Kenza eBookz

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 45

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 45

Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 45: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 45. ..........Bayan na idar da sallar na fito da nufin naje…

3,174 words

..........Bayan na idar da sallar na fito da nufin naje na tashi yaya yayi Sallah, knocking din ƙofar falon da'ake shiya tsaidani. Kofar na nufa na buɗe bayan na tambayi waye? Aunty zuhura ce, faɗaɗa fara'a nayi nace, "Aunty zuhura sannu da zuwa" "yawwa Mamana" ta faɗa tana shigowa falon tare yin sallama, amsa mata nayi ina gaba tana bina a baya. Kallon yanda Maryam take tafiya yasa Aunty zuhura ta gane abunda ya faru, duk da maryam ɗin tayi iyakar ƙoƙarinta wajen ganin ta daidaita tafiyar tata yanda baza'a ganeba, amma seda zuhura ta harbo jingin. zama sukayi akan kujera suka ƙara gaisawa, Aunty zuhura ta mata ya jiki. Maryam ta amsa da faɗin "da sauki dannama warke" Aunty zuhura na murmushi tace, Allah ya ƙara sauki" Maryam tatambayeta ina Abul, tace yanacan gurin mama. Aunty zuhura bata wani jimaba tatafi tacewa maryam zataje ta dawo anjima... mustapha yana cikin baccinshi cike da jin daɗi da nishadi, amma tashin Maryam datayi ta barshi duk se yadena jin daɗin baccin. lalube_labule kawai yakeyi da hannunsa a gefensa koze jiyota amma sedai yaji filo, haka dai yacigaba da baccin babu daɗi. A hankali na tura Kofar dakin na shiga, kan gadon na nufa na hau na zauna ina tunanin ta ina zan fara tashinnashi. kyakkyawar fuskarsa me cike da kwarjini na kurawa ido da murmushi ɗauke a fuskata. wani irin farin ciki nakeji mara misaltuwa a cikin zuciyata, jina nake a wata duniya me nishadi da annashuwa, gani nake yau a duniya babu wanda yakaini farin ciki, saboda kasancewata da mutumin da bantaba zaton ze zamto miji a gareniba, amma ikon Allah gashi mun kasance matsayin ma'aurata har mun haɗa shimfida. Lumshe idona nayi saboda kwallar dabansan kota meceba data cikamun ido, tafin hannuna na kai kan cikakkiyar sumar kansa baka sidik me laushi da daɗin shafawa a hannu, na fara shafa masa idona a lumshe cikin tsananin shauki ina sauke ajiyar zuciya. nayi 6 minutes ina shafa kannasa zuwa zajen fuskarsa da bayan kunnensa. Mustapha kuwa duk da bacci yake amma ba ƙaramin jin daɗin abinda take masa yakeba, har wata ajiyar zuciya yake sassaukewa. baccin daya dena masa daɗi ya fara masa yanzu. ƙasa nayi da hannuna ina shafa wuyansa zuwa saman kirjinsa, tunawa danayi lokacin sallah na kurewa yasa nayi ƙoƙarin ɗauke hannuna daga jikinsa domin na tasheshi yayi Sallah, amma naji zaraf ya rikemun hannunnawa, a hankali nake ƙoƙarin zarewa amma ya rike gam da hannunsa. kyale masa nayi senaga ya maida hannun kan kirjinshi ya ɗora nashi akai ya manne. murmushi nayi kawai cikin jin daɗi da farin ciki. A hankali nasa ɗayan hannuna na ɗauke nashi sannan na zare nawa daga kirjinnasa, hakan danayi kuwa kamar tashinshi nayi daga baccin. a hankali ya buɗe lumshashshun idanunsa da suka sirka saboda baccin yayi, ya saukesu akan fuskarta, nima kallon fuskartasa nake hakan yasa idanunmu suka sarke cikin na juna, kasa janye idona nayi daga nasa kamar koyaushe idan ya kalleni, kallon cikin kwayar idonnasa nake zuciyata na tsananta bugu, banfi 30 seconds ina kallonsaba na lumshe idona saboda wata kasala datake lullubeni a sanadiyyar kallon kwayar idansa da nayi, batare dana buɗe idonaba a hankali nace, "ka tashi kayi sallah, kar lokaci ya kure" lumshe ido mustapha yayi cikin rashin jin daɗin rufe idonta datayi ta katse masa wani abu dake bin ilahirin jikinsa a sanadiyyar kallon kwayar idonta dayakeyi gashi ta masa kyau sosai. Tafin hannunsa yasa ya kamo nata a hankali ya haɗesu guri guda yana murzawa, a tare sukaji wani irin shock a jikinsu. batare daya saki hannunnataba ya buɗe idonsa tare da tashi zaune jin abinda tace. zama yayi a daf da ita har jikinsu na gogar na juna, bakinsa yakai daidai kunnenta cikin cool voice dinsa data ƙara sanyi saboda daga bacci ya tashi yace, "haka ake tashin miji a gurinku?" ya ƙarashe zancen yana ɗan matse hannunta dake haɗe da nasa. wayyo Allah, bansan ya misalta muku yanda naji ba a jikina sanadiyyar wannan maganar dayamun, turo bakina nayi gaba bance komaiba. kissing kuncinta yayi sannan yasa ɗayan hannunsa ya kama lips ɗinta da finger dinsa guga biyu ya matse yace, "wannan lips ɗin, nasan mezan masa a dena turomunshi gaba" da sauri na gimtse su, dan ban manta tsotsar dasukasha jiya agurinsaba ta fitar hayyaci har zafi seda sukamun. Tattausan murmushinsa yayi ya cire hannunsa daga bakinta, tare da zare ɗayan daga nata ya sakko daga kan gadon bakinsa ɗauke da salati. ban iya wani yunkuriba duk da yadda naso hakan har ya shige toilet din, duk da ya saki hannuna amma bandenajin wani yarrrr...... ajikinaba gami da kasala. Ajiyar zuciya na sauke na tashi na fara gyara gadon daya yamutse. kafin ya fito harna gyara ɗakin shap_shap na fice falo, zama nayi akan kujera ina sauke numfashi ɗankwalin kaina na cire saboda kan ya ɗan sha iska dan har yanzu da lema a jikin gashin duk da uban man kitson dana shafa kuwa, danma kitsone akan amma datuni na busar da gashin.............

*KADUNA*

Su Aunty sun sauka lafiya, tun a daren jiyan sukayi waya da ammi data kirasu dantaji ko sun sauka lafiya. Tun da suka taho suhailat take damun Aunty da tambaya akan gidanwa sukaje, da kuma tambayar me Maryam take a gidan dan daga baya ta fuskanci maryam ba aiki take a gidanba, itama tana rayuwar yanci ne kamar kowa na gidan. se kuma ammi dataga tana mata kama da mustapha musamman ta idanunsu da yanayin yanda suke kallon mutum, dansu ba normal kamar kowa kallonsu yakeba kuma Maryam ma taga irin kallon take. shine abunda ya ƙara bata mamaki ya kuma ɗaure mata kai, Aunty dai bata kulataba da tambayoyinta balle ta bata amsa, hakama Aliya dataketa karatun Novel ɗinta a wayarta. Yau da safe bayan suhailat tagama shan baccin asararta ta tashi tayi wanka ta fito falon Aunty. Babu kowa a falon, fridge ta nufa ta buɗe ta dakko hollandia me sanyi ta nemi guri ta zauna ta fara sha a yangance. tana cikin sha Aunty ta shigo falon ta dawo daga part din abbansu aliya ne. sallama tayi suhailat ta amsa mata ciki_ciki, dan har yanzu haushin Aunty taƙi barinta a jos take. batare da Aunty ta zaunaba tace, "suhailat wai banace kidena shan abu me sanyi bane, bakisan illa bane a gareki da abunda ke cikin ba." Zunburo baki tayi gaba tace, "To Ni fa Aunty banajin daɗin komai se abu me ɗan sanyin." Harararta Aunty tayi bata ƙara cewa komaiba, se kwace sauran hollandia'n datayi ta shige bedroom ɗinta bayan tacewa suhailat ta shirya zasuje asibiti anjima. suhailat ta amsa mata kamar zatayi kuka saboda kwace mata hollandia'n datayi. Itafa ta gaji da wannan wahalallen cikin, ace kullum cikin shan wahala take, tun daga ranar da Dr. Ta tabbatar tana da ciki, har yau bata ƙara samun ishashshiyar lafiya ajikintaba, inda Allah ma yataimakama bata kwadayi_kwadayi, gashi cikin yayi sanadiyyar katsewar karatunta, kuma a tunaninta shiya hana Aunty tada maganar auransu da mustapha, shiyasa take ƙara tsanar cikin. Kamal ne ya faɗo mata a rai, tanason kiranshi kodan ta sanar masa tana ɗauke da cikinshi amma kuma tana tuna gargardin mommy data mata akan karta sanar masa, kuma ko yanzu ta kunna wayarta seya kirata kokuma ya mata text. kawar da tunanin kamal tayi ta faɗa na masoyinta mustapha, ita yanzu kawai neman hanyar dazata koma Jos take batare da Aunty ta saniba, dan yanda takeson kasancewa da yayannata ko'a motar haya zata iya zuwa Jos ɗin, Ita dai burinta kawai taganta kusa da masoyinta kota halin ƙaƙa..... Aunty zuciyarta babu daɗi ta ajiye guntun hollandia'n akan bedside locker. Tanajin ciwo sosai a cikin zuciyarta akan cikin dake jikin suhailat, kawai tana dannewane, ita fargabartama ta yanda zata iya sanar da daddy maganar cikin dake jikin suhailat ɗin, ita kanta suhailat ɗin tanason ta zaunar da ita ta mata tambayoyi akan cikin da kuma wanda ya mata cikin, amma taga suhailat ɗin kwata_kwata babu nutsuwa a tattare da ita, gashi wani abu dayake ƙara bawa Aunty takaici, suhailat bata da tarbiyya ko ladabi ko kaɗan. duk kwanakin datayi agidannan har yau bata san gari ya waye taje ta gaishedda Abbansu Aliya ba, kullum se Aunty ta turata take zuwa, masu aikin gidanma ta lura hakuri kawai suke da halinta, amma basajin daɗin zama da ita. shiyasa yayan Aliya kwata_kwata baya shiga sabgarta tunda canma bare kuma yanzu, duk da shi mutum ne me fara'a da barkwanci kamar Aliya, Aunty har faɗa take masa akan yanda yakewa suhailat ɗin. Ajiyar zuciya Aunty ta sauke ta bar tunanin danba mafita bane a gareta, addu'a itace kawai mafita. wayarta ta dakko ta kira likitan su ta sanar masa zasuzo asibiti anjima.........

************

Ya ɗan jima a toilet din sannan ya fito, dakinnasa ya shiga bi da kallo ganin yanda Maryam ta gyareshi, yanda ta ɗame gadon ta jera filollika yafi komai burgeshi, gadon tamkar ba'a taɓa hawa ankwanta a kanshiba. Ashe shi da duk jagwalgwala abunsa kawai yake be iyaba, kuma shi idan zeyi gyaran dakin seya ɗauki lokaci da me tsayi kafin yagama amma ita gashi acikin lokaci kaɗan harta gyara ta fice. Karasawa yayi gaban madubi ya ɗauki lotion ɗinsa ya fara shafawa a lallausar farar fatarsa wadda ta jiku da hutu. Cikin some minutes ya gama shirinsa cikin ƙananun kaya wanda suka amshi jikinsa da matuƙar yi masa kyau sannan ya tada sallah.... Falo ya fito hannunsa riƙe da wayarsa yana latsawa, maryam da hankalinta yake kan kallon datakeyi batamasan ya shigo falonba.

A bayan kujerar datake ya tsaya, sunkuyo da fuskarsa yayi daidai da tata ya hura mata iska daga bakinsa a fuskarta, lumshe idona nayi da sauri a ɗan tsorace saboda bansan da zuwansa falonba, yanzu daddaɗan kamshinsane ya tabbatarmun da shine. batare daya janye fuskarsa daga kusa da tataba yace, "ya jikinnaki?" numfashi na sauke me ƙarfi saboda yanda yake gogamun sajen fuskarsa a kumatuna nace, "da sauƙi" cikin matuƙar raunin murya. kafin ya kuma magana aka fara knocking kofar falon, wayarsa ya ajiye a gefena sannan ya zagayo ya nufi kofar, da ido nabi bayanshi da kallo cikin wani irin baƙon yanayi ina sauke numfashi. Ammi ce hannunta ɗauke da basket data haɗo musu launching aciki. Murmushi suka saki a tare ita Mustapha lokacin da sukayi 4 eyes. cikin murmushin yace, "sannu da zuwa AMMINAH" itama da murmushin a fuskarta tace, "yawwa MY NOOR" tare da yin hugging ɗinshi lumshe idonsa yayi yana ƙara hugging ɗinta shima cikin tsananin so da kaunar dake tsakanin ɗa da mahaifiya. sakinsa ammi tayi ta shafa kansa tace, "ya jikin takwarata?" Da mamaki ya kalleta dan be san ta saniba. shanye mamakinsa yayi yace, "da sauƙi" ya ƙarashe zancen da karɓar basket din hannunta. Ammi tace, "Allah ya ƙara sauƙi yasa kaffarane" "Ameen" ya amsa yana kama hannunta suka shiga cikin falon. kallonsu nake cike da ban sha'awa da burgewa, sunmun matuƙar kyau, kana ganinsu kaga uwa da ɗanta. sakin hannunsa ammi tayi ta ƙaraso gurin Maryam tana faɗin, "ɗiyata sannu ya jikinnaki?" da sauri na zamo daga kan kujerar danake ina daura ɗankwalina cikin girmamawa nace, "da sauƙi ammi, ina wuni" ammi cikin jin daɗin yanda taga jikin maryam tace, "lafiya kalau ɗiyata, Masha Allah haka akeso, naga jikinnakima da sauƙi bayanda nayi zaton ganinkiba, Allah ya ƙara sauƙi, ya inganta" "ameen" na'amsa ina ƙara yin ƙasa da kaina cikin jin kunya, gani nake kamar tasan meyafaru. zama ammi tayi akan kujerar danake, Ni kuma na zauna a ƙasan kujerar. Shima Mustapha zama yayi a gefen ammi ya kwantar da kanshi akan kafadarta. Kallon fuskarsa ammi tayi tace, "meke damunta ne?" yace, "zazzaɓi" atakaice. Ammi tace, "amma kuma shine bakuje asibiti anduba taba NOOR?" Yace "na kira family doctor ɗinku tazo ta dubata" da mamaki ammi tace, "Dr husnah?" Yace "ehh" ammi tace, shine bata shigo part ɗina mungaisaba" yace, "may be, tana sauri ne, danda early morning tazo, kuma daganan zata wuce aiki" ammi tace, "ehh hakane ai nasan Dr husnah akwai kirki, amma duk da haka Yakamata ku fara zuwa asibiti dan adinga duba lafiyarta dana abunda ke cikinnata" dagowa nayi da sauri na saci kallonsa, shima kallon maryam ɗin yayi sannan yayi murmushi yace "to ammi zamuje insha Allah" shafa kuncinsa ammi tayi tace, "yawwa, Allah ya ƙara lafiya, ya muku albarka ya baku ƴaƴa na gari masu albarka" "Ameen summa ameen" muka amsa a tare. tashi nayi na ɗauki basket ɗin da ammi ta shigo dashi na abinci na nufi kan dinning dashi na ajiye sannan na shiga kitchen.......✍️ Meson complete Whatsapp 08166674823

*ABINDA KASHUKA....!*

_*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_

*6️⃣8️⃣*

*Bismillahirrahmanirrahim*

.......... Umaimah suna tafiya a mota tana tunanin maganganunsu da farida, da kuma shawarar datake bata a kodayaushe akan Mustapha, duk da tsananin so da kaunar datakewa mustapha bazata iya tunkararsa da wata mu'amala ta banza ba, saboda hakan ba dabi'arta bane kuma ko ba don haka ba, bataga fuskar dazata iya tunkarar mustapha da wani zance na banza ba, mutumin da ko gaisuwarta seyaga dama yake amsawa ta ina zata iya tunkurarsa da wannan abun......

Bayan fitar umaimah ba jimawa Aunty zuhura ta shigo falon, bayan tayi sallama na amsa mata ta dubeni tace, "mamana ya jikinnaki?" A hankali nace, "da sauƙi" tace, "Allah ya ƙara sauƙi, dazu kuma nace miki zan dawo ban dawoba, aiki ne yamun yawa kinsa yau ni kaɗai ce" nace, "babu komai Aunty zuhura ainama warke" tace, "dama abu zan baki, amma idan babu damuwa yanzu kibini part ɗina sena baki" tashi zaune nayi ina ɗan yamutsa fuska nace, "ok muje to, amma bari na miƙawa ammi wayarta" tace, "to" ammi tana haɗa kaya na shiga ɗakin, bayan nayi sallama nace, "ammi sannu da aiki" tana dubana tace, "yawwa ɗiyata, ya jikinnaki dai" nace "naji sauƙi sosai ammi" ammi tace, "to Allah ya ƙara sauƙi, kindaici abincin ko?" "A'a banciba amma zanci kafin na kwanta." Na fadi haka ina miƙa mata wayarta. Karba tayi tana faɗin, "har kin gama wayar?" Nace, "A'a taƙi shiga may be network ne" ammi tace, "ai haka yake dama wani lokacin, kema yakamata noor ya sai miki waya, na rasa meyake jira har yanzu yaƙi sai miki" murmushi nayi kawai na juya fita. Magungunan mata Aunty zuhura ta bani, dana sha, dana tafasawa a shiga ciki, dana tsugunno" na karba a kunyace na mata Godiya na koma part ɗina. Adanasu nayi a kitchen, inayin sallar isha'i na tsakuri abinci naci kaɗan nasha maganin ciwon kai, dan har lokacin kan na ɗan saramun. da kyar na iya watsa ruwa saboda yanda nake jin jikina, ina fitowa na shafa mai da turare sama_sama, na zira wata rigar bacci na haye gado na kwanta, ba jimawa bacci ya ɗauke ni.....

Mustapha tun yamma da Maryam ta tafi part din ammi yake aiki a system ɗinsa, jibi su daddy zasu dawo daga Saudiyya shine daddy'n ya bashi wani aiki yanaso ya kammala masa kafin su dawo, seda aka kira sallar magriba ya ajiye ya tafi masallaci, be ƙara dawowa gidan ba seda tara na dare ta wuce. Time ɗin daya dawo maryam tana ɗakinta tana wanka, be mayi zaton ta dawo ba, saboda sanda zata tafi part din ammi ce masa tayi acan zata kwana. ɗakinsa ya shige shima a ɗan gajiye yake hakan yasa ya rage kayan jikinsa ya faɗa toilet. Bayan ya fito ya shirya cikin wata jallabiya brown colour, wadda ta masa kyau sosai se tashin daddaɗan kamshinsa yake. wayoyinsa ya kwasa guda biyu a hannu ya fito ya fice daga part din gabadaya ya nufi na ammi domin yakirawo maryam. Umaimah ce kaɗai zaune a falo tana cin abinci, yau da yunwa ta wuni saboda ɓacin rai seyanzu da taji yunwa ta kusa kasheta shine tana dawowa ta sauka akan abincin. Yana turo ƙofar tun kafin ya shigo daddaɗan kamshinsa ya fara kai wa hancinta ziyara, lumshe madaidaitan idanta tayi tana ƙara bubbuɗe kofofin hancinta yanda zata shaki kamshin yanda yakamata. sallama yayi babu yabo ba fallasa. Umaimah ta gyara zama tana tattaro nutsuwarta ta buɗe idonta ta sauke akansa cikin iyayi da neman suna ta amsa masa sallamar ta ƙara da faɗin, "yaya NOOR sannu da zuwa, ina yini" beko kalli inda take balle ma ya nuna yasan da zamanta a falon ya nufi ɗakin ammi ganin bata falon ita da wadda yazo nema. Ita kuma sakarya ta bishi da kallo baki buɗe. kamar koyaushe baya shiga ɗakin ammi se yayi knocking, yanzunma knocking din yayi. Ammi dake tsaye a gaban madubi tana fesa turare ta ajiye turaren ta nufi kofar ta buɗe. Sallama yayi cikin sanyin murya, ammi amsa masa tare da bashi hanya ya shigo cikin ɗakin. Ammi tana k gyara kayan kan mudubinta tace, "inata jiranka tun dazu ka shigo najika shiru har ina shirin kwanciya" yace, "kwanciya kuma da wuri haka ammi?" Ammi tace, "ehh na gajine yau baccin wuri zanyi" yace, "ayya sannu" ammi ta amsa da "yawwa, ta ƙara da faɗin. "Yaushe daddynka ze dawo ne, dazu munyi waya da uncle ɗinka yacemun yau yaje sun haɗu, harma daddy'n yace masa a cikin week ɗinnan zasu dawo." Mustapha yace, "jibi yace mun zasu dawo" ammi tace, "Allah yakaimu lafiya, kukuma se yaushe zakuje?" Yace, "Ran laraba insha Allah, amma ni kaɗai zani" ammi ta juyo ta dubeshi tace, "kai kaɗai kuma banda Maryam?" yace, "ehh" atakaice. Ammi tace, "shikenan, dama naji tana za'ayi bikin kawarta a cikin watannan seta biya ta dubashi idan taje" bece komai ba, saboda shi sam bayason wata alaƙa dazata ƙara haɗa Maryam da Sadik. ammi ta nufi kofa ta fita batare ta ƙara ce masa komaiba. wayarsa dake hannunsa ya shiga latsawa yana jin zuciyarsa babu daɗi. Ammi da plate ɗin abinci ɗauke a hannunta ta dawo ɗakin, agabansa ta ajiye tana faɗin "NOOR sakko kayi dinner" yamutsa fuska yayi bece komaiba ya sakko ya zauna a saman carpet din bakin gado, yasan ko yace baze ciba, ammi seta tursasashi. Ammi taga yanda yayi da fuska tayi kamar bata ganiba, tasan yanda taga ransa a bacennan ba ƙaramin aikinshi bane ya kwanta beci abincinba, shiyasa bazata barshi ya tafi ba seya ci abincin ko kaɗanne. dawowa ɗakin ta ƙara yi dauke da ruwa da ƙaramin cup ta ajiye a gabanshi tana kallon fuskarsa, shima kallonta yake cike da tsananin kaunarta. Hannunta ya kama ya sumbaci tafin hannunta, a hankali yace, "thanks UMMUNAH" murmushi kawai ammi tayi batace komaiba, zama tayi a kusa dashi tana kallonshi cike da so da kauna. A hankali ya fara cin abincin cikin nutsuwa kamar bayason ci bayan yayi bismillah. kaɗan yaci ya ajiye spoon din ya rufe abincin ya dakko ruwa ya tsiyaya ya sha. A fili ya furta "Alhamdulillah" mikewa yayi ya ɗauki wayoyinsa yayiwa ammi sallama ya tafi. ammi tayi murmushi bayan ya fita, komai idan mustapha yana yi se taga kamar midibbontane, komai nasu iri ɗaya ne sak babu ta inda Mustapha ya bar mahaifinsa seta yanda yake kallon abu da yanayin idanuwansa shine kawai ya dakko na ammi. abincin ta ɗauka ta fice dan ta kai kitchen tana jin zuciyarta babu daɗi itama, saboda tuno tsohon mijinta datayi.........

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull