Kenza eBookz

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 49

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 49

Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 49: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 49. ...........Se azhar na baro part din aunty zuhura, acan…

2,470 words

...........Se azhar na baro part din aunty zuhura, acan na wanke kannawa, na busar dashi Bayan mun gama tsifar, part din ammi na koma nayi Sallah sannan na shiga kitchen muka ƙarasa girki Ni da umaimah, har lokacin baƙin ammi sunanan, muna gama girkin ko tsayawa cin abincin banba na koma part ɗinmu, sosai kewar yaya ta cikamun zuciya kamar mara lafiya haka nake jina, komai ina yinsane cikin dauriya da ƙarfin hali, amma idan na tuna yau ze dawo se inji farin ciki ya lullubeni, gyaran part ɗinmu na shiga yi bakama ƙafar yaro cikin zumuɗi, ko ina na shareshi nayi mopping na sauya zanin gadon ɗakina dana ɗakinshi bayan na feshesu da turare, gidanma gaba-daya na buɗade shi da turaren wuta me daɗin gaske, se wajen ƙarfe shida na gama gyaran gidan, wanka na faɗa toilet na tsalo na shirya cikin wata atamfa super ɗinkin riga da zani, ɗinkin rigar yayi matuƙar kyau yamun dass a jikina, gashin kaina na faka a ƙeya, ya sauka har gadon bayana, nannade gashin nayi a jikin ribbom ɗin kaina na kafa daurin ture kaga arziki(ba ture kaga tsiyaba🙁), dankunne da sarka masu kyau na saka, harda agogo da abun hannu duk na saka, ba wata kwalliya nayiba amma Ni kaina nasan ba ƙaramin kyau nayiba, powder kawai nasawa fuskata kalar fatata, se kuma kwalli da white lipstick me ɗan ɗanko se cikakkiyar girata dana taje da brush ɗin tajeta, humra na me sanyi da daɗin kamshi na buɗaɗe jikina da ita, tare da turaren fesawa shima me sanyin kamshi da daɗi, se kamshin ya haɗu ya bada wani kamshi me daɗin gaske, kallon kaina nayi a madubi na ƙara kallo a fili nace, "ALHAMDULILLAHILLAZI, AHSANIL KALK'I WA KALK'IHI" jin cikina ya fara kiran ciroma saboda yunwa, na dakko mayafina daya shiga da a tamfar na yafa a saman kaina, na fito na nufi part din ammi danna ci abinci. Fitowar Maryam daga part ɗinta yayi dai_dai da zuwan fareedah gidan, tazo ne dantaga Mustapha ta fara nuna masa kudirinta a kansa, amma ita da kissa zata masa bada hauka irin na umaimah, tana sanye da zunbulelen hijab har ƙasa, a matsayin ita mutuniyar kirki ce. Maryam na gaba batama lura da itaba ita kuma tana binta a baya, ƙurawa bayan Maryam ido tayi tana kallon yanda jikinta yake juyawa duk da mayafi, zanin data daura ya fito mata da shap ɗin jikinta sosai, ta taka step ɗin bakin part din ammi mayafinta ya zame daga kanta, bata tsaya gyarashi ba tunda tana ganin ta ƙaraso part ɗin, kallon gashin Maryam daya fito ta ƙasan daurinta kawai fareedah takeyi, ƙara sauri tayi domin zuciyarta cike take da son ganin fuskar me wannan dirarren jikin da kuma uban gashi haka baƙi sidik se sheki yakeyi yaji man kitso. da sallama na shiga falon, suna zaune dukansu da ammi da Aunty zuhura da umaimah, suka amsamun a tare har umaiman tunda taga ammi tana falon, amma batare data ɗagoba, zuhura data saki baki tana kallon Maryam tace, "wow Masha Allah, gaskiya Mamana kinyi kyau sosai, kin fito zam a amaryarki, sedai kash ɗan'uwana bayanan" murmushi kawai nayi na zauna a gefenta, araina nace _ai danshi nayi kwalliyar_ umaimah ta dago da kanta da sauri, jin bayanin zuhura ta kalli Maryam, sosai itama Maryam ɗin ta mata kyau, cikin kyashi da hassada tace, aranta, " _shegiyar yarinya se kyan tsiya kamar aljana_" ta tabe ta maida kanta kan wayarta, ammi na murmushi tace "ai dama ɗiyata akwai kyau Masha Alla.." shigowar fareeda ta katse mata zancenta, gaba-daya muka kalleta muna amsa mata sallamar datayi. idon fareedah na kan Maryam ta tsugunna ta gaida ammi da zuhura. suka amsa mata cikin fara'a, gaisheta nayi nima tunda daga gani ta girmeni, ta amsamun tana ƙara ƙuramun ido, umaimah ta tabe baki ganin kallon da fareedah takewa Maryam ta mike tana faɗin shigo mana kika zauna a nan, fareedah tana tafe tana satar kallon Maryam ta bi bayan umaimah zuwa ɗakinta, Aunty zuhura ta ajiye Abul dake hannunta ta tashi ta ɗauki wayar ammi tace, "na baro wayata a wajena, bari na miki hoto a wayar ammi" ammi ta mike ta shiga kitchen tana murmushi, gyara mayafina nayi Aunty zuhura ta fara mun hoton, tayi kusan kala biyar nace, "Aunty zuhura a barshi haka" zuhura tace, "Tom shikenan, amma bakiga yadda kikayi kyau ba, tasowa nayi na karba wayar na duba, hotunan na duba sunyi kyau sosai, bata wayar nayi nace, "yayi kyau gaskiya sosai" zuhura tace, "hmmmm, ainaso kanina yananan yaga wankannan, amma duk da haka bazan bari yayi missing ba seya gani a hoto" dariya kawai nayi na nufi kitchen dannaci abinci. ammi na ƙoƙarin fita da plate a hannunta na shiga kitchen din, nace "sannu ammi" tace "yawwa ya jikinnaki" nace "na warware" ammi tace, "Masha Allah, aina gani gakinan kinyi shar dake" murmushi nayi cikin jin kunya. ammi ta ƙara cewa, "jiya da daddare NOOR yakira kinyi bacci, dazuma ya kira kina part din zuhura" lumshe idona nayi bugun zuciyata na sauyawa jin ambaton farin cikinta da ammi tayi, ammi bata jira amsataba tace "idan kin gama cin abincin seki kirashi" nace "Toh" a hankali ina ƙarasawa cikin kitchen din, ammi kuma ta fice. A ɗakin umaimah kuwa bayan sun shiga, umaimah ta zauna a bakin gado tana bata rai batare da tacewa fareedah komai ba, Fareedah bata damu da yanda ta mata ba ta zauna a gefen ta tace, "kawata wace waccan dana ganta a falo kyakkyawa da ita, amma dai yar'uwar ammi ce ko?" Umaimah ta kebe baki tace "to uwar gane_gane, aidama naga tunda kika shigo kallonta kawai kikeyi" fareedah tace "ba dole na kalleta ba, naga mace ga kyau ga diri ga gashi ga daɗin murya, ga iya tafiya, ga wani kamshi datake zubawa me daɗi da sanyi ga...." Umaimah ta katseta cikin tsananin baƙin ciki, da fareeda tasan yanda yabon Maryam yake tafarfasa mata zuciya da bata yi a gabanta, tana hararar fareedan tace "to itace matar yaya NOOR ɗin" fareedah ta gwalalo idonta waje tace, "wanne yaya NOOR ɗin? ba dai wanda kike so ba?" Umaimah ta gyada mata kai tana haɗiyar wani yawu me ɗaci. Fareedah taja wani uban numfashi tace "wannan ƴar yarinya ɗanya shagab itace matar tasa?" Umaimah tace ",se kuma kiyi" fareedah ta jinjina kai a ranta tace _"dama yana da wannan tsaleliyar yarinyar me zeyi dake?"_ amma a fili se tace "ya maganar abunda nace miki kiyi dafatan dai kinyin?" Kafin umaimah ta bata amsa ammi ta shigo ɗakin da sallama, plate din hannunta ta ajiye a ƙasan gadon tana faɗin "fareedah ga abinci" bata jira amsartaba ta dubi umaimah tace, "ki kawo mata ruwa auta" umaimah tace "toh" fareedah na murmushi tace "Nagode ammi" bayan umaimah ta kawo mata ruwan ta ƙara dubanta tace "baki bani amsar tambayar dana miki ba" Umaimah ta kalleta cike da tsananin takaici tace "babu amsarne shiyasa banbakiba" "kamar ya? Ko baki gane akan me nake magana ba" cewar fareedah tana cire hijabin jikinta danya fara takura mata, umaimah tace "nagane mana, akan gurguwar shawarar dakika bani mana" fareedah ta haɗe rai ganin yanda umaimah take mata tunda tazo tace "wai mene hakane ina miki magana kina wani amsamun kamar ana miki dole, se wani babbata rai kike, idan dannazo gidankune sena tashi na tafi" ganin yanda fareedah tayi se umaimah ta ɗan saki fuska tace "ina cikin haushin abunda shawarar da kika bani ta haifarmunne, kin takuramun nayi harda kirana a waya kina ƙara jaddadamun, duk da banaso amma haka na daure na aikata ƙarshe ba'ayi nasaraba se uban mari dana sha" fareedah tayi ƙoƙari ta danne dariyar dake neman kufce mata tace "bangane me kike nufi ba? Shi yaya NOOR ɗinne ya mareki?" umaimah ta sauke wani numfashi tabawa fareedah labarin abunda ya faru, ta ƙara da faɗin, "tun daga ranar ban ƙara bari mun haɗu da shi ba, saboda bansan matakin daze dauka a kainaba, ga wata irin kunyarsa danake ji" fareedah zuciyarta fari ƙal kamar takarda, a ranta tace _"wawiya, haka zanta sakaki kina yin abunda ze kara tsanarki"_ afili kuwa setace "to mene danya miki haka, ai wannan shine alamun nasara" umaimah ta mata wani kallo na baki da hankali amma batace komaiba, fareedah ta ƙara gyara zama tace "mantawa nayi ban faɗa miki ba, ai dama su maza haka suke, dazarar ke kika fara nuna musu kuyi irin wannan harkar sai sun miki haka, karki wani damu danya miki haka, burga ce kawai ya miki da kuma ya nunu miki irin shidin na Allah ne, amma idan kika cigaba da masa zakiga ya dawo shima yana biye miki, wataranma shi ze nemeki da kanshi" umaimah jitayi kamar ta rufe fareedan da duka saboda haushin maganganunta, amma ta danne bacin ranta tace "kinga kibar fa wani dagon jawabi, aini anyi na farko anyi ƙarshe bazan kuma ƙara masa irin abinda na masa ba" fareedan ta kebe baki tace, "kin haƙura dashi kenan, duk da irin tarin soyayyar da kike masa?" umaimah tace "ban haƙura ba, amma na yanke shawarar danake ganin ita kaɗai zata fishsheni" fareedan tace "wacce shawara kika yanke?" Tace "na yanke shawarar zan faɗa wa ammi kawai ina sonsa, nasan...." Fareedah dataji tamkar ta caka mata mashi a kahon zuciya takatseta da faɗin, "lallaima umaimah, aiko wannan shine babban kuskuren dazaki tafka a arayuwarki, ki faɗawa ammi ta tursasashi ya aureki, kije a matsayin matar tushe mara daraja a idon namiji, ya samu damar wulakantaki kenan son ransa" umaimah da jikinta ya fara ɗan yin sanyi jin abunda fareedah ta faɗa tace, "kuma fa hakane fareedah nima da nace bazan faɗa mataba, amma nayi tunanin,nayi tunanin naga bani da wata mafita se hakan" fareedah tace "to karma ki soma faɗa mata wlh, indai zaki ɗauki shawarata, amma kiyi tunani sosai akan hakan" shiru umaimah tayi, ta rafka tagumi, fareedah kuwa se harararta take a fakaice, aranta tana cewa _"senayi duk yanda zanyi banbarki ki faɗawa ammi wannan maganar ba, dannasan dazarar kin faɗa mata magana ta ƙare, yanda ammi ta matsu kiyi aurennan zashi zatayi ya aureki, Ni kuma bazan taɓa bari kiyi aure kibarniba, balle kuma har ki auri wanda zuciyata takeso..."_ umaimah ta katse mata tunaninta da faɗin "ki sakko kici abincin karyayi sanyi" fareedah bata musa ba ta sakko daga kan gadon ta fara cin abinci....

Bayan na gama cin abincin na zauna a falo muka cigaba da hira da Aunty zuhura, wayar ammi na hannuna na ajiye ta a gefe ban kira yayanba shima kuma be kira ba, Ni duk a tunanina yau ze dawo, shiyasa rashin kirannasa be dameniba. Se bayan sallar magriba fareedah ta tafi, bayan ta gama ƙara dora Umaimah akan gurbatacciyar hanya da munanan shawawarinta, ita kuma dayake bata da wayo ta yarda da shawarwarinnata, fareedah dazata tafi haka taita kallon Maryam harseda Maryam ɗin ta tsargu. har bayan sallar isha'i wayar ammi na hannuna ina dakon kiransa, Ni kaɗai ce zaune a falon yanzu, Aunty zuhura ta koma part dinta ammi kuma na ɗakin ta umaimah ma haka, tunanin yaya kawai nake da kewarsa ta cikamun zuciya, ammi ce ta shigo falon, zama tayi a kujerar dake fuskantata tace "kin kirashi kuwa?" Buɗe idona nayi a hankali nace "nakirashi ammi, amma wayar taƙi shiga" ammi tace "sharrin network ne, nasan ze kira anjima, may be shi idan yakira ta shigo" mikewa nayi na miƙa mata wayar nace "ammi gashi zan koma part dinmu na fara jin bacci" ammi tace "yau ba'anan zaki kwanaba, ko kinbar jin tsoron yanzu?" Nayi murmushi kawai, ammi tace "kiyi kwanciyarki anan, gobe idan yadawo seki koma" _"gobe kuma_?" na maimaita haka a raina, komawa nayi kan kujera na zauna saboda wani irin zafi danaji ya ziyarci raina, daure abinda naji araina nayi a hankali nace "Toh ammi Allah yakaimu" ammi tace "ameen" kwanciya nayi akan kujera zuciyata na mun suya, Ni inanan kewarsa ta hanani sukuni, inata shirye-shiryen tarbarsa, shi kuma yanacan yana sha'aninsa hankali kwance, yacemun yau ze dawo ashe se gobe, nasan tunda ammi ta faɗa haka ne, kuma gashi har dare ma yayi bedawo ɗinba, ta tabbata se goben, tashi nayi na koma ɗakin ammi na rage kayan jikina na kwanta ko wanka banyiba saboda yanda nake jin zuciyata babu daɗi, na daɗe da kwanciya inata juyi bansan sanda bacci ya kwasheniba, yau ma seda maryam tayi bacci mustapha ya samu kansa ya kira ammi, yau kam beyi nauyin bakinba, ya tambayi ammi Maryam, ammi ta shaida masa tayi bacci. Washegari tunda asuba da mukayi sallah muka fara aikin snacks na tarbar yaya bisa umarnin ammi, danni duk shirin danake na dawowarsa na manta da batun yi masa abun tarba, bayan mungama aikin, na koma part dinmu, yauma banyi sanyaba na ƙara gyara part dinnamu fiye da jiya, bayan nayi sallar la'asar naci abinci na kwanta bacci saboda gajiyar dake addabar jikina.....

Mustapha yau tun safe ya gama shirinsa na komawa Jos, amma Daddy ya hanashi tafiya, su haidar ma se roƙonsa suke ya ƙara kwanaki kar ya tafi yau, shidai murmushi kawai yake musu, shikanshi bayason ya tafiyar ya barsu, amma dole ya tafi a yau, dan wata irin kewar Maryam ce take addabarsa wanda idan begantaba a yau akwai matsala, kwana biyun da yayi be gantaba beji muryartaba jinsu yake kamar wata biyu sukayi rabonsu da juna, wajen 12 na rana,faruq ya kaishi super market ya lodowa Maryam kayan zaki, su sweets da choculates da popcorn, su kuma su ammi turaruka yasai musu kala_kala, se can yamma Daddy ya barshi ya tafi da ƙyar, su haidar kamar zasuyi kuka, shima cike da kewarsu ya barosu, a Jet din daddy za'a maidashi, dama driver'n ammi already ya koma Jos tun jiya da safe... Maryam bata jima tana baccinba ta tashi, ƙara gyara gadon tayi sannan ta shige wanka, cikin wani haddadden less black colour an masa zanen fulawa me kyau da orange colour ta shirya, ɗinkin riga da skirt, ɗinkin ya zauna dass a jikinta yayi matuƙar yi mata kyau, hips ɗinta ya fito sosai ajikin skirt, daurinta ta kafa irin na zamani wanda ya ƙara kawata kyawun kwalliyar tata, ɗan kunne da sarka da zobuna da abun hannu haɗi da agogo masu kyau tasaka, ta bulbule jikinta da turaruka masu sanyin kamshi da daɗi, sosai yau tayi kyau fiye da jiya kamar ka saceta, har aka kira sallar magriba tana gaban madubi tana shiryawa, duk da fushi take da yayannata amma so take ta burgeshi sosai, seda aka shiga sallah ta bar gaban madubin ta shimfida darduma ta zira hijabi ta tada sallah dama da alwalarta tayi tun da ta shiga wanka. Mustapha se daf da magriba suka ƙaraso gida, hakan yasa be shiga gidanba ya bawa megadi ajiyar kayan tsarabarsa ya nufi masallaci...........✍️ Comments update 8pm Meson complete Whatsapp 08166674823

*ABIN DA KA SHUKA....!*

*BY* *ZEEY KUMURYA*

*7️⃣4️⃣*

*Bismillahirrahmanirrahim*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull