Kenza eBookz

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 55

Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 55

Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 55: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 55. Washegari misalin ƙarfe goma da ƴan mintuna na safe,…

3,078 words

Washegari misalin ƙarfe goma da ƴan mintuna na safe, mustapha ne kwance akan doguwar kujera yana kallon Maryam data ke ta ɓata rai tana turo baki, tun bayan da suka karya tace ya kaita gurin Aunty shikuma yaki, saboda yasan bacci takeji dan jiya be barta tayi wani baccin kirki ba, ya rarrasheta akan tayi baccin yanzu kona 1 hour ne amma taki, shikuma yaƙi barinta taje gurin Aunty'n, shine ta kwace wayarsa ta matsa daga kusa dashi ta koma wata kujerar ta zauna, shikuma ya tasata a gaba da kallo yana murmushi, dan kallonta kaɗai ma ya isa sanyaya masa zuciya, wayarsa dake hannuna nace ta fara ƙara, dubawa nayi naga number ce babu suna, k'in bashi nayi harta katse aka sake kira, ya tashi zaune tare da faɗin "a bani wayata mana, tunda ana kira na ko" na turo baki gaba na tashi na kai masa, ya karbi wayar tare da janyota ta faɗa jikinsa ya matse gam yanda baza ta iya tashi ba, nima banyi yunƙurin tashin ba nayi luf a jikinsa, d'aga wayar yayi ya kara a kunne, Muryar mace yaji kuma kamar yasan muryar, daga ɗaya ɓangaren aka ce "Ranka ya daɗe, dafatan ka tashi lafiya" yace "lafiya" a taƙaice, ta ƙara cewa "nasan har yanzu baka gane da wa kake magana ba, kana magana da P.A dinka ce" yayi shiru kamar yadda nayi shiru ina sauraren sautin muryar mace da naji, can yace "Ok nagane" P.A tayi murmushi cikin jin daɗi tace "na kira in gaishe kane, in maka ya jiki da kuma jajen abubuwan da suka faru" cikin mamakin yanda akai P.A tasan abubuwan yace "Ok thank" tare da kashe wayarshi. na d'ago kaina nace "dawa kayi waya?" yayi wani munafukin murmushi yana kashemun ido yace "budurwatace" nace "wacece ita?" yace "nace miki budurwa tace, kuma kinsan me?" nayi shiru ina ɓata fuska sosai, ya ƙara kashemun ido yace "tana sona sosai, kullum tana cemun I LOVE YOU" na fashe da kuka ganin da gaske yake, har wani nishaɗi yake yi yana faɗamun wai tana sonshi" yace "menene kuma na kuka, tambayata fa kikai na faɗa miki" cikin kuka nace "to sai ka faɗamun kuma, ba sai kacemun watace da banba amma ba budurwa kaba harda wai...." na kasa ƙarasawa naci gaba da kuka na yace "sai nai ƙarya kuma, a'a gwara dana faɗa miki gaskiya, budurwace tana sona sosai kamar ranta, ko da yaushe tana cemin I LOVE YOU" ya ƙarashe zancen da kissing lips ɗinta yana murmushi, kuka nasa sosai na shiga dukan kirjinsa ina kukan nace "ai nima ina faɗa maka" yace "baki taɓa faɗa mun ba ni" na masa banza na cigaba da kukana, ganin yanda take kukan bil haqqi ya shiga rarrashin ta, taƙi saurarensa, bakinta ya buɗe a hankali ya zira mata lips ɗinsa, da sauri na cafka na fara tsotsa kamar jariri na shan nonon uwarsa ina sauke ajiyar zuciya, inajin daɗin sucking lips ɗinsa sosai yanzu, sai inji kamar na samu sweet, ya sauke ajiyar zuciya jin tayi shiru ya shiga shafa bayanta a hankali, sai da na tsotse masa lips ɗin son raina sannan na cizeshi kaɗan, ya zare bakinsa da sauri daga nata yana sauke numfashi, na kwantar da kaina a ƙirjinshi ina turo baki gaba, ya leko da kansa wajen fuskata yace "sweetheart harda cizo kuma" nace "um" yace "da zafi fa" nakai finger na kan lips ɗinnasa nace "sannu" yace "yawwa" tare da sharemun hawayen fuskata, ya dagoni daga jikinsa yace "muje mu gaida Daddy da Aunty, tunda kinki yin baccin" na tashi na shiga ɗaki na dakkona hijabina na fito, ya mikomun hannunsa na mak'e kafada naƙi riƙe masa, ya matso kusa dani yace "to zo in ɗaukeki" na ƙara maƙe kafad'a, yace "goyo fa" da sauri na d'aga masa kai, yayi murmushi ya tsugunna yace "hau" na haye bayansa ina dariya yace "shikenan" nace "Ehh" ya tashi tsaye yana faɗin "wash kina da nauyi fa" na masa gwalo ina dariya, a bakin k'ofar part d'in ya sauke ni yana maida numfashi, yace "kin sagarmun da baya" nace "sannu, amma goyon da daɗi zaka kuma mun?" ya murmusa yace "zan dinga miki kullum ma" cikin jin daɗi nace "Nagode" ya kama hannuna muka fice, part ɗin Mommy muka fara zuwa muka gaida Aunty, aunty kallon Maryam kawai take yanda taga ta ƙara dashewa tayi fari ga nishi da takeyi kaɗan_kaɗan irin na masu ciki. Bayan sun gaida Daddy ya ɗauketa suka nufi gidan gwaggo.

Mommy Tasha cinya sosai, daga ciwon kannan ya koma mata cuta mai tsanani, Binta kawartace ta samo mata mai kula da ita tana biyanta, Mommy kamar bazata rayu ba, sai a satinnan ta fara samun sauƙi, ta rame sosai tayi baƙi ga wasu kurashe manya duk sun fito mata a jikinta, yau ta tashi da jikinnata da kwari babu laifi, tun safe ta shirya zasu fita ita da Binta, duk da har yanzu ba wai lafiyar ta isheta bane amma tsabar masifa zata fita, tana ciwonne amma hankalinta gaba-d'aya yana kan Daddy da Mustapha akan mummunan kudirinta akansu, yanzu fitar daza tayima zataje tayi visa ne na zuwanta London neman Mustapha, tana ta jiran Binta zata rakata amma shiru_shiru bata zoba, gashi tana ta kiran wayarta bata shiga, ganin har 12 ta wuce ta ɗauki mukullin motarta tayiwa mai jinyarta sallama ta fice dan zuwa gidan Binta. Mustapha suna zuwa gidan gwaggo basu wani jimaba Maryam ta kwaso kayan ta ta musu sallama, Mustaphama ya shiga yayi wa gwaggo sallama shima, har gidan umman saleemat ma ya shiga ya mata Allah ya sanya Alkhairi, sannan suka tafi. A titin commissioner road Mommy tazo zata karya kwana, su sukuma su Mustapha suna ɗayan hannun an tsaidasu, kamar ance Mommy ta juya, tana juyawa tayi katarin ganin Mustapha kasancewar glass din motar tasu a zuge yake........✍️

Idan naga Comments akwai shafin karshe 10pm Meson complete Whatsapp 08166674823

*ABIN DA KA SHUKA....!*

*8️⃣0️⃣*

*Bismillahirrahmanirrahim*

.........Cikin tsananin kad'uwa Mommy ta bisu da kallo kirjinta na mahaukacin bugu, gaba-d'aya ma ta manta tuk'i take a tsakiyar babban titi, gani take tamkar mafarki take zata farka ba Mustapha'n ta gani ba, mutumin da take nemansa ruwa a jallo, horn d'in da ake ta danna mata ya dawo da ita cikin nutsuwarta, tuk'i tacigaba dayi slowly tana waigen su Mustapha, ganin anbasu hannu sunyi gaba yasata juya motarta da sauri a ƙoƙarin ta na zagayowa ta bi bayansu, wata Babbar Mota ce ta danno kai, tunda titin yana tafiya ne a hannu ɗaya, Motar baisan da motar Mommy ba, tunda yasan yuturn akeyi idan mutum zai zagayo, a guje ya taho hakan yasashi yin ciki da motar Mommy tayi tsalle ta jirkice a tsakiyar titi.

Mai motar bai tsayaba yayi gaba abinsa da mugun gudu, tsayawa mutane suka fara yi na cikin Mota suka fara fiffitowa da tsirarun masu tafiya a ƙafa, aka fara ƙoƙarin ceto ran Mommy, sai da aka ɗaga motar sannan aka samu aka zaro ta cikin mawuyacin hali, jini na zuba a jikinta, wani bawan Allah ne yayi shahada yace a sata a motarsa, aka nufi Asibin Nasarawa da ita.

Sai da suka biya ta super market suka yiwa su ammi tsara ba sannan suka koma gidan Daddy, anayin sallah azhar Mustapha yace su tafi, Maryam bata soba tayiwa Aunty sallama suka tafi, Daddy kuwa sai da ya rakasu har airport. Suhailat bata samu bacci ba a daren jiya, sai da garin Allah ya waye baccin yayi gaba da ita, har su Maryam suka tafi bata tashi ba, Aunty tanata buga mata kofa tun safe ko dan ta tashi ta karya amma taƙi tashi, sai bayan tafiyarsu Mustapha ba jimawa tatashi, Aunty tana daki tana waya da Abban su Aliya, Suhailat ta shiga ta sameta, zama tayi ta jira Aunty'n ta gama wayar, Aunty ta dubeta fuskarta babu walwala sam tace "Sai yanzu kika ga damar tashi?" Suhailat tace "Banyi bacci bane jiya, sai da safe na samu ya ɗaukeni" Aunty tace "meya hanaki baccin?" Suhailat tayi shiru, Aunty ta tab'e baki tace "kije kiyi ta sa damuwa aranki, tun kina yar ƙaramarki kijawa kanki wani ciwon" Suhailat tana hawaye tace "Aunty wlh inason yaya sosai, kuma kun sani, amma shi naga yanzu ya dena sona baya tani, ko nemanama bayayi" Aunty tace "amma tun kwanaki da kika damu danki kika ƙi ci kika ƙi sha nace miki kibar wata maganar yaya sai Allah ya saukeki lafiya ko?" Suhailat tace "Aunty wlh bazan iya ba, ni kaɗai nasan yanda nake ji a raina, dan Allah ki rokeshi ya dawo mu cigaba da rayuwar mu kamar da" ta ƙarashe zancen tana fashewa da kuka. Aunty tayi shiru cikin jin tausayinta, tana ji a ranta da zata iya da tasa Mustapha ya aure ta, amma tasan idan tayi haka tayi rashin adalci, dan Suhailat sam bata dace da kamilin namiji irin Mustapha ba, sai dai idan shi ya furta yana sonta da kansa. Aunty ta dubeta da kyau tace "Suhailat Muhammad ɗin da kika sani yanzu ba na da bane, yanzu rayuwarsa ta canza zaiyi wuya ya iya auranki, musamman idan yasan abinda kika aikata" Suhailat ta d'ago da sauri tana kallon Aunty tace "Aunty bangane rayuwarsa ta sauya ba, kuma dama baisan ina da ciki ba? to Meyasa yakemun haka? Ko akan abunda Mommy ta masa ne?" Aunty tace "ko ɗaya ba akan abinda Aunty Atika ta masa bane, Mustapha yanzu yana rayuwa ne cikin nutsuwar da kwanciyar hankalin da ya rasa a da, Muhammad yayi gamo da mahaifiyarsa, kuma da ita yake rayuwa a Jos sannan kuma a halin yanzu yana da mata wato Maryama dan haka....." mikewa tsaye Suhailat tayi Zuciyarta na wani irin bugu, ilahirin jikinta ya ɗauki rawa kamar an jona mata shocking, so take tayi magana amma ta kasa, wata ƙara ta kwalla tare da zubewa ƙasa a suma, Aunty dake kallonta tayi kanta cikin tashin hankali tana kiran sunanta tare da jijjigata, Fahimtar da tayi suma tayi yasata tashi ta ɗauko ruwa mai sanyi a cikin fridge ta shiga shafa mata a fuska zuwa wuyanta, Suhailat taja wani dogon numfashi tare da buɗe idonta da suka matuƙar yi mata nauyi a hankali ta saukesu akan Aunty, Aunty cike da tsananin tausayawa tace "sannu Suhailat" Suhailat ta fashe da wani irin kuka hawaye masu ɗumi suna kwaranyo mata, cikin kukan tace "Aunty dan Allah dagaske kike yaya yayi aure da waccan yarinyar?" Aunty tace "Ehh, Suhailat idan zan baki shawara ki ɗauka ki cire Muhammad daga ranki tun wuri, dan yanzu ba take yake ba" Suhailat ta yunkura ta tashi zaune numfashinta na fita da kyar tace "Aunty bazan iyaba, wlh bazan iya jurar rashinsa ba a rayuwata, komai zai faru sai dai ya faru amma wlh sai na aureshi, aida yana sona sai dai in shiga tsakaninmu a kai, a yau ba a gobe ba sai na bishi har Jos ɗin" Aunty data saki baki tana kallonta tace "Tun farko Suhailat ke kika cushi kanki, da'ace baki ɓata rayuwarki da yawon banza ba, dana san tabbas Mustapha ke ze aura" Suhailat bata bi takan maganganun Aunty ba ta cigaba da maganganunta na hauka cikin ihu kamar zautacciya, Aunty ta shi zata fita ganin abunnata harda iskanci, kafin ta kai ga fita faruq ya shigo a gigice yana faɗin "Aunty! Aunty!' a dan ruɗe Aunty tace "lafiya faruq kake mun wannan kiran, ko wani abu ne ya samu Sadiq ɗin?" Faruq cikin tashin hankali yace "yanzu wani freind ɗina likita a Nasarawa hospital ya kirani, wai an kawo Mommy sunyi accident kuma tana cikin mummunan hali" Aunty tace "Subhanallah dama Aunty Atikan tana ƙasar nanne?" Yace "ban sani ba Aunty, dannima tunda tabar gidannan rabona da ita" Aunty ta dafe kanta tana kiran "innalillahi..." Suhailat ma shiru tayi tana sauraren faruq, Aunty ta dubeshi tace "kaje asibitin yanzu da sauri, ni zan zauna gurin Sadiq kafin yaya ya dawo, sai mu taho asibitin muma, ka kira su Haidar ka sanar musu" ya amsa da toh sannan ya fice, Aunty tabi bayanshi zuwa part din Daddy domin kula da Sadiq zuciyarta cike da jimanta accident din Mommy, suka bar Suhailat nan zaune zuciyarta na mata wani irin zafi da k'una, yanda takeji a ranta a yanzu idan tayi arba da Maryam zata iya kasheta, ko kaɗan labarin accident d'in Mommy bai wani daga mata hankali ba, ita damuwarta kawai akan Mustapha ne. Aunty tana zaune a falon Daddy cikin damuwa Daddy'n ya dawo, miƙewa Aunty tayi fuskarta na nuna tsantsar damuwa tace "yaya kaji wai Aunty Atika tayi accident" Daddy cikin rashin damuwa yace "when" Aunty tace "yanzu faruq ke faɗamun yama tafi asibitin" Daddy yace "Allah ya sawwake ya kiyaye gaba" yana ƙoƙarin hayewa sama Aunty ta tsaidashi da faɗin "haba yaya, yanaga kana ƙoƙarin shigewa, kamata yayi ai ka tafi asibitin kaima, amma naga ko damuwarka baka nuna ba" Daddy yace "damuwar me kuma zan nuna akan macen data zama silar sanyani cikin tashin hankali, macen da babu Alkhairi kwata_kwata a tattare da ita sai sharri, macen da..." "Haba yaya, abinda ya faru ya riga daya wuce, kome tayi dan kanta, aiko ƴaƴanta da suka gujeta ya isheta ishara, kai kuma ko dan darajar ƴaƴan dake tsakanin ku kaje ka dubata, dan faruq bakaga yanda hankalinshi ya tashi ba, kuma kasan da yafi kowa jin takaicin abinda ta aikata yafi kowa yin burus da ita, amma dake uwa uwa ce yanajin tayi hatsari hankalinshi ya tashi bakaga ba, a gigice yazo ya faɗamun" Daddy ya sauke nannauyen numfashi yace "shikenan bari naje driver ya kaini" Aunty tace "ko kaifa, Allah ya kiyaye sai munyi waya naji jikinnata, nima inna gama abunda nake zanzo asibitin" Daddy ya amsa mata tare da ficewa daga ɗakin, Aunty kuma ta shiga kitchen ta fara kiciniyar dafa abinci. Mun sauka lafiya a garin Jos, Part ɗinmu muka wuce direct muka ajiye kayanmu, kwanciya nayi akan gadon ɗakinsa ina maida numfashi, ya dubeni yace "taso muje part ɗin Ammi" na daure na tashi ba dan nasoba saboda naji daɗin kwanciyar, ya kama hannuna muka fita, muna tafiya nace masa "kuma yaya bamu biya ta kadunan ba" yace "to ba Aunty'n tana Kano ba" nace "hakane fa" ammi ta tarbemu cikin tsananin murna da farin ciki, muna munyi murnar ganinta dan munyi kewarta ba kaɗan ba, abinci kala_kala ta mana na tarbarmu, bayan mun gama cin abincin yaya ya fita ni kuma na zauna muna shan hira dasu ammi da Aunty zuhura, sai dare na koma part ɗinmu.

*BAYAN SATI D'AYA*

Duk wata alama da zata nuna Maryam tana da shigar ciki ta bayyana, amma ita da Mustapha basu gane ba, kasancewar basu san takan abun ba, bata da aiki yanzu sai kwanciya dan ko a zaune take sai ta dinga jin jiri, ga kwadayin dare data fara, rigima da shagwaba kuwa harda na siyarwa dan yanzu har ammi yi mata take. Mustapha sun koma Kano shida ammi sun dubo jikin Mommy, wadda ke kwance rai a hannun Allah bata masan inda kanta yake ba, ta samu karaya a hannu da kafa duka na dama, sai kuma buguwa da tayi akai da ƙananun ciwuka abun dai babu kyan gani, jikin Sadik ya fara sauƙi tunda yanzu har yana gane inda kansa yake, amma dai duk da haka sai dai a kwantar a tayar. Suhailat sosai ta tada hankalinta a cikin satinnan, bata da aiki sai kuka ko abinci bata iya ci sai Aunty ta tilasta mata take dan watsawa kaɗan, tayi baƙi ta rame duk ta fice daga hayyacinta, kamar ba ita ce wannan uwar gayun ba, to ga ciki gashi tasawa kanta damuwar abunda bazata samu ba, hakan ya haifar mata da zazzaɓi mai zafi da ciwon kai, Aunty tayi lallamin tayi faɗan amma duk a banza, ƙarshe ta zuba mata ido tace taje ta kashe kanta ita bazata iya ba, tunda ita bata da tawakkali.

Misalin ƙarfe goma da ƴan mintuna na dare, ina kwance akan gadon yaya inacin dabino, shi kuma yana ƙasa yana operating system, isata dabinon yayi na tashi na ajiyeshi akan bedside, sakkowa nayi na zauna a kusa da yaya ina kallon fuskarshi, a hankali ya dago ya zuba mata narkukkun idanunshi, na matsa jikinsa sosai na kwantar da kaina a kafaɗarsa, ya shafi fuskata yace "har kin gama cin dabinon?" Nace "ehh, ya isheni" wuyanta ya taɓa yace "jikinki da zafi fa jewel" na lumshe ido bance komai ba sai ƙara manne masa jiki da nayi, a hankali nace "yaya zanci kaza gashashshiya" yace "kaza kuma a darennan" na ɗan turo baki nace "uhm" ya shafa ɗamamman cikinta yace "baby kin koyi ci da yawa, yanzu duk abubuwan da kika ci baki k'oshi ba?" cikin shagwaba nace "nidai dan Allah yaya kasiyomun" yace "ki bari gobe idan Allah ya kaimu, yanzu kinga aiki nake kuma dare yayi" nace "a'a nidai yaya ina son ci sosai, idan banci ba bazan iya bacci ba" ya sauke numfashi yace "shikenan ɗauko hijabinki muje" na tashi da murnata na saka hijabi muka tafi, da ƙyar muka samu gurin sai da kazar tunda har yau shima ba gama sanin garin yayi ba, guda uku ya siyo mun yace inta ci, tun a Mota na fara ci dan ina ganin kazar yawuna yayi wani irin tsinkewa, baifi rabin ɗaya ba naci naji na k'oshi, adana abata nayi nace da safe zanci, ina gama ci nasha ruwa na kwanta bacci a jikin yaya, cikin dare cikina yace baisan zance ba ya dinga murdamun, tun inajin abun kaɗan_kaɗan har ya farkar dani daga bacci, juyi na shigayi akan gado ina addu'a, wani irin amai naji yana tasomun da gudu na tashi nayi toilet hakan ya farkar da yaya, amai na shiga kelawa, sai da na amayar da kazarnan tass yaya na zuba mun sannu, ya taimakamun na wanke bakina da fuskata ya dawo dani d'aki, shi kuma ya gyara toilet d'in, da nayi aman naji daɗin murdawar cikin harna samu bacci ya kuma ɗaukeni. Sai dai me kafin asuba na tashi aman ya kai sau huɗu, sai da na amayar da duk wani abu da naci kafin na kwanta, duk jikina yayi laushi ga wata kasala gami da jiri da suka lullubeni, Mustapha hankalinsa idan yayi dubu ya tashi, tausayinta gaba-d'aya ya gama cikashi, gashi sai kuka take masa sannu kawai yake zuba mata kamar shima zai mata kukan, yana jin tamkar ya dawo da ciwon jikinsa, ruwa ya samu ya tofa mata addu'a ya bata tasha, Allah ya taimaka aman ya tsaya ta samu bacci ya ɗauketa da asuba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull