga dauko" cikin girmamawa nace "toh ammi, idan zan wuce zan dauka. Angode Allah yasaka da Alkhairi, yajikan mahaifa. murmusawa Ammi tayi cikin jin daɗin addu'ar Maryam tace, "Ameen ɗiyata, ina NOOR ne tun safe ban ƙara ganinshiba" ina ɗaukar Abul dake kwance a ƙasa ganin ya fara kuka nace, "dazu kuma ya fita Masallaci" tabe baki umaimah tayi cikin jin haushin Maryam, kayanta ta kwasa bayan taja tsaki ƙasa_kasa tayi dakinta. Mama da mama A'isha ma, nasu suka dauka suka fita. Aunty zuhura ta karbi Abul ta bashi nono. Bayan yagama sha na ƙara karbarsa ina masa wasa yanata bingiramun dariya. yaya sadam da mustapha ne suka shigo falon. Umaimah da fitowarta kenan daga ɗaki tace, "yaya NOOR sannu da zuwa" tana karashe maganar tana wani fari da ido. beko kalletaba ya zauna a gefen Maryam bayan sun gaisa dasu ammi, kamarma bejitaba. kallonsa nayi ya harareni ɗauke kaina nayi daga kansa nacigaba dayiwa Abul daketa bingiramun dariya wasa. kaina babu ɗankwali bansan jelar kitsona tafito ta gefen wuyanaba seda naji Abul ya riƙe mun. A Hankali nake ƙoƙarin kwacewa daga hannunsa dan kar yayi kuka, shikuma ya rikte gam yaƙi saki. Mustapha dake kallon Maryam ta gefen ido yana ganin abunda ke faruwa, murmushi yayi ganin Maryam se yatsina fuska takeyi. hannunsa ya zira ta bayanta ya zagayo dashi ya cire gashin maryam daga hannun Abul cikin dabara. Ɗaukar Abul ɗin yayi yana faɗin. "Seka cire mana gashin saboda mamanka umaimah bata dashi ko?"...
ABINDA KASHUKA...*
_*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_
*6️⃣0️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
..........Ya ƙarashe zancen da lakucewa Abul kumatu, shiko se bingira masa dariya yake abunsa. murmushi Aunty zuhura da YaSaddam sukayi me sauti. Umaimah kuwa sakin baki da hanci tayi tana kallonsa cikin tsananin baƙin ciki da takaicin yanda ya dizgata a gaban matarsa. ita mamakima take ko a ina yasan gashinnata oho?. kallonsa nake nima cikin mamakinsa, kamar bashi yayi maganar ba ya wani waske yanawa Abul wasa. A hankali ya juyo ya kalleni ya kannemun ido ɗaya tare da dagemun gira, lumshe idona nayi a hankali saboda salonnasa ya tafi dani. Mayafin Maryam daya ɗan zame yasaka hannunsa ya janyo tare da maida mata gashin daya fito ciki. numfashi na sauke a hankali still idona na lumshe saboda tattausan hannunsa daya taɓa gefen fuskata. umaimah ta hadiye wani yawu me daci da kyar, duk abunda mustapha yayiwa maryam akan idonta. mikewa tayi fuu cikin bacin rai ta shige dakinta. Dan idan tacigaba da zama a falonnan se zuciyarta ta buga. suna haɗa ido da ammi ta hararareshi tace, "ka kyauta ka batamun ran autah" murmushi ya mata kawai bece komaiba. numfashi na jawo na fesar da kyar na buɗe idona. batare dana kalli kowaba ba mike na shiga dakin Ammi na dakko kayana. Kafin na fito har yabawa yaya sadam Abul ya fice, sallama na musu nima nabi bayansa. yana zaune a falo idanunsa a lumshe na shigo falon bakina dauke da sallama ƙasa_ƙasa. A zuciyarsa ya amsa mata. Bedroom ɗina na wuce ganin be kulaniba, da niyyata inje innuna masa kayan sallar da ammi tamun. Bayan fitar su Maryam Ammi ta shiga bedroom din Umaimah ta rarrasheta, umaimah harda kuka dan bakin ciki. misalin ƙarfe 11 na dare ina kwance akan gadon idona a lumshe amma ba bacci nakeba, tunanin *heartbeat* kawai nakeyi, tunda nashigo dakin na kwanta amma nakasa bacci se juyi nake, har light din dakin na kashe. a hankali naji turowar kofar dakin gami da shaƙar kamshinsa. buɗe idona nayi amma ban motsaba zuciyata na ɗan bugawa. Kunna touchlight ɗin wayarsa yayi ya haska kan gadon, yasan dama zuwa yanzu tayi bacci. Ledar daya shigo da ita ya ajiye a gaban madubi. Seda ya ɗanyi jimmm, kamar me nazarin wani abu sannan ya fice. Ajiyar zuciya nasauke, na ƙara maida idona na rufe. Inajin kamar na tashi na bishi mu kwana tare amma bazan iyaba, duk yanda nakeson hakan dole na jure na hakura.....