Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 54
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 54: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 54. Anyi bikin saleemat Lafiya, angama lafiya, kwana uku…
3,242 words
Anyi bikin saleemat Lafiya, angama lafiya, kwana uku akayi ana bikin, ran Friday akayi bridal shower, asabar kamu, Lahadi aka daura aure aka miƙa amarya gidanta, amarya da ango sun sha kyau ranar bukukuwa, kuma ango yayi ƙoƙarin kama guraren biki masu kyau daidai ƙarfinsa, kullum sai munyi waya da yaya, amma har yau Monday bai dawo ba, ayyuka sun sha masa kai, kullum saidai ya lallaɓani. ina zaune bayan sallar azhar ina cin dubulan da alkaki na garar saleemat wayata ta fara ringing, na dakko na duba ganin suna ammi yasani dagawa da sauri tare da yin sallama, ammi ta amsamun nace "ina wuni ammi" tace "lafiya kalau ɗiyata, ya taro?" nace "Alhamdulillah, yasu Aunty zuhura da mama?" tace duk sunanan kalau, yaushe zaku dawo ne?" nace "ammi har yanzu bai dawo daga Abujan ba" ammi tace "haka yacemun da mukayi waya, yace ayyukan da yawa" nace "haka yacemun nima, amma insha Allah wani satin zamu dawo" ammi tace "Allah yakaimu, ki gaida gwaggon naki da maman amarya" nace "zasuji insha Allah" mukayi sallama ta kashe wayar. kiran wayar yaya nayi bai dauka ba, na ajiye wayar cike da takaici, tashi nayi na dakko turarukansa daya bani, kullum sai na fesa su duka a jikina amma basa mun irin kamshin jikin yaya, kuma na masa complain yacemun da iya su kaɗai yake amfani, kwanciya nayi akan gado ina tunanin yaya, nayi missed komai nasa over, muryarshi, maganarshi, murmushin sa, kamshinsa, lallausar fatar jikinsa da nake lolewa kullum. na daɗe a kwance har saida gwaggo ta shigo tana faɗin, "Maryam kina d'aki a kwance, bazaki gidan amaryar bane? gashi can za'a tafi" na ɓata fuska nace "ehh" gwaggo tace "saboda me?" na mata shiru dan bazan iya ce mata kewar yaya ce take damuna ba, gwaggo tace "ai shikenan, ki tashi kici abinci to" nace "naci dubulan na koshi" gwaggo tace "ke, Maryam ki raba kanki da shegen cin zakinnan, sai kinje kin haifi ɗa mara cikakkiyar lafiya ko?" nace "gwaggo nifa banda komai, tun da nazo kike fadar haka" gwaggo tace "to ai duk wanda ya san ciki, yana kallonki ya ga mai ciki" nayi shiru amma ban ɗauki zancen gwaggo da mahimmanci ba, tunda nasan nidai bani da komai, har dare yaya bai kirani ba, ni kuma ban ƙara kiranshi ba, ga kewarshi na daɗa addabata, har kuka nayi. Har washegari bai kiraniba, kuma banga ya hau online ba, hankali na ya fara tashi, yau babu walwala kokaɗan na tashi, jikina ma kamar mai cuta, ko abinci ban ciba, dama kwana biyu bana iya cin abincin. Wajen sha biyu na rana umma ta aiko in shirya zamuje gidan saleemat nida kanwarta, banso zuwaba amma haka na shirya muka tafi, mun jima a gidan kuwa muna shan hira, dan sai bayan la'asar muka dawo.
Mustapha sai yau ya samu kansa ya baro Abuja, ayyuka sun sha masa kai ba kaɗan ba, yana abujanne amma hankalinshi gaba-d'aya yana gurin Maryam, yayi matuƙar kewarta, ji yake kamar baya tare da wani ɓangare na jikinsa, bai taɓa tunanin a rayuwarsa zai so mace irin haka ba, sati ɗaya da yayi basa tare, jinsa yake kamar wani mara lafiya, baccima dan dai ya iya sata ne, yake sake ci, gashi bazai iya barin aikin Daddy ya taho ba, amma da tuni ya dawo yaga ƴar matar tasa, jiya da yau baisamu kansa ba sai cikin dare, saboda yanda ya matse aikin yanaso yayi ya dawo, shiyasama bai samu ya kira Maryam ba, Bayan la'asar jirginsu ya sauka a Kano, yana zuwa gidan Daddy wanka kawai yayi, yayi Sallah, ko abinci bai tsaya ciba ya nufi gidan gwaggo. ina kwance akan gadon gwaggo ina kallon pics ɗinmu da mukayi ranar a mota, fitowata daga wanka kenan ko kaya bansaka ba. Mustapha ya turo yaro gidan gwaggo ya sanar da zuwansa, gwaggo tana zaune a tsakar gida tace aje ace ya shigo, ya shigo suka gaisa da gwaggo, gwaggo ta shiga masa godiyar kuɗin daya bata, shidai ya mata shiru, ta kwalawa Maryam kira, maryam bata jiba tana can duniyar begen *hearbeat* ɗinta, gwaggo tace masa ya shiga ɗakin, ya mike ya shiga. tsayawa yayi a bakin kofa yana kallonta, saboda ta juyawa ƙofar baya batasan da shigowarshi ba, Lumshe idona nayi jin kamshinsa da nayi missing na mun gizo a hanci, yanda kamshin yake ƙara ziyartar hancina yasa na buɗe idona tare da juyowa da sauri, gabana nane ya yanke ya faɗi, lokacin da nayi arba dashi tsaye a bakin k'ofa ya harɗe hannayensa a kirji, na rufe idona na ƙara buɗewa dan gani nake kamar gizo yakemun, wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyata dana tabbatar da shidinne, yayi mun murmushi tare da waremun hannayen sa, na tashi da sauri na ƙarasa na faɗa jikinsa, ya rungumeni tsam ajikinsa tare da sakin ajiyar zuciya yana faɗin "i missed you" na ɓata fuska sosai zanyi kuka nace "Ni ban yarda ba" yace "really" nace "bacin kaje ka daɗe, kuma jiya baka kirani ba, yauma haka" yace "kar kice haka, kinsan bazan taɓa kin kirankiba, duk a ƙoƙarin son nazo na ganki ne nayi busy" nace "to amma..." Ya katseni da faɗin "Am sorry, yanzu gani ai na dawo, mai kika ajiyemun?" na bar jikinshi ina murmushi nace "me kake so?" be amsa mata ba, sai bin jikinta da yayi kallo, kasancewar daurin kirji ne kawai a a jikinta, yana jin wani feeling ɗinta na bijiro masa, ya sauke numfashi ya shafi fuskarta yace "kinsan ke kaɗai nake so ai" na kwanta a jikinshi ina boye fuskata a kirjinshi, a hankali ya zare ta daga jikinshi yana fesar da numfashi yace "ki shirya, ina jiranki a mota zamu wuce gidan Daddy" nace "toh" ya juya ya fice dan idan yana kallonta zai iya yin abin kunya a gidan surukai. Cikin mintuna ƙalilan na shirya cikin wata doguwar riga mara nauyi irin me bin jikinnan, na ɗora hijabi akai, wayata kawai na ɗauka na fita tsakar gida nacewa gwaggo "gwaggo zamu gidan Daddy tare da yaya" gwaggo tace "to sai kun dawo, Allah ya kiyaye" nace "ameen" a cikin motar na samesa, yana latsa waya, ganin ta shigo ya ajiye wayar ya bita da kallo, na ɗan ɓata fuska nace "wannan kallon fa?" yace "naga kin ƙara kyau abinki" nace "hmmmm, nayi muni dai" zai yi Magana wayarsa tayi ƙara, dubawa yayi tare ɗagawa, bayan yayi sallama, an amsa yace "na ɗan fita ne, amma yanzu zan dawo" ya katse wayar, ya janyoni jikinsa, na lumshe idona nace "turarunka daka bani, basa mun irin kamshin jikinka" yace "kuma duka wanda nake amfani dasu na baki" nayi shiru kawai ina shaƙar kamshinsa da yake saukarmun da nutsuwa, ya kunna motar muka tafi.
Bayan fitar Mustapha zuwa gidan gwaggo ba jimawa sukayi sabani da su Aunty sukuma sun zo, a part ɗin mommy suka sauka, babu kowa a gidan sai masu aiki da faruq dake kula Sadiq, Daddy da su Haidar duk suna gurin aiki basu dawo ba. Ko zama basuyiba Aunty taja suhailat part ɗin Daddy suka duba jikin Sadik, suna zaune a falon Daddy, Aunty tacewa Faruq "Muhammad bai dawo daga Abujan bane? Munyi waya ɗazu yacemun before 5 jirginsu zai sauka, yanzu kuma naga 6 saura. Faruq yace "yadawo tun ɗazu, may be yana part ɗin shi yana hutawa" suhailat na jin haka ta miƙe ta fita ta nufi part dinnashi, Aunty batayi tunanin komai akan fitar suhailat ɗin ba, ta ɗauka part din Mommy zata koma, wayarta ta ɗakko ta kirashi, yace mata yafita amma gashinan zuwa. Muna tafe ina bawa yaya labarin bikin saleemat, har muka ƙaraso gida, beyi parking a parking space ba, har ƙofar part ɗinsa ya ƙarasa damu, suhailat dake tsaye a bakin k'ofar ɗinnasa tana jiransa, tana ganin mota anyi parking tasan shine, nufo gurin motar tayi da sauri, Mustapha ya buɗe murfin motar ya fito ya zagaya ya buɗewa Maryam ta fito itama, dai_dai lokacin suhailat ta ƙaraso gurin motar..........✍️ Comments update 8pm Meson complete Whatsapp 08166674823
ABUNDA KA SHUKA
kumurya*
*7️⃣9️⃣*
...........Wani wawan burki suhailat taja tare da waro idanuwanta duka waje, Mustapha yaga Suhailat sarai amma yayi kamar bai san da wanzuwar halittarta a gurin ba, ya kama hannun Maryam ɗinsa, tare rufe murfin motar. Suhailat ta haɗiye wani yawu mai ɗaci, ilahirin jikinta rawa yakeyi hannunta ta ɗaga da ƙyar ta nuna Mustapha cikin ƙara da rawar murya tace "yaya! wacece wannan?" gabanane ya yanke ya faɗi da naji muryar suhailat, domin bansan da ita a garin bama balle nayi tunanin ganin ta a gidan, riƙe hannun yaya nayi gam, ina kallonsa. Ya shafi gefen fuskata yana murmushi ba tare da yace komai ba, ya jani muka fara tafiya, Suhailat data sandare a gurin ta bisu da kallo, cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa, wani irin juyawa kanta yayi, lokacin da tayi katarin ganin Mustapha ya ɗauki Maryam cak a hannunsa kamar wata y'ar baby, lokacin da zasu haura kan step ɗin bakin part ɗinsa, dafe kanta tayi kirjinta na wani irin bugu, _"mafarki nakeyi ko gaske my life ne tare da wata mace, macen ma house girl ɗinmu, to me hakan yake nufi?"_ ta faɗi haka a fili cikin ƙaraji tana yarfe hannu, juyawa tayi tamkar mahaukaciya ta nufi part ɗinnasa, amma kafin ta kai har sun shige ya rufe kofarsa. bubbuga ƙofar ta hauyi tana faɗin "wlh bazan yadda ba, bazai yiyu ba, ina duniyar inganka da wata mace ba niba, wlh sai na kasheta!" ihu take tayi tana zuba surutanta, data gaji kuma sai ta bar bakin k'ofar ta kwasa da gudu ko nauyin cikin jikinta bata jiba ta nufi part din Daddy, a hanya suka ci karo da Aunty zata koma part din mommy, cikin tsawa Aunty tace "ke, baki da hankali kike gudu haka? kina lafiyar ki kuwa?" Suhailat ta tsaya tana zuba uban haki tare da fashewa da kuka tace "Yaya ne" Aunty tace "Muhammad?" Suhailat tace "Eh shine" Aunty bata ƙara cewa komai ba tayi gaba abinta, Suhailat ta bita a baya tana cigaba da kukanta, a falon Mommy aunty ta zauna tana faɗin "ke banason shirme, uban me Muhammad ɗin ya miki kika sani a gaba kina mun ihu haka, kuma me ya kaiki gurinsa ma?" Suhailat taja majina tace "Aunty tare fa naganshi da waccan kujakar yarinyar sun sauka a mota, kuma harda kama mata hannun" Aunty tace "ke mene naki a ciki to?" Suhailat da bata taɓa tunanin aure ne tsakanin Maryam da Mustapha cikin kuka tace "Aunty dole na damu mana, yaya fa shine wanda zan aura, kuma naganshi tare da wata, nasan duk dan ya k'untatamun yayi haka, Aunty dan Allah ki bashi haƙuri, nasan duk akan cikinnan yake mun haka" Aunty ta kalleta ta tabe baki kawai, Suhailat taci gaba da kukanta zuciyar na mata zafi da kuna, musamman idan ta tuna yanda mustapha ya ɗauki Maryam, a haukanta ita ta ɗauka duk abunda Mustapha yayi dan ya k'untata mata yayi dan tasan babu abunda zai haɗa Mustapha da Maryam wanda ya wuce aikatau, tasan abunda yayiwa Maryam ɗinma dan taji haushi yayi.
A kan gadon ɗakinsa ya dire Maryam, lumshe idona nayi inajin ba daɗi sosai a cikin raina ganin Suhailat da nayi, takalmin kafarshi ya cire tare da zare mata na ƙafar ta itama, hawa kan gadon yayi ya zauna tare da ɗora kanta akan cinyarshi, a hankali ya zare mata hijabin jikinta gami da hular kanta ya shiga shafa kitson kanta yana sakin ajiyar zuciya. Buɗe idona nayi a hankali cikin jin daɗin yanda yake shafamun kan nace "yaya" ya ɗan fesar da numfashi yana bin jikinta da kallo yace "uhm" shiru nayi bance komai ba, yace "menene?" na ɗan turo baki gaba nace "ba komai" tattaremun rigata ya farayi ta ƙasa, na riƙe hannunsa zuciyata na ɗan bugawa, cikin cool voice yace "ciremun zanyi, kisha iska naga ana zafi" na tashi zaune da sauri nace "banajin zafi ni" ya janyoni jikinsa ya rungumeni a kirjinshi, a jiyar zuciya na sauke me ƙarfi tare da kwantar da kaina a ƙirjinshi, hannunsa yasa ya zagaye bayanta yana sakin ajiyar zuciya, yana jin yanda ɗumin jikinta yake ratsashi ga wani ni'imtaccen ƙamshi da take mai daɗi da kwantar da zuciya, bai yi yunƙurin yi mata komai ba, duk da yanda yake cikin tsananin buk'atuwa da ita. kiran sallar magriba ya sashi zare ta daga jikinsa a hankali yana sauke numfashi, komawa jikinsa nayi dan bangajiba, yayi murmushi tare da ƙara zareta daga jikinsa, na kwabe fuska tare da turo baki gaba, kissing lips ɗinta yayi yace "sorry, muje muyi sallah" ya ƙarashe zancen tare da sauka daga kan gadon, na bishi da kallo kawai har ya shige toilet, alawala ya dauro ya fito, na sauko daga kan nima ina kallonshi nace "ka tahomun da alawa Please bakina ɗaci" ya dagamun kai kawai ya fice. Bayan an idar da Sallah ina kwance akan gado ina game a wayata ya shigo ɗakin, bakinsa ɗauke da sallama, na amsa masa ina dubansa, tun da muka shigo na fuskanci yanayinsa gaba-d'aya ya sauya kamar na me ɓacin rai, tashi zaune nayi nace "sannu da zuwa" yace "yawwa" tare da mikomun hannu, sakkowa nayi na kama hannunnasa, gyara mata hijabin jikinta yayi ya jata suka fice, part ɗin Mommy ya nufa dasu domin su gaida Aunty, na ɗan shagwabe fuska nace "yaya ina alawata?" yay mun banza, shikam tunda yaga suhailat yaji ransa yayi wani mugun ɓaci, yaso yayi control ɗin kanshi gurin boye ɓacin rannasa dan kar Maryam ɗin ta gane, amma ya kasa boyewa, ga abunda ya gani a jikin suhailat ɗin ya dugunzuma masa hankali, yana fatan Allah yasa idonshi gizo ya masa, dan har yanzu yana kallon suhailat a matsayin ƴar uwarsa ta jini, a sanin da yayiwa suhailat ko tumbi bata dashi cikinta a shafe yake, amma yau duk da hijabi a jikinta ya ga cikinta ya ɗan turo irin na masu ciki, runste idonsa yayi tare da matse hannun Maryam yana jin wani irin ɗaci a ransa, ƴar ƙara na saki ya buɗe idonsa da suka fara kadawa sukayi ja tare da sassautawa mata riƙon hannun. Aunty na zaune a falo ita kaɗai, Suhailat kuma tana ɗaki ta kulle kanta tana kuka da bori kamar sabuwar kamu, sai yanzu take takaici da bata damk'o Maryam ta mata dukan mutuwa ba, amma ta kudirce a ranta indai suka ƙara haɗuwa sai ta yabawa aya zak'inta. Inayin sallama na hango Aunty kwace hannuna nayi na ruga da gudu na rungume Aunty cikin murnar ganin ta ina gaisheta, Aunty na murmushi tace "Lafiya kalau Maryam, ya biki" nace "Alhamdulillah" Aunty tace "Allah ya sanya Alkhairi" na amsa da "ameen" Aunty ta dubi Mustapha suka gaisa, bayan sun gama gaisawar ya tashi ya fice, binshi nayi da kallo harya fice, sosai na hango damuwa a tattare dashi, sai naji zuciyata duk babu daɗi, na sauke numfashi kaɗan na dubi Aunty nace "Aunty baki zo da Aliya ba?" Aunty tace "Ehh, basuyi hutun school ba" nace "shiyasa da mukayi waya batacemun zaku zo ba" Aunty tace "ai bazata faɗa miki ba, tanata fushin nace bazan zo da ita ba" nayi murmushi kawai, muka ɗanyi shiru na wasu mintuna, ni inata baza su ido inga ta inda suhailat zata bullo, can dai na dubi Aunty nace "Aunty ina baaba Talatu kuwa?" Aunty tace "tana garinsu, kinsan masu aikin gidannan duk sun tafi, sai masu mazaje masu aiki a gidanne kawai suka rage, tun da babu mace a gidan" nayi shiru ina tuna Mommy da yanda ta zuba iko a gidannan, amma yanzu kamar ba'ayi ba, "ko tana inama oho?" Sai bayan sallar isha'i yaya yazo muka koma part d'insa, har na taho banga ko da gifatawar Suhailat ba, shikuma har lokacin fuskarsa babu walwala, a falo ya zauna nima na zauna a kusa dashi, cikin lallami da karyar murya nace "yaya nah" ya juyo ya kalleta yana jin ɓacin ransa na raguwa, nace "meke damunka?" ya girgizamun kai alamar ba komai, na marairaice sosai nace "dan Allah kayi haƙuri ka faɗamun, ko ni na maka wani laifin?" na ƙarashe zancen idona na kawo ruwa, janyota jikinsa yayi yace "karki kuka Please" na turo baki nace "to ka faɗamun meke damunka, tun ɗazu sai bata rai kake kuma kaki kulani" yayi murmushi yana kallon fuskarta yace "dagaske babu komai, ina tare da ke mai zai dameni" ganin ya saki fuskarsa sai naji daɗi sosai a raina ina kallon cikin idonshi nace "banason naga kana damuwa ko kaɗan" ya lumshe idonsa cikin jin daɗin maganarta yace "dagaske" nace "dagaske mana yaya" ya ƙara rungumeni a jikinsa, knocking din da akeyi yasashi sauketa ya tashi yaje ya buɗe Kofar, faruq ne hannunsa ɗauke da leda da yayi musu take a way na abinci da drinks, Mustapha ya karba ya dawo ciki, yunwa nakeji sosai dan rabona da abinci tun safe shima kaɗan naci, shiyasa yana kawo wa ba musu na zuba mana muka fara ci, da kanshi yake bani a baki, kuma duk lauma ɗaya idan naci sai yamun kiss a saman lips ɗina, wai dan nafi cin abincin da yawa, aiko naci sosai dan abincin yamun daɗi. Bayan mungama mukaje part din Daddy muka gaisheshi, Daddy ya dubi Mustapha yace "yaushe zaku koma gida?" Yace "Gobe insha Allah" Daddy yace "yaushe zaku dawo Kanon gaba-daya da zama?" yace "Bayan sallah kamar da sati biyu haka" Daddy yace "Allah ya kaimu, itama ammin taku zata dawo Kanon da zama insha Allah" Mustapha ya murmusa kawai baice komai ba, bamu jima sosai ba muka dawo part ɗinsa, wanka kawai mukayi muka kwanta.
Aunty ce zaune a falon Daddy ita da Suhailat data taso ta da ƙyar, Daddy kawai ido ya zubawa Suhailat gumi na yanko masa ta ko'ina a jikinsa, idanunshi sun kada sunyi jajur saboda tsananin ɓacin rai da kunar zuciya bayan Aunty ta gama rattabo masa jawabi akan cikin dake jikin Suhailat, Aunty ta kwantar da murya ganin yanayinsa tace "kayi haƙuri yaya, kada ka sanya damuwa a ranka har wani ciwon ya kamaka, bawa baya taɓa kaucewa ƙaddararsa, wlh nima ba ƙaramin tashin hankali na shiga ba a lokacin dana gane tana da cikin, na kulle kaina a daki ni kaɗai naci kuka na, daga baya kuma na fawwala wa Allah komai." Daddy ya sauke numfashi kawai baice komai ba, tsana da danasanin auran Mommy suka ƙara cika masa zuciya, domin duk lalacewar da suhailat tayi ita ta ɗora ta akan hanya, itace silar lalacewar tata, ya dubi Aunty yace "nama rasa me zance sauda, jin abunnake kamar almara ƴar ɗan'uwa guda ɗaya jal da ya barmun amanar ta itace take ɗauke da cikin shege" sai kuma yayi shiru yana maida numfashi, itadai Suhailat tana durk'ushe tana kuka, Aunty ta danne tata damuwar cikin kwantar da murya ta shiga bawa Daddy baki, ganin yanda ya damu matuƙa fiye da yanda tayi tunani, da ƙyar ta samu Daddy'n ya sassauta damuwarsa yace "shikenan Sauda, babu yadda zanyi nasan wannan wata jarrabawar ce daban, kuma zanyi ƙoƙari wajen ganin na cinyeta, Allah ya bata lafiya ita da abunda ke cikinnata ya kuma raba lafiya" Aunty tace "ameen" Daddy ya dubi Suhailat yace "kafin ku koma kadunan, ki turomun wanda ya miki cikin zamuyi magana" yana gama faɗar haka ya tashi ya shige ɗakinsa, dan Kaɗaici kawai yake buƙata a halin yanzu, Aunty taja Suhailat suka koma part ɗin Mommy, Suhailat ta tambayi Aunty ina Mustapha ya kai sau biyar amma Aunty ko sau ɗaya bata ganka mata ba, ta mata banza.