Kenza eBookz

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 41

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 41

Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 41: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 41. ...........Jikinane ya kama kyarma jin yanda yake tsotsar…

3,268 words

...........Jikinane ya kama kyarma jin yanda yake tsotsar lips ɗina kamar ze ciremun. yanda jikin Maryam yake rawa haka shima Mustapha jikinsa yakeyi, se numfashi yake fitarwa da sauri da sauri yana ƙara manneta da jikinsa kamar ze maidata ciki. Yakai 7 minutes yana kissing ɗinta cikin nutsuwa da salo me wuyar mantawa da tsayawa arai. a hankali ya zare bakinsa daga nata yana maida numfashi badon ya gaji da kissing ɗinnataba sedan kawai ya barta ta sarara. lumshe idonsa yayi cikin mawuyacin hali na bukatuwa da ita. Ni kuwa boye kaina nayi a kirjinsa ina maida numfashi kamar wacce nayi tseren gudu, har yanzun hawaye be bar zuba daga idonaba. A hankali cikin dauriya ya dagota daga jikinsa domin zamanta ajikinsa yana ƙara masa feeling. fuskarta ya dago da tafin hannunsa a karo na biyu ya zuba mata tsumammun idanunsa da suka rine sukayi ja, wanda suke ƙara rikitata. Idanunsa cikinnata yasa tafin hannun damunsa a hankali ya fara share mata hawayen fuskarta. rufe idona nayi ina turo baki gaba nace, "kadena kallo na haka" murmushi ne ya subuce masa dabe shirya masaba. cikin wata irin murya kamar me rada yace, "why?" a shawabe nace, "ina jin wani iri a jikina" be ƙara cewa komaiba ya sakeni. A hankali na mike da kyar jikina kamar anmun duka saboda kasala, ban ƙara dubansaba na nufi ɗakina na nashige domin na wanke fuskata. Binta yayi da kallo har ta shige, ajiyar zuciya ya sauke yana maida numfashi, harna fito yana zaune a falon yanda na barsa, sena ganshi kamar mara lafiya kokuma wanda wani abu ke damunsa, senaji duk babu daɗi ganinsa a haka, kamar na tambayesa abunda ke damunsa,tunawa da nayi su Aunty sun jima da zuwa, sena ja ƙafata na fice daga falon cikin sanyin jiki. seda nazo zan shiga falon kuma naji wani iri na abunda danayi sanda naga suhailat a jikin yaya, wata kunyar su naji ta lullubeni, musammanma ammi. Daurewa nayi na shiga falon da sallama. suna falon gaba-ɗaya sunata shan hirarsu, su ammi sun cikawa su Aunty gabansu da kayan ciye_ciye da drinks. suka amsamun sallamata atare amma banda umaimah da suhailat data dago da sauri jin Muryar Maryam. Da gudu Aliya tataso ta rungume maryam cikin tsananin murna. Nima rungumeta nayi ajikina cikin farin ciki. Suhailat kallon Maryam kawai take da matuƙar mamaki. " _kamar maryam me aikin mommy ?_" suhailat ta furta hakan aranta cikin tantama, tana tunanin ba Maryam din bace, kamace kawai, dan wannan tafi Maryam ɗin data sani fari da kyau gami da wayewa. sakin juna mukayi da aliya cikin murmushi, ƙasa_ƙasa tayi da murya yanda ni kaɗai zanji tace, "matar yaya, mene sirrinne? Irin wannan kyau haka, ga abubuwa se juyawa suke duk kiwon yayannawane haka?" Harararta nayi nace, "daga zuwanki zaki fara, Ni matsamun inje gurin auntynah" dariya aliya tayi, Ni kuma na wuce gurin Aunty daketa sakin murmushi tun shigowar Maryam, daga yanda taga Maryam ɗin tasan tana cikin kwanciyar hankali. Suhailat Binta tayi da ido kamar wata doluwa. Rungume Aunty nayi ina faɗin "oyoyo Aunty nah, dafatan kunzo lafiya" aunty na ƙara faɗaɗa fara'arta tace. "Lafiya kalau Maryam dita, dafatan kina lafiya?" "Lafiya lau Aunty" na faɗi haka ina sakinta da murmushi dauke a fuskata. Suhailat ta haɗiye wani yawu tana duban Aunty tace. "Aunty wai wannan Maryam ɗin dana sanice house girl dinmu?" cikin rashin jin dadin house girl da suhailat ta kira Maryam Aunty tace, "ehh" maida kallonta tayi ga Maryam cikin tsananin mamakin yanda taga yarinyar ta sauya mata. Ba yabo ba fallasa nace, "ina wuni Aunty suhailat" tana ɗauke idonta daga kallon Maryam ɗin tace. "Fine" zuciyarta cike da mamakin wai gidan waye sukazo? da taga Maryam da yayanta. Tasan dai Aunty tace mata yaya yayi tafiya ne, to kenan nan garin shine inda yazo, to ita kuma Maryam ɗin metake a gidan? "May be nan ɗin ma aikatau tazoyi" suhailat tabawa kanta a cikin zuciyarta. (Ke kaɗai dai🤕) ƙara kallon kofar falon tayi a karo na ba adadi sannan ta juyo ta dubi Aunty tace, "wai ina yayanne Aunty, naga haryanzu be ƙara shigowa ba?" Harararta kawai Aunty tayi, bata bata amsaba cikin takaicin yanda take nuna rashin kunyarta a fili a gaban kowa, tun daya fita take ta maganarsa ita tayi missing ɗinsa kaza_kaza. Aliya ta dubi Maryam tace, kawata zo innuna miki wani abu" ta faɗi haka tana latsa wayarta. tashi nayi fuskata dauke da murmushi na koma kusa da aliya. tana cigaba da latsa wayartata tace, "Ina yayan wai?" "yana part dinmu" na bata amsa. wayartata ta mikomun tana faɗin "kalli hotunan kayan nan" karba nayi nafara kalla, waro idona nayi waje saboda ganin hotunan wasu ƴan'iskan kaya wanda idan mutum yasasu basu da maraba da tsirara. kallonta nayi so surprise nace, "wannan kayanfa ina kika samosu aliya?" wani murmushin tayi tace, "kike wani zaro mun ido dankinga wannan kayan, to sune tsarabar dana kawo miki" ƙara waro idona nayi waje nace, "inye me dasu Aliya?" Hararata tayi tace, "bangane kiyi me dasu ba, kiyiwa yayana kwalliya mana" nima harartata nayi nace, "kwalliyo mata, to ba daniba wannan tambaɗar, a inama kika samo kayanma tukunna?" "Bansabiba ke, tunda na miki gwanintama ban burgekiba kinsan wahalar danasha kafin nasamosu?" ganin yanda tayi da fuska senayi murmushi nace, "haba kawas, kema kinsan ba haka bane, kinsan babu ta yanda za'ayi in iyasa wadannan kayan ajikina" "to cewa nayi kisa kifita dasu, mijinki kawai zakisawa ya gani ai" kallon aliya nayi baki buɗe, araina ina faɗin. "Abunda baze taɓa yiyubama kenan" kafin wani acikinmu ya ƙara magana, Ammi ta katse mana muhawarar tamu da faɗin, "yata kizo kuci abinmana karyayi sanyi, tun dazu ankawo muku amma kunki ci kamar wasu baƙi" tana kallon Aliya tayi maganar. cikin girmamawa aliya amsa mata da "to" sannan tatashi ta nufi gun dinning, ta barni da wayarta a hannu. Suhailat ma seda ammi ta mata magana sannan ta mike itama. Umaimah ta rakata da harara, tunda suka zo ƙala bata haɗasu da suhailat ɗin ba, ta lura yarinyar nada jin kai da dagawa ga kuma fuskanta datayi itama tanason abunda takeso wato Mustapha....

Mustapha yayi fiye da 20 minutes a zaune a inda Maryam ta barshi, koda ƙwaƙwkwaran motsi beyiba, saboda yanda yakejin wani feeling na bijiro masa, se sassauke numfarfashi kawai yake a wahalarce. ganin zaman baze ƙaresaba ya mike da kyar, yana taune lips dinsa ya wuce bedroom ɗinsa. Rage kayan jikinsa yayi ya shige toilet yasakarwa kansa ruwa, kozeji sauƙin abunda yakeji ajikinsa. Suna cikin cin abincin suhailat ta dubi Aunty tace, "Aunty wai nan gidan wa mukazo" batare da Aunty ta kalletaba tace, "gidan freind ɗina ne" da mamaki suhailat tace, "Amma me ya kawo yaya gidan?" Kafin Aunty ta bata amsa mustapha yashigo falon da sallama. a tare suhailat, umaimah da Maryam suka kallesa zuciyar kowaccensu cike da kaunarsa. Maryam ce ta fara janye idonta daga kansa ta maida kan wayar dake hannunta tana amsa masa sallamar da yayi. mikewa suhailat tayi da sauri, cikin daka tsawa Aunty tace mata. "Dawo ki zauna ki ƙarasa cin abincin ki" cikin sangarta suhailat tace, "Aunty nina koshi da abincin kibarni naje naga yaya, nayi kewarsafa over wlh" tabe baki aliya tayi tacigaba da cin abinta. Aunty na ƙara haɗe rai tace, "nace ki dawo ki zauna ko?" Suhailat kamar zatayi kuka, ta koma ta zauna tana kunkuni aranta. becewa kowa ƙala ba, se Maryam dayabi da kallon ƙasan ido ya nufi gurinsu Aunty. Aunty na kallonsa da fara'a tace, "son manya, nayi zaton zakuzo mana yawan sallah ai" murmushi yayi ya kawar da zancen da faɗin. "Kun zo lafiya" "lafiya ƙalau son, ya al'amura dafatan anyi sallah lafiya?" Shafa kansa yayi yace, "lafiya" atakaice yana kallon suhailat data kura masa ido kamar zata cinyeshi ɗanye. Aliya cikin nutsuwa tace, "yaya ina wuni" batare daya kalletaba ya amsa mata, yana jan kujerar kusa da Aunty ya zauna. Mikewa suhailat tayi tsama ta nufo gurinsa da niyyar hugging ɗinsa, wani mugun kallo ya watsa mata saboda gane nufinta da yayi. sanin halinsa da tayi yasata tsaya kamar zatayi kuka tace, "yaya baka kulaniba" kallonta yayi yana ɗan sakin fuskarsa yace, "how are you" "fyn and you" ta bashi amsa da haka cikin farin cikin ganinsa, banza ya mata bebata amsaba. Komawa tayi ta zauna cikin karayar zuciya, fargaba da tsorone suka cika mata zuciya, dan batasan matsayin soyayyartaba yanzu a gurinshi, amma dayake tasan halinsa na miskilanci ko a da canma haka yake mata, seta dauka yanzumma hakane........

Bayan sungama cin abincin suka koma cikin falon, hira suka shigayi da Aunty, gabadaya akan kasuwan daddy ne da kuma ciwon Sadiq, har mustapha yacewa aunty yaso zuwa dubashi amma daddy ya hana, Aunty tace masa. "Ai jikin Sadiq ɗinma yayi sauƙi, a satinnan zasu dawo seyaje ya dubashi a gida." suna cikin hirarne aunty ta dubeshi tace, "karka nunawa suhailat Maryam matarkace a yanzu, kayi duk yanda zakayi karta gane, na gargadi Aliyama tun daga gida akan haka." da mamaki yake kallon Aunty amma bece komaiba. Aunty ta cigaba da magana da faɗin, "saboda banaso Aunty Atika ta sani yanzu, kuma idan suhailat ta sani kamar ta sanine, Allah shine abin tsoro, amma kaji tsoron sharrin mutum ma, kuma ko badan Aunty atikaba, suhailat ɗinma idan tasani hauka zata mana a gidan mutane kasan halinta dai sarai." gyadawa Aunty kai yayi amma yasan dole se suhailat ɗin ta sani ko a bakin su ammi ne. suka cigaba da hirarsu cikin kaunar juna. Niko part ɗina naja Aliya muketa hirarmu cikin nishadi, aliya dabata gajiya se zuzuta kyan dana ƙara takeyi. Suhailat kam tana dakin da suka sauka tana shan baccinta.

Da daddare muna daki nida aliya a part din ammi, wani littafi nake karantawa me daɗi a wayarta, dazu take bani labarin book ɗin, shine nace tabani nakaranta. tanatamun hira Bama saurarta nakeba. Aunty ce tashigo ɗakin, bayan tayi sallama mun amsa mata tace. "Maryam ki tashi ki koma part dinku dare yayifa har goma saura." Batare da tunanin komaiba nace, "Aunty anan zan kwana yau" "nan ina?" Aunty ta tambayeta haka. "Aunty anan tare daku" wani kallo Aunty ta mata fuskarta babu wasa tace, "tashi ki wuce ni, banason shiririta" tashi nayi daga kwancen danake badon nasoba, sedan bazan iya musu da Aunty ba na dubi aliya nace, "taso muje mu kwana tare" kallon Aunty aliya tayi taga ta harareta. girgizamun kai aliya tayi alamun a'a. Nace "dan Allah kizo muje kinji kawata" "Aunty ce tace. "Akanme zata biki, kizo ki wuce ki tafi ke kaɗai" mikewa tsaye nayi da wayar aliya a hannuna. Aliya tace, "ke karki tafarmun da waya mana" ina cigaba da tafiyata nace, "ki bari da safe na baki, na matsu na ƙarasa labarinnan" mikewa tsaye Aliya tayi zatabi Maryam ta kwato wayarta. Dakatar da ita Aunty tayi da faɗin, "bar mata mana, idan dan wayane ga wayatanan kikira, keda baza ki iya hakuraba na dare ɗaya" komawa aliya tayi ta zauna tana faɗin, "to bani wayar taki" mika mata Aunty tayi. Maryam kuwa harta fice daga ɗakin. A falo na tarar da ammi na mata sallama na fice, suhailat ma tana falon tana bacci akan kujera. Tun dazu Aunty tace taje daki ta kwanta, taƙi ita setaga shigowar yayanta sannan zata koma daki, be shigoba kuma bacci ya ɗauketa.

A falo natarar dashi a zaune akan kujera yana kallo kamar kullum, da sallama na shiga, banji ya amsamun ba amma dai na masa sannu da hutawa na shige ɗakina. ajiye wayar aliya nayi akan gado na rage kayan jikina na shige toilet..... Binta kawai Mustapha yayi da kallo harta shige dakin. Ajiyar zuciya ya sauke me ƙarfi, dama zaman jiran dawowarta yake. Hankalinsa gabadaya baya kan kallon dayakeyi, idan da za'a titsiyeshi bezece ga abunda ake acikin TV'n ba. zuciyarsa gaba-daya tana gurin Maryam yarasa meyasa tunaninta ya yawaita acikin zuciyarsa a kwanakinnan. wani numfashi me ƙarfi yaja ya fesar yana runtse idonsa, wani irin sanyi yakeji ajikinsa, dumin jikinta kawai yakesonji a halin yanzu yasan shikadaine ze masa maganin abunda yakeji, amma kuma idan matsalar take besan ta yaya hakan zata faruba, tun yayi sallar isha'i yadawo gidan tunanin ta yanda zasu kwana tare yau kawai yakeyi amma haryanzu ya kasa samun hanyar, miskilancinsa kuma baze barshi ya tunkareta da bukatarsaba. Ɗan ƙaramin tsaki yaja, ya buɗe idonsa dasuke wani lumshewa ya mike batare daya kashe kayan kallonba ya nufi bedroom ɗinsa, toilet ya shige domin yin wanka zuciyarsa babu daɗi......tunda na fito daga wanka ake kiran wayar Aliya banbi ta kantaba na ƙarasa gaban mudubi na fara shafe jikina da lotion, harna gama shafe_shafe na ba'adena kiran wayar aliya ba. Rigar bacci kawai na zira na ɗauki hijabina kato har ƙasa shima na zira. wayar na ɗauka har lokacin kira ake ba kakkautawa. Sweet dita danake sha kullum na ɗauko na jefa a bakina sannan na fita falo da wayar a hannuna, banganshi a falo. Hakan yasa nayi sauri nanufi kofa domin na kaiwa Aliya wayarta, dan bazan iya da wannan addabar kiranba. Mustapha yana hango Maryam ta cikin window'n dakinshi, tunda ya fito daga wanka ya kasa komai, zarya kawai yakeyi a dakinshi yana sake_sake. Ajiyar zuciya ya sauke bayan ta fice daga falon, yasan part din ammi zataje, kuma yasan kome zatayi Aunty bazata barta ta kwanaba seta korota. Jallabiya ya ɗauka ya zira ya fesa turare kaɗan, ya fito ya nufi kitchen domin ya haɗa coffee ya sha, dan jiyake kamar hancin cikinsa ze tsinke. Babu kowa a falon ammi se suhailat dake barci haryanzu, dakin dasu Aunty suke na shiga sallama. Fitowar Aunty kenan saga wanka taga Maryam kamar daga sama. Da mamaki tace, "Maryam yanaga kin dawo" ina mikawa Aliya dake kwance tana kallona da alamun mamaki nace, "wlh aunty tun ina wanka ake kiran wayar Aliya, harna gama shiryawa ba'adena kiranba shiyasa nace bari nakawo mata" numfashi Aunty ta sauke tace, "hmmmm" kawai. ƙara kiran wayar akayi, Aliya ta ɗaga da sauri ta tashi ta raba ta gefena ta fice tana satar kallon Aunty. tabe baki kawai Aunty tayi tacigaba da shirin kwanciyarta, seda safe nayiwa Aunty na fito. Aliya ganin Maryam ta fito ta katse wayar datake tana dubanta tace, "matar yaya, irin wannan zuba kamshi haka kamar anyi barin turare ajikinki ko duk na zuwa office din oga ne" murmushi nayi bance komaiba na fice, dan idan na tanka mata shakiyancinta zata cigaba damun. Bansan daliliba ina fitowa naji wata irin faduwar gaba ta riskeni, bugun zuciyata kuma ya sauya ta fara bugawa da sauri da sauri. dafe kirjina nayi ina kiran sunan Allah araina. jikina a sanyaye na koma part dinmu, still yanzuma banganshi a falon ba, ɗakina nayi ƙoƙarin wucewa, fitowarsa daga kitchen hannunsa ɗauke da cup yasani tsayawa. Kallonsa nake ina ƙoƙarin daidaita nutsuwata har ya zauna akan kujera yana kurbar Black tea din a hankali. damuwa na hango ƙarara akan fuskarsa kuma yanayinsa kamar bashida lafiya ma. A hankali na fara taku still idona na kansa, kusa dashi naje na zauna cikin tausayawa nace. "Yaya baka da lafiya ne?" Lumshe idonsa yayi yanajin kamar ya yanyota ya rungumeta ajikinsa, daga mata kai kawai yayi alamar eh. kamar zanyi kuka nace, "Ayya sannu meke damunka?" " _Kece!_ ya faɗa acikin zuciyarsa amma a zahiri seya nuna mata kansa kawai da hannu batare daya buɗe idonsaba. Sannu na masa tare da fatan samun sauƙi na wuce dakina ganin kamar bayason magana. buɗe gajiyayyun idanunsa yayi yana fesar da wani zazzzafan numfashi daga bakinsa, kamar ya bita yace karta tafi amma baze iyaba yana kallo ta shige dakinta. Ajiye cup din hannunsa yayi ya mike yana taune lips ɗinsa, hannunsa dafe da mararsa ya shige bedroom ɗinsa. Kan gado yana faɗa cikin rashin kuzari zuciyarsa babu daɗi sosai mararsa ke murda masa kamar yayi hauka haka yakejin kansa, be taɓa jin kansa a irin wannan yanayinba se sau ɗaya a rayuwarsa, lokacin da accident ya haɗashi da wata yarinya yaje gidan su abokinsa. gumi ne yake tsatstsafo masa a jiki ta ko'ina.... Tunda na koma daki sena kasa sukuni, zuciyata ta kasa nutsuwa, yanayin dana ganshi nasan yana jin jiki bakadanba musamman yanda idanunshi sukayi ja, nasanma da kyar ma idan yasha magani. Tuna lokacin da nayi ciwon ciki nayi da azumi, haka ya dinga zarya a dakina yana duba jikina, nima Yakamata ace naje na bashi kulawa,dan yana buƙatar kulawar tawa a halin yanzu a matsayina na matarsa. Kamar antsikareni na mike, inda nake ajiye magungunana naje na buɗe na dakko Panadol na fice daga ɗakin, seda na ɗauki robar ruwa mara sanyi sannan na nufi dakinnashi zuciyata na ƙara tsananta bugu.....✍️ Comments update 12pm Meson complete Whatsapp 08166674823

*ABINDA KASHUKA.....*

_*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_

*6️⃣2️⃣*

*Bismillahirrahmanirrahim*

........... Har na ƙaraso bakin kofar dakinnasa sena tuna ban dauko cup ba, juyawa nayi na koma kitchen na dakko na dawo. A hankali kamar mara gaskiya na murda handle din dakin tare da turawa. kwance na hangoshi yayi ruf da ciki idanunshi a lumshe, hannunsa ɗaya dafe da kansa. Tausayinsane ya ƙara lullubeni, a hankali nake takawa har na ƙarasa gaban gadon idanuna akansa. Tunda ta shigo dakin yaji alamun anshigo, amma ya kasa buɗe idonsa yaga ko waye, seda ta ƙaraso ya gane itace ta hanyar sassanyan kamshinta daya ziyarci hancinsa. Farin ciki mara misaltuwa ne ya lullube zuciyarsa gami da mamakin abunda yakawota dakinsa adaidai wannan lokacin, dan be taɓa zatoba, ko motsawa beyiba duk da yanda zuciyarsa take azalzalarsa akan ya buɗe ido koda kallontane yayi koyaji sauƙi aransa. Ajiyar zuciya na sauke ina tunanin ta ina zanfara, dan atunanina bacci yake. A jiye ruwan da cup din gami da maganin nayi akan bedside, a hankali na hau kan gado na zauna daf dashi zuciyata na ƙara tsananta bugu, tafin hannuna na dora akan forehead dinsa, bayan na zame hannunsa a hankali daga kannasa, zafi naji akannasa ga jijiyoyin kansa duk sun fito rada_rada se gumine dake ɗan tsatstsafowa kadan_kadan a goshinsa, daga gani kan bakaramin ciwo yake masaba. Ƙasan hijabina nasa na fara goge masa gumin. Ajiyar zuciya ya sauke sassanya yana ƙara lumshe ido lokacin dayaji tattausan tafin hannunta akan goshinsa. seda na goge masa gumin tass sannan a hankali na fara kiran sunansa domin na tasheshi na bashi maganin yasha, dan banga alamun yasha maganinba. "Yaya..yaya!" Buɗe idansa yayi a hankali ya saukesu akan kyakkyawar fuskarta. cikin tausayawa nace, "sannu ya jikinnaka?" Daga mata kai kawai yayi still idanunsa na kan fuskarta. "Allah ya ƙara sauƙi" na faɗa a hankali ina tashi na sauka daga kan gadon. Robar ruwan na ɗauka na tsiyaya a cup na ballo maganin guda biyu, kan gadon na dawo na taimaka masa ya tashi zaune, filo nasa masa ya jingina bayansa, sannan na dakko maganin na bashi, karba yayi ya sha ya kora da ruwan, sannan ya mikomun sauran maganin yana sauke ajiyar zuciya, Ni Ko se jera masa sannu nake cikin tausayawa. Zamewa yayi ya koma ya kwanta tare da lumshe idanunsa. kamar kar na tafi na barshi haka nakeji, zuciyata ta cika da tausayinsa yanda yake taune lips dinsa nasan ba ƙaramin jin jiki yakeba. jiki a sanyaye na tashi na fice bayan na kashe masa light din dakin, ina masa addu'ar samun sauƙi a cikin raina. Yana jinta harta fice amma yakasa tabuka komai, murnarsa duk ta koma ciki na zuwanta, ya rasa meyasa daya ganta yakasa aiwatar da komai akanta, duk da yanda yake cikin tsananin bukatarta a yanzu. hangota yakeyi a idanuwansa yanda takeyin komai cikin nutsuwa da sanyinta lokacin datake bashi magani, yaga tsananin tausayasinsa a cikin idanunta. ciza lips ɗinsa yayi cikin takaici. besamu bacci ya daukeshiba se can dare........

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull