Kenza eBookz

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 44

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 44

Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 44: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 44. Kitchen ya shiga ya tafasa mata ruwan zafi da kansa, a…

2,965 words

*ABINDA KASHUKA....!*

_*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_

*6️⃣5️⃣*

*Bismillahirrahmanirrahim*

..........Batare datayi knocking ba ta murda handle din ɗakin ta shiga babu ko sallama. Maryam tana kwance akan gado tayi rigingine idanunta a lumshe, mustapha kuma ya zaune ta wajen kafafunta ya ɗora su akan cinyarsa yana mammatsa mata a hankali, daya shigo ne take masa complain din har yanzu bata jin daɗin kafartata shine yace bari ya mata tausa. Umaimah da bata taɓa tunanin ganin Maryam a ɗakin ba ba ƙaramin shock ta shigaba data ganta harta kusa yarda tire ɗin hannunta, Allah dai ya taimaka be faɗin ba ta ajiyeshi. Ita duk a tunaninta Maryam tanacan ɗakinta tana bacci shiyasa ma Mustapha'n yace ta kawo masa daki. "ashe tananan kwance ita hamshakiya yana mata tausa kamar wani bawa da uwargijiyarsa" umaimah ta faɗi haka aranta ranta na ɓaci. Wani irin ɗaci ne ya ziyarci zuciyarta ƙasa kawai tayi kanta zuciyarta na wani irin bugu saboda kunci batare datace ƙalaba ta mike da niyyar tafiya. Mustapha dake kallonta yace, "jirani" buɗe idona nayi a hankali mukayi ido huɗu da umaimah, kallonta nake cike da mamaki dan banmasan sanda ta shigo ba, maida kallona nayi garesa da'alamun tambaya, dagemun gira yayi tare da mun wani lallausan murmushi, nima martanin murmushin na maida masa. A hankali mustapha ya sauke kafar Maryam daga jikinsa yana faɗin "my one kinji daɗin kafar yanzu ko?" Gyada masa kai nayi ina yunkurin tashi zaune. ƙara kallon Umaimah nayi nace mata. "Sannu fa" umaimah dake tsaye kamar dogari ta haɗiye wani yawu me ɗaci makut tace, "yawwa" kamar an mata dole tana kau da kai gefe. Sakkowa mustapha yayi daga kan gadon yana duban umaimah ya mata nuni da hannu alamar ta kawo masa kayan abincin kusa dashi, ɗauka tayi cikin sauri ta kai masa tana tunanin zece ta tafi karta ƙara ganin abunda ze ɓata mata rai, amma setaga ya ƙara tsaida ita, badan tasoba ta tsugunna ɗan nesa dashi kaɗan tana hararar Maryam ta gefen ido. Juyawa yayi ya kalli Maryam cikin wata irin murya me daɗin saurare da tsumar da zuciya yace, "luv sakko kiyi break" dan ɓata rai nayi na girgiza kaina tare da faɗin, "na koshi fa" wani kallo yamun wanda na kasa gane masa sannan ya lumshe idonsa ya buɗe cikin wani irin salo me narkar da zuciya. hannunsa ya mikomun yace, "to zo kiji" batare dana kama hannunnasaba na sakko daga kan gadon ina ƙoƙarin zama a gefensa bazantaba kawai naji na janyoni na faɗa kan cinyarshi. Cikin shagwaba nace, "washhh....ka kusa ballanibafa" gefen fuskata ya shafa yana murmushi cikin rada yace mun, "idan na karyaki dawa zan dinga....." (🥺 nidai zeey musty be barni naji ƙarshen zancennashiba) Fuskata na rufe cikin jin kunyar abunda ya faɗa ina murmushi. Kissing gefen wuyana yayi ya ƙara gyaramun zamana ajikinshi, tire din ya ƙara janyowa gabanmu ya shiga bubbɗewa. kamshin stew ne ya daki hancina lumshe idona nayi yawuna na tsinkewa. Soyayyayiyar doya da kwai ya dakko yanka ɗaya ya kai bakina yana faɗin "haa" make kafada nayi ina turo baki gaba nace, "nace maka na koshifa" marairaice fuska yayi cikin lallashi yace, "haba tawan ki daure kici ko kaɗan ne, banason yunwa ta illatamun ke" ƙara shagwabewa nayi na kwantar da kaina a kirjinsa nace, "nifa bakina babu daɗi, kabarni kawai kaikaci" hannunsa yasa yazagaye jikina yace, "ki daure kici ko kaɗanne Please, kinsan idan bakiciba bazan iya ciba nima, Please dear eat" ya ƙarashe zancen yana kuma marairaicewa. a hankali nace, "to bani zanci" kiss ya sakamur a gefen kuncina yace, "yawwa matar Aljannah ta." murmushi nayi cikin jin daɗin yanda yakemun. Doyar ya ƙara mikomun bakina a hankali na buɗe bakinnawa ina jiran ya samun kawai se kai bakinsa yana dariya ƙasa_ƙasa wadda ta ƙara fito da tsananin kyawunsa dimples ɗinsa na kunci biyu suka ƙara lomawa abun sha'awa. bata rai nayi na turo bakina gaba kamar zanyi kuka. a hankali cikin nutsuwa ya fara taunawa yana jifana da wani irin kallo ƙasa_ƙasa yana wani munafukin Murmushi. seda ya cinye sannan yaja karan hancina yace, "yadai Madam" cire hannunshi nayi daga fuskata na yunkura da nufin na tashi ina faɗin, "kuma ba ruwana dakai" maidani yayi jikinshi yace, "am sorry zo in baki" kawar da kaina nayi nace, "bazanciba kuma" batare da yayi maganaba ya ƙara dakko yankan doyar guda ɗaya ya saka a bakinsa amma ba dukaba dan gefe kaɗan, Juyo da fuskata yayi daf da tasa har muna jiyo hucin numfashin juna, 'yan yatsunsa guda biyu yasa ya buɗe bakina banzataba kawai naji ya haɗe bakina da nashi ya sakamun doyar bakinshi acikin bakina. umaimah dake tsugunne a gefe tamkar almajira tana kallonsu tamkar ta samu TV, wani irin zafi zuciyarta take mata, takaici da baƙinciki duk sun lullubeta abunda yafi kona mata rai yanda mustapha ya tsayar da ita, kuma tamkar ya manta da ita se sha'aninsu sukesha wanda ke ƙoƙarin tarwatsa mata zuciya, gashi bazata iya tafiyaba batare da mustapha ya bata umarniba dan gudun karta saɓa masa. Lumshe idona nayi ganin yadda yake kallona kuma yaƙi sakin bakinnawa, wani irin yammm..nakeji ajikina saboda lips dinsa dake gogar nawa, a hankali nake taune doyar harna cinye, ƙoƙarin janye bakina nayi daga nasa amma yaƙi bani damar hakan sema ƙara mamular lips ɗina da yake yana tsotsa, seda ya tsotsa san ransa sannan ya sakarmun bakin yana sauke numfashi, nima sauke numfashin nake cikin wani irin baƙon yanayi daya riskeni. Harga Allah na manta da wata umaimah a ɗakin, seda naji yana mata magana da faɗin. "Sorry na barki kina jirana ko? dama gyaran falo zaki ɗan gyara mana idan babu damuwa" yanda yayi maganar zaka gane da tsantsar rainin hankali yayita. Umaimah datake jin kamar ta fasa ihu, ta tattaro duk wata dauriyarta tace. "Ok babu damuwa" buɗe idona nayi da sauri na kallesa nace, "data barshi nima zan iya fa" lakacemun kumatu yayi yace, "no kibarta tayi kawai keda baki da lafiya ina ke ina wani aiki" zanyi magana ya ɗora finger dinsa aka lips ɗina yace "shiiiiii, kinsan banaso kina wahala ki barta tayi kawai" maida kallonsa yayi ga umaimah yace, "you can go" mikewa umaimah tayi cikin wani irin mummunan yanayi, har wani jiri_jiri takeji tsabar baƙin_ciki, tana fita falo ta saki kukan datake ta dannewa, durkushewa tayi a ƙasa, mustapha da Maryam kawai take hangowa a idonta manne da juna suna zuba love. datasan wannan baƙincikin zatazo tatarar da wlh bazata kawo musu breakfast dinba, gashi abunda yafi bata mata rai wai ta gyara musu falo, wato bayason matarsa ta wahala itace baiwa kenan ita zata wahala. Kwafa taja ta share hawayenta ta mike ta fice batare data gyara falonba. Ni kuwa bayan fitar umaimah na dubeshi srioustly nace, "Allah yaya daka barta tatafi zan iya gyara gidan da kaina" hararata yayi yace, "baki da lafiyar zan barki kiyi wani gyaran gida." ina tashi daga jikinshi nace, "nafa warke Ni, dama kuma ba cuta nakeba." Be ƙara mun magana se abincin daya cigaba da ci hankali kwance cikin nutsuwa. Seda ya gama ya dubeni fuska babu wasa yace, "zo" ganin yanda yayi yasa na matso kusa dashi, abincin ya dinga ɗiba yana bani a baki fuskarsa babu walwala kamar bashi yagama yintaba ɗazu. seda ya tabbatar data koshi sannan ya rufe sauran. Tashi yayi ya dakko magani da ruwa yazo ya ɓalle ya mikomun, nida banason shan magani harda zanyi musu naga yamun wani kallo, ba shiri na karba na sha ina yatsina fuska. ganin yanda ta tsorata dashi seya ɗan saki fuskarshi, ɗaukarta yayi cak suka kwanta akan gado, bargo yaja ya lullubesu cikin tsokana yace, "tunda kin warke bari na ƙara" "Ni ban warkeba" na fadi haka kamar zan fashe da kuka danna ɗauka dagaske yake ze ƙara yi ɗin. daga kafadarsa yayi yana tabe baki yace, "ke kika faɗa da bakinki, Ni baruwana ƙarawa zanyi" kuka tasa wanda kana gani kasan na taɓara ne tace, "nidai A'a kuma sena faɗawa Aunty idan ka ƙara" murmushi yayi yasa hannunsa yana ƙara rungumeta ajikinsa ganin tana ƙoƙarin tashi. Kuka Maryam take bilhakki, shafa kanta ya hauyi cikin lallashi tare da hura mata iska daga bakinsa a cikin kunnenta. amma bece mata komaiba, ganin kukannata bana ƙare bane, seya dago fuskarta, idanunta a rufe suke baccima ya fara ɗaukarta amma tsabar rigima batabar kukanba, a hankali ya zira mata lips dinsa na ƙasa acikin bakinta, dif ta dauke kukan ta fara mamular lips dinnasa kamar jaririn daya kama nonon uwarsa tana sakin ajiyar zuciya. seda ya tabbatar bacci ya ɗauketa sosai sannan ya zare lips dinnasa a hankali daga cikin bakinta. Kwabe fuska tayi ta turo baki gaba alamun bataso hakanba. lips dinta ya shafa a fili yace, "rigima girl" yana aikin kallonta besan sanda shima bacci me daɗi ya ɗaukeshiba.....

Su ammi suna falo sukaga umaimah ta shigo kamar anjehota, ammi ta dubeta da mamaki tace "lafiya kuwa auta?" girgiza kai kawai umaimah tayi alamun a'a batace komaiba. Mama dake cin abinci tace, "yazakice a'a bayan gakinan kin shigo kamar wata mara lafiya, kuma daga kai wa mutane abinci kinje kin zauna tun dazu, yanzu amminki tagama zancenki tana ko abinci baki ciba zataje ta kirani." Mikewa umaimah tayi tana faɗin "batajin daɗi ne shine yaya NOOR yasa na gyara musu gidan" zuhura dake bawa Abul tea tace, "gyaran gidan da'aka sakine shine kike bata rai haka?" Umaimah bata bata amsaba ta shige ɗakinta. Ammi kuwa tuni hankalinta yayi kan ƴar surukartata dataji ance bata da lafiya, wayarta ta ɗauka ta lalubo number'n Mustapha tayi dialing dantaji meke damun maryam din. Har Kira uku ta masa amma bedagaba. Fuskarta da alamun damuwa take duban su mama tace, "Allah yasa dai jikinnata ba tsanani yayiba, gashi kuma na kira NOOR ɗinma bedagaba. Cikin son kwantar da hankali mama tace, "karki wani tada hankali 'yata, kinsan mace me ƙaramin ciki ba'a rabata da dan laulayiba, insha Allahu ciwon ba wani me tsanani bane" cikin sanyin murya ammi tace, "Allah yasa, amma da zuwa zanyi na dubota, dan idan banga yanda jikinnata yakeba hankalina baze kwantaba." mama tace, "to kije kawai ki dubotan, kice muna mata sannu, idan mungama muma zamu shigo." mikewa ammi tayi tana amsawa ta fice ta nufi part ɗin su Maryam. Knocking tayi taji shiru hakan yasata tura Kofar ta shiga bakinta ɗauke da sallama, tayi sallama takai uku amma taji shiru. Ɗakin maryam ta shiga taga wayam ba kowa. fitowa tayi ta nufi ɗakin mustapha, duk da zuciyarta na mata tuni da hakan kamar bedaceba, amma hankalinta baze taɓa kwanciyaba idan bataga yanda jikin Maryam ɗin yakeba. Seda tayi knocking nanma taji shiru sannan ta tura kofar ɗakin a hankali ta shiga bakinta dauke da sallama. Ajiyar zuciya ta sauke ganin su kwance suna bacci, se yanzu hankalinta ya kwanta tasan tunda Maryam ɗin ta samu bacci jikin da sauƙi kenan. fita tayi taja musu ƙofar a hankali, seda ta rufe musu ta falonma yanda sena cikine kawai ze iya buɗewa sannan ta koma part ɗinta......

A hankali na buɗe idona tare da zare jikina daga nasa na tashi zaune ina salati acikin zuciyata, fuskarsa na kalla inajin wani sonsa na ƙara ratsa zuciyata, kusancin damuka samu daga jiya zuwa yau, da kuma kulawar daya bani ba ƙaramin tasiri yayi acikin zuciyataba. Hannuna nakai a hankali na shafi kwantaccen sajensa wanda yake ƙara fito da kyawunsa cikin raina ina faɗin, _"Ya Allah kanunamun ranar da wannan bawannaka ze soni, kamar yadda nake tsananin sonsa."_ ɗauke hannuna nayi daga kan fuskarsa ina sauke ajiyar zuciya, a hankali cikin lallabawa na zare hannunsa daga jikina dan kar ya farka, sauka nayi daga kan gadon na ɗauki tire ɗin damukaci abinci na fice daga ɗakin. seda na fita falo na duba time naga har 12 na rana ta wuce, lallai mun dade mune shan bacci, amma naji daɗin jikina sosai danayi baccin. Dan ciwon da kaina yakemun ya dena, kawai dai ina jin jikina fayau babu kwari ne. ko ɗakina ban shigaba na fara gyaran gidan, falo na fara sharewa nayi mopping na saka turaren wuta, sannan na nufi kitchen na gyarashi nayi wanke_wanke, sannan na shiga ɗakina shima na gyarashi tass. Bayan na gama na faɗa toilet nayi wanka na ƙara gasa jikina, tare da dauro alwalar sallah azahar. Cikin wata doguwar rigar atamfa na shirya, banyi wata kwalliyaba amma na budade jikina da turaruka masu daɗin kamshi. ganin har 1 ta wuce, sena tada sallah ta......✍️ Meson complete Whatsapp 08166674823

*ABINDA KASHUKA....!*

_*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_

*6️⃣6️⃣*

*Bismillahirrahmanirrahim*

Chapter notes and social links

Kitchen ya shiga ya tafasa mata ruwan zafi da kansa, a kitchen din ya haɗa mata tea me kauri a cikin wani madaidaicin cup din roba me murfi. Da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga ɗakin. ina jinshi amma ko matsawa banyiba sema ƙara rufe idona danayi gam gabana na faduwa. A jiye cup din yayi ya ƙarasa kan gadon, hannunsa yasa a wuyanta yaji zafin jikinnata ya ragu, ajiyar zuciya ya sauke Sannan ya fara ƙoƙarin dagota a hankali duk da yasan ba bacci takeba, yanda take ta kifkifta idantane yasa ya gane hakan. cire hannunshi nayi daga jikina hawaye ya fara zuba daga idona. Dafe kansa yayi a fili ya furta "ya Salam" ganin yanda take hawaye hannunsa yasa ya juyo da ita suka fuskanci juna, tattausan tafin hannunsa yasa ya fara share mata hawayen, kamar ƙara zugata yayi ta fashe da kuka, janyota yayi ya rungumeta tsam a jikinsa yana sauke numfashi, a hankali yasa hannunsa yana ɗan bubbuga bayanta amma bece mata komaiba, shi kanshi har kansa ya fara masa ciwo. daidai kunnenta yakai bakinsa murya ƙasa_ƙasa yace, "what happened? Ko jikinne? girgiza masa kai nayi alamun a'a ina ƙoƙarin sauka daga jikinsa. Riketa yayi gam da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma ya dago fuskarta a hankali ya matso tasa daf da ita, a hankali yasa harshensa ya lashe hawayen nata dasuke cigaba da zuba. dif na ɗauke kukan se jan numfashi kawai nake. seda ya shanye hawayennata tass sannan yayi kissing saman idonta duka biyun, wanda hakan yasa naji tsigar jikina na tashi yarrr.... finger ɗinsa yasa yana shafa cikakkiyar girarta da murmushi ɗauke a fuskarsa, yanda take ta kifkifta ido ne yake bashi dariya, tanaso ta buɗe idonta amma ta kasa. a hankali yace, "ki buɗe idonki karyaje ya manne yaƙi buduwa" make kafadata nayi na turo bakina gaba. yana dariya ƙasa_ƙasa yace, "shikenan tunda kinki buɗewa nidai babu ruwana idan idanki ya manne, bakisan mutum idan yayi kuka ya rufe idansaba kuma idan ya dade arufe mannewa yakeba." Kafinma ya ƙarasa na buɗe idannawa da sauri, murmushi yayi cikin jin daɗi dama soyake kawai ya kalli cikin idonnata. ƙoƙarin sauka nayi duk da yadda nakejin daɗin zama ajikinnasa amma zuciyata cike take da tsoronsa kar naje ya ƙara tumurmusheni, kin bata damar hakan yayi. Kyabe baki tayi kamar zatayi kuka Ɗan sassauta riƙon da yayi mata yayi yace, "sorry pls karkiyi kuka" cikin shagwaba nace, "to ba kai bane" waro fararan idanunsa yayi waje yace, "me nayi kuma?" bata bashi amsaba se ƙoƙarin saka masa kuka datayi. Kwantar da kanta yayi akan kirjinsa yana danne dariyar dake cinsa, dan yasan yanda take kan darunnannata idan yayi dariya kuka zata sa masa. Luf nayi a kirjinsa ina shaƙar daddaɗan kamshinsa. tunawa yayi da tea din daya shigo dashi, dagota yayi daga kirjinsa yana faɗin. "Muje kiyi brush kizo kisha tea" maida kaina nayi cikin kirjinsa nace, "um'um bazanshaba" "why?" Yatambaya yana ƙara dago dani. Cikin shagwaba nace, "Ni bazanshaba kawai, kamaidani gurin ammi kuma bazan ƙara kwana a part dinnanba" murmushi yayi me sauti yace, "to se kinsha tea din sannan zan kaiki gurin ammin" tashi nayi daga jikinshi kamar zanyi kuka nace, "to zan sha" barinta yayi ta sauka daga kan gadon da kanta, so yake yaga kozata iya tafiya yanzu da kanta. A hankali kamar yar kaciya take tafiyar, tashi yayi da sauri ya kama hannunta suka ƙarasa toilet din, sabon brush ya dakko ya matsa mata MacLean ya bata. da kanta tayi brush ɗin dan da cewa yayi ze mata taƙi yarda, ƙara kama hannunta yayi suka fito, duk da yanzu ta ɗan kwarara tafiyartata ba kamar dazu dasuka shigoba. Akan cinyarsa ya ɗora ta, yana bata tea din a baki kamar wata yar baby cikin lallabawa. seda tasha sosai sannan ya kyaleta. kulawar da mustapha yake bawa Maryam ba ƙaramin daɗi takeji arantaba, duk da tasan bawai soyayyace tasa yake mata hakaba, saboda abunda ya matane, a nata tunaninfa. duk da tagama shan tea ɗin besauketa daga jikinsaba, a ganinsa idan ya kwantar da ita akan gadonma jikinta ciwo zeyi, yanda yakejin kansa a wani irin yanayi na shauki dazata yarda goyatama zeyi. knocking kofar falo dayaji anayine yasa ya sauketa daga jikinsa badan yasoba. Fita falon yayi ya buɗe Kofar bayan ya tambayi waye, umaimah dake ɗauke da basket na abincin breakfast dinsu ta amsa masa da cewa itace. Taci uwar kwalliya kamar aljana da safiyarnan, cikin rangwada da iyayi tana wani far da ido kamar wata sabuwar makauniya tace, "yaya NOOR ina kwana, dafatan ka tashi lafiya" "lafiya" ya bata amsa a takaice yana komawa cikin falon. Dinning ta nufa ta ajiye basket din, tana tafe tana satar kallonsa harta kusa tuntube. Mustapha dake tsaye yana kallonta yace, "ki zuba komai kaɗan_kaɗan ki kawomun ɗaki" bejira amsartaba ya juya ya koma daki. Cikin tsananin farin ciki umaimah ta shiga kitchen din Maryam ta dakko tire da ƙananun plates ta zuzzuba masa komai kaɗan kaɗan kamar yadda yace, jikinta har rawa takeyi tsabar zumuɗin zata kaiwa Mustapha abinci har ɗaki, domin damar data ɗade tana jirane yau Allah yabata. Zuciyarta cike fal da murna ta ɗauki tire din ta nufi dakinnashi tana wani karkada jiki yanda zata ƙara rikita mustapha ya faɗa tarkonta. (🤣🤣🤣🤣 _Ni ba zance komaiba, Team ɗin umaimah da Maryam 👉gareku_).....✍️ Meson complete Whatsapp 08166674823

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull