Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 48
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 48: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 48. Mustapha be samu kansaba se kusan ƙarfe goma na dare,…
2,467 words
Mustapha be samu kansaba se kusan ƙarfe goma na dare, part ɗinsa na gidan anan ze kwana, daddy yayi zaton tare zasuzo da Maryam shiyasa yasa aka gyarashi tsaf idan sunzo su sauka. yana shiga ɗakin shi ya zaro wayarsa daga aljihunsa, missed call ya gani har 5, na ammi 2 sena Aunty 1 se kuma wata bakuwar number 2. Layin ammi ya kira dan cike yake da kewarsu musammanma yar meronsa. Ammi ta ɗaga wayar da sauri dama tana hannunta, mustapha ya mata sallama ta amsa ta ƙara da faɗin, "NOOR ina shiga ne inata jiranka baka ɗagaba?" Mustapha yace, "babu inda na shiga ammi, muna tare dasu daddy ne banma dakko wayarba se yanzu" ammi tace, "amma kasan ai zan nemeka inji ya kukaje kanon, yanzu hankalina harya fara tashi danaji shiru ina shirin kiran dad dinnakama tunda kai na kiraka baka ɗaga ba, kiranka ya shigo" mustapha yayi murmushi yace, "ayi hakuri Amminah kinsan mun daɗe bamu haɗu ba muna ta hirar yaushe gamo" ammi tace, "shikenan kunje lafiya?" Yace, "lafiya kalau" ammi tace, "Masha Allah" shiru yayi yanaso ya tambayi Maryam amma miskilancinsa ya hanasa, ammi jin yayi shiru tace, "kaje ka kwanta ka huta to, da safe mayi waya" yace, "Allah yakaimu" ammi tace, "Ameen, karka manta fa, idan Allah yakaimu goben kaje kagaida gwaggonta" yace "insha Allahu" ammi ta katse kiran. ajiyar wayar yayi ya rage kayan jikinsa ya shiga toilet ya watsa ruwa, be tsaya yin komai ba ya kwanta saboda gajiyar dake damunsa, lumshe idonsa kawai yayi amma sam bacci yaƙi zuwa, sosai kewar Maryam take damunsa, yanzu daya kwanta kamar an ƙara masa kewartata, ya saba kwanakinnan manne da ita yake bacci yana shaƙar kamshinta dayake matuƙar yi masa daɗi, yana shafa lallausar fatarta, secan dare ya samu bacci ya ɗauke sa bayan yagama juye_juye da rungumar filo.....✍️
Hehehe wlh kun kusa daina ganin book din nan banji kihuyar posting ba saikune kuke ƙihuyar Comments 🤔🤔 update 8pm Meson complete Whatsapp 08166674823
*ABIN DA KA SHUKA....!*
_*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_
*7️⃣2️⃣*
*Bismillahirrahmanirrahim*
..........Washegari haka na tashi sukuku dani kamar mara lafiya, baccinma gabadaya be mun daɗi ba, a daren jiya na farka ya kai sau uku, zuciyata babu daɗi ko kaɗan, kallo ɗaya mutum ze mun ya gane hakan. Gari na fara haske muka shiga kitchen nida ammi, duk dauriyar danake na boye abunda yake raina seda ammi ta gane. Ina cikin ferayar dankali ta dubeni tace, "ɗiyata jikinne dai?" A hankali nace "A'a, aina warke" ammi tace, "ki koma ɗaki ki kwanta, yanzu zuhura zatazo semu ƙarasa aikin tare, idan mun gama sena kaiki asibin" nace, "Toh ammi" na ajiye wukar hannuna na fice, ɗakin ammi na koma na kwanta akan gado. Lumshe idona nayi ina hango yaya a idona cikin matuƙar kewarsa, yanda nakeji a raina kamar bana tare da wani sashi na jikina, Har ƙarfe tara na safe inanan kwance, da naga kwanciyar bazata munba, sena tashi na hau gyaran ɗakin ammi, bayan na gama na fito falo da nufin na gyarashi shima sena tarar da umaimah tana mopping, bance mata komaiba kamar yadda itama naga babu alamar hakan a tattare da ita, ficewa nayi daga falon gaba-daya, umaimah ta raka Maryam da harara tana tabe baki. part ɗinmu na koma dannayi wanka, kafin nayi wankan seda na gyara gidan duk da babu wani datti a cikinsa, na daɗe a ɗakin yaya ina shaƙar kamshinsa dake manne a ɗakin kamar yananan, kamar kar na bar ɗakin haka nakeji, ba dannasoba na fito ɗaga ɗakin na koma ɗakina bayan na gama gyarashi, wanka nayi na shirya cikin sauri saboda nasan ammi tanacan tana jirana zamu asibiti. ina komawa part din ammi na tarar har sungama aikin sun karya, itama ta shirya jirana kawai take. Abinci na debo na faraci a ɗakinta, kafin na gama cin abincin ammi tayi baƙi, Bayan na gama cin abincin na fito falo muka gaisa dasu, mata ne guda uku se kallona sukeyi, ammi ta dubeni tace, "Maryam kinga nayi baƙi, ki bari gobe idan Allah ya kaimu sai muje" nace "Allah yakaimu lafiya" ɗaki na koma na ɗauka comp da kibiya na fara tsifar kaina.....
Da ƙyar ya iya tashi yaje masallaci yayi Sallah saboda baccin dake cinsa tunda besamu wani ishashshen bacciba a daren jiya, yana dawowa daga sallah ya ƙara bin lafiyar gado, wayarsa dake gefen kansa ta fara ringing wanda shine yayi sanadiyyar farkawarsa daga baccin. yana yatsina fuska na dakko wayar ya duba, Aunty ce take kiransa kafin ya kai ga ɗagawa har kiran ya katse, bin bayan kiran yayi, ringing ɗaya ta ɗauka tare yin sallama, cikin murya me cike da bacci ya amsa mata yana tashi zaune, ya ƙara da faɗin "ina kwana Aunty" aunty tace, "lafiya kalau Muhammad, bacci kake ne naji Muryar haka?" ɗan gyaran murya yayi yace, "ehh yanzu na tashi" Aunty tace, "Toh ko inbari later mayi maganar?" yace "A'a dama ina son kiranki naga missed call ɗinki jiya" aunty tace "ehh dama inason kamun transfer din kudi ne" yace "ok kamar nawa?" Aunty tace "1.5 ma is ok" aransa yana mamakin me Aunty zatayi da Kudi haka, amma ya danne mamakinsa yace, "ok zantura Miki anjima" Aunty tace "thank you, kana kanonne?" Yace "ehhh nazo tun jiya" Aunty tace "nima a satinnan zan shigo insha Allah" yace "Allah yakawoki lafiya" daga haka sukayi sallama ya katse kiran. jingina bayansa yayi da jikin gado yana lumshe idonsa, Maryam kawai yake hangowa a idonsa, tafiyarta, maganarta da yadda takeyin komai cikin sanyi duk yake tunawa, buɗe lumshashshun idanunsa yayi, wayarsa dake hannunsa ya latsa, pics ɗin daya mata tana bacci ya lalubo ya fara kalla, wani murmushi ne ya subuce masa, yayi missing shagwabarta sosai, yayi 10 minutes yana kallon hotonnata cike da shauki, zooming pic din yayi dai_dai pink lips ɗinta daketa kyalli kamar a zahiri yake ganinsu, wayar ya kai bakinsa yayi kissing pic ɗin, a fili ya furta "I MISSED YOU" badan yagaji da kallon pic dinba ya a jiye wayar ya mike a hankali ya nufi toilet. Ya ɗauki lokaci kafin ya gama shiryawa ya fito falo, a falon ya tarar da haidar zaune yana latsa waya. haidar yana ganinshi ya ajiye wayar hannunsa cikin murmushi yace, "ina kwana yaya" mustapha ma dan murmusawa yayi yace, "lafiya kalau" haidar ya nuna masa dinning yace, "your breakfast is ready, tun dazu Mami ta shirya maka" murmushi yayi ya juya ya nufi gun dinning din, da kanshi ya tsakuri ɗan abin da ze iya ci, yaci ya barshi, goge bakinsa yayi da tissue ya mike yana hamdala ga Allah. tsadadden agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ya duba yaga har 11am, ta wuce, wayarsa ya zaro daga aljihun gaban rigarsa yayi dialing number ammi, lokacin ammi tana falo tare da baƙin ta,Maryam kuma tatafi part ɗin Aunty zuhura domin tayata tsifa, ammi ta ɗaga bayan sun gaisa tace masa. "Ya me jikin kuma?" yace, "da sauƙi" ammi tace "Allah ya ƙara sauƙi" yace "ameen" haidar daya fahimci dawa mustapha yake wayar yace "yaya bani mugaisa da ita" mustapha bece komaiba ya miƙa masa wayar, tasowa haidar yayi ya karba, suka gaisa da ammi sosai cikin mutunta juna, ammi ta masa yame jiki tace kuma ya gaida daddy, miƙawa mustapha wayar yayi sukayi sallama da ammi ya kashe wayar, yanzuma miskilancinsa ya hanashi tambayar Maryam duk da yanda zuciyarsa take cike da tsananin kewarta, gashi ammi itama taƙi masa zancenta bare yasan halin datake ciki, sosai yake bukatar jin koda muryar tane ko yaji sauƙin a bunda yake a cikin ransa, kamar ya kuma kiran Ammi yace ta bata wayar haka yakeji, amma baze iyaba. siririn tsaki yaja ya fesar da huci, a ransa yace _"da tana da wayarta da duk haka bata faruba"_ mikewa yayi yana duban haidar yace, "muje na gaida daddy da mami ka rakani wani guri" haidar ya amsa masa suka fito suka nufi part ɗin daddy, bayan sun gama gaisawa da daddy ya ƙara duba jikin Sadik dake ta bacci still, yacewa daddy zeje wani guri ya dawo, kasuwar sai da wayoyi yacewa haidar ya kaishi, waya me kyau da tsada ƙirar kamfanin samsun ya siyawa Maryam, suna komawa gida yayiwa Aunty transfer din kudin da tace ya mata.
Da yamma bayan sallar la'asar mustapha da daddy ne suka fito cikin shirinsu zasu gidan gwaggo domin gaisheta, da mustapha yacewa daddy ze jene, shine daddy'n yace suje tare shima ya gaishenta ya kuma duba jikinta, seda suka kira Aunty tayiwa driver'n Daddy kwatance gidan sannan suka tafi. basusha wahalar gane kwatancen layinba tunda babu nisa da titi kuma wajen firamare ne, direban yasan gurin, gidannedai seda suka tambaya aka nuna musu. A Kofar gidan gwaggo direban ya faka motar kasancewar motar tana shiga har layin. fitowa sukayi daga motar mustapha ya shiga bin layin da kallo, dan wannan shine karo na farko daya zuwa irin wannan unguwar a rayuwarsa, abokinsa lukmanne ya fado masa rai, ya manta rabon da suyi waya dashi gashi yanzu yayi aure baya unguwar gandun sarki, daya biya ta gidansu sun gaisa. yaro Daddy ya samu ya turashi gidan gwaggo dan a sanarmata da zuwansu, gwaggo na zaune a tsakar gida akan tabarma ita da asabe wadda take zaune a gurinta yaron ya shigo yayi sallama, su gwaggo suka amsa masa. Yaron yace "wai ana sallama da gwaggo" gwaggo tace, "Ni kuma dannan suwaye?" Yace "wasu ne a mota me kyau su biyu suma masu kyau" gwaggo tace, "jeka tambayo kace suwaye" yaron ya fita bajimawa yadawo yace, "wai yace Alhaji mainasara ne da.." gwaggo ta kwalalo ido waje ta katse yaron da sauri tace, "wakace yaro?" Yaron ya kuma cewa "Alhaji mainasa" gwaggo ta dubi asabe da dunbin mamaki a fuskarta tace "asabe! Kinji wa akace yana sallama, wai Alhaji mainasara ko kunnenane beji daidaiba?" Asabe tace, "a'a gwaggo shi akace" gwaggo ta dubi yaro tace, "jeka maza kace ya shigo" ta juyo ga asabe tace, "dakko musu wannan ƙatuwar daddumarnan sabuwa ki shimfida musu" asabe ta mike da sauri ta dakko dardumar ta shinfida, daidai lokacin su Daddy sukayi sallama. gwaggo ta amsa musu tana washe gajiyayyun haƙoranta tana binsu da kallo cikin tsananin farin ciki tace "sannunku da zuwa Alhaji, dafatan kunzo lafiya?" Daddy ya zauna da fara'a yace "lafiya kalau baaba ina wuni" gwaggo kamar zata ɗauki Daddy ta ɗora a cinya yanda take acting tace "lafiya kalau Alhaji, ya iyali?" Mustapha dai kawai kallonta yake ta ƙasan ido, a ganin farko daya mata a rayuwarsa yaji sam matar bata masaba" bayan sun gama gaisawa da daddy kamar wanday akaiwa dole yace "ina yini" gwaggo ta kalleshi da Fara'a tace "lafiya kalau dannan" daga haka be ƙara cewa komaiba, asabe ta gaishe da daddy da mustapha suka amsa mata. gwaggo ta dubeta tana kunce hannun zaninta tace "ungo ɗari biyu nan kisiyo musu lemo da ruwa, bari in kawo muku abinci" Daddy ya dakatar da ita da faɗin, "A'a baaba ki barshi, a koshe muke mukam" gwaggo tace "to ai ko ruwa kwasha Alhaji" Daddy yace "ki barshi baaba mungode, ya jikinnaki kuwa" gwaggo tana maida 200 ɗinta cikin zani tace, "jiki ai yayi sauƙi Alhamdulillah" Daddy yace "Masha Allah, Allah yakara lafiya, ai naso zuwa tun wancan lokacin to sai kuma wani uzuri ya tsaidani" gwaggo tace "bakomai ai Alhaji, a hakanma Nagode ai naga saƙo gurin Hajiya(Aunty) nagode" Daddy yace "babu komai, sai kuma maganar yarinya Maryam dana aurar da ita batare da neman izni ko yardarku ba, da....." Gwaggo ta katseshi da sauri da faɗin "haba alhaji, babu komai ai, kaima uban Maryam ne kana da iko akanta, ka kai da zartar da duk wani hukunci dakaso, mune da godiya ai dabaka kyamacemuba ha haɗa zuri'a damu" Daddy yayi murmushi ya mata Godiya, shidai mustapha yayi tsit kamar babu shi a gurin. Gwaggo se sakarwa daddy zantuka takeyi, shi kuma kawai sedai ya bita da murmushi da eh'ko A'a, ganin ƙarfe shida ta gabato Daddy yacewa gwaggo su zasu wuce, nuna mata Mustapha yayi yace "ga sirikinnakifa, shine mijin Maryam ɗin" gwaggo ta gwalalo ido waje tana kallon Mustapha, aranta tace _"yanzu wannan mutumin me kama da Balarabe shine mijin maryam"_ jinjina kai tayi tace, "Masha Allah, ɗana ashema kaine sirikinnawa to Allah ya baku zaman lafiya, dafatan dai baka fuskantar wata matsala daga gurinta?" Mustapha ya gyada mata kai kawai. Tace "aidama nasan Maryama yarinyar kirki ce gata da biyayya da hankali, bata da wata matsala ko...." maganar gwaggo ta makale lokacin dataga uban kuɗin da Daddy ya fito dasu daga alhajinsa ya ajiye a gabanta.Gwaggo ta wangale bakinta tana duban Daddy dake cewa, "bamu samu mun taho da komai ba ga wannan a sai goro" gwaggo ta haɗiye wani yawu tace, "Alhaji angode Allah yasaka da Alkhairi, ya raya zuri'a yajikan mahaifa, Allah ya ƙara buɗi" Daddy ya amsa da "Amin" yana bin bayan mustapha wanda tuni yayi gaba, gwaggo har ƙofar gida ta bisu babu ko lullubin kai se ɗan kwali tana zuba musu Godiya, mustapha yana jingine jikin motar yana latsa wayarsa, saleemat ce ta fito daga gidansu hannunta riƙe da leda zata kaiwa wata kawarta a tamfar anko, kallon su Daddy take cike da mamaki ganinsu a ƙofar gidansu, gasu ƴan gayu dasu wanda kallo ɗaya zaka musu kasan Naira ta zauna a gurin su, bata lura da gwaggo sai daga baya anan ta gane ashe gurinta sukazo, gaishe da Daddy tayi cikin girmamawa duk da batasanshiba, amma tana ganin kamar tasan fuskarsa, amma ta kasa tuno inda tasan sa, Daddy ya amsa mata da fara'a, shima Mustapha gaisheshi tayi a ranta tana yaba kyawun da Allah yayi masa kamar ba ɗan ƙasar nan ba, ya amsa ba yabo ba fallasa, ta gaida gwaggo ma ta wuce, seda gwaggo taga barin motar su daddy layin, Sannan ta dogara sandarta ta koma cikin gida da ƙyar kamar wadda zata bisu. Zama tayi akan dardumar dasu daddy suka tashi ta ɗauki kuɗin tana jujjuyashi a hannunta kafin ta dubi asabe tace "Asabe kinga ikon Allah ko, nida na ɗauki Maryam na kaita aikatau danta wulakanta se gashi ita aikatau ɗin ma ya zamar mata Alkhairi, jibi fa wanda akace shine mijinnata kamar shi yayi kansa dan kyau, anya kuwa wannan ma bahaushe ne kuwa?" Asabe tace "ikon Allah kenan gwaggo yafi gaban komai, amma dai Maryam tayi sa'ar miji" gwaggo tace "Ni duk ba ma wannan ba, wai yau Ni Ladi nice Alhaji mainasara yazo har cikin gidana da sunan ya gaisheni, wayyo daɗi kasheni wlh jinake kamar mafarki nake asabe..." Haka gwaggo taita zubarta cikin tsananin farin cikin yau Alhaji Mainasara ya zo gidanta, asabe dai se dariya take mata, Maryam kam tasha addu'oi kala_kala, kamar ba ita ce da gwaggo take tsine mata ba gami da aiba tataba........✍️
Meson complete Whatsapp 0816667482
*ABIN DA KA SHUKA....!*
_*BY*_ _*ZEEY KUMURYA*_
*Bismillahirrahmanirrahim*
*7️⃣3️⃣*