Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 40
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 40: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 40. Washegari ranar idin sallah ƙarama, ranar da kowanne…
2,906 words
Washegari ranar idin sallah ƙarama, ranar da kowanne musulmi yake farinciki da fatan zuwanta, hakance ta kasance nima a gurina. Tunda asuba na tashi nayi ayyukana saboda nasamu damar zuwa sallar idi. kafin karfe bakwai nagama shirina cikin wata dakakkiyar shadda milk colour, tasha ɗinki me matuƙar kyau. feshe jikina nayi da turaruka masu sanyin kamshi. ledar dana gani tunda na tashi najanyo na shiga dubawa. Takalmane masu kyau kala biyu da jaka, da mayafai da sarka da ɗan kunne harda agogo duk a cikin ledar. murmushi nayi cikin jin daɗi. ƙarfe bakwai da rabi nanufi part din ammi cikin shirina tsaf na zuwa Masallaci. Acan na tarar da yaya sadam da Aunty zuhura suma cikin shirinsu. Gaisawa mukayi cikin fara'a. Ammi bata falon hakan yasa na wuce dakinta. bansan yana cikiba seda nashiga na ganshi zaune gefen gadon ammi da waya kare a kunnensa alamun waya yake. zama nayi akan carpet din dake gaban gado bayan mungaisa da Ammi, ina satar kallonsa ta gefen ido. yayimun kyau sosai fiye tunanin me karatu, shadda ce fara ƙal ajikinsa, kansa dauke da hula wadda ta masa kyau bakadanba. ƙasa dauke idona nayi daga kansa. Maganar ammi naji tana cewa, "NOOR kabata wayar su gaisa da UNCLE dinnaka, kullum yana tambayata ita amma basu taba gaisawaba. gyada mata kai mustapha yayi sannan ya mikawa Maryam wayar. tashi nayi a hankali naje na karbi wayar ina kallonsa shima kallonnawa yakeyi se idanunmu suka sarke cikin na juna. Runtse nawa idon nayi da sauri saboda yanda naji bugun zuciyata ya sauya. kara wayar nayi a kunnena tare da faɗin "Assalamu alaikum" cikin murya me cike da nutsuwa naji ance, "wa'alaikimussalam" "ina kwana" na furta hakan bugun zuciyata na karuwa. "Lafiya kalau, *Maryama*" yanda na faɗi sunannawa senaji wani iri a zuciyata dana kasa tantance menene, numfashi na jawo na fesar da kyar nace. "Dafatan anyi sallah lafiya".... Mungaisa dashi sosai, yamun addu'oi dafatan nasara arayuwata. godiya na masa na mikawa yaya wayar. Bayan sun gama wayar mustapha ya dubi ammi yace, "yace zezo cikin watannan insha Allah" da'alamun mamaki akan fuskar ammi tace, "dakuma yacemun baze samu zuwaba, saboda ayyuka sunsha masa kai sedai wani watan." "Hakadai yacemun yanzu" mustapha ya fadi haka yana mikewa da niyyar fita. "To Allah yakaimu lafiya." Gaba dayanmu gidan muka dunguma zuwa masallaci. Nida ammi da umaimah muka hau motar yaya. Aunty zuhura, da mama da mama A'isha da mijinta suka hau motar yaya sadam. Anyi sallar idi lafiya antashi lafiya sedai fatan Allah ya maimaita mana. bayan antashi Aunty zuhura tayiyyi mana pictures a wayarta sannan muka dawo gida, aka cigaba da hidimar Sallah......
*KADUNA*
Aunty ce tafito cikin shirinta na zuwa Masallaci dakin da suhailat da aliya suke ta nufa domin takirasu ganin sunki fitowa. da sallama ta shiga amma saboda cacar bakin dasukeyi basujiba. tsayawa kawai Aunty tayi tana kallon aliya dake magana cikin tsiwa. "Wlh nidai nagaji da kazantarnan taki gaskiya, amma kome zaki faɗa sedai ki faɗa Ni... Tsawa Aunty ta daka mata da faɗin. "Aliya mene haka? wanne shashancine wannan?" Cikin bacin rai aliya tace, "Aunty kullum fa bata ɗauke ko tsinke a dakinnanan amma bana magana haka zangyara, amma baya jimawa ta ƙara batawa, yauma ina tashi na gyara shi amma daga fitowarta daga wanka harta fara batawa, danna mata magana ta fara zagina wai zan mata rashin kunya, ko dan naga gidanmu tazo." Rai a haɗe Aunty tace mata. "Shine dan baki da kunya zaki faɗa mata haka, sa'arkice. Kuma dan bata gyara dakiba seya zama abun magana bakya ganin bata da lafiyane." Aliya zatayi magana Aunty ta katseta da sauri. "Banason na ƙara jin bakinki anan, zoki fice kikirawomun abbanku mu wuce, karmu makara." Aliya kamar zatayi kuka dan takaici ta fice ɗaga ɗakin. Fuska babu walwala Aunty ta dubi suhailat dake cika tana batsewa ganin bata da alamun shiryawa tace, "ke bazaki masallacin bane?" Suhailat na yamutsa fuska tace. "Banajin daɗin jikina bazan iya zuwaba." wani kallo Aunty ta mata me kama dana tuhuma harseda suhailat ɗin ta tsargu sannan ta fita batare datace mata komaiba. Suna tafiya a mota ammi ta dubi aliya cikin ƙasa_ƙasa da murya dan kar abbanta dake gaba yaji tace mata. "Kidena kula suhailat kuna hayaniya, yar uwarkicefa Aliya, kuma gaba take dake." aliya kamar zatayi kuka tace, "Aunty itacefa..." Cikin lallami Aunty ta katseta da faɗin, "kiyi hakuri da duk abunda zata miki, kidena kulata kinji 'yar albarkata" gyada kai aliya tayi tana turo baki gaba. Bayan sun dawo daga masallacin sunci abinci ammi ta nufi ɗakin da suhailat take. suhailat tana kwance tana aikin kallon hoton mustapha daya zame mata jiki Aunty ta shigo dakin. zama Aunty tayi akan gado tana duban suhailat dabatasanma ta shigoba tanacan tana tunanin Mustapha tace. "Suhailat!" Firgigit suhailat ta dago ta kalli Aunty, amma tagaza cewa komai. Aunty bata damu da yanayin datake cikiba tace, "meyake damunkine wai naga bakida walwala.?" Idantane ya kawo ruwa cikin raunin murya tace. "Inason ganin yaya, nayi kewarsa" Aunty na tsareta da ido tace. "Bayan wannan fa?" tana kauda kai daga kallon Aunty tace. "Nothing" fuska babu walwala aunty tace. "Suhailat kina boyemun kina da ciki ko?" Rassss gaban suhailat ya yanke ya fadi duk tsagerancinta seda ta girgiza dajin Aunty ta gane tana ciki. Tashi zaune tayi cikin rudu tace, "Aunty ciki kuma?" Harararta Aunty tayi tana ƙara haɗe rai tace. "Karki ƙara yunkurin boyemun, tun kafin kizo duniya nake ganin mata masu ciki, kuma nake ganesu. Tun kafin azumi nagane ciki gareki ta alamomi masu yawa da suka nuna musamman yanzu da cikinnaki ya fara fitowa." Aunty ta ƙarashe zancen tana kallon cikin suhailat daya fara dagowa dan wata huɗu da kwanaki. suhailat kasa magana tayi se kuka data fashe dashi. Tausayintane ya kama Aunty, duk da abu yana tadda hali amma suhailat mommy ce ta cuceta dabata tarbiyya tagariba. Lokacin da Aunty ta gane suhailat tanada ciki bakaramin dimuwa da damuwa tashigaba. ƴar ɗan'uwanta guda ɗaya jal daya mutu ya bari itace da wannan abun kunyar, tasan baƙaramin tashin hankali daddy ze shigaba idan yaji wannan zancen, shiyasa har yau ta kasa sanar masa......Muncigaba da shagulgulan sallah cikin kwanciyar hankali, munjejje unguwa da ammi munje gidan su Aunty zuhura har danginsu mama duk mun zazzaga.
Yau Biyar ga sallah tun asubar fari mommy ta sauka a garin Kano. Tun kafin azumi suka baro garin NIGER, Binta ta dawo Nigeria yayin da mommy ta wuce ƙasar da suka zauna acan baya tayi azuminta acan, a cewarta bazata iya azumi a naija ba rana tayi yawa. se washegarin sallah ta dawo Nigeria ta sauka a garin Abuja gidan wata kawarta matar wani ɗan majalisa, seyau kuma tayi asubanci ta biyo jirgin ƙarfe 6 na safe zuwa Kano, batason asan da dawowarta harta se ta gama gudanar da kudirinta akan daddy da mustapha harma da maryam. shiyasa ta dako sammako dan karma wani daya santa ya ganta. Tana sauka a filin jirgi ta saki wani murmushin da ita kaɗai tasan ma'anarsa, zuciyarta fari ƙal tanajin kamar burinta ya gama cika. Driver'n ta data kira tun daren jiya ta sanar mata zuwannata yana gurin yana jiranta. Jan trolly dinta tayi ta nufi inda ta hango motarsa. dasauri ya fito daga mota shima ya karbi trolly'n hannunta yana jera mata sannu da zuwa cikin girmamawa. a ƙasaice ta amsa masa. Buɗe mata gidan baya yayi ta shiga, shima yazagaya ya shiga driver seat bayan yasaka trolly'n nata a But. gidanta dake lamido cresent tace yakaita. Cikin mintuna 20 suka karasa gidan kasancewar hanyar babu go slow tunda safiyace. Har cikin falo driver'n yakaimata kayanta. mommy dake tsaye tana karewa falon kallon cikin tsananin mamaki, ko sauraren sallamar dayake mata batayiba, ganin falon duk yayi kura. dakin da suhailat ta zauna ta nufa tana kwada mata kira, amma taji shiru. mamakine ya ƙara kamata ta shiga dube gidan tana kwala kiran sunan suhailat ɗin amma taji tsit. hankalintane ya fara tashi, cikin sauri ta fito ta nufi dakin megadi ta kwala masa kira. megadi dake ƙoƙarin komawa baccin da zuwan mommy ya katse masa ya fito da sauri daga dakinsa. A rude mommy tace, "inuwa ina yarinyar dana bari a gidannan?" Megadi na kallon mummy da mamaki yace, "wacce fa?" "Yarinyata dai dana bari budurwa, kafin na tafi nace maka karka barta ta fita ko da leke" megadi yace. "To to, nagane. Ai wata matace tazo suka tatafi da ita." Agigice mummy tace, "what? wacce matar?" Megadi daya fara ɗan firgita yace. "Bansantaba Hajiya" cikin tsawa mommy tace, "bakasantaba shine kabari tafitarmun da yarinya, saboda bakasan me kakeba, bakasan aikinkaba." Masifa mommy ta masa sosai kamar zata cinyeshi ɗanye. shikuma yanata aikin bata hakuri, bata saurareshiba ta wuce ciki fuuu, bayan ta tabbatar masa da duk abunda yasamu yarinyarta seta hukuntashi. tana shiga falon ta buɗe handbag dinta ta dakko wayarta jikinta na tsuma tayi dialing number suhailat. Suhailat na kwance tana baccinta wayarta ta fara vibrate, har Kiran ya katse bata dagaba. seda mommy ta mata 3 missed call sannan tatashi dakyar ta janyo wayar tana jan tsakin katse mata baccinta da akayi. batare data duba wake kirannataba ta ɗaga wayar tare da karawa a kunnenta. "Suhailat!" Mommy ta faɗa da ƙarfi. Zunbur suhailat ta tashi zaune tare da cire wayar daga kunnenta ta duba wanda yakirata. *Sweet mom* ta gani. "Suhailat bakya jinane" mommy ta ƙara faɗa. Cikin damuwa suhailat tace. "Mom, se yau kika tuna dani?" Cikin faɗa mommy tace, "niba wannanba suhailat, wacce matar ce tazo ta daukeki har gidana?" "Aunty ce" ta bata amsa. "What!? Aunty, wacce Aunty'n?" Mommy ta tambayeta cikin karaji. "Aunty'n Kaduna mana" "kina nufin saudart" "eh ita" mommy tana kankance ido cikin bala'i kamar suhailat na ganinta tace. "Waya faɗa mata inda kike?" Suhailat data fara gajiyawa da faɗan mommy tace. "Nina faɗa mata" mommy tace, "akan me to, banayi warning dinkiba kafin na tafi, kuma ina matar dana barku tare a gidan?" Suhailat tace, "kirana tayi a waya shine na faɗa mata, ita kuma matar aranar da muka taho ta sallameta tatafi." masifa mommy ta shiga yiwa suhailat kamar taɓabbiya akan bin Aunty datayi, a karshe tace mata kuma ta shirya kayanta zata turo a ɗauketa a yau dinnan, suhailat ta amsa mata sannan mommy ta kashe wayar. Babu ɓata lokaci suhailat tatashi ta hau haɗa kayanta, dama zaman gidan auntinnan duk a takure take jinta. Aliya bata dakin tana kitchen suna haɗa breakfast dan yau zasuje Jos sukaiwa su maryam ziyara. Aunty ce tashigo ɗakin ɗan ganin ko suhailat tatashi. ganin yanda suhailat ɗin take haɗa kayan se Aunty ta tsaya turus tana kallonta kawai. can ta nisa tace, "kayan me kike haɗawa haka suhailat, bafa dadewa zamuyi a Jos dinba, jibi insha Allahu zamu dawo" suhailat tana haɗa kayan yari dinta tace, "Aunty nifa Kano zankoma" aunty na mata wani kallo tace. "Akanme?" Shiru suhailat tayi dan batasan me zata cewa Aunty ba. Babu wasa a fuskar Aunty kokaɗan tace, "ki hada kayan da zaki bukata na 2 days kamar yadda nace miki jiya, ki kuma shirya, karki bata mana lokacin" tana gama fadar haka ta juya ta fice. suhailat tabi bayanta da kallo ranta babu daɗi. ta rasa wazatabi maganarsa mommy ko Aunty? zama tayi kawai a bakin gado ta rafka tagumi. Tasan halin Aunty sarai, tun tana yarinya. Aunty nada hakuri amma bata daukar raini ko wani mis_behav. Mommy kuma yanzu ta koyi yimata masifa amma duk da haka tafi tsoron Aunty akan mommy, kuma bazata bijirewa Auntyba dan tasan ita kaɗaice zata sa mustapha ya yayarda ya aureta, dan haka dole tadinga bin umarnin ta. badan tasoba ta tashi ta ƙara haɗa kaya kamar yadda Aunty tace mata. Ƙarfe tara suka fito cikin shirinsu tsaf suka yiwa masu aiki sallama da abbansu aliya driver'n Aunty ya daukesu zuwa Jos. Suna fara tafiya mommy ta Kira suhailat, seda ta saci kallin aunty sannan ta ɗaga, amma ta kasa magana. Mommy tace, "daughter ga shinan naturo za'azo a daukeki" kasa_kasa suhailat tace, "mommy bama kaduna fa" a harzuke mommy tace "kuma ina?" "Munje wani gida da su Aunty a Jos, amma yanzu muna hanyar dawowa, idan muka dawo sena kiraki" tsaki mommy taja tace, "to sekun dawo ɗin, karfa kifada mata na dawo garinnan, dan banaso kowa yasani." "Toh mommy bazan faɗaba" har mommy zata katse wayar tatuna tace, "dafatan dai baki faɗa mata maganar cikinnanba" satar kallon Aunty suhailat tayi tace. "Ehh" daga haka sukayi sallama.
Yau ina cikin farinciki, wanda kallo ɗaya zakamun kagano hakan saboda zuwansu Aunty. Tun jiya muka fara haɗa musu delicious, yauma munayin sallar asuba muka fara. Se wajen 12 muka gama komai. Part dinmu na koma naɗan kwanta akan gado da nufin na ɗan huta bansan sanda bacci ya ɗaukeni. Su Aunty sun iso lafiya inda aka musu masauki a part din ammi. Su mama dasu ammi se maraba da zuwa suke musu. Aliya kam baza ido takeyi taga ta inda zataga Maryam ɗinta ta bullo. Suhailat kam kallon su kawai take da mamaki, tasandai wadannan ba yan'uwan daddy bane sedai ko yan'uwan babansu aliyane. Amma duk inda ammi tayi se binta take da ido. Bayan sungama gaisawa ankawo musu ruwa sunsha Aunty tace, "ina Maryam ne da Muhammad?" Ammi tace, "bari nakirasa naji" ta ƙarashe zancen tana latsa wayarta tayi dialing number mustapha. Mustapha yana kwance a dakinsa akan gado kiran ammi yashigo wayartasa, dauka yayi ya daga ammi ta sanar masa su Aunty sun iso suzo shida Maryam. Mikewa yayi da hanzari ya fito ya nufi dakin maryam. Fitowata daga wanka kenan ina shiryawa naji ana knocking, sauri nayi na karasa shirinnawa sannan na buɗe Kofar. kallo ɗaya yayi mata ya dauke kansa, kamar bayason yin magana yace. "Su Aunty sun karaso" bandamu da yanda yamun maganaba dan naga kwana biyu miskilancinnasa ya motsa. faɗaɗa fara'ata nayi cikin jin daɗi na dakko mayafina nabi bayansa. Sunata shan hirarsu yayi sallama ya shiga falon. da sauri suhailat ta mike tsaye jin muryarsa da kuma ganinsa da tayi un_expected da ƙarfi tace, "yaya!" cikin tsananin mamaki da farinciki tana waro idonta waje, domin bata taɓa tsammanin ganinsa a wannan lokacinba a kuma nan garinba. kallo ɗaya ya mata yaɗauke kansa batare dayace mata ƙala ba. suhailat babu jira ko tunanin komai ta taho da gudu ta faɗa jikinsa ta rungumeshi tana murmushi cikin tsananin murnar ganinsa. daidai lokacin Maryam ta ƙaraso falon. Tsayawa nayi cak cikin matsananciyar faduwar gaba, Muryar Aunty suhailat ce ta tabbatarmun da itace inda take cewa. "Yaya i missed you so much" kallonsa kawai nakeyi naga yanayin re_action ɗin dazeyi ina ƙoƙarin fizgo numfashina ganin yana ƙoƙarin daukemun. Wani irin kishi naji acikin raina ganin wata mace kwance a kirjin mijina, bansan ya a kayiba kawai gani nayi najuya na fice daga falon ina haɗe hanya. Cire suhailat yayi daga jikinsa batare yace mata komaiba yana yamutsa fuskarsa kamar yaga kashi shima ya juya yabi bayan Maryam. suhailat dabatama lura da zuwan Maryam ba, balle tasan ita tabi ta taho itama zata bishi. Tsawar da Aunty ta matace yasa ta tsayawa zatayi magana ammi ta ɗaga mata hannu, fuskarta a haɗe tace. "dawo ki zauna" suhailat kamar zatayi kuka ta dawo ta zauna tana leken kofa. Umaimah kallon suhailat take cikin kishi, yanda tayi ya tabbatar mata da itama son mustapha'n take.
Part dinmu na nufa na faɗa kan kujera ina sakin kuka, wani irin zafi da daci nakeji a cikin zuciyata, duk murna da farincikin zuwansu Aunty danake ya gushe. Banmasan haka nake da kishiba seyau, idona yarufe gani nake yayan shima ya rungume suhailat ɗin, kifa kaina nayi a hannun kujera ina sakin kuka mara sauti dana tuno yanda suhailat ta kwanta a kirjinsa. Yayi 3 minutes tsaye yana kallon Maryam da batasan yana tsayenba, a hankali ya tsugunna zuciyarsa babu daɗi ganin tana kuka ya dagota tare da janyota a hankali ta faɗa jikinsa. Rikesa nayi sosai ina ƙara volume din kukana, tare da sakin ajiyar zuciya. Lumshe idonsa yayi zuciyarsa na bugawa jinta ajikinsa. A hankali yasa tattausan hannunsa ya dago fuskarta. Narkarkkun idanunsa ya zuba acikinnata idon dake cike da hawaye. dif na hadiye kukannawa ina kallonsa nima, duk yanda naso nadauke idona daga cikinnasa amma nakasa. Kallon cikin ido mukewa juna, sosai bugun zuciyata yake ƙara ninkuwa, ganin bashi da niyyar dena kallona na runtse idona, wani abu naji yana yawo ajikina a sanadiyyar wannan kallonnasa dana kasa gane masa. Mustapha kallon Maryam yake with out control, batare daya saniba. Komai ya kwance masa daga kwanyarsa fuskarta ya matso daf da tasa har sunajin hucin numfashin juna, tare da bugun zuciyoyinsu. hawayene suka cigaba da shatata daga idona, ga tsoro da fargaba danaji sun lullubeni saboda betamun irin hakaba tunda muke, bamu taɓa kusanci me taɓa zuciya irin wannan ba, duk da idona a rufe yake amma nasan be dauke idonsa daga kainaba, saboda yanda nakejin wani abu kamar tsinkewar jini ajikina. Lumshe idonsa yayi tare da fesar da numfashi cikin wani irin yanayi mara misaltuwa. A hankali yake ƙara kusanto da fuskokinsu, bakinsa ya dora akan lips din Maryam batare daya shiryawa hakanba. zabura nayi cikin tsananin tsorata na fara kokawa da numfashina dake ƙoƙarin daukemun saboda dimuwa, kuka na saki ina ƙoƙarin raba jikina da nasa. Ajiyar zuciya ya sauke me ƙarfi yana ƙara manneta da jikinsa karon farko a rayuwarsa ya fara sucking lips ɗinta cikin tsananin zaƙuwa........✍️
*BARKANMU DA JUMA'ATU BABBAN RANA🕋*
COMMENTS Meson complete Whatsapp 08166674823
ABINDA KASHUKA....*
_*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_
*6️⃣1️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*