Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 47
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 47: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 47. ........Bacci me daɗi ne yayi awun gaba da maryam cikin…
3,334 words
........Bacci me daɗi ne yayi awun gaba da maryam cikin kankanin lokaci. A jiyar zuciya ya sauke jin saukar numfashinta alamun bacci take. a hankali ya lallaba ya janyeta daga jikinsa ya kwantar da ita a gefensa. filo yasa mata tare da gyara mata kwanciya ya tofeta da addu'a. tashi yayi zaune yana jin kamar kar ya matsa daga kusa da ita. Fuskarta ya kurawa ido cikin wani irin yanayi kamar me son gano wani abu a fuskar. a wani ɓangaren kuma sosai ta masa kyau yanda take yin baccin, zara_zaran gashin idonta sun kwanta har ƙasan idonta abun sha'awa, bakinta ya kalla yayi murmushi ta ɗan turoshi gaba kamar kodayaushe idan tana bacci. ɗan yatsansa yasa a hankali ya shafi pink lips ɗinta cikin sauƙi, kamar ya zugata ta ƙara turo lips ɗin gaba, hakan da tayi ba ƙaramin kyau ta ƙara masaba yana son yaganta cikin yanayin shagawa shiyasa some times yana sane yake tabota, amma bayason kukanta ko kaɗan. wayarsa dake gefensa yasa hannu ya dakko, kunnawa yayi ya shiga Camera ya fara ɗaukar face ɗinta a hoto, kala uku ya mata pics din, kuma tayi kyau sosai a hoton murmushi yayi ya ajiye wayar, blanket yasa ya lullubeta sannan ya sauka daga kan gadon. Toilet ya fara shiga yayi wanka, bayan ya shirya cikin fararen kayan bacci masu taushi ya fita zuwa falo. kitchen ya shiga ya haɗa cofee ya yasha. Light din falon da ɗakin maryam dana kitchen din ya kashe ya koma ɗakinsa. seda ya ƙara duba wani abu a laptop dinsa sannan ya kashe musu light din ɗakin ya hau gadon ya kwanta shima. janyota yayi jikinsa yana sakin ajiyar zuciya, sosai yake cikin buƙatuwa da ita, amma wani tausayinta yakeji danshi kallon yarinya ƙarama yakewa maryam, a ganinsa idan ya fiya takura mata kamar da matsala, lumshe idonsa yayi kawai ya ƙara mannata a kirjinshi kamar ze maidata ciki, mutsu_mutsu Maryam ta farayi hakan yasa ya sassauta mata riƙon daya mata ya shiga shafa bayanta, shiru tayi taci gaba da baccinta, shikam ya ɗan jima kafin bacci ya daukesa.....
Washegari, Bayan anyi sallar asuba Maryam ta shiga gyaran gida mustapha kuma ya koma baccinsa. Bayan na gama gyaran gidan na koma ɗakina nayi wanka na shirya cikin wata doguwar rigar a baya dark blue, an mata ado da Stones masu sheki da walwali a gaban rigar da kasan hannunta. Ribbom nasa na daure gashin kaina, wata hula nasaka me kyau Black colour gaban hular me V ne, hakan yasa gaban kitsona ya fito se yayi kyau sosai, kwalli kawai nasa da white lipstick me ɗan ɗanƙo, se barima da na sa a kunnena. amma ni kaina nasan nayi kyau. Agogo na kalla naga goma na safe saura 2O minutes, falo na fito da nufin naje ɗakin yaya, kafin na ƙarasa se gashi ya fito cikin shirinsa shima, sanye yake cikin wani milk ɗin yadi me matuƙar kyau da tsada. Kallonsa Maryam take kamar yadda shima ya kura mata ido yana kallonta, tayi masa kyau sosai ze iya cewa ma tunda suke take be bata ganin ta masa kyau irin na yauba, kallon idanunta yayi yanda take kallonsa se yaji gabansa ya faɗi saboda abunda ya gani, sosai ya cika da mamaki mara misaltuwa zuciyarsa na ɗan bugawa ya ƙarasa takowa gareta, daf da ita ya tsaya harsuna jiyo hucin numfashin juna. Ƙasa nayi da idona da sauri murya ƙasa_ƙasa nace. "Ina kwana" be amsamunba se haɓata daya kama ya dago fuskata, lumshe idona nayi da sauri ganin yasaka idonsa cikin nawa bugun zuciyata na sauyawa, numfashi ya furzar a hankali kamar me rada yace, "Please ki buɗe idonki I want see something" bude idonnayi a hankali amma ba'akan fuskarsaba dan bazan iya haɗa ido dashiba. kallon idonta yake sosai da yanda take kallon gefe zuciyarsa nacigaba da bugawa, ya kai mintuna uku yana kallon idonnata, a hankali ya saki haɓartata yana sauke numfashi. shafa gefen kuncinta yayi yana murmushin gefen baki yace, "kinyi kyau" kallonsa nayi da sauri dan be taɓa faɗamun hakaba tunda muke, gira ya dagemun yace, "sosai fa" ƙasa nayi da kaina a hankali nace, "Nagode" cikin tsananin jin daɗi, murmushi yayi ya kama hannuna muka ƙarasa muka zauna akan kujera. Kwantar da kaina yayi akan kafadarsa yace, "me kikeso in siyo miki tsaraba" ya ƙarashe zancen yana haɗe hannuna da dashi. girgiza kai nayi alamar A'a, yana kallon fuskata yace, "why?" nace, "banason komai nidai kawai ka tafi dani dan Allah" wayarsa dake gaban rigarsa ce ta fara vibrate, hakan yasa be bani amsaba ya zarota ya daga ya kara a kunnensa, 3 seconds yace "Wa'alaikumussalam" ya ƙara ɗan jim kafin yace, "ohk ganinan" katse wayar yayi yana duban fuskar Maryam yace, "ki faɗamun me kikeso zan wuce ne yanzu" dago kaina nayi daga jikinsa da mamaki nace, "yanzu zaka tafi?" gyadamun kai alamun eh. Nace, "baka cifa abinci ba" yana bina da wani irin kallo yace, "ehh zanci acan" zan ƙara magana ya tashi tsaye tare kamo hannuna nima ya tadani. Tafiya ya farayi still hannunsa riƙe da nawa, hakan yasa nima na fara binsa kamar raƙumi da alaƙa, a zuciyata ban yarda ko kaɗan tafiyar zeyiba da gaske, saboda babu wata alama data nuna haka , tunda bacin wayarsa banga komai a hannunsaba. a bakin kofa ya tsaya yana kallona ƙasa nayi da kaina cikin wani irin sanyin jiki, ɗayan hannuna ya kama ya haɗe a hannunsa fuskarsa ya matso da ita daf da tawa yace, "zan wuce kimun addu'a" dago da kaina nayi na kallesa kwalla na taruwa a idona cikin sanyin murya nace, "wai dagaske kake tafiya zakayi yanzu?" daga mata kai yayi cikin matuƙar tausayinta, jiyake kamar ya canza ra'ayinsa ya tafi da ita amma akwai dalilin dayasa baze tafi da itanba. hawaye sosai Maryam take yi, rungumeta yayi tsam a jikinsa yana ɗan bubbuga bayanta, riƙe shi Maryam tayi sosai itama kamar me tsoron kar a rabata dashi. sosai yakejin ba daɗi a cikin zuciyars, ga kukanta dake taɓa masa zuciya yanajin kamar tana watsa masa garwashi a cikin zuciyarsa. Sun kai 6 minutes a haka kafin a hankali ya rabata da jikinshi jin tayi shiru se ajiyar zuciya datake saukewa. Hannunsa yasa ya share mata hawayen fuskarta. Idanunta ya kalla yace, "menene?" Girgiza masa kai nayi alamar A'a sannan nace, "Allah ya kiyaye hanya ya kaiku lafiya" "ameen" ya faɗa cikin wata irin murya, yanajin wani abu na yawo acikin zuciyarsa akanta. ƙasa na ƙara yi da kaina, inajin zuciya ba daɗi kamar na fashe da kuka haka nakeji. Kallonta yakeyi tamkar yau ya fara ganinta, kamar ya fasa tafiyar haka yakeji shima, danne duk abunda yakeji a zuciyarsa yayi ya kalli tsadadden agogon hannunsa yaga lokaci, sakin hannunta yayi yace, "bye, kikula da kanki" dago kaina nayi hawayen danaketa ƙoƙarin maidawa suka zubo. Lumshe idonsa yayi ya buɗe, ƙara janyota yayi jikinsa ya share mata hawayen fuskarta yana jifanta da wani kallo, amma bece komaiba. Cikin sanyin murya nace, "yaushe zaka dawo?" "Gobe" ya faɗa cikin wata irin siririyar murya. Ajiyar zuciya na sauke nace, "Allah ya kaimu, ka gaishesu sosai" yace, "zasuji insha Allah" ya ƙarasa zancen tare da kissing forehead ɗina, murmushi nayi na lumshe ido ina ƙara lafewa a jikinsa ina jin tamkar mu dawwama a haka. Shima Mustapha a nasa bangaren haka ne, ga kamshin jikinta daya masa daɗi sosai harya sanya ya fara jin wani irin baƙon yanayi ajikinsa, daurewa yayi ya rabata da jikinsa, gefen fuskarta ya shafa ya fice batare daya yarda ya ƙara kallon idontaba, saboda karta karya masa zuciya. binsa nayi da kallo harya fice daga falon gabadaya, sosai nakejin wata irin kewarsa tun yanzu ta lullubeni, jan ƙafata nayi na faɗa kan kujera na zauna ina sauke numfashi. Mustapha shima jikinsa duk a sanyaye ya nufi part din ammi. A falo ya tarar da umaimah tana mopping tana ganinshi kamar wadda taga dodo ta zura da gudu tayi ɗakinta, tabe bakinsa yayi dan ba ita yakeba ya shiga ɗakin ammi. Ammi na dubansa bayan sun gaisa tace, "bangane tafiya zakayiba yanzu bakaci komaiba, yau bamu tashi da wuri bane shiyasa mukayi late gurin aiki" mustapha ya ɗan ja numfashi yace, "karki damu ammi zanci abinci idannaje can" ammi ta masa wani kallo, batace komaiba ta mike ta fice daga ɗakin. binta yayi da kallo cikin kaunar ta, shi kanshi yana jin yunwar amma yanda zuciyarsa take cike da ɗokin ganin daddy dasu haidar yasa baya ta abincin. Bayan wasu mintuna ammi ta dawo ɗakin hannunta ɗauke da cup data haɗa masa tea me kauri, batace komaiba ta mika masa. ba musu shima ya karba ya fara sha, a hankali yake kurba har yasha sosai, ya ajiye sauran, ammi bata kyaleshi haka ba seda ta bashi dabino me ɗan yawa tace yaci, be cinye dukaba a leda tasa masa sauran tace yaci a hanya. Sallama ya mata ya tafi, bayan ta kwarara masa ruwan addu'a tare da jaddada masa karya manta ya tahowa da Maryam da wayar hannu. daze tafi yana kallon part ɗinsu kamar ya shiga ya ƙara ganin yar matartasa, amma dai ya hakura be shigaba ya nufi inda driver'n ammi yake jiransa tun dazu.....
Tunda na zauna nayi jugum ni kaɗai, ƙwaƙwkwaran motsi banyiba, na kusa awa a haka da ƙyar na yunkura na tashi na shiga ɗakina na dakko hijabi na saka na fito zuwa part ɗin ammi. Suna falon duka matan gidan har mama nafisa datayi tafiya dangin mijinta se jiya da daddare ta dawo. danne damuwata nayi muka gaisa da kowa faran_faran nayiwa mama nafisa sannu da zuwa. umaimah se jifan maryam take da wani mugun kallo, ita dai maryam tunda ta gaisheta kota kanta bata ƙara biba. ɗaki ammi ta kaimun abinci tace inje inci, yanda nake jina wani iri abincinma bana son ci, haka dai na daure na cuccusa, duk da hakanma kaɗan naci na barshi.....✍️ Meson COMPLETE Whatsapp 08166674823
*ABINDA KASHUKA....!*
_*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_
*7️⃣1️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
..........Wunin yau gabadaya a ɗakin ammi na yishi, ina ta juyi akan gado ko aiki banyiba. Sosai kewar yaya ta cikamun zuciya, gashi Ni ba wayaba balle na kirashi koshi ya kirani. Bayan sallar la'asar ina zaune akan dadduma a ɗakin ammi, idar da Sallah ta kenan ammi tashigo ɗakin, zama tayi a gefen gado tana dubana tace, "ɗiyata ya kannaki?" _Dayake dazu data tambayeni meke damuna nace mata kaina ke ciwo_ nace "da sauƙi" tace, "to Allah ya ƙara sauƙi, bari na kawo miki abinci kici kisha magani, gobe da safe idan Allah yakaimu da kaina zan kaiki asibiti, wannan ƙananun ciwukan su suke zama babba Allah ya kiyaye dai" nace "ameen" ammi ta ɗauki wayarta tayi dialing number'n mustapha, amma be ɗagaba mikomun wayar tayi tace, "gashi idan yakira ki ɗaga bari na kawo miki abincin. Karbar wayar nayi ita kuma ammi ta fice, number salimat na lalubo nayi dialing, karawa nayi a kunnena jin tana ringing, ringing uku ta ɗaga da sallama. Amsa mata nayi na ƙara da faɗin "Amaryarnan baki da kirki ko kaɗan" dariya tayi tace, "rashin kirkin menayi kuma kawata?" nace, "ko nemana bakyayi, rabon da muyi waya dake tun sallah" saleemat tace, "wlh bahaka bane, kinsan ba wayarki bace banason na kira bansamekiba" nace, "idan kika kira kodayaushe zaki sameni, sedai da daddare ne baza ki sameniba" saleemat tace, "to dama ina Ni ina kiranki da daddare ai nasan lokacin kina...." Katseta nayi da fadin, "naji karkimun iskanci da kika saba, ina ummata?" Umma tananan kalau wlh, ya Jos ɗin?" Nace, "Masha Allah kigaidamun da umma sosai dan Allah, Jos lafiya kalau" saleemat tace, "zataji insha Allah" nace, "saura kwana nawa ne bikin?" Tace, "saura sati huɗu duk da satin bikin" nace, "Allah yakaimu, baki turomun ankon ba to, kar lokaci ya kure na rasa ɗinki" saleemat tace, "ke umma ta sai miki ankon duka, dama guda biyu ne, harta bada a miki ɗinki." Cikin jin daɗi nace, "Allah sarki ummata, ita datake da hidima amma shine harda saimun anko, Nagode sosai Allah yasaka da Alkhairi, ki bata wayar na mata Godiya. Saleemat tace, "ameen, amma ta fita yanzun taje kasuwa, anjima idan ta dawo zankiraki na haɗaku" nace, "to Allah yakaimu, ina gwaggotah" tace, "gwaggo tananan kalau, dazu ma ta shigo da rana" nace, "inason kiranta a waya ko har yanzu bata da wayane?" Saleemat tace, "akwai waya a hannunta bari yanzu zan fita sena karbo miki number ta, naturo Miki" nace, "to Nagode" mukayi sallama na kashe wayar. Ammi ta shigo ta kawo mun abinci da ruwa da maganin ciwon kai, ta tambayi har yanzu be kiraba, nace mata eh. Ina cikin cin abinci wayar ammi ta fara ringing, ni kaɗai ce a ɗakin ammi ta ƙara fita. Ɗauka nayi na duba gabana na faduwa, na ɗauka yaya ne senaga bakuwar number, kamar kar na daga se kuma dai na daga tana daf da tsinkewa. Muryar wadda naji tayi sallama yasani saurin cewa, "gwaggo!" Cikin doki, gwaggo ma a ɗaya ɓangaren cikin fara'a tace, "na'am Maryama" nace, "gwaggo nayi kewarki da yawa" tace "nima haka Maryama, ai bansan ana samunki a wayaba da tuni na karbi lambar na kiraki" nace, "nima gwaggo bansan kinyi wayaba ai, ya jikinnaki?" gwaggo tace, "jiki da sauƙi, amma har yanzu da sanda nake dogarawa nake tafiya" cikin tausayawa nace, "ayya Allah ya ƙara sauƙi, yaushe zakizo gwaggo?" gwaggo tace, "ina son zuwa naganki Maryama ko dan na nemi yafiyarki akan irin cutarwar dana miki, amma ƙafata bazata juri zaman mota ba" nace, "gwaggo dan Allah ki bar wannan zancen, Ni babu abunda kikamun idanma da akwai na yafe miki tuntuni" gwaggo cikin kuka tace, "kayya Maryam da akwai abunda na miki mana, gashinan yanzu tun ba'aje ko'inaba na fara ganin sakayya nasanma kaɗan nagani dan...." "Dan Allah gwaggo kidena faɗin haka karki sani kuka nima, Ni bakimun komaiba" gwaggo tace, "shikenan yar albarka nadena, Allah ya miki albarka, ya baki ƴaƴa nagari kamar ke masu hankali da biyayya, Allah yajikan mahaifiyarki Maryama da yaya Fatima(inna), ya kuma bayyana miki mahaifinki idan yana raye da danginsa" nace, "ameen gwaggo ina su baba Ilya da sauran mutan ƙauyen?" Gwaggo tace, "sunanan kalau, suna yawan zuwa suna dubanima ba subi ta halinaba" nace, "to duk a gaidasu" tace, "zasuji ya maigidannaki?" Nace, "yananan kalau, yau yama taho Kanon" gwaggo tace, "Allah yakawoshi lafiya, dafatan dai komai lafiya" nace "lafiya kalau gwaggo" mun ɗan jima muna hira da gwaggo sannan mukayi sallama, wayar da mukayi da gwaggo ta ragemun damuwar kewar yaya danake ciki, cin abincina nacigaba dayi.....
*KANO*
Tunda suka shigo Kano yake bin garin da kallo yanajin farinciki na ratsa zuciyarsa, ji yake kamar yayi wasu shekaru rabonshi da Kanon, wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da suka shigo katon layinsu ya hango gidansu. Sedai kuma lokaci ɗaya ya tuna wani abu daya dishashe masa farincikin da yake ciki, ba komai ya tuna face mommy. Lumshe idonsa yayi ya jinginar da kansa a jikin kujera yana ɗan jan numfashi. A ƙaton gate din gidan na tsakiya driver'n ya tsaya ya fara danna horn, bajimawa wasu daga cikin masu gadin gidan suka taso suka wangale musu gate din, dama already sun san da batun zuwansa. Buɗe idonsa yayi a hankali jin sun shigo gidan, glass din barin dayake ya zuge ƙasa a hankali, ma'aikatan gidan ya shiga ɗagawa hannu kamar yadda suma suke masa, kasancewar driver'n slowly yake tafiya da motar har sannu da zuwan da suke masa yana ji, parking space suka nufa yana cigaba da bin gidan da kallo, babu abunda ya sauya a gidan tun bayar tafiyarsa har zuwa yau. Zannurain, haidar da faruq da tundazu suke dakon zuwansa a harabar gidan suka nufo gurin motar tasu da sauri zuciyoyinsu cike da ɗoki da son ganin ɗan'uwansu. A hankali ya buɗe murfin motar ya ziro ƙafarsa guda ɗaya, seda ya ɗanyi wasu sakanni sannan ya ziro ɗayar itama, kafin ya fito dukansa daga cikin motar, dai_dai nan su haidar suka ƙaraso gurin, haidar ne yayi sauri ya rigasu ƙasarawa garesa yana dariyar farinciki ya rungumeshi yana faɗin, "welcome big bro" rungumeshi shima Mustapha yayi cikin tsananin farinciki yace, "Thank you dear" suma su faruq rungumeshi sukayi gaba-ɗayansu suna welcoming dinshi, abun gwanin ban burgewa. duka ya haɗa su shima ya rungume cikin jin daɗi da farin ciki mara misaltuwa, da kyar suka sakeshi kowa yana faɗa masa yanda yayi missing ɗinsa, shidai murmushi kawai yake saki yana binsu da kallo, haidar riƙe da hannun damansa zannurain kuma na hagu, faruq kuma yana gabansu suka nufi cikin gidan, bayan sun haɗa driver'n da wani ma'aikacin gidan domin ya kaishi masauki, part ɗin daddy yaga sun nufa dashi.
A main parlour suka tarar da daddy zaune shida wasu yan'uwansa har da wata mace cousin din su daddy ce, tun randa su daddy suka dawo tazo gidan, a gidan da aka riƙe Aunty take sunanta Hajiya zuwaira yara kuma na kiranta da mami. Daddy na hango mustapha ya mike ya taryoshi cikin farincikin ganinsa fuskarsa ɗauke da murmushi, Shima Mustapha sakin su haidar yayi, yayi hugging daddy cikin tsananin kewarsa. Daddy yace, "welcome son, dafatan kun ƙaraso lafiya" mustapha na sakin daddy yace, "thank you Dad, mun ƙaraso lafiya kalau" daddy ya shafa kansa cikin tsananin farin cikin ganinsa, yayi matuƙar kewar ɗannasa ba kaɗan ba. daddy riƙe da hannunsa suka ƙarasa cikin falon, gaishe da mutanen falon Mustapha yayi cikin girmamawa, suka amsa masa suma cikin fara'a. daddy se nan_nan yake da mustapha yarasa inda ze sakashi dan farincikin ganinshi. Bayan sun gama gaisawa daddy ya tambayeshi ya su Maryam da ammi, yace masa duk sunan kalau. daddy da kanshi ya masa jagora zuwa bedroom ɗinsa kamar wani bako, mustapha murmushi kawai yake ciki jin daɗin yanda daddy yake masa, a toilet din daddy yayi wanka, kafin ya fito faruq ya kawo masa wasu sabbin ƙananun kaya. Bayan yagama shiryawa yayi sallar la'asar dabe samu yayita akan lokaci ba, ya fito falo inda yatarar an shirya masa lifaya ta abubuwan ciye_ciye dana sha. Mami da kanta ta kama hannunsa ta kaishi har dinning, zama yayi yadubeta yace, "Nagode mami" mami na serving dinshi cikin tausayinshi akan abunda mommy ta aikata masa tace, "bakomai ɗana, ashe haka al'amura suka faru" gyada mata kai kawai yayi alamar eh, danshi bayason ana tuno masa da abunda ya faru abaya. mami tace, "Allah ya kiyaye gaba,ya rabu da mutane masu irin halin Atika, Allah ya rabamu da sharrin makiya" cikin sanyin murya yace "ameen" mami ta tura masa abincin data zuba gabansa tana faɗin, "ya iyalinnaka, Alhaji yace kayi aure" yace "sunanan kalau" mami tace, "Masha Allah, Allah yabaku zaman lafiya da zuri'a dayyiba ya haɗa kanku" yace, "ameen" yana cin abincin mami tana masa hira, harta masa murnar gamuwa da mahaifiyarsa. Bayan ya gama cin abincin daddy ya masa jagora zuwa ɗakin da Sadiq yake. Yana kwance akan gado yana bacci kamar gawa, ya rame yayi baƙi bakadanba. Mustapha tsayawa yayi yana kallonsa cike da tausayawa, kallon daddy yayi yace, "dad wai meke damunsa ne?" Daddy ya sauke dogon numfashi yace, "gashinan dai Son, ciwonnasane dai ankasa gane kansa, a Saudiyyan dai suna masa maganin Islamic, shine jikinnasa yayi kyau haka" jinjina kai mustapha yayi cikin jimantawa aransa yana mamakin abunda daddy yace, akan jikin Sadik duk yanda yaganshi ɗinnan ace wai ahakanma jikin yayi kyau. Kiran sallar magriba ne yafitar dasu daga ɗakin. Bayan sun dawo daga masallaci su haidar suka zagayeshi suna masa hira, shima sakin jikinsa yayi ya biye musu suka sha hira, hakan ya ɗauke hankalinsa be kira ammi ba, ya sanar mata sun sauka lafiya, saidai duk abunda yake tunanin Maryam na nan manne a cikin ransa.......
Bayan na gama cin abincin na fita falo muka ɗan taɓa hira dasu Aunty zuhura, har akayi sallar magriba wayar ammi na hannuna ina dakon kiransa amma naji shiru, ammi ma ta tambayeni ya kira nace mata A'a, har akayi sallar isha'i be kiraba. Ajiye wayar nayi zuciyata babu daɗi na kwanta akan gadon ammi, dan anan zan kwana, bacci ne ya ɗaukeni batare dana shirya masaba.........