Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 43
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 43: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 43. Tun ina bashi amsa har na dena se lum_lumshe idona nake…
3,268 words
Tun ina bashi amsa har na dena se lum_lumshe idona nake bacci na cina, ganin tana gyangyadi seya janyota jikinsa a hankali, kwantar da kanta yayi akan kirjinsa a tare suka saki wasu boyayyun ajiyar zuciya, lumshe idonsa yayi saboda yanda sassanyan kamshin turaren datasa ya bugi hancinsa, tunda ta shigo dakinsa yake jin kamshi, amma yanzu da kusancinsu ya Karu se tasirin kamshi ya sauya a gareshi. A hankali batare daya buɗe idonsaba ya dafa kanta ya karanto addu'ar da Annabi (S.A.W) ya koyar game da sabbin ma'aurata a fili. zarcewa yayi da shafa gefen fuskarta bayan yagama karanto addu'ar. bacci me daɗi ne yayi awon gaba da Maryam, se ƙara manne masa take a jiki kamar mage. jin saukar numfashinta a hankali yasan baccin ya ɗauketa, ajiyar zuciya ya sauke tare da jan numfashi ya buɗe idonsa da suka fara canza kala, kurawa kyakkyawar fuskarta ido yayi yana kallonta, a duk lokacin da yayi mata kallo irin haka se yaji gabansa ya faɗi, hannunsa yasa a hankali yana zagaye kananun pink lips ɗinta data dan turo gaba, masu taushi. Yayi 10 minutes a haka yanata aikin kallonta da shafa fuskarta cikin tsananin shauki. Tallafota yayi gabadaya a jikinsa ya yunkura ya mike ya kwantar da ita akan gado. Lallabawa yayi ya rabata da jikinsa. Daddumar da sukayi sallah ya nade ya ninke ya ajiye, tea flaks da cup din dayasha coffee ya ɗauka ya fita dasu yakai kitchen ya dawo. Hangota yayi tanata mutsu_mutsu akan gadon, plate din indomie'n ya ɗauka, jinsa da nauyi yasashi buɗewa, mamakine ya kamasa ganin yanda yabar indomie'n haka take, "kenan bata ciba?" Ya tambayi kansa. Shi duk daukarsa taci. girgiza kai kawai yayi itama yakaita kitchen din. Kafin yadawo Maryam harta farka, amma bata buɗe idontaba, saboda baccin besaketaba kawai dai yadena mata daɗine. laptop din da yayi amfani da ita ya ɗauka ya kaita ma'ajiyarta. Sannan ya cire jallabiyar jikinsa ya ajiye, besan meyasaba yakejin wani iri a zuciyarsa akan abinda yake son aikatawaba, tun kafinma ya tunkari Maryam ɗin kasala ta fara lullubeshi. ƙwarara zuciyarsa yayi ya nufi kan gadon. (Bawai ragontakace take hana mustapha kusantar Maryam ba, idan baku mantaba a bayanan mommy na abubuwan data aikata harda asirin hana mustapha iya mu'amala ta sex da kowacce mace, sha'awarsama aka ɗauke masa gabaɗaya, shiyasa ko feeling be taɓa jiba a rayuwarsa se lokacin da suka fara haɗuwa da maryam kafin ta fara aiki agidansu. Amma boka yatabbatarwa da mommy cewa, mustapha ze iya yin sex da mace amma se wadda ta kasance jininsace. Ma'ana yar'uwarsa ta jini, kuma daga ranar da hakan ta faru asirin da'aka masa ze karye ya koma kamar kowanne lafiyayyen namiji kuma ze iya yin sex da kowacce mace koda ba jininsa bace. Mommy bata taɓa zaton mustapha ze haɗu da wani jininsaba a lokacin shiyasa ta amince da sharaɗin boka akayiwa mustapha asirin, shiyasa yake shiga wani yanayi a duk lokacin da yayi niyyar yin wani abu da Maryam. dafatan kun gane🤝.) seda ya kashe light din ɗakin sannan ya hau kan gadon ya kwanta a hankali cikin dauriya da abunda yakeji ajikinsa. Janyota yayi jikinsa yasa hannunsa ya zagaye bayanta. Ajiyar zuciya ta sauke tana ƙara gyara kwanciyarta a kirjinsa wani bacci me daɗi na fizgarta. A hankali yake ƙoƙarin cire mata hijabin jikinta, cikin muryarta me cike da bacci tace, "yayaaaaa..." taja sunannasa. "Uhm" ya amsa mata batare daya dena ƙoƙarin cire mata hijabinba, tsigar jikinsa na tashi yarrrrr. tana jinshi amma baccin dake cinta yasa batayi yunkurin hanashiba. A hankali yake shafa bayanta tare hura mata iskar bakinsa a fuskarta. Ƙara cusa kanta tayi cikin kirjinsa tana sauke ajiyar zuciya, kwantaccen gashin kanta baƙi sidik ya fara shafawa a hankali yana lumshe ido tare da fitar da numfashi zuciyarsa na bugawa da sauri_sauri. Yanayi biyune, ya riskesa a lokaci ɗaya. yanayin dayakeji a koyaushe idan yana tare da Maryam, da kuma wani irin feeling dayake bijiro masa, ga kamshin jikinta dayake ƙara masa tasiri gurin jin wani fitinannen feeling akanta. A hankali ya buɗe idonsa ya ɗan rabata da jikinsa, habarta ya dago ya dora bakinsa akan lips ɗinta ya fara bata wani hot kiss yana lum_lumshe ido. wata irin sarawa kansa yake masa kamar ze tsage amma duk da haka baze iya fasa aiwatar da kudirinsa ba yau kome zeji. tsotsar lips dinnata yake kamar ze cire mata yana ƙara manneta ajikinsa tare da shashshafa jikinta zuciyarsa na tsananta bugu. Maryam tun tanajin abun kamar a mafarki harta farka a tsorace ƙoƙarin kwace jikinta tayi saboda rashin sabo da abunda yake mata amma hakan ya gagara.....wasu sakonni masu wuyar faɗa Mustapha yake aikawa maryam cikin wani irin salo me tsayawa arai da wuyar mantawa. hawayene kawai yake shatata a idon Maryam wanda batasan dalilinsuba. Jikinsu gabaɗayansu kyarma yakeyi. zuciyar Maryam banda dokawa a miliyan ba abunda take saboda tsabar firgicin yanda mustapha yake yamutsa mata jiki a zafafe amma kuma yanayin komai cikin nutsuwa. mustapha baya hayyacinsa kwata_kwata sarrafa maryam kawai yakeyi a matuƙar buƙace, duk da yanda yakejin jikinsa tamkar ana yayyanka naman jikinsane saboda azaba, ga kuma wani bakon yanayi mara misaltuwa daya tsinci kansa a ciki. Maryam bata ƙara firgicewa seda taji yana karanto addu'ar saduwa iyali cikin wata iri murya dabata fita sosai.(Battery low....🤐).......
Adaidai wannan lokacin mommy dake zaune akan gadonta tanata trying number'n suhailat taƙi shiga Tun shekaran jiya, taji gabanta yayi wani irin yankewa ya faɗi, tamkar wadda akayiwa wani abun sega gumi yana tsatstsafowa daga jikinta kuma fanka da ac'n ɗakinta duka a kunne suke, ajiye wayarta tayi a gefe cikin wani irin tashin hankali datake cikinsa tun kwana 2 dasuka wuce, sakamakon jin labarin ciwon Sadiq datayi da kuma labarin cewa mustapha baya Kano shida maryam, tun jiya tasa a binciko mata inda Mustapha'n yake amma har yau shiru babu wani labarin samun inda yake. Maryam kuwa bata jin ta ita, domin duk a tunaninta tana gurin Aunty ne. sauka tayi daga kan gadon ta fara kaiwa da komowa tana zancen zuci. taso ta fara gudanar da aikinta akan su Mustapha tun jiya, amma se gashi sunzo sun ɓata mata shiri. wayarta dake kan gadoce ta fara ringing, da sauri ta nufi kan gadon domin ta dauka, dan ita yanzu cikin maraba da kowanne kira take. Haidar ne yake kiranta wanda taita kiransa tun yamma amma be ɗagaba. Da sauri ta ɗaga tare da kara wayar a kunnenta tace "se yanzu kaga damar kirana kenan?" Cikin kakkausar murya tayi maganar. Haidar dake kwance akan gadonsa idanunshi a lumshe, cikin murya me cike da gajiya yace, "ba haka bane mommy, wlh yanzu ko Lokacin kanmu bamu dashi saboda yawan sabgogi, mu biyunefa yanzu akan komai na daddy muyinan muyi can shiyasa." Tabe baki mommy tayi tace, "hmmm wai ace ina matsayin mahaifiyarku amma babu me nemana a cikinku tsawon kwanakin da muka ɗauka Bama tare, saboda angama hure muku kunne ko?" Haidar yace, "wlh mommy munnemeki amman bamu samekiba yaza'ayi ac....." Katseshi mommy tayi da faɗin "naji Ni duk ba wannanba, inashi mustapha'n yake?" Haidar yayi ɗan jimmm, sanin halin mahaifiyarsa yasan zata kuma iya yin wani mugun abun seya mata ƙarya yace, "yana London mommy" "London?" Mommy ta maimaita a matukar razane. "Ehh" haidar yabata amsa a takaice. wani gumi daya yanko mata a goshi ta goge da tafin hannunta sannan tace, "me ya jeyi a London ɗin?" Yace, "bansaniba mommy" "ƙarya kake haidar kasani" srioustly yace, "mom da gaske bansaniba dana sani mezesa bazan faɗa mikiba." shiru mommy tayi cikin rashin sanin abunyi. Jin shirun yasa haidar yace, "mommy yau nagaji dayawa ina bukatar hutawa yanzu da safe zankiraki" mommy saboda tsabar takaici kasa bashi amsa tayi. cillar da wayar kawai tayi akan gado ta rafka tagumi hannu biyu ta fara tunanin mafita, dan ita wlh kome ze faru bazata fasa aiwatar da kudirintaba, idan ba gani tayi mustapha da daddy sun bar duniyarnanba bazata taɓa samun nutsuwaba. dan haka dole tayi shirin zuwa London a satinnan domin binciko Mustapha a duk inda yake..........
Ƙarshe azaba da wahala Maryam yau tashata, tayi kuka iyakacin ƙarfinta harseda muryarta ta dashe, duk wanda ta sani kuwa yau seda takira sunansa da neman agaji da taimakonsa har inna dake ƙasa yau tasha kira gurin Maryam. Mustapha kam bemasan tanayiba, yau Maryam ta kaishi duniyar dabe taɓa tunanin zuwantaba ko a mafarki, ta kaishi duniyar dabesan yaze misalta daɗin taba da sanya nutsuwa a zuciya da gangar jiki ga duk wanda yajeta. Rungumeta yayi tsam a kirjinsa bayan komai ya lafa, yanajin wani farinciki, nishadi, annashuwa, daɗi, nutsuwa dabe taɓa jin irinsuba a rayuwarsa. sauke numfarfashi kawai yake tare da ajiyar zuciya yana shafa kan Maryam, wadda tuni baccin wahala ya kwasheta. Addu'a kam yau Maryam tashata a wajen mustapha kamar ba gobe, sunfi 30 minutes a haka sannan da kyar mustapha ya iya rabata da jikinsa. A hankali ya yunkura ya tashi zaune, ciwon kan da yanayin dayake ciki da kasala, gabaɗaya sun barshi. sauka yayi daga kan gadon yana jinsa tamkar bashiba tsabar shauki, murmushi ne kawai yake subce masa batare daya san yanayiba. wani wasai yaji kansa tamkar ansauke masa wani abu me nauyi daga kannasa, duk wani kunci da damuwa dayakeji acikin zuciyarsa a yau duk ya kau, tarin farin ciki ne kawai acikin zuciyartasa yau. Toilet ya shiga ya sakarwa kansa shower, seda ya tsarkake jikinsa sannan ya fito daga toilet din daure da towel a kirjinsa. Light din ɗakin ya kunna haske ya gauraye ɗakin agogon dake manne a bangon ɗakin ya kalla, yaga har uku na dare ta wuce. Aransa yace, "lallai ya dade yana abu ɗaya" wardrobe ɗinsa ya nufa ya dauko boxer da wata jallabiyar yasaka a jikinsa. Dadduma ya dauko ya shimfida ya fuskanci alkibla yatada sallah. Raka'a biyu yayi, amma ya dade yana addu'a a cikin sujjadarsa akan Allah yabasu zaman lafiya da zuri'a dayyiba, ya kawar musu da duk wata fitina a zaman auransu. Bayan ya sallame ya koma kan gadon, zama yayi ya tasa Maryam a gaba yana kallonta, yana jin wani baƙon abu yana ratsa zuciyarsa akan Maryam ɗin, a hankali yake shafa fuskarta datayi jage_jage da hawaye cikin tsananin tausayinta, yasan wahala iya wahala ya wahalar da ita. Mikewa yayi da sauri tunawa da yayi tana buƙatar taimako a halin yanzu, be kamata ya barta hakaba. Toilet ya shiga ya tara mata ruwan ɗumi acikin bahon wanka, komawa dakin yayi ya dakkota cancaskat yasata a cikin ruwan hakan yasata farkawa daga baccin datake ba shiri, zabura tayi jin wata irin azaba na ratsata tare da fashe da kuka. Kwantar da kanta yayi akan kirjinsa ganin tana ƙoƙarin tashi, a hankali yake shafa kanta cikin tausayawa. Kuka sosai Maryam takeyi saboda wata azaba dake ratsata ta ƙasan ta kamar an jajjaga mata attaruhu a gurin haka takeji. idanunta a rufe suke gam duk da tafarka daga baccin datake, wata irin matsananciyar kunyarsa takeji. Seda ruwan yayi sanyi sannan ya ɗauketa daga ciki, barin ruwan yayi ya tsiyaye sannan ya ƙara tara mata wani. Seda ya canza mata ruwan sau uku sannan ya barta a ciki yace idan yayi sanyi tayi wankan tsarki ta fito. Banza ta masa bata amsa masaba. Murmushi yayi kawai ya fice. Ajiyar zuciya nasauke me ƙarfi, zuwa yanzu Ni kaina daɗin ruwan nakeji. radadin danake ji ya fara sassauta mun, seda ruwan yayi sanyi kamar yadda yace, sannan na barshi ya tsiyaye, wankan tsarkin nayi na lallaba a hankali na fito daga bahon wankan, taku ɗaya nayi na kwalla ƙara na tsugunna a gurin ina sakin kuka. Mustapha dake saka rigar filon zanin gadon daya sake ya barshi ya nufi toilet din da sauri. Ƙarasawa inda take yayi ya rungumota ajikinsa a rude yace, "meyafaru?" cinyata na nuna masa da hannu ina dungulewa guri ɗaya saboda babu komai a jikina. "Sorry" ya faɗi haka yana bubbuga bayana alamar rarrashi. ƙoƙarin daukata yayi naƙi, ganin yanda take dunkule jikinta ya gane metake nufi, murmushi yayi kawai ya mike ya dakko towel ɗinsa babba ya kawo mata. karba nayi har yanzu na kasa buɗe idona cikin shagwaba nace, "ka dena kallona to" juya mata baya yayi yana murmushi yace "to nadena" buɗe idona nayi a hankali kamar me tsoron kar naga wani abu, ganin ya juyamun baya nayi sauri na daura towel ɗin. juyowa yayi da sauri na maida idona na rufe ina turo bakina gaba. ɗaukarta ya ƙarayi still fuskarsa ɗauke da murmushi. A kan gadon ya kwantar da ita, shima kwanciyar yayi ya rungumeta a jikinsa yana shafa bayanta a hankali, ba jimawa wani baccin ya ƙara ɗauke ta.......✍️
Meson complete Whatsapp 08166674823
*ABINDA KASHUKA....*
_*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_
*6️⃣4️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
.........A hankali ya lallaɓa ya rabata da jikinsa ƙoƙarin tashi yayi Maryam ta ƙara matsowa jikinsa ta kankameshi tana ƙara turo bakinta gaba, cikin lallabawa da dabara ya ƙara zareta daga jikinsa, filo yasa ya maye mata gurbinshi da shi. Kissing goshinta yayi sannan ya sauka daga kan gadon. AC'n ɗakin ya kashe saboda sanyin asuba daya fara busowa. zanin gadon da ya cire ya ɗauka ya shiga toilet dashi ya wanke. Da ƙaramin towel dauke a hannunsa ya fito, gashin kanta data jika gurin wanka ya tsane mata, sannan yaje ɗakinta ya dakko mata wata doguwar riga me ɗan kauri ya saka mata, bacci takeyi amma daga gani kasan na wahala take, yanda take dunkule jikinta yasan sanyi takeji. Fankar dakin ya kashe gaba-ɗaya ya ƙara lullubeta da bargo. Daze tafi masallacin sallar asuba yaso ya tasheta tayi sallah, amma yasan yana tashinta rigima kawai zataita masa ta hanashi zuwa masallacin shi kansa shiyasa ya fasa tashinnata. light ɗin dakin ya rage mata sannan ya tafi zuwa masallaci. Har ya dawo tananan yanda ya barta a ƙudundune, lallaɓawa yayi ya tasheta domin tayi Sallah, da kyar ta iya tashi tana zuba masa taɓara, ɗaukar ta yayi ya kaita toilet din ya taimaka mata tayi alwala, wani tausayintane yake ƙara lullubeshi ga jikinta yayi zafi zau alamar da Zazzaɓi ajikinnata, a zaune tayi sallar danko tsaiwa bazata iya yiba. Bayan ta idar da sallar ya ƙara lallabata ta koma bacci. Ajiyar zuciya ya sauke bayan tayi baccin, tana kwance akan faffaɗan kirjinsa ta kankameshi gam kamar zata koma cikinsa, bayanta yake shafawa a hankali cikin tsananin shauki. Farincikin dayake ciki yau baze misaltuba, tabbas a yau ya ƙara tabbatar da aure ni'ima ne. A hankali ya zare Maryam daga jikinsa, tausayinta yakeji sosai har can ƙasan ransa, dare ɗaya amma fuskarta hartayi fayau ta faɗa. Sauka yayi daga kan gadon ya ɗauki wayarsa dake kan bedside, duba time yayi yaga 6:32 am. Contact ya shiga ya lalubo number'n famili doctor din su ammi da ammi ta taba tura masa saboda tsaro kokuma idan irin haka ta faru yayi dialing, kira ɗaya yayi sa'a kuwa ta shiga, amma harta katse ba'a ɗagaba, ajiye wayar yayi ransa babu daɗi, yana ganin idan har bakwai tayi doctor'n bata biyo bayan kiranba ɗaukar Maryam kawai zeyi ya kaita asibiti a dubata, dan yanda ta kasa tafiyarnan ba ƙaramin tayar masa da hankali yayiba, yana tsoron kar yaje koya jimata ciwo ne. yana ƙoƙarin tashi wayarsa ta fara yin vibrate, dauka yayi ya duba, DR.husna ya gani yana yawo akan screen ɗin, da sauri ya daga bakinsa ɗauke da sallama. Amsa masa sallamar tayi suka gaisa duk da bata ganeshiba, a takaice ya mata bayani daga gidan dayake kiranta yace mata yanada patient ne. Doctor tace, "ok gidan marigayi Alh Nasir kenan?" Yace "eh" tace "Ayya Allah ya ƙara afuwa, yanzu ina shiryawa ne zani asibiti amma kajirani nanda 40 minutes insha Allah zan biyo ta gidan kafin na wuce hospital" godiya mustapha ya mata sukayi sallama ya kashe wayar. kan gadon ya koma, hannunsa ya dora akan wuyanta yaji har yanzu jikinta da zafi, gyara mata kwanciya yayi, sannan yayi kissing pink lips ɗinta da suke matuƙar burgeshi. Falo ya fito ɗauke da Alkur'ani mai girma. Akan Centre carpet ya zauna ya buɗe Alkur'anin ya fara karantawa cikin kira'arsa me daɗin sauraro.....
7:28 kamar yadda Dr.Husnah tace ta ƙaraso gidan, wayar mustapha ta kira ta sanar masa zuwanta, fita mustapha yayi domin ya taho da ita. tunda ya taho Dr, take kallonsa da alamun mamaki domin batasanshi a gidanba, ita a zatonta duk Saddam ne ya kirata har ya ƙaraso bata ɗauke idonta daga kansaba. Sallama ya mata ta amsa ta ƙara da faɗin, "kaine wanda mukayi waya?" daga mata kai mustapha yayi alamun eh. Kallonsa ta kuma yi tace, "ok muje naga mara lafiyar" gaba yayi ta bishi a baya. A falo ta zauna shikuma ya shiga domin ya tada Maryam. yana shiga ɗakin ya ganta zaune akan gado harta tashi. karasawa yayi gareta da sauri, Maryam kuwa tana ganin ya shigo ta fara matso hawaye. Rungumota yayi ajikinsa yana faɗin, "am sorry, na barki ke kaɗai ga doctor nan tazo zata dubaki" gyada masa kai Maryam tayi cikin dauriya tana cize lips ɗinta, ta dan jima da tashi daga baccin amma ta kasa koda sakkowane daga kan gadon saboda yanda takejin kafarta tamkar ba'ajikintaba, ga ƙasanta dake mata radadi har yanzu. rabata yayi da jikinsa sannan ya fita suka shigo tare da doctor. Dr,husnah ta ƙarasa gaban gadon, duk da yanda Maryam takejin jikinta haka ta daure ta gaisheta. Amsa mata tayi ta tambayeta jiki kuma. dakai maryam ta amsa mata. Tambayar Maryam tayi meke damunta, shiru Maryam tayi ta kasa bata amsa se satar kallon Mustapha datayi. Murmushi doctor tayi ta kalli Mustapha tace ya ɗan basu guri, be musaba ya fita falo. ƙara kallon Maryam dr tayi ta tambayeta meke damunta, batare da maryam tayi maganaba ta nuna mata kanta da kafarta, cikin hikima doctor take tambayarta ina da inane yake mata ciwo ita kuma tana bata amsa, murmushi doctor tayi lokacin data gano bakin zaren. Duba Maryam tayi sosai duk da dakyar Maryam ɗin ta bari ta duba kasannata, mustapha beji mata rauniba kamar yadda doctor tayi zato ruwan zafi kawai jikin Maryam ɗin yake buƙata. kama Maryam tayi ta kaita toilet ta gasa mata jiki tayi sosai da ruwan zafi, musamman ƙasanta da cinyarta da taketa complain akan tana mata ciwo. Ai kuwa Maryam taji daɗin gashin jikin da Dr, ta mata duk tsamin da jikinta yake mata yanzu babu, zugin datake ji a ƙasantama ya ragu sedai kaɗan_kaɗan da kantama ta lallabo ta dawo daki daga toilet din, kan gadon ta ƙara hayewa ta kwanta tana sassauke ajiyar zuciya. dubanta doctor tayi tace, "yanzu ya kika jin jikinnaki?" cikin sanyin murya Maryam tace, "naji daɗin shi sosai, kainane kawai har yanzu yakemun ciwo" doctor tace, "shima ze dena insha Allah, nizan wuce Allah ƙara sauƙi" a hankali Maryam tace, "ameen nagode" sallama doctor ta mata ta fice. yana zaune akan kujera idanunsa a lumshe, jin fitowar Dr, yasashi buɗe idon a hankali. doctor na murmushi tace, "to ango nizan wuce, Allah ya ƙara sauƙi ya kawo mana twins nanda 9 months" murmushin gefen baki yayi yace, "Amin nagode sosai" "babu komai ai, na mata duk abunda ya kamata, yanzu a samu a bata ko da tea ne ta ɗan sha, da kuma maganin ciwon kai, dan tanata complain kannata na mata ciwo." Amsa mata mustapha yayi sukayi sallama tatafi, bayan yace tatura masa account number ɗinta. Doctor taso shiga su gaisa da ammi amma ganin har 8 ta wuce, kawai seta tafi, se yanzu data ƙara kallon Mustapha taga kamarsa da ammi, hakan yasa ta tabbatar ɗan tane. duk da bata da tabbas a hakan hakan, dan ta kwana biyu batazo gidanba, tun lokacin haihuwar Abul datazo Barka bata ƙara zuwaba sedai waya kawai sukeyi da mutanen gidan lokaci zuwa lokaci.....